Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin sa.

A hankali su ka fara gudanar da abubuwa akan kujera. Nishin da Najeeb yai lokacin da wani daɗi ya ziyarce shi ya sa Farida faɗin "za a jimu fa"
"Soundproof" kawai ya iya faɗa ya cigaba da shiga ciki ciki...
Sai lokacin ta tuna da mafi yawan lokuta da ta ke son jin gulma amma ba ta iya ji ba saboda duk abinda ake a office ɗin ba ka jin sa a waje, Lokacin da ta ke Miss Salihu...

Yana kwance ya miƙe akan kujera ita kuma tana kwance a kansa su na maida numfashi, kayan su na yashe a gefe.

" ina so ya kasance namiji mai kamannin ka" Farida ta faɗa hannunta na wasa da nipples ɗin sa.

"Ina son mace mai irin jarumtar ki. A no nonsense cute princess"

"De ka ce mai baki kamar ni, ta dinga cika ma ka kunne da surutu"

"Ina son ta kasance mai komai irin na ki, everything na ki"

"I love you" Farida ta faɗa tana kissing ƙirjin shi...


Anas ya zo zai shiga office ya ga tag ɗin da aka sa *do not disturb*

"Naomi mi Najeeb ke yi a ciki?"

Naomi ta langwaɓar da kai ta ce "Madam ce ta zo"

"Madam....He's wife?"

Naomi ta amsa da yes.

Anas yai murmushi ya juya yana cewa nima ba zan dawo da amaryata aiki anan ba kuwa...

Banɗakin da ke office ɗin su ka shiga su ka yi wanka, da ke garin akwai zafi shiyasa Farida ta daure ta yi wanka da ruwan shower ɗin wanda ba irin na gidan su ba ne mai ba da ruwan sanyi ko ruwan ɗumi, wannan ruwan sanyi kawai ke bayarwa.

Bayan sun kimtsa ne Najeeb ya ƙarasa duba wani aiki, ya yi su a gurguje cikin minti shabiyar. Sannan su ka fito daga office ɗin maƙale da juna.

Farida ne ta cewa Naomi sun tafi sai gobe. Naomi ta bi bayan su da kallo.

Office ɗin Anas su ka je, Anas sai dariya ya ke mu su, har da tsokala wai zai bawa Najdah aiki a office ɗin sa, saboda aci soyayya a gida da office.

Daga wajen Anas su ka fita daga kamfanin sai gida. Tana shiga falo ta cire gyale da ɗankwalin ta wanda ya jiƙe saboda wankan da su ka yi ɗazu kan bai gama bushewa ba ta ɗaura ɗankwali, dan ma gashin da kitso ba wai a tsefe ya ke ba.

Tasallah ta leƙa a kitchen ta ma ta sannu da aiki sannan ta haura sama.

Yana tsaye yana waya ta shigo. Zuwa ta yi ta rungumeshi ta baya. Yadda ya ke wayan ta tabbatar da Daddy ya ke magana. Minti ɗaya kafin ya gama wayan.

"Miji na da Daddy ka ke magana?"

"Yes Love, he's so excited that ya kusa ganin 'ya'ya na"

"Yanzu ba ka ji kunyar gaya ma sa ba?" Ta faɗa tana ƙoƙarin cire ma sa riga.

Dariya yai ya ce "wani kunya kuma my Queen"

"Dan Allah ya ka gaya ma sa? Cewa ka yi Dad matata tana da ciki? Ko cewa ka yi Dad Aysherh na da ciki?"

Jawota jikin sa yai ya ce "cewa na yi Dad abubuwan da mu ke yi da wife ɗina an samu sakamako mai kyau kum...."

Toshe bakin sa ta yi ta fara dariya...



.............................

Rintsawar kirki Naomi ba ta yi ba daren ranan. Ta jima tana kallon hotunan Ogan na ta a waya. Ta sani Ogan ta ya ma ta nisa hakanan ga matar san nan da alama masifaffiya ce. Ta tuna ranan da ya fara resuming aiki tana zaune ta hangoshi yana tahowa. Tafiyar sa kaɗai abun kallo ne, balle shigar sa. Ta dulmiya da kallon sa har ya zo ya buɗe office ya shiga ba tareda ta iya buɗe baki ta gaida shi ba.

