Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

and white, Tafka tafkan ginin bene ne guda uku, Wanda kallo d’aya zaka musu ka gano hamshak’in kamfani ne, babu abunda babu domin har restaurant akwai, da b’angaren swimming pool, Gymnasium, da research center, Foreign languages, Library, Cafe, boutique, kai abubuwan da wajen ya ‘kunsa da yawa, kowanne gini da sunan sa, Na tsakiyar an rubuta SAB PENTHOUSE AND MORE. Na gefen farko rubuce yake da LIBROS, sai na ‘karshen kuma ansa CAFFE24. Sai a sannan tunanin Aliya ya dawo, ta d’aga kanta tana kallon katafaren kamfanin dake rubuce da; LIBROS/CAFFE24( SAB PENTHOUSE AND MORE) sai walwali (glittering) rubutun suke da wasu irin arnayen fitilu, wani kakkauran yawu Aliya ta had’iye tana ‘kara tabbatar wa zuciyarta wannan katafaren wajen ko shakka babu na jajayen fata ne. Domin fasali da tsarin sa da yanayin dukiyar da aka narkawa ginin tabbas ba zaka tab’a kawo wa a kano bane.

Nawal dake bin Aliya da kallo tai murmushi kafin ta sanya hannu taja kafadar Aliya su shiga ciki, tun a farfajiyar wajen Aliya ke kokawar kwatar hannun ta, Cikin tura baki gaba tace,

“Bestie! Sake ni, wannan wajen masu hannu da shuni ne, Ina ni ina internship anan wajen? Waye ma zai ‘dauke ni? Dan Allah sake ni mu tafi, banason ma a disga mu..”

Nawal ta tuntsire da daria, Sai da tai mai isarta kafin ta sha kunu, ta ja hannun Aliya suka ‘karasa shiga ginin farkon, wanda ke rubuce da Libros, gira ‘daya ta’dagawa Aliya kafin tace,

“Kakki damu bestie! Sai an gwada akan san na ‘kwarai. Bro Sameer yace mai wajen mutumin kirki ne, kuma yaro ne, So lets try our luck. Allah hukkumo sa’a!..”

Aliya ta danji sanyi aranta jin Nawal ta ambaci mutumin kirki ne mai wajen, COO OFFICE ( chief of officers /office) nan suka ‘kwan’kwasa, Zaune yake akan kujerar sa mai jujjuyawa dinnan, sanye cikin suit army green! Yasha kyau ba ‘karya. Jin kamar ana faman doka masa ‘kofa hakan yasanya shi ‘dan daga muryar sa yadda na wajen zasu iya jiyo shi, batare da ya ‘dauke kansa daga desktop ‘din da yake dannawa ba yace,

“Yes... Come in!”



*SAY OK.. AND THEN DO WHATEVER YOU NEED TO DO, TO PROTECT
YOUR PEACE*
_*MX🧕🏼*
*41*

Ya fasa yin maganar ya wuce sama, lift yaje ya shiga wacce itace zata sadaka da office d'insa. Ita kuma Aliya office d'in Yazeed ta nufa sam batama san da wata lifta ba saboda duk lokacin da take zuwa ta step d'in bene take zuwa babu wanda wa tab'a sanar da ita ko taga yabi ta litfa ba. Koda taje bata tarar dashi ba, anan masinjansa ya shaida mata cewar Yazeed bai karaso amman CEO yana nan, cikin rashin damuwa Aliya tace.

“No ai ba gurinsa nazo ba, nazo gurin COO ne.”

“Toh ai nasan yana kan hanya ga kujera nan ki zauna.”

“Toh na gode.”

Ta fad'a tare da zuwa wajan kujerar ta zauna ta zare wayarta tana dannawa. Shi kuwa Shamsuddeen yana shiga office aiyukansa ya fara yi ba tare da ya jira Yazeed ba duk kuwa da cewar yana bukatarsa a lokacin tunda har yau bashi da sakatare/sakatariya shi yasa abubuwa suka taru suka yi masa yawa, gashi yau litinin kowa zaizo aiki. Aliya kuwa tana nan zaune suna chatting da Fa'iza har d'aukar pic d'in wasu guraren take yi sai ta tura mata a haka har mutane suka fara taruwa, harta gaji zata tashi sai ga Yazeed, yana fitowa daga lifta idanunsa suka sauka akanta saboda jan mayafin da tayi amfani dashi yana kuma sanya mutane suyi saurin dora ido akanta. Ya d'an dake yaki nuna ya santa ya nufi hanyar office d'insa, ganin kamar ba zata kulashiba yasa shi juyowa yana kallanta yace.

