Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin kuma Ummi take bawa labarin komai babu abunda ta cire, Shi yasanya da Sahal ya shigo parlorn Ummin ta girgiza kai kawai adai-dai lokacin kuma Husnah ta gama fayyace mata komai. Ummi ta mike tashiga dakin baban su Sahal din, Alhaji Tahir Abubakhar yana kishingide a kujerar d’akin sa yana duba wata newspaper idanuwansa saqale da gilashi, Ummi tayi sallama ta zauna a gefen sa, Batare daya ajiye jaridar hannun saba ya dubeta da kallon ‘meke tafe dake?. Muskutawa tayi ta shiga labarta masa duk yadda husnah ta sanar da ita. Tunda ta fara magana har tagama idanuwan sa na kan jarida har tagama bai ce komai ba sai ma cigaba da motsa bakin sa yayi alamun yana fahimtar abinda jaridar ta kunsa,

“Alhaji ba kace komai ba..”

“Me kike son nace?!”

“Alhaji ya dakace kayi magana akai, wallahi yana cikin mawuyacin hali, bai jima da shigowa ba a matukar galabai ce, yana dafe kirjin sa tamkar wani makaho yana faman hada hanya..”

Murmushi Alhaji Tahir yayi irin nasu na manya, ya ajiye jaridar hannun sa ya dubi Ummi,

“So kike goto-goto dani na je gidan su ita yarinyar ina rok’on su tallafa su bashi yarinyar kokuwa? Idan har haka kike nufi ba zan je ba gaskia..”

“Haba Alhaji! Babban ‘dan kane fa baka ganin idan ya rasata muma zamu rasa rayuwar tamu d'an?”

“Yadda kika bani labarin nan gaba d’ayan sa Sahal ne mai laifi, Don me zai yi wasa da zuciyoyinsu tamkar wani film? Raba zumuncin su zai yi, Saboda ni babu ruwa na..”

Haka dai sukai ta bugawa da shi, Sam yak'i yadda suje gidan su Fa'iza, sai dai ita taje shi ba zashi ba wai girman sa zai zube, haka tabaro d'akin ranta a b’ace, Sahal kuwa washe gari nayi yabi jirgin safe ya koma Abuja, A ranar da ya koma driver ya d’akko shi a airport suka tafi gidan uncle sa’idu. Suna shiga farfajiyar gidan Sahal ya yanke jiki ya fad’i, Sam babu alamar numfashi a tattare dashi, dawowar senator Sa’idu kenan daga presidency yaga abunda ya faru, Shida abokan sa suka ciccibi Sahal suka sa shi a mota sai asibiti, likitoci suka shiga dashi theatre room don ceto rayuwar sa, A kuma lokacin Sen Sa’idu ya kira Alhaji Tahir ya sanar masa yadda ake ciki, Suna tare da Ummi a lokacin kuma ta jiyo abunda uncle Sa'idu ya fa’da, mik’ewa tayi ta lalubi hijabin sallar ta dake gefe, Ta dubi Husnah dake k’ok’arin sa wayarta cike da kidimewa tace mata,

“Tashi ki rakani gidan su Aliyah..”

Adaidai kuma lokacin Senator Sa’idu ya sake kiran Alhaji Abubakhr don sanar dashi....

•••••. ••••••. ••••••

Ranar alkhamis aka turo nemarwa Shamsuddeen auran Fa'iza, cikin girma kuwa daman an tambayeta tace eh tana sonshi hakan yasa Baba Suleiman yace an basu suka dire kud'in nagani ina so duba hamsin sannan aka sanya rana cewar nan da gama level 3 d'inta za'a sha biki idan yazo ta karasa karatun acan gidan mijin. Yayin da itama Aliya aka turo daga gidan su Mu'azzam itama kuma an bashi domin tace tana son shi, sun bada dubu hamsin suma. Sai dai bayan 'yan tambaya sunzo sun tafi Baba Suleiman yaje ya sanar da gwaggo nan take tambayar sa waye Shamsuddeen bayan ya gama gaya mata ko wanene Mu'azzam, sam Baba Suleiman ya manta da wancan case d'in dan haka yace.

