Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita da Fa'iza ba. Wanka suka yi sannan suka shirya, abincin suka ci sannan suka kwaso kayan da Sahal ya kai musu suka nunawa Umma da gwaggo suka kuma shaida musu cewar sun rabar da wasu kayan. Sam hankalin Umma bai kwanta da Sahal ba, Saboda ganin yadda yake barnar kud'i sai taga tamkar da biyu yake son Aliya, amman bata nuna ba a zahiri tabar abin a ranta kafin tayi bincike akansa, Aliya kamar Fa'iza take har cikin ranta dan haka batajin zata yi abinda zai tozartar da rayuwar Aliya musamman da take marainiya.

Kayan kwalam da makulashen suka babbawa yaran kayan sawar kuma kowa yasa nashi a cikin kayansa. Cikin kwanciyar hankali suka ci gaba da gudanar da rayuwar su suna kuma jiran fitowar jarabarwarsu, gashi Baba Suleiman yace musu zasu yi jamb saboda zasuci gaba da karatu yana son su samu zurfaffen ilimi yadda zasu dogara da kansu...

•••. •••.

Zaune take a tsakar gida yau kam fad'a ya tashi dan ko magana kayi mata toh zaka sha masifa, Umman su Fa'iza tayi tambayar tayi har ta gaji amman gwaggo tayi mata biris sai ma harara da take binta dashi idan ta wuce. Baba Suleiman ne ya shigo gida bakinsa dauke da sallama, tunda yaji taki amsawa yasan akwai matsala cikin ladabi ya karasa gurinta ya zauna yana gaida ita, bata amsa ba sai ce masa tayi,

“Rike gaisuwar na yafe, yanzu kai fisabilillahi sai fama nake yi da kai cewar ka maidani gidana amman sai faman raina min wayyo kake yi? toh yau ba sai gobe ba ina son na koma gidana na gaji da nan d'in.”

Shiru Baba Suleiman yayi bayan ya sauke nauyayyan numfashi, cikin kunnansa ya fara sosawa tare da cewa,

“Kiyi hakuri gwaggo yanzu unguwar nan taku ba zata shigu ba.”

“Saboda wane dalilin ne zai sanya mu kasa shiga jakara? Karfa ka maidani wata bican, wannan karon ba zaka min wata dabara ba, Bari kaji na gaya maka yau a dakina zan kwana.”

“Allah gwaggo titi ake yi muku, yanzu bakiga yadda unguwar tayi ba, su kansu makotanki an rushe gidan kuma ina kyautata zaton zasu dade basu dawo ba, dan Allah kiyi hakuri kici gaba da zama tare damu hankalina yafi kwanciya.”

Tabe baki gwaggo Talatuwa tayi tare da maida kai can gefe tace masa,

“Wane makotan nawa ne suke rushe gida? Kaga karka raina min hankali nice na haifeka bawai kaine ka haifeni ba.”

Murmushi kawai Baba Suleiman yayi tare da cewa,

“Gidan malam Al'amin Buhari.”

Nan da nan gwaggo ta had'e rai tare da kallan Baba Suleiman wanda kansa yake a kasa yana jujjuya mukullin motarsa tace,

“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu mutanan nan da wannan salon suka zo? Ince ko wannan d'an iskan yaron ya dawo daga inda sukaje suka b'oye shi? shi yasa suka tashi daga gidan dan sun san shi muke jira ya dawo.”

Dariya ce ta kusa kwacewa Baba Suleiman amman ya had'iye, Saboda baya son ta kuma jin wani haushin tunda lallabata yake yi. Harara ta sake dank'ara masa da alama amsarsa take jira amman yaja baki yayi shiru sai da tace dashi,

“Ba magana nake maka ba kayi min shiru?”

“Kiyi hakuri gwaggo ban san abinda zance miki ba, amma insha Allahu zan binciko naji inda suka koma.”

Daga haka mik'ewa yayi ya shiga d'akinsa, yana shiga Umma ta fito tabi bayansa gwaggo ta bita da kallo tare da tab'a baki cikin ranta tace. 'Wai ita mai miji an tashi an bishi sad'af-sad'af, Allah yasa kifi son shi dan idan yafi son ki toh ba zaki barshi ya kuma yin wani auren ba’.

