Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*ABUJA*

*CEDAL CREST HOSPITAL’s LTD*

Gumi ne ke faman kwarara ajikin Sen Sa’idu duk kuwa da sanyin na’urar Ac dake busa ofishin likitan, Dr Kola yai murmushin gefen baki kafin yace da Sen Sa’idu cikin harshen turanci,

“Honorable kenan! Karka damu da yawa, ‘Dan ka zai samu lapia da zarar kun biya masa bukatar sa..”

“Kana nufin kace rayuwar sa tana cikin hatsari idan ba’a bashi abunda zuciar sa ke soba?”

Cewar Sen Sa’idu, Dr Kola ya gyada kai alamun tabbas haka zancen yake, Sannan ya mik’awa Sen Sa’idu tissue don ya goge gumin dake ambaliya a fuskar sa sai naso yake yi. Salati Sen Sa’idu ya shiga rafkawa, wayar sa ya zaro ya kira wani Personal Assistant dinsa,

“Yes Salis! Ka.. kayi booking min next flight yanzu na kano, Gani nan zan taho airport.”

Yana gama wayar ya mike ya tafi bayan yayiwa dr kola sallama, dakin da Sahal ke kwance ya leka yaga he’s still unconscious, cikin sauri ya wuce mota aka jashi zuwa airport. Kafin isha’i ya isa kano..

*KANO*

Gab da isha’i driver ya d’akko Sen Sa’idu daga airport basu tsaya a ko’ina ba sai gidan su Sahal, luckily Alhaji Tahir yana nan, shiga Sen Sa’idu yayi cikin gidan, suka gaggaisa, ganin sunyi mamakin ganin sa ya sanar dasu komai bai rage ba, Nan ummi dake gefe ta labarta masa komai tun farkon yadda al’amarin ya kasance har kawo wa yau da sukaje gidan su Fa’izan da yadda sukai da ita, Mamaki sosai ya mamaye Sen Sa’idu. Aka barwa Safiya zuwa gidan su Aliya.

Washe gari kuwa da safe Sen Sa’idu ya tasa Husnah a gaba ta raka shi gidan su Fa’izah, sanin tsattsauran ra’ayi irin na Alhaji Tahir, domin tun jiya ya kwaso rantsuwa ya dire kan babu inda za shi.

Baba Sulaiman na gidah lokacin da Sen Sa’idu suka je, sun gaisa a mutunce domin sun san juna, Don tun kafin Baba sulaiman yayi aure yasan Sen Sa’idu domin sun yi zaman unguwa d’aya a baya dasu Gwaggo a jakara. Sen saidu ya fayyace masa abunda ke tafe dashi, Baba Sulaiman ma ya zayyane masa abunda ya sani. Nan ma aka sake kiran Fa’izahhh, Tanbayr duniyar nan nanma tayi shiru babu cas bare As. Baba Sulaiman ya mike zai faffala mata mari Sen Sa’idu ya hana shi, ya dubi Fa’izah bayan sun mike zasu tafi yace da ita,

“Toh d'iya ta! Komai sai da tunani, Na baki lokaci daga nan zuwa ‘Karshen sati ki gaya mana zuciar ki. Karki takurawa kanki, ‘Dan adam ba’ayi masa dole..”

Yana gama fad’a ya fice husnah na biye dashi hakama Baba Sulaiman. Nan suka bar Fa’izah a tsugunne kamar wadda taje ro’kon gafara..

Ni Nana Hafsat nace I cannot jeep taking Panadol for this couples undetected headache Oo.. Fili gare ku Masoyan KAI MIN HALACCI, 🔥
___

🤝*Wannan littafin na kuɗine, kiji/kaji/kuji tsoron ALLAH karki/karka/karku shiga haƙin wanda ya saya, kema idan kina buƙata ki nema wannan Numbers ɗin._👇🏻*

*08030811300*
*07067124863*


_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*_MISS XOXO🧕🏼_*_


_*NO: 45C_*


Gabaki d'aya tunanin ta ya nemi tsayawa, shi kuma sai faman kallanta yake yi fuskarsa kunshe da tsantsar damuwa da alama lamarin Aliya ne ke sake ratsa shi. Wani irin numfashin takaici ta sauke tare da gyara tsayuwa tana cizon lips tace.

