Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai hankali wallahi sam ba irin Shamsu bane da ya raina mana hankali ja'irin yaro kawai, wai har yau yaki baro inda ya gudu saboda yasan abinda ya aikata d'an iska k'ank'ani da shi yasan komai.”

Dai-dai lokacin da tayi maganar ita kuma Fa'iza ta shigo d'akin dan haka taji zagin da gwaggo ta yiwa Shamsu ranta kuma ya sosu, sai da ta zauna nesa da gwaggon sannan tace.

“Haba gwaggo ya zaki yi ta zagin bawan Allah bayan da ba haka kike masa ba? Wallahi nasan bakin dawowa yayi ba, kawai yanayin karatu ne.”

“Toh sannu wadda aka zagi kanin baban ta, ni zaki zauna kina karantawa kabali da ba'adi? Na fad'a d'in d'an iska zoki rama masa dan naga yadda kike b'ata rai tsab zaki iya zagini.”

Cewar gwaggo tana faman zazzaga masifa, itama Aliya tashi zaune tayi tana kallan Fa'iza dake gefenta tana matse lemon tsami a cikin kofi, cikin takaici Aliya tace mata,

“Wai ke Fa'iza dan Allah me yasa bakya son laifin Shamsu ne ha? Duk lokacin da aka sako zance irin wannan indai aka fadi laifinsa saiki fara karesa, ince a gakan idanunki kinga ya hawo saman soro bare kice sharri ne.”

Ganin yadda suka sanyata gaba kowa da irin abinda yake cewa akanta sai kawai ta mik'e ta bar musu d'akin, duk da tasan cewar Shamsu yayi abin a zargesa amman tunda Umman su ta warware komai tasan bada saninsa hakan ta faru ba, amman ya zata yi tunda wad'anda aka yiwa laifin sunki su fahimta? Mamanta ce ta kalleta bayan ta gama matsar lemon taje ta tace kasan cewar duk kannanta suna makaranta ya sanya suka shiga can d'aki inda maman take tambayarta,

“Fa'iza ki sanar dani abinda yake faruwa, bana son kiyi min karya ko ki b'oye min wani abun, ni mahaifiyarki ce baki da wadda zaki tunkara da matsalarki ko wani damuwarki da zai warware miki komai cikin sauki ba tare da kinje kin tonawa kanki asiri ba, ina lura dake tun sanda kuka dawo hutu akwai abinda kike b'oyewa a zahiri da bad'ininki, shin menene matsalarki da ta Aliya.?”

Numfasawa Fa'iza tayi, tabbas tasan duk duniya babu wanda ya cancanci jin sirrinta bayan mahaifiyarta, dan haka cikin sanyi jiki tace mata.

“Haka ne Mama, daman akwai wani wanda bansan ko wanene ba, tun kafin mu tafi boarding ya kawo min kayan provision da yawa tare da cewa na kular masa da kaina, Mama wallahi ban san ko wanene ba har yanzu, sannan ranar visiting ya aiko min da turaruka bari na d'akko miki ki gansu, rashin sanin ko waye shine yasa naki amfani da abinda ya kawo min saboda gaskiya bana san lokacin da zaizo naji beyi min ba.”

Tashi tayi bayan ta gama maganar, can bayan wardrobe d'inta Mama ta janyo ledar taje ta kaiwa Maman tare da zazzage mata dan ta gani. Sosai Mama tayi mamakin ganin irin tulin kayan da Muhamman S yake aikowa da Fa’iza su, kayane masu tsadar gaske da kuma kyau, cikin zaro idanuwa Mama ta dubi Fa’iza tana ‘daga wani mai na coco butter kafin tace da ita,

“Haka kayan ke da yawa? Shin ko da wasa wani a nan jakara bai tab’a furta yana son ki ba?..”

Fa’iza taja numfashi kafin ta sauke tace,

“Gaskia Mama babu, idi mai gurasa ne da ‘dan asabe mai kayan miya...”

Mama ta jaddada kai, Fa’iza ta cire tagumin data Zabga tace,

“Kuma kinga Mama duk cikin su ba mai halin da zai ta kashe wannan uban kud’in, ni sai nake ganin ko..”

Tai shiru bata ‘karasa ba, Mama dake son jin ‘karashen zancen tace,

“Uhum! Ina jinki sai kike ganin me?”

