Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ake yi sannan suka fito, gidan banda k'amshi babu abinda yake saboda shukokin dake zagaye sune suke bada wani irin daddad'an kamshi. Motar da ya bata ta gani a can wani guri shima na tanadar mota ne amman gurin na motar tace kawai saboda yadda kirar motar take haka aka yiwa gurin.

Tasowa suka yi Yazeed yana kaiwa Nawal harara kafin ya saki fuskarsa yana yiwa Aliya murmushi tare da cewa.

“Amarya bakya laifi ko kin hana maigida zuwa office”

Hannu tasa tana rufe baki idanunta a waje tace.

“A'ah oga Yazeed rufamin asiri.”

“Arufe yake ai madam kuzo mu shiga ciki.”

Dama aunty Afiya tunda suka shigo taja mijinta gefe suka fara d'an kuskus d'insu kafin suma subisu a baya. Har yanzu fa Aliya bata yadda cewar gidanta bane saboda tsabar tasan yafi k'arfin ta, idan kuma ance muhallinta ne toh tabbas Shamsuddeen yana sata idan ba haka ba ya akai ya samu uba-uban kudadan yin wannan gidan, sannan ance kamfani ma nashi ne mamallaki? Har suka gama ganin ko'ina suka b'ararraje suka ci kajin da Yazeed ya fita ya siyo musu har wajan takwas na dare suna tare kafin Yaya Garzali ya kwashi iyalinsa suka tafi, suma su Humaira ta gidan su Aliya drive ya tafi mayar dasu gida, ya rage daga Aliya sai Nawal da Yazeed wanda yake jiran shigowar Shamsuddeen.

“Ke wai baxaki tashi ki tafi gida bane?”

“Ah sir anan zata kwana na tambayi Mami ai.”

Yaji Aliya na fad'a ya saki baki sagalala yana kallansu, yaja d'an karamin tsaki tare da cewa.

“Amman dai baku da hankali wallahi, shi yasa ake cewa mace karamar kwakwalwa gareta, idan ba haka ba ta yaya daga tarewarku aje wannan gand'amemiyar budurwar tazo kwana? Toh wallahi ba zai yiwu ba ki shirya ma idan zan tafi naje na ajiye ki uwar yawo kawai.”

Nawal ta zumburi baki tana k'unk'uni Yazeed yace.

“Yi magana karki sake min magana ciki-ciki kona tashi na had'aki da kujerar nan”

“Wai kai ina ruwa na dakai ne a'ah? Duk kabi ka takurawa rayuwata da kai muka zo da zaka matsa min?”

“Ba dani kika zo ba, amman nine zan maida ke dan bazaki kwanar musu a gida ba.”

Kuma turo baki tayi tare da harararsa bata san cewar yana ganinta ba. Suna nan zaune sai ga Shamsuddeen ya shigo bakinsa dauke da sallama duk suka amsa suna kallansa har ya shiga ciki ya zauna kusa da Yazeed yana furta.

“Washh Allah na.”

“Dude an gaji ko?”

“Sosai ma kuwa, wallahi bakaji ba kaina harya fara ciwo”

“Sorry Dude bari mu tafi amarya zata gasaka tayi maka massage nasan zakaji relief.”

Daga Nawal har Aliya cikin ransu cewa suke 'kaji iskanci.' Amman a fili ido suka had'a Nawal na yiwa Aliya dariya harda gwalo. Shi kuwa Shamsuddeen da yasan ba wani samu yake yi ba murmushi kawai yayi tare da d'ora k'afa d'aya akan d'aya yana girgizawa. Sun jima a gidan anata game d'in cewar sai Nawal ta tafi su kuma su Aliya da Shamsuddeen suna cewa ya kyaleta kuma daman ita ba kwana zata yi ba sunyi maganar da Aliya take cewa bari ta bari sai lokacin da Yazeed zai tafi sai ta bishi. Ganin Yazeed ya kafe ne yasa Nawal d'aukar jakarta tare da cewa.

“Ku rabu dashi bari kawai mu tafi.”

