Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*SAKATARIYA TA*
......(My Secretary).......

__
*©Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Ban yarda wani ko wata su yaɗa min wannan labari ta ko wani siga ba, ban yarda a karantashi a youtube channels ba, ban yarda a kwafa ko a juya wannan labari ba. Wannan labari Hakkin Mallakan Azizat Hamza ce*


*Free page*


0️⃣0️⃣1️⃣



Idon sa ya rintse, lokaci guda kuma ya daka tsawa "get the hell out of here!" Gigicewa yarinyar ta yi, jikin ta na rawa.
Sai da ya sake ma ta magana cikin tsawa " out of my office!" Sannan ta fita daga office ɗin a bircike, yai tsaki tareda jawo wayar landline ya danna kira, cikin muryar shi mai ɗauke da amo ya ce " Anas, i need another secretary"
Bai saurari mai zai ce ba ya ajiye phone ɗin. Ya ja tsaki sannan ya fara latsa laptop da ke gaban shi...



"Ene what happened?" Matashin saurayin ya tambayi yarinyar da ke harhaɗa files ta na yi ta na share ƙwalla.
Ta ɗago jajayen idanun ta ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba sannan ta cigaba da abinda ta ke yi.

A hankali ya ce " please stop crying, i'll talk to him" ya wuce cikin katafaren ofishin da ya fi kowanne girma acikin kamfanin.


Har yanzu aiki ya ke yi, shi ya sa ko da ya ji alamar buɗe ƙofa bai ma ɗago ya ga waye ba. Ya san sarai mutum ɗaya ne zai iya shiga ma sa office karangatsau haka.

" what exactly is your problem, wai kai for once ba za ka iya haƙuri da juriya da zama da mutane ba. Yanzu mi ta ma ka dan Allah?"

Ya fi minti biyu bai ce komai ba kuma bai ɗago ba.

"Najeeb magana fa na ke yi"

Sai a lokacin ya ɗago kykykyawar fiskar shi ya ce " Oh na ɗauka ƙara ka kawo ai"

Ya ja kujera ya zauna sannan ya kalli Najeeb ya ce " wannan kuma mi ye matsalarta?"

Kamar abin da Najeeb ɗin ke jira kenan ya fara kwarwa " the girl is so dumb, imagine jiya na ba ta report ba ta yi ba, wai ta manta. Yau kuma na ba ta wani, ta je ta yi min shirme....."


" ya isa haka ba sai ka kai ƙarshe ba, na san ƙarshen labarin. Yanzu ya ka ke so ayi?"

"Change her, May be wannan karon ka kawo namiji"

" kamar da gaske, Secretary biyu kafin wannan ba maza ba ne, su ma ba korar su ka yi ba"


Najeeb ya ɗan haɗa rai yace " look dude, ka san yanda na ke son aiki na, you either work perfectly or you leave. Ba na son shirme"

"Na ji za a nemo wani, but gaskiya Najeeb this time around ka yi haƙuri da koma wanene"

"Yallaɓai Anas na ji na amince. Sai me kuma?"

Anas yai dariya ya ce " duk yadda ka ce Engineer"




...............................................



Waya ce ɗare a kunnen ta lokacin da ta tsaida mai keken. Sai da ta zauna sannan ta ce Muda-Lawal ta ci gaba da waya wanda duk rabi masifa ta ke yi.
Ta na ajiye wayar ta kalli ƙeyar mai keken ta ce " nawa ne?"

"Ɗari da hamsin" ya faɗi hankalin sa na tuƙin da ya ke.


" hala ka fara fashi da makami ko?"

Mai keke ya tunzura ya ce" ban gane maganar ki ba"

"Idan na baka tamanin ka sa makami ka ƙwaci sauran kuɗin"

" gaskiya 'yan mata idan ba za ki ba da ɗari da ishirin ba ki sauka" ya na magana ya na rage gudun keken.

" sai ka zo ka fitar da ni ai"

Mai keke ya ja keken sa ya tsaya "sauka dan ba zanje a naira tamanin ba"

" duniya da 'ya'yan ta. Idan na sauka a keken nan na zama turmi" ta daka ma sa tsawa "za ka ja keken ka mu tafi ko dai!"