•••. •••. •••.

Sanye ta fito cikin dogon hijabi ta nufi hanyar fita, 'yar karamar kofar dake kusa da gate nan ta bud'e kafin ta fita sai da tayi addu'ar fita daga gidah,

“: بِسْمِ اللَّهِ ، تَوَكَّلْتُ عَلَى اللَّهِ ، وَلَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِ لَّا بِاللَّهِ

Pronunciation: Bismil-lah, tawakkaltu alal-lah, wala hawla wala quwwata illa billah

Translation: I depart with Allah's name, relying on Him. It is Allah who saves us from sins with His guidance (the ability to do so)

Benefit: Prophet ﷺ also said, “If a man goes out of his house and says (This Du’a) it will be said to him, 'this will take care of you, you are guided, you have what you need and you are protected.' The Shaytan will stay away from him, and another Shaytan will say to him, 'what can you do with a man who is guided, provided for and protected’.

[Abu Dawud and Tirmidhi]”

kafin ta sanya k'afarta ta dama a waje. Mota ta nufa wacce ke a jiye a bakin gate d'in, kafin tasa hannu ta bud'e kawai taga an bud'e mata da alama wanda yake cikin motar shine yasa hannu ya bud'e mata. Zama tayi tare da kallansa fuskarta cike da murmushi tace,

“Yayan Shamsu maimakon ka barni na bud'e da kaina shine har sai ka wahalar da kanka?”

Yaya Garzali dake shirin kunna motar yayi 'yar dariya tare da cewa,

“Haba Umma meye abin wahala a cikin bud'e miki k'ofa? muka yiwa matayen muma bare kuma mahaifiya.”

Wani murmushin ta kuma yi tare da cewa,

“Toh ai ba d'aya bane muda su k...”

Yayi saurin katse ta, ta hanyar cewa,

“Umma kiyi shiru dan Allah, duk wani abunda zamu yiwa wasu toh naku na daban ne, ni 'yan mata nawa na bud'ewa murfin mota kuma daga ‘karshe su yaudare ni sai dai kawai naji ance nayi hakuri wani ya riga ni. Wannan matar tawa itama da na aura wallahi d'ar-d'ar nake yi da ita saboda kar sai na zurma cikin kaunarta itama tazo tana juyani daman gashi yanzu ta fara laulayi sai tsirfar jaraba, wani lokacin har motar take cewa ba zata hau ba wai warin petur sai dai naje na aro machine din abokina na kaita inda take so.”

“Kayi ta addu'a, duk wadda kagani tana da juna biyu toh daman can da irin yanayin da zai zo mata, kuma rabonkane wahalar dan sai kayi shi, nasan duk abinda zata yi ko tace maka toh karka damu domin ba yin kanta bane ciki babu abinda baya sanyawa.”

“Toh Umma insha Allahu zanci gaba da yi. Yanzu gidanwa zan fara kaiki?”

“Muje na fara dubo hajiya uwani daga nan sai ka kaini hotoro d'an marken idan ka dawo da yamma sai ka biya ka d'akko ni mu dawo gida.”

Kad'a kai Yaya Garzali yayi tare da daukar hanyar gidan hajiya uwani, suna zuwa basu dad'e ba yaje ya kaita gidan aminiyarta wato hajiya Maryam mahaifiyar Khadija wacce suke fatan had'a auranta da Shamsu. Yana ajiyeta ya tafi da nufin idan aka idar da sallar isha'i zaije ya d'auketa su koma gida domin yanzu su Umma sai godiyar Allah dan katon gida suka sake anan hotoro tsamiyar boka, babu abinda babu a gidan komai Abba da Garzali sun zuba mata dan Shamsu cewa yayi ayi mata duk abinda batayi zaton zata samu ba a cikin gidan ta.

“A'ah'ah sannu da Zuwa aminiyar yau kece a gidan?”

Cewar hajiya Maryam mahaifiyar Khadija wacce take nunawa Umma hanyar shiga parlour.

“Kinganni tuntuni nake wak'ar zanzo amman ban samu fitowa ba, saboda anyi aiki a can gidan gonar auta an zuba shanu, toh da yake nike kular masa da b'angaran sai da na tabbatar mutanan sun gama komai sannan nace da yayansa yau zai kawo ni kwana biyu bamu gaisa ba ko a waya.”

