Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'auka ta kara a kunne.

“Sweetie na karaso.”

“Okay tom bari nasa Humaira ta shigo dakai.”

“No ke nake son na fara gani kuma ke nake son ki shigar dani ciki.”

“Toh gani nan one minute.”

“Na baki sweetie.”

Ajiye wayar tayi tana murmushi mai dauke dajin dad'i, bata tab'a sanin cewar soyayya akwai dad'i ba sai yanzu da ta mallaki Shamsuddeen suke soyayya. Juyawa tayi tana kallon Aliya data gama waya da Mu'azzam tana game tace da ita.

“Sissy bako fa zanyi gashi harya zo.”

Ba tare da ta dago daga kallon wayar da take yi ba tace mata.

“Yayi kyau.”

Babu wanda ya sake cewa komai har Fa'iza ta yafa mayafi tasa takalmi ta fito, wajan Umma ta nufa dan sanar da ita bakonta ya iso zataje ta shigo dashi Umma tace to. A can kuma k'ofar gida Shamsuddeen ne da Yazeed suke jiran fitowar Fa'iza, shi Yazeed ma bai san nan ne gidan su Aliya ba sai kawai ga wata motar tazo tayi parking a bayan su, sam babu wanda ya gane wani a cikinsu har sai da Sahal da Fareed suka fito sannan ne Sahal da Shamsuddeen suka had'u gaban Sahal yayi wani irin bugawa domin yasan Fa'iza ce ta bawa Shamsu izinin zuwa gidan su, gashi kuma dole yaje ya gaida abokinsa kuma ogansa a wajan aiki. Fuskar ko wannensu cike da murmushi banda ta Sahal da take ta yake akace yafi kuka ciwa, suka yi musabuha da juna daga nan Yazeed kasan cewar duk yasan su shima yace da Fareed.

“Ina zuwa?”

“Wallahi abokina na rako bawa shuka ruwa.”

“Oh daga gidan gona kuke kenan?”

“No tad'i mukazo.”

“Ohh anan gidan?”

“Eh wallahi.”

“Masha Allahu wajan wa kuka zo muma shi muka zo.”

“Uhmmm wajan Faizaah.”

Nan da nan suka kalli juna su duka hudun, sai aka bar Fareed da Yazeed wajan yin maganar.

“To waye yake son Faizaah a cikin ku? Kai ko Sahal d'in.?”

“Sahal mana, kai kuma kaine kazo ko Shamsu?”

'”Ahh ni Oga na rako, kan uban can, yanzu what shoul...”

Kafin Yazeed ya karasa magana sai ga Fa'iza ta fito hakan yasa duk suka bita da kallo yayin da ita kuma gabanta ya buga tamkar zai fad'o tsabar tsorata da tayi da ganinsu su duka.

“Wannan ce Faizaah'n?”

Cewar Yazeed yana kallon Shamsuddeen wanda yama rasa uban da zai yi, yayin da Sahal ke tsaye hannunsa dafe da saitin kirjinsa da alama zuciyarsa ke yi masa zugi duba da yadda yake faman rintsa ido akai-akai.

“No I think gurin Aliya yazo ko?”

Cewar Shamsuddeen yana kallon Sahal wanda ya kasa cewa komai, ita kuwa Fa'iza cak ta tsaya a bakin kofa ita bata koma ciki ba, sannan ita bata fito ba dan bama tasan yadda zata yi ba. Da mamaki jin an ambaci Aliya Yazeed ya kalli Shamsuddeen yace.

'”Aliya kuma? Wace Aliyar kake nufi? Wai kota caffe?”

“Itafa.”

“Nanne gidan su daman?”

Cikin gajiya da bashi amsa yace.

“Kwarai kuwa, wannan sister d'inta ce, shi kuma Sahal a yadda na sani shine saurayin Aliya ban san lokacin da ya dawo soyayya da Fa'iza ba.”

Mamaki ya kusan kashe Yazeed sai ya matsa can gefe d'aya ya zaro wayarsa yana k'ok'arin kiran Aliya. Tana kwance tana game har lokacin dan ba karamin d'auke mata hankali game d'in yayi ba, sunan sir Yazeed ne ya bayyana dan haka ta yatsina fuska dan tasan kila magana zai yi mata akan Shamsuddeen ita kuma baso take yi ba, ganin yadda yake ta faman kira yasa ta d'auka muryarta tamkar irin wacce ta tashi daga baccin nan ta fara gaida shi, amman sai taji yace.