Mutumin da ke gefen ta ya ce " mai keke mu je zan biya kuɗin"

Sai a lokacin ta kalli mutumin. Saurayi ne dan a ƙalla ba zai wuce shekara ishirin da tara zuwa talatin ba. Ta ce "yawwa shishshigi. An gaya ma ka ban da ɗari da hamsin ɗin biyan sa ne?"

"Allah ya ba ki haƙuri" ya faɗi ya na kauda kai gefe saboda yadda ta tsare shi da manyan idanun ta.
"Ba zan gaya ma ka sunana ba hakanan ba zan ba ka numbata ba dan na san dalilin shishshigin kenan"

Murmushi yai ba tareda ya kalleta ba. Mai keke ya cigaba da tafiya, a hankali mutumin ke satan kallon ta sai dai ita hankalin ta ya karkata ne kan wayan ta. Chan ta lura ya zuba ma ta ido. Ta ɗago idon ta da sauri ta ce "Malam kallon yai yawa, idan idon ka bai faɗo ba zan ƙwaƙwaleshi da kai na"
Mai keke ya fashe da dariya a zuciyar shi ya na mamakin masifar budurwan nan.
Har aka iso inda za ta sauka ba wanda ya tanka ma ta. Ta na sauka ta fito da naira ɗari biyu ta miƙawa mai keke ta ce ban ɗari da Ishirin. Mai keke ya ce "Oga ya biya mi ki duka kuɗin"
" chan ta matse mu ku " ta faɗi tareda maida kuɗin ta cikin purse.

Ta ƙarasa wajen park ɗin ta na tafiya ta na waya. Yayinda hayaniyar masu mota ke tashi a tashar.

"Dan Allah baiwar Allah ki saurare ni" ta ji an faɗi a bayan ta, ta juyo a tsanake.

"Sai aka yi ya?"

Yadda ta yi maganar da faɗa-faɗa ya sa ta ƙara burgeshi. Yai Murmushi ya ce "suna na Rayyan, kar ki min fassara amma idan ba za ki damu ba ko zan iya sanin sunan ki? Please" yai maganar yana haɗa hannun sa alamar roƙo.
"Ai da ma na san dalilin biya min kuɗin kenan. To ba zan faɗi sunan....."
Chak ta tsaya lokacin da aka ƙwala sunan ta
*'Aisha mai gwanjo'*

ta juya ba ta ga mai kiran ba, ta yi tsaki.
Wani saurayi ne ya ƙaraso akan machine ɗin sa ya na murmushi
" Allah ya ja zamanin ki 'yar kasuwa"
Sai a lokacin ta gane shi.
"Sabi'u Inuwa Manzo" ta faɗi ta na maida hankalin ta gareshi.
"Aka ce kina Yola, ya na ganki a Bauchi"

"Wallahi na je gida biki ne yanzu ma na ke son komawa Yolan. Kai fa ina aka turaka?"

"Sun turani Ilorin amma na relocating na dawo Bauchi, kin san mutum mai iyali sai a hankali"

'Yola...Yola..Yola mutum ɗaya' ake kira ta yi saurin sallama da Sabi'u Inuwa Manzo ta wuce wajen motar.
Har Sabi'u zai wuce Rayyan ya tambayeshi sunan Aisha da numbarta. Sai da Sabi'u ya sha dariya kafin ya bashi numbar bayan da Rayyan ɗin yai ma sa bayanin masifar da ya sha shi da mai keke. Sabi'u ya ce ai indai Aisha Farida Salihu ne to kaɗan ka gani.


................................

Tana shiga makarantar aka ce principal na neman ta ta sani saboda tafiyar da tayi ne dan haka hankali kwance ta wuce office ɗin sa. Da mamakin ta sai taga ashe neman saboda wasu 'yan mata 'yan aji shida da ta daka ne kafin ta tafi.

