Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗakin...


Washe gari da kunyar sa ta tashi tunowa da tai da abinda ya faru jiya. Sai dai shi kam ko ajikinsa, nuna ma ta yai wannan shine amfanin auren domin sun riga sun zama ɗaya. Duk wani matsalarta na shi ne, haka nan duk matsalarsa na ta ne.

Da dare su ka je gidan su sallama, daga nan su ka wuce gidan su Maijiddan. A wannan lokacin Farida ta tambayeta ko gudawar ta tsaya kafin ango ya shigo. Maijiddah ta ce "inaa, Anty ni kam ai na sha kunya" a taƙaice ta gaya ma ta abinda ya faru Faridan ta yi ta ma ta dariya.
Ba su jima ba su ka wuce saboda da sassafe jirgin su zai tashi.

Daren ranan ya gaya ma ta basic abubuwan da ya kamata ta sani gameda airport da jirgi. Sannan ya jaddada ma ta ba abinda zai faru yana tareda ita.
Ko breakfast ba ta iya yi ba saboda kar ta ci wani abu ya dameta. Ƙarfe tara jirginsu ya wuce Lagos. Kuma Alhamdulillah Maijiddah ba ta yi gudawa ba, sai dai ta tsorata kam lokacin da jirgin zai tashi, ba dan AbdulWahab na riƙe da hannunta yana kwantar ma ta da hankali ba ƙila da ta yi kuka. Sai da jirgi ya lula sama sannan ta ɗan samu nitsuwa kaɗan...

Asha amarci lafiya Maijiddah (banda gudawa plz😁)


.........................


Safiyar Monday Farida ta fito aiki duk da kuwa gajiya bai saketa ba, sai dai kamar yadda ta yiwa Maijiddah dariya sai gashi itama tana tsaka da aiki cikinta ya hautsina. Da farko sharewa ta yi tana mita " mutum ya yi ta ciye-ciyen mai kwana biyu ba dole ciki yai ta kuka ba"

Sai dai fa lokaci guda ta kasa yin komai ta tashi ta nufi office ɗin Najeeb da gudu dan nan ne kusa da ita sannan ta ɗauka baya office ɗin dan ya fita ɗazu ya je meeting. Abinda Farida ta manta shine ya riga ya dawo tuntuni.
Da gudu ta zo ta wuceshi yana zaune yana aiki, kafin ta ƙarasa ma ta saki tusa a hanya.
Yana shirin buɗe baki yai magana kan shigo ma sa office da ta yi da gudu ya ji ƙaran tusan da ta yi...


Hankali kwance Farida ta zauna ta zazzage kayan cikinta, dama tun ran asabat rabon da ta yi, ga shi ba ƙaramin abinci ta ci ba a bikin nan. Ta jima a ciki kafin ta wanke ta yi flushing, kasancewa banɗakin yai gum sai ta ɗau air freshner ta feffesa ta ƙara buɗe windown banɗakin da kyau saboda iska ya ratsa.

Ta fito tana ɗan daddanna ciki tana faɗin "kai abubuwan da na ci a bikin nan ai sai barka. Kashi rahama ne Allah, ka ji yadda na ji wani saƙayau lokaci guda"

Cak ta tsaya da tafiya lokacin da muryan da ba ta taɓa tunanin ji ba a wannan lokacin ya doki kunnenta

"Miss Salihu"

Kaman ta nitse cikin office ɗin haka ta ji sai dai ita Aisha Farida ce dole ta nuna dakewarta. Tukunna ma dama yana office lokacin da ta shigo? ko dai bayan ta shiga banɗakin ne ya shigo office ɗin.

"Miss Salihu whats the meaning of this?"