“Ina k'ofar gidan ku please idan babu damuwa ki fito dan Allah.”

“Kai da CEO ne?”

“Bazan miki karya ba amman dan girman Allah kar ya hanaki fitowa kizo ina son sanin wani abu ne please.”

“Shikenan amman wallahi banda kace Allah da bazan zo ba saboda bana son duk wani abinda zai had'a ni dashi.”

Katse kiran tayi tare da sakkowa daga kan gadon, babu abinda ta tsaya shafawa kawai hijabin da tayi sallah ne ta dauki tasa tare da daukar wayarta ta fito. Tana fita taga Shamsuddeen gefe d'aya Sahal ne kusa da Fa'iza kuma Fareed ne sun sata a tsakiya da alama magana suke yi, ita kuma tayi musu banza tana d'aga kai taga inda zata hangi Yazeed. Hannunsa ta hango yana d'aga mata daga can nesa sannan ta fito ba tare da ta kula kowa daga cikin su ba ta wuce wajan Yazeed d'in. A can wajan su Fa'iza kallonta Fareed yayi cike da son ta sanar dashi gaskiya yace.

“Toh ke gashi duk sunzo da kokwan barar neman auranki, ki tsaya ki nutsu ki bawa zuciyarki abinda take so, shi dai gaskiya Sahal ya riga ya illatu da soyayyarki, shi kuma Shamsuddeen a yadda na lura baku dad'e da fara soyayya ba, shin a cikin su wanne zaki iya aura?”

Kallon Shamsuddeen tayi wanda ya kawar da kai zuciyarsa cike da fargabar karta dizga shi, amman sai ta kasa yin magana sai hawaye da suka fara zirarowa daga cikin idanunta, jin yadda take kuka shine yasa Sahal yin murmushin k'arfin hali ji yake tamkar shima yayi kukan saboda yadda zuciyarsa ke zugi yace.

“Karka takura mata Fareed, na hakura da soyayyar Fa'iza tunda Ogana yana so kuma itama zuciyarta tafi karkata akan shi. So daga yau daga rana mai irinta yau ba zaki sake gani na ba sai dai ko a hanya, ina muku fatan alkairi cikin rayuwarku, Allah yasa shine farin cikin ki a duniya. Amman ki sani Fa'iza ina sonki so irin wanda baki ba zai iya furtawa ba, hannu bazasu iya rubutawa ba sai dai kawai nace miki, If the only place that I can meet you is in my dream, I don't want to wake up anymore, bye-bye Faizaah....”

Yana gama fad'a ya juya da sauri saboda wasu azzababbun hawaye da suke shirin zubowa daga cikin idanunsa, Fareed ya kalli Fa'iza sannan ya kalli Shamsuddeen kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru tare da juyawa yabi bayan Sahal dake ta k'ok'arin bud'e mota amman ya kasa, cikin sauri ya bud'e masa ya shiga ya zauna sannan shima ya shiga drive seat ya kunna motar suka bar wajan. Shamsuddeen ya kurawa Fa'iza ido ganin yadda take razgar uban kuka sai ya fara tunanin anya bata son Sahal kuwa? Amman dan ya tabbatar domin ba karamin tausayi Sahal d'in ya bashi ba yace mata.

“Faizaah kina son Sahal ne?”

Tayi shiru domin ita kanta taji wani iri lokacin da Sahal din yake mata bankwana, sai dai soyayyar Shamsu tana ranta dan haka ta girgiza masa kai, ya gyara zama tare da cewa.

“Banzo da wasa nan k'ofar gidan naku ba, Fa'iza batun yanzu ba nasan cewar kina sona kawai dan dai a baya ina son 'yar uwar kine shi yasa kika kasa bayyana min, nima a lokacin idona ya rufe shi yasa na kasa gano manufarki amman a yanzu a shirye nake dana aureki idan har kin bani wannan damar.”

Gabaki d'aya sai ta rasa inda zata tsoma ranta, wani irin farin ciki ya mamaye ta sai dai ta kasa b'atar da yanayin da Sahal ya tafi dashi, ji take tamkar ta bishi ta bashi hakuri amman babu dama, tana share hawaye kwalliyar da tayi duk ta b'aci saboda kuka tace masa.