Ba ta bashi haƙuri ba balle ta nuna ta yi nadamar abinda ta yi sai da ta bari ya gama masifar shi ta ce " Mr principal dududu saura sati uku na bar makarantar nan. Yara kuma na dake su ne saboda raini da izgilanci da su ke min, ko gobe su ka sake zan dake su dan ni ba sa'ar su ba ce"

"Idan ba dan Yasir ba ai da tuni mun rabu da ke. Aisha tunda ki ka fara bautar ƙasa a makarantar nan koyaushe ana complain ɗin ki"

"Zan iya tafiya?"

Principal ya girgiza kai "kai kai kai, wannan mijin ki ya shiga uku wallahi"


Lokacin da aka tashi break ta haɗu da Yasir a staff room.

"Tawan ya ki ke, gida ya ƙarɓe ki fa sai wani ƙyalli ki ke"

"To miya fi raina"

Kujera ya ja zuwa kusa da ita kamar kullum ya na ƙoƙarin shawo kan ta. Sai dai kamar kullum ɗin zancen ta ɗaya ne.

"Mun kusa gama bautar ƙasan nan fa Farida ki taimakeni ki amince da ni" ya faɗa haɗe da haɗa hannunwan sa biyu alamar magiya.

"Yasir kenan, soyayyar talaka da maikuɗi a Nigeria its a nonono option for me. Wahala kawai zan sha ni kuma ban shirya ba. Balle kai da ka ke ɗan bare-barin nan ina zaman zama na iyayenka su turomin Yasin mai walƙiya na bi duniya"

Yasir ya sa dariya sai da ya yi mai isar sa ya ce "wallahi shiyasa na ke ƙara son ki, ba kya rabuwa da abin dariya. Yanzu miye kuma Yasin mai walƙiya"

"ka fini sani sarai"
Yasir ya cigaba da dariya.


......................

*Wacece Aisha Farida Salihu?*

Malam Salihu ɗan ƙaramar hukumar Wase ne da ke jahar Plateau. Sai dai tun yana ɗan shekara sha takwas da ya ƙare sakandare ya dawo cikin Jos da zama. Sana'ar sai da kayan gwari ya fara kuma Alhamdulillah yana samu. Su biyar ne a wajen mahaifin su wanda ya jima da rasuwa tun yana shekara bakwai a duniya, shi ne na huɗu a gidan kuma su biyu ne maza. Babban yayansu Musa shi yana Kano inda yake kasuwancin sa acan sai yayun sa mata Halimah, Asma'u da ƙanwar sa Fatima, wanda a lokacin duka sun yi aure Shekarar sa biyar a Jos yai aure.

Aminah 'yar Jos ce domin iyayen ta anan su ke da zama tun shekara da shekaru sai dai asalin su Fulanin Dukku ne da ke Jihar Gombe.
Shekarar Aminah shabiyar aka yi auren wanda a lokacin JSCE kawai ta kammala. Suna zaune da Salihu lafiya cikin so da ƙauna har wata takwas kafin mummunan ala'amari ya faru. Tana zaune ta shirya abincin rana ta tsara kwalliya tana jiran sa, saboda ko yaushe Salihu a gida ya ke cin abincin rana, taji sallamar mutane daga waje. Ta sa mayafi ta fita inda taga Alhaji Nuhu ne wanda su ke haya a gidan sa da kuma Yusufu wanda rumfar sa ke kusa da na Salihu a kasuwa. Yanayin su kaɗai ya tabbatar ma ta akwai matsala. A hankali Alhaji Nuhu ya sanar ma ta Salihu ke asibiti ya yi hatsari. Cike da tashin hankali ta bisu asibitin inda Salihu ke kwance rai a hannun Allah. Da asuba Salihu ya cika wanda sanadiyyar haka ya sa Aminah suma. Da ta farfaɗo ma dai rikicewa ta yi wanda da ƙyar Nanna wato mahaifiyar Aminan ta shawo kan ta. Sai da aka yi bakwai ɗin Salihu Nanna ta fahimci Amina ciki gareta wanda ko Aminan ba ta san da shi ba. A hankali Aminah ta dinga renon cikin ta wanda Inna mahaifiyar Salihu ta ke matuƙar farin ciki da cikin. Tsakar daren ranan Alhamis Amina ta tashi da naƙuda,aka kira wata nurse da ta ke ƙasan layin su, zuwa asuba ta haihu, ta samu ɗiya mace. Aisha Farida aka sa ma ta saboda sunan da Salihu ke cewa zai sawa 'yar sa ta fari kenan saboda sunan innar sa Aisha ya ce zai haɗa da inkiyar Faridah.

