Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Mr Zakari ya bamu?”

Cikin rashin kwarin gwiwa tace,

“Inafa nayi Husnah, wallahi duk na duba inda zan samu solution na rasa, nifa yau sai dai ya koreni a lecture dan wallahi banyi ba.”

Dariya Husnah tayi harda dukan gefen seat d'in da take kai, tana cewa,

“Ashe dai za'a koremu da yawa dan wallahi nima banyi ba, ke rabu dashi ni wallahi yanzu baya bani tsoro farkon zuwan mune nake tsoransa.”

Sahal yana jinsu ji yake kamar karya k'arasa amman babu yadda zai yi, yana k'ok'arin yin parking Fa'iza ta d'ago kawai suka had'a ido dashi ta cikin mirror, cikin sauri ta dauke nata tana shirin fita.

“Thank Yaya na, Allah yabar mana kai, ranar bikinka dole ne ma na rak’ashe na liya bada kanka a sare.”

Cikin satar kallo Fa'iza take ganinsa dan taga ya zai yi, aikuwa taga ya rab'e baki tare da murza key alamun zai tafi. Wani haushin sa na ya sarke wuyan Fa'iza taji kamar taje ta makeshi amman ba hali, cikin takaici ta juya ko jiran Husnah ba tayi ba wadda ta tsaya tana ce masa sai ya bata nacin awara.

D'ari biyar ya bata sannan ya kuma bata dubu d'aya, kallansa tayi cikin son jin karin bayani kamar ya san abinda take jira ya kawar da kai tare da cewa.

“Kiba kawarki ita.”

“Kai, Yaya 1k ni kuma 500 hundred?”

Wani kallo ya watsa mata wanda yasa Husnah yin shiru tare da juyawa ta tafi tana tafiya tana mita ji take kamar ta sauya ta bawa Fa'iza five hundred d'in ita kuma ta rik'e one thousand d'in, sai dai ba zata iya ba saboda bata saba ha'inci ba, kuma ma dai tana tsoran karya tambayi Fa'izan Idan sun had'u yace nawa ta bata, tasan idan yaji sauyin da tayi bazai sake bata wani abun ba bare kuma ya kawo ta makaranta. Koda Husnah ta bawa Fa'iza kud'in da kyar ta karb'a tayi godiya tasa a jakarta suka shiga lecture.

Suna fitowa Fa'iza da Husnah da Raheenah da Amina Modu sai Salaamah khamis suka zauna jira kafin su shiga wata lecture d'in, Fa'iza da take jin kamar zuciyar ta zata fito saboda son bawa Raheenah shawara ta mik'e tsaye tare da cewa,

“Sister's kuyi hakuri please zan d'an yi magana da Raheenah dan karku ga mun ware.”

“No p Fa'iza kuje.'”
Cewar Amina Modu.

Tashi suka yi har Raheenah tana cewa idan kaji kira samu ne tana yi musu dariya wayarta a hannunta tana faman jujjuyawa, suka samu can gefe inda babu kowa babu kuma mai jinsu suka zauna, sai kallan Fa'iza Raheenah take yi tana faman lumshe ido tare da kai hannu tana matsa mata cinya, a dabarance Fa'iza take janyewa, cikin yin gajeran numfashi ta fara magana,

“Raheenah ke kawarmu ce tun shigowar mu school d'in nan, amman kwanan nan na lura da wasu dabi'u da suke son shigowa cikin rayuwarki wanda sam bai kamata ace kinyi shi ba a matsayinki na 'yar musulmai, shin Raheenah kinsan illar neman juna kuwa?”

Wani irin wulakantaccen kallo Raheenah tayi mata, cikin b'acin rai ta kalli fa'iza tare da cewa.

“Kinyi min bincike a phone ko? Toh kema ai abinda kikai min babu kyau dan me yasa zaki bincika min waya ba tare da amincewa ta ba?”

Mamaki ya kama Fa'iza cikin tsantsar mamakin tace,

“Daman muna da shamaki tsakanin abunki da nawa? Ina ce kema kina daukar wayoyin mu bama nawa kadai ba kina d'aukar tawa da ta su Salaamah kuma babu mai cewa dan me, shine yanzu ni zaki cewa wai na d'auki wayar ki babu izini. Toh wallahi bari kiji na gaya miki Raheenah, Mad'igo haramun ne a addinin musulunci, malamai sun sanya shi daga cikin manya-manyan zunubai kamar...”

