Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa godiya Shamsuddeen yace babu komai ai duk yiwa kaine, duk dai ta kira wanda tasan nata ne duk ta sanar musu cewar ta samu aiki a office d'in mijinta. Fa'iza kuwa dama suna hanya za'a dawo da ita gida saboda haihuwa yau ko gobe wanda da kyar Sahal ya bari sai da Ummi ta cicci masa sannan ya yarda akan cewar da tayi arba'in zata koma.

Shima Yazeed da Afrah ta kasa shi wato aka aura mata wani prince dole tasa yanzu zai dawo kan Nawal, yana fitowa daga office d'in Shamsuddeen bayan yaga irin kaunar da suke bugawa ya zauna a office d'insa tare da zaro wayarsa yana kallon numbers d'in Nawal, tunani yake ya buga ko ya barshi? Sai dai kawai ya daure zuciyarsa domin yasan sai ta cab'a masa magana yau. Kundunbala yayi wajan dannawa tare da karawa a kunne yana faman lumshe idanunsa a haka yaji tayi picking cikin izza tace dashi.

“Ya akai?”

“Ke! Baki da kunya ni kike yiwa irin wannan tambayar?”

“Gaskiya Yaya Yazeed ina gurin saloon bansan raina ya b'aci.”

“Dallah can yi min shiru, a wannan kwaikwaidon zaki wani ce saloon kikaje, kuma karki kashe min waya domin magana nake son muyi dake.”

Wayar ta gallawa harara kai kace shine a wajan kafin ta yatsina tayi masa banza ai yasan tana jinsa.

“Kina jina ko? So nake idan kin koma gida ki samu Abbie kice masa ni kike so, insha Allahu gobe zan turo kud'in auren mu.”

“Kut! Aure? Wazaka aura?”

“Ke, nace ke zan aura so what?”

“Tabd'ijam toh ai ba rasa miji nayi ba bare kazo min da gadara irin wannan.”

“Nidai na gaya miki kije kice musu ni zan kawo kud'in aure idan kuma kika bari naje da kaina ranki ne zai b'aci.”

Katse kiran yayi Nawal tabi wayar da kallo tana mamakin tsantsar son girma irin na yaya Yazeed, da ace ya gano cewar tana sonshi da kila wulak'ancin da zai dinga yi mata sai yafi wannan, shi da alama ta karfi zai aureta ita kuma ba zata yadda ta nuna masa so ba har sai ya furta mata domin taga irin wahalar dasu Aliya suka sha wacce bata fatan ko a mafarki tayi irinta. Koda ta koma gida bata gayawa kowa ba haka ta share maganar taci gaba da hidimominta kawai. Su kuma can suna ta shi gidan Baba Suleiman suka nufa suna zuwa gwaggo Talatuwa ta shaida musu cewar Umma bata nan taje kasuwa su kuma su Fa'iza suna sauka ta fara nakuda hakan yasa suka wuce aka kaita asibiti, lemulan da Shamsuddeen ya kawowa gwaggo su kawai suka ajiye mata suka wuce asibiti, nan suka tarar da aunty Yagana dasu aunty Hawwa kanwar Ummi mahaifiyar Sahal sai shi kanshi uban gayyar wato Sahal wanda gabaki d'aya yabi ya rud'e musamman da yaji tun a mota Fa'iza take ta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.

Da sauri Aliya ta karasa wajan aunty Yagana tana tambayar ta yadda ake ciki, tace mata suyi ta addu'a shima Shamsuddeen can yaje gurin Sahal yana ta tausar zuciyarsa, sai gashi kamar daman jiransu Aliyar ake yi nurse ta fito hannunta d'auke da sunkucecen jariri a cikin towel yana ta tsorar babban yatsansa. Murna farin ciki kuwa ba'a magana sai tambayar uwar suke ana cewa lafiya lau shirya ta ake yi idan an gama za'a kaita d'akin hutu sai suje su ganta. Sahal sai dashare baki yake yi aka bashi ya yiwa yaron huduba sannan ya bawa Aliya shi wacce bakin yak'i rufewa, da sun had'a ido da Shamsuddeen zai kanne mata ido ita kuma sai ta yi murmushi tana girgiza. Sai da aka gama shirya ta tsab sannan aka kaita d'akin hutu su Aliya suka bita sai dariya take kamar ba itace ta gama kukan mutuwa zata yi ba.