“Raliya biyo ni ina son ganinki.”

Yana gama maganar ya shiga office ita kuma ta faki idanun mutanan wajan ta zabga masa harara saboda ta tsani wannan sunan da yake kiranta dashi wato Raliya. Bayansa tabi ta shiga lokacin yana k'ok'arin zama akan kujerarsa, gurin zama ya nuna mata fuskarsa a sake yace da ita.

“Good morning Raliyaah...”

Ya dan ja yaaah din. Sai da ta had'iye wani yawu mai daci kafin ta kallesa taga idanunsa kur a kan fuskarta tayi saurin kawar da kai tare da cewa.

“Lafiya lau ya aiki?”

“Gashi zamu fara hajiya Raliya.”

Yayi maganar yana kashe mata ido d'aya cikin wani salo da yasa gaban Aliya bugawa amman ta maze tayi kamar bata gani ba. Shiru na d'an lokaci kafin ya gyara zama tare da gyara zaman glasses d'in idanunsa ya d'an d'ora gwiwar hannunsa saman tebur tare da kura mata ido yace.

“Hajiya Raliya, naso na barki a cafe, amman na yaba da nutsuwarki duk da kin kasance karamar yarinya kuma budurwa mai karancin shekaru, gashi baki da aure ko”

“Eh amman an kusa insha Allahu.”

Tayi maganar tana d'an murmushi sabida ta sake gano manufarsa akanta, aikuwa Yazeed ya zaro ido yana kallonta yace.

“Yaushe kenan?”

“Idan lokacin yazo zan sanar dakai sir.”

Dariya taga yayi alamun bai gamsu da maganar taba, ya maida bayansa jikin kujera yana d'an jujjuyawa yace.

“Karki min karya domin matsayin da nake son doraki anan babban matsayi ne da bama buk'atar makaryaci sai mai gaskiya. Kuma da har ina cewa CEO nayi kamun mata.”

Da sauri Aliya ta kallesa tana zaro ido tace.

“Tab! Ka rufa min asiri sir kar mijin da zan aura yace bazan yi internship d'in anan ba saboda kar ayi masa kwace.”

“Babu komai dan na kwace ki daman mace ai allura ce cikin ruwa mai rabo yake d'auka, kika sani ko nine rabon.?”

“A'a nidai sir ka rufa min asiri. Sir mai zanyi yanzu? A wane guri zan fara aikin nawa?”

Murmushi yayi tare da zare hular zannarsa dake kanshi ya shafi sumar tare da kallonta yana kuma kashe ido yace.

“CEO d'in mu yana da buk'atar sakatariya, munata bincikawa har yau bamu samu ba amman ina son na baki kona rikon kwarya ne domin sai magana yake yi akan asamo masa ni kuma har yau banga wadda zan iya dorawa akan matsayin ba sai ke.”

Aliya bata san lokacin da ta dora hannu a kirji tana zaro ido ba, Yazeed yayi murmushi yasan mamaki abin ya bata amman wannan ba abin mamaki bane duba da yadda suke neman wadda zata zama sakatariya ko aiyukan Shamsuddeen zasu ragu.

Wayar dake kan teburin Yazeed wato landline itace ta fara ringing, yasa hannu ya d'auka tare da karawa a kunne. Lumshe idanunsa yayi tare da bud'e su ya daura akan fuskar Aliya yana cewa da na cikin wayar.

“Haba Dude kwantar da hankalinka, wallahi na samo maka sakariya mai nutsuwa ma kuwa.., okay tom karkaji komai bari nazo muyi sallama.”