Bata fara fad'a ba taji Raheenah ta buga mata tsaki tare da cewa,

“Rik'e wa'azinki Fa'iza bana buk'atar shi, idan kina son muci gaba da mutunci karki sake attempting yi min wa'azi, kinsan tun lokacin da nake muradin yin harkar nan dake amman na hakura? Kinsan yadda nake ji kuwa duk lokacin da kika shigo? Toh nasan ke ba zaki yadda ba shi yasa banyi gigin nuna miki ko wacece ni ba, wannan ya zamo na farko kuma na karshe da zaki min irin wannan maganar idan kuma ba haka ba wallahi tallahi zaki jiki tsundum a cikin harkar ba tare da kinyi zato ko tsammani ba, dan haka kibi a hankali bani da mutunci wani lokacin.”

Raheenah na kaiwa nan ta mike tabar wajan ranta a b'ace, can wajan wata kawar ta da suke irin harkar ta nufa ko gurin su Husnah bata koma ba saboda b'acin rai. Fa'iza kuwa jikinta ne ya hau rawa jin yadda Raheenah ke cewa zata sanya ta a cikin wannan kazantar wadda take k'ok'arin fito da ita daga cikin bala'in, jiki a sanyaye ta koma wajan su Husnah tana musu yak'en dole....

*MALAM AMINU KANO AIRPORT*

Malama Bintu tai saurin juyawa tana duban Shamsudden, wanda alokacin hawaye ne ke zurara daga kyakkyawar fuskar sa, Shafa kansa tayi tana dan bubbuga bayan sa, Juyawa yai ya rungume Garzali dake bin sa da kallo, Gaba d’aya ya canza musu, kyawun sa, tsaftar sa, Girman sa, da hankalin sa, komai sabo ya dawo musu, domin lokacin daya tafi bai fi shekaru 22 zuwa da uku ba, dakyar Yaya Garzali ya ‘ban’bare Shamsudden daga jikin sa, nan suka shantake akan kujerun passengers lodge suna hirar yaushe gamo, sun jima kafin su rankaya waje, suka shiga motar Yaya Garzali, Shamsudden sai bin garin yake da kallo, Lalle wuri ko wata kai baka jeba sai ya canza maka, ballantana shekara da shekaru! Ko a mota, Umma sai bin Shamsudden take da kallo, gaba d’aya kallo d’aya zakai mata kasan admiring ‘dan autan nata take, cikin zuciyar ta kuwa Allah take sake godewa bisaga wannan babbar kyauta daya yi mata, ta ‘yaya biyu rak a dunia amma suna yi mata komai, hade da d’ebe kewa. Ni kaina dana dubi Garzali na kalli Shamsu sai da na kara kallon Shamsudden, Don kowannen su kamannin sa daban, Sai dai jini dole akwai ta inda sukai yanayi, ta tsawo da kuma gashin kansu, Shi Shamsudden farin mahaifin su yayi da yanayin gashin sa, da ‘kirar jikin sa, Amma kamannin Ummah yayo, shi kuma Garzali bakar fatar Umma ya ‘dauka, Amma yanayin sa komai irin na mahaifin su ya ‘dakko, Toh abun dai sai sam barka kawai, domin Allah yayi cikar halitta akansu, TubarkAllah!!!

Suna tafe suna hira gwanin sha’awa, amma Shamsudden lokaci zuwa lokaci yakan saka baki, Sosai su Ummah sun lura Shamsudden yanzu baya magana ba kamar sanda yana yaro ba, Surutun nan na da kamar zubar kanya yanzu sam babu, gayu da jan Aji sun zauna a tattare dashi, Ta Kan titin Maiduguri Road suka biyo, Yaya Garzali yai parking a Oasis bakery ya shjga ciki, ‘Dan kayan kwalam da makulashe ya sissiyo, ya koma ya shiga ya cigaba da tuki, Traffic Light ce ta tsaida su, Nan Garzali ya juya yana duban Shamsudden kafin yace,

“Ina abokan tafiyar taku ne? Naga kai kadai ka dawo inasu Yazeed?”