“Sissy! Innalillahi yau gamu da d'an kanmu daman zaki iya haihuwa?”

Duka Fa'iza ta kai mata tana murmushi kowa na gurin yana dariya shi ko Shamsuddeen toshe baki yayi jin irin maganar da Aliyan keyi, kai daga ji kasan da gaske take maganar bawai wasa ba. Sai dare sannan aka sallame su daman tun d'azu Shamsuddeen ya tafi da nufin zai dawo ya tafi da ita. Ana idar da sallar isha'i yayi parking k'ofar gidan Baba Suleiman aka yi masa iso ya shiga, zazzaune ya tarar dasu suna ta hira ga 'yan barka makota suna shigowa yace da Aliya ta tashi su tafi, sam bata yi musu ba amman fa taso ya barta susha hira sai dai gobe zata dawo, suka tafi a mota sai tsiya yake yi mata yana cewa.

“Yarinya kema damun koma zan ajiye miki nawa babyn a cikin ki.”

“Kaji ka, ai kai rago ne shi wancan ai da zafinsa ya ajiye.”

“Okay nine rago ko? Zamu koma gida zaki bayani.”

Tayi dariya harda tafa hannaye kafin ta kallesa cikin shauki tace.

“Habibi wallahi ji nayi ina ma d'an mu ne, ni ban san ma haka nake da son yara ba sai yanzu da naga na Sissy, kai ya bani sha'awa wallahi, kasan me?”

“A'a sai kin fad'a.”

“Da kyar ta bashi nono, wai wallahi bazata fito dashi ba.''😂

Tayi maganar tana kuma sakin dariya kamar yadda tayi a lokacin da ana diramar, shima Shamsuddeen ya kyalkyale da dariya, ita kuwa Aliya ta kasa denawa taji shamsuddeen yace.

“Amman ai tana bawa Oga Sahal ko?''🤭

Aliya ta kuma fashewa da dariya tana rike ciki tace dashi.

“Wallahi Habibi kamar kana gurin haka gwaggo Talatuwa tace, dan kaniyar da zaki hanashi abincinsa ai kya bawa kato yayi ta dumulmula.”

Baki d'aya suka saki dariya da haka ya k'arasa dasu wajan wani mai gashin nama ya siyo musu sannan suka karasa gida. Soyayya suke mai cike da burgewa komai tare suke yi sun shaku iya shakuwa a cikin kankanin lokaci. Da safe shi kadai ya tafi wajan aiki ita kuma data shirya ta wuce gidan su a ranar ma su Nawal su Husnah su Nour su Amina Modu duk sunje sunga d'ansu sunsha hira, kwanakin Fa'iza uku da haihuwa Shamsuddeen ya tafi wani taro da zasu yi a Switzerland hakan yasa Aliya tattara kayanta ta koma can gidan su wajan mai jego. Sosai Sahal yayi hidima ya kashe kudi kamar nan gaba bashi da buk'atar su. Shima Shamsuddeen ya yiwa Aliya bajinta, wani hadadd'an gado na jarirai da kayan sawa da kayan wasa da sauran abubuwa ya siya ya bata yace ta kai gudun mawa shi kuma ya bawa Sahal kudi saboda yasan sai yafi bukatar su akan ya siya masa wani abun. Ranar suna maijego taga kara taci kwalliya tayi kyau abunta, itama Aliya ba'a barta a baya ba haka suka dinga shiga suna fita kowa yaga Aliya sai yace sauran ita tayi murmushi saboda ko b'atan wata bata tab'a yi ba har yanzu. Anci ansha taro ya tashi lafiya, bayan suna da kwanaki uku ne Shamsuddeen ya dawo a kuma ranar suka koma gida shida ita suma sunata addu'a Allah ya basu nasu rabon.