Sai da ta ji ya rufe ƙofan ta yi saurin miƙewa tsaye tana sake kallon kan ta a screen ɗin wayarta. Wig ɗin da ke kanta ta sake bazawa da kyau kafin ta ƙara goga janbaki a lips ɗinta sannan ta shiga office ɗin.

"Good morning Sir" ta faɗa tana jiran ya amsa.
Bai yi kamar akwai mutum a wajen ba ya cigaba da latsa system ɗin da ke gaban sa.

"Oga i'm Naomi Masoyi your new secretary"


"Get back to work then" ya faɗa ba tareda ya ɗago ya kalleta ba.
Ranan ba ta tunanin duk shige da ficen da ta ke tsakanin office ɗin sa ya ɗaga ido ya kalleta.
Washe gari ma cikin ƙananun skirt ɗinta ta zaƙulo ta sa ta tafi office, skirt ɗin rabin cinyar ta ya tsaya. Yadda jiya ta kasance hakan ma ta kasance yau ko sau ɗaya ba su haɗa ido ba. Tana ma sa magana bayan ya ce ta tafi ya daka ma ta tsawa, sosai ta tsorata da shi duk da ma ta samu labarin halinsa sai dai ance tunda yai rashin lafiya ya rage faɗa.

Sati ɗaya da ya fara zuwa aiki gaba ɗaya ta shiga wani hali. Soyayyar Ogan na ta ya ma ta wani mugun kamu. A kullum ta kalleshi ƙara dulmiya ta ke cikin son sa. Ta rasa ya za ta yi da wannan so da ka iya jawo ƙarshen aikinta. Wanda shi ke ciyar da su yanzu. Ta gama service ba aiki, tana manage a wani shago inda ta ke salesgirl kafin mamansu ta yi hatsari...

Mahaifin su Pastor John Masoyi ya jima da mutuwa kusan shekara shabiyar kenan. Shi mutumin Ɓilliri ne da ke jahar Gombe amma matar sa Comfort 'yar Tafawa Ɓalewa ne da ke Bauchi. Sun haɗu a wani church seminar ne da aka yi a Kaduna tun lokacin bai ma zama Pastor ba.
A BUK yai karatu, bayan ya yi service ya samu aiki a wani Kamfani daga baya kuma ya ajiye aikin bayan ya tsunduma cikin harkan Choci. Mrs Comfort 'ya'ya uku ta haifa ma sa. Elizabeth ce babba sai Naomi da ƙanin su Abel.

Kasancewa Pastor John ya mutu ya barta da yara ƙanana ya sa ta nemi aiki ta samu a wani babban Kamfani. Da albashin ta ke ciyar da yaranta ta kuma kula da ɗawainiyar su.
Elizabeth tana dawowa daga makaranta ta yi hatsari ta mutu lokacin ajinta Biyu a Unimaid.
Ya saura Naomi da Abel.

Koran ma'aikata da aka yi a Kamfanin da Mrs Comfort ke aiki ya sa ta rasa aikin ta, kafin daga baya ta samu aiki a Najeeb constructions.


Naomi typical catholic church girl ce until lokacin da ta fara Jami'a ta haɗu da Daniel wanda cikin watanni kaɗan ya rabata da duk wani shiru-shiru da rashin wayewa da ta ke yi. Sun shekara uku su na gurzan junan su wanda har cire ciki ta yi sau biyu. A shekara ta huɗu ne su ka rabu bayan ta kamashi a kan ƙawarta su na abubuwa. Tundaga Daniel ta cire soyayya a ranta amma ganin Najeeb ya sa ta faɗa wani yanayi wanda ko lokacin suna tareda Daniel ba ta ji irin sa ba. Soyayyar Najeeb ce ta ma ta babban kamu.


.............................

Ba ta jima da zama ba su ka shigo hannun su cikin na juna. Ta yi saurin miƙewa tsaye tana gaishe su. Farida ce kawai ta iya amsa ma ta shima ɗin kaman ana roƙonta.