“Kasan mu mun tsaya munyi diploma dinnan, su kuma yawanci muna gama masters suka dawo, wasu dama tun muna kammala degree suka dawo, ni da yazeed dama muka rage, Toh shi kuma bai gama defense ba na project, yacemin sai zuwa next month zai dawo..”

“Anyi haka, Toh Allah ya baku sa’a, yasanya albarka a karatun da kuka yo..”

“Ameen..”

Hotoro Nndc quarters, Nan Yaya Garzali ya shiga, ba suyi tafiya mai nisa ba, yai parking a wani madedecin gidah dai dai misali, da kansa ya fita zai bude, Shamsudden ya riga shi fita ya bude gare din, Garzali ya shigar da motar ciki, D’as dashi, ko ina na gidan a gyare, gidane na zaman mutum d’aya, komai na amfani an tana deshi dai dai misali, daki hudu parlor biyu da dining area, sai parking space mai cin mota d’aya, da dan madedecin kitchen da store dinsu. Ummah ta nuna wa Shamsudden dakin sa, mededeci, ya sha katifa katuwa an lailayeta da zanin gado, da pillows guda biyu. Ga y’ar karamar TV set nan a ajiye, sai dan mini cooler(fridge), a gefe shima, da standing fan, ga drawer nan itama a gefe, sai kamshin turaren wuta ne ke tashi a ‘dakin, harda stick incense (turaren tsinke) shima an saka har guda biyu, da ‘dan karamin bandakin sa acikin ‘dakin dai-dai misali.

Bandaki ya fada yayo wanka da alwala, sai daya rama sallolin da suka riske shi a jirgi tukun sannan ya canza kayan jikin sa, zuwa jallabiya fara ‘kal da ita, ya taje kansa ya bulbula turaren Black oud, sannan ya nufi inda yaga ummah tayi da alama nanne parlorn, yana shiga kuwa ya tarar an jere abinci kala kala akan wata madediciyar taburma, Parlorn sai kamshi yake yi, Ummah na ganin sa ta fadada Murmushin ta kafin tace,

“Yawwa! Yanzu dama nake shirin na kira ka, kar abincin yai sanyi, ga shinan na cikin korayen flasks din Afiya (matar Garzali) ce tayo tace a baka..”

“Kai! Umma duk ni kadai? Nagode Allah ya saka da alkhairi..”

“Ameen..”

Ummah ta fada, tana karasawa inda ya zauna, zuzzuba masa abincin tayi tasa shi agaba ya fara ci, Alokacin Garzali da Abban su suka shiga ciki, Da alama Garzalin ne ya dakko Abba awajen aiki, dake Abban yanzu visiting lecturer ya zama kawai, da yamma yake zama a shagon da Shamsudden ya bude masa, anan cikin kasuwar tarauni! Kamar karamin yaro haka Shamsudden ya rungume Abba ya kankame shi, Sun jima a haka kafin Abban yace,

“Toh cika ni ‘dan albarka! Ci abincin ka karya huce, ai ni na dauka wani baturen ne ya biyo ka ashe kai ne, Masha Allahu, Allah yasanya albarka a karatun ku, ya dafa muku..”

“Ameen!”

Dukkan su suka fad’a, Ummah sai kallon su take yi, Don bakaramin burgeta suke ba, musanman dake auren yarinta su kai itada mai gidan nata, sai ya zamto kamar su Shamsudden din ‘kannen su ne ba ‘ya’yan su ba, Tare suka cinye abincin tas, Shamsudden na yaba santin dadin girkin Ummah, Suka shiga hira, sai sallah ce kawai ke sasu su tafi masallaci su dawo, ta isha’i kuwa a gidah sukayi jam’i, Nan suka shjga hirar yaushe gamo? Cikin hira Abba ke cewa da Shamsudden,

“Yanzu kuma sai fafutukar neman aiki ko?”

Shamsudden dake k’ok’arin jona wayar sa a power bank yace,

“Toh gashi nan dai Abba, ai sai mun fara yin bautar ‘kasa tukun sannan a shiga zancen aiki, ni fa Abba bama nasan wani aiki, kasuwanci na ya ishe ni..”

Garzali yayi murmushi kafin yace,

“Ko kanada kyau ka dad’a da wanka auta! Kudin aikin da zaka samu yasa ka toshe wata kafar..”