“Kazo mu shiga ciki.”

'”A'ah Faizaah wallahi tsoran masifar gwaggo nake karta ganoni.”

Tayi murmushi tare da sunkuyar da kai tace.

“Kazo muje bama tasan da zuwanka ba, sannan nasan bama zata zo inda muke ba.”

Shamsuddeen ya jinjina kai tare da juyawa ya kalli inda Yazeed yake, tare ya gansu da Aliya ita a zaune saman wani dutse shi kuma a tsaye a gabanta ya rungume hannaye bakinta sai motsi yake alamun magana take yi masa. Hannu Shamsuddeen ya zura cikin mota ta glass ya danna horn hakan yasa Yazeed kallo gurin nan yayi masa alamun yazo amman ya girgiza kai alamun a'a yaje ya gama ya fito shi kam yana nan yana shan labari mai cike da tsantsar mamaki da damuwa. Haka aka yi Fa'iza tayi masa jagoranci har cikin parlourn Baba Suleiman inda ta shirya masa abubuwan tarba, ya zauna akan kujera yana karewa parlourn kallo. Can nesa dashi ta zauna kafin ta kuma mik'ewa taje ta zuba masa abubuwan data tanadar masa shi kuma sai kallanta yake amman hankalinsa yana can wajan su Yazeed wanda bai san abinda suke tattaunawa ba.

Su kuwa Yaseed ne ya nuna mata kan dutsen bayan taje inda yake, suka gaisa cikin mutunci tare da wasa da dariya kafin ya gyara tsayuwarsa ya kalleta yace.

'”Aliya tambayar ki nake son nayi, amman dan Allah ki gaya min gaskiya.”

“Indai nasani zan gaya maka sir Yazeed saboda kayi min komai da nake so babu abinda zance dakai sai godiya.'”

“Godiya nake, ammh dama sonake naji dan Allah meke tsakaninki da CEO? Yace min a baya ya soki sai dai ke ba hakan bane, amman abinda na lura dashi a dan zamanku tare kamar akwai wani abu daya kasa mantawa wanda kuma kila kece sila shi yasa yake neman yin ramuwar gaiya, shin menene?”

Dariya Aliya tayi dan sosai abin ya bata dariya, cikin rashin damuwa tahau bawa Yazeed labari sai dai itama ta boye masa leken toilet saboda tana ganin kamar sirrinta ne. Ta karkare da cewa.

“Sahal shine wanda nake ce maka zan aura, toh shi kuma yace daman tun farko soyayyar kanwa yake min kaga dole na rabu dashi ya auri zabinsa tunda shi namiji ne.”

“Haka ne amman ni a yadda nake ganin lamarin CEO wallahi har yanzu yana sonki Aliya, abinda yasa nace haka tunda mukaje karatu har kawo lokacin da muka baro Switzerland baya kula ko wace bebe, gashi da shegen farin jinin 'yan mata amman wallahi baya kula su cewa yake ma bashi da lafiya, sai gashi kinzo ma'aikatar shi duk yabi ya addabi kansa wasu abubuwan yakan yi amman bai san dalilin yinsu ba kuma duk akanki,shin mai zai hana ku amincewa junanku kuyi soyayya tunda ke wanda kike so din 'yar uwar ki yake so, shi kuma nasan karya zuciyarsa take masa baya wani son Faizaah wallahi.”

“Toh amman a ganina sir Yazeed gara kowa ya bawa zuciyar sa abinda take muradi, ni yanzu ina da wanda yake sona kuma a shirye nake da na aure shi, so ka barshi shima yayi abinda yake ganin yafi masa kaga babu wanda zaiga laifin wani a cikin mu.”

'”Aliya kina son Shamsuddeen?”

“No! sir Yazeed bana sonshi tuntuni so kaga babu batun yin aure tsakanin mu.”

“Toh shikenan Allah ya zab'awa kowa abinda yafi alkairi.”

“Amin dan ni yariga ya zab'ar min.”

Dariya Yazeed yayi jin yadda tayi saurin amsa masa daga nan hirarsu suka yi har lokacin da Shamsuddeen ya fito shida Fa'iza. Booth ya bud'e tare da zaro wata katuwar leda babba ya dire mata a gabanta tare da cewa.