“Kai gwaggo Shamsu fa na gidan malam Al'amin makotanki na can jakara, kinsan suma da dadewa suka dawo nan hotoro amman suna can nndc quarters.”

Tunda gwaggo ta gano waye Shamsuddeen take faman zabgawa Baba Suleiman harara amman bai kulaba har sai da ya dire zance, yana shirin dorawa da zancen irin abubuwan aikhairin da suka samu Shamsu a yanzu sai kawai yaga ran gwaggo a had'e hakan yasa shi yin gum da bakinsa. Cikin tsantsar b'acin rai yaji tana magana tamkar shine yayi abun a baya koda yake shima ai da laifinsa tunda yace jira yake Shamsu ya dawo yaje ya kaisa police station.

“Shamsuddeen ya koma kuma? Ohhh saboda yanzu yayi kud'i ya koma Shamsuddeen ya gama lekamin jikata shine kai yanzu zaga zagaye ka had'a Fa'iza dashi ko? Kai d'an nan kaji tsoran Allah, toh bari kaji na gaya maka Fa'iza ba zata auri Shamsu ba duk maitarku da son haka, kaje ka sanar da ita ta kawo kowaye sannan karta sake kira min sunansa a cikin gidan nan.”

“Gwaggo wallahi tallahi bani na had'a su ba can suka had'a kansu ba tare da na sani ba ki tambaye su.”

“Suwa zan tambaya bayan kai? Karka raina min hankali ka nuna min halinku na zamani, nace maka babu wani Shamsu da zuriyata zata aura mishi koda kuwa shine yafi kowa arziki a duniya, ita banda Fa'izar munafukace ta kwace Sahal shine yanzu ta lallab'a zata auri Shamsu da ya gama wulakantamu? A gabanta akace ya bamu hakuri amman da yake d'an zamanine sai yaki saboda ya raina kowa, toh ku mayar musu da kud'in su indai ina da rai bazata aure shi ba munafukai kawai.”

Gabaki d'aya jikin Baba Suleiman yayi la'asar musamman da yaji gwaggo na had'awa dashi tana yi musu kud'in goro. Mik'ewa yayi kai tsaye d'akin su ya nufa ya tarar da su suna kwance akan gado ko wacce da waya a hannunta, ya kallesu tare da kiran su.

“Kuzo d'akina ina son ganin ku.”

“Toh Baba.”

Duk suka amsa a tare kafin su mik'e tsaye ko wacce ta zaro mayafi ta yafa sannan suka jera suka tafi sai kallan juna suke kowa yana murmushi a tunanin su zancen kudin auren za'a yi musu. Zaune suka tarar dashi a bakin gado yayi shiru hannunsa dafe da goshi sukaje suka zauna a gefensa ya gyara zaman tare da jan numfashi ya kalli Aliya.

“Aliya an kawo kudin na gani ina so an kuma sanya rana nan da sabuwar shekara insha Allahu sai dai ba'a fitar da month d'in ba bare kuma date, za'a jira sai lokacin yazo sai duk a saka. Ke kuma Fa'iza ina son ki bud'e kunnanki da kyau kiji ni, sakamakon abinda ya faru a baya tsakanin Shamsu da Aliya gwaggo ta kasa mantawa hasalima tana kan bakarta na cewar sai na kai kararsa police station, kiyi hakuri ki canza wani a matsayin mijinki domin tace duk cikin zuciyarta babu wanda zata iya bashi koshine mai arzikin duniya, kinga kuma mahaifiyata ce dole sai na bi umarninta ke kuma dole kibi nawa umarnin, dan haka kiyi hakuri da Shamsu za'a mayar masa da kud'in sa.”

Ba Fa'iza kadai ba hatta Aliya sai da kirjinta ya buga jin maganar Baba Suleiman, kafin kace komai tuni hawaye suka fara zirarowa daga cikin idanun Fa'iza wacce ta kasa cewa komai. Sallamarsu yayi suka fito kai tsaye Aliya ta wuce d'akin gwaggo Talatuwa fuskarta cike da damuwa taje ta zauna tana turo baki tare da harare-harare gwaggo tace.

“Aliyan Mu'azzamu ya aka yi ne?”

“Gwaggo kika ce Faizaah ba zata auri Shamsu ba saboda me?”