Wassu files Naomi ta kawowa Najeeb dan yai signing, daga ɓangaren Farida ta hango shigar Naomi da kuma yadda ta yi bending tana nunawa Najeeb wani abu a takardar da ke hannun sa. Shirt ne da pencil skirt ta sa. Pencil skirt ɗin ba ƙaramin matseta yai ba, dan tafiya ma da ƙyar ta ke yi, rigan kuma ta buɗe buttons uku na sama har ana ɗan hango bra ɗin ta.

Ba ta ankara ba ta ji an damƙi gashin ta. Sai da ta jita a ƙasa sannan ta ɗaga ido tana kallon angry Farida tsaye da gashin wig a hannun ta.

"Ke karuwa ce? Ko kwartuwa ce? Wannene a ciki?" Ta faɗa da tsawa.

"I'm sorry Madam, I'm sorry"

"Dan uban ki miyasa za ki bar nonuwan ki a waje? Nan hotel ne? Ko aiki ki ke a hotel?"

Naomi ta birkice tana ta bada haƙuri.

"Albarkacin Mrs Comfort ki ke aiki anan, idan ba za ki kama kan ki ba, za ki yi gaba dan ba zan yi aiki da karuwa ba"

Ta cilla ma ta gashin wig ɗin ta ce " ki je ki sake reviewing dresscode na wannan kamfani. The next time ki ka sake shigan banzan nan za ki gane kuren ki. Now get out"

Naomi ta ɗau gashinta ta yi waje da gudu.

Najeeb na kallon su bai ce komai ba, Farida ta juyo tana huci.

Najeeb ya taso ya kama hannunta, sai da ya zaunar da ita a kan kujerar sa sannan ya ce "My Queen kin san fa yanzu ba ke ɗaya ba ce. You have to take things easy"

"Take it easy? bayan ga sakatariyar ka tana girgiza ma za nonuwanta"

Najeeb ya fashe da dariya ya ce " My Queen anya ba za ki haƙura da zuwa aikin nan ba"

"Wallahi sai na zo. Da ba na nan fa inaga sai dai ka ɗaga ido ka ga ta buɗe ma ka rugujajjun nonuwanta"

Najeeb mi zai yi banda dariya...



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣5️⃣0️⃣





Tun daga wannan rana Naomi ta risina, tsoron Farida ta ke sosai. Ko office ɗin ta ta shiga za ta ma ta wani aiki ko za ta ba ta saƙo haka za ka ga jikin ta na rawa. Farida kam tana lura da yanayin Naomin sosai dan ta ga alama kaman tana yiwa Najeeb kallon so. Sai dai ganin ta dena shigar banza da kuma rawar ƙafa idan tana office ɗin sa ya sa ta ɗan ɗaga ma ta ƙafa. Ita ba dan tausayin Mrs Comfort da ta ke yi ba da tuni ta kori Naomi...

Tana zaune a falon ƙasa su na hira da Faruƙ wanda yazo hutu sai ga Najeeb ya sauko. Yau weekend ba su je aiki ba, sai da ya mannawa matar sa kiss a kumatu kafin ya mu su sallama akan zai je ya gaida Daddy wanda ke fama da ciwon ƙafa. Farida ta tashi ta raka Najeeb zuwa wajen mota.
Tana rungume jikin sa ta ce "za mu je gida anjima ni da Faruƙ"

"Kar ku daɗe plz kin san nima ba zan jima ba zan dawo"

Ta manna ma sa light kiss a lips ɗin sa. Shi kuwa ya rankwafo ya kissing cikin ta yana faɗin "baby, Daddy zai je gaida granny dont disturb your mom"

Farida ta yi dariya...


Kamar kowani zuwanta, yau ma maganar auren Ummi ta kuma yi wa Baffa Musa, wannan karan hatta Faruƙ sai da ya sa baki, shima ya nuna goyon bayan sa ɗari bisa ɗari.