Da ƙarfinta ta waiwayo bayan ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya. Ita ɗin expert ce wajen waskewa, ta ce

"Daɗin abin ma kowa yana yi, abinda na yi ba farau ba ne akai na. Ni'ima ce da ubangiji ya baiwa bayinsa dan ya nuna ma na mu ɗin ba komai ba ne. Da Sarki da shugaban ƙasa da maikuɗi da talaka, malami da jahili, mai kyau da mummuna, mace ko namiji, fari ko baƙi. Dukkan mu muna da buƙatar wannan ni'ima. Abu ne ba babba ba yaro"

Ta ɗan haɗe rai ta ce " yanzu haka Sir Najeeb kai ma wannan ni'imar sai da ka yi ta kafin ka zo office yau, ko tun jiya rabon da ka yi?"

The girl is really crazy, taya za ta yi abin kunya and pretend kaman ba komai. Masifa ya ke so ya ma ta amma maganganunta sai su ka kusa sa shi dariya. Ya daure ya ce " Miss Salihu a wani dalilin ya sa ki ka yi min amfani da banɗaki?"

"Saboda ya fi kusa da ni mana"

"This should be the last time da za ki yi haka"

"Ok Sir"

Har za ta wuce sai ta juyo ta ɗan yi gyaran murya ta ce " Sir ina da magana"

Ido ya ɗaga ma ta alamar miye.

"Sir, tsakani da Allah tusar da na yi ɗazu ka ji ta?"

Kallon-kallo su ka tsaya yi. Har ga Allah tana son sani dan bayan ƙarar da tusar ta yi ba ƙaramin wari ne ya biyo bayan tusar ba.

"Get out of my offfice"...

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Last Free page*

0️⃣1️⃣5️⃣


"Mama har yanzu bai kirani ba, ina ga bai san ma na yi yaji ba fa" Aneesa ta faɗa cike da damuwa a ran ta.

"Ya ki ke so na miki? Na kira AbdulWahab na ce ka zo ka bada haƙuri matar ka ta yi yaji ko ya?"

"Mama do something please, ba zan iya sharing mijina ba"

"An riga an ɗaura auren Aneesa live with it. Ke ne za ki san yadda za ki riƙe gidan ki ta yadda yarinyar ba za ta samu kan shi ba"

Aneesa ta ɗan ɓata fuska ta ce "Mama ta ya zan yi hakan bayan bana zama a Lagos"

"Za ki ajiye aikin ki kenan?"

"Hell no. Ta ya zan bar career ɗi na when i'm at its peak. Ko kaɗan"

Mama ba ta ce komai ba, to mi za ta ce. Itama mace ce da mijinta ba ya gabanta. Ta taso da aƙidar 'yan cin kai, yau tana Dubai gobe tana China wajen saro kaya, kasuwancin ta shine a gaban ta. Auren fari ta haifi Aneesa da Nazir, da ta auri Alhaji Abdullahi ma ɗa ɗaya ta haifa ta rufe haihuwa. Kuɗi kuɗi su kawai ta sa a gaba ba ta da lokacin kula da iyalin ta balle tarbiyyan yaran ta, shi ya sa ko kishiyoyin ta ba sa gaban ta, dama kuma kowa gidan ta daban...


.....................

Farida na zaune wani saurayi ya shigo neman Najeeb.
"Wa za a ce?" Ta tambaya lokacin da ta ɗau wayar.

"Ki ce ƙanin shi"

"Sir wai ƙanin ka na neman ka"

Ajiye wayar ta yi ta ce " ya ce ka shiga"

Ba a jima da shigar wannan baƙon ba Anas ya zo shima ya shiga.

Dukkan su uku zama su ka yi ana taɗin bayan rabuwa.

"Big B tunda ka ƙi auruwa mu zamu shige gaban ka fa, dan na gaji da zama tuzuru"

"Shege yaushe ka dawo da za ka fara maganar aure. Anas see this small boy fa"

Anas dai murmushin ya ƙe yai dan ya san inda maganar za ta tsaya ba za ta ma sa daɗi ba.

Farida ta shigo ta samesu a haka, bayan Anas ba ta taɓa ganin Najeeb ya sake yana taɗi da wani ba. Sai dai kamar yadda wannan saurayin ya ce shi ƙanin sa ne ƙila su na da alaƙa tunda dai a yadda Anas ya gaya ma ta ƙanwar Najeeb ɗaya ce wato Najdah. Wata 'yar girman kan kaman yayan na ta.
Kai tsaye wajen Najeeb ta nufa a wajen kujerun da su ke zaune wanda anan ya ke saukan baƙin sa.