Shi kuwa b'angaren Yazeed da ya gama tabbatar da cewa Nawal ba zata yi abinda yasa ta ba sai yayi gundunbala yaje ya sanar da iyayensa cewar yaji ya gani zai auri Nawal kuma baya son asa lokaci mai yawa. Aikuwa duka side d'in sunji dad'i, koda aka tambayi Nawal tana sonshi ko kuwa? Shiru ta yi hakan yasa akace ta yadda aikuwa aka sa wata uku dan tuni Shamsuddeen ya mallaka masa dankareran gida mata kawai yake jira kuma gashi ya samu. Cikin kankanin lokaci aka gama komai duk da cewar har biki yazo amman basa zaman lafiya Yazeed yana yi mata duk maganar da tazo bakinsa ita kuma zata nuna masa bata damu ba tunda shine ya nace sai ya aureta. Su Shamsuddeen da Aliya sune kan gaba komai sune suka d'auki nayi hakan yasa ko a babban aboki shamsuddeen Yazeed yasa itama Nawal Aliya tasa haka aka yi biki lafiya aka tashi lafiya kuma aka kai amarya gidan ta....






ZAZZAFA DAYA
MX🧕🏼
[27/03 6:57 PM] Bilkisu: *_KAI MIN HALACCI.......!💕_*

_(LEGACY OF UNREQUITED LOVE)_

_*NA_*

_*NANA HAFSATU_*
_*(MISS XOXO)🧕🏼_*

_*NI KADAI WRITER ASSO*💃🏿_
_Self defensible writer.. Alhamdulillah Ya Rabb for the unlimited blessings_😎😍💕_

_*NO: 54-55_*


_*EPISODE FINALE😁_*
_*(‘KARSHE)💃🏿_*

Shamsuddeen da Aliya sune suka tsaya siyan baki, sun dad'e Shamsuddeen yana yi musu nasiha kafin su tashi tafiya, Yazeed yaje ya raka su suka shiga mota yana ta yi musu godiya har suka bar gidan ya kulle sannan ya nufi ciki. Tana nan inda suka barta ko motsawa bata yi ba, yaje sai faman had'e rai yake ya tsaya a kanta tare da cewa.

“Tashi kiyo alwala.”

''Bana sallah.''

Yazeed ya zaro ido sosai yaji bugun zuciyarsa ya kuma tsananta dan ya gama shiryawa daren nan duk masifarta shine yanzu zata ce bata sallah. Hannu yasa ya d'ago da ita yana k'ok'arin tabowa ita kuma tana bubbuge masa hannu amman sai da yasa hannunsa ya jiyo.

''Karya kike yi, ni zaki yiwa karya? Kin manta yanzu a karkashina kike ko?''

Banza tayi dashi ya kuma cewa taje tayi alwala tace tayi sallah ya kad'a ya raya amman ta kangare, ya fita harabar gidan ya kira Shamsuddeen yana sanar dashi, lokacin kuma su tafiya suke a mota suna ta gulmarsu sai gashi kuwa ya kira Shamsuddeen najin abinda Yazeed yake cewa shi kuma yace dashi.

''Dude mata fa ba'a yi musu dole koda kuwa auran soyayya kuka yi indai daren farko ne, yanzu kaje ka lallab'a ta da kalamai masu sanyaya zuciya ina gaya maka indai kayi haka toh a daren yau zaka angonce.''

''Wallahi Dude ta raina ni ne, kuma ni wallahi ina sonta.''

''Good tunda kana sonta kayi amfani da wasu ways d'in ta hanyar nuna nata soyayya.''

''Okay zan gwada, idan nayi sa'a toh gobe bazanje office ba, idan ta hanani kuma zanyo sammako nazo.''

Dariya Shamsuddeen yayi yana kallon Aliya daga nan yaji Yazeed din ya katse kiran. Cikin parlourn ya koma tana nan inda ya barta a tsaye ya karasa wannan karan jikinsa a sanyaye yake yaje ya kamo hannunta suka nufi d'akin ta. Kafadunta ya kamo yana k'ok'arin shigar da idanunsa cikin nata amman taki bari yace.

''Nawal..!''

Tayi saurin d'agowa saboda batajin yana kiran sunanta sai dai yace ke! Ko dalla, hakan yasa da ya fad'a taji wani banbarakwai ya lumshe idanunsa tayi saurin kawar da kai.

''Kiyi hakuri kiyo alwala muyi sallah kamar yadda annabin rahama ya koyar damu please badan ni ba.''

Zare hannunta tayi ya ga ta nufi bathroom ya lumshe idanunsa kafin shima ya fito ya nufi nashi d'akin. Alwala yayi ya fito ya koma nata inda ya tarar da ita zaune a bakin gado ta tashi suka yi sallar, suna idarwa ta mike ta hau gado zata kwanta, yayi saurin dakatar da ita yana cewa.