“Gashi nan babu yawa sweetie, idan 'yar uwar ki ta tashi wucewa ta tayaki kamawa dan nasan bazaki iya ba ke d'aya.”

Fa'iza tayi murmushi tare da yin godiya, har Yazeed yazo suka yi sallama da Fa'iza ita kuma Aliya data tsaya gaisawa da wata makociyarsu tana ganin lokacin da sukaja motar suka tafi sannan itama tazo zata shiga gida taji Fa'iza na cewa.

“Sissy please zoki taya ni mu shigar dasu.”

Kamar zata ki sai kuma tayi tunanin karta zargi wani abun hakan yasa taje ta temaka mata suka shigar da ledar har cikin parlourn Umma, sannan Aliya ta wuce d'akin gwaggo bata sake fitowa ba sai da safe.

••••••. •••••••. ••••••.

Tun ranar da yaje gidan su Monday na zuwa yasa aka maida masa da Aliya matsayinta na sakatariya duk kuwa da cewar sun kusa gama siwes d'in, tunda taga haka tasan so yake ya samu damar da zata sanya ta samu matsala a siwes d'in dan haka koda ta koma matsayinta kullum cikin yi masa biyayya take har ya zamana ya rasa ta inda zai gano kuskuranta. Sai ma wasu bakwannin al'ammura ne da suka fara wanzuwa a tsakaninsu cikin wannan d'an datsin da Aliya take shirin barin ma'aikatar. Tana zaune a can seat d'in ta aiki kawai take saboda ganin suna neman yi mata yawa, wayarta dake gefe ce ta fara ringing tasa hannu ta d'auka taji yace.

“Ina son ganinki.”

“Okay gani nan.”

Ta fad'a tare da ajiyewa ta juya tana hangensa ta cikin transference glass din daya raba tsakaninsu, ai kuwa suka had'a ido taga ya sakar mata murmushi ta lumshe ido tare da juyawa ta fito tana murmushi. Sallama tayi tare da shiga idanunsa kur a kanta taje ta tsaya tana murmushi tace.

“Sir gani.”

“Zagayo nan kiga.”

Cikin rashin damuwa bata yi zaton komai ba saboda taga yana bud'e wani document dake gabansa da alama wani abun ya gani wanda zai tambayata a ciki shi yasa taje kusa dashi d'in kai tsaye, tana zuwa cikin rashin.......

_*BUK OLD SITE_*

Zaune suke a cafeteria, sun gama cin abinci suna hirar lecture din da suka gama, Fa’izah dake gefe kusa da Amina Modu tace,

“Babes! Raheenah fa shiru bata zuwa school tunda mukai resuming.”

“Kuma fa haka ne...”

Amina Modu tafada tana jaddada kai, Suwaida Basher dake jotting ta ajiye biron hannun ta kafin ta dube su gaba d’aya tace,

“Toh akira ta awaya mana aji ko lapia? Bamu kyauta ba gaskia.”

Amina Modu ta d’aga waya ta kira Raheenah sai da tayi ringing uku sannan aka ‘dauka.

“Assalamu Alaikum, Oh Ayyah! Subhan’Allah wallahi bamu sani ba, Sai yanzu da mukaga kwana biyu bata zuwa shine muka ce bari mukira muji lo lapia? Okay wanne asibitin, Toh shikenan zamu so In Shaa Allahu! Allah ya bata lapia.”

“Batada lapia?”

Suka hada baki wajen tambayar Amina Modu. K’ada kai tayi alamun Eh, cikin damuwa tace dasu,

“Eh wallahi wai satin ta uku ma a asibiti itada Naina ta nursing’. Suna AKTH.”

“That’s serious, accident su kai?”

Suwaida ta tambayi Aminaa Modu, Fa’izah dai tayi shiru tana jimami domin Naina lesbian partner din Raheena ce, domin tasha ganin love messages d’insu. Haka dai suka jimanta abin, k’arfe 3 suka tashi daga lectures, kai tsaye suka wuce asibitin Malam. Suka kira aka musu kwatancen ‘dakin suka shiga, D’auke da ledoji biyu d’aya lemon ‘bawo d’aya kuma apples ne aciki. Hankulansu ya tashi matuk’a ganin yanayin dasu Raheemah ke ciki, gaba d’aya kowacce gadonta daban, anrufe daga’kirjin su zuwa tafin’kafa tamkar wadanda suka samu mugun rauni ko ‘kuna.