Tashi tsaye yayi yana cewa Aliya ta biyo shi. Ta mike tare da gyara mayafinta suka jera kamar wasu masoya suka fito, lifta suka shiga Aliya kirjinta na bugawa ita sam ba taji wani alamun tafiya fa bare taji karar na'ura sai kawai ganinta tayi a cikin wani rantsattsan guri gabaki daya transference glass ne a gurin kana iya hango waje, Yazeed ya nufi wani guri da ita inda ta tarar da teburi da kujeru na baki guda biyu da tata daga can gefe sai na'urar sanyaya ruwa da lemuka ga Despenser da locar mai dauke da tarin littattafai, gurin a tsare yake babu wani tarkace ko shirgi a ciki, glass ne ya raba gurin da office d'in Shamsuddeen sai dai akwai labulaye da aka sanya wanda ya rufe tsakanin gurin.

“Toh hajiya Raliya nan shine gurin zamanki, bari dai naje muyi sallama da ogan saboda zaije unguwa.”

“Okay bye.”

Fita Yazeed yayi ita kuma Aliya ta soma kallon tsarin gurin, yayi mata matuk'a sai dai tana ganin kamar bata kai matsayin yin aikin ba, wai sakatariya abun sai kace tana mafarki. Zuwa tayi ta zauna a kujerar da take matsayin sakatariya sai taji abin wani iri, ta kalli landline d'in kan tebur d'in tare da d'agawa ta kara a kunne. Murmushi tayi da alama gwadawa take yi idan oga ya kirata ga yadda zata yi, burinta da fatanta Allah yasa CEO d'in mai tsananin mutunci ne, tana fatan Allah yasa babba ne sabida zaifi ganin k'ok'arin ta a wajan aiki, idan yaro ne saurayi tasan zai yi girman kai.

Tana ajiye wayar kuwa aka kira, bin wayar tayi da kallo ta kamar karta d'auka, sai kuma tasa hannu ta d'auka tare da karawa a kunne, ji tayi ance.

“Yau babu wanda zan gani kisan yadda zaki yi da mutane.”

Kafin tayi magana taji an katse tayi saurin bin wayar da kallo tare da kallon labulen daya rabata da office d'in ogan. Bata gama mamakin ba yazeed ya shigo yana murmushi tare da tafa hannaye yaje ya dafa tebur d'in ta yace.

'”Ke nine ba dude ba, gwada miki nayi saboda koda zakiji hakan daga garesa sai kisan yadda zaki yi da mutane.”

Numfashi ta sauke tare da gyad'a kai alamun ta gane, daga nan Yazeed ya dinga nuna mata yadda zata dinga yin komai akan tsari, a ranar dai Aliya taga abubuwa domin har yanayin yadda CEO zai dinga kiranta sai da ya nuna mata komai practically sannan ta shirya ta koma gida cike da gajiya. Wanka tayi ta shirya cikin kaya marasa nauyi ta nufi d'akin gwaggo sai hira suke yi suna dariya gwanin ban sha'awa. Koda dare yayi suna tare da Fa'iza a parlourn Umma amman ana kiran wayarta ta tashi ta ruga dakin su, Aliya ta bita da kallon mamaki, sai da aka dan dade taga taki dawowa ita kuwa sai kallon wayarta take taga ko Sahal zai kirata amman shiru hakan yasa tabi Fa'iza d'aki dan suyi shawara.

Waya taji tana yi Fa'iza sai jujuya kafa ake fuskarta a sake tana ta murmushi taji tana cewa.

“A'ah Yaya na ni bani da wani saurayi.. Allah ka yarda dani ni ban tab'a soyayya da kowa ba,.. Kai a'a abokinka fa kace, idan ya ga banyi masa bafa yayi min wulak'anci, ni dai karka had'a mu...”

“Toh ya zaki ce ke baki da saurayi kina budurwa?okay kinga da ace na isa fara soyayya da sai nayi kinga na ciri tutar cewar dani kika fara soyayya ko?”

“Kai Yaya kaine baka isa soyayya ba yanzu? Ka manta tun kafin ka zama big man ka...'' Ta kasa karasawa saboda bata son tayi masa zancen Aliya musamman da taga har zuwa wannan lokacin bai tab'a yi mata maganarta ba”

Sam Aliya ba taji mai na cikin wayar yake cewa ba taje ta kwanta a kusa da ita duk taji Fa'iza nata b'arin zance abin ya bata mamaki, lallai wannan VIP d'in yana da muhimmanci a gurin a gurin Fa'iza. Itama wayarta ta zaro ta kira Sahal amman taki shiga ta tura masa text nan ma yake zuwa sai ta kira Husnah a lokacin kusan karfe tara da arba'in, suka gaisa sannan take tambayarta ina Sahal ta shaida mata ya koma abuja jiya da daddare, Aliya taja numfashi tare da cewa.