Ummah dake gefe tace,

“Toh Allah ya xaba abunda yafi alkhairi dai, amma neman aikin ma yanada kyau”

“Yaron dake shagon kama a jakara jia mukai waya yake cewa, kayan ciki sun yiwa shagon/kiosk kadan, na ce masa toh za’a duba agani dai tukun..”

Cewar Abba, ya karasa fad’a yana gabzar namijin goro, Shamsudden dake gefe yace,

“Insha Allah zuwa gobe ko zan shiga unguwar nagani..”

“Hakan yayi, domin danlami mai adai-daita sahun kama ba shida lapia nace zanje na dubo shi, Toh tunda ka dawo sai mu je kawai..”

Cewar Garzali, cikeda muryar tausayawa Shamsudden yace,

“Ayyah! Allah ya bashi lapia yasa kaffarane, da fa shi nace zan kira ma ya ‘dan zazzagaya dani gurare!”

“Ya kamata ka sai ‘yar mota ai”

Cewar Abban su, Shamsudden ya jaddada kai alamun Toh, amma azahirin gaskia bashida niyyar siyan wata mota, Nan dai suka shiga lissafawa Shamsudden ‘karuwar abubuwan da kasuwancin sa ya samu, Abban su ya ‘kark’are da,

“Yanzu Alhamdulillah kanada shagunan kayan masarufi (provision store) guda uku a jakara, Kanada gidan gona guda hudu d’aya a sumaila, d’aya a maidile, d’aya anan ‘kasan tarauni, sai daya acan cikin farawa, akwai gidan kiwon dabbobin ka guda uku suma, d’aya a sani kauyen Sumaila, d’aya yana fagge sai daya a tal’udu, sannan akwai gurin kiwan kajin ka dasu zabbi, shekaran jia ankai barun ka, da kuma salwa da talatalo, Sai sabon gurin ka nan cikin unguwar sulaiman crescent dake nassarawa Local Govt. ‘SAB (Shamsudden Al’amin Buhari) POULTRY AND AQUATICS LTD’, abun dai sai hamdalah kawai, sannan yayan ka ya tambayo filin kusa da shi har sunyi ciniki, wai me zaka bude awajen ne?”

Shamsudden dake hawaye tun lokacin da Abba ya fara magana, yai saurin gogewa, cikin dakushewar murya yace,

“Abba bani da bakin gode muku, kalmomi sunyi kadan wajen kwararo godia ta agare ku, kai da Yaya da Ummah kunyi matukar ko’kari wajen bunkasa harkar kasuwanci na, Nagode Allah ya sa muku da gidan aljannatul frdaus..”

Ummah dake gefe tai murmushi kafin tace,

“Alhamdulillah! Allah yasa nasibi akai gaskia, Allah ya kara daukaka ameen!”

“Ameen.”

dukkan su suka ce, Cikin rawar murya Shamsudden yace,

“Baba so nake na bude kaman penthouse haka, da library da zai kunshi wajen shan coffee da snacks haka, gefe d’aya kuma research center da cafe, shine nakeson nayi amfani da sunan: LIBROS/CAFFE24 (SAB PENTHOUSE AND MORE)..”

Nan suka shjga sanyawa abun albarka, aka shiga wata hirar, cikin hirar ne Shamsudden ya dubj Garzali kafin yace,

“Yaya studies din?”

“Alhamdulillah Auta!, kaga yanzu na fara PhD..”

“Alhamdulillah! Nima inason fara phd dinnan amma gaskia sai na huta, maybe ma sai nagama nysc Insha Allah..”

Garzali ya ‘kyakyale da daria kafin girkin gwada/kwaikwayar muryar Shamsudden yace,

“Wai dan girman Allah karatun bokon nan shi za'a tambaye mu a kabarin mu? ahh nace na gama neman ilimin boko dole sai nayi ne? gaskiya ni babu wata *Dabo English academy* d'in da zanje bare na b'atawa kaina lokaci, idan naje guri ban iya turanci ba dan Allah a zageni ko ayi min dariya, ba dai abinda mutum yake ji dashi zai yi amfani ba? toh ayi min turanci sai nayi hausa dan shine yare na.”