Shi kuwa duk a zaton shi jan idon da yayi ne yasa tace to zata tafi besan daman can a tsare hakan yake ba. Har wajan motar Yazeed suka rakasu bayan sun tafi suma suka koma ciki Aliya ta zauna a parlour sai satar kallansa take yi yana tsaye yana kwance agogon hannunsa, shareta yayi ya wuce zai nufi sama yaji kamar an matse mata baki tana cewa.

“Na gode da hidima.”

Kamar bayajin ta haka ya share ya hau saman, ganin ita kadai ce a parlourn yasa ta mik'ewa da sauri ta shige bedroom d'in dake kasa bata sake fitowa ba shima kuma bai sake nemanta ba har sai da safiya tayi sannan suka had'u a parlour ta gaidashi a amsa a shak'e kafin yasa hannu ya zare wayarta dake hannunta, ta kasa yin magana tana kallo ya fita da wayar sai ta yi zaton ko yanzu zai dawo mata da ita amman shiru har dare, nan da nan ta damu domin ba karamin d'ebe mata kewa take yi ba yau kuwa ko kallon kasa yi tayi. Sai dare ya dawo ta tambayesa wayarta yace.

“Bata da wani amfani shi yasa na karb'e ta dan ina kyautata tsammanin tana taka mihimmiyar rawa wajan kin sanin darajar Auren ki.”

Tana jin haka kuka ya kwace mata ta dinga bashi hakuri ganin haka yasa shi tashi ya tafi sama ya kulle dan karma tabishi domin ba wai bata zai yi ba..

*ABUJA*
(Maitama/Ganges Street).

Rayuwa ce suke yinta cikin lumana da kaunar juna, duk kuwa da Fa’izah bata fito tafadawa Sahal tafara son saba, Amman dai ta mallaka masa gangar jikinta sai yadda yayi da ita. Tana kuma k’ok’arin yi masa biyayya da gudun ‘b’acin ransa. Sahal irin mazan nanne masu sha’awa da yawa, shiya sanya kullum yana mak’ale da Fa’izah idan sunyi nisa shine taje lectures alokacin yake sarara mata. Ya kuma san tana kokari. Ranar asabar ta tashi da matsananciyar tashin zucia, dama duk sauran satin baya da zazzabi take kwana, tana dawowa daga lab ta zube a parlor tana numfarfashi. Sahal fitowar sa kenan daga wanka yaga tadawo bayan sunyi da ita shi zai je ya d’akko ta.

“My Queen! Baki kira ni ba kika dawo da kanki..? Meyasa? Uhm?”

Fa’izah ta tab’e baki tana yamutsa fuska, karasawa yai kusa da ita yana shafa bayan ta, ganin kamar zai ballo mata ruwa bata shirya ba tai hanzarin zare hannun sa,

“Uber na hau! Jiri nake yi shiyasa..”

“Subhan’Allah meya same ki? Tun yaushe kika fara?”

“Calm down Ya Sahal, I think malaria ne kawai...”

“Kin tabbata? Kai tashi ma dai muje clinic.”

“Bafa wani serious bane..”

“Banason musu, tashi tashi mu je..”

Temaka mata yai ta mike, tana dafe da kafad’ar sa suka karasa mota ya zaunar da ita sannan ya koma driver seat ya jata suka tafi wani asibiti na kusa dasu. Gwaje gwaje likita ya mata tana rufe baki da kasan hijab d’inta. Sahal duk a kidime yake, mintina kadan ya dube ta cike da damuwa,

“Ko zaki ci wani abun? Baki ci abinci ba”

“No I’m okay..”

Ta fada tana janye hannun sa don dik kwana kinnan ta tsani ya rab’e ta. Shi kuwa duk yabi ya damu, Dr Areef ya fito daga lab yana cire hand gloves d’insa, Sahal ya mike yana masa kallon karin bayani. Duk kuwa da shi da Fa’izah sun ‘dauka malaria ce. Hannu Dr Areef ya bashi yana murmushi, Sahal ya mika masa suka gaisa, cikin farin ciki likitan yace,

“Congratulations sir! Ka kusa zama da daddy, your wife is...”