"Baba idan ba ka amince ba Allah zan je Toro na ɗauko Abdul da Hamza su zo mu taru mu yi ta ma ka kuka har sai ka amince"

Baffa Musa yai murmushi ya ce "kin zama babbar banza kenan tunda yara na karatu za ki je ki ɗauko su"

Ta ɗan shagwaɓe fiska ta ce "Baba to ai duk cikin so ne"

Tafiyar su Farida ya sa Baffa Musa dogon tunani. Amina ta sha wahala da yaranta tun bayan rasuwan mijinta na ƙarshe. Da tana tareda iyayenta ne to yanzu kuma dukkan su biyu sun rasu, ita ɗaya za ta yi rayuwarta sai dai zama da yayyenta da matan yayyen. Yaranta ma ba sa kusa. Farida na nan Kano, Faruƙ na Kaduna. Sauran biyun suna boarding school a Toro sai hutu su ke zuwa gida.
Zai taimaka ma ta wajen haɗa kan yaran idan ya aureta. Kuma hankalinta zai kwanta idan tana kusa da 'ya'yan ta. Da wannan tunani ya yanke shawaran tuntuɓar Aminan ya ji mi za ta ce.

Ranan Asabat ya je yai aski, ya zauna aka ma sa gyaran fiska. Ɗan tsoho mai shekara hamsin da takwas ya fito fes da shi. Ranan Lahdi da sassafe ya ɗau hanyar Jos. Yana tuƙi yana jin wani nishaɗi. Sabon kaya ya saka wanda cikin ɗinkin shi na sallah ne da bai sa ba. Shadda ce ash da ta sha aikin hannu mai kyau, ya ɗaura hular Zanna a kan sa wanda ya shiga da kayan...

Da ke Ummi ba ta san da zuwan sa ba, ta ma fita barkan suna chan ƙasan layin su lokacin da ya zo, Aliyu babban yayan su wanda shima ke zaune da iyalin sa a gidan ya kirata akan ga Baffan Farida ya zo. Sai da ta ji wani jim a ranta, ta dai amsa ma sa da cewa tana zuwa yanzu.

Baffa Musa kam tuni ya bayyanawa Aliyu buƙatar sa na son auren Amina. Yaya Aliyu ya nuna ba su da matsala da wannan infact su na murna da wannan haɗin. Kawai dai ita Aminan ne sai a hankali dan tun rasuwan Alhaji Kabiru ta ƙi aure fau-fau bayan kuma har yanzu da sauran ƙuruciyar ta...


Ummi ta shiga falon Yaya Aliyu da sallama wanda anan ne aka sauki Baffa Musa. Atamfa ce ajikin ta ɗinkin doguwar riga sai babban gyalen Khashka da ta yafa, hannunta ƙunshe da jan lalle.

Ta samu kujera ta zauna tana gaida shi a ɗan kunyace. Ta rasa dalili tun lokacin da su ka yi maganar aurensa da Farida sai ta ke jin kunyar sa.

"Amina" ya kira sunan ta ahankali.
Ta ɗan ɗago ido ta kalleshi kafin ta sauke.

"Lallen hannun ki yai kyau"

Ta maida hannunta cikin gyale tana wata munafukar murmushi ƙasa-ƙasa.

Shiru ne ya biyo bayan abinda ya ce kafin daga baya ya katse shirun da cewa "Amina na zo da ƙoƙon bara ne. Ina fata dai ba za a barni da ƙishirwa ba. Haƙiƙa ke mace ce ta gari, kin yi goggormaya da rayuwa kuma kin sha fama da jarrabawa kala-kala. A hakan kin nuna jarumta da bajinta mai ban mamaki. Ina neman alfarma da ki kasance cikin rayuwata. Mu haɗu mu rufawa juna asiri har iya ƙarshen rayuwar mu"...

Bayan ya gama bayanan sa Ummi ta ce ya bata lokaci ta yi tunani duk abinda ta yanke zai ji a wajen Yaya Aliyu...


Sati ɗaya da zuwan Baffa Musa Jos Yaya Aliyu ya kirashi akan Ummi ta amince za ta aureshi. Murna a wajen Baffa Musa ba a magana. Da ke abu ne da an riga an san juna sai abin bai ɗau lokaci ba. Bayan Baffa Musa ya tura magabatan sa. Yaya Aliyu ya sa biki nan da sati biyu...



