Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa'a tana zuwa bakin titi ta samu napep ta shiga kai tsaye gidan aunty Yagana ta nufa bayan sun gaisa ta zauna suna hira dan auntyn taji sauki sosai har taci gaba da aiyukanta kamar yadda ta saba. Ba'a jima ba kuwa aka aiko Shahid dake kofar gida shi da yaran makota suna wasa yazo ya kira aunty Fa'iza.

Da mamaki aunty Yagana ta kalleta tace,

“Dama kunyi da wani zaizo nan gidan ne, naga daga zuwanki an turo kije?”

Yatsina fuska tayi tare da gyara lafayar tana turo baki tace.

“Eh na sani, wallahi wani natacce ne Allah ya had'ani dashi, wannan fa wanda Umma take baki labarin cewa sai b'arin kud'i yake min amman yaki bayyana kanshi, shine yazo yanzu, nimafa sai yau zan fara sakashi a idona”

Aunty Yagana ta kalleta jin tace itama sai yau zata fara ganinshi, kad'a kai tayi tare da cewa.

“Toh dai karki bari yajaki inda babu mutane, yanzu duniyar nan babu gaskiya ko gurin motarsa karkije ko mashin tunda bamu san a abinda yazo ba karya dannaki cikin mota.”

“Kai aunty Yagana sai kace wata kaya.”

“Au, mamaki kike yi nace za'a dannaki cikin mota? Toh jeki Allah ya tsare ki kula da kanki dai banda rashin kunya.”

Tashi Fa'iza tayi tama amsawa tare da fita, tana sanya k'afarta a kofar gidan taji kirjinta ya buga da karfi, ta rintsa ido tare da yin addu'a ta k'arasa fita. Mota ta hango a can nesa da gidan ta kallo wajan sai faman horn yake mata ai kuwa ta tuno maganar aunty Yagana na cewa za'a dannata a mota hakan yasa ta make kafad'a alamar ba zataje can ba. Jikin bango ta tsaya tare da ciro wayarta dake faman ringing, Muhamman S ne ta yatsina fuska tare da karawa a kunne bata yi magana ba.

“Please ki karaso wajan motar mana.”

“No! Ba mutunci na bane yin hakan, idan har kasan kanada gaskiya toh sai dai ka fito daga motar kai ka karaso nan tunda ai bamu yi da kai cewar a mota zamu had'u ba.”

“Oh my God, soulmate bafa zan cutar dake ba, please dan Allah kizo maganar ba zata yiwu a tsaye ba.”

“Gaskiya bazan iya zuwa nan ba, ka karaso nan zan shiga ciki na samo maka kujera sai ka zauna.”

Babu yadda ya iya hakan yasa yace mata toh, ta shiga shi kuma ya karaso k'ofar gidan yayi parking, a gaban gidan ta ajiye farar kujerar irin ta roba d'innan ta d'auke kai tana jiran ya fito dan taga kamar yana jin tsoron yin hakan. A hankali ya bud'e k'ofar ya zaro kafarsa waje kafin ya fito gabaki dayansa, sanye cikin wata dark brown d'in shadda bugaggiya d'inkin riga da wando rigar iyakar gwigwarsa yayi masifar yin kyau sai kamshi yake yi. Tattakawa yayi har kusa da ita kanta a kasa gashi ta bashi baya, taji sassanyar muryarsa tana yi mata sallama a saitin kunnenta, Fa'iza ta d'ago tare da d'an matsawa daga kusa dashi dan kad'an ya rage ya had'e jikinsa da nata, ta juya bakinta yana amsa masa sallamar. Tar idanunta akan na Muhammad Sahal saurayin Aliya, tayi saurin zabura tare da dafe kirji tana zaro ido kamar zasu fad'o tace.

“You...?”

“Yeap..!”

Shima ya bata amsa tare da jan kujerar ya zauna yana dora mata dara-daran idanunsa akan kyakyawar fuskarta, yana kallan yadda jikinta yake faman rawa idanunta sun kasa komawa yadda suke saboda tsabar fito da su da take yi irin na tsantsar mamakin nan.