Sai wari ne ke tashi daga jikin su, Yayar Raheenan ce kawai awurin, domin sauran iyayen sunje sallah, ganin ‘kawayen su ne yasanya yayar Raheenan fita tabasu wuri. Sannu kowannen su ya shiga yi musu, Suwaida da bata shiru da bakinta sai da ta tambayi Raheenan da,

“Rahee! Meya faru daku haka?”

Nainah dake kan gadonta a kwance sai kwararar hawaye take yi kawai. Raherrnan ma haka, cikin sa’a kuwa Dr Damboa ya shigo ‘dakin shida wata nurse dauke da allurori. Yad’an dudduba jikin su, sannan ya fara tambayar su,

“Meke damunku yanzu? Amma tsutsotsin sun dena fitowa ko? Babu itching din yanxu?”

“Tsutsotsi?!”

Kowacce cikin su Fa’izah tafara tunani, Raheenah ta amsa dakyar

“Gaba na yana zafi dai dr, kuma dazu sister na tace taga tsutsa d’aya ya fito.”

“Ni dai duk babu amma dr gabana yana zafi kamar anzuba yaji awajen.”

Naina tafada dakyar, Su Fa’izah sai suka maidasu tv, kowannensu da abinda zuciar sa ke kawo wa. Dr Damboa ya jaddada kai bayan ya duba gaban kowaccen su yace,

“In sha Allahu it shall be well, with time zaku denaji, shekaran jia akai operation din so dole sai a hankali ku dai cigaba da addua kawai, ALLAH ya tsare gaba.”

Yana gama fad’a ya fice shida nurse din. Raheenah tayi murmushin ‘karfin hali tace,

“Nasan ku zakuyi mamakin haka, Amma Fa’izah tasan komai, Saboda nayinayi na janyota ta shiga harkan mu taki, idan ba zaku manta bama last taron da akai na Mss ai Amira tayi bayani akan illolin da Mad’igo ke haifarwa, Toh long story short dai lesbianism ne janyo mana haka nida Naina, kaicon mu domin gaba d’aya yanzu gaban mu ya rub’e, tsutsotsi na fita ta duburar mu da gaban mu. Dan Allah Fa’izah da sauran ku kuyafe mana, Kuma ku tayamu neman gafarar ubangiji..”

Tana gama fad’a tasa kuka, Naina dake kan gadonta tana numfashi dakyar tace,

“Bayan anyi hutu ne naje gidan su Rahee mu kayi masha’armu sai gabanmu ya fara fitarda wani irin ruwa mai wari da guda gudan jini, shine muka zo asibiti, ashe asirinmu ne zai tonu, Shikenan mun ‘bata rayuwar mu, babu irin wa’azin da Fa’izah bata mana muka toshe kunnuwan mu bama ‘daukar maganar ta..”

Ta fashe da wani irin kuka, Gaba d’aya sai jikin su Fa’izah ya ‘kara yin laushi suma suka shiga matse nasu hawayen, domin dole ka koka musu idan ka gansu, gaba d’aya sun jele tamkar ba su yan gayu a daba, suna ganin sunacin duniar su babu babbaka sai gashi rana tsaka ALLAH ya kamasu tun a gidan dunia. Raheenah ta goge majinar hancin ta, cikin rawar murya ta sake cewa,

“Hakika mun ‘dauka cin kashin kanmu muke ALLAH bazai kama mu ba, domin muna gamsuwa da junanmu, Idan bamuyi ba har jin gaban mu muke kamar ana tsinkulunmu yana tsirawa dole sai munyi mukejin dai dai, ashe tsutsotsi muke baiwa abincin su, muke renen su a gaban mu, bamuda masaniya, Lalle Fa’izah kinyi gaskia da kikace mun fada kogin halaka, mun cuci kanmu, mun’bata rayuwar mu, kuma bamuyi wa iyayen mu HALACCIn tarbiyyar da suka bamu ba...”