"Sir ga wannan ana buƙatar signature ɗin ka anan" ta faɗi lokacin da ta miƙa ma sa wasu takardu.

Ya amshi takardun ya fara dubawa.

"Kai Big B wannan hottie as a secretary ai za ta ɗauke hankalin ma su zuwa wajen ka"

Najeeb ya ɗago ido ya ma sa wani kallo wanda ya sa yai saurin chanja magana da cewa.

"Ba wanda ta kai sweety na kyau ai. Najdah is the epitome of beauty ba ƙarya"

Gyaran murya Anas yai sannan ya ce "Musty zan wuce office, sannu da zuwa"
Musty ya miƙa ma sa hannu su ka gaisa. Idon Farida na kan Anas wanda ta ga ya chanja lokacin da Musty yai maganar Najdah. Tun farko-farkon fara aikinta ta san Anas ya na son Najdah, duk da kuwa Anas ɗin bai iya buɗan baki ya faɗawa Najdan ba har yau.

"Ya Anas dan Allah ka ɗan jirani minti biyu" ta faɗa tana murmushi.

Sauke idon da za ta yi domin ƙarɓan takardun da Najeeb ya gama signing sai ta ga idon shi chul akan ta. Ba ta san ma'anan wannan kallon ba amma ta fassara shi da cewa kallo ne da ke nuni da zan gamu da ke.
Da ta amsa takardun ta ce "Allah na gani ni ban ci bashin kowa ba, kurwata kur"

Har ta fita daga office ɗin bai daina kallon ta ba.
Musty cikin fake American accent ɗin sa ya ce " Your secretary is funny and cute"

"Ba ka daina halin na ka ba ko?"

"Sorry Babban yaya"

Tana fita ta tadda Anas na tsaye yana jiran ta. Gaba ɗaya fiskar sa ta chanja bisa yadda ta san shi da, shi ba kaman Najeeb bane kullum fiskar sa a sake ta ke gashi da son barkwanci.

"Yaya na ban gane wannan ɗan adawar ba fa, shi waye?"

Murmushin ya ƙe yai ya ce "ɗan ma su gida ne. Mustafah Sulayman Jibo kenan"

Kalmar da ya faɗa ta 'ɗan ma su gida' ya sa ta tuna da audion da aka ce ta yi kwanakin baya inda ake cewa shi ɗin ɗan Maigadin gidan su Najeeb ne, kenan da gaske ne.

"Ya Anas kar ka damu mu akai za mu dangwalawa. Idan da so ai ya share komai"

"Ki na ga Najdah za ta tsallake ɗan uwanta ta zaɓe ni ko kuma Daddy ne zai watsar da zumunci ya zaɓe ni?"

"Ya Anas da wannan ma amma tun farko kai ka yi sake. Da ka gina soyayyar ka a zuciyar ta da tuni an wuce wajen"

Girgiza kai yai ya ce " Farida ba za ki gane ba"
Wucewa yai ya bar office ɗin ran sa ba daɗi...

Najeeb na zaune da Musty ne amma hankalin sa na kan tunanin mai Farida za ta faɗawa Anas. The girl is mischievous, yanzu haka wani gulma ta ke yi.

A wajen cin abinci Farida ta samu Anas shi kaɗai, bai ordering abinci ba, ruwa ne kawai a gaban sa, yana zauna amma hankalin sa yai nisa cikin tunani.

"Ya Anas yau da garau-garau na zo, za ka ci" Farida ta ajiye kular tana ƙoƙarin buɗewa.

" 'yar uwa yau ba na jin yunwa" ya faɗi ba tareda ya kalli abincin ba.