“If I heard you clearly, Kana nufin kace kana son Aliya?”

“Tausayinta nake ji sweetie, kince taso Sahal amman daga baya yace bece yana sonta ba. Yanzu tana son Mu'azzam har ya kawo kud'i gashi yanzu anzo ance a bata hakuri harma an d'aura masa aure, shin Aliya yanzu ba abar tausayi bace?”

“Uhmm duk inda kaji tausayi ya shigo cikin lamari toh tabbas akwai soyayya a cikin sa, Yaya Shamsuddeen ka sanar dani gaskiya shin har yanzu akwai soyayyar Sissy cikin zuciyarka?😭”

Kame lips d'insa yayi na kasa da hakoransa yana matsawa sai faman yi yake bashi da alamar cewa komai, hakan yasa Fa'iza tabbatarwa da zuciyarta cewar dama alfarma kawai yake yi mata ba wai sonta yake yi irin na Aliya ba. Ganin yaki magana yasa ta juya gida da gudu tana kuka, Baba Suleiman da yake sallama da bakinsa da suka kawo mishi zancen matsalar Mu'azzam ya bita da kallo cike da mamaki. Shamsuddeen yana k'ok'arin shiga mota yaji Baba Suleiman ya dakatar dashi, cike da jin nauyinsa Shamsuddeen ya tsaya sai yaji duk bazai iya had'a ido dashi ba, cikin sanyin jiki Baba Suleiman yake masa magana.

“Ya akai naga mutuniyar taka ta wuce tana kuka? Ince dai lafiya ko?”

Shamsuddeen ya shafa keyarsa ta kasan hularsa tare da sunkuyar da kai yace.

“Baba hirarku muka jiyo na zancen Mu'azzam, toh shine wai dan nace ina tausayawa Aliya zan had'asu duka na aura, shine tasa kuka tana cewa daman nafi son Aliya sai ta ruga gida.”

Baba Suleiman yaja numfashi tare da jijiga kai yace.

“Allah k'adiran Alamanyasha, shine kadai yasan abinda yake nufi da wannan al'ammura da suke faruwa a cikin gidana. Ahmm Shamsuddeen ina son naji gaskiyar magana daga bakinga ka, domin ina son na yanke hukunci. Shin kana son Aliya har yanzu ko kuwa a'a kawai dan kaji wanda zai aureta ya fasa shine yake son had'awa da ita? Karka b'oye min gaskiya aje nan gaba abu yaki yin dad'i, ka gaya min kana son Aliya soyayyar ku ta baya tana nan har yanzu?”

Rabon da Shamsuddeen yayi gumi ina jin tun yana saida rake domin tunda Baba Suleiman ya fara kwaso masa tambaya yaji gumi yana tsattsatsowa daga cikin jikinsa. Ya dad'e cikin yin shi hakan ya tabbatarwa da Baba Suleiman cewar har yanzu yana son Aliya wata kila dan yaga bazai sameta bane yazo yace yana son Fa'iza zai aureta kila saboda ya dinga kallanta ne a matsayin Aliyar shi yasa yake son Faizaah, amman yanzu dole Baba Suleiman ya godewa Allah tunda ya bayyana masa gaskiyar zuciyar wanda yake son auran 'yarsa, da ace yazo yana raba case din miji gara ace mijin ne yake cutar matar yasan zata yi hakuri ta jure amman wani lokacin namiji bashi da hakuri tsab zai dinga yin abinda zai nakasa su.

“Shikenan Shamsuddeen shirunka ya nuna min abinda yake cikin ranka, karka damu duka Fa'iza da Aliya 'ya'yana ne kuma naji dad'i da baka b'oye min ba, kud'in auranka da ka kawowa Fa'iza sun koma kan Aliya daman kuma family d'in Mu'azzam sunce sun yafe kud'in a barmata, ita kuma Fa'iza nasan abinda zanyi, abinda nake son da kai yanzu, shin kana da gurin zama? Ina nufin kana da inda zaka ajiye matarka idan an d'aura aure?”

Sai a yanzu Shamsuddeen ya samu damar kallan Baba Suleiman amman da sauri ya dauke idanunsa saboda kunya, kamar zai nutse yace.

“A'ah Baba a yanzu bani da muhalli.”