''Kiyi hakuri kizo muje kici abinci.''

''Alhamdulillah na koshi.''

''Please Nawal karki min haka ki daure kizo muje.''

Da kyar ya samu nan ma ta fito suka koma parlour, kad'an taci kazar tashi lemo sannan ta tashi ta koma d'aki ta kwanta saboda ta gaji bacci take son yi. Jinsa tai ya shigo yana kashe wutar d'akin yana cewa.

''Shine babu jira sweetie.?''

'Sweetie' Nawal ta maimaita a cikin zuciyarta tana sake kudundunewa, tana jin ya hau kan gadon kirjinta ya buga ta sake rintsa ido. Jikinsa ya janyo ta ta fara kiciniyar kwacewa tana bata so shi kuma yana sake matseta, murya na rawa taji yana cewa.

''Sorry for doing things that hurt you, believe me that my intention was clear, I did not mean to let you down, my intention was not to make you frown, if I made a mistake then I apologize, for doing so in life, I am so sorry, and I mean when I say this will not happen again sorry again my dearest wife...''

Wasu zafafan hawaye suka zoraro mata soyayyarsa ta kuma shigewa cikin ruhinta amman taki nuna masa. Tana jinsa yana ta bata hakuri yana kuma jaddada yadda yake sonta da haka Yazeed ya samu ya cimma muradin zuciyarsa yana sake matseta. Tun daga ranar suka ajiye 'yar tsamar dake tsakaninsu suka rungumi junansu suna gudanar da soyayyar su tamkar babu gobe.

••••√ ••••√ •••••√

*BAYAN SHEKARU BIYU*

Zaune take a cikin office d'inta tana ta harhad'a wasu documents a gaban tebur d'in ta da aka rubuta Secretary, mace ce matashiya wacce bata zaka tab'a gano cewar matar aure bace saboda yanayin jikinta. Sanye take cikin riga da zani na atamfa ta sanya hijabi idanunta sanye cikin glasses fari. Tsaye ta mike da kyar duk da cewar a zahiri ba zaka tab'a gane cewar ciki ne a jikin ta ba har na tsawon watanni takwas. Wani office ta nufa wanda ke bayanta sai turo baki take tana yatsina fuska, Sahal dake kusa da Shamsuddeen wanda yake rubutu yace.

''Toh gatanan fa, wannan matar taka ta fiye daru.''

A hankali Shamsuddeen ya d'ago daradaran idanunsa ya watsa su akan Aliya dake tahowa gurinsu tana cuno baki.

''My Simba ya akai ne, waye ya tab'a minke?''

''Ba kai ne ba.''

''Kai..kai..kai, mai nayi?''

''Kak'i zuwa ka ganni.''

''My Simba yanzu fa zuwan Sahal na baro wajan naki shine har nayi laifi?''

''Eh mana ba idan ka bashi gurin zama sai ka koma ka sake gani na ba shine zaku yi zamanku kuna hira.''

''Sorry my Simba zoki zauna ina yi ina kallonki.''

Murmushi tayi wanda ya bayyanar da fararan hakoranta masu d'auke da hakorin makkah sai walwali yake. Mik'a masa documents d'in tayi ya karb'a sannan ta juya zata tafi ta jiyo muryar Sahal yana cewa Shamsuddeen.

''Oga ya kamata fa ka bata hutu wallahi karta sauke mana baby anan.''

''Wallahi taki yadda, na bata tun cikinta yana wata biyar amman ta’ki saboda wai shi cikin yazo mata da laulayi na son gani na, duk minti d'aya biyu sai naje na ganta ko tazo ta ganni.''

''Ooh wai daman da gaske ne wannan abun? Maman Sultan (Fa'iza) ta sanar dani amman kawai na jita ne saboda a lokacin tace babu inda zan fita sai take min zancen na dauka ta fad'a ne kawai dan itama na zauna a gida.''

Shamsuddeen ya jinjina kai Sahal ya kyalkyale da dariya har yana buga tebur d'in gabansa ya kuma cewa.

''Haba, kace shi yasa kake k'ok'arin yaki cewarka wajan tafiya landon d'in nan ko?''