Amina ta cigaba da renon Aisha Farida a gidan su. Tana son ɗiyar ta sosai, ko kaɗan ba ta ma ta karan 'ya'yan fari irin na fulani. Shekarar Aisha Farida biyu da rabi Baba ya fara yiwa Amina maganar aure saboda a lokacin akwai manema dayawa da suke son ta. Duk ciki ba ta da zaɓi dan ita tun Salihu ba ta kuma sa soyayyar wani namiji a ranta ba. Cikin maneman ta Baba ya zaɓa ma ta Malam Haruna wanda shima mutumin Dukku ne yana ɗin ki a Terminos. Matar sa ɗaya da yara shida. Lokacin da Amina za ta tare Inna ta so a bar ma ta takwarar ta sai dai Amina ta nuna batason hakan dan a ganinta Farida ta yi ƙaranci a raba ta da uwarta. Ba laifi Haruna na ƙoƙarin nuna adalci tsakanin matansa sai dai Laraba sam ba ta da haƙuri kullum cikin tsangwaman Amina da 'yarta ta ke yi. Amina za ta lamunci komai amma idan akan Farida ce to ba za ta bari ba. Watarana Amina ta dawo daga unguwa lokacin watan ta takwas a gidan ta samu Laraba na dukan Farida tsabar wahala sai da yarinyar ta suma amma haka Laraba ta cigaba da jibgar ta. Da gudu Amina ta yi kan 'yar ta tana ihu. Daga asibiti dai Amina gidan su ta wuce ta yi yaji. A ranan Haruna ya zo biko sai dai ta nuna ma sa matuƙar za ta zauna da shi to dole ne ya raba mu su gida. Yai-yai da ita ta ƙi chanja ra'ayinta, daga baya ya yarda da hakan. Har ya kama ma ta haya ɗaki ɗaya a wani gidan haya a tudun Fera. Ana saura kwana ɗaya tak ta tare saboda har an je an jera ma ta kayanta sai ga Haruna ya zo neman ta da yamma, ta fita ta sameshi a ƙofar gida. Bai amsa gaisuwarta ba ya damƙa ma ta takardar saki ɗaya. Ba dalili ba komai. Ƙarshe dai yadda aka je aka jera kayanta haka aka dawo da su gida. Ta ƙare iddar ta ta cigaba da zaman gida. Da tanada hali ma makaranta za ta koma sai dai iyayenta ma su ƙaramin ƙarfi ne. Kuɗin makarantar Farida. Baffanta Musa ke aikowa tareda kuɗin buƙatunta duk wata, ya so ya ɗauketa sai dai Amina ta ƙi musamman da ya maida Inna zuwa gidan sa a Kano.
Ganin zaman gidan shiru ya sa ta fara yin su kunun zaƙi da zoɓo tana siyarwa. Shekararta ɗaya tana zawarci Ibrahim ya fito neman ta shima dai yanada mata, ba ta bashi dama ba sai dai ganin Haruna ya dawo yana son maida auren su ya sa ta yi saurin amincewa da Ibrahim. Haruna yai nadamar sakin ta acewar sa bai san ya akayi ya saketa ba.

A Saminaka Ibrahim ya ke da zama da shi da matarsa da yaran su uku. Watannin farko an tafi lafiya-lafiya sai daga baya Matar sa Kubura ta fara nuna halin muguntar ta, ƙarshe sai raba mu su gida Ibrahim yai Lokacin Amina na laulayin ciki. Sai da su ka raba zama Amina ta samu sakewa ita da 'yar ta. Da cikin ya cika wata tara Amina ta haifi ɗa namiji. Hakan ya farantawa Ibrahim rai saboda yaran Kubura duka mata ne. Wannan haihuwar ya jawo Kubura ta sake jin tsanar Amina. Da daɗi dai ba daɗi su na zaune har Faruƙ ya shekara biyu. Kasancewa abubuwa sun fara ja baya wa Ibrahim ya sa su ka bar gidan haya su ka koma gidan sa. Zama tareda Kubura dai sai ma abin da ya ƙaru.