“Au! Wai ke kin manta duk abinda ya faru a baya? Koda yake lokacin ke ba cikakken hankali gareki ba keda Fa'izan shi yasa har kuke muradin ya shigo cikin zuriya ta.”

“Na sani gwaggo babu abinda na manta, amman banga dalilin da zai sa ki hana Fa'iza auran shi ba tunda ai ba ita ya yiwa ba, kuma ko a baya can Fa'iza bata damu da abinda yayi min ba dan haka ki barta ta auri zab'in ranta karta ce kinfi sona akan ta.”

“Ke dalla can matsa kema da baki san ciwon kanki ba, lokacin da abin ya faru aka ce ya bani hakuri dan iskanci yaron nan yaki saboda ya raina ni, amman shine yanzu ko kunya baiji ba zai zo yace zai auri jikata to ban bayarwa, yaje can ya samo wata.”

Ganin yadda gwaggo take faman kafewa yasa Aliya matsawa kusa da ita tare da kammo hannayenta tana murzawa, cikin kwantar da kai murya k'asa-k'asa idanunta na k'ok'arin zubar da hawaye tace.

“Haba gwaggo me yasa kike son hana Fa'iza abinda take so? Karki zama irin kakan nin nan masu takurawa jikokinsu yazo ki mutu a dinga murna, dan Allah gwaggo karki hana mata zab'in ranta kinga kece uwata kece ubana a duniyar nan, idan kika hana wannan auran za'a ce Faizaah ce bakya so bayan kuma a baya kinmafi ji da ita, wallahi gwaggo indai ni kike so ki kwatowa 'yanci kin riga kin gama tunda kina bani duk abinda nake so. Please gwaggo ki barsu suyi aure ni ba son Shamsu nake yi ba, ko Sahal dana so a bayan ai kinga da ya nuna bani yake so ba na hakura duk da cewar na shiga firgici time d'in. Gwaggo na ki barmu mu auri mazajen da suke son mu suke kaunar mu domin shima Shamsuddeen din na lura yana son ta sosai.”

Kawar da kai gwaggo tayi domin ba zata iya yafewa Shamsu ba saboda kin bada hakurin da yayi a baya, sam Aliya ba tayi zaton abin yakai haka ba tayi-tayi amman gwaggo ta kafe kaida fata ba zata bawa Shamsu auran kowa a cikin family d'inta ba, haka Aliya ta barota ta koma d'aki inda ta tarar Umma na faman lallashin Fa'izar wacce take ta razgar kuku kamar an aiko mata da mutuwa.

Kasa cewa komai Aliya tayi har Umma ta mik'e ta bar d'akin, ganin ta kuma fashewa da kuka yasa Aliya tabbar da lallai Fa'iza ta mutu akan Shamsu, kome ta gani take sonsa haka oho. Ita dai kyawunshi ko dukiyarsa sam basu rudeta ba bare taji sonshi yazo mata amman tana jin Mu'azzam har cikin zuciyarta, tana jin zata iya zama dashi ko bashi da komai saboda yana da wasu nagartattun halaye da take son mijinta ya kasance.

“Fa'iza kiyi shiru ki dena wannan kukan domin ba zai sanya gwaggo canza ra'ayi ba”

Jin haka yasa Fa'iza jin wani irin zafi a cikin ranta. 'Wato ma ita Aliya murna take yi an rabasu da Shamsuddeen saboda abinda dama take son ayi tuntuni da ta gano suna soyayya kenan, lallai itace ta zuga gwaggo Talatuwa kan cewar karta bari a bata Shamsuddeen saboda abinda ya faru, idan banda haka ta ya za'ace wannan dalilin shine zai sanya a hanata wanda zuciyarta take so? Ta bud'e ido da kyar ta kalli Aliya tare da cewa.

“Kinyi murna yanzu ko? Kinji dad'i gwaggo tace bazan auri Shamsu ba ko? Shikenan amman karki manta ni daman bani nace ina son Sahal ba, hasalima b'oye kansa ya dinga yi saboda yasan abinda zai yi ba mai dad'i bane. Amman bari kiji na gaya miki abinda baki tab'a sani ba, na fara son Shamsu ne tunda na taso na fara ganinsa a jakara, lokacin da na gano ke yake so nayi kuka sosai ba tare da kowa ya sani ba, shine yanzu na samu hankalinsa yazo gareni kinje kin cewa gwaggo karta yadda ko? Shikenan Aliya nagode.”