Wayarta ta zaro da sauri tare da nemo sunan sa, kiran layin tayi dan ta tabbatar aikuwa taji ringing daga cikin aljihun wandonsa, kallanta yayi jin tana kiransa kasan cewar yasan ringtone d'inta ne domin babu kowa a cikin sim d'in sai ita kadai, yayi murmushi wanda ya sake kawata fuskarsa yace da ita.

“Ya kike kiran wayana bayan gani a gaban ki?”

“Ya Sahal! Kasan me kake shirin aikatawa kuwa?daman kaine Muhamman S?”

“Yeah nine Faizaah, nine wannan Muhamman s d'in wanda yake tsananin kaunarki tintuni, na kasa bayyana kaina gareki ni saboda 'yar uwarki wadda take sona ni kuma gaskiya soyayyar kanwa da yayanta nake yi mata kamar yadda nake dasu Husnah, amman ke kece burin zuciya ta kece kullum nake mafarkin ki zama mallakina daga ranar dana ganki Faizaah na kasa tantance menake ji a tare dake ashe love ne ki....”

“Ya isheka haka malam, kayi min shiru.”

Tayi saurin katse shi cikin kuka, tsayuwa ta gyara tana zirarar da hawayen bakin ciki tace dashi.

“Yaya Sahal kasan mekake shirin yi kuwa? Kasan wace irin masifa kake shirin jefani a ciki? Shin kasan irin soyayyar da Aliya take yi maka? Wannan abun da kake son muyi tsakanina dakai sunansa cin amana a gareni, kuma cin amana yana daga cikin halayen munafurci. Manzon Allah (saw) ya lissafta wasu halaye guda uku, yace duk wanda yake dasu acikin halayensa, to hakika shi munafiki ne. Koda yayi sallah yayi Azumi, koda yayi Hajji yayi Umrah, koda yace shi Musulmi ne (Subhanallah!). Wallahi Yaya Sahal cin amana yana daga cikin abubuwan da suke tauye Imanin Mutum. Mutukar mutum zai rika cin amanar Mutane, to kullum Imaninsa raguwa yake yi. Ka rufa min asiri kace min wasa kake yi ko zuciyata zata yi sanyi. Idan kuma mafarki nake yi dan Allah kayi gaggawar tashina na farka domin wannan mugun mafarki ne marar dad'in ji bare sauraro...”

Shiru kakejin Sahal ba wai maganganunta ne suka sanya jikinshi yin sanyi ba illa kukan da yaga tana yi hawaye shab'e-shab'e gefen laffayarta sharkaf da ruwan kuka, duk sanda yaji ta ja kukan sai yaji kamar zuciyarsa ake janyowa hakan yake sashi rintsa ido. Da yaji tayi shiru ne ya samu damar yin magana yana jin kamar ya janyota jikinsa ko zatafi jin yadda zuciyar sa keyi, yace da ita.

“Naji duk abinda kika ce my soulmate, amman ina son ki sani cewar. Ban tab'a cewa ina son Aliya ba tunda muke da ita koda zaki tambayi Husnah, kawai dai nasan ita tana sona kuma ni baxan iya cewa bana sonta ba saboda rashin da cewar Kalmar. Amman ina son ki sani ni tuntuni bance ina son Aliya ba, dake zuciyata ta amince hakan yasa nazo gareki har nake jure duk wani wulak'anci da kike min. A yau gani a gabanki da kokon barata na soyayya kuma da aure bawai wani abun ba, ki amince min kodan zuciyata ta samu sassauci Faizaah please..!”

Wani sabon kuka ne ya kwace mata ganin yadda ya durkusa a gabanta da girmansa da mutuncinsa uwa uba ajinsa amman ya sanya gwiwarsa a kan k'asa yana neman alfarmar ta so shi. Cikin sauri ta juya masa baya tare da sanya gefen lafayyar tana goge ambaliyar hawayen da suke zirarowa babu kyakkautawa. Bata waigo ba tana faman jan majina irin ta kukan nan tace dashi.