''Kuma ba zashi ba kaine zaka tafi insha Allahu.''

Aliya tayi maganar tana kallansa shi kuma yana dariya Shamsuddeen yana ta kallonta domin kullum kyau take sake yi, cikin kara mata haske da walwali yake yi, ta turo masa baki ya had'e hannayensa guri d'aya alamun afuwan sannan ta fita tana cewa Sahal.

''Yau har tsayuwar dare zanyi kawai dan kaje ni abar min miji na ya gaji da tafiye-tafiye komai a ce shi.''

Da haka ta fita Sahal yana dariya ya kalli Shamsuddeen tare da cewa.

''Gaskiya Liya har yanzu 'yar fari ce, gashi ta had'a da autanci da ace iyayenta suna da rai toh ina tunanin tabararriya za'a wallahi.''

Shamsuddeen yayi murmushi shi kadai yasan tabarar Aliya domin komai ma sai tayi masa barar ma ace sunzo kwanciya wayyo tamkar su kadai ne a duniyar haka take maida su. Haka suka ji gaba da tsare-tsaren su domin tuni suka baro kano suka dawo Abuja ya bar Yazeed a can wanda shine ya zama Oga Yaya Garzali yana tallafa masa ta wasu abubuwan da ake buk'atar taimakon sa. Haka rayuwarsu taci gaba da gudana har watan haihuwar ta ya kama, nan kuma aka sha daru domin tace sai ta koma gida itama amman Shamsuddeen ya kafa ya tsare yace babu inda zataje sai dai a kawo wata mai kula da ita anan, har fad'a suka yi na kwanaki biyu suka sha wahala suka koma suka shirya kansu domin ba zasu iya rabuwa da juna ba.

Yakumbo Zulai aka d'akko mata daga bunkure aka kaita Abuja, zuwanta garin da sati d'aya wata ranar lahadi Aliya sun fito daga wanka ita da Shamsuddeen kawai yaga ta dafa gado ta kasa zama yace.

''My Simba zauna mana.''

''Habibi marata bazan iya zama ba.''

''Mara kuma? Ciwo take miki?''

''Yeah wayyo harda baya na yanzu.''

Tayi maganar tana kuma durkushewa kasa, Shamsuddeen yayi maza ya tallafota, da sauri ya kwantar da ita akan gado amman ta kasa kwanciya ya d'akko mata doguwar riga yasa mata cikin tashin hankali ganin yadda take duddurkushewa. Kayansa shima yasa sannan ya sakko da ita kasa yana kiran yakumbo Zulai wacce ke zaune cikin d'akin da aka bata. Da sauri ta fito hannunta rike da d'ankwali tana amsawa, ganinsu a haka yasa ta koma da sauri ta d'akko hijabi tana cewa.

''Subahanallahi Aliya haihuwar ce tazo?''

''Yakumbo zo mu wuce asibiti wannan ciwon bana gida bane.''

''A'ah ranka ya dad'e ka barta yanzu zakaga ta haihu da ikon Allah.''

Ganin zata yi masa gaddama ne gashi ita kuma Aliyar sai kuka take tana innalillahi wa'inna ilaihir raji'un tana rirrik'eshi kamar zata yaga masa riga yasa shi yin waje da ita. Mota ya kaita yace da yakumbo Zulai itama ta shiga, sannan ya tayar da motar yakumbo tana rik'e da ita sai zabga mata sannu take yi, shi kuma tun a hanya ya kirawo Fa'iza yana sanar da ita daga nan ya kirawo Umma yana cewa a taya su da addu'a. Suna zuwa aka shigar da ita labour room abar tausayi duk tayi zuru-zuru da kyar ta saki hannun Shamsuddeen saboda gani take yi tamkar ba zata fito ta same shi ba. Shi kuwa ta maza kawai yayi amman tashin hankalin dake zuciyarsa yafi k'arfin tunaninsa, yana ta faman zagaye har su Fa'iza suka karaso.

''Yakumbo suna ciki ne?''

''Eh Maman Sultan tana ciki Allah dai ya sauki yarinyar nan lafiya.''

Fa'iza ta amsa da amin tare da shiga cikin room d'in kai tsaye. ID card d'inta kawai ta nuna musu ta dada da cewa ita sister d'inta ce kafin suka barta ta karasa wajan Aliyar.

