Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana fashi da makami kafin daga baya ya koma harkan kidnapping. A Kaduna ya ke operation ɗinsa sai dai wata ɗaya da ya wuce Joseph ya kira shi akan yanaso ya kidnapping Najeeb saboda ya ɗau fansar abinda ya ma sa. Wannan ya sa ya zo Kano su ka fara tsare-tsaren yadda komai zai tafi. Da ke Joseph yai aiki a Najeeb constructions hakan ya bashi daman sanin hanyoyin da za su aiwatar da ƙudirin su.

Da safe ba a basu abinci ba haka da rana, gaba ɗaya Farida ta galabaita. Tana chan ta cure gefe guda ta yi kukan ta yi surutun har ta gaji. Najeeb kam ko ehem bai ce ma ta ba.

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, ɗaya daga cikin ma su tsaresu ya shigo ɗauke da bindiga. Zuwa yai ya jawo Farida da ƙarfi, Najeeb ya tashi zai yi kan sa. Ya nuna ma sa bindiga tareda cewa "sit"

Farida ganin anyi hanyar waje da ita ta fara cewa Najeeb ya taimaketa.

"Dont hurt her" Najeeb ya faɗi da kakkausar murya

Wani ɗakin ya shiga da Farida bayan ya kulle Najeeb a ɗakin da su ke da farko.

Ganin ya yo kanta ya sa ta ƙwalla ƙara tana kiran Sir Najeeb da Umminta.
Guje-guje su ka fara yi a ɗakin wanda ya ke cike da tarkacen kayan maye. Cak ta tsaya lokacin da ƙafarta ya taka wata fashashshiyar kwalba. Hakan ya bawa mutumin damar kamata ya kwantar da ita da ƙarfi, sai ihu ta ke ta na ƙoƙarin tureshi amma ta kasa. Ya kama hannayenta da hannunsa ɗaya, ɗaya hannun kuma yana ƙoƙarin zuge zip ɗin wandonsa.
Wani razannannen ƙara ta ƙwala wanda gaba ɗaya gidan sai da ya ɗauka.

Emeka da wasu biyu su ka yo ɗakin da su ka ji ƙaran da gudu. Ganin Larry na shirin afkawa Farida ya sa Emeka ya ture Larry tareda kwaɗa ma sa mari.

"Are you crazy?"

Larry ya ce" the girl too hot Oga. I feel...."

"Will you shut up. You want to ruin my business abi"

Ce wa ɗayan yai ya maida Farida ɗakin da Najeeb ya ke.
Da ɗingishi ta shigo ɗakin saboda har lokacin kwalbar da ta caketa na ƙafar.

Tunda aka fita da Farida hankalinsa ya tashi yasan ba kasheta za'ayiba amma ba makawa sai sun yi raping ɗinta. Lokacin da ya ji ƙaran da ta yi sandarewa yai a wajen jikinsa ya fara ƙyarma yana ayyana abinda zai yiwa Joseph da crew ɗin sa idan sun fita anan. Ganin yadda aka shigo da ita ya sa yai kan ta da sauri. For the first time tun jiya da aka kawo su ya ma ta magana.
"Miss Salihu are you Ok. Mi su ka miki?"

Shiga jikinsa ta yi tana kuka jikinta na rawa. Ta gama tsorata dan ta sadakar Larry shigarta zai yi. Tausayinta ya mamayeshi dan ya san saboda shi ta shiga wannan haɗarin dan Joseph da shi yake gaba. Cuddling ɗin ta yai so tight yana ba ta haƙuri. " I'm sorry, i'm very sorry Miss Salihu"
Sun jima a haka shi kan sa ya rasa dalilin da ya sa ya ji wani nitsuwa ya shigeshi farat ɗaya, like kada ya saketa su cigaba da tsayuwa a haka.

Zafin da ta ji a ƙafarta ya sa ta tuno da kwalbar da ta taka. Cikin sheshsheƙar kuka ta ce "Sir Najeeb ƙafa na" sai alokacin ya saketa ya fara duba ƙafan wanda ke ta zubar da jini.