Haka dai Naina da Raheenah suka cigaba da basu labati suna kuka, Su Fa’izah suka basu baki had’a da ‘kara fadakar dasu akan illolin da Mad’igo ke haifarwa, gurbata lapiar jiki yake haifarwa da samun b’ulluwar wani ciwon, yin fatali da tarbiyyar iyaye sannan yana kara kusantarwa ga shed’anu yana kuma nisanta ka ga ibada uwa uba sab’awa Allah, dayin fatali da sunnar da manzo yace muyi koyi dasu na aure da sauran su, Amma saboda dabbanci da sab’awa Allah da neman zaman dunia wasu ke bin junan su suna mu’amala tamkar ma’aurata, shin wane dadi zakiji ajikin yar uwarki mace? Me take dashi da baki dashi? Allah ya halarta maza da mu aure su mu raya sunnar manzo S’A’W! Amma Saboda gidadanci da aiki da ‘kwakwlwar alade kike biyewa yar uwarki mace, Tir da masu aikata haram irin nasu Raheenah, ALLAH ya shrya ya kuma sanya ku gane gaskia, mu da bamayi ALLAH ya kara karemu ya tsarkake mu dunia da lahira.. Haka su Fa’izah sukaita basu baki har iyayen suka dawo sukai musu sallama suka tafi, tunda suka tafi suke maimaita zancen, gaba d’aya a tsorace suke da sharrin’kawa da kuma dunia,

Lalle annabi ya rok’a mana, da tuni ankife duniar nan wallahi! Allah ya karawa Annabi daraja, Allahumma salli Ala sayyiduna muhammadin wa ashabihi wa sallim, Toh duka duka anan na kawo ‘karshen ‘bangaren su Raheenah, yan uwa kunga yadda masu irin halinsu suka ‘kare tun a dunia, Lalle wata shari’ar sai a lahira, ALLAH ya ‘kara karemu da tsarkakemu daga aikata aikin dana sani...
___
?_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*_MISS XOXO🧕🏼_*_


_*NO: 44D_*

Cikin rashin sa'a ya waigo kenan suka yi gware da goshinan su, Aliya ta rintsa ido tare da dafe gurin saboda wani jiri da taji yana niyar k'ofar da ita a gurin. Shima rik'e goshin nasa yayi sai dai bai kaita jin azabar ba saboda yanayin halittar jikinsu ba d'aya bane. jan baya tayi sai da ta dawo normal sannan ta d'ago suka had'a ido yana murmushi ya maida kansa kan file d'in yana cewa.

“Raguwa kawai.”

Dariya itama ta saki kafin ta kuma matsawa kusa dashi yana nuna mata abinda tayi kuskure a cikin file d'in sai faman d'aga kai take tamkar kadangaruwa kafin ya gama ya d'ago yana mik'a mata file d'in da alama mayar dashi zata yi sai ta gyaro shi yana cewa.

“Na gode Secretary.”

“Me nayi maka na godiya?”

“For everything.”

“Idan haka ne ai nice zanyi maka godiya tun daga yarinta har zuwa yanzu.”

“Saboda me zaki min ke?”

“Saboda kasan ance zuciya mai HALACCI bata manta alkairi duk girman sharri. Na gode daka karb'e ni a matsayin sakatariyarka, Allah ya barka da Sissy Fa'iza.”

Kallanta yayi sosai saboda kalamanta na karshe sun matuk'ar bashi mamaki domin koda wasa be tab'a zaton zata masa wannan fatan ba, shi duk a tunaninsa ma ya fara burgeta ashe ba haka bane tana son ya auri Fa'iza, ko dai kuma irin abun nan ne na kaji dashi. Cikin basarwa ya mik'e tsaye ita kuma ta juya zata tafi kawai taji ya rik'o mayafinta tayi saurin rikewa ganin yana shirin zamewa gabaki d'aya, idanunsa suka kankance, Shamsuddeen ya zuba mata su cikin idanunta murya a sarke yace da ita.

“Yazeed zaki godewa domin shine silar komai.”