''Sissy..!''

''Na'am Sissy sannu kinji, Allah ya saukeki lafiya.''

''Amin Sissy kema haka kikaji lokacin?''

''Haka naji Sissy, amman karki damu insha Allahu kema zaki samu sauki, kiyi ta addu'a a cikin zuciyarki.''

Aliya ta dinga daga kai tamkar kadangaruwa duk ta kankame hannuwan Fa'iza, shiru-shiru ga haihuwa tazo amman karfinta ya kare ta kasa yin wani kwakwaran yunkuri. Ruwan nakuda aka sanya mata nan da nan kuwa Aliya ta fara samun karfi amman duk da haka sai da ta dad'e kafin haihuwar ta taho gadangadan, Shamsuddeen kuwa sai kiran wayar Fa'iza yake yi amman bata d'auka saboda tafi son kawai sai ta haihu taje masa da kyakyawan labari. Cikin hukuncin Allah Aliya ta sunkuto santaleliyar 'yarta kyakyawar gaske fara tar kamar iyayenta. Fa'iza ce ta karb'i 'yar ta shiga gogeta da zaitun sannan ta nannad'e ta cikin towel ta nufi waje tana dariya. Shamsuddeen yana daga bakin k'ofar dan haka tana fitowa dashi suka fara cin karo tayi saurin mik'a masa tana dariya.

''Congratulation Yaya Shamsuddeen.''

''Ina take ita? Lafiyar ta kalau?''

Ya tambaya ba tare da yabi takan 'yar ba, Fa'iza ta sake mik'a masa tana dariya tace.

''Toh ka karb'i babyn mana tukunna.''

''A'ah ki fara sanar dani halin da matata take ciki tukunna saboda ni da ita na saba bada wannan ba.''

Baki duk suka bud'e sannan yakumbo taje ta karb'i jaririyar tana hamdala tare da komawa gefe ta zauna tana kallon 'yar. Su kuwa can shamsuddeen ya tsare Fa'iza akan sai ta sanar dashi halin da Aliya take ciki amman ta tsaya sai raina masa hankali take yi, ganin yana neman fad'uwa yasa tayi saurin sanar dashi cewar lafiyar ta kalau shirya ta ake yi yanzu zasu fito. Duk da haka hankalin Shamsuddeen ya gaza kwanciya har sai da aka bashi gado ya kwanta dan jininsa ya soma hauhawa sakamakon fargabar ko Aliya ta yi wani abun shine ta kasa sanar dashi. Sai da aka fito aka maida ita d'akin hutu sannan aka sanar dasu Shamsuddeen, ya sakko da sauri ya nufi d'akin yana bud'e idanu. Kwance ya ganta suna had'a ido ta sakar masa murmushi tana lumshe idanuwa, Sahal yaja Fa'iza suka fita dan yaga abin nasu da gaske ne sai jifan juna suke da kallon soyayya, kamar jira yake suna fita ya nufi wajan ta yana tattab'a kamar ance masa an gutsireta.

''Me yake damunki? Meke miki ciwo? Sannu kinji my Simba, ba zaki sake haihuwa ba wannan babyn ta ishemu dan gaskiya na shiga tashin hankali.''

Kanta ta d'ago ta d'ora saman k'afarsa tana rufe ido, yasa hannunsa yana shafar gashinta. Shi kansa sai yanzu yaji hankalinsa yana kwanciya duk da cewar jikinta babu kwari. Sun jima kafin a basu sallama suka koma gida yakumbo taje ta fara k'ok'arin had'a ruwan wanka. Tun lokacin da ta shiga toilet taga ruwan wankan yana tururi ta kalli yakumbo tana turo baki.

''Yakumbo a jikin waye zaki zuba wannan ruwan?''

''Haba Aliya, haihuwa fa kikai yanzu jikinki duk a bud'e yake yana buk'atar gashi keda jaririyar.''

''Tabd'ijam gaskiya bazan iya tsayawa a narka min wannan uban ruwan zafin ba.''

''Toh Aliya meye amfanin zuwa na garin nan tunda kina da yadda zaki yi?''

Sake turo bakin tayi hawaye ya fara taho mata sai ga Fa'iza nan ta tambaya yakumbo Zulai ta sanar da ita, Fa'iza ta kyalkyale da dariya tana dukan kafad'ar Aliya tare da cewa.