Zaunar da ita yai sannan ya ɗaura ƙafar a cinyarsa ya ce " zan cire mi ki kwalbar, sorry it will hurt"
Girgiza kai ta yi tareda rufe idonta, ta cize leɓe. A hankali ya cire kwalbar tareda ɗaure ƙafarta da farin hankerchief sannan ya sake jawo ɗankwalinta wanda ya faɗi lokacin da Larry ya fita da ita. Ya yaga ya sake ɗaure ƙafar sosai.

"Are you Ok?" Ya tambaya yana kallonta.

Girgiza kai ta yi ta ce nagode.

Bayan minti shabiyar aka kawo mu su abinci, ko kallon wajen Farida ba ta yi ba duk da kuwa yunwar na cinta.

"Ki tashi ki ci abinci" ya faɗi lokacin da ya ga ta share abincin.

"Ba zan ci ba. Wataƙila ma sun sa magani"

Zuwa yai ya ɗau take away ɗaya da ruwa ya kawo gabanta. " ba abinda za su sa aciki, because they need us alive. Besides na san yunwa ki ke ji"

Ta kalleshi ta kalli abincin ta ce " to kai ma ka ci, tunjiya ba abinda ka ci"

"Na saba da rashin cin abinci"

"Ana sabo da yunwa ne?" Bai amsa ma ta ba sai sokalin abinci da ya kawo dai-dai bakinta ya ɗaga ma ta kai alamar ta ci. Ba tai musu ba ta fara ci. Haka ya dinga bata abincin a baki har ta cinye.

"Kin ƙoshi?"

Ta gyaɗa ma sa kai...

Da dare zazzaɓi ya rufeta, tsoratar da tayi da kuma ciwon da taji su suka haɗu su ka sa mata ciwon kai da zazzaɓi. Tana kwance ta fara rawan sanyi harda kakkarwa. Daga inda ya jingina ya jiwo nishinta.

"Miss Salihu are you OK?"

Jin shiru ya sa ya taso ya je wajenta. Jikinta yai zafi sosai ga ba ruwa balle ya dinga shafa ma ta.
A hankali ya ɓalle buttons ɗin shirt ɗin sa ya mannata da ƙirjin sa. Thats the only option he can think of...

Ta jima a haka kafin zazzaɓin ya saketa amma bai janyeta daga jikinsa ba har bacci ya tafi da ita. Shi kam ya manta yaushe rabon da yai bacci without his pills.

Farkawan da za ta yi ta jita ajikinsa. For the first time tun haɗuwarsu sai ta ji kunyar sa. Da ƙyar ta iya tashi, nan ma sai da ya tallafa ma ta saboda ƙafarta da ya kumbura yana ma ta zogi.

Suna buƙatar ruwa dan haka ya je ya fara bubbuga ƙofa.

"What do you want?" Aka faɗa da kakkausar murya.

"Water"

"Una no go get any water for here ooo"


" please, give Us some water" Najeeb ya rintse ido saboda tuno matsayinsa ada da kuma matsayinsa a yanzu wai shi ke roƙon ruwa.

Da ƙyar wanda ke gadin ƙofar ya kawo mu su ruwa biyu, nan ma sai da ya cire belt ɗin Najeeb wai itama designer ce idan ya sayar zai samu kuɗi...

Ƙarfe shabiyu na rana Emeka da Joseph su ka zo mu su da albishirin yau za a sake su idan har an biya cikakken kuɗin da aka buƙata.

A fili Farida ta ce " miliyan hamsin ɗin. Kai amma karayar arziƙi ta sameka Sir Najeeb"

Dariya ta bashi saboda bata san networth na shi a shekara ba. Ko za a cire miliyan hamsin sau goma ba zai girgiza ba. Balle ya san idan har da gaske za a biya waɗannan kuɗaɗe to Dad ɗin sa ne zai biya, ba sai ya nemi taɓa masa kuɗi ba.