Ai sahal bai bari dr Areef ya K’arasa magana ba ya kamo hannun Fa’izah yana sumbatar sa, farin ciki ne kawai ke dawainiya dashi, Fa’izah gaba d’aya binsu take da kallo wai itace yau da ciki? Ta dubi shafafffen cikin ta kamar an kife mara, kwata kwata kamar babu yan hanji acikin sa ballantana shigar ciki, Dr Areef ya girgiza kai kawai ya juya ya koma office ya bar Sahal na faman yiwa Fa’izah sumbatu.

“My Queen kinji abunda dr dinnan ya fada? I’m gonna be a daddy. Alhamdulillah ya mujeeb for the unlimited blessings.!”

Fa’izah tai murmushi tana duban sa, Sosai yake cikin annashuwa ya kasa boye farin cikin sa. Kafin subar asibitin sai da Fa’izah ta kelaya amai sau uku, dr yabasu magunguna kala kala wanda zasu tai maka mata tayi laulayi cikin sauk’i.Dak’yar ta yadda ta jingina a jikin sa suka tafi gidah, yoghurt kawai ta iya sha ko a gidah tukun sannan da temakon Sahal tayi wanka, ya dakko ta suka koma parlor! Nan ma sumbatun cikin kawai yake mata, ita harta gaji ma sai yatsina fuska take,

“By being in my life, you gave me a reason to live, a cause to fight for and hopes to look up to every day. Thank you for being a part of me. My Queen , you give me so much happiness and I want to give you nothing less. Forever is just a start for us. We belong in each other’s arms. I love you. Uwar ‘ya’yana, mamallakiyar zucia ta. Dan Allah My Queen *KI MIN HALACCI* ki so ni koda kuwa rabin wanda nake son ki ne...”

Fa’izah tai murmushi tana kamo hannayen sa duka biyun daya riko nata, cikin rawar baki tace dashi,

“Ya Sahal kenan! Ka sani zucia mai HALACCI bata manta alkahiri komai girman sharri, duk alkhairin da kamin a rayuwa taya zan butulce maka nace bana son ka, Tabbas a da, idan nace ina son ka nayi k’arya. Amma yanzu fa? Wallahi kana cikin raina Ya Sahal, ka mallaki zuciata bama gangar jiki na kad’ai ba, ka sani har gaban abadan ba zan taba juya maka baya ba, duk wani farin ciki kana iyakar K’ok’arin bani shi, kana kula dani tamkar yadda masoyi zai kula da masoyiyar sa, saboda haka ka sani a rana irin ta yau zuciar Fa’izah gaba d’aya mallakin kace, gangar jikin Fa’izah ya zama naka kayi yadda kaga dama dashi. Ina maka so, ina maka son kauna fisabilillahi. Hak’ik’a kai gwarzo ne acikin gwarzaye,

“Ya Sahal Most times, I lie around wondering whether love is worth fighting and dying for. Then I sit back and think about us, and I get ready for you because I would die for you, without a second thought. That is how much I love and treasure you. You are simply, the best. I love you so much hubby na..”

Sahal ya gwalalo idanu yana binta da kallo, bakin sa a bu’de yana mamakin kalaman ta na k’arshe, cikin tsantsar mamaki yace,

“Say that again...”

“Nace Most times, I lie around wondering whether love is worth fighting and dying for. Then I sit back and think about us, and I get ready for you because I would die for you, without a second thought. That is how much I love and treasure you. You are simply, the best. I love you so much hubby na..”

Mikewa yayi yana daga hannuwa,

“Yes..Yes..”

Rufe idanu tayi, d’aukar ta yai ya dora ta kan cinyarsa yana so ta bude idanun ta,

“My Queen, pls look into my eyes and tell me how much you love me..”

Fa’izah ta sake damke idanun ta kamar zai kwakwule su, hannun tasa tana zagaye lips dinsa,

“Ya Sahal! Ka sani kalmomi sunyi kadan wajen fado matsayin ka a zucia ta, ni dai kawai inason kai min wani favor, I knw i might sound silly but please kayi hak’uri da duk abubuwan da nai maka a baya, *KAI MIN HALACCI* ka karbi kokon barar soyayya ta kaji Ya Sahal..?”