Watarana Farida da Safiya 'yar Kubura su ka yi faɗa. Kubura na kitchen ta ji kukan Safiya aikuwa ta fito da gudu, ba tareda bin bahasi ba ta kama jibgar Farida daga ƙarshe ta kaita kitchen ta sa wuƙa a cikin wuta sai da ta yi jaa sannan ta cire ta manna a bayan Farida. Farida ta calla ihu wanda Amina da akewa kitso a makwabta sai da ta ji kukan 'yarta. Da gudu ta sa hijab ta taho gida inda ta samu har lokacin Kubura ba ta cire wuƙan da ya ke kwance a bayan Farida ba har wajen yai rami, tsabar wuya tuni Faridan ta suma. Amina ta yi kan Kubura ta kama ta da faɗa wanda a sanadiyyar kokawa da sukayi Amina ta rasa cikin ta. Wannan ya sa Amina ta nemi saki a wajen Ibrahim. Duk wani magiya da roƙo ya yi amma ta ƙi yarda ƙarshe cewa ta yi idan bai saketa ba da shi da matar sa za ta shigar da su ƙara a kotu na zubewar cikin ta da kuma ƙunar da Kubura ta yiwa Farida. Dole haka Ibrahim ya saketa ba tareda ya so ba. Ba ta bar ma sa Umar Faruƙ ba ta ce idan ya cika shekara uku za ta bawa ƙanwar sa Sadiya da ba ta jima da aure ba. Hakan kuwa aka yi dan Amina da kanta ta kai Faruƙ wajen Sadiya da ke aure a Kaduna. Ta ce ma ta madamar Ibrahim yana tareda Kubura bata yarda ta mayar da Faruƙ Saminaka ba.

Aikin cleaner Amina ta fara a wata private school da ke anguwar su. Inda anan ta saka Farida. Dalilin Farida ta haɗa Amina da Alhaji Kabir mai makarantar. Wata rana ta yiwa wata 'yar ajin su duka iyayen yarinyar su ka kawo complain makaranta. Da komai ya lafa Alhaji KB ya kira Amina ya fara ma ta faɗa akan rashin ƙwaɓar Farida da ta ke wanda hakan ya jawo Farida ta zama ba ta jin magana. Amina ta sa kuka tareda cewa tunda kallon da ake yiwa 'yarta kenan za ta cire Farida a makarantar. Alhaji KB da ya ke da tausayi ya fara bata haƙuri. Daga ranan su ka fara mutunci, watarana da ya ji tarihin rayuwarta ya ce ma ta mi zai hana ta koma makaranta. Ta ce za ta so hakan amma yanzu kam ba hali sai dai gaba. Alhaji KB ya ce ma ta idan ta samu mai taimaka ma ta zata koma? Amsar da ta bashi ya sa zuwa sati biyu ya samo ma ta form ɗin SS1 a wani makarantar gomnati. Da farko ta ƙi sai dai daga baya data yi shawara ta amince. Ta dena aikin cleaning ta koma makaranta. Bayan shekara biyu lokacin tana SS2 Alhaji KB ya bayyana manufar sa. Da farko ta ƙi shi daga baya ta amince amma da sharaɗin ba za ta zauna da matarsa ba. Sai a lokacin ya tabbatar ma ta shekara huɗu da rasuwar matar sa kuma basu taɓa haihuwa da Ita ba har ta rasu.