"Kenan za ka kori ma'aikata dayawa idan ka koma. Dan Allah kar ka kori ɗan uwana. Yakubu shi kaɗai yai degree a gidan Baffa Musa, kaga yayansa Faruƙu mai ƙaton hancin nan, ko sakandari bai gama ba, kasuwanci ya jona kaman na ubansa. Dan Allah ka min alƙawari ba za ka koreshi ba"


Murmushi kawai Najeeb ya yi.

"Sir Najeeb ka ga yadda ka yi kyau kuwa da ka yi murmushin nan. Dan Allah idan an koma office ka dena haɗa ran nan, ba ka kyau"

Juyar da kai yai yana kallon gefe duk da kuwa hankalinsa na ga surutun da Farida ke yi...


........................


Har za a tashi Dad ya ce ayi addu'a.
Aka ɗaga hannu aka yi addu'a sannan aka shafa.

Anas ya ce Dad " Insha Allah ko mi zai tafi according to plan"

"Allah ya sa Anas"

Anas ya kalli sauran officers ɗin ya ce "gentlemen, let's go"...


Emeka yana zaune da Joseph su na jiran Larry da ya tafi ɗauko kuɗi. Tun ɗazu aka ce an ajiye kuɗi a inda su ka buƙata.
Sun gargaɗi Larry akan ya tabbatar ba wanda ke binsa lokacin da ya ɗau kuɗin, shi ya sa ma su ka ce yana tabbatar da kuɗin na cikin jakar to ya sa jakar a ƙatuwar jakar Ghana-must-go da su ka bashi.

Minti biyu sai ga kiran Larry. Emeka ya sa ihu lokacin da Larry ya ce ya ɗauka kuɗin. Ya kalli Joseph ya ce "Bros we are rich"

Plan ɗin da su ka shirya shine, dama suna da mota, a daren za su bar Kano shi kuma Joseph saboda Najeeb ya ganeshi suna barin Kano daga Kaduna zai wuce ƙasar Ghana. Anan zai zauna har komai ya lafa kafin ya dawo.
Suna cikin tattauna plan ɗin su Larry ya shigo da jakar kuɗi.

Da sauri Emeka ya buɗe jakar ya ce su duba kuɗi sannan su duba ko akwai tracker aciki dan a matsayinsa na wanda ya kwana biyu yana aikin yasan ana iya samun wannan idan aka aiko da kuɗin ransom. Ganin babu tracker ya sa su ka fara jera kuɗin a wata jakar daban.

Abinda ba su sani ba shine sai da aka buɗe jakar aka sa ƙaramar tracker chip aciki sannan aka ɗinke kamar ba a sa komai ba.


Su Emeka na duba kuɗi sauran na shan giya suna ihu su ka ji kamar ana buɗe ɗaya daga cikin ƙofofin gidan.

Emeka ya ce su je su duba ko su Najeeb ne ke son guduwa.

"Larry, you sure say nobody follow you"

Larry ya gyaɗa ma sa kai.

Fitar sauran ke da wuya su ka ji ƙaran bindiga...


"Shi kenan, Sir Najeeb kashe mu za su yi. Ga shi sun fara harbin junan su" Farida ta faɗi kamar za ta yi kuka ta kuma matsowa kusa da Najeeb ɗin.
Shi Najeeb ya gane abinda ke faruwa dan ƙaran bindigan ba iri ɗaya bane.

Jin ana shirin buɗe ƙofa. Najeeb ya kalli Farida ya sa yatsunsa biyu a baki alaman ta yi shiru...

Joseph ne ya buɗe ƙofar ɗauke da bindiga,yana shigowa bai gansu ba zai juya kenan aka kwaɗe kan sa daga baya, sai bindigar ta faɗi, yai taga-taga zai faɗi shima Najeeb ya kuma jawoshi ya gwara shi da gini. Ƙiɓar Joseph ya ke kamar wanda aka aiko shi.
Wani police ne da Anas su ka shigo ɗakin lokacin da Farida ta ga Anas ta ce "Alhamdulillah ashe ku ne"

Najeeb kam yana kan Joseph yana ƙiɓar sa sai da Anas da police su ka zo su ka ɗaga shi, dan tuni Joseph ya suma jini na fita ta hanci da baki...