“Haba Queen! Yanzu har sai kin nemi wani favor? You are the love of my life, my life is meaningless without you. HALACCI d’aya zamuyi wa zukatan mu shine mu rike soyayyar junan mu.kinji?”

“Naji Ya S..”

“Kar ki kara plss, ki dena wani cemin Ya Sahal, duk ka pet names nan, sai wani Ya Sahal ko da’din fada babu. D’axu I heard kamar kince Hubby! A taimaka dai a canza min suna pls..”

“Toh Hubby am....”

“Menene am din?”

“Fulfulde ne yana nufin mine..”

“Yayi kyau! Toh mezan samu?”

Fa’izah ta shiga kiciniyar kwace kanta ya hanata yana hade bakin su waje d’aya, wata irin deep and passionate kiss yake mata wadda jikin ta sai daya saki, haka ya shiga sarrafata duk yadda taso ta ‘kwace kanta abun yaci tura, sai data bada kai bori ya hau, a ranar dai a parlor suka shiga sarrafa junan su, kowanne yanason yasanya dan uwan sa cikin farin ciki...

*KANO STATE*

Tanaji tana gani ya karb'a ya hanata har hawayen bakin ciki sai da tayi, gashi wayar itace take d'ebe mats kewa. Yana ajiye mata duk wani abu na hakkinta babu abinda ya tauye mata, ita kuma ta baje a gidan sai dai kadaici yana damunta gashi zai zo ya tambayeta koda abinda take bukata sai tace a'a haka zaija motarsa ya tafi, kuma duk abinda ya gani indai ya burgesa kuma indai yasan na mata ne toh sai ya siyo mata ya kai mata, wani tayi amfani dashi yana nan wani kuma sai baya gidan take take sakawa ko taci yadai dan ganta da abinda ya kawo mata. Wannan tarairayar da kulawar tare da kare mata duk wani mutunci nata sune suka fara sanyaya zuciyar Aliya. Wata ranar lahadi ne yasa ta shirya zasuje unguwa shida ita. Tsab ta gama komai tana tason ya sakar mata jikinsa amman ina domin ta riga taki karbarsa tun farko hakan yasa yanzu take rasa yadda zata yi koda hira dashi ne.

Wata blue d'in abaya tasanya tayi mata kyau sosai tayi kwalliya sama-sama sai dai batasa janbaki ba kasan cewar baya so ransa b'aci yake duk lokacin da yaga tasa ta fita. Yau kam tasha mamaki domin lokacin da ta fito a parlourn kasa ta ganshi tsaye yana danna remote, waigowa yayi suka yi ido hud'u ya rab'e baki duk da cewar tayi masa kyau amman ya maze tare da dauke fuskarsa daga kallonta. Itama a b'angarenta wani bakon lamari ne ya ziyarce ta domin tunda take da shi tun kafin yakai haka bai tab'a burgeta ko ya bata sha'awa ba irin yau. Sanye yake cikin dakakkiyar shadda light purple ya d'aura hularsa zanna bukar ta karasa a hankali ji take tamkar ta rungumesa musamman da ta tuna wani pic da Fa'iza ta turo mata ta rungume Sahal suna murmushi, lokacin da ta gani ko a jikinta amman a yanzu ji take tamkar taje ta rungumesa sai dai kunya da nauyi bazasu barta ba.

“Kije kisa lipstick.”

“Na'am..?”

“Cewa nayi kije kisa wani abun a lips d'inki kodan kin rainani shine ba zaki zaka ba sai sanda zaki tafi ke d'aya?”

“Kayi hakuri.”

Tayi maganar tana juyawa ta koma cikin d'aki kamar zata fashe da kuka dan taga yanzu wani irin wulak'anci yake yi mata. Red ta sanyi yayi mata d'as aikuwa kishi ya taso masa, kamar yace taje ta goge sai kuma ya daure yace da ita....