..........................

"My Champ kana ganin kuɗin nan bai yi kaɗan ba" Farida ta faɗa tana miƙawa Najeeb check ɗin da ke hannun ta.

"Make it 20" Abinda ya faɗa kenan.

Farida ta ƙarɓi check ɗin ta yaga ta ciro wanni ta sake cikawa, maimakon 15million da ta sa ɗazu sai ta mai da shi 20million.

Yau ta ke so ta je gidan Baffa Musa dan ta kai mishi.
Wayar ta ne ya fara ringing. Tana dubawa ta ga sunan Ummi. Ta katse kiran kafin ta sake kira.

"Farida wanni shirmen ne wannan. Ba ki da kunya ko"

Farida ta yi dariya ta ce "Ummi to za ki yi aure ba gyaran jiki ne?"

"Ungo na ki da gyaran jiki" ta faɗa tana kashe kiran.

Farida kam sai dariya ta ke. Matar da ta musu gyaran jiki ne ita da Najdah ta tura ma ta maƙudan kuɗi akan ta je ta yiwa Ummi gyaran jiki...


Yammacin ranan Farida ta je gida. Baffa Musa bai dawo daga kasuwa ba sai bayan Maghrib. Ta tsaya ta naɗi tuwon shinkafa miyan bushashshen kuɓewa da Baaba Sabuwa ta yi, dama wannan cikin mahaukacin kwaɗayi ya ke sata.
Bayan sallan Isha ta samu gamawa da Baban na ta.

Su ja gaisa ana ɗan raha sannan ta miƙa ma sa check ɗin kuɗin wanda ke cikin ƙaramin envelop.

Baffa Musa ya zaro ido ganin maƙudan kuɗin da ke jiki.

"Farida! Wannan yai yawa. A'a Farida" ya maida check ɗin cikin envelop ya miƙa ma ta.

Maimakon ta yi magana sai ta fashe da kuka.
"Farida lafiya?" Ya faɗa da ɗan damuwa.

"Baba sai ka ce wanda na baka kuɗin jini za ka maida min. Baba ba za ka samin albarka ba kenan? Mijina ya mallaka min kaso 25 na kamfanin sa, duk wata inada kuɗaɗe dayawa da ke shiga account ɗina. Idan ban kyautata ma ka ba ya zan yi da su? Ban taɓa ganin Baba na ba sai a hoto. Kai na sani a matsayin Uba, dan Allah ka sa min albarka"

Baffa Musa ya maida check ɗin cinyar sa yana sa ma ta albarka.

Bayan ya gama Farida ta ƙara ba shi wani abin mamakin ta hanyar gaya ma sa cewa mijin ta ya biya mishi Hajjin bana, ba shi kaɗai ba harda Baaba Sabuwa da Ummi. Ita Anty Wasilah da ke tana da tsohon ciki sai wata shekarar.

Baffa Musa ya ɗaga hannu sama yana kwararo addu'a wa marigayi ɗan uwansa, yanayi yana hawaye.
Faridan ma sai da ta yi kuka. Ba ta rayu ta ga wannan Bawan Allah ba amma duk wanda ya san shi har yau labarin kirkin sa ake ba ta. Tana fata su haɗu a Aljannah ta ganshi ya ganta...


Bayan sati biyu aka ɗaura auren Baffa Musa da Ummi bisa sadaki dubu Hamsin. Ba ta tare a lokacin ba sai bayan sati ɗaya...

Daren ranan Baffa Musa ya shigo ɗakin amarya wanda ya sha tsadaddun furnitures da Farida ta yiwa Ummin ta.
Ledar kazarta ya ajiye a centre table sannan su ka gaisa da amarya. Bayan sun yi sallan godiya anci kaza sannan su ka shiga raya dare. Baffa Musa round uku yai a wannan dare. Yai biyu a jere na ukun kuma ƙarfe huɗun asuba su ka yi shi. Amina ta na nan matse ga shi ta sha gyara. Ba ƙaramin daɗi ya kwasa ba. Itama Ummin ta ji daɗi sosai, shekaru takwas kenan rabonta da namiji. Ashe dai har yanzu tana buƙatar namiji dan sai ta ke jin duk wassu ƙofofin jikinta sun buɗe suna karɓan wannan ni'ima...