Umman Shamsu ta ‘karasa maganar tana gyara zamanta, Hajiya Maryam ta zauna kujerar kusa da ita suka fara gaisawa inda take cewa,

Kai masha Allah kaga matashin saurayi mai dogaro da kai, wai yaushe zai dawo ne?”

“Uhmmm kinsan ya gama karatunsa wanda ya tafi yi, toh kuma sai ya sake yin waya cewar ya d'ora master's, kina ganin yayansa har yanzu project supervisor d'insa sai wahala yake bashi, amman naji shi abban su yace nan da can ba d'aya bane shi zai iya riga yayan nashi kammalawa, Saboda su basu da bakin ciki.”

“Kai ai abinda ake yi a k'asar nan ya isa wallahi, Allah sarki Shamsuddeen akwai kwaxo gashi dai yaro dashi amman dubi yadda ya tara kadarori kamar wani babban mutum.”

Murmushi Umma tayi tana jin dad'i idan ana yabon autanta ruhinta har wani narkewa yake saboda tsabar jin dadi.

“Ai shi yasa nake son daya dawo ba za'a ja lokaci ba za'a yi bikinsa shida Dijama dan karma ya dawo ya fara daukar zugar abokai kinsan 'yan uwa.”

“Hakane kam Umman Shamsu dan nima nan ina nan ina kular miki da 'yar taki dan har yanzu na hanata kula kowa nace mata ba yanzu ba.”

Dai-dai lokacin Khadija dake lab’e tana jinsu ta had'e fuska tamkar tana gabansu ta lailayo rantsuwa ta dire a zuciyar ta, kafin ta watsa hannu baya tana mita ciki-ciki ta ‘karasa dakin ta, a lokacin wayar ta dake kan wata y’ar madedeciyar katifa wadda da alama tata ce ta hau ‘kara, da sauri jin ringing tune din yasa ta ‘karasawa ta ‘dau wayar, wanda sunan dake rubuce a jikin screen ‘din wayar ke ‘dauke boldly da kalmomin, ‘My Whole world...’..

Sake shake muryar ta tayi, tana magana dana cikin wayar, wanda lokaci d’aya zaka gano saurayin ta ne, dubada yadda take sake shak’e murya tana shagwab’a, basu wani jima suna wayar ba ta ajiye tana sake bararraje wa akan katifar ta, har wani rufe idanuwa takeyi, da alama kalaman da saurayin ya zuba mata ba kad’an bane....

‘Bangaren Salman Sa’ad kuwa suna gama waya da Khadija ya ajiye yana sakin tsaki, Abokin sa Faysal dake gefe ya saki daria yana fadin,

“Shegen kaya halan y’ar anacen ka ce?”

Salman dake shan lemon dake hannun sa ya kara kurba ‘daya kafin ya dubi Faysal yace dashi,

“Itace mana, Khadija, yarinyarnan ta uzzura wa rayuwa ta da yawa wallahi, kana kallo missed calls bakwai tamin kafin na kira ta..”

Faysal yai daria yana dukan cinyar sa, kafin cikin daria ya sake cewa,

“Wai har yanzu sunan ta yana nan a yadda kai saving da Khadija Dan Marke? Aboki ko ‘dan My Khady ka mayar mata mana, Naga ita kace da me tayi saving ma..?”

Salman ya saki tsaki, kafin cikin takaici yace,

“Wai wani Her wold world, kaji mahaukaciya...”
🤝🏽🤝🏽

_ALLAH KA JIK’AN IYAYEN MU AMEEN😭🤲🏻_
——
*R/S/18/19/S*

*MISS XOXO🧕🏼*


Dariya Faysal yayi yana bubbuga kafa a kasa tsabar mugunta, Salman ya kallesa cikin b'acin rai yace,

“Ba wannan ne zai baka haushi ba, kasan yarinyar nan har yanzu taki bari naje gidan su, kullum sai tace min ba yanzu ba wai Maman su ta hanata kula samari na bari duk lokacin da aka ce ta fara zata min magana.”