“Mai yasa kaima ba zaka tausayawa 'yar uwata ba kaso ta kamar yadda take sonka?bari kaji na sanar dakai kamar yadda nake gaya maka a waya, ina da wanda nake SO, yana cikin zuciyata yaki fita hakan yasa nake da yakinin cewa shine mijina kuma uban 'ya'yana, ya kamata ka yiwa Aliya *HALACCI* ka aureta kodan irin makauniyar soyayyar da take yi maka. Sannan kayi hakuri nima ka barni naje na auri wanda zuciyata take tare dashi domin ban tab'a jin ina sonka ba yaya Sahal I’m very sorry, and leave me alone please.”

Mik'ewa yayi daga durkushen da baiyi tsammanin zai yiwa wata mace shi ba, zagayowa yayi wajan fuskarta tare da cewa.

“Faizaah! You are asking me to end not only our relationship but also everything else between us.. Faizaah I can't believe how someone like you hurt me this much. And bazan iya rabuwa dake ba domin da zan iya da tuni nayi kodan albarkacin liya, zuciyata ta riga ta mutu akan soyayyar ki Faizaah, zuciyata babu wanda ta aminta ta bawa yardarta sai KE. Ki soni Faizaah ko yaya ne zanji dad'i dan Allah..”

A fusace ta dago jajayen idanunta ta narkasu akan nashi suka yi ido hudu, ganin yadda idanunta suka yi ne yasa kirjinsa bugawa da karfi, yayi saurin janye nashi domin ba zai iya jure kallansu ba, yana jin kamar ya janyota saman kirjinsa, muryarta a sarke take masa magana.

“Ya Sahal ka dena batun wannan domin nace maka cin amana ne, kuma yana daga cikin halayen da suke Qaskantar da darajar mutum awajen Allah. Mutukar mutum bai rike amanar bayin Allah ba, to Allah ne zai zama abokin rigimarsa aranar Alqiyamah (Subhanallah). Ya Sahal kasan cin amana yana sanya mutum yayi baqin jini acikin al'ummah? Sannan darajarsa da mutuncinsa su zube? sannan kuma al'ummah su rika gudunsa.? Cin amana yana zama sanadiyyar Dulmiyar mutum acikin wutar Jahannama. Kamar yadda yazo acikin hadisi, Allah zai sanya amanar acikin chan Qasan Wutar Jahannama, sannan a umurci maciyin amana cewa ya shiga ya d'auko ta. Sai ya d'auko ya hauro wani babban tudu, sannan sai ita kuma Amanar ta sub'uce ta koma chan Qasan ramin Jahannama. Sai Mala'iku su daka masa tsawa suce ya koma ya d'aukota. Haka zai yi ta yi har Illa ma sha'Allahu. Ka rufa mana asiri domin cin amana yana zubar da albarkar dukiya. Domin kuwa komai yawan kudi, in dai aka chud'anyashi da kudin Cin amana sai ya lalace. Ya Sahal ya zama wajibi mu rika kiyaye amanar junanmu don samun mutunci awajen Allah da bayin Allah, karka sake kirana karka sake min message sannan karka kuma kulani dan ba zan iya auranka ba koda baka auri Aliya ba saboda yadda muke da ita.”

Tana kaiwa nan ta ruga da gudu cikin gidan yana ta faman kiranta amman tayi masa banza, tana shiga suka yi kicibus da aunty Yagana wadda ta jiyo Sahal yana ta faman kiran Fa'izan. Rik'o ta tayi da sauri ganin tana kuka hankali a kashe take tambayarta.

'”Ke tsaya ki sanar dani abinda yayi miki, menene kika shigo kina wannan uban kukan, kuma gashi can ana kiranki a waje, menene?”

Ta kasa magana sai fadawa jikinta da tayi tana faman kuka, da sauri aunty Yagana ta zare jikinta tare da shiga d'aki ta dakko hijabi, fita tayi da sauri dan taga waye ya sanya mata 'ya kuka. Sahal yana k'ok'arin bud'e motar tamkar wani marar lafiya yaji ana dakatar dashi ta hanyar cewa.

“Kai! Wanene?”

A hankali ya juya suka had'a ido da aunty Yagana, da sauri ya matsa wajan da take wato kofar gida yace da ita.

“Aunty ina yini?”

“Lafiya lau, meka yi mata ta shiga tana kuka?”