“Husscy wai mai yasa Yaya Sahal yake shareni ne sam baya nuna kulawarsa akaina kamar da? Kinsan yanzu ko kiransa nayi baya d'auka kuma baya biyowa idan ya gani, wani lokacin ma wallahi har text message nake tura masa amman wallahi baya min reply ina tantamar anya ba wata Yaya Sahal ya samu ba shi yasa yake min haka.”

Ba Husnah kadai ba hatta Fa'iza dake kwance suna waya da Shamsuddeen sai da gabansu ya fad'i, gabaki d'aya ya zamana suna munafuntarta domin sun san komai amman an rasa wanda zai sanar da ita gaskiyar lamarin. Jin Husnah tayi shiru shine ya kuma sanyayar da gwiwar Aliya ta katse kiran tare da juyawa tana kallon Fa'iza wacce take zaro ido da alama ta manta waya take yi sai ji tayi Aliyan tana cewa.

“Sissy idan kin gama wayar bani aron wayar ki please.”

Tana gama fad'ar haka ta mike tsaye ta fita daga d'akin, ita kuma Fa'iza kasa ci gaba da wayar tayi dan haka ta nemi alfarmar Shamsuddeen da ya bari ta dawo ko kuma gobe sayi wayar. Haka kuwa aka yi domin shima yana da aikin da zai yi kawai ba zai iya yi mata rashin mutunci ba kuma baya manta irin kin goyan bayan su gwaggo da tayi gashi yana ji har a ransa bazai iya yi mata abinda zataji babu dadi ba saboda tayi masa HALACCI a lokacin baya da suna jakara.

Saurin cire numbern Sahal tayi daga blacklist ta kuma goge numbers d'in da duk yake kiranta dasu tare da text messages d'in da ta dinga b'oyewa saboda tana son ya zame mata garkuwa nan gaba koda matsala zata taso, toh yanzu abinda yasa ta goge bata son Aliya ta gano cewar akwai alak'a tsakanin ta da Sahal. Tashi tayi taje d'akin gwaggon ta mik'awa Aliya wayar ta fito gabanta banda bugawa babu abinda yake yi, haka taje ta fad'a kan gado tare da kudundunewa cikin bargo tana sauke numfashi da kyar.

Ita kuwa Aliya tana karb'ar wayar tasa lambar Sahal a cikin wayar Fa'iza sannan ta kira, kamar almara bugu d'aya ya d'auka yana shirin yin magana yaji muryar Aliya tana cewa.

“Finally wayarka daman lafiyar ta kalau kawai nice baka son na kiraka ko?, Yaya Sahal mai yasa yanzu kake min haka? Kodai wata ka samu shi yasa ni kuma zaka juya min baya?”

Idanunsa a rufe yaja wani gauran numfashi tare da lasar lips d'insa daya bushe saboda tsabar rashin cin abinci, kamar tana gabansa ya karaikaraye murya tare da cewa.

“Sorry liya zamu yi waya bani da lafiya ne yanzu, amman idan naji sauki san kiraki.”

Yana kaiwa nan ya katse ya jefar da wayar yana dafe goshinsa saboda wani irin sarawa da yake yi. Aliya tabi wayar da kallo lokacin da taji ya katse, bata san lokacin da hawaye suka biyo ta kuncinta ba, gwaggo bata luraba domin har ta fara gyangyad'i.

Tashi tayi duk jikinta a sanyaye ta fito tare da rufe mata k'ofar ta nufi d'akin su, tana zuwa ta fashe da kuka Fa'iza ta kuma rintsa ido tana sake kudundunewa a cikin bargo duk a tunanin ta Sahal ya furta mata kalmar ki hakan yasa taki bari ta gane cewa bata yi bacci ba. Cikin sa'a itama Aliya bata tashe ta ba taje kawai ta bud'e wardrobe d'inta tana hawaye ta zaro kayan da zata saka gobe saboda Yazeed ya sanar da ita cewa dole ya dinga zamtowa ta riga CEO d'in zuwa, saboda tayi arranging d'in duk wani abu da zai yi amfani dashi a office.