Yana gama fad'a ya sakar mata mayafin tare da shigewa toilet, Aliya ta bishi da kallo ko menene manufar kamo mata mayafin oho, ko kuma ta maganar Yazeed d'in da yace har yanzu Shamsu yana sonta kawai ya kasa ganewa ne? Amman ya zai yi da soyayyar Fa'iza gashi har ana shirin turowa a tambaya a gidan su nan da ranar alkhamis. Kafad'a ta d'aga alamun ko'ajikinta ta wuce gurin zamanta tana ci gaba da aikinta hankali kwance sai ma tunanin Mu'azzam da take yi wanda yayi mata text message yana shaida mata cewar karta tafi yau ta bari dan Allah yazo ya d'auketa ya kaita gida saboda tsaro badan tsoro ba. Haka akayi kuwa tana tashi yazo ya d'auketa ya kaita gida bayan ya siyo mata kayan makeup da turaruka.

*MUHAMMAD SAHAL*

Gaba d’aya tunda suka shiga mota bai ce komai ba, Fareed ne mai driving sab’anin da dashi ne me driving din. Lokaci zuwa lokaci Fareed kan juya ya kalle shi, jinshi yai yana shesshekar kuka,

“Aboki wai kuka kake yi?!”

“A’a..!”

Cewar Sahal a hankali cikin rawar murya. Yasa hannun sa guda d’aya yana goge hawayen dake yar tsere a fuskar sa.

“Ka bani dama mana na fa’dawa su Ummi komai please, Kada ka cuci kanka Aboki, Ina ganin idan manya suka shiga maganar komai zai yi sauk’i..”

Sahal yai murmushin yak’e jin kalaman Fareed, Hannu yasanya a kan ‘k’irjin sa yana bubbugawa, Ya dubi Fareed murya a dak’ushe yace masa,

“Aboki kenan, Fa’izah bata so na, Kuma mahaifinta yace ba zan raba kan zumuncin su ba, Tunda ai Aliya tace soyayya muke da ita, Nayi admitting laifi na tabbas nayi kuskure da ban sanarwa Aliya tun farko ba, kawai dai soyayyah ba tai min HALACCI ba, ta had’ani da jidalin son maso wani, ni yanzu Aliya ce ke bani tausayi ma wallahi..”

“Aliyah kuma?! Meyasa take baka tausayi.?”

“Aboki da ciwo ne wallahi ace daga ni har Shamsun Fa’izah kowannen mu keso, bayan da kuma ita Aliyan muke kulawa, gaskia babu dadi..”

“Da ciwo gaskia, duba da Fa’izan kuma ‘yar uwarta ce, wadda suka taso wuri d’aya sun zama kamar yan biyu.”

Sahal ya dafe saitin zuciar sa yana runtsa ido, cikin wata irin wahalalliyar murya yace,

“Ni zan hak'ura da Fa’izah kawai..”

“Kana nufin zaka koma wajen Aliya kuma again?”

Fareed ya bashi amsa yana ware idanu lokacin danja ta tsaida su a titin jakara. Sahal ya ‘dan bibbigi kirjin sa kafin yace,

“No! Kawai dai na hakura da Fa’izah, don da alama tawa ta k'are Aboki. Bana jin dadin rayuwar gaba d’aya wallahi..”

“Kadena cewa haka, soyayyar Fa’izah ce tai silar jawo maka koma menene, Amman ka bani dama dan Allah na sanarwa Ummi yadda ake ciki, kalle ka mana dubi yadda ka rame tamkar ba kai ba..”

“An bamu hanu muje..”

Sahal yai saurin kad’ar da maganar yana nuna masa danjar/traffic light data basu hannu.Fareed ya girgiza kai kawai don yasan sarai Sahal kauda zancen yai ta haka, Suna zuwa ‘kofar gidan su Sahal fareed ya shigar da motar Sahal gate ya d'auki tasa ya tafi gidah ko sallama baiwa Sahal ba, domin ransa ya b’ace ganin ya babbashi shawara yak’i d’auka, Gashi nan a banza ciwon so zai kashe shi. Wai shi jarumi, Sai kace film wai ya barwa Shamsudden Fa’izah..

Sahal ya shiga gidah yana had’a hanya domin kansa barazanar fad'owa yake yi, gashi hajijiya/dizziness yake ji, idanuwan sa na masa dishi-dishi/blurred, zuciar sa kuwa tamkar zata tsaga kirjin sa ta fito saboda tsabar ciwo. A haka ya shiga parlor su Ummi na binsa da kallo, sallama kawai yayi ya wuce sashen sa. Ummi ta girgiza kai kawai, Husna dake gefe ta dubi Sahal gaba d’aya tausayi yake bata, A

Please Login or Register in order to submit comment