"Allah sai ka ci, nan nan na hana Yakubu abincin nan na ce a yaya na zan kaiwa amma ka gwaleni ba ka isa ba"

Ta fara zuba abincin a plate tana faɗin "Ya Anas yajin ya ji maggi fa, ga man ma sai ƙanshin albasa ya ke"

Sai da ta gama haɗawa ta tura gefen sa ta ce " dan Allah ka ci"

Ba yadda zai yi dole ya ɗau spoon ya fara ci. Ita ma ta haɗa na ta ta fara ci. So ta ke ta ma sa maganar Najdah shi ya sa ta zo.

"And what is the meaning of this?" Muryan Najeeb ya gauraye ilahirin wajen.

"Anas miye haka?, babu respect tsakanin Oga da mere secretary. Ta ya za ka bari ta zauna a inda na ke zama na ci abinci. Are you trying to disrespect me kamar yadda ta ke disrespecting ɗi na"

"Najeeb is not..."

"Shut up" Najeeb ya katse Anas da tsawa. Wannan ya ja hankalin kowa ya koma kan su.

Ta shi Anas yai zai bar wajen. Farida ta ce "Yaya dan Allah ka tsaya ka ci abincin ka, ni barin bar ma sa wajen"

"Bar shi na gode Farida" ya faɗi sannan ya bar wajen.

"Girma ya faɗi, kuma wallahi an ji kunya"

Hannu Najeeb ya kai zai ma ta mari sai kuma ya tsaya yana huci hannun na reto a sama " I'm warning you Miss Salihu, ki kama matsayin ki ko kuma na nuna mi ki"

Haɗiye miyaun da ya tokare ma ta maƙoshi ta yi lokacin da Najeeb shi ma ya juya ya bar wajen. Ta gama sadakarwa Najeeb marin ta zai yi. Har ta hango yadda fiskarta zai koma idan da marin ya sauka a fiskarta.

Ranan dai ita ɗin ma ka sa cin abincin ta yi. Mi ya ke damun Najeeb da har zai yiwa Anas haka, hakan ma agaban jama'a wanda duk a ƙasan Anas ɗin su ke...

Kai tsaye office ɗin Anas ta wuce da ga canteen. Yana zaune yana ta kan zane a takarda wanda da ka gani ka san yana zanen ne saboda huce haushi.

"Yaya na kar ka ce na cika gulma amma anya Sir Najeeb yana da lafiya kuwa. Gaskiya a binciki ƙwaƙwalwar sa"

"Lafiyar sa ƙalau Farida, kawai dai he has a rough life ne. Mahaifiyar sa then Sabreen, su suka maida shi haka"

"Sabreen?" Farida ta faɗa da alamar tambaya.

"Macen da Najeeb ya fara so ba"

"Dama duk girman kan Sir Najeeb ya taɓa soyayya? Abun mamaki"

"Kar ki damu da abinda ki ka ga ya yi ɗazu, anjima kaɗan za ki ga ya zo ba da haƙuri"

"Duk da haka Ya Anas, abinda yai bai ma ka adalci ba wallahi"

"Kar ki damu, abinda yai bai kai zuciyar sa ba"

"Wannan sirikin na ka Allah kaɗai ya san yanayin sa. Yau ka gan shi shiru anjima ya fara faɗa gobe idan ya fara banbamin bala'i har wani spark bakin sa ya ke yi"

Ai Anas bai san sanda ya fara dariya ba "kai Farida kinada abin dariya ba kaɗan ba"

"Allah Ya Anas wani lokacin kaman majnuni ya ke, ka san lokacin da aka kidnapping ɗin mu haka mu ka kwana mu ka wuni bai min magana ba daga baya kuma bini-bini sai ya ɗaukeni"

"To waya sani ko ke ce ke sa shi haukan"

"Ni Aisha Farida! Rufa min asiri kafin yanzu na ga query letter"


Ta ɗan gyara zama ta ce " yawwa, da ma maganar Najdah zan ma ka"

Ya ɗago ya kalleta

"Mi zai hana ka faɗa ma ta kana son ta, you never know, sai ka ga an dace. Balle ni ina ganin tana son ka ma"