Tunda take tare da Sahal bata tab'a zaton zai iya yi mata haka ba koda kuwa a ce yana cikin tsananin yanayi koda a ce yana tsakanin rayuwa da mutuwa ne, amman wai ita yake cewa bashi da lafiya ta bari sai ya warke sannan suyi magana why? Kenan ko kalmar sannu baya buk'ata daga gurinta? 'Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un me yasa Sahal zai dinga yi mata haka bayan yasan ta rayu da so da kaunarsa gashi har yanzu tana son shi bata ganin kowa da aski sai shi, bata ganin wanda ya fishi indai a b'angaran wanda take so ne amman yake wulak'anta ta, kodai gaskiyar Fa'iza ne yana da wadda zai aura ba ita ba? Idan haka ne me yasa tunda suke tare bai tab'a gaya mata ba, sannan Husnah ma bata tab'a sanar da ita cewar Yaya Sahal yana da budurwa ba.

Haka ta dinga shirya duk abinda zata tafi dashi tana yi tana zubar da hawaye har kusan karfe sha biyu babu alamun bacci a idanunta. Da kyar ta samu ta rintsa cike da mafarki marar dad'i ita dasu Husnah, ta tashi tayi addu'a sannan ta mik'e ta fita zuwa alwala lokacin ne kuma taga Fa'iza ta fito daga band'akin bata nuna mata komai ba haka itama bata nuna mata taji komai ba suka yi alwala kowa yaje yayi sallah, bayan sun idar ne Aliya ta fara shirin tafiya gurin siwes d'in ta daman ita Fa'iza hutu suke sun gama exam. Tsab ta shirya cikin doguwar riga blue tasha stone a gaban sannan tayi mata masifar kyau da alama kyawun bawai na rigar kawai bane harda na halittar wadda tasa rigar domin ba ta da maraba da balarabiya sak.

Tana rataya jaka hannunta rik'e da tea cup d'in da Fa'iza ta bada ta bata tana d'an sha tace mata.

“Sissy idan Yaya Sahal ya kira kice masa ya kira wayata saboda bana gida.”

“Ahh kinji ki, yace zai bugo miki ne?”

“Eh yace idan yaji relief zai kira so ban sani ba ko daga jiyan zuwa yau ya samu sauki nasan zai kirani.”

“Toh tunda zai kira ba sai ki tafi da wayar ba, ni daman yau ba wani amfani zanyi da ita ba, ki d'auka kawai Sissy.”

Murmushi Aliya tayi tare da ajiye cup d'in ta gyara rolling d'in kanta tare da cewa.

“No bazan tafi da wayar ki ba, bayan ina turo miki duk wani rahoto da yake faruwa a cikin office d'ina.”

Dariya suka yi sannan Aliya ta fito yayin da Fa'iza ta biyo bayan ta, sai da taje ta gaida kowa da kowa sannan Fa'iza tayi mata rakiya har k'ofar gida sannan ta koma ita kuma taje ta tari napep ta wuce. Yau kam ta tarar da mutane sunje da yawa kuma da wuri har ta fara tunanin ko wani taron za'a yi, tana shiga reception shi kuma Shamsuddeen yana sakkowa daga cikin napep, yana gama biya ya shigo harabar gurin kowa ya fara k'ok'arin karb'ar brief case d'in sa dan a taimaka masa amman ya hana, cikin sauri sauri ya shiga ciki. Aliya kuwa sai da taje ta gaida wani masinja haka kurum taji ya kwanta mata saboda tsoho ne amman akwai kaskantar da kai kowa gaidashi yake yi har kasa duk kankantarka, tana fitowa daga wajan masinjan ta bud'e lifta ta shiga, kafin ta fara tafiya Shamsuddeen yasa hannu ta bude shima ya shiga ba tare da ya kalli wacce take ciki ba bare yasan ko wacece.