“Toh kayi k'ok'ari kayi shi domin a cikin ragowar 'yan watannin nan da suka rage shekarar nan da muke ciki ta kare zan aura maka Aliya, sharad'i na ina son koda wasa karka nuna cewar Aliya zaka aura ina son wannan ya zama sirri tsakanin shak'ik'anka dani bana so maganar nan ta fito kana jina?”

“Toh Baba insha Allahu.”

“Yau kaje ka fara shirye-shirye ka kawo abinda Allah ya hore maka.”

“Abba na gode, sannan kud'in da na kawowa Fa'iza bana son a karb'a na bar mata halak malak zan aiko dana ita wannan d'in.”

Yaki cewa Aliya saboda tsananin nauyin abinda ya faru a d'an lokacin nan, Baba Suleiman yace a'a bazai karb'a mata ba, da kyar Shamsuddeen ya samu ya amince sannan suka yi sallama Baba Suleiman ya shiga gida shi kuma ya shiga motarsa Benz ya wuce gida kai tsaye.

Yana shiga d'akinsa ya wuce ya rage kayan jikinsa ya watsa ruwa domin ba karamin zufa bace ta jika shi, yana fitowa d'aure da alwala ya zura jallabiya ya janyo sallaya ya hau kai tare da tayar da sallar godewa Allah, ya yarda zai auri Aliya koda bata sonshi bare ma yana son idan ya aureta ya cusa mata soyayyarsa dan yaga tana da saukin kai idan ka bita yadda take, amman idan ka taho gabaki d'aya to tabbasa zaku samu sab'ani domin bata da juriya a wannan fannin. Ya dad'e a sujjudunsa yana neman zab'in Allah idan har khairan ce tare dashi Allah ya bashi juriyar shanye duk wani abu da zata yi masa, idan kuma ba alkairi tare dasu yana fatan sassaucin soyayyarta dake zuciyarsa ya basu mafita daga shi har ita harda fa'iza ma. Yana idarwa ya sake kaya zuwa kananu army color trouser da white color t.shit ya dora p.cap tare da sanya takalmi trainers fari mai ratsin baki a jiki, yayi kyau sosai ya fito a matashin saurayi maiji da kansa.

“Kai yanzu daman ka shigo amman ko motsinka banji ba?”

“Sorry first love nah zafi ne ya isheni naje nayi wanka.”

“Toh sannu da dawowa, gashi nan kud'in kwai ne aka kawo yace min dubu d'ari hud'u ne cif sai ka dauka kaje akai su banki.”

Zama yayi Umma ta kallesa kud'in ya dauka yana zurawa cikin jakar da ya taho da ita daga d'aki yana cewa.

“Bari na had'e su dana gurin Nazeefi shima d'azu ya kawo min su, idan Yaya Gazah ya shigo Umma ki bashi tunda shi yake kai su bankin.”

“Toh idan yazo na bashi.”

“Umma anfa canza min matar aure.” Cikin rashin fahimta Umma ta kallesa.

“Ban fahimceka ba, kamar ya an canza maka mata?”

P.cap d'in ya cire tare da sanya yatsansa guda d'aya a cikin hanci yana sosawa yana cewa.

“Eh wallahi Umma yanzu Aliya zan aura ba Fa'iza ba.”

Kafin ta tambayi dalili yayi saurin dorawa da bata labarin duk abinda ya faru, amman sai yace da Umman ai Fa'iza ce tace ta dena sonshi tunda daman can Aliya yake so. Ba karamin mamaki Umma ta shiga ba ta dinga juya maganar har sai da Shamsuddeen ya mik'e yabar gidan, kai tsaye ya nufi gidan su Yazeed domin yace masa daman yau bazai fita ko'ina ba a gida zai zauna yana son ya huta. A can gidan Baba Suleiman kuwa yana shiga ya wuce d'akin su Fa'iza wacce take kwance babu wanda ya sani tana ta sharb'en kuka har buga kai take yi akan gado, taji muryar Baban su yace ta bishi d'aki. Yana zama sai gata yasa ta rufe d'akin sannan ta tsuguna kanta a kasa ya fara magana.

“Nasan kinji komai da yake faruwa, ina son ya zama sirri karki sanar da kowa cewar Mu'azzam ya fasa auran, kibar komai a hannuna zan nemeku idan na gama shawara kina jina ko?”