Nan Fa’iza ta shiga bata labarin Shamsu, da duk abunda yafaru, ta ‘karasa da,

“Sai nake ganin ko shine Muhamman S din dake aiko min da sak’onnin nan..”

Mama ta kad’a kai, jin abunda Fa’iza tagama zayyane mata, cikin hikima ta shiga wayar mata da kai, Kan halin rayuwa da samarin zamani, ta ‘kark’are da,

“Yanzu duk ki ajiye kayan nan da ake miki aike dashi, kar ki ‘kara tab’a wani aciki ko amfani dasu, har sai shi Muhamman S din ya bayyana miki kansa, Ina fatan kingane?!”

Fa’iza tai saurin kad’a kanta alamun eh kafin tace,

“Insha Allahu Mama bazan ‘kara ba..”

“Yawwa toh Allah ya yi muku albarka, yasa ku kare karatun ku a sa’a, ya baku mazaje nagari, Allah ya ‘kara kare ku daga sharrin mutum dana aljan..”

“Ameen Mama..”

Da wannan suka shiga wata hirar ta daban...

**Da safe Aliya ta shiga ‘dakin da Gwaggo talatuwa take, dake su acikin gidan suke kwana itada Fa’iza, Gwaggo kuma na ‘dakin waje, nan ta iske Gwaggo jan carbi tana gyangyadi Aliya ta shiga tana y’ar wakar ta, kafin ta zauna kusa da Gwaggo tace,

“Tsohuwa mai ran ‘karfe, Hajia Gwaggo Talatuwa kakar Faizeze da Aliya matar Sahal..”

Gwaggo dake bacci tai saurin farkawa tana sakin wata siririyar tusa jikake,
‘Siiit...’

Aliya tai hanzarin toshe hancin ta, tana duban Gwaggo kafin tace,

“Gaskia Gwaggo Aji down ce ke, yanzu ana abun arziki sai ki bada iska, Haba Gwaggo to nama fasa fad’ar abunda ya kawo ni..”

Gwaggo ta wani maze kafin ta dubi Aliya tace,

“Uban kowa yana tusa ja’ira, ai cuta na fitar, yanzu me yakawo ki ‘daki na ne ma?”

Aliya tai narai-narai da idanuwa kafin ta dubi Gwaggo, cikin murya tausayawa tace,

“Gwaggo dan Allah ki ce da Baba Sulaiman mu koma gidan ki na jakara, Allah sahal kunyar zuwa gidan nan yake Shiysa inaga bai zoba, amma da acanne Allah Gwaggo kinsan sai ya isheki da zuwa, kayan ‘kwalam da makulashe kuwa sai kin gaji dasu, Kinsan za’ai ta kawo mana, Amman dubi yanzu ko Muhamman S din Fa’iza ai kinga tunda mu kazo nan bai kawo komai ba..”

Gwaggo ta kad’a kai, alamun ta gamsu, domin matukar suna jakara ko Aliya zata d’ebo magana dai ana aiko musu da kayan dad’i, na maneman Aliyan, domin Gali mai tsire ma duk talata sai ya aika musu da tsire kuma ‘daurin Gwaggo na daban ne, Gwaggo na cikin tunani ta tsinkayo muryar Aliya na faman rokon ta da,

“Dan Allah Gwaggo kinji? Ki cewa Baba Sulaiman zaki koma gidan ki dan Allah..”

Gwaggo ta amsa da Toh! Ta aika aka kira mata Baba Sulaiman da daddare bayan ya dawo daga wajen aiki, ta sheda masa zasu koma jakara, Shi dai baso yake ba, domin hutun su Fa’izan ma ya ‘kare, ba kuma yasan sai sun koma ba dadewa su tafi, abar Gwaggon ita kadai, ya amsa da toh kawai dan kada ya mata musu, gobe ko jibi zai maida su, A haka dai har su Aliya suka koma makaranta basu koma can unguwar tasu ta jakara ba...