Itama b'angaran Aliya bata san ko waye ba hasalima kamshin turaransa ne ya nemi ya hargitsa mata kwakwalwarta hakan yasa ta kasa d'agowa ta kalleshi, sai gabanta nema da yake tsananta bugawa dan harga Allah ita bata son irin wannan liftar kar taje a ashaketa a ciki ko ayi mata kwace ko dai wani abun marar dad'i. Gani tayi ya danna numbern office d'in da zata hakan yasa ta saci kallansa sai dai bata ga fuskarsa ba dan lokacin ya kara waya a kunnansa, kwantaccen gashin gefen fuskarsa kawai ta gani sai jin wata husky voice a kunnanta taji yana cewa.

“Kai ka sani ni dai ba zan d'auki yarinyar da zata b'ata min aiki ba, shi yasa tun tuni na sanar dakai cewar ka samo min mai jini a jiki mai kazar-kazar ba wadda zata zo ta langabe ba kullum ciwo ko zuwa gidan biki.”

Dai-dai lokacin suka zo inda zasu sauka, ba tare da ya kalleta ba hasalima wayar yake shirin sanyawa cikin aljihun wandonsa kawai taji yace mata.

“Ke! Idan kinga manya a cikin ma'aikatar nan indai kinsan ya girmeki ki dinga gaida su kinaji na?”

Aliya ta d'aga kai kamar yana kallonta, jin tayi shiru shine yasa Shamsuddeen tafiya ba tare da ya kuma yi mata magana ba. Cikin offishin taga ya shiga itama tayi saurin shiga tare da wucewa inda zata dinga aikinta. Tana zama taji kiran waya a landline tayi saurin d'agawa sai ji tayi yace.....

___
_As-Salam Alaikoum wa Rahmatul Allah sisters😻.. Nagode da kulawar ku agare ni💕I’m feeling much beta😌_The calls, messages, prayers...means a whole lot much🔥#Deeply appreciates 💋❤_
MX🧕🏼

*_KAI MIN HALACCI...💕*_
_(LEGACY OF UNREQUITED LOVE)_

_WRITTEN BY THE ELOQUENT_ _WRITER; *MISS XOXO🧕🏼_*

_ZAFAFA BIYAR NA *KUDI NE, * YAR UWA IDAN KINA SO *KI BIYA KI KARANTA*, KADA KI SHIGA *HAKKIN WANDA YA SAYA*, DOMIN ADDUAR WANDA AKA *ZALUNTA BATADA HIJABI DA ALLAH_*

_Nemi wa’ennan nambobi domin siyan naki_
👇🏾
_+234 803 081 1300_
_+234 706 712 4863_

*_I’d rather trust and regret than doubt and regret..🤞🏽*_

_*PAGE 43_*

*
Jikin Fa'iza Aliya ta fad'a taci gaba dayin kukanta kamar wadda aka aikowa da mutuwa, ita kanta Fa'iza jikinta rawa yake zuciyarta kamar zata fashe dan fargaba, tana son ta sanar da ita ragowar abubuwan da bai sanar da ita ba amman ta rasa ta ina zata fara dan duk taji maganganunsu lokacin da tazo fitowa dan ta yi masa magana cewar yasan yadda zai sanar da Liya gaskiyar lamarin, sannan karya sake ya jefasu cikin matsala amman bataji ya sanar da ita wadda yake so d'in ba. Murya na rawa jiki a sanyaye tana bubbuga bayan Aliyan tace.

“Sissy me yake faruwa ne?”

Aliya taja majina tana goge hawayen dake y’ar tsere daga idanun ta cikin numfasawa tace,

“Sissy! Ya sahal, gaskiar ki. Ashe...Ashe...Ashe yaudarata yake yi, Wai bai tab’a min soyayya irin wadda saurayi kewa budurwar sa ba, Wai wallahi soyayya yake min irin ta yaya da ‘kanwar sa wadda suka fito ciki d’aya, Wai ya ‘dauke ni tamkar Husnah, Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Sissy ki tashe ni daga wannan mummunan mafarkin please, Dan Allah ki gayamin kice wasa ne ba faruwa yai dagaske ba, ba kiji zuciata ba, Da..Dama kingaya min lokacin da muna boarding a sumaila kika ce yaudarata yake yi, kenan dama can kinsani kenan?”

