Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"eh ni ce"

"Madam you are under arrest"

Farida ta yi murmushi ta ce "mu je ko"

Tasallah da ke chan wajen dining ta fashe da kuka tana faɗin "Alhaji ka yi wani abu dan Allah. Za su tafi da ita"
Ko gizau Najeeb bai yi ba balle ya sa baki.

Maureen na faɗin "evil woman. You'll rot in jail for this"

Haka Farida ta bi bayan su suka fita. Tasallah na ihun matar gidan ne fa, mi ta yi?.
Ganin ba wannan ba ne zai fishsheta ya sa ta nufi ɗaki ta ɗau wayarta ta kira Mom...

Ganin gidan Najeeb ya ƙara haukata Naomi. Duk ciwon da ta ke ji sai ya zamana ta watsar da shi gefe, babban burinta shi ne yadda za ta mallaki wannan gida ita kaɗai...


...........................


Tun kan su isa police station ɗin Daddy ya fara kiraye-kirayen waya. Su na zuwa ma ba wani dogon bayani kawai sake Farida aka yi. Domin Comissioner of police ne ya kira ya ce a saketa.
Abinda ya ƙara sa Daddy ya tsorata da lamarin shine jin cewa Najeeb ne ya zo ya bada report sannan ya ce a arresting Farida. Gaskiya Najeeb yana buƙatar addu'a.
Farida kam har su ka iso gida ba ta ce ƙala ba. Mom ce ma ke ta aikin ba ta haƙuri.
Daddy ya ce wa Mom gobe Tasallah ta kwasowa Farida kayanta. Daga yanzu a nan za ta dinga kwana tunda abin ya kai ga haka kar su wayi gari Najeeb ya kashe Farida.

Farida sai da ta shiga tsohon ɗakin su sannan ta fashe da kuka. Tun ɗazu ma tanajin kukan, kawai ta daure ne saboda su Mom. Wai ita ce yau Najeeb da kan shi ya ke kawo ma ta police har gida.
Najeeb ɗin da lokacin da Sabreen ta sa aka kamata haka hankalin sa ya tashi ya zo police station yana masifa kaman zararre. Ta tuna first kiss ɗin su a ranan. Shi ne yau Najeeb ke gani ana tafiya da ita amma ko ajikin sa, kai duniya!...


..........................


Washegari kamar yadda Daddy ya ce haka Tasallah ta ɗebo wa Farida wa su daga cikin kayan ta. Daddy ya ce ta fita hanyar Najeeb kar ya illata ta tun da abin ya kai ga haka.

Addu'a aka ci gaba da yiwa Najeeb dan addu'ar ce kaɗai garesu. Tasallah ba ta fasa sawa Najeeb ruwan zamzam a abinci ba kaman yadda Farida ta buƙata...

A ɓangaren Naomi duk faɗa da wani masifa da Mrs Comfort ke yi ba wanda ya shigeta. Tun da su ka shiga ɗaki ita da Maureen su ka fara shirya yadda za su kawo ƙarshen Farida saboda ma kar a samu matsala a gaba...

Bayan kwana biyu


Maureen da Naomi su ka sake duƙufa gaban Boka Ifagbemi.
Lokacin da Naomi ta gama kwararo buƙatunta Boka ya kece da mahaukaciyar dariya. Sai da yai mai isar sa sannan ya ce "a kasheta? Ko kin manta annurin matar sa ya ke gani a idon ki, ko kin manta duk ranan da Matar sa ta mutu zai dena miki kallon so?"

"To Baba ya za ayi tunda idan aka kasheta maganin zai warware?"

Boka ya fara buga ƙirji yana surkulle sannan ya ɗago ya kalli Naomi ya ce "akwai abinda za a yi amma da ɗan wahala"

Naomi ta ce ko minene za ta yi.