_Kunji ni shiru ko? Afuwan pls😊👏🏻 wallahi mahaifina aka kwantar a asibiti, Ina barar addu’oinku daga bakunan ku masu albarka, Allah ya bashi lapia da duk marrasa Lapia Ameen😘😍 Thank you all_




_MISS XOXO🧕🏼_

——
_ASSALAMU ALAYKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUH, YA KUKE SISTERS? INA FATAN KUNA CIKIN KOSHIN LAPIA, INA MIKO GAISUWA TA A GAREKU DA BABBAR MURYA, HAKIKA KUNYI MIN HALACCIN DA BAKI KO ALKALAMI BA ZAI IYA RUBUTA DINBIN GODIATA A GARE KU BA, NAGODE DA ADDU’OINKU WAJEN NUNA ALHININ RASUWAR MAHAIFINA, NAGODE MUKU DA KIRA NA DA KUKAI, MESSAGES, TA WHATSAPP DA SAURAN SOCIAL MEDIA APPLICATIONS, ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI, NAGODE ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA BAKU LADA. ALLAH YA JIKAN BABA DA RAHAMA, YASA ALJANNATUL FIRDAUS MAKOMACE A GARE SHI, ALLAH YA SHAYAR DASHI RUWAN ALKHAUTHARA, DA SHI DA SAURAN IYAYENMU DA SUKA RIGAMU DA GIDAN GASKIYA🤲🏻ALLAH YA JIKAN SU, YA BAMU HAKURIN RASHIN SU, NAGODE, NAGODE, NAGODE. JAZAKUM ALLAHU KHAIRAN🥰..._

_Salam alaykum warahmatu Allah wa barakatuh! Thank you all for your beautiful du’as of peace and comfort. Jazakum Allah khairan for your supports... Your words/prayers have been very helpful to me in this time of grief. I’m having a hard time putting my gratitude into words. Jazakum Allahu bil jannah.. Allah ya bada lada! Allahummagfirli jami’e mautal muslimeen!🤲🏻💕_
_NANA HAFSAT MUHAMMAD HADEE(MISS XOXO)_


*N/O/14/15/S*

*Haka* rayuwa taci gaba da gara musu ta kowanne b'angaren, kowa da abinda yake cikin zuciyarsa da kuma abinda yake buri. Wani hutu dasu Aliya suka yi ne Baba Suleiman ya kwashe su suka tafi garin malam wato dangin gwaggo Talatuwa, sunyi murna da farin cikin zuwa kauyen, Dan an nuna musu soyayya tak'in karawa, ga samari da suka dinga sha'awar son kasancewa da 'yan matan wato Fa'iza da Aliya amman babu wanda yake iya yi musu magana saboda class d'in ba d'aya bane, kusan satinsu uku sannan Baba Suleiman yaje ya d'akko su ya maida su Hotoro, kwanaki biyu da dawowarsu ya d'auki Aliya da Fa'iza ya kai su Bunkure wato dangin mahaifin Aliya, nan ma an karbe su hannu biyu-biyu duk da cewar sunyi fad'a ganin yadda jikar tasu ta girma amman babu aure.

Inna Adama ce dake zaune kusa da mai gidan ta wato kakan Aliya ma'ana mahaifin da ya haifi babanta tana bud'e masa langar tuwo da miya, sai da ta tura masa komai a gabansa ya faraci sannan ita ta samu guri ta zauna, kallon Aliya tayi wadda ke zaune tana cin gyad'a marau, Fa'iza kuma na cikin rumfa tana sallar isha'i, muryar inna Adama ta katsewa Aliya cin gyad'ar da take yi ta hanyar cewa,

“Wai ke Aliya zaman me kuke yine keda Fa'iza haka baku yi aure ba? Dan Allah ki duba yadda kukai rid'a-rid'a (manya-manya) daku amman ace ko maganar aurenku ba'a yi har yanzu, dubi su d'ahare dasu Altine duk kin girmesu amman ko wanne da yara uku ke kin zauna ko uban me kuke yi ban sani ba.”

Toshe baki Fa'iza tayi wadda yin sallamarta kenan daga sallah dariya ta taho mata jin yadda inna Adama take cewa uban me suke jira. Aliya kuwa hannu tasa ta rik'o hab'arta tare da kurawa inna Adama ido, sam taji ta kasa cewa komai saboda yadda taga inna Adama ta had'e rai ita a dole ga wadda take cikin b'acin rai,

“Wai ba kyajin ina yi miki magana ne, ko kin zama bebiya ne?”