Shamsudden ya shiga babbaka daria harda rike ciki, gaba d’aya parlorn ya hautsine da dariar su, cikin daria Shamsudden yace,

“Such is life (haka rayuwar take), wai Ni Shamsudden ni ke da wa’danna kadarori, Idan na duba rayuwa ta ta baya nakan yi murmushi, babu irin sana’ar da banyi ba, rake ne, charging wayoyi, siyarda hatsi, kayan masurufi, kiwon baru and lots of others, indeed Allah is the most merciful,Allah ya cigaba da dafa mana Ameen!”

“Ameen..”

suka amsa baki d’aya, hira sosai suka dinga yi, domin Yaya Garzali dama anan zai kwana, takanas yace matar sa Afiya ta tafi gidan su, sa had’e gobe, shima yana bukatar kebancewa da iyayen sa, hakan kuwa akayi, sai hira suke yi, inda Shamsudden ya karkare da cewa,

“Inason bude sashen boutique ma a cikin penthouse din, domin nayi order kaya daga Switzerland, tare zasuxo da kayana da y’ar tsarabar da nai muku, Insha Allahu soon, zuwa first week of next month zasu iso a cargo..”

Sai da dare ya tsala, su Shamsudden sukaiwa Iyayen su saida safe suka koma ‘dakin Shamsudden, Nanma wata hirar suka dasa bayan sun idar da sallar daren su, sai bayan asubah sannan suka shiga ramuwar baccin jia...

*WASHE-GARI*

Da safe unman su khadija ta harhada mata kayan abinci acikin wani ‘katon basket, gefen zaninta ta kunce ta dakko dari biyu, tana jaddada mata da,

“Kinga khadija ki dena cin wani magani wallahi, tun d’axu mai Opay yana jiran ki a waje, Dan tsabar wulakanci amma kin ki ki fito ki tafi ko? Wallahi ni da kene, muddin naji ance ga yadda kika shiga gidan wallahi kika dawo gidan nan sai na gunguri uban ki wallahi, zagewa zanyi na lakad’a miki duka wallahi, yarinya sai shegen fad’in rai, mata nawa ta tsallake tace sai ke zata had’a da ‘danta? Uhm? Zaki fito ki wuce ko sai na shigo cikin dakin na karairaya ki?”

Khadija dake cikin daki ta janyo zurmemen hijab ta zura, sai ‘kunk’uni take yi, haka tafito tsakar gidah wajen umman nata, tana cin magani, Dari biyun umman ta mika mata tana fadin,

“Mai Opay din yasa miki a wallet gashi nan, ki kai mata abincin nan, ku gaysa, kuma ba ynxu zaki dawo ba, Zan kira ki tukun..”

Khadija ta zumburo baki tana kunkuni tafita daga gidan, tana zuwa ta mikawa mai adai-daita sahun tace yasa mata a wallet, tunda suka fara tafiya take mita ita kadai, ta kamo sunan Shamsudden ta kunduma masa ashar yafi sau dari, Mai adai-daita dake kallon ta ta cikin mudubi yace,

“Yayata lapia kuwa?”

Dama a hak’e take da kowa, dan haka ta shiga surfa masa masifa, cike da isa tace,

“Sa’idunawa ana ruwa kuna kirgawa masu bacci da ido d’aya..Ina ruwan ka? Ba nason shisshigi da fad’i ba atambaye ka ba”

Shi dai mai Opay shiru kawai yayi, Dan yaga alama babu alamun hankali a tattare da ita, har kofar gidan su Shamsudden ya kai ta, sai data mula tasha iska tukun sannan ta biya shi, ta fice tana kara sakin wani tsakin akaro na ba adadi.. Bakin ta ‘dauke da sallama ta shiga cikin gidan, tanata ayyano rigar y’ar sharar shamsu, da wannan kan nasa mai ‘kuda-kuda, batasan lokacin data ja wani mugun tsaki ba, lokacin kuma Ummah tafito kenan jin sallamar da ake ta dokawa..

“A’ah Wa’alykm Salam! Dijama kece?, maraba shigo mana..”

Cewar Ummah, Khadija ta kakaro murmushi, ta durkusa tana gaishe da ummah, dai-dai lokacin Shamsudden ya fito zai..............