“Eh Baba.”

Tayi maganar cikin kuka daga nan yace ta tashi ta tafi ba tare da ya kuma cewa komai ba, ta mike ta tafi shi kuma ya kishin gid'a tare da fad'awa cikin zuzzurfan tunani. Wato dai idan kana da yara mata idan basu shiga gidan miji ba baka gajiya da ganin kalubale kala-kala, yanzu dubi yadda ake ta kwallo dashi da yaransa, amman zai warware matsalar zai aurar dasu tun kafin wata mummunar kaddarar ta kuma saukar masa wacce ba zai iya yafewa kansa ba, gara ya aurar dasu komai zai faru yasan daga baya ne kuma yana ma fatan komai da zai yi ya zama alkairi a cikinsa.

••••¥. ••••¥. •••¥.••••¥

Gidan su Yazeed yaje bayan sun d'an tab'a hira Shamsudden yacewa Yazeed yai masa rakiya zuwa gidan su Aliya, Sai da sukai sallar la’asar sannan suka wuce gidan su Aliyan, Yazeed sai zagin sa yake wai ya hargitsa shi bayan hutawa yai niyyar yi ranar ba fita. A sahad suka tsaya Shamsudden yayi shopping cikin ledoji suka zura a boot suka wuce gidan su Aliya. A lokacin kuma sunyi sab’ani da Fa’izah domin ta tafi gidan Aunty Yagana ko zataji dad’in zuciyar ta. Dan haka suna zuwa ‘kofar gidan Shamsudden yasa Yazeed ya kira Aliya a waya kan tazo ta shigar dasu. Aliya ta zura hijabi lokacin duk tana cikin jimamin rashin kiran Mu’azzam. Gaba d’aya ta kira duka layikan sa biyun a kashe, batasan yana can unguwar sheshe suna cin amarci da zankad’ed’ediyar amaryar sa Rahinerth cuisine ba. A tsakar gidah ta tarar da Gwaggo da Umma akan tabarma suna hira. Aliya ta rissina tace dasu,

“Ummah zanje na shigo da bak’o wai zai gayda Gwaggo.”

Gwaggo najin ance bako ta kaikace zamanta tana gyara zaman hular kanta ta rufe gashinta daya koma fari tas kamar auduga, Lalle tsufa labari ne. Ta b’azgi goro tana murmushi tuni fara’a ta mamayeta domin tasan d’aya daga cikin samarin su Aliya ne yazo yake son su gaisa. kuma basa zuwa hannu biyu sai da mai maik’o-maik’o. Cikin dashe bakin ta daya rune ya koma ja saboda cin goro tace,

“Mu’azzamu ne ko Sahalu?”

Aliya tai daria kafin ta mike tana fadin,

“Gwaggo zaki ga ko wanene bari naje na shigo dashi..”

Fita tayi wajen su Shamsudden, Tun daga bakin kofa yake binta da kallo, gaba d’aya soyayyarta ta mamaye masa zuciya, Sai yanzu ya tabbatar itace ginshik’in rayuwar sa. Murmushi tayi musu, ya basar yana gyara zaman p.cap dinsa. Yazeed ya dube su duka biyun kafin yace,

“Secretary Aliya..”

“Na'am Sir Yazeed, Barkan ku da rana..! Oga Sir mijin Sissy to be ina miko gaisuwa..”

Yazeed ne ya amsa mata, Shamsudden yai murmushi kawai, a zuciar sa yace.

“Mijin ki dai yarinya..”

A zahiri kuma yace,

“Ki mana iso please..”

A tare suka shiga tana gaba suna biye da ita har tsakar gidan. A tare suka zube shida Yazeed suna gaishe da Gwaggo da Ummah, suka amsa kafin Ummah ta mike ta shiga kitchen dan kawo musu ruwa da meat pie, Tana ajiye musu kuwa ta koma d'akin ta. Domin idan har bak’in Gwaggo ne to bata zama awajen saboda girmamawa da kuma karrama Gwaggon a matsayin ta na uwar mijin ta. Gwaggo sai raba idanuwa take domin ta kasa gane ko su waye, ita dai tasan wa’innan dangin larabawa ne domin daga Yazeed har Shamsudden kyawawa ne bana yarwa. Ganin ta kasa gane ko suwaye yasanya ta juya wajen Aliya tana mata kallon ‘karin bayani. Kamar daga sama tajiyo muryar Shamsudden na shaida mata,

“Gwaggo su ogagogina ne na wajan siwes, babban ogan shi kin sanshi ma, Shamsu ne na gidan Malam Al’amin Bu...”