Da ɗingishi ta ke takawa lokacin da su ka fito, komai ya lafa, Anas ya ce mu su an kashe ɗaya daga ciki sauran kuma duk an kamasu. Emeka da yake ogansu ma an halbeshi a cinya.

"Miss Salihu" muryarsa ya doki kunnenta, ta tsaya da tafiya sannan ta juyo a hankali. Kafin ta yi magana ya sa hannu ya ɗauketa cak.
Mamaki ƙarara ya bayyana a fiskarta. Anas da ke gefe ma mamakin ne ya kamashi.

Kai tsaye motar Anas ya nufa da ita sai da ya kwantar da ita a backseat sannan ya dawo gaba ya shiga, Anas ya ja su su ka bar wajen.

Suna cikin tafiya Anas ya ce "asibiti za mu je ko gida"

"Asibiti" Najeeb ya faɗi a hankali....


Ƙarfe goma da rabi su ka baro asibitin bayan an duba ƙafar Farida. Ganin an yi wata hanya da ba ta gidan su ba ya sa ta ce " Ya Anas ka kaini gida ina so na ga Ummi na. Na san tana chan hankalinta ya tashi"

Anas ya ce " ai su Baffan na ki su na gidan su Najeeb"

Ba ta sake cewa komai ba har su ka isa gidan su Najeeb.
Ana jin tsayuwar mota gaba ɗaya aka fito dan dama duk iyalen gidan a matse su ke. Baffa Musa, Yakubu da Ya Faruƙ su ma suna nan suna jiran dawowarsu. Dama tunda abin ya faru su ke sintiri tsakanin gidan su Najeeb. Ummi ta so ta biyosu Baffa Musa ne ya hana...

Najeeb ne ya fara fitowa da sauri ya buɗewa Farida ƙofa ya taimaka ma ta ta fito duk da kuwa yanzu ƙafar ta rage zogi.

Baby ce ta fara zuwa da gudu ta rungume Najeeb kafin sauran su ka ƙaraso.

Baffa Musa abinda bai saba ba yau ya yi. Shima zuwa yai ya rungume Farida yana hamdala. Ita kaɗai ce ɗiyar ɗan uwansa, ita ya ke gani ya tuna da ɗan uwansa.

Daga compound ɗin gidan Baffa Musa ya ce za su wuce gida. Dad ya ce su bari sai da safe tunda dare ya yi. Baffa ya ce " Alhaji ai idan ban kai 'yar nan wa uwarta ba, uwarta za ta iya haɗiyar zuciya. Bari mu tafi kawai"
Musabaha su ka yi da Dad sannan su ka wuce wajen na su Motar. Yakubu ne ya tallafa ma ta har su ka isa wajen motar Baffan...


Idan ka cire yara ƙanana duk sauran kowa idon sa biyu saboda jiran dawowar Farida. Su Baffa ba su iso gida ba sai sha biyu saura na dare.

Su ma ɗin daga bakin gate aka taresu. Farida ta rungume Ummi tana kuka Ummin ma na yi. Da kyar aka raba su.

Wanka da ruwa mai zafi ta yi, ta gasa jikinta sosai, ta jima a banɗakin dan kwana biyu kenan ba wanka. Tana fitowa Ummi ta sa ta a gaba da abinci. Allah na gani bacci ne yanzu a idonta ba abinci ba amma da Ummi ta takura dole ta zauna za ta ci.
Ummi ta ƙarɓa cokali ta fara ba ta abincin a baki. Hakan ya sa Farida ta tuno lokacin da Sir Najeeb ke ba ta abinci, haka kawai sai ta tsinci kan ta da murmushi.





*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣1️⃣0️⃣


Tana tsaye jikin balcony na gidan tana kallon mai yankan flower wanda ke faman gyara flowers ɗin gidan, ya saƙalo hannunsa ta ƙugunta sannan ya manna ma ta kiss a wuya ya ce "do you like it?"

"Gidan yai kyau sosai. Its perfect" ta amsa ma sa

Juyo da ita yai ya ce"This is our home Aysherh"

Murmushi ta yi ta manna ma sa light kiss sannan ta ce "our home is beautiful my love"....