"Baba na gadi yai a gidan su har ya rasu, karamci na Daddy ne ya sa ya sponsoring karatuna tun daga primary har masters da na yi shi ya sa na zama abinda na zama a yau. Daddy is like my father amma kuma na san indai akan maganar Mustafah ne to zai zaɓeshi ya bar ni, domin Mustafah jinin sa ne"


" tsoro shi zai sa ka rasa masoyiyar ka wallahi. Ba ka taɓa ce ma ta kana son ta ba, ba ka gayawa Najeeb ba balle kuma Daddy, to dan Allah ta ya za su san kana yi balle har a dubi wanne ya fi dacewa da ita tsakanin kai da Mustafah"

"Ki bari kawai Farida. Gara na zauna a matsayina"


"Dan Allah kar ka bani kunya ma na"...

...........


Lokacin da aka dawo daga break ta koma office ɗin ta. Ko da aka zo neman Najeeb ta kira office ɗin sa amma bai ansa ba, ta shiga office ɗin amma baya nan. Har banɗaki sai ta leƙa amma shiru. Numbar sa ta fara kira amma ba ta shiga.
Daga ƙarshe dai ranan har aka tashi ba ta ga Najeeb ba. Haka nan ba ta san inda ya je ba dan da ta fita ƙasa ta tambayi security aka ce ma ta Najeeb ya fita da mota tuntuni.
A zuciyarta ta ce "ai dole ka gudu tunda ka yi abin kunya"...

Tunda ya bar canteen kai tsaye motar sa ya je ya ɗauka ya bar kamfanin, ya na shiga gida ɗakin sa direct ya wuce ya samu gefen gado ya zauna tare da dafa goshin sa. He cant believe wai shi ne yai wa Anas tsawa. Anas fa, Anas da duk faɗin duniyan nan ba shi da aboki kamar sa. Saboda me?
Shi kan sa bai san dalili ba, ya san ba laifin Anas a zaman da Farida ta yi a wajensa. Sai dai ya rasa dalilin da ya sa maimakon ma ya ji haushin Farida sai ya kasance ya fi jin haushin Anas akan ta. Bai san ya za'a yi ya dena jin haushi ba duk lokacin da Farida ta ke tareda Anas.
Ya jima yana tunani a ran sa kafin ya tashi ya fara cire kaya dan ya watsa ruwa.

...............



Samun Anas ta yi akan dan Allah ya kaita gidan su Najeeb ta bashi wa su takardu sannan ta bashi saƙonnin wanda su ka zo ba su sameshi ba tunda wayar sa a kashe ya ke. Yana sauketa a compound ɗin su ya juya ya tafi dan shima bai shirya fuskantar Najeeb ɗin ba, ko da kaɗan ne to ya ji haushin abinda Najeeb yai.

Ranan da su ka zo gidan da dare ba ta lura da gidan ba, saboda dare da kuma hali na gajiya da rashin lafiya. Amma yanzu kam ta ga yadda gidan ya ke da girma da kyau, sai da ta gama yabon kyaun gidan a zuciyar ta kafin ta wuce ciki. Doorbell ta danna tana jira a buɗe.

Najdah da Afrah ke cin abinci a dining saboda har yanzu Mom ba ta dawo daga Bahrain ba.

"Adama.... Adama ki zo ki buɗe ƙofa"

Adama ta fito da sauri ta nufi ƙofan.

"Sannu, wa ki ke nema?" Adama ta tambayi Farida da ke tsaye a bakin ƙofa.

"Ni sakatariyar Najeeb ne, na kawo ma sa saƙo yana nan?"

" ki shigo"
Ta matsa ma ta ta shiga.

"Adama waye?"

Kafin ta bada amsa Farida ta ce "Aisha Farida ce"

Sunan ba baƙon suna ba ne a wajen su duka biyun, dan sun san labarinta a Najeeb constructions. Ranan da su ka fara zuwa wajen Najeeb farko-farkon fara aikin Farida. Hana su shiga office ɗin sa ta yi ta sa su ka jira shi a office ɗin ta har sai da ya dawo. Ranan cikin shagwaɓa Najdah ta dinga complain wa Najeeb har da cewa "Big B, your secretary was rude to us". Daga baya Najeeb ya ce wa Farida duk lokacin da ƙanwar sa ta zo yana nan ko baya nan ka da ta hana ta shiga office ɗin sa.