.............................


A falon Najeeb su ke aikata abubuwa. Yammacin ranan litinin. Daga dawowar su daga office kenan ko abinci ba su ci ba. Bayan komai ya kankama su ka je su ka yi wanka.

Yunwa ta ke ji dan haka ta sauka ƙasa dan ta nemi abinda za su ci. Tasallah bata nan an musu rasuwa ta ɗau hutun kwana uku.

Tana kitchen ta ji ana danna doorbell. Ta ajiye frying pan da ta ke son ɗaurawa a gas ta fito. Shirt ɗin Najeeb ne a jikin ta, ga cikinta ɗan wata biyar da ya fito sosai. Leƙawa ta yi dan ta ga ko mace ce ta buɗe ba sai ta je ta nemi hijab ba. Ganin mace cikin liƙabi ya sa ta buɗe ƙofa.
Tana buɗe ƙofar ta amsa sallamar da matar ta ma ta.
Ɗaga liƙabin da matar ta yi ne ya sa Farida faɗin "Sabreen!"

Sabreen ta yi murmushi ta rungumeta...

A falo ta zauna tana jiran Faridan ta sauko. Bayan ta haura sama dan ta kira Najeeb.

Najeeb na aiki akan laptop Farida ta shigo ɗauke da murmushi.

"Ga amarya ta biyo angonta" ta faɗa da sigar tsokana.

"Hmm ki ce ango zai yi abubuwa kenan"

Farida ta ja hancin sa ta ce "Sabreen ce ta zo"

"Sabreen!" Ya faɗa da mamaki...


Sosai Sabreen ta bawa Farida tausayi. Cewa ta yi ta zo mu su bakwana ne dan ba lallai su sake ganin ta ba. Mahaifinta ya rasu wata biyu da su ka wuce. Ta ajiye aikin film gaba ɗaya, ta biya tara ta fanshi kan ta saboda ba ta gama aikin da ta signing za ta yi ba da wani production company.
Dukiyarta da dukiyar da ta samu na gadon Baban ta da shi ta ke son buɗe foundation dan ta dinga taimakawa marayu da mabuƙata da su.

"Sabreen aure fa" Farida ta tambaya da zuciya ɗaya.

"Ba wanda zai iya aurena Ayshah. Ni ma kuma na haƙura da aure. Allah bai yi zan yi aure a rayuwata ba. Zan cigaba da istigfari da neman ilimi har iya ƙarshen rayuwata"


Farida sai da ta yi hawaye itama ganin yadda Sabreen ke kuka cikin nadama. Yes duniya ta yi yayinta na ɗan wassu shekaru amma yanzu duniya ta juya ma ta baya. Wanda su ke tareda ita duk sun watse.

Tare su ka shiga kitchen su ka yi girki. Bayan sun ƙare cin abinci kafin Sabreen ta tafi akan ranan Monday za ta tafi.

...........................



Naomi gani ta ke yi abinda IfaGbemi ya gaya ma ta ba mai yiwuwa ba ne. Tun da ta ke ba ta taɓa ganin Najeeb yai fushi da Farida ba. They are inseparable. They are madly inlove.

Wannan weekend ɗin da ta wuce ta je jahar Ekiti chan cikin wani ƙauye tareda ƙawarta Maureen.
Ba komai ne ya kaita wajen ba sai saboda Najeeb ɗ. Tsawon watanni tana dakon soyayyarsa amma shi kam bai ma san tana yi ba. Har aranta ta ƙudura idan har Najeeb zai so ta to za ta bar kiristanci ta koma musulunci.

Maganganun Ifagbemi na ma ta yawo a ka lokacin da ta ke jujjuya kwallin da ya bata a hannunta.

"Mace ɗaya aka rubuta mi shi a gaba ɗaya rayuwar sa. Duk inda zai je ya dawo mace ɗayan nan ita ce ƙaddarar sa"

"Baba to ya zan yi kenan? Ba zai taɓa sona ba kenan?"