A hankali ya buɗe idonsa wanda su ka ma sa nauyi saboda gajiya, ya rufesu saboda hasken da ya karaɗe ɗakin yaiwa idonsa ƙarfi. Ɗan wasu daƙiƙai ya ɗauka kafin ya sake buɗe idon a karo na biyu.
Lokaci guda kuma mafarkin da yai ya dawo ma sa. Da sauri ya tashi zaune saboda tunowa da yai da abinda ya gani a mafarkin. Agogo ya duba ya ga ƙarfe shaɗaya na safe, kenan ya jima yana barci. Idan ya tuna da kyau to ba maganin bacci ya sha ba jiya. Ya shigo ɗaki, ya taking hot shower ya sanya jallabiya ya gabatar da sallar maghrib da Isha, kaman yana azkar bacci ya tafi da shi. To wa ya maidashi kan gado? Ya janye tunanin ta hanyar tashi ya shiga banɗaki...


Fitowar da zai yi bayan ya shirya cikin ƙananun kaya baƙar shirt da guntun wando baƙi na jeans ya haɗu da Mom tana haurawa sama.

"Son ya jiki?" Ta faɗa a hankali


" lafiya Justice" ya faɗa ba tareda ya kalleta ba.

Mom ta bishi da ido tana haɗiye wani abu mai ɗaci da ya taso ma ta tun daga wuya.


Adama ya samu tana goge-goge a falo.

"Hey ina baby?"

"Sir ta tafi makaranta"

"Dad fa"

"Yana waje"

Fita yai daga falon dan ya san inda zai samu Dad ɗin.

A wajen gazebo da ke garden ya samu Dad, yana zaune yana karatun littafi.

"Come here son" Dad ya faɗi lokacin da Najeeb ke ƙoƙarin zama a ɗaya kujeran.
Zuwa yai ya tsugunna a gaban Dad, Dad ya manna ma sa peck a goshi ya ce "Allah ya ma ka albarka"
Najeeb ya amsa da Amin

"Ya jikin na ka?"

"I'm fine Dad"

"Allah ya ƙara sauƙi"
Dad ya ajiye littafin ya fara bayani

"Ka ga irin abinda na ke gaya ma ka ko. Joseph ya ce korarsa da ka yi shi ya sa shi ɗaukan wannan mummunan mataki a kan ka. Ɗa na, ka dinga danne zuciyarka kana haƙuri da mutane, Allah ya baka ɗaukaka da daraja ne domin ya jarrabaka. Su wanda su ke ƙasa da kai akwai haƙƙin su akan ka kuma Allah zai tambayeka ranar gobe"
Ƙaran wayan Dad ne ya katse hirar ta su. Yana ɗauka ya ce " to muna shigowa"

"Najeeb, Hajiya ce ta zo. Mu shiga ciki"

Ba mu su ya tashi su ka jera da Dad ɗin.

Hajiya Mama da kan ta ta yiwa Najeeb girki ta kawo, wai dole sai ya cinye dan ta san bai ci abinci ba a chan. Haka ta tisa shi a gaba yana cin abinci tana tambayarsa gameda kwana biyun da yai a hannun su Joseph. Mom na gefe tana kallon su, kwaɗayin wannan dama da ta rasa ta ke yi, hira tsakanin uwa da ɗa.
Ko sai yaushe Najeeb zai ba ta dama ta gyara kura-kurenta na baya?...


........................


Da yamma Yakubu ya kawowa Farida wayarta wanda aka samu a gidan da aka tsaresu duk da kuwa an yarda sim ɗin ciki.

"Anas ya ce zai zo ya gaishe ki bayan sallar isha"

"Allah ya kawoshi lafiya" ta faɗi tana cin farfesun kayan cikin da Ummi ta haɗa ma ta...

Tana sallar Isha aka kira wayar Maijiddah. Maijiddah ta duba numbar ta ja tsaki ta ajiye wayar gefe.
Kwana biyu kenan Aneesa matar AbdulWahab tana damunta da kira da texts, ranan da ta fara kira ba irin ɗibar albarkar da ba ta ma ta