“Yauwa aunty dan Allah ki lallab'a min ita, wallahi daga cewa ina sonta zan aureta shine ta fara kuka, wai ai Aliya na Sona.”

Shiru aunty Yagana tayi domin ta ganshi ba irin mazan nan bane da za'ak'i, dan haka a mutunce ta fara yi masa magana,

“Daman kaine Muhamman S?”

“Eh aunty nine.”

“Shikenan kaje kawai zamu yi magana da ita.”

“Toh aunty Yagana na gode dan Allah ki sake bata hakuri, sannan dan Allah ta dena kukan nan haka.”

Aunty Yagana ta amsa tare da komawa cikin gidan, shi kam duk maganar da yayi mata yanzu idan ka tsaresa kace ya maimaita ba zai ce ga abinda ya ce da aunty Yagana ba saboda tsabar tunaninsa yana can gurin Fa'iza da ta shiga tana kuka. Da kyar yaja motar yabar Quarters d'in kansa yana sarawa duk da yasan dama zataji shock idan ta ganshi amman beyi zaton zata yi masa haka ba. A can gidan kuma aunty Yagana taja Fa'iza suka shiga d'aki suka zauna ta kalleta tare da tambayarta.

*WANENE MUHAMMAD SAHAL?*


*NANA HAFSAT🧕🏼*
*KAI MIN HALACCI.....💕*
*(Legacy Of Unrequited Love)*

*WRITTEN BY: THE GIRL WITH GLASSES🧕🏼*

*PAGE; 37*


Da murna ta koma gidan aunty Yagana, duk kallanta suka yi itama ta kallesu tana dariya kai da ka ganta kasan tana cikin farin ciki, Aliya ta kalleta tare da cewa.

“Wai ke dan Allah ina kika sani a quarters d'in nan da duk lokacin da zamu zo sai kin fita?”

Fa'iza tayi dariya tana k'ok'arin zama akan kujera tace.

“Ke gidan su Shamsu naje na gaida Umman su.”

Tabe baki Aliya tayi tare da janyo jakarta tana ciro awarwarayenta, sanyawa take tana cewa.

“Malama tashi mu tafi ni ko karatun jarabawar gobe banyi ba, uwar shisshigi.”

Fa'iza tayi dariya daga nan aunty Yagana tayi musu zancen samari har tana haskawa Aliya irin rashin ko in kula d'in da Sahal yake yi mata da kyar idan sonta yake yi da aure. Maganar kawai shiga take ta kunnan daman Aliya tana kuma fita ta hagu, tana mamakin yadda za'a ce Sahal baya sonta bayan kuma gashi nan yana zuwa gidan su yana kawo mata abubuwa yana mata komai idan ka cire love messages da kuma rashin furtawar da baya yi, amman duk da hakan tasan yana sonta dan da baya kaunarta da tuni ya watsar da ita.

“Aunty bari mu tafi kar dare yayi sosai.”

“Toh dai kuci gaba da addu'a Allah ya baku mazajen kwarai.”

“Amin aunty ni dai Allah ya bani sauran Fa'iza ita kuma taki kula kowa, ga wani Muhamman S, wallahi aunty bakiga wulak'ancin da take yi masa ba.”

Kallan juna Fa'iza da aunty Yagana suka yi kafin aunty Yagana tayi murmushi tace.

“Shi yasa nace kuyi addu'a.”

“Zamu yi aunty mun tafi.”

Cewar Fa'iza cikin son katse hirar domin sam bata son hirar Sahal b'ata mata rai take yi sosai. Har bakin kofa aunty Yagana ta raka su tana basu sakon gaisuwa gurin Umma. A lokacin kuma Shamsuddeen yana shan kwanar gidansu su kuma suka fito Allah ne yayi ba zasu had'u ba. (Ko kuma ni miss xoxo).

Lafiya kalau sukaje gida bayan sunyi sallar isha'i suka zauna dan yin karatu a lokacin ne kuma Fa'iza ta d'auki wayar ta tana faman kallan numbers d'in Shamsuddeen wanda tama rasa da wane irin suna zata yi saving. Ganin yadda take kallon waya tana murmushi yasa Aliya saurin fizge wayar tana kallon screen d'in, rasa abin da Fa'iza takewa murmushi tayi dan haka ta cilla mata wayar tare da cewa.