MX
*KAI MIN HALACCI.....💕*
*(Legacy Of Unrequited Love)*

*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER; MISS XOXO🧕🏼*

*PAGE; 34*

Sake bud'e ido tayi tana kallan rubutun sai faman sosa idanuwa take cikin son tabbatar da sunan da ta gani wato SAHAL, wani banzan murmushi ne ya kwace mata zuciyarta na zafi tare da jin tsanar ganin sakon. ‘Karasowar Amina Modu wajan shine yasa ta saurin saita nutsuwarta suka jera suna tafiya suna hirar sai dai gaba d'aya hankalin Fa'iza baya jikinta yana can yana tunanin sakon da aka yi mata har suka k'arasa gate, sallama suka yi kowacce ta shiga napep ta nufi gida batare da sunje coke village din bama dake new site.

Sai da tayi wanka taci abinci tayi duk aiyukan da tasan zata yi sannan ta shiga d'aki ta kwanta tare da janyo wayar ta, kai tsaye messages ta shiga ta kuma karanta sakon tana tunanin abinda zata ce saboda tsananin mamaki da yake neman rikita mata brain. Numbernsa ta nemo a cikin wayarta tayi kundunbala wajan kiransa, wannan shine karo na farko da zata fara kiransa a karan kanta kasan cewar duk shine yake kiranta, amman ita koda wasa bata kiransa. Kamar daman jiran kiran yake domin ringing d'aya tayi ya d'auka, ita Fa'iza ma sam bata ji lokacin da wayar ta fara dialing sai ji kawai tayi yace.

“Alhamdulillah my soulmate”

D'an k'aramin tsaki taja wanda iyakarsa makogwaranta, cikin b'acin rai kamar tana gabansa tace dashi,

“Naga text message d'inka, karka tabbatar da cewar Yaya Sahal ne Yayan Husnah sannan saurayin 'yar uwata Nana Aisha ma'ana Sissy liya, idan har hakan ya tabbata kaine ina son kayi gaggawar fita daga cikin rayuwata domin ni ban iya cin amana ba ka gane ko?”

Shiru yayi tamkar wanda yake d'aukar darasi, jin tayi shiru kuma da alama shi take jira yayi magana, sai yaja numfashi tare da saukeshi har saida Fa'iza taji shi can cikin kunnanta, ta harari wayar tamkar itace tayi mata laifi muryarsa a matuk'ar sanyaye taji yana cewa,

“When zamu had'u dake please? Ina sone zamu yi magana dake ta fahimta, dan Allah koda gidan aunty Yagana kizo mu had'u, badan nakai matsayin da zaki yi min wani abun ba sai dan Allah dana rokeki dashi..”

Kamar zata musa mishi sai dai kawai ta fasa domin itama tana son tayi tozali da Shamsuddeen kasan cewar tun ranar da suka rabu bata sake jin daddar muryarsa ba bare kuma ta sanya shi a cikin idanunta da kullum suke mararin sake kallan kyakyawar fuskarsa,

“Shikenan! jibi zanje gidan da yamma.”

“Yauwa na gode my Soulm....”

Bata bari ya k'arasa fad'a ba tayi saurin katse kiran daman kuma ga Aliya ta shigo dan haka ba zata bari ma ta gano cewar waya take yi ba. Jakar hannunta ta wurgar saman katifa tare da fad'awa itama ta kwanta tana furta.

“Wash Allah na.!”

“Kin gaji ne Sissy?”

“Ba dole ba, duk da kawo ni aka yi amman ji nake kamar da kafa nazo. Kinsan da kyar Nawal ta bari na taho?”

“Allah sarki Nawal ai tana sonki da yawa, ki duba kiga tazarar dake tsakaninku amman bata nuna tafi ki ko taki zuwa nan gidan, kina ganin idan tazo ma babu abinda takeji ko kyankyami ko wulak'anci haka, Allah dai yayi taku taxo d'aya.”

Murmushi Aliya tayi ita kanta tasan suna kaunar juna ita da Nawal, sosai aminci ya shiga tsakaninsu dan har abinda ya faru tsakanin ta da malam Dino duk sai da ta bata labari. Aliya ta mike zaune tare da kallan Fa'iza tace.,

“Ke yaufa an gama da batun malam Dino har an kawo mana wani sabon lecturer d'in.”

“Kai dan Allah? Meya faru?”