ZAFAFA DAYA😹


MX🧕🏼?
??[27/03 6:57 PM] Bilkisu: *Wannan littafin na kuɗine, kiji/kaji/kuji tsoron ALLAH karki/karka/karku shiga haƙin wanda ya saya, kema idan kina buƙata ki nema wannan Numbers ɗin._👇🏻*

*08030811300*
*07067124863*


_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*_MISS XOXO🧕🏼_*_


_*NO: 52-53_*

*ABUJA*
(Maitama/Ganges Street)

Sanye Fa’izah take cikin wasu irin kayan india mai kirar riga da wando na Pakistan. Rigar ja ce har gwiwa, wandon kuma baki ne har kasa, batasa dankwali ba tayi parking gashin ta da ribbon, ba kwalliya a fuskar ta sai dai ta goga man baki, sai jefa dan santsin take a tafashashshan ruwan dake zab’al b’ala akan gas. Tana rera wakar Ed Sheeran mai suna shape of you. Humaira dake gefan ta tana temaka mata da yankan tumatir da albasa, Sahal na parlor yana kallon wasan ‘kwallon ‘kafa na La liga. Wayar Fa’izah dake kusa dashi tafara ringing, yanata dokawa Humaira kira dake kitchen sam bata jiyo shi ba. Daukar wayar yai yana bin screen din da kallo. ‘Sissy’ shine sunan dake rubuce akan screen din. Ganin Aliya ce mai kiran yasa ya d’auka ,

“Sissy in-law.”

“Na’am brother in-law! Barka da rana ya harkoki?”

“Alhamdulillah wallahi! Ya ogan mu da sauran kowa na family?”

“Lapia lou! Yana office. Maman unborn na kusa?”

“Tana kitchen tana yin farin ‘danwake ni ina parlor wayar na kusa dani ganin kece yasa nai karambanin dauka.”

“Heheh! Farin danwake kuma ko dai dan sub’ul da ake cewa dan santsi na fulawa/flour?”

“Eh fa.. Bari na mika mata.”

“Okay brother in-law! Nagode.”

Tashi yai ya shiga kitchen Humaira ta basu waje, domin Aunty Yagana ta kora mata warning din kada ta sake ta dinga zama wajen inda suke, ta dinga excusing kanta. Ta bayan ta ya rungume ta yana shinshinar wuyan ta, hannun sa d’aya kuma ya nana mata wayar a kunnen ta, ta cikin kunnenta ya rada mata,

“Sissy in-law ce! Ta kira bakwa wajen..”

Ture shi ta shiga y gaba d’aya Sahal ya cukwikwiye ta, hakura tayi tasa wayar a speaker ta shiga kokarin kwace kanta awajen Sahal, sai manne mata yake tana ture shi.

“Hello Sissy!..”

“Na’am Maman unborn! Ya kike?”

“Lapia Alhamdulillah ya komai?”

“K’alau wallahi! Sorry kwana biyu wayana ya samu matsala ne sai yau Habibi ya syan sabuwa shiyasa ban ga messages dnki ba, ya lapiar unborn.”

“Alhamdulillah, kingani yanzu ma unborn din yasani cin dan santsi. Kun cika kwadayi..”

“Awwn! That’s my fave little munchkin. Allah ya raba lapia, Ameen.”

“Ameen ya Allah! Saura ke duk da nasan yana nan a boye.”

“Hehehe! Sissy kenan! An gaya miki kowa irin Ya Sahal ne? Ni mijina ba Sharp shooter bane..”

Fa’izah ta kyal’kyale da daria, Sahal dake kwakwume da ita ya ciji kunnen ta, Fa’izah ta saki ‘kara, tana nanata,

“Ka bari pls..”

“Kutsin uban can! Sissy a speaker kika sani? Kina nufin kice agaban Ya Sahal muke waya?”

“Wallahi shine ya hanani sakat, Dan Allah kice ya bari..”

Aliya ta kyalkyale da daria hartana bubbuga kafa cikin sauri tace,

“Munafuka da ba ki fada ba sai yanzu.? Nide sai anjima a gaida Humaira da unborn. Brother in law ka cacumeta dakyau. Bye bye..”

“Yawwa babbar Yaya, Nagode da umarni..”