''Ke wallahi 'yar rainin hankali ce, kin manta lokacin da Umma zata yi min kikaje kika ce ruwan ya huce tsabar mugunta sai da kikaja aka dafa wani aka kara min shine ke yanzu da yake yazo kanki shine zaki ce yayi zafi?''

''Sissy bazaki gane ba, kinga fatarmu dake ba d'aya bace.''

Ganin da gaske ba zata tsaya ba yasa Fa'iza cewa.

''Bari na gayawa Baba.''

''Ke dalla wasa nake yi miki, yakumbo muje ma ta gani gulmammiya.''

Fa'iza tayi dariya ta san idan ba haka tayi ba toh ba zata yi wankan a haka ba sai ya huce sosai. Tana jiyo ihunta ta dinga dariya harda yin recording. Washe gari 'yan uwa da abokan arzik'i musamman 'yan wajan aikinsu suka dinga zuwa barka abin dai sai wanda ya gani komai acan-acan.

Dangin mahaifiyar Shamsuddeen k'wansu da kwarkwatarsu sunzo, sai b'angaren Abban shi suma sunzo, hakama Aliya motoci biyu Shamsuddeen ya bada akaje aka d'akko mata mutanan bunkure saboda ta nuna masa bukatar hakan. Gabaki d'aya dai 'yan uwa da abokan arzik'i anzo suna, Shamsuddeen kuwa yayi abinda ba kisa zai iya na a sunan nan, ya zubar da dukiya gidan marayu kansu sunsan anyi masa haihuwa domin special abinci yasa aka yi oder aka kai musu da ruwa da lemoka suma suka gwangwaje. Umma ma dake gida a kano sai da yasa tayi taron suna aka yi mata girki da abubuwa itama tayi nata taron a can gaskiya abin sai wanda ya gani Shamsuddeen yana da alkairi sosai. Yarinya taci suna Zainabu suna kiranta Mirha saboda sunan gwaggo Talatuwa ne da tayi ta mita cewar idan macece ita za'a yiwa takwara. Anci ansha an gyatse wasu sunyi guziri. 'Yan suya na musamman Shamsuddeen ya samo saboda sa uku ya yanka sai raguna guda biyu na maijego.

Bayan sati d'aya da suna yasa aka sake gyara gidan. Suna cika sati biyu ne su Umma suka zo wadda sai a ranar taga Mirha yarinyar da Sultan ya dawo gidan saboda ita, yana sonta hakan yasa ya zauna a can duk da Sahal yana kewarsa dan ba karamin shakuwa suka yi da yaron ba, amman saboda karsu Shamsuddeen su zata wani abun ne sai yaja bakinsa yayi shiru dan yaga itama Fa'iza shirun tayi gashi tayi planing taki yadda ta samu wani cikin saboda tana karatu ga aiki. Haka rayuwa taci gaba da gudana Aliya nayin arba'in dukansu da Fa'iza dasu Nawal wacce itama take fama da laulayin ciki suka tafi omara abinsu gwanin ban sha'awa gashi da sun dawo zasu wuce kano saboda bikin Husnah da Fareed wanda Sahal shine ya had'a dan yaga suna son juna amman kowa ya kasa bayyanawa. Cikin ikon Allah suka yo umara suka dawo kwanakinsu biyar suka tafi kano dan shan biki.

A gidan su Shamsudden Aliya ta kafe sai sun kwana acan. Babu yadda Shamsudden ya iya haka suka tafi gidan su. Ummah tayi murnar ganin su sosai, tashiga yi musu hidima Itada Abba, Ya Gazah ma ya kawo gashin kifi daga gidan sa. Har sha biyu su ummah dasu Aliya suna parlor suna hira. Shamsudden sai yiwa Aliya sign yake ta tashi su tafi daki ta’ki sai ma kara bararrajewa da tayi. Tashi yayi yana sosa keyar sa,

“Ummah sai da safe...”

Ummah dake yiwa Mirha wasa ta bashi amsa tana cigaba da yiwa baby Mirha rawa,

“Toh Abban Mirha ALLAH ya tashemu Lapia”

Aliya ya sake yiwa magana da ido tayi banza tana cigaba da latsa wayar ta. Har bakin kofa ya

Please Login or Register in order to submit comment