Boka ya miƙa ma ta wani ƙaramin ƙwarya ya ce " ki samu gashinta ko farcenta ki sa a cikin wannan ƙwarya sai ki rufe. Da ƙarfe ɗayan dare ki toni rami ki sa wannan ƙwaryan a ciki sai ki saka saurayin kare wanda bai taɓa hawa mace ba akan ƙwaryan ki bisine tare. Yadda karen nan ya danne ƙwaryan nan haka za ta ƙarasa rayuwarta a kwance ba za ta taɓa tashi ba har sai idan wani ne ya tone ramin ya ɗaga karen daga kan ƙwaryan shi ne za ta tashi"

"Baba taya za mu gane saurayin kare da be taɓa hawa mace ba?" Naomi ta faɗa cike da fargaba.
Boka ya kwashe da dariya...


Sai da ya gama mu su bayani ya ce " ikilo pataki. Kar ki yarda wani mutum ya gan ki lokacin da ki ke businewa"

Naomi da Maureen su ka haɗa kai wajen cewa wannan mai sauƙi ne...



..........................

Bayan sun dawo Kano tunanin samun gashin Farida ko farcenta ya sa su ka shiga ruɗani dan da sun ɗau abin da sauƙi. Daga baya Maureen ta ba ta shawara akan su je gidan ko za su samu. Hakan kuwa aka yi. Naomi ta tambayi Najeeb ya kai ta gidan shi. Ba tareda ya musa ba ya amsa ma ta.
Suna zuwa ɗakin Farida ta ce ya kaita. Tasallah ganin tare su ke da Najeeb ya sa ba ta iya hana Naomi ba...

Su na zuwa wajen dressing mirror ɗin ɗakin ta je tana dube-dube. Ta jima tana dubawa ko za ta ga gashin Farida ko da tsilli ɗaya ne amma ba ta gani ba. Har za ta tafi ta lura da wani baƙin Comb da ke wajen da kyau ta ga akwai tsillin gashi guda biyu a jiki ta yi murmushi ta cire su...



Bayan kwana ɗaya...

Tun da yamma ta je bayan gidan su ta tone shi da ɗan zurfi. Ta sa kwali da buhu ta rufe wajen.

Ƙarfe ɗaya saura ta ɗau ƙwaryan da Boka ya bata ta fita. Karen da ta siyo na kwance a wani keji gefen ramin da ta tona. Dama tun da yamma ta ma sa alluran bacci saboda Boka ya ce ba matacce za ta sa ba.

Lokacin da ta sa ƙwaryan a cikin ramin dai-dai agogon hannun ta ya cika ƙarfe ɗaya na dare. Ta cicciɓi karen za ta sa a cikin ramin aka dallota da torchlight.

"Anty Naomi what are you doing there?" Muryan ƙaninta Abel ya doki kunnen ta....




Skt 55


Naomi ta ɗago ido ta kalli Abel da ke nufo wajenta. Lokaci guda ta ji wani abu ya shiga kunnen ta, ta fara girgiza kai da sauri-sauri.

"Anty Naomi..." kafin ya ƙarasa maganar sa Naomi ta cilla ma sa Karen da ke hannun ta, ya goce da sauri har torchlight ɗin hannun sa sai da ta faɗi.

"Yirrrrrrrrrr, Ah Ah Ah, Chinkokoko kokokokoko Chichichichi..." waƙar da Naomi ta fara kenan tanayi tana rawa.

Abel ya tsaya yana kallon ta tareda kiran sunanta amma sam ba ta san yana yi ba sai tiƙar rawa ta ke yi, tana yi tana dariya.
Ganin fa ba dena rawar za ta yi ba, ya je ya kamota da ƙarfi yana faɗin "stop this nonsense please"
Naomi ta yi wani kuka sannan ta wancakalar da Abel ta baya ya faɗi ƙasa yana haki, "i'm coming oo i'm coming oo" abinda ta ke faɗi kenan kafin ta ranta a guje. Shi kuwa Abel ya fara ƙwala wa Maman su kira...


Ƙarfe ɗaya saura na dare ta tashi fitsari. Ganin idan ta koma bacci za ta iya kasa tashi ƙarfe biyu kamar yadda ta saba ya sa ta yi alwala kawai ta fara sallah. Ba ta kwanta ba sai ƙarfe uku da rabi bayan da ta ji ƙafafuwanta sun ma ta nauyi...