Bokan yai wata baƙar dariya ya ce " idan ki na so ya so ki sai dai ya gan ki a matsayin matar da ya ke so. Idan ki ka yi kamaceceniya da ita zuciyar sa zai so ki"

Maureen da Naomi su ka haɗa baki wajen faɗin "ba mu gane ba"

Wata ƙwarya da aka lulluɓe da jan ƙyalle ya ɗauko sai da yai ta surkullen sa sannan ya buɗe ƙwaryar sai ga kwalli a ciki.
Ya ɗau kwallin da hannun hagu ya miƙawa Naomi ya ce ta amsa da hannun hagu.
Naomi ta amshi kwallin tana jujjuya shi.

"Duk ranan da yai fushi da matar sa, ki saka wannan kwallin a idon ki ki ƙyafta ma sa ido ki kwantar ma sa da hankali. Zai dinga kallon ki a matsayin matar sa, duk soyayyar da ya ke mata zai dawo kan ki Amma..."



"Naomi" muryan Farida ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.

"Yes ma" ta faɗa da muryan girmamawa.

Akwai Dr Lukman da zai zo wajena anjima ki barshi ya shigo.

Naomi ta gyaɗa kai...

Najeeb ya fita supervision. Ita kaɗai ke office. So ta ke ta surprising Najeeb amma bayan Lukman ya amince za ta sanar da shi komai.

Ba'a jima ba sai ga Lukman ya shigo.

"Hajiya Farida ya aiki"

"Lafiya Dr, ya hanya"

"Alhamdulillah"

"Ya haƙuri kuma na ji ance Alhaji Magaji ya rasu"

"Hakane kusan 5weeks ma yanzu"

Farida ta ce Allah jiƙan sa.

Shiru ya ɗan ratsa office ɗin. Kafin daga baya Farida ta ce " Doctor har yanzu ka ƙi aure"

Lukman yai murmushi mai ɗaci ya ce " har yanzu Allah bai nufa ba. Kowacce mace ba ta son auren ɗan shege"

"I'm sorry" Farida ta faɗa cike da tausayin shi.

"No dont be. Allah ba ya taɓa ɗaurawa bawa jarrabawar da ta fi ƙarfin sa"

Farida ta ce hakane.

"Amma ba ka sake nema ba ne ko ya?"

Lukman ya nisa ya fara ba ta labarin yadda yai sanadin musuluntar da wata colleage na shi Dr Jennifer, har sun tsara za su yi aure ta amince da shi duk da ya gaya ma ta matsayin shi. Ƙwatsam wani abokin aikin su wanda ya ke da mata biyu fa Dr Faisal ya shiga nemanta yai ta hure ma ta kunne da ma ta burga da asalin sa yana kushe Lukman a matsayin sa na shege. Ƙarshe dai Dr Faisal ta aura.

"Kai duniya, yanzu musulmi ɗan uwan musulmi amma sai ya ha'inci ɗan uwan sa. Shi da ke da mata biyu amma ba su ishe shi ba sai sun hanaka samun mata?"

Lukman yai dariya mai ciwo ya ce " mi za ta yi da shege bayan ga cikakken namiji mai asali"

Jikin Farida yai sanyi. Yadda ta tsara anya zai yadda da shawaranta kuwa? Dama so ta ke ta ma sa maganar Sabreen. Sabreen tana buƙatar aure sannan tana buƙatar auren mai addini wanda zai kula da ita. To kuma Lukman shi ne candidate ɗin da ta ke ganin ya dace ya auri Sabreen dan ya ƙara gyara ma ta rayuwar ta...

Shigar Dr Lukman office ɗin Farida ya sa Naomi ta sa do not disturb tag a jikin ƙofa tana addu'ar Allah ya sa Najeeb ya dawo da wuri.

Tana zaune kuwa sai ga Najeeb, as usual ko kallon ta bai yi ba ya zo zai shige office sai ya ga tag ɗin da ta sa.
Ya juyo a fusace yana tambayar dalilin saka tag ɗin.

"Sorry Sir, Madam ce ta ce na sa dan ta

Please Login or Register in order to submit comment