"Ehen, duk haɗuwar ku na office bai isa ba sai kin biyoshi gida" Afrah ta faɗa tana huhhura hanci.

"Idan aiki na ya tsone mi ki ido, kya iya zuwa ki ƙarɓa"

"Mtsww" Afrah ta ja tsaki

"Mi ki ka zo yi?" Najdah ta faɗa ita ɗin ma fiskan ba yabo ba fallasa.

"Na kawo wa Sir Najeeb wa su files ne, sannan na zo neman bayanai gameda masoyina Anas kasancewa kin fini sanin shi"

"Masoyin ki Anas?" Najdah ta maimaita

"Wanni Anas tukunna?" Afrah ta saka baki.

"Abokin yayanki ma na, ko kin san wani Anas ɗin bayan shi?"

Najdah ba ta ce komai ba sai haurawa da ta yi sama da gudu fuuuu itama Afran ta bi bayanta tana kiran ta.


Ganin su duka biyun sun bar wajen ya sa Adama ta je wajen SHS ɗin falon ta danna 6 muryarta na rawa ta ce "Ranka shi daɗe ga Sakatariyar ka ta zo neman ka"

Shiru kusan minti ɗaya ba a ce komai ba, har Adama ta fidda rai sai ga muryar sa ya na cewa " send her to my room"

"Ina ne ɗakin?" Farida ta tambaya

"Idan kin haura sama shine ɗaki na ƙarshe a ɓangaren hagu"

Ok kawai ta ce ta haura saman. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta yi lokacin da ta iso. Ta tsaya na aƙalla minti biyu kafin aka buɗe ƙofar.

Sanye ya ke da jallabiya na 'yan Morocco kalar toka.

"What do you want?" Ya faɗi fiskar sa tamau.

"Ya Allah, wai haka gidan ma su kuɗi su ke ne, daga ka zo sai a fara tambayarka mi ka zo yi. To ni ba maula na zo yi ba ziyara na kawo"

Ƙofar ya jawo zai rufe ta yi saurin sa hannu ta ce " yi haƙuri Sir Najeeb saƙo na kawo"

Ya dakata da rufe ƙofar yana kallonta. Ta fito da wani file ta miƙa ma sa sannan ta ce " Sir MD na Hafzal suites ya zo neman ka ya ce da ka ji saƙon nan ka kira shi akwai magana mai muhimmanci da za ku yi sannan dan Allah ka bawa Ya Anas haƙuri abinda ka..." baam ya rufe ƙofar sa.

" Mr Egocentric" ta faɗa kafin ta juya ta fita.

A falo ta haɗu da Daddy shi ma ya shigo gidan kenan, har ƙasa ta rusunna ta gaida shi.

"Kaman na san fiskar nan"

"Yallaɓai ai ni ce sakatariyar Sir Najeeb wanda aka sace mu kwanaki"


"Oh Aisha ko?"

"E"

"Sannu ya Baban na ki"

"Ya na lafiya"

"Ki gaida min shi ko"

"Insha Allah zai ji"

"Gida za ki je ne?"

Ta amsa da E

"To to, Adama ki fita ki ce Iliya ya kaita gida ko"

"Na gode Daddy"

Ya fito da kuɗi a Aljihu ba tareda ya irga ba ya miƙa ma ta ya ce ta sha ruwa a hanya.

"Daddy ka barshi na gode"

"Idan ki ka yi haka ba ki ɗauke ni Daddy ba kenan"

Ai tuni Farida ta karɓa tana ƙara faɗaɗa murmushinta lokacin da ta ji kaurin kuɗin zai iya kaiwa dubu goma.