....................................


Karfe biyar alarm ɗin ɗakin ya fara bugawa. Ya sa hannu ya laluba agogon ya kashe alarm ɗin. Idon sa a rufe ya fara jawo pillow jikin sa saboda yadda ya ke jin daɗin baccin. Daga saman pillow har ƙasansa ya shafa kafin ya ankara pillow ya rungume ba matar sa. Ya sa hannu ya fara laluba gadon ba tareda ya buɗe ido ba. Sai da ya ga hannunsa ya kai ƙarshen gado bai ji laushin mutum ba, sannan yai saurin buɗe idon sa tareda kai hannun sa wajen switch ɗin wuta ya kunna shi. Ɗakin ya ƙaraɗe da haske, yadda hannun sa ya lalubo ma sa babu hakanan idon sa ya gano ma sa babu. Tunanin sa banɗaki ta shiga dan haka yai murmushi haɗe da miƙa yana addu'ar tashi daga bacci a zuciyar sa.
Ya ziraro dogin ƙafafuwan sa ƙasa hannun sa akan idanun sa yana murza su saboda nauyi da su ka ma sa. Sai da yai minti biyu zaune kafin ya miƙe tsaye ya fara ƙoƙarin cire kayan baccin sa...
Lokacin da ya shiga banɗakin ma dai wayam ne ba kowa a ciki. Ya girgiza kai yana sawa a ransa ƙila ta je cin abinci ne dan 'yan kwanakin nan har dare ta kan tashi ta ce yunwa, ta je ta yi girki ta ci.
Akwai ranan da ƙarfe ukun dare ta tashi ta je ta fara wanke wake wai ƙosai za ta ci. Ƙosan ma na manja irin wanda maƙociyar su Iya Abosede ta ke yi a Jos.

Cikin bacci ya farka da niyyar su yi abubuwa saboda kafin su kwanta ba su yi komai ba saboda ciwon kai da ya takura shi, ya ga gadon wayam. Ƙarshe a kitchen ya samu matar sa tana ta faman wanke wake.
Sai da ya tsaya a bakin kitchen ɗin ya ƙare ma ta kallo kafin ya ƙaraso wajen ta.

"My love mi ki ke yi da daren nan please?" Ya faɗa yana rungumeta ta baya.

"Ƙosan manja na ke son ci shine na ce barin zo na haɗa shi da sauri"

"Queen ki bari da safe sai ki yi mana, kin san ƙarfe nawa yanzu?"

" kar ka damu yanzu zan haɗa, na ma gama wanke waken saura marƙaɗe"

Ya sani ba haƙura za ta yi ba dole haka ya tsaya kusa da ita har ta markaɗa waken a blender ta zo ta soya ƙosan cikin manja. Duka duka ƙosan ma guda shida ne wanda ta yi su manya.

A kitchen ɗin ta zauna ta fara ci, tana ci yana kallon ta. Lokacin da ba ta da ciki ma ya aka ƙare da ciye-ciye balle yanzu da abun nema ya samu.

"My Champ ka taɓa ka ji, yai daɗi sosai Wallahi"

Ya girgiza kai ya ce " ƙosan mangyaɗa ma bana ci balle na manja. Ki ci da kyau Maman princess"


Tana ci tana lashe manjan da ke yatsunta.
"Ka san da yanzu na yi da niƙaƙƙen waƙe da ba zai taɓa yin daɗi kamar wannan ba. Amma this one is fresh and yummy"

Gyaɗa kai kawai ya ke dan ba wai yana gane maganganun ta ba ne. Haka ya tsaya har ta take ƙosan nan gaba ɗaya...