“Sai kace wata tababbiya kin tasa waya sai murmushi kike yi, meye sirrin ne Sissy?”

“Uhmm Sissy ba zaki gane ba yi shiru kawai.”

Cewar Fa'iza tana k'ok'arin bud'e littafinta dan yin karatu wanda ba ta da tabbacin ma zai zauna sabida tsabar farin cikin, yayin da Aliya ta gallara mata harara tare da cewa.

“Eh ke kuwa ga dak'ik'iya ba dole na kasa gane duk wani bayani da zaki min ba.”

Dariya Fa'iza tayi ba tare da tace da ita komai ba ta tafa karatunta.

Washe gari suka gama jarabawa murna ba'a magana daka gansu zaka gano tsantsar farin ciki. Raheenah ce ta k'arasa wajan Fa'iza jikin ta sanye da wani fitinannan turare wanda daka jishi zakaji yayi maka. Kusa da kunnanta taje tana rad'a mata cewar.

“Kinyi sa'a kin tsallake duk wani tarko na akanki, amman ina son ki sani wannan harkar itace mafita akan aure, kinga idan kina yi? Baki da wani damuwa sannan babu mai takura miki, aure wahala ne da takura namiji da ya sameki shikenan kin tashi daga aiki zai fara tunanin kawo wata yazo ya had'a ku kuyi ta rigima akanshi, amman kije kiyi tunani duk sanda kika shirya kizo ki sameni kinji my love?”

Baki bude Fa'iza take kallanta kafin ta janye jikinta daga rikon da Raheenah tayi mata, a wulak'ance take mata wani kallo tare da cewa.

“Nafi karfinki dake da shaid'an din da yake tare dake, wallahi nace Allah kuma kullum sai nakai kararki gurinsa sakarya kawai. Gara ai nayi auran na mutu cikin wahala ko ba komai Allah yaga akan turbar dana koma gurinsa ba irin taki ba ta kazanta. Ke yanzu daman duk irin fadakarwar da aka dinga yi duk ji kikai kika barta a gurin? Allah yayi min tsari dake ya nisanta tsakanin mu, idan ban zama alkairi a gurinki ba insha Allahu sharrinki ba zai shafeni ba.”

Daga haka taja tsaki tabarwa Raheenah wajan tana Allawadarai da hali irin nata tare da yi mata fatan shiriya gurin Allah. Husnah ce tayi saurin tare ta ganin tana shirin tafiya tare da cewa dan Allah tazo ta rakata ofishin malam Inyas, kamar ba zata ba sabida ranta duk a bace yake sai dai kuma itama Husnah tana rakata duk inda take so hakan yasa suka tafi suna ta hira, suna zuwa suka yi sallama wani daddad'an kamshin turare ya sake dukan hancin Fa'iza wanda yasa ta sake bud'e ido tana mamakin yau malam Inyas ya sako turare na yau mai dad'i ne ba kamar wad'anda yake sakowa ba.

Sai da suka shiga lokacin kujerar malam Inyas ta juya baya kuma yana kai duk a zaton Fa'iza sabon salo ne irin na shi kawai sai taga an juyo cikin wani irin juyi, karaf suka yi ido hud'u da Muhammad Sahal gaban Fa'iza ya buga da karfi domin bata yi zato ko tsammanin ganinsa ba.

“Toh Yaya Sahal gata nan na kawo maka ita, sauran muje gida kaki bani wayar hannun taka.”

Tashi yayi tsaye ya nufo su yana jinjinawa Husnah tare da tabbatar mata cewar idan ya koma gida zai cire sim card d'insa ya bata wayar kamar yadda yayi mata alkawari cewar indai ta kawo masa Fa'iza nan cikin dabara zai bata ita. Husnah ta juya ta fita Fa'iza ma tayi saurin bin bayan ta sai dai Sahal bai bari ba yayi saurin rik'o mata hannu tare da tura kofar da kafarsa guda d'aya. Cikin tsananin fushi ta d'aga hannu zata kai masa mari nan ma yayi caraf ya rik'o shi, sai ya zamana ya rirrik'e hannuwa kamar wanda yake shirin rungumeta.