“Hmmm kamar nasan idan nayi recording d'in nakai sukaji zasu goge na wayata, shine ina fitowa nayi sending d'insa zuwa wayata kinsan dole sai na gaya miki. Aikuwa suna gama sauraro HOD ya tura wayarsa ya goge nawa, na baro ance za'a kai masa form d'in resignation, gashi yau da sabon lecturer muka yi darasin mu na yau.”

Zaro ido Fa'iza tayi tare da cewa,

“Kai! Da sauri haka?”

“Eh toh mai za'a jira?kinsan exam zamu fara ranar Monday kinga ai dole a nemo wanda zai karb'i course's d'in kodan yin marking, kinsan waye sabon malamin?”

“A'a sai kin fad'a yanzu.”

“Wannan Garzalin na gidan malam Al'amin Buhari, yayan Shamsu.”

Sai da gaban Fa'iza ya buga lokacin da taji Aliya tace taga yayan Shamsu domin ji tayi kamar tace mata Shamsuddeen d'in ta gani. Ganin yadda Fa'izan tayi ne yasa Aliya kura mata idanuwa tana son jin karin bayani akan reaction d'inta. Murmushi ta kirkiro tare da janyo wani littafinta dake gefenta tana bubbudewa tace da ita.

“Tab kice Yaya Gazah ne sabon lecturer d'in? Lallai ina taya ku murna.”

“Wallahi kuma ko Sissy? Ya iya lecture mai shiga cikin kwakwalwa, yau dai ko kai ka kawo rashin fahimta babu abinda zai hanaka ganewa, kinsan babu wanda yaso aka gama, kowa cewa yake sir a cigaba kawai shi kuwa yana murmushi, wannan yayan nasa yafi Shamsu kyau da aji wallahi.”

Da sauri Fa'iza ta d'aga ido tare da kallan Aliya, cikin tsantsar mamaki tace,

“Toh ke yaushe rabonki da kiga Shamsu bare harki tabbatar da Yaya Gazah yafi Shamsu kyau?'”

“Tab yaushe rabona dashi, tun ina kwaila lokacin da ya lekoni a bayi.”

Dukansu dariya suka yi tare da tafawa kafin Aliya ta zaro babbar wayarta, recording d'in ta sanyawa Fa'iza itama taji tana ta salati tana rik'e goshi, sai da ta gamaji tas sannan Aliya ta goge saboda tsoran kar wani ya tura wayarsa yaje yana yamad'id'i dasu.

“Allah ya shirya shi toh, wallahi da ina ganin mutuncin malamin nan saboda yakan zo wajan wani abokinsa shima lecturer d'in mu ne anan ma ni na sanshi, banza wallahi ya bata min rai.”

“Kedai kawai sai addu'a duniyar nan babu gaskiya komai son zuciya yayi yawa sai fatan Allah ya tsarkake mu su kuma masu yi ya shirye su.”

Daga haka sukaci gaba da hirarsu sam Fa'iza bata sanar da ita maganar Sahal ba hasalima ita zuciyarta bata gama tabbatar mata da cewar Sahal saurayin Aliya shine yake mata wannan abun, ta d'auki hakan kawai a matsayin shi Muhamman S d'in yasan Sahal shi yasa yake yi mata wasa da cewar ai shine, amman tana jiran ranar asabar tazo taje gidan aunty yagana suyi ido hudu dashi harma ta sanar dashi burin zuciyarta. Haka dai suka ci gaba da rayuwar su suna ta karatu, ranar asabar daman tun daran juma'a suka sanar da Umma, ita Fa'iza tace gidan aunty Yagana zataje yayin da ita kuma Aliya zasu je duniyar Maman su kawarsu ita dasu Nawal da Nour da sauran wasu daga cikin department d'insu.

Haka aka yi kuwa washe gari asabar bayan anyi sallar la'asar rana tayi sanyi wajan karfe hudu duk suka fito cikin shirin su, cikin laffaya suke ta fa'iza yellow da ratsin fari a jiki yayin da ta Aliya ta zamto green da ratsin baki a jiki. Sunyi kyau sosai yaran sai san barka, Fa'iza tayi musu sallama domin ita napep zata hau ita kuma Aliya su Nawal zasu biyo gidan su dauketa hakan yasa fitar tasu ta banbanta. Taci

Please Login or Register in order to submit comment