Yai wanka ya ɗauro alwala ya fito, ya sa jallabiyar sa ya sauko ƙasa ganin har lokacin ba ta ɗakin. Duhun da kitchen ɗin ya ma sa ne ya tabbatar da babu mutum a ciki, amma duk da haka sai da ya kunna wutan kitchen ɗin, still ba kowa. Ya kashe wutan ya fita yana sawa a ransa tana ɗakin ta ne. Ya wuce masallaci dan gabatar da sallar Asuba.

Bayan an idar da sallah ya tsaya ya ɗan yi azkar sannan ya fito. Musabaha su ka yi da Alhaji Abubakar maƙocin sa inda Alhajin ke tambayar ko ya yi tafiya ne kwana biyu baya ganin yana fitowa asuba.
Najeeb ya girgiza kai tareda ƙoƙarin nemo dalilin da zai sa ba zai fito sallan Asuba ba bayan yana gida. Dalili biyu ne za su iya sawa, ko dai ya makara bai tashi ba ko kuma ana ruwa. To duk babu ko ɗaya aciki domin zai iya cewa tun da su ka dawo anguwar indai yana gida to baya fashin fita sallar Asuba, hakanan ko ruwan farko ba a fara a garin ba balle ya ce ruwan sama ne.
Bai ma san lokacin da Alhaji Abubakar ya tafi ba saboda nisan tunani da yai.
Yana tafiya abubuwa da dama na ma sa yawo a kwanyar sa.
"Its not possible" ya faɗa da ƙarfi lokacin da kwakwalwarsa ta tuno ma sa da mafi yawancin abubuwan da su ka faru cikin abinda bai wuce sati biyu ba.

Yana shiga gidan ya fara kiran sunan ta da ƙarfi.

"Alhaji Barka da Asuba" Tasallah ta faɗa wanda fitowanta kenan daga ɗaki za ta je ta fara haɗa ma sa breakfast saboda fitar sassafiya da ya ke yi.

"Ina Aysherh?" Ya faɗa da muryan da ta ke tattare da damuwa. Ba abinda idon sa ke gani kamar Aysherh a tsugunne gaban sa tana kuka.

"Alhaji ba kai ka sa folisawa su ka zo su ka tafi da ita ba kwanaki"

Yadda ka san guduma aka kwaɗa ma sa a kai haka ya ji saukar maganar Tasallah.

Maganar da ta yi ya sa ya tuno abinda ya faru ranan. Numfashin sa ne ya fara ɗaukewa ga wani duhu-duhu da ya ke gani. Ya fara ƙoƙarin dafa bango saboda kar ya faɗi amma bangon ya ma sa nisa, ƙarshe dai da shi da hannun duk ƙasa su ka yi. Tasallah ta fara Salati tana kiran Alhaji.
Dafe ƙirjin sa yai saboda zafi, ga uwa uba kan sa da ke sarawa.
Idon sa a buɗe ya ke amma baya ganin komai sai duhu.

Salatin da Tasallah ke yi ya sa shi ya fara maimaita kalmar Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. Ya jima yana maimaita kalmar kafin ya fara jin sauƙin ƙuncin da ya ke ciki. Tashi yai a hankali ya rasa ma ina zai je waje zai fita ko sama zai haura.

"Aysherh Aysherh Ay..." bai ƙarasa na ukun ba ya faɗi ƙasa yigif...



............................


Bayan ta yi sallar Asuba sai da ta jima tana addu'o'i kafin ta ɗauko Ƙur'ani ta fara karantawa. Kusan ƙarfe takwas sannan ta ajiye ƙur'anin ta yi addu'a ta naɗe sallayar. Sai da ta je ta yi fitsari kafin ta zo ta kwanta tunda ba abinda za ta yi kuma ba yunwa ta ke ji ba. Tana kwance ne dai amma baccin ya ƙi zuwa, kewar mijinta ta ke yi sosai. Ba ta san yaushe wannan abu zai zo ƙarshe ba amma ta sani duk min daren daɗewa za a sami nasara tunda Allah su ka riƙe shi kaɗai. Ba dan kisa babban laifi ba ne da ba abinda zai hana ta je ta shaƙe wuyan Naomi har sai ta mutu.
Ta ƙara lissafta kwanakin da ta yi ba tareda zaman lafiya da mijinta ba. Kwanaki goma shauku ne rus yau ne ma cikon na sha ukun. Tunda ta dawo gidan Daddy kuwa ko zuwa bai yi ba balle kuma kira. Mafiya yawan lokuta takan wuni da waya a hannu ko za ta ga kiran shi ko text amma shiru. Dama tun ranan da ya faɗawa Daddy zai auri Naomi da su ka yi baran-baran har yau baya zuwa gidan.
Tana cikin wannan tunanin Aka fara buga ƙofar ta.
Yes ta faɗi tana miƙewa dan ta buɗe ƙofar.
Lokacin da ta buɗe ƙofar kafin ma ta ce ƙala Mom ta rungumeta tana faɗin "Alhamdulillah Allah ya amsa roƙon mu"