“Ina zakije?”

“Malam sakar min hannuna ko kaga nayi maka kama da 'yar bariki?”

“No soulmate, ai rashin kamarki da 'yan bariki shine dalilin da yasa kika sace min zuciyata. Da ace kinyi kama dasu toh da ko hanya bazamu had'a dake ba, wannan abun ma daya faru ina da dalili na nayinsa.”

“Naji sakarni bana son namiji yana rik'e ni.”

Tayi maganar cikin fushi. A hankali kuma taji ya saketa tare da d'an matsawa yaje ya danne kofar da bayansa yana mai kallonta kamar wata tv.

“Mekake buk'ata daga gareni yanzu?”

“Your LOve, Fa'iza please love me Faizaah, shin baki san love is a soft feeling of heart ba? but it's very hard to feel...and when it feels Faizaah its too hard to drop...bcoz true love happens once in lifetime. I love you Faizaah, kinsan irin wahalar da kike bani? Faizaah soyayyarki gareni ba yin kaina bane daga Allah ne, wallahi Faizaah I'm totally into you. Dan Allah ki barni na shiga cikin rayuwarki mu rayuwa da juna insha Allahu zaki yi alfahari dani idan kin aure ni.”

Hannunta na dama tasa a goshi tare da dafewa tana rintsa ido, ta d'an jima a haka tana sakawa da kwancewa kafin ta d'ago idanunta ta dora akan nashi, saurin janyewa tayi sabida sunyi mata girma da kwarjini, ta samu cikin sassayan murya wadda ta sake shagalar da Sahal a kogin kaunarta tace dashi.

“Naji Yaya Sahal amman ka sani ni bana son na yaudareka, ina da wanda nake so kuma koba haka ba ni kam ba zan iya auranka ba saboda Sissy Liya ta soka hasalima tana kan sonka, so kayi hakuri ka manta dani ka manta da inda kasan Fa'iza saboda love is impossible between me and you, sannan ina mai baka shawara akan cewar ka sanar da Aliya ba son aure ta kake yi ba saboda ta samu ta zaida nagartacce saurayi wanda zai zamo miji a gareta.”

Sahal yayi shiru jikinsa duk yayi sanyi sai dai ba zai iya rabuwa da Fa'izan ba komai zata yi masa saboda shima ji yake ana kara masa wutar sonta.

“Dan Allah ka bud'e min na fita kar mutane su zargemu da wani abun.”

“Zan barki ki tafi amman sai kinyi min alkawari.”

Cikin jin haushinsa tace.

“Namefa?”

“Kice zaki dinga d'aukar kirana, sannan ki cire ni a blacklist da kika sani.”

“Kayi hakuri bana d'aukar alkawari gaskiya.”

“Toh kuwa baki shirya barin office d'in nan ba kenan?”

“Dan Allah kayi hakuri ka barni na tafi.”

Matsawa yayi daga jikin kofar tare da komawa gefe wai ya gwadata ko zata tafi, aikuwa kamar jira take nan da nan ta nufi k'ofar zata fita yayi saurin rik'o hannunta.

“Da gaske tafiya zaki yi?”

Fa'iza tayi shiru gani take kamar Aliya na bakin k'ofar saboda tsabar fargaba, tayi saurin fizge hannunta tare da cewa.

“Eh! Mezan tsaya yi?”

“Wai me yasa bakya tausayi na ne Fa'izaah?”

“Saboda kai ma baka tausayawa 'yar uwata ba dan me zan tausaya maka?”

“Shikenan zan barki ki tafi, zanzo gidan na bayyana kai na a wajan mahaifinki da nufin son auranki idan yaso koma menene ya faru, na gaji da wahalar min da zuciya da kike yi ina jin tana yi min zugi dan haka zanzo gidan ku nan bada dadewa ba.”