Bata ‘karasa fa’da ba, Tusa ta ‘kwacewa Gwaggo Talatuwa a jere guda uku ji kake, ‘Siit, Fuss, ‘birrr..’

Kowannen su yai ‘k’ok’arin danne dariar sa banda Yazeed da ya daure ya mik’e ya tsiri wayar ‘karya yana amsa wa da 'hello’ ya fice waje can ya shiga babbaka daria ba ‘kakkautawa. Aliya da Shamsudden kuwa kowanne mazewa yayi, sai a sannan Gwaggo ta farga da aika-aiken da tayi, tai hanzarin kallon Aliya, Aliya ta maida mata da kallon karki damu Gwaggo kowa yana gocewa ya sau tasa ko ka shirya ko baka shiryawa. Cikin waskewa Gwaggo tai dauriyar cewa dashi,

“Toh-toh marar kunya har ka iya zuwa ka ganni ko? meke tafe da kai? Idan ma akan auren Fa’izah ne toh ka kwana da sanin wannan aure ba zai yiwu ba wallahi, ka kalli bulus a da ka kuma ci banza a yanzu, inaaa wallahi, wane mutum, Ahir d'inka wallahi dan a gabana aka haifeka yaro..”

Ta ‘karasa fada tana matse hanci domin warin tusar tata bata gama wucewa ba, Shamsudden ya sake langab’ar da kansa cike da ‘kaskantar da kansa yace,

“Dan ALLAH Gwaggo kiyi hak’uri ki kuma saurari bayanai na, ki dubi girman ALLAH ki yiwa zancena auni a mizanin basira..”

Gwaggo tai ‘kwafa tana karkada ‘kafa, cike da basarwa tace,

“Ina jinka, ka kuma yi sauri domin akwai shirin dana ke saurare a radi’oo na (radio).”

Shamsudden ya shiga sanar da ita dukkanin abunda ya faru a ranar da idanuwan sa suka janyo masa wannan ta’a sa, Aliya dake gefe ta shiga nazari ta kuma yi na’am da tabbas bada gangan ya lek’a taba, idan ma haka ne komai ya wuce. Shamsudden yai ta kwararo zance ya ‘kark’are da,

“Wallahi tallahi billahi Gwaggo kamar yadda na shaida miki, gudumata naje d'auka, kuma na rantse da ALLAH banga Aliya ba, domin na ‘dakko kenan zan sauka daga kan katangar ta ‘kwala ihu, ni kuma wallahi bansan ihun menene ba, na dauka na neman agaji ne, juyawar nan da zanyi idanuwana suka sauka akan na Aliya, kuma na rantse da Alllah kallo d’aya na mata na ‘dauke kaina nayi saurin runtse idanuna wallahi tallahi banda idanuwanta da mukai kallo d’aya gata a tsugunne idan na kalli jikin Aliya kada ALLAH ya bani ikon tashi daga wajen nan. Wallahi tallahi billahi karshen gaskia ta kenan Gwaggo idan na kalli wani sassa na jikin Aliya kada ALLAH ya bani ikon tashi daga wajen nan. Wallahi tallahi gata a zaune bayana gabas yake kalla, band’akin da take kuma a kudu ne, Tana sakin k'ara na juya muna hada idanu na rintse idanu na, ALLAH shine shahidi Gwaggo.

“Jikina na rawa na durgo kasa, banida nutsuwa, Bansan me ta gaya muku ba naga kun shigo gidan mu kuna maganganu, Tabbas a lokacin bani da tacewa domin har agaban ALLAH nasan ni ne da lefi, shin menene lefi na? Lefi na shine haura katangar wani gidah ba tare da na nemi amincewar su ba, na biyu kuma dole Aliya taga lefi na saboda nace ina sonta tace bata ra’ayina nasan dole ta ‘dauka da gangan nayi, lefi na na uku shine rashin baku hak’uri, domin a lokacin na hau doron zuciya rai na yayi matukar b'aci jin sharrin datai min wai na kalle ta..”