Ba ta fahimci mi Mom ke nufi ba ko kuma dai ta fahimta ba ta gaskata hakan ba ne kawai.

"Ɗazu Tasallah ta kirani wai Son ya faɗi, dreba ya wuce da shi asibiti. Ni da Daddy mu ka fita ɗazu mu ka je asibitin. He's back Ayshah. Mijin ki na neman ki, he wants to see you"

Tabbas ɗazu da tana azkar ta ji fitan su Mom amma ba ta kawo aranta wannan ne dalilin ba.

Hawayen daɗi ne su ka fara sauko ma ta, Mom ta sa hannu tana goge ma ta su tana faɗin " ba kuka za ki yi ba, farinciki za ki yi Ayshah. Allah ya dube mu da rahama. Wassu su kan shiga wannan yanayi su jima a ciki, a ɗau watanni ko shekaru ana ta roƙon Allah kafin daga baya a samu sauƙi amma mu Allah ya mana gata cikin ƙanƙanin lokaci ya bawa Najeeb lafiya"

"Alhamdulillah, Alhamdulillah" Farida ta faɗi tana murmushi.




Skt 56


Lokacin da su ka shiga ɗakin yana kwance yana bacci an ɗaura ma sa ledar ruwa. Daddy ke gefen sa yana kallon ɗan na sa yadda abubuwa da dama su ka dinga faruwa da shi a rayuwar sa. Kowa da tashi ƙaddarar, shi kam Daddy bai fuskan ci irin waɗannan ƙalu bale ba kamar na ɗan na sa. Tunda ya mallaki hankalin sa, idan ka cire mutuwar Aisha baya tunanin akwai lokacin da ya shiga yanayi na ƙunci sai a kan Najeeb. Shi ne yai rayuwar kaɗaici shekara takwas saboda ya rasa Sabreen, shi ne aka kidnapping, shi ne yai accident yai kusan wata tara kwance a asibiti shi ne ya ɗau watanni kafin ya dawo dai-dai, shine kuma mace ta ma sa asiri har ya ke ƙyashin matar da ya ke mutuwar so. Kai Alhamdulillah, dama dole ne mutum ya fuskanci jarrabawa a rayuwar sa.
Yai wa ɗan na sa addu'ar Allah ya sa ya ci dukkan jarrabawar sa ta duniya.

Mom ta ce " ya yi bacci ne?"
Daddy ya ce " Likita ne ya ma sa allurar bacci saboda ya samu ya huta"

Farida ta gai da Daddy tareda ma sa ya mai jiki. Daddy ya amsa da cewa "Aishah kin ga al'amari na Ubangiji ko. Allah ya share ma na kukan mu, sai mu dage da addu'a kuma, kar mu taɓa sakaci da addu'a"

Farida ta amsa da Insha Allahu. Kallon Najeeb ta ke tundaga gashin kan sa har tafin ƙafar sa. Ya mata kyau sosai amma kuma ya rame...