Ya k'arasa maganar yana jan d'an guntun tsaki tare da cusa wayar tasa a aljihu ransa duk a b'ace. Faysal ne ya bugi gefen kafad'ar Salman tare da cewa,

“Toh kai abinda na kasa ganewa shine, shin kana sonta ne kokuwa dai kara yawa kake yi da ita?”

“Wallahi nima ban sani ba Faysal, ban san tak'amaimai wane iri nake ji akan Khadija ba, ina sonta ban sani ba, bana sonta shima ban sani ba kawai dai naji ina son kulata wani lokacin, gashi idan muna waya ko idan mun had'u a hanya wallahi bana jin wani abu akanta.”

“Kai dalla can baka sonta haka kawai zaka ce bawai ka tsaya rainawa mutane hankali ba, idan banda rainin hankali ai abu uku ne zaka zabi d'aya, kodai kana so ko baka so ko kuma kawance kake da ita, meye na tsayawa yi min kwana-kwana.”

Shafa kai Salman yayi tare da huro iska daga cikin bakinsa, kasa cewa komai yayi domin babu abinda zai fad'a dan haka ya mik'e yana gyara wuyan rigarsa tare da kallan Faysal yace.

“Abokina zan wuce, idan na samu amsar tambayoyinka zanzo na sanar dakai, amman yanzu bani da ta cewa, sai anjima mu hadu a gidan kallo ya za'a buga mai zafi.”

Faysal ya tab'e baki tare da mikewa shima ya shige cikin gida.

A can b'angaren su Umman Shamsu kuwa sun tattauna maganganu ita da aminiyarta wato mahaifiyar Khadija akan yadda suke son komai ya tafi ba tare da ko wanne b'angare yaga anyi masa rashin adalci ba. Umma ce zaune akan sallaya ta idar da sallar magriba taji kira, tana dubawa taga sunan auta, cikin murmushi ta d'aga tare da karawa a kunne tayi masa sallama cikin farin ciki,

'”Assalamu alaikum Ummah nah.”

“Wa'alaikas salam d'an auta yaron kirki, ya kake?'”

Shamsuddeen dake zaune kan teburin cikin abinci a wani katafaren restaurant gabansa drink ne kawai yana sha, bayansa ya jingina a jikin kujerar yana sauraran Ummansa wadda yake jin tamkar yayi tsintsuwa yaje ya ganta, ya shafa kwantaccen bakin gashin dake kwance a hab'arsa tare da cewa,

“Umma lafiya ta kalau, sai fama da rashinku a kusa dani, ina Abba ne? sai kiransa nake amman ana cewa a kashe take.”

“Aikuwa nima kaga sai kiransa nake bana samu da yake nazo nan gidan Maman Khadija.”

Cikin murmushi mai d'an sauti Shamsu yace mata,

'”Ahh yau ankai ziyara kenan? Umma a mika min gaisuwa wajan Maman.”

Dai-dai sannan Maman Khadija ta shigo dakin hannunta dauke da tray na abincin da ta kawowa aminiyar tata.

“Gata ma kawai ku gaisa.”

Cewar Umma tana mika mata wayar. A kunne ta kara cikin kulawa itama ta fara yi masa magana, cikin girmamawa ya gaida ita ta dinga sanya masa albarka sannan ta mik'awa Umman sa, hirar sukaci gaba da yi lokacin ne Khadija ta shigo hannunta d'auke da jug na ruwan sanyi ta kawowa Umma ta ajiye mata a kusa da tray din abincin, tana k'ok'arin fita Umma ta dakatar da ita ta hanyar cewa.

“Khadija zoku gaisa da Shamsuddeen.”

Khadija ta juyo tare da zuwa kusa da ita, ranta duk babu dad'i sai dai babu wanda zai fahimta sakamakon murmushin yak'en dake saman fuskarta.

“Shamsu ga Khadija ku gaisa.”

Cikin rashin damuwa Shamsu yace.

“Okay Umma bata”

Mik'a mata Umma tayi tare da juyawa tana kallon aminiyar tata, a hankali ita kuma Khadija ta fice daga d'akin ta koma nata sai faman tsuke fuska take tamkar yana kusa da ita tace.

“Ya karatu?”