Kamar ta tsaya maida mishi martani sai dai kuma tayi shiru tare da bude k'ofar ta fita, rufuta tayi da karfi kamar zata balla ta wanda har Sahal sai da yaje ya duba k'ofar dan ya gani kota b'alla musu sai yaga lafiya lau. A can nesa taga Husnah ganin ta fito yasa ta nufota amman Fa'iza tayi mata banza, tana ta yi mata magana amman ta shareta saboda itama yanzu haushinta takeji, dole Husnah ta hakura ta kyaleta har suka isa bakin gate kowa ya hau napep ya wuce gida.

•••••• ••••••• •••••••

Ranar jumu’ah yan uwa da abokan arziki suka halarci liyafar da aka shirya na bude wajen Shamsudden mai suna; LIBROS/CAFE24 (SAB PENTHOUSE AND MORE), ranar asubahin ranar aka sauke karatun Al-Qur’an mai girma a babban masallacin jumu’ah dake hotoro. Abba yasanya akai addu’oin bude taro lapia, da kore sharrin masu sharri, ayi taro lapia a watse lapia, yawancin ‘yan uwa na nesa dana kusa sai da suka zazzo halattar ‘dan bikin da za’ai na bude kamfanin Shamsudden. A lokacin abubuwa sun taru sunyiwa Shamsudden yawa, ga harkar embassy ‘din Switzerland da aka bude reshen sa a kano wanda Shamsudden na d’aya daga cikin gurbin ma’aikatan dake ciki. Na biyu ga harkar bautar ‘kasar sa da a ranar ne suke yin Pop (passing out parade). Shiya sanya abubuwan sukai masa yawa. Da safe ya hau jirgin safe ya koma Abuja akai Pop dashi ya karb’i certificate ‘dinsa ya biyo jirgin rana ya dawo, sun gaggaysa da mutane awajen company launch dinsa, bai jima awajen ba ya koma can embassy! Ya bar Yazeed da Ya Garzali akan komai na kamfanin sa. Abun dai sai sam barka kawai! Domin anyi taro lapia babu matsalar komai, Lalle addu’a makarar muminice. Ya Allah ka biya mana bukatun mu na alkhairi Amiin...’

Ranar Monday kamar yadda dokar makaranta ta tanadar musu, Su Aliya suka fara rakwacafniyar neman inda zasu yi internship. Nour su Lamfat sun sa ma mata, Nawal Mukhtar ma mahaifin saurayin ta manager din banki ne, Don haka manemin nata yace kada ta damu har gidah zai kawo mata acceptance lettern. Aliya ce kawai ido ya raina fata, tayi tsuru tsuran rashin samun wajen siwes. Gararanbar neman wajen internship kuwa sune har laraba, gashi Kwana biyu ya rage a deadline din da Malam G.A.B ya basu! Sai zazzaga gari suke neman wajen da Aliya zatai internship, Nawal ce ke driving, Aliya a gefen ta, idanuwan ta taf da ruwan hawaye, cikin dakushewar murya ta dubi Nawal dake driving kafin tace,

“Bestie! Kinga kawai muje state library dinnan, Na hakura zanyi kawai a can”

Nawal ta dubi Aliya dake fitar da ambaliyar hawaye, kafin cikin jan tsaki had’e da dankara mata harara tace,

“Wallahi yadda kikasan na kwashe ki da mari dan takaici, ya za’ai ki rasa inda zaki internship sai wannan shakararren state library din da suna ya tara ba books ba, Allah ya sawwake, Wai dan kinga mun biyo Ahmadu Bello Way kin ‘dauka can zamu? Tab zuba ido ki kallo.”

Aliya tai shiru kawai tana bin yadda mutane ke rayuwa akan titi da kallo, mutane da ransu da Lapiar da zasu iya yin aikatau su samu na abinci sun kashe zuciyar su da yin bara akan titi suna maula had’e da yin ‘karyar rashin cin yau bare na gobe. Tana can tana tunanin Allah wadai da masu barar kan titi, sai ji tayi Nawal taci birki ta faka motar awani had’adden waje da Aliya ta kasa gasgata shin mafarki take ko kuwa film take gani? Had’adden waje ne daya amsa sunan sa, domin tafkeken ‘kerarren gini ne daya amsa sunan 3D Switzerland style. Yasha fentin blue

Please Login or Register in order to submit comment