Sahal yabawa Aliya amsa kafin suyi sallama takashe wayar. Sai da suka shan soyayyar su a kitchen tukun sannan Fa’izah ta kwashe dan santsin ta ta kai parlor suka ci. Wata irin so da shak’uwa ce take ginuwa a gidan Sahal da Fa’izah, sun fuskanci juna kuma suna baiwa soyayya hakk’in ta. Sai dai muce tubarkAllah kawai, ALLAH ya kara zaman lapia da kaunar juna...


*KANO STATE*

Rayuwar Aliya da Shamsuddeen gwanin burgewa su kansu suna bawa kansu sha'awa ballantana kuma wasu su gansu, kowa yana bawa d'an uwansa hakkinsa. Kasan cewar yau Monday yasa Shamsuddeen Aliya shiryawa zai kaita unguwa, da ta tambayesa ina zasu kawai yace ta shirya surprise zai mata, tayi murmushi tare da ajiye cum d'in da ta gama taje gashinta tasa ribbon ta d'aure shi. Riga da zani tasa na wani green d'in lecce ta gama shiryawa Shamsuddeen ya tsaya yana kallon ta, matarsa ko bata yi makeup ba kyau gareta shi yasa yanzu ma da take gabansa yake jin tamkar yace tayi zamanta ya fasa zuwa da ita, sai dai yana son ya kaita dan haka dole ya hakura ya fara gyara mata zaman mayafinta ita kuma tana gyara masa botir d'in rigarsa.

“My Habibi kaya kyau ina kishin kaje gurin aiki.”

“Me yasa kika riga ni yin magana? Nifa saboda kishinki har na fara jin zan fasa fita dake unguwa.”

“Toh Habibi kawai mu fasa zuwa ko'ina muyi zaman mu a gida ka kalleni na kalleka shikenan.”

Hancinta yaja tare da murmushi yana janta zuwa jikinsa ta kuwa kankamesa tana sauke numfashi da kyar, suna masifar jin kishin juna kowa baya son a kalle masa surar d'aya amman ya zasu yi? Shi dole ya fita wajan nema ita kuma dole ta shiga dangi da 'yan uwa, hakan yasa suka tsaya lallashin juna kafin ya daukar mata jakarta itama ta dauki tashi suka fito suna manne kamar za'a kwace d'aya. Motarshi suka nufa sannan yaja suka fita suna ta hirar su gwannan burgewa. Kai tsaye kamfaninsa taga sun nufa suka had'a ido yayi mata murmushi har zata yi shiru sai dai ta kasa zuciyarta ta na buk'atar karin bayani, ta gyara zama tana kallansa sosai tace.

“Zaka dauki abu ne a can?”

“Yeah! Kona fasa?”

“Nooo muje.”

Dariya ya sake yi har suka k'arasa, tun a gate ma'aikatan suke lek'awa suna kwasar gaisuwa Shamsuddeen ya kalli Aliya tare da cewa.

“Kija mayafinki sosai ki rufe fuskarki, kinga yadda gate man d'in nan yake lasar baki kamar wani kwarto?”

Aliya ta zazzaro idanuwa tana rik'e baki, har suka k'arasa inda yake parking tace.

“Nifa ko kallansu banyi ba ta yaya ma ya wani ganni bare ya lashi baki?”

“Ehh ai ke bazaki gani ba saboda bani wata ta kalla ba.”

Baki ta turo yasa hannu yana kamo lips din nata ta saki 'yar kara yace.

“Ki sake turo shi sai na cije shi.”

Tare suka fito ya mik'a mata jakarta shi kuma tashi masinjansa ya karb'a sannan suka jera suna tafiya ana mik'a musu gaisuwa masu yi musu kirari nayi kamar wasu sarakuna da haka har suka k'arasa office d'in Shamsuddeen. Hannunta ya kamo tayi murmushi tana kallansa yajata har zuwa wajan da ta taba zama yaje ya zaunar da ita ya kallonta cike da kauna da soyayya yace.

“Congregation Mrs Shamsuddeen, kin dawo sahihiyar sakatariya ta domin babu wanda ya cancanci kujerar nan sai ke.”

Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Aliya ta kurawa mijin nata idanuwa wanda ya zaro wayarsa a cikin aljihu ya fara yi mata hutuna, yana cikin yi mata ne yaga hawaye suna zirarowa daga cikin idanunta yayi saurin mayar da wayar tare da kamo hannunta yana tambayar ta.