“Toh inna Adama fisabillahi me zance dake? Tunda kikaga har yanzu bamu yi aure ba ai Allah ne beyi ba, shifa aure bawai kiransa ake yi ba no! Shi yake zuwa kuma ko kanaso ko baka so sai kayi shi, toh ki taya mu da addu'a kawai bafa samarin ne bamu dasu ba, akwai su wallahi kawai dai sai mun gama karatu sannan zamu fito dasu.”

“Ikon Allah, karatun banza karatun wofi, kaji min yarinya mu karatun bokon da bamu yi ba meya rage mu gamu a raya muna ci muna sha?”

“Hahahaha unbelievable..!”

Cewar Aliya tana wata muguwar dariya, jin abinda tace ne yasa inna Adama kallanta tare da cewa,

“Kardai ki zageni da yaran arna ya hudawa dan naji kin fara yi min.”

“Tab! toh inna kinga rashin ilimin boko yaja miki na fadi abu kin juya shi da cewar zagi ne, ya kamata ki daure koni na dinga koya miki dake da malam.”

Allah ya kiyaye mana, kuma kema yanzu nayi nadamar maidake can dan nasan ba zasu aurar dake da wuri, kuma yanzu ma ba zan bari ki koma ba sai da auran ki, anan kinfi yin samari masu sonki dan har yanzu d'an Bala mai markade be dena tambayar kina ina ba.”

Tsikaro baki tayi jin abinda inna Adama ke cewa, tasan tsab zasu iya!aurar da ita a gobema ba sai an wani ja lokaci ba, karasowar Fa'iza kusa da ita ne yasa ta cewa,

“Sis dan Allah bani da samari a can gidan?”

“Kina dasu mana bama d'aya ba ba biyu ba.”

Cewar Fa'iza tana murmushi, cikin tab'e baki inna Adama tace musu,

“Oho kwaji dashi, mudai ba zaku raina mana wayyo ba, Allah ya kaimu safiyar gobe da rai da lafiya wallahi zanje nace da d'an Bala ya fito ayi.”

Tamkar Aliya ta d'ora hannu aka haka take ji sai faman turo baki takeyi, malam dai bece komai ba tuwonsa kawai yake ci harma baya son asako shi, dan yasan ko kashe Aliya za'a yi yanzu ace sai tayi aure za'a dawo mata da rai toh ta gwammace a barta ta mutu,

“Wallahi Babu wani d'an Balan da zan aura tab d'i, ni wallahi sai na dena zuwa gidan nan idan har kunsan auran dole zaku yi min.”

“Kanki kika yiwa ai dan kin dena zuwa nan, Saboda mune tushenki yarinya.”

Inna Adama ta fad'a, kafin Aliya tayi magana Malam Ishaq yayi gyaran murya yana sud'e hannu tare da cewa,

“Adama dan Allah kibar yarinyar nan haka haba, kin zauna sai faman biye mata kike tamkar wata sa'ar yinki.”

“Atoh gaya mata dai Malam, dan Allah Malam auran soyayya kuka yi da inna ko kuma dai ladan gona ce aka baka? Naga ta dage nima sai tayi min irin auran.”

Fa'iza na gefe banda dariya babu abinda take yi, sosai Aliya take wasannin kakanni dasu fiye da tunanin mai karatu.

“Aisha ai bakya buk'atar amsa.”

“Toh kuwa a dena cewa za'a min auran jika nayi ko auran dole ko sadaka.”

“Aliya kiyi shiru dan Allah, kibar bayin Allan nan su huta.”

Ganin yadda Fa'iza take rokonta shine yasa ta yin shiru tare da cewa,

“Nayi shiru, taso muje dandali nasan yanzu ana can ana wasanni.”

Dukansu suka tashi daman Fa'iza hijabin da tayi sallah yana jikinta, Aliya ce kawai ta shiga d'aki ta d'akko nata sannan suka yiwa su inna Adama sallama suka fita, tunda suka isa wajan kallo ya koma kansu, sanye suka cikin wata purple d'in atamfa da ratsin fari da baki a jiki iri daya komai da komai daman haka Baba Suleiman yake yi musu, baya banbanta su ko a wajan takalmi duk iri daya yake siyo musu. Sun jima sosai dan har sai da inna taje ta kira su sannan suka koma, kwanciya kawai suka yi sai bacci dan gabaki d'aya a gajiye suke barema Aliya da sai da ta shiga ta tuna baya daman tana drama club a can makarantarsu.