Auren Alhaji KB Amina ta samu kwanciyar hankalin aure wanda rabonta da shi tun aurenta da Salihu. Bayan da result na Waec ɗin ta ya fito Alhaji KB ya nema ma ta admission a UJ ba ta samu ba dan haka kawai ya nema ma ta ADR CLIS (AD Rufa'i College for Legal and Islamic studies) da ke Misau inda ta fara karantar Law. Da ta gama diploma lokacin ɗan su ɗaya Hamza, ta fara koyarwa a makarantar sa kafin ta cigaba da karatu. Sai dai samun wani cikin ya sa ta ajiye batun karatu a gefe tukunna. Ta cigaba da renon cikin ta.
Zaman Amina da Alhaji KB zamane na amana yana son Farida tamkar shi ya haifeta har lokacin da ta haifi Hamza bai taɓa nuna wa Farida banbanci ba. Alhaji KB ɗan asalin Jahar zamfara ne yanada 'yan uba amma a wajen mahaifiyar sa su biyu ne shi da ƙanwar sa Hannatu. Mahaifiyarsa ta rasu tun yana shekara shida. Uƙuba na matan uba ya sa ya koma wajen ƙanwar Mamansa da ke aure a Jos lokacin yana shekara sha ɗaya. Anan yai karatu ya zauna har ya kai matsayin da ya ke yanzu. Hannatu ta jima da rasuwa. Ta rasu jim kaɗan da barinsa Zamfara. Raliya ɗiyar Hajiya Aina'u mariƙiyar sa ya aura. Sai dai har Allah ya ma ta rasuwa ba su taɓa haihuwa ba. Haka nan bai ƙara aureba sai akan Amina. Sau biyu tak ya kai Amina Zamfara inda anan ta gane 'yan uwan Alhaji KB ba sa ƙaunar ta, shi ɗin ma abin hannunsa ya sa su ke ɗan girmamashi.

Abdul na da shekara biyu Alhaji KB ya rasu. Mutuwar da ta gigita Amina da Hajiya Aina'u. Lafiya-lafiya ya tafi Zamfara kawai sai yayan sa Ubaidu ya kira wai Kabiru ya rasu zazzaɓi ya sashi a gaba da dare kafin safiya ya cika.
Amina ba ta shiga tashin hankali ba sai da kwana ishirin kacal da rasuwan Alhaji KB 'yan uwan sa su ka zo su ka koreta a gidan sa. Ƙarshe a gidan su ta ƙare takaba. Kafin wata uku da rasuwar sa su ka saida makarantar sa da gidan sa da mafi yawancin kadarorin sa. Hajiya Aina'u da Amina sun yi ƙoƙarin shigar da ƙara Kotu sai dai tun farko da su ka yi yunkurin hakan aka rufe bakin su. Haka nan Amina wadda 'ya'yanta ke kira da Ummi ta koma gidan jiya sai dai wannan karan tana da ilimi daidai gwargwado da kuma wayewa. Wata makarantar ta nema aiki kuma ta samu da wannan ta ke yin hidimar yaranta da shi. Tsohon mijinta Ibrahim ya nemi ta yi kome saboda yanzu ya rabu da Kubura kuma Alhamdullillah matar sa Hafsatu tanada kirki. Ummi ta ƙi tace ita da aure har abada. Ba yadda Babanta bai yi ba amma ta ƙi ta ce aure huɗu da tayi a baya sun isheta. Yaranta uku na gabanta Farida, Hamza da AbdulMalik. Shi ma Faruƙ ya kan zo hutu wajen Ummin sa lokaci zuwa lokaci har lokacin a Kaduna ya ke. Hajiya Aina'u na ƙoƙarin taimakawa Amina da ɗawainiyar yara daidai gwargwado sai dai fa har yau 'yan uwan KB ba su waiwayeta ba balle su nemi taimakawa yaran marigayi. Gado da ya bari kuma babu batunsa dan tuni sunyi wasan kura da dukiyar sa.

Aisha Farida Salihu yarinya da ta taso da ƙiriniya ga surutu. Ba dai ka faɗa ta yi shiru ba. Kwata-kwata ba ta da tsoro, tana son umminta sosai gashi ba ƙaramin shaƙuwa su ka yi ba, idan ka ga suna hira tamkar wa su ƙawaye. Sau tari ma akan ɗauka ya da ƙanwa ne su. Tunda su ka koma gidan su Ummi, Farida ta dena zaman banza ganin dai yanzu ba da bane. Ta koyi kitso da lalle tana yi, ga saida kayan ƙwalama

Please Login or Register in order to submit comment