“Lafiya lau khady ya naku karatun?”

Yadda taji muryarsa sai yasa ta fara tunanin anya wannan Shamsun da ta sani ne a baya kuwa? Wannan muryar bata san ma yadda zata fassara yadda taji taba domin jikinta ko'ina sai da ya amsa, amman da ta tuno waye Shamsu da wad'annan shegun d'inkunan nasa sai ta kuma had'e rai kai kace suna tare yana ganinta, sai da ta zauna a bakin katifarta kafin tace dashi.

“Normal wallahi ai na gama tuni.”

“Secondary school kika gama ko?”

“Eh amman ai zan cigaba dan har nayi jamb.”

Shiru taji yayi har tayi tunanin ko ya kashe hakan yasa ta tab'e baki tana kallan screen d'in, still taga yana nan bawai kashewa yayi ba, ta kuma maida wayar jikin kunnata sai taji yana cewa.

“Masha Allah ai hakan yana da kyau, nasan yanzu kin kara girma ko khady?”

Tsaki yaji tayi hakan yasa shi bud'e ido tamkar yana gabanta, cikin basarwa dan kar tayi tunanin ko da nufin iskanci ya fad'a yace mata.

“Ina Umma bata wayar.”

“Bari na kai mata tana d'akin Maman mu.”

“Su khady harda warewa wai Maman mu, toh mu kuma fa? Ko an cire mu daga ciki?”

Khadija ta harari wayar ji take tamkar ta shiga cikin wayar ta shako shi, sam Shamsun baya take tunani bata san yanzu ya kerewa saninta ba, dan haka da sauri taje ta mik'awa Umman sa wayar ita kuma ta baro d'akin hankalinta na kan wayarta tana jiran Salman ya bugo mata suyi hira. Shamsu kuwa basu dad'e da Umma ba ya katse ya kira Yaya Garzali har ya bawa matarsa aunty Afiya suka gaisa kafin yace dashi.

“Kanina bari naje na d'akko Umma na maida ita gida, idan na dawo zan kiraka sai mu k'arasa maganar.”

“Toh babban Yaya a dawo lafiya.”

Daga haka suka ajiye wayoyin, inda Yaya Garzali ya tafi d'akko Umma shi kuma Shamsu daga inda yake tashi yayi ya koma hostel daman yazo nan ne dan karsu Afrah su dameshi kasan cewar duk inda yake zama ta sani nan d'in ne dai bata gano ba kuma baya fatan ta gano sabida shi sam baya wani son suyi mu'amula ko wace iri ce da mace sabida abinda Aliya tayi masa ya kasa barin zuciyarsa, gani yake kamar duka mata masharranta ne dan haka yake kafa-kafa da rayuwarsa yake baya-baya da duk wata d'iya mace..

•••••. •••••. •••••.

Result din su Aliya ne ya fito na SSCE wato ‘senior secondary school certificate na waec da neco..’ kowannen su yaci dai-dai gwargwadon yadda ake buk’ata, Dan haka tuni Baba sulaiman ya cike musu komai na jamb, Fa’iza Mbbs aka sanya mata wato ‘medicine/harkar lapia, second option kuma ya sanya mata agricultural engineering. Ita kuma Aliya da ta karanci Art ya cike mata first option dinta da Law, second option kuma Library science duka kowannen su gurbin karatun jami’ar Bayero yacike musu. Sannu a hankali kowaccen su ta dage da karatun jamb dan guntun fad’uwa, domin baba Sulaiman yace idan suka fad’i tofah yi musu aure shine mataki na gaba, ‘ABU mai labule kenan..’