Ita kam bajau ɗin ta, ta tafi gida a mota mai kyau ga AC ga dubu takwas da Daddy ya bata...


Ai ba ta gama zama ba Anas ya kira ta.

" 'yar uwa mi ki ka faɗawa Najdah ne? Ta kira ni wai muna soyayya da ke kuma na ɓoye ma ta bla bla bla..."

Sai da Farida ta yi dariya mai isar ta sannan ta ce " Yaya na kenan, idan akwai kishi to akwai so. Najdah na son ka, ka saurari plan ɗina ka ji..."


............


Su na cin breakfast a dining Najdah ta ce " Big B wai ashe Ya Anas da sakatariyar ka soyayya su ke"

Tea ɗin da Najeeb ya kai baki ya furzar da sauri.

"Anas ya gaya mi ki?"

"Jiya da sakatariyar ka ta zo ta ke gaya min. Big B, Ya Anas ya rasa wanda zai nema sai masifaffiyar yarinyar nan, that girl fa ba za ta rasa mu'amala da ƙwaya ba"

Miƙewa Najeeb yai bai ce komai ba ya bar dining ɗin.

Ranan da Anas da Farida ban san wanda ya fi shan masifar Najeeb ba. Abu kaɗan masifa, lokaci guda Najeeb ya dawo wa Farida Najeeb ɗin da ta sani farkon zuwan ta. " get out, fuct you, stupid, nonsense" waɗannan kalmomi da su na tsiro da sun tsiro a jikin Farida saboda tsabar yadda ta ji su a wajen Najeeb. Idan ta kawo takarda ya signing kuwa yana gamawa zai wurgeta da shi ba zai miƙa ma ta da hannu kamar yadda ya saba ba.

Anas ma ya ɗauka da Najeeb ya zo zai ba shi haƙuri a wuce wajen sai ya ga saɓanin haka. Yana tambayar sa abu maimakon yai magana sai ya fara ma sa tsawa...

Farida na tattara wasu takardu da Najeeb ya watsar Anas ya shigo office ɗin.

"Najeeb ka dubi wannan presentation ɗin nan na gobe. Wannan shi ne final edit da na yi"

Ko kallon laptop ɗin da Anas ya ajiye a gaban sa bai yi ba ya ce " kar ka damu kan ka, ba za ka yi presenting gobe ba"

"What"

"Ka jini da kyau"

"Najeeb are you serious? I've been planning for this pitch for a week now"

Da ƙarfi Najeeb ya daki table ɗin sa ya ce " Ni Najeeb Adam Jibo, CEO of Najeeb constructions na ce Architect Anas Ali AlMustafah ba za ka yi presentation gobe ba, ka na da ja?"

Da Anas mai saurin kuka ne da ya yi a wajen nan saboda wannan cin fuska da Najeeb ya ma sa. Sai dai ya daure ya ce " ba ni da ja, Sir Najeeb"

Wannan karo na farko da ya referring Najeeb da 'Sir' kenan, a cikin shekaru bakwai da su ka fara aiki tare.

Gwiwar Farida yai sanyi. Tausayin Anas ya mamaye zuciyar ta. Da ta na da iko da ta je ta wankawa Najeeb mari.

Wai a wani dalilin zai yiwa Anas haka, a wani dalilin?
(Ni dai da 'yan group ɗi na ma su albarka mu ka haɗa baki mu ka ce *a dalilin ki*)

*plz numbar da za a nemi yadda za'a shiga paid group ɗin sakatariya ta ita ce 08137311900, duk wani number da ba wannan ba scam ne. Kar ku manta, #200 ne kacal ko kuma ka biya #300 ka samu sakatariya ta da tsohuwar soyayya. Za ka iya biya ta wannan account ɗin 3099546325, firstbank,Azizat Hamza. Ko kuma ka turo katin waya zuwa ga wannan layin 08137311900. (Plz duk wani means of payment da ba wannan ba, babu hannun marubuciyar a ciki. Mutanen Niger za ku iya biya ta link da zan turo da yamma Insha

Please Login or Register in order to submit comment