“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wannan wace irin magana ce kike min Fa'iza? Kinsan yanzu yadda naje muka fafata da gwaggo akan ta hanaki auran Shamsu, idan na hanaki me zanyi dashi ni tunda ban tab'a sonshi ba? Bari kiji ko a baya da nace ku rabu na d'auka zaki min HALACCI ne akan abinda yayi min, da naga ba zaki iya ba ai rabuwa nayi daku sai yanzu kice wani nice naje nace da gwaggo tace kar a baki shi? Toh akan wane dalili? Karki min sharri Fa'iza domin Allah ma sai ya saka min saboda babu sanya hannuna akan lamarin ki da Shamsuddeen.”

“Haka daman zaki ce.”

“Lallai Fa'iza kin fara bani mamaki wallahi, zargina ma kike yi kenan akan nice na rabaku ko?”

“Ai ba zargi bane wannan abun a bayyane yake.”

Nanfa suka hau fad'i in fad'a kafin daga bisani su fara kokawa abinda basu tab'a yi ba tun tsawon tasowarsu tare, su Hydar dasu Humaira sune suka shigo d'akin nasu suna ganin abinda yake faruwa suka fara kiran Umman su suna cewa Yaya Fa'iza da Yaya Aliya suna fad'a. Umma ta taho da gudu ranta a matuk'ar b'ace lokacin su Hydar sunje sun sanarwa da gwaggo itama ta fito suka had'u a dakin, Umma ta rabasu da kyar dan sai da ta wanke Fa'iza da mari ganin yadda take fiffik'alewa tamkar mai iskokai. Gabaki d'aya sunci uban juna saboda kowa ya kufula zuciyoyinsu sai tafasa suke karo na farko da suka samu sab'ani har haka ta faru.

“Ashe baku da hankali marasa mutuncin yara kawai, uban meye ya had'a ku haka.?”

Duk suka yi shiru kowa sai faman jan numfashi yake, kafin Umma ta kalli Aliya dake mammatsa kafad'a wadda da alama ta bugu a gurin tace.

“Aliya meya had'a ku.?”

Kamar tace a tambayi Fa'iza sai kuma taga rashin da cewar hakan tunda ita aka tambaya, nan fa ta fara bawa Umma labarin yadda aka yi.

“Kawai wai bayan kin fita shine nake bata hakuri akan abinda ake shirin yi mata, shine kawai ta fara cewa ai nice naje na zuga gwaggo akan tace dole sai an raba ta da Shamsu, nace mata bani nace amman yarinyar nan ta dage nice shine kawai muka fara kokawa.”

Gwaggo dake gefe a tsaye ta fara tafa hannuwa tana salati tare da kallon Fa'iza tace.

“Ke! Kiji tsoran Allah, kinga yadda yarinyar nan tasani a gaba akan dole sai na barki da wannan marar kunyar yaron, saboda naki yadda tayi fushi ta baro dakina shine zaki ce itace ta zuga ni? Ohh ni dama bani da ra'ayi sai abinda aka zo aka ce dani ko Fa'iza? Toh bari kiji na gaya miki ba zaki auri Shamsu ba na fad'a na k'ara fad'a baxaki auresa ba, wato ya gama kalle 'yar uwar ki shine ke kuma zakije kema ya gama kare miki kallo ko? Toh ban yadda da wannan banzan tsarin ba, idan kinga kin auri Shamsu toh tsarin Allah ne babu yadda zanyi amman tabbas ba zaki aure shi ba indai za'a zo a gaya min.”