“Menene? Nine? Ko bakya son aikin? Shikenan idan bakya so ai bazan miki dole ba, taso..taso bana son wannan kukan naki.”

Ji yayi ta rungumesa tana kuma sakin wani kukan shi kuma sai faman bubbuga bayan ta yake, muryarta a sanyaye take masa magana.

“Hak'ik'a my Habibi *KAI MIN HALACCI* ta hanyoyi da dama wanda bana tsammanin su, bansan da wane bakin zanyi maka godiya ba ko nuna tsantsar jin dad'i na a gurin ka ba. Babu wani *HALACCI* dana tab'a yi maka a rayuwata, amman kai *KAI MIN HALACCI* wanda ba ko wane d'an Adam ne zai iya yiwa wani ba. *KAI MIN HALACCI* tun ina kankanuwata ta hanyar nuna min soyayya. *KAI MIN HALACCI* a lokacin da nake siwes a wajanka. *KAI MIN HALACCI* wajan jurewa bayan ka aure ni, ka barni da halina wanda nake ganin kamar cinyewa ne. Shin dame zan nuna maka nawa HALACCIN? bayan duk ka kwashe komai?.”

Sai kawai yaga ta sake shi tayi kasa da gwiwoyinta tana kuma rik'e masa kafarsa tana cewa.

“Please Habibi *KAI MIN HALACCI* guda d'aya wanda nima zanyi alfahari dashi wajan jin cewar nima na tab'a yi maka koda sau daya ne. Dan Allah dan annabi *KAI MIN HALACCI* ka barni na soka kai ba sai ka soni ba kabar iya wanda kake min ya isheni. Ka barni nasha wahalar sonka saboda nima na d'and'ani irin *HALACCIN* da kake yi min, wannan shine rokona a wajanka na ka daure *KAI MIN HALACCI* pleaseeeee nima ina son nayi maka...!”

Yazeed da tun da suka fara shagalinsu ya shigo yake hangensu sai yanzu da yaga Shamsuddeen ya d'aga ya rungume sannan ya juya ya fita yana kad'a kai wad'annan mutanan basu da kunya, sunyi a gida a office ma baza a hakura ba salan suja masa kasa yin bacci. Hawayen ya dinga share mata yana binta da wani marayan kallo, ita kuma tana sake narke masa, muryarsa taji yana cewa.

“My Simba, mallakar zuciyar mu, shine abun so da jin dad'in rayuwar mu. Zuciyata ta riga ta mutu akan soyayyar ki, kinsan kuma duk wanda ya mutu baya dawowa. Zuciyata babu wanda ta aminta dashi sai ke matata. Ina sonki karki sanya wata damuwa a cikin zuciyarki domin ba yin kaina bane soyayyarki daga wajan Allah ne, shine ya dasa min kuma yaki cire min, kedai kawai kiyi min *HALACCI* wajan tsare min kanki da mutunciki dana 'ya'yan da zamu haifa nan gaba.”

Wata irin sakaryar runguma ta kuma yi masa tana shashekar kuka.

“Idan har ka tafi ka barni, zuciya ta bata da sukuni har sai ka dawo gareni Habibi ana. Having you is the most kindable, and kissing you is the most sweetable in my life. I could spend the whole day hugging you. Habibi I love you so very much. Allah ina rokanka ka bawa bawan nan naka duk abinda yake buk'ata na duniya da lahira. Allah bawanka kuma Habibi na ka rabashi da iyaye lafiya, ka kareshi a duk inda yasa k'afarsa domin kai maji rokon duk wani bawa naka ne...”

Daga nan suka kankame junansu daga bisani ya tafi nashi site d'in dama tuni yasa aka cire masa labulayen da suke yi masa shamaki da ganin ta, yanzu kuwa ta haka kowa yake jefawa masoyinsa sakon kaunarsa zuwa ga junansu. A take a gurin ta kira Baba Suleiman ta sanar dashi, yayi mata murna sosai tare da kiran Shamsuddeen din shima yayi

Please Login or Register in order to submit comment