Fa’izah tai tsuru tsuru tana tunanin yadda zata gayawa Liya komai, Tasan idan har ta sanar da ita gaskiar lamari to ba makawa a yau ba sai gobe ba, zumuncin su da Aliya zai tarwatse! Dan haka taja wani gwauron numfashi kafin ta dubi Aliya tace da ita,

“Sissy! Tabbas Ya Sahal yana ‘kaunar ki, kuma nima na ‘dauka soyayya ku ke yi lokacin da muna jakara, Toh sai daga baya da kikace min bai tab’a furta miki kalmar soyayya ba sai nayi wani nazari naga tabbas da soyayya kuke yi maganar aure ma zata shigo ciki saboda kun ‘dau shekaru kuna tare, Kuma dai kawai alamun sa na ‘yan yaudara ne, irin wa’innan mazan y’ayan manya ‘kwarya tabi ‘kwarya suke yi, koda kunyi aure dangin sa ba darajtaki zasuyi ba...”

Aliya ta sake jan majina akaro na ba adadi, kafin cikin daskarewar murya tace da Fa’izah,

“Hakane kuma Sissy! Amma meyasa zai dinga tarairayata kamar irin saurayi na ne shi? Lalle soyayya batai min HALACCI ba, Amma bakomai.”

“Kiyi hak’uri Sissy! Kede muyita adduar Allah ya bamu mazaje nagari kawai, dama haka rayuwar take, abunda kake muradin ka samu ba lalle ya zama alkhairi agare kaba, Allah dai ya zab’a mana mafificin alkhairi kawai.”

“Ameeen!”

Aliya tafad’a tana goge hawayen dake kwarara daga fuskar ta, Lokaci d’aya ta zabge, Manyan idanuwan ta TubarkAllah sun ‘kara fitowa luhu luhu saboda kukan da tayi, abun ka fa farar mace alkyabbar mata tuni fuskar ta tayi ja sosai, zazzabi ya rufe ta, Hankalin Fa’izah ya sake tashi jin yadda jikin Aliya yayi zafi rau kamar gaushin wuta, paracetamol ta ‘dakko mata tabata tasha, har bacci ya ‘dauke ta, cikin baccin ma sai faman ajiyar zuciya take yi, lokaci zuwa lokaci hawaye kan wanke kyakkyawar fuskar ta, da alama cikin baccin ma tunanin abun take yi.

*WASHE-GARI*

Dake Asabar ce kowannen su yana gidah, Aliya na ‘daki sakamakon zazzafan zazzabin daya rufe ta, Amma ba laipi tasha magani ciwon ya ‘dan ragu, cikin haka Husnah tazo tasame su, Fa’izah na kitchen tana taya Ummah girkin rana, suka gaysa da Husnah tarakata wajen Aliya, sun ‘dan taba hirar school sannan tabasu waje ta koma kitchen ‘karasa taya Umman su aiki. Husnah ta zauna a gefen Aliya bayan sun gaisa tamata ya jiki? Gaba d’aya sai taga Aliyan tamkar an canza mata halitta tausayin ta ya sake mamaye mata zucia, gaba d’aya itada Ya Sahal ‘din kowanne ciwon son maso wani ke damun su, abun dai sai fatan Allah ya zab’i abunda yafi alkhairi, Husnah tayi lak’was tana harhad’a maganganun da zata fad’awa Aliya, cikin tausasa harshen ta tace da Aliyan,

“Liyaa, Kafin nace komai inaso na baki hak’uri akan duk abubuwan dana aikata, Saboda ni ce ummul aba’isin din duk shigar ku wannan yanayi keda Ya Sahal, Saboda ta sanadiyyata kikasan Yaya, kuma ta sanadiyyata yaya yasan ki, kuma ni ce na fara sanar dake Ya Sahal na sonki, A hasashe na ko ince anawa shirmen na ‘dauka Ya Sahal soyayya yake dake, Saboda yanayin yadda kuka shaku, sai dai kash banyi tunanin yadda yake miki ba shin hakan SO KO SHAKUWA? (Littafi na) ne ko kuwa, Na dauka So yake miki, Soyayya irin wadda masoyi yakeyi da masoyiyar sa, daganan kika ‘dau magana ta, kika fara kallon Yaya

Please Login or Register in order to submit comment