Yana magana yana sharce zufa Aliya dake gefe itama na sharce nata, Gwaggo duk sai tayi laushi, k’afafuwan sa ya sanya a ‘kasa alamun kneeling down, ya sake rissina kai cike da girmamawa yace,

“Gwaggo ni Shamsudden Al’amin Buhari ina mai had’aki da girman Allah ki dubi darajar sa badan ni ba kiyi hak’uri, ki yafemin komai ya wuce, nayi lefi na amsa lefi na, Kiyi hak’uri dan Allah, Allah ya huci zuciyar ki keda Aliya ku yafemun bana son Allah ya d'auki rai na da haushi na a zukatan ku, ku gafarce ni please...”

Aliya ta fashe da kuka, ganin k’ima da daraja da kud’i da aji da kyawu da da da... Na Shamsudden CEO, ya ajiye komai a gefe yana neman gafara, cikin rawar murya tace dashi,

“Ni ce zan baka hak’uri Shamsudden! Wallahi har gaban abadan wannan batun ya wuce, domin xuciya mai HALACCI bata manta alkahiri komai girman sharri. Kayi mun alkhairai kala-kala a rayuwa ta, shin wacece ni da bazan yafe maka ba? Komai ya wuce inaso ka yafemin nima, wallahi kuruciya ce a lokacin, kuma kaga bazan yi zaton bada saninka kayi min ba. Dan Allah ka yafemin nima, har gaban abadan wannan zancen ya wuce. Allah ya yafe mana gaba d’aya. Domin ada dinma dana dauka da sani kai haka, lokacin da son maso wani ya rufemin idanu ne, Gidadanci da toshewar basira duk sune sila, ka yafemin duk kanin abubuwan da nai maka a baya, domin idan da mai babban lefi cikin mu nice, domin ni nayi sauti mai kara wanda ya karkato hankalin ka gare ni wadda ta zamo musabbabin komai, nayi zaton a lokacin kallo na kawai kake yi, Dan Allah Shamsudden ka yafemin duk kanin kurakuren da nai maka a baya kawo yanxu...”

''Na yafe miki ni tuntuni, yanzu ma zuwa nayi na bawa gwaggo hakuri dan nasan ban kyauta mata ba da ban bata hakuri ba a lokacin.''

Gwaggo ta karkace ta kuma gyara zama tare da cewa.

''A'ah Shamsu rabu da ita, sai kace ita kaxo bawa hakurin ta zake sai bayani take yi. Naji ka bani hakuri amman karka sake naga yanzu ka sake girma ince can garin daka koma sake turaraka suka yi ka koma haka?''

Murmushi Shamsuddeen yayi a lokacin Yazeed ya dawo ya zauna a inda ya tashi yana ta danna waya.

''Gwaggo kenan, basu turara ni ba amman dai garin ba irin nan bane koke kika koma can sai kin dawo kamar Aliyar ki.''

Gwaggo Talatuwa ta washe baki tana dariya tare da kallon Aliya wacce itama dariyar take hannunta toshe da baki.

''Ni in zama Aliya d'an nan ai bazan dinga fita ba saboda samari.''

Duk suka yi dariya anan ne kuma Yazeed ya mik'a mata ledojin da ya taho dasu yanzu da ya fita yana cewa.

''Gwaggo gashi nan inji Shamsuddeen.''

Kallan ledojin tayi tare da murmusawa tana mika godiya, Shamsuddeen ganin ta karbi hakurin da ya bata yasa shi jin dad'i ya saci kallan Aliya wacce take d'aurawa Humaira d'ankwali, Yazeed yayi saurin mik'ewa yana cewa.

''Toh gwaggon mu bari mu tafi Allah ya kara girma da lafiya.''