Najeeb bai farfaɗo ba sai kusan ƙarfe ɗaya na rana. Yana buɗe ido ya ga matar sa zaune. Kamar wadda aka tsikara haka ya tashi zaune da sauri. Ganin ta haɗa rai lokacin da su ka haɗa ido ya sa ya tashi tsaye ya iso wajenta. Tana zaune akan kujera ko gizau ba ta yi ba balle ta tashi sai ma juyar da kai da ta yi.
Tsugunnawa yai a gabanta yana kallon gefen fiskarta.

"Na sani abinda na yi is unforgivable. Na sani kina da hujjar da za ki yi fushi da ni. Amma Dan Allah my Queen ki yafe min, I love you, only you"

Juyowa ta yi ta kalli ƙwayar idon sa wanda ke nuna tsananin so da begen ta. Ba abinda ta tuna irin yadda ta tsugunna gaban sa tana hawaye tana roƙon sa amma yai watsi da ita.


"I forgive you" ta faɗa a hankali. Ya taso da sauri zai kissing ɗin ta ta sa hannu ta tare bakin sa ta ce " i forgive you amma kuma..."



..........................


Kafin a samu a kamo Naomi sai washe gari a chan wani bola tana kwance duk kayan jikinta a yayyage. Kai tsaye gidan Pastor Chukudi aka wuce da ita, wanda ya ke shine pastor ɗin church ɗin da su ke zuwa. Maureen ce ta faɗi silar haukan Naomi shiyasa aka wuce da ita gidan Pastor ɗin. Ita kan ta Maureen ta tsorata da yadda ta ga haukar ƙawar na ta, acewarta su koma wajen Ifagbemi ya basu magani amma Mrs Comfort ta ce ba za su aikata saɓo biyu ba. Ga saɓon zuwa wajen Boka dan asiri ga saɓon neman magani a wajen boka. Ita ta yarda Jesus zai warkar da 'yarta.

Annointed water da oil kam Naomi ta sha su kamar ba gobe amma shiru ka ke ji kaman an suka dusa. Ba sauƙi balle ayi tunanin za ta warke. Da dare Pastor Chukudi da tawagar su su wuni akan Naomi suna ma ta holighost fire amma su na yi tana ƙara rikice mu su...



.......................


Cikin kwana biyu Najeeb ya fita hayyacin sa. Farida ta ƙi dawowa. Ta ce ta yafe ma sa amma ya bata lokaci ta yi tunani. Mom ma ta goya ma ta baya akan ya barta ta huta.

Yau ma dai gidan ya zo roƙo amma ba ta nan, Adama ta ce sun fita da Sabreen.

Ya zauna a falo yana jiran dawowar su duk da kuwa Adaman ta ce ba su jima da fita ba.
A falon Daddy ya dawo ya sameshi lokacin har ya fara bacci. Jin takun mutum ya sa ya farka.
Gaishe da Daddyn yai yana faɗin yana son magana da shi. Daddy ya ce ya biyo shi. A falon Daddy su ka ya da zango inda Daddy ke tambayar ko lafiya.

"Dad ka sa baki dan Allah. Ta ce wai sai ta haihu kafin ta dawo. 3 months yai yawa, ba zan iya jure rashin ta ba"

Daddy yai murmushi ya ce " so ka ke na sa ta tayi abinda ba ta so?"

"No Dad amma idan ka ma ta magana wallahi ba za ta ƙi maganar ka ba"

" Son kenan, wannan tsakanin ka da iyalin ka ne ba ni da wani hurumi a ciki. Ka bata lokaci kaɗan za ta sauko, she went through alot saboda kai dan haka ka bi ta a hankali"

Najeeb ya haɗa rai dan bai ji daɗin maganar Dad ba, maimakon ya supporting ɗin sa sai ya ke maganar wai ya amince da hukuncin da ta yanke...



Lokacin da su ka dawo ma haka ta wuce shi, yana magana ko uhum ba ta ce ma sa ba ta haura sama.

"Sabreen please help me talk to her" ya faɗa yana haɗa hannu.

Kaman Daddy itama cewa ta yi ya ba wa Farida lokaci.

Ɗakin su ya wuce ko zai samu daman magana da ita amma ya samu ta kulle ɗakin.