Ana’i gobe zasu zana jarabawar Aliya taje gidan su ‘kawar su dake nan baya dasu wato A’ilo ‘kwaila wadda sukai boarding school tare, A’ilo nada waya dake ita batada burin cigaba da karatu, dan haka suna ‘kare karatu form master ‘dinsu dake nemanta ya turo akai magana da kudin zancen su a hannu, aka tsaida ‘yan watanni masu zuwa za’ai bikin, wayar A’ilo da ita Aliya ke karba tana waya da Sahal, kamar Kullum tana shjga gidan kai tsaye da sallama ta shjga dakin A’ilo dake kwance tana waya da saurayin ta, wato class teacher ‘dinsu na da dake sumaila, Aliya ta zabga tagumi har A’ilo tagama wayar tata, nan sukai ‘yar hirar su kafin Aliya cikin sauri tace da A’ilo,

“Aikin dai kenan, Kullum cikin waya, tun baki tafasa ba zaki k’one, wannan dai gwara ai auren ku cinye junan ku”

Ta ‘karasa fad’a tana kara wayar a kunnen ta, da alama ta kira Sahal ‘din, A’ilo ta tuntsire da daria kafin ta mike tana mik’a, sai da tai mai isarta kafin tace,

“Lokaci na ne, Dan haka nafi gaban k’onewa ma ingaya miki, inde akan malam Sadeeq ne to fa na babbake wallahi, ba gwara ni bama akan ki, gama wayar dai, bara na shjga band’aki..”

Cewar A’ilo kafin ta shiga band’akin ta dake cikin ‘dakin, Aliya kuwa tuni ta nutse cikin kogin soyayya, Dan da alama batama ji abunda A’ilon ke fad’a ba, cikin sake shak’e muryar ta tace,

“Dan Allah Ya Sahal kazo goben mu had’u a school, wallahi nayi missing ‘dnka da yawa...”

Sahal dake zaune akan kujerar ‘dakin sa, sai faman yatsina fuska yake, wayar tasa na kare a kunnen sa yana amsa Aliya, cikin tab’e baki yace,

“Zan duba nagani...”

“Uhm, uhm Ya Sahal, ni..ni kawai kazo..”

Kamar tana gaban sa, ya had’e rai kafin yace,

“Zan kai Husnah ma, dunno ko wuri ‘daya zaku yi, A’ina zaku zana...?”

“Ya Sahal ni a new site ne fa..”

Cikin sub’ucewar baki yace,

“Fa’iza fa?”

Kamar tana gaban sa yai saurin rufe bakin sa yana danne dariar data taho mai, da alama mutuniyar taku bata gano shi ba, domin ca tai,

“Ya Sahal nasan duk dan saboda bakason ganin tane yasa ka tambayi haka, kasha kurumin ka domin Fa’iza a old site zatai tata..”

Hamdalah ya sauke, jin a tare suke da Husnah, bugu da ‘kari kuma yanason sake tozali da kyakkyawar fuskar ta, cikin waskewa yace,

“Okay glad.. Till then Liya, Taya zamu had’u kenan?”

Cike da jin dadi Aliya tace,

“Zan ari wayar Gwaggo! Sai anjima Ya Sahal I love and miss you...”

“Okay bye..”

Kawai Sahal yace, kafin ya katse kiran, cike da jin dadi ya ‘daga hannuwa sama yana mai-maita,

“Yes...Alhamdulillah!”

A’ilo dake gefen Aliya ta buga tsaki tana fad’in,

“Toh Romeo ta Juliet bani wayata tunda kun gama farantawa juna rai..”

Aliya tai murmushi, tana yin ‘kas ‘kas da yatsun hannayenta kafin cikin kad’a idanuwa tace,

“Ai soyayya akwai dadi, Allah dai ya barmu da masu son mu...”

“Toh Ameen...Kuyi aure kawai..”

“Hmm! Da za’ai hakan sai nafi kowa jin dadi, Sai dai kash Baba Sulaiman yanaso muyi karatu, Kuma burin Ya Sahal ma shine yanason ya auri cikakkiyar ‘yar boko..”

A’ilo ta tab’e baki, kafin cikin rashin damuwa tace,

“Ai se kuyi tayi, lokacin da zaku kammala boko nasan na haifi yara uku ko hudu..”

‘Mtcew! Aliya taja tsaki tana tura ‘daurin ‘dankwalinta gaba, wato ture kaga tsiya, sai da ta jera tsaki uku, tanayi tanaiwa A’ilo kallon Kin renawa kanki hankali kafin tace,

“Ke fa A’ilo gwara kowa dake, ai da bari kikai ki zama babbar mace ba ‘kwailar ki ba, zaki kama ki wani aure yanzu, auren ma da ba zamu wani gyagije muyi rawa ba, Kin kama kin wani tsayar da malam sadeeq a matsayin mijin aure, bayan kinsan yadda yakewa mutane kwarji ni, banza mai kan kwa-kwa...”