Aikuwa Fa'iza ta kuma fashewa da kuka abin ya sake daurewa su Umma kai, wai yau Fa'iza ce take wannan abun akan namiji, ko Aliya da ake tunanin zata yi wannan haukan ba tayi ba sai ita da koda wasa ba'a yi tunanin zata yi ba. Dan tsabar haushi Umma barin d'akin tayi dan sosai Fa'iza ta bata kunya, tama rasa a cikin wane sahu zata saka wannan lamarin kishi ko hauka oho. Aliya ma fita tayi ta koma d'akin gwaggo takaici duk yayi mata yawa, ji take tamkar taje tayi yadda zata yi ta fara soyayya da Shamsuddeen kodan ta gumawa Fa'iza taji haushin da gayya, sai dai sam a ranta bata sha'awar yin hakan saboda ko kad'an bata son suyi wani abun da zai bayyana cewar ta soshi amman da sai ta nunawa Fa'iza karyarta, zata rabu da ita ta dena shiga harkarta koda da hira ne tunda abin yazo da haka.

Gwaggo ta zauna bakin gado tana ta yiwa Fa'iza fad'a akan abinda ya faru, tana nuna mata koda wasa karta sake bada kofar da zai sa wani ko wata suzo su shiga tsakaninsu da 'yar uwar ta, sai dai fa abin da kowa be gane ba akan lamarin nan indai akan Shamsuddeen ne zata iya rabuwa da kowa saboda yazo ya bud'e mata k'ofar soyayyarsa ya lasa mata zuma ta kuma lasa batajin akwai wanda zai iya rabasu. Gwaggo ta gama b'ab'atunta ta fita aka bar Fa'iza wacce ta zaro wayarta tana shirin turawa Shamsu sako.....
🏽*Wannan littafin na kuɗine, kiji/kaji/kuji tsoron ALLAH karki/karka/karku shiga haƙin wanda ya saya, kema idan kina buƙata ki nema wannan Numbers ɗin._👇🏻*

*08030811300*
*07067124863*


_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*_MISS XOXO🧕🏼_*_


_*NO: 45A_*

_”Things will get worse before they get better. But when they do, remember who put you down, and who helped you up.”_

Tana gama rubutawa ta tura masa tare da komawa kan pillow tana matsar kwalla, gabaki d'aya taga 'yan gidan sun tsane ta yanzu. Shi kuwa Shamsuddeen yana cikin mota Yazeed na tuki zaije ya kaishi airport zashi lagos kayansa sun iso yana son yaje ya rarraba su kawai yaga sakon Fa'iza. Gabaki d'aya rasa gano akan dalilin da yasa tayi masa wannan sakon yayi dan haka cikin murmushi ya kalli yazeed yana karanto masa sakon ya karkare da cewa.

“Na rasa dalilin da yasa tayi min shi Dude.”

“Kila ko ta gano cewar ba ita kake so ba shi yasa take tuna maka.”

“Dallah can waya ce maka bana son ta? Bana sonta zance a kai kudun aure gidan su?”

“Ohh haka nefa ashe ankai kud'i, toh ka tambayeta mana ni ka isheni da tambayar da bansan amsa ba.”

Murmushi Shamsuddeen yayi tare da yi mata reply da.

_”Life without mistakes is like, education without books. What is wrong with you sweetie?”_

_”I'm not lazy. Someone just stole my motivation.”_

_”Just be yourself. Let people see the real, imperfect, flawed, quirky, weird, beautiful, magical person that you are.”_

“Mubar wannan maganar mu koma ta gaskiya, a nan gida gwaggo tace bazan aure ka ba saboda abinda ya faru tsakaninka da Aliya, Childhood is like being drunk, everyone remembers what you did, except me. Ya zanyi? Losing a relationship hurts. But losing yourself in a relationship hurts longer.. I love you Yaya Shamsuddeen.”

“Everything in life is temporary. So if things are going good, enjoy it because it won't last forever. And if things are going bad, don't worry. It can't last forever either. Ina hanya zanje lagos, idan na dawo zanzo gidan, Love doesn't need to be perfect, it just needs to be true. Sai nazo sleep well sweetie.”

Dai-dai lokacin suka karaso filin jirgi na tashi da sauna na malam Aminu kano, Yazeed ya rakashi ya gama komai sannan sukai sallama tare da jaddada masa cewar ya kula da komai yasa ido akan komai, da haka suka rabu Shamsuddeen ya wuce ya shiga jirgi shi kuma Yazeed ya koma mota ya tayar ya wuce gida.