Kwanansu biyar suka koma gida lokacin anata yi musu shirin komawa makaranta, komai suce zasu tafi dashi, harda su k'anzo da busassjiyar taliya da shinkafa itama suka dafa aka shanya ta bushe da dambu, komai suka gani haka suke tattarawa su jefa cikin kayansu kasan cewar final year suke zasu zauna zana jarabawar waec da neco.

Suna murna suka koma makaranta saboda sunsan daga wannan ba zasu sake ba. Gadan-gadan suka shiga karatu wannan karan babu batun wasa, kowa so yake ya fito da sakamako mai kyau saboda a samu a shiga makarantar gaba da sakandire.

Wata rana da yamma wajan karfe hud'u aka aiko kiran Aliya da Fa'iza, cikin d'oki suka taho suna murna dan sun san Baba Suleiman ne yaxo kasancewar sunyi masa waya sunce a kawo musu mai da yaji da garin kwaki saboda na gurinsu sun kare, sai dai mai, suna shiga office d'in examiner su kaga Sahal da Fareed zaune akan kujeru sun zubawa bakin k'ofa ido da alama jiran shigowarsu suke yi.

Cak suka tsaya idanun Aliya a waje tana bud'e baki dan ba k'aramin mamakin ganinsa tayi ba, yayin da shi kuma gogwan naku ya kafe Fa'iza da ido wadda haka kurum taji gabanta yayi wani irin bugawa,

“Aisha Abbakar da Fa'iza Suleiman ga visitor's d'inku nan.”

Cewar sir Hussain (examiner). Wanda ya fara k'ok'arin tashi ya fita ya d'an basu waje,

'”Yaya Sahal..!”

“Na'am liya, ya study?”

“Alhamdulillah wallahi, yasu Ummie da Husnah?”

“Suna gaida ku.”

Muryar Fa'iza ce ta shiga cikin kunnansa inda take gaidashi ya kura mata ido kamar yana son ya gano wani abun a cikin jikinta.

“Ina wuni.”

“Lafiya lau Faizaah.”

Kawar da kai tayi, Saboda duk lokacin da ya kira sunanta sai taji shi ya fita daban da yadda kowa yake ce mata, koda yake idan tayi la'akari dashi yakan canza furucin sunan mutane tunda ga Aliya nan itama ba fad'a yake yi ba sai dai yace mata liya.

Fareed ne ya tashi ya fita cikin sauri itama Fa'iza ta mike daga tsugunnen da tayi zata fita taji muryar Sahal yana cewa,

“Ina kuma zakije Faizaah?'” Shiru tayi can kuma tace,

“Zanje daga waje kafin ku gama hirar.”

Ta fada jikinta a sanyaye. Sake shirin fita take ya kuma tsayar da ita,

“Dan Allah karki fita saboda ni na dauke ku duk d'aya so ki zauna ayi hirar dake.”

Sam ba zata iya zama a wajan ba. Saboda taga alamun guy d'in akawai lafiyar kallo dan haka tace masa,

“Toh wajan abokinka zanje kaga ai ba'a barshi shi kadai ba.”

Bata jira cewarsa ba tayi ficewarta, gurin Fareed taje wanda yake zaune a wajan staff room ta zauna suka sha hirarsu, kamar ta tambaye shi wai da gaske ne Sahal baya son Aliya? sai kuma ta rasa ta ina zata fara. Kasa tambayar tayi har su Aliya suka fito da alamun tafiya su Sahal din zasu yi, nan Fareed ya nuna musu manyan jakunkunan da suka kawo musu, Fa'iza tayi godiya yayin da Aliya ke faman b'oye fuska ita a dole kunya taji. Kiranda sir Hussain ya yiwa Aliya shine ya bawa Sahal damar yin magana da Fa'iza personally inda ya rab'a gefenta yace mata,

“Da alama baki sanar da sister d'inki abinda nace ki gaya mata bako?”

Wani irin kallo ta watsa masa wanda yasa Sahal jin kamar ya janyota jikinsa ko zai samu sassaucin abinda yake ji a ransa, amman babu dama. Fareed na gefe yana kallansu sai dariya yake musamman da yaga abokin nasa ya zama kamar rakumi sai wani faman sunkuyar da jai kasa yake,

“Bansan lokacin da alak'a ta shiga tsakaninku da Aliya ba, dan haka babu ruwana da shiga tsakaninku. Yanzu baka tunanin halin da sister na zata shiga a lokacin da ta gano cewar kana da wadda zaka aura? Maza kuji tsoran Allah kai da irin salon da kaxo mata kenan? Hmmm nima akwai wanda yake raina min wayyo kila ya d'auka abin duniya zai sa na so shi besan ba haka bane a cikin tsarina ba.”