A’ilo tayi dariar ta mai isarta kafin tace,

“A kwailar dai aka ganni aka susuce har aka aiko da kudin aure, a kwailar kuma zanyi aure nabar masu shi fal kirji, a kuma ‘kwailar ne zan auri shalelen maza, kuma dole a zube a gaida miji na a wajen biki, sani ne baki ga wallahi da sunji lapiyayyun hannu zasu tashi kamar funkaso..”

Aliya ta mike tana zaro idanuwa kafin tace,

“Su waye zasu tashi kamar funkaso?”

A’ilo tasa tasa hannu tana nuni da kirjin ta, Aliya ta shjga daria ba ‘kakkautawa, sai datai mai isarta kafin tace,

“Kinfi ‘karfina A’ilon Form master. Ta Malam Sadeqeqe mai komai dozen, sai kinji ni, idan Inna tadawo ki gaisheta..”

Ta ‘karasa fad’a tana zura takalmanta, har ‘kofar gidah A’ilo ta rakata, tana musu fatan samun nasara a jarabawar da zasu zana..


*WASHEGARI*

Da wuri su Fa’iza suka shirya don tafiya zana jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, Fa’iza ta shirya cikin doguwar riga baka ta yane kanta da bak’in mayafin rigar, batai wani kwalliya ba ta dai shafa jan jambaki, Aliya kuwa shigar doguwar riga tayi dinkin A shape, blue ce an mata kwalliyar pink, ta yafa mayafi pink komai pink hatta jambakin lebanta, karfe bakwai saura kwata Baba Sulaiman ya ‘debe su a motar sa, Fa’iza ya fara saukewa a old site, ya wuce da Aliya new site dake can gwarzo Road.

Tunda Baba Suleiman ya sauke ta a wajan venue d'in ta take ta faman d'aga kai ko zata hango ta inda Sahal zai bollo amman shiru, ko wacce mace idan tazo gurin takan yi k'ok'arin yiwa na kusa da ita magana amman Aliya tunda ta diro daga mota batama nufi inda suke ba bare tayi kawa, duk hankalinta yana wajan da duk tasan mota ko d'an Adam zai bollo amman shiru. Yayin da shi kuma Sahal yana zuwa yayi parking Husnah ta fito, shima fitowa yayi tare da kulle motar ya zura key d'in cikin aljihun jeans d'insa blue yasa yellow d'in riga armless gashin kasan sai sheki yake yi, da mamaki Husnah ta kallesa tare da tsayawa tace dashi.

“Yaya Sahal ina zaka kuma?”

“Rakaki venue d'in zanyi.”

“Ahhhh ka barshi ai nasan wajan kayi zamanka a mota.”

Kallanta yayi sai yaga tamkar ta gano abinda yasa shi biyo ta, amman dan ya tabbatar da ta gano ko bata gano ba sai ya yatsina fuska tare da kallan gefe yace......

——-
_Afuwan jia bakuga post dina ba, hakan ya faru ne abisa rashin ajiyayyen Page da bani dashi, dake 2 Pages din dana turo shekaran jia waccan da washegarin ta nayi su ne tun kafin rasuwar baba, Shiysa ku kaga banyi post jia ba, bugu da ‘kari kuma kunsan da glass nake amfani, sanyin nan idanun sai a slow wallahi, kuyi mana uzuri dan Allah.. wallahi abubuwanne sai a slow😢🤲🏻_🤝🏽
——
*R/S/18/19/S*

*MISS XOXO🧕🏼*


Dariya Faysal yayi yana bubbuga kafa a kasa tsabar mugunta, Salman ya kallesa cikin b'acin rai yace,

“Ba wannan ne zai baka haushi ba, kasan yarinyar nan har yanzu taki bari naje gidan su, kullum sai tace min ba yanzu ba wai Maman su ta hanata kula samari na bari duk lokacin da aka ce ta fara zata min magana.”

Ya k'arasa maganar yana jan d'an guntun tsaki tare da cusa wayar tasa a aljihu ransa duk a

Please Login or Register in order to submit comment