••••••. •••••••. •••••••

A dai-dai lokacin senator Sa’idu ya sake kiran Alhaji Tahir ya d'auka had'e da sanyawa a speaker lokacin Ummi ta gama zura hijabi a jikinta,

“Salam Alaikum Yaya! Nace yanzu Alhamdulillah Sahal ya farfad'o yanzu, Amman gaskia yana cikin wani hali, Shin anyi masa wani abun ne anan gidan? Domin likitan yace harda hauhawar jini/Blood pressure, ga chronic ulcer, harda allurorin depression aka yi masa, cutuka dai kala-kala wallahi Yaya..”

Tunda yafara magana idanun Ummi ke ambaliyar hawaye, Gaba d’aya gurin yayi tsit, Shi kansa Alhaji Tahir d'in dauriya kawai yake yi amman cikin zuciar sa babu dadi, cikin kwantar da murya yace da Sen Sa’idu.

“Subhan’Allah! Allah ya tashi kafad’un sa..”

Ummi sanin tsattsauran ra’ayin mijin ta tasan ba zai tashi suje gidan su Aliyan ba, Hakan yasanya tai hanzarin gyara zaman hijabin, ta zura takalmi tana cewa,

“Alhaji na tafi gidan su Aliyan, Husnah zo muje.”

Bai bata amsa ba, Sai ma canza channel da yayi na tv ya kamo labarai, Husnah ta zura hijab tabi bayan Ummin su, Gidan Malam Rayya suka fara shiga Ummi ta yiwa Asabe bayani a tak’aice saboda tana son tayi mata rakiya, Daga nan driver ya rankaya dasu gidan su Aliya, Gaba d’aya Ummi a hargitse take ko a mota ta kikkira Sen Sa’idu kan ya bata Sahal yace bai farfad’o ba amma dai numfashin sa ya dawo normal ya fita daga coma stage. K’arfe uku dai-dai direba ya ajiye su a k’ofar gidan Baba sulaiman. Husnah ce tafara shiga da sallamar ta sai su Ummi suka bi bayan ta, A tsakar gidah suka tarar da Gwaggo bararraje akan taburma tana goge goro a magogin sa, sai bin wakar d'an k'wairo take yi a ‘yar radion dake gefen ta, Husnah ta tsugunna tana gaishe ta, Gwaggo ta washe bakin ta da hakoran suka koma kalar goro tace,

“Asma’u ce agidan sannun ki su Fa’izan na ciki.”

Sai a sannan ta lura dasu Ummi dake gaishe ta, Ta amsa da fara’a tana tambayar Asabe da,

“Yasu Malam Rayya da yaran?”

“Lapia suke Gwaggo..”

Asabe ta amsa tana bin gidan da kallo, Husnah ta mike ta nufi d'akin su Fa’izah tabar su Gwaggo suna gaisawa har Umma tazo itama suka gaisa dake ba sanin su tayi ba, sai a baki, Ruwa takai musu da sauran cincin din da suke yi dik sati saboda baki. Cikin haka kuwa su Fa’izah suka je suka gaishe su, Ummi sai bin Aliya take da kallo, Ta rasa mai yasa Sahal baya son ta sai Fa’izah, Gashi yarinyar nada nutsuwa da son shiga cikin jama’a. Suna gama gaishe su suka koma da’ki harda Husnah, Husnan dai sai hira suke da Aliya, Fa’izah bata magana, gaba d’aya kowa na gidan haushin sa take ji, musanman Aliya, Tayi mata tanadi na musanman a zuciar ta, lefin ta yafi na kowa aganin ta. Ummi ta zayyanewa Gwaggo abunda ke tafe dasu, Asabe ma ta d’ora da nata bayanin bayan Ummin tagama. Gwaggo tai shiru tana sauraron su, gaba d’aya sun ‘daureta tarasa ta cewa. Cikin sauke nannauyar ajiyar zucia tace,

“Duka su biyun ma an kawo kud'in su, Fa’izan cema nace a mayarwa yaron nasa.”

Ummi ta dafe kirji tana ware idanuwa, cikin tsantsar mamaki tace da Gwaggo,

“Wai har Fa’izan ma wani ya bada kud'in auren ta?”