Gaban Sahal ya buga duk sai yaga tamkar ta gano shine yake mata basaje, amman yana son ya gasgata ko ta ramfo shi sai yace mata.

“Waye ke kuma yake raina miki hankali? Shin me yayi miki da har kike tunanin so yake ya karbi zuciyarki ta hanyar yi miki wani abun da bakya so?!”

Dogon numfashi Fa'iza ta sauke tare da b'ata rai, kamar ta bayyana masa komai da yake faruwa tsakaninta da boyayyan masoyinta sai kuma tace dashi,

“Sirrina ne kayi hakuri bazan iya bayyana maka ba.”

Jinjina kai Sahal yayi tabbas yarinyar kullum sake siyar zuciyarsa take yi, kafin yayi wani abun Aliya ta fito ta k'arasa kusa dasu fuskarta dauke da murmushi..

“Zamu tafi sai Allah ga dawo daku gida.”

Cewar Sahal yana satar kallan Fa'iza wacce take kallan can gefe,

“Toh ya Sahal godiya muke yi Allah ya saka da alkairi, dan Allah ka gaida su Ummie da Husnah duk da nasan itama yanzu kai ya dauki charge wajan karatu”

Murmushi yayi yana d'aga mata kai, alamun tabbas haka ne Husnah na gida karutu take kamar zata kashe kanta. Har gurin mota suka raka su, Fa'iza ta riga Aliya barin wajan dan haka basu jima ba Sahal yaja motar suka tafi, Saboda daman dan ita yazo kuma taki bashi had'in kai wajan ganin sunyi hira sosai,

Suna komawa hostel suka bud'e kayan, dukkansu babu wanda be girgiza ba saboda kaya ne na sakawa ya kawo musu duk iri daya masu tsada kala uku-uku, ga kayan graduation na gifts da yayi musu wato memo's, key holders, stickers da sauran abubuwa kuma duk dauke da sunayensu su biyu. kayan provision kuwa ba'a magana wani abun ma basusan me ake yi dashi ba. Murmushi Aliya tayi cikin nuna yakini ta cewa Fa'iza,

“Sis kika ce ya Sahal ba ya sona da aure? shin idan bada aure yake sona ba me yasa yake kawo min wad'annan abubuwan gashi yanzu hardake yake had'awa saboda tsabar muhimmancin da nake dashi a gurinsa?”

Girgiza kai kawai Fa'iza tayi ashe har yanzu kalmar tana cikin ranta?murmushi ta saki tare da cewa,

“Babu wanda yasan zuciyar bawa sai Allah, so yanzu kawai kiyi addu'a Allah ya bamu mazaje nagari.”

“Haka ne sis, toh amin amman insha Allahu nasan Yaya Sahal miji ne na gari.”

“Uhhmmm!”

Shine kawai abinda Fa'iza ta fad'a, daga nan harkokinsu suka ci gaba da yi kamar yadda suka saba komai tare suke wanka ne kawai sai daya ta jira d'aya tukun suke komawa hostel..

*BAYAN WASU LOKUTA..*

_''Munjinjina muku mun rausayaaaa, wasu cikin mu idan mun rabuuuu, sai a k'iyama a darrussalam wayyooo...!''_

_''Daga yau shikenan..gobe i'yanzu muna gida..''_

_''Candy..candy..candy..candy On 7july.!''_

Haka ss3 final year student na makarantar GGSS sumaila suke ta wak'e-wak'e a cikin hostel suna kid'e-kid'e da raye-raye, kai daka gansu kasan suna cikin farin ciki.

Fa'iza ne da Aliya suke bin hostel by hostel suna kaiwa kawayensu abubuwan graduation d'in su, idan sun kai suma sai a basu abin gwanin ban sha'awa, rayuwar makarantar kwana akwai wahala kafin ka saba, amman idan ka dad'e musamman idan ka shiga ajin karshe wato aji shida aljannar boarding, toh sai kaji duk baka son barinta saboda d'in bin al'umar da kuka yi sabo dasu. Haka dai suka raya ranar cikin nishad'i babu wanda yake son b'atawa wani kowa so yake ya rabu da mutane lafiya, har asuba suna abu d'aya k'alilan ne daga cikin aji shidan suka yi bacci saboda tsabar murnar zasu tafi gida.