Gwaggo ta dinga amsawa da amin tana bude ledar gaban ta ko jira su fita bata yi ba. Suna fita Aliya tabi bayan su dan raka su hannunta rike dana Humaira. A bakin motarsu suka tsaya ta tsaya itama daga nesa tana yi musu godiya, Shamsuddeen ya karka ce yana tambayar ta ina Fa'iza tace dashi tana can unguwar su gidan aunty Yagana, ya kad'a kai yana jin tamkar yace mata yanzu fa itace zabinsa amman yana tuna gargad'in Baba Suleiman hakan yasa ya daure be kwafsa ba suka shiga mota suka tafi....
🏽*Wannan littafin na kuɗine, kiji/kaji/kuji tsoron ALLAH karki/karka/karku shiga haƙin wanda ya saya, kema idan kina buƙata ki nema wannan Numbers ɗin._👇🏻*

*08030811300*
*07067124863*


_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*_MISS XOXO🧕🏼_*_


_*NO: 45D_*


Suna tafiya Yazeed na dariya kamar cikinsa zai yi ciwo, tun Shamsuddeen yana tayashi har yayi shiru dan yaga abin bana karewa bane. Sai da yayi mai isarshi sannan ya bar dariyar yana kallon Shamsuddeen wanda yake faman harararsa yace.

“Dude wallahi kakar matarka akwai abin dariya, koni rabon da na karkace nayi iska a bayyane wallahi harna manta, amman ita tsofaitsofai da ita gamu a gurin amman ta saketa.”

“Toh malam bakaga yanzu itama ta fara abubuwa irin na yara ba?ai ayi mata uzuri kawai, ni kaina dan ta yarda dani bakaji yadda na dinga kwaso rantsuwa ina direwa ba bare kuma wata tusa abinda baka san zai fito bama”

Shi dai Yazeed dariyarsa yaci gaba da yi kafin daga bisani suci gaba da hirarsu har Shamsuddeen yaje ya kaishi gida sannan shima ya wuce gidan Yaya Garzali da alama yana cikin nishad'i. Bayan yaje ya dawo ne da daddare yana kwance a d'akinsa ya kira Fa'iza, tamkar bazata d'aga ba sai dai taji tana son jin abinda zai ce mata hakan yasa sai da ta kusan tsinkewa sannan ta samu damar d'agawa tare da yin shiru taki cewa komai, sai shine taji muryarsa a sanyaye yana bata hakuri.

“Sorry might be a small word I know, but, surely there is a meaning behind sorry, I know the fault was mine sweetie, I understand that it was there in time, I am sorry for whatever happened between me and you, sorry for making it that way, sorry for doing things I did not say hope you will forgive me. Abin ya dami zuciyata da naga kin gudu kin barni kina kuka.”

“Crying is the only way my eyes speak when my mouth can't explain how things made my heart broken..”

“Toh wai duk menene ya kawo wannan kukan sweetie? Daga cewa zan had'a ku na aura shikenan zaki fara kuka uhm? Please kidena kuka kici gaba da addu'a Allah ya sanadamu da abubuwa mafi alkairi, ina so ki tashi yanzu kiyi alwala kiyi sallah ta nemar mana zab'in Allah nima bari na tashi nayi kinji?”

Fa'iza tasa yatsunta ta sharce hawayen fuskarta tare da amsa masa sannan taji yana cewa da ita.

“Sweetie close ur eye's and go to sleep for angle are there for u to keep, karki sanya wata damuwa a cikin zuciyarki night is a wonderful opportunity to pray, to love, to care to sleep and thank God for all the blessing we relieved. Good night and sweet dreams.”

Aikuwa taji dad'i sosai akan wannan maganar da yayi mata, hakan yasa ta lumshe ido tana ji ya katse kiran sannan itama ta zare wayar daga jikin kunnanta ta fita dan yin alwala, a lokacin Aliya na wajan gwaggo.

Tun daga wannan lokacin Shamsuddeen ya fara yin baya-baya da yin hirar soyayya da Fa'iza sai dai ko zai yi sai ya dinga yin nasiha-nasiha, wa'azi-wa'azi, shawara-shawara haka yake yi mata har zuciyarta ta fara sanyaya tanaji a ranta cewa koda Allah yayi basu auri juna ba zata karb'i kaddara amman zuciyarta tafi bata cewar itace mallakin shi, kuma ba zai tab'a had'asu da Aliya ba dan ba zata so suyi zaman kishi tare ba, wannan saurayi kawai suka had'a dubi irin case d'in da ya biyo baya inaga an had'a miji abin ba

Please Login or Register in order to submit comment