"My Queen please ki bari na ganki ko na minti ɗaya ne"

Tana zaune akan gado tana jin magiyar sa amma ko ajikinta duk da chan ƙasan ranta tana son kasancewa da shi amma ba za ta janye ƙudirinta na son horashi kaɗan ba. Haka ya gama magiyar sa ya bar wajen....

Bayan kwana biyar da haukar Naomi Pastor ya bada shawaran a je a bawa wanda ta yiwa magani haƙuri saboda idan su ka yafe hakan zai sa Naomi ta samu sauƙi.
Mrs Comfort, Pastor Chukwudi da Saint Janet suka je gidan su Najeeb. Maigadi ne ya sanar da su Farida tana gidan au Najeeb, su ka karɓi address a wajen shi su ka wuce chan...


Mrs Comfort kuka ta dinga yi wiwiwi a gaban su Farida tana roƙon su gafartawa Naomi. Daddy ya ari bakin Najeeb da Farida ya ce sun yafe, Najeeb ya haɗe rai dan shi plan ɗin shi ma sai Naomi ta je jail.

Pastor ya mu su godiya sannan su ka tafi. Duk da wannan yafiya da aka yi bai sa Naomi ta warke ba. Kwana biyu da dawowar su daga gidan su Najeeb ta tsere daga gidan Pastor ta shiga gari. Wasa-wasa aka baza neman ta amma har sati guda ba labarin inda ta ke...


.........................


Shirye-shiryen bikin Sabreen ake yi duk da kuwa Sabreen da Lukman ɗin sun amince akan ba za ayi hidima ba amma Mom da Farida sun ƙi. Wata guda aka saka har yanzu kuma saura sati uku.

Fitowarta kenan daga wanka ta kalleshi zaune akan gado. Mantawa ma ta yi ba tarufe ƙofan ba.
"Ni fa ba na so ana shigo mini ɗaki ba izini"

A hankali ya taso ya zo ya tsugunna gaban ta ya kamo hannunta biyu ya riƙe gam. Kallon sa ta ke yi yadda idon sa yai ja.

"Aysherh I cant, ba zan iya ba. Kafin 3 months ɗin nan zan iya mutuwa idan ba kya tareda ni. Please ki manta da komai ki dawo gida mu cigaba da rayuwar mu. I promised to make it up to you, ba zan sake ɗaukan sakatariya ma ce ba, yalla yarinyace ko tsohuwa. Zan dage da addu'an dare saboda kar wata ta kuma samun galaba a kaina. Zan yi duk abinda ki ka ce amma please come back to me. I love you"
Ya kai hannun ta kan kirjin sa ya ce " My heart beats for you Aysherh, only for you. Ki taimakeni ki taimaki zuciyata kar rashin ki kusa da ni ya min illa. Na ɗauka zan iya jurewa amma Wallahi ba zan iya ba, its being 2 weeks amma gani na ke kamar 2 years ne. I miss you Aysherh, I miss us. Please my Queen..."


*team Farida kun karɓi haƙurin Najeeb ko ya?*




Skt 57


"Ka yi haƙuri amma ba zan koma yanzu ba" ta faɗa a hankali duk da kuwa maganganun sa sun karya ma ta zuciya.

Ya cize leɓen sa na ƙasa yana huci, bayan 'yan daƙiƙai ya miƙe tsaye ya ce "tunda abinda ki ke so kenan zan jira ki"...

Ba ta iya ɗaga ido akan sa ba har ya fita daga ɗakin.
Anya ta ma sa adalci kuwa? Ta tambayi kan ta. Sai dai kuma ta rasa gane amsar da za ta bawa kan ta...

Yinin ranan sai sintiri ta ke tsakanin falo da ɗaki amma Najeeb bai dawo ba. Washe gari ma bai zo gidan ba...

Su uku ne a dining su na cin breakfast lokacin da Najeeb ya shigo. Kwana biyu kenan bai zo gidan ba.
Wajen Mom ya je ya gaisheta, ta shafa

Please Login or Register in order to submit comment