Washe gari kuwa bayan sun dakko kayan su wad'anda zasu koma dasu gida duk suka kai bakin gate suka ajiye, sai da aka yi musu Assembly malamai suka yi musu nasiha sosai sannan suka yi musu fatan alkairi cikin rayuwarsu, ta nan gaba sannan aka bud'e musu gate 'yan uwa suka fara shigo da motoci, motar Baba Suleiman itace ta biyar a jerin motocin wanda shima yazo dibar yaransa.

Kamar wasu yara haka suka ruga da gudu suka rungume shi, cikin jin dad'i ya dinga shafar kansu kafin yace su zuba kayansu a booth, suna gama zubawa sukaje suka yi sign out sannan ya kwashe su harda wasu kawayen su da suka ragewa hanya kasancewar suma 'yan hotoro ne. Suna tafiya suna hira shi dai Baba Suleiman jinsu kawai yake yi, kowa da irin burinsa wani yayi dariya wani kuma yasa musu baki wajan cewa karatu kaza akwai wahala fa gara kiyi kaza, haka dai har suka k'arasa hotoro, sai da ya fara ajiye kawayen su Fa'iza a gidajen su sannan suma suka nufi gida.......



_ALLAH KA JIK’AN IYAYEN MU DA RAHAMA, AMEEN! ALLAH KASA MUTUWA HUTU CE A GARE SU, RABBI KA SASU A ALJANNATUL FIRDAWS, KA SHAYAR DA SU RUWAN ALKHAUTHARA, ALLAH KA BAMU HAKURIN RASHIN SU, AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM_



_MISS XOXO🧕

*P/Q/16/17/S*

*Tsayuwar* motar da suka ji ne yasa yaran gidan fitowa da gudu suna yiwa yayyun nasu Oyoyo, suna b'alle murfin motar yaran suka fara k'ok'arin rungume su cikin tsantsar nuna kewa. Su kuwa Aliya da Fa'iza bakin su yaki rufuwa kai da ka gansu kasan cewar candidate ne da zafin su,

“Ku fito da kayan ku daga booth, ku shigar dasu ciki.”

Baba Suleiman ya fad'a ganin suna shirin bar masa kayan su a mota, yaran suka bawa, su kuma kuwacce ta dauki school bag d'in ta suka shiga suna kiran gwaggo Talatuwa. Tana tsaye itama a bakin kofa tana jiran shigowarsu, jinta take kamar anyi mata bushara da gidan aljanna, Saboda murnar dawowar jikokinta, gida ya cika sosai daman 'ya'yan Bashir sunzo wato kanin Baba Suleiman, Aliya ta makalkale jikin gwaggo har tana shirin kayar dasu zuwa k'asa, gwaggo ta yakito ta daga jikinta tana cewa,

“Toh kayar damu 'yar bakin ciki salon kija Sahalu ya dena kawo min yugut (yoghurt) da tufa idan yaji labarin na kayar dake.”

Dukan su babu wanda beyi dariya ba a wajan, janta suka yi ita da Fa'iza suka nufi ciki, Umman su tana ta d'inki kasancewar telace kuma ‘kwararriya akan d'inkin mata. Gurinta suka nufa itama tana faman fara'a suka gaida ita cike da ladabi domin ita bata sakar musu fuska sosai, Saboda karma su rainata ko su gagareta hakan yasa Aliya bata son suci gaba da rayuwa a gidan domin Umma ko aiken su bata yi bare su dinga fita suna ganin gari,

“Sannunku da dawowa, Allah ya yiwa rayuwarku albarka.”

Duk suka amsa da amin kafin tace,

“Sai kuje ku cire uniform din kuyi wanka kuzo kuci abinci, gashi nan yana jiranku.”

“Toh Umma! sannu mun gode.”

Cewar Aliya tana shirin mik'ewa, d'akin gwaggo ta tafi kasancewar tafi son can bata fiye zama d'akin da aka ware musu

Please Login or Register in order to submit comment