Umma ta daga kai don tabbatarwa Ummi zancen Gwaggo gaskia ne, Gwaggo Talatuwa ta b'azgi goron dake hannun ta,

“Eh wannan munafukin yaron shamsu d'an gidan Bintu matar malam Al’amin Buhari shine ya kawo kudin, bayan kuma a da Aliya yace yana so, tak’i yadda shine don tsabar tsagwarar iskanci ya lek’a ta a bandaki, yanzu kuma yake son Fa'iza..”

Asabe tayi shiru kawai don taga har yanzu Gwaggo taki yadda shamsu bai lek'a Aliya da gangan ba, Ummi dake gefen Gwaggo ta k'ara muskutawa kusa da ita tace,

“Gwaggo ni dai dan Allah ku temaka ku bawa Sahal Fa’izah wallahi yana cikin wani hali saboda kaunarta, yanzu haka yana asibiti a can Abuja, ya yanke jiki ya fadi a gidan ‘kanin babansu, sen Sa’idu da dake jakara d'innan, To wallahi Gwaggo har yanzu bai farfad'o ba, numfashin sa dai yadawo don da ya shiga coma stage..Gwaggo ki duba lamarin dan girman ALLAH”

Ummi ta shiga rok’an Umma da Gwaggo, Asabe na taya ta. Gwaggo data gaji da magiyar su tace,

“Ni dik kun d'aure ni da jijiyoyin jiki na wallahi! Ni ban hana Faiza auran Sahal ba, musamman da na tabbatar da dama can Sahal bai tab'a cewa yama son Aliya ba, A kira Fa’izan aji daga bakin ta idan harta amince toh shikenan ai Sahalu yaron kirki ne..”

Hakan kuwa akayi, Umma ta dokawa Fa’izah kira, Fa’izah ta fito da sauri, Gwaggo tace ta zauna, Fa’izah ta rakub’e a gefe tamkar munafukar da aka tisa a gaba, kanta a duk’e sai kace sabuwar amarya sai raba idanuwa take yi. Gwaggo ta kwararo jawabin su Ummi ta gayawa Fa’izan tak'ark'are mata da,

“Toh gasunan a gaban ki, Sai kowa yaji ta bakin ki, Ba cewa nayi lallai ba ban kuma ce dole kiyi ba, Shin kinason Sahal zaki aure shi ko kuwa?”

Fa’izah tai shiru, Gwaggo Talatuwa ta sake tambayar ta har sau uku, Nan ma Fa’izah tayi shiru. Daga ‘karshe Gwaggo tace,

“Idan bakyaso kice A’a! Babu lallai babu dole, kin yi shiru kamar kin ajiye kayan wanki..”

Nanma Fa’izah tai shiru, juyin duniyar nan Gwaggo tayi Fa’izah ta’ki cewa komai. Gwaggo tace ta tashi ta tafi, Ummi ta mike kawai, tace dasu,

“Toh shikenan Gwaggo, babu komai! Haka ALLAH yayi, tasa kaddarar kenan, Inna Asabe muje ko? Ina Husnah ne? ta fito mu tafi..”

Umma ta kira Husnah, Aliya tayi musu rakiya har suka shiga mota suka tafi, A mota ummi ke ta jera tsaki kamar tsaka minti kadan tace,

“So makaho ne, baya shawara idan zai mamaye ka, Ni wallahi nafi yiwa Sahal sha’awar Aliya, yarinyar faran-faran kowa natane, ALLAH ya zab’a masa abinda yafi alkhairi..”

Husnah da Asabe suka had’a baki wajen fadar,

“Ameen ya ALLAH!”

Haka suka koma gidah rai a b’ace, Minti kad’an Ummi ta balbale kowa da fad’a. Baban su Sahal kuwa bar mata gidan yai gaba d’aya.

Toh haka ma gidan su Aliya, minti kad'an Gwaggo Talatuwa taja tsaki, ta b'azgi b'arin goro tana cewa,

“Amma anyi ja’irar yarinya, Bari baban naku yazo nasa ya lallasamin ke, ja’ira da idanu zuru-zuru tun na haihuwa. Ke banda sakarai ce ga mai sonki da gaskiya zaki wani tsaya akan wanda bashi da buri sai na ya ganku.”



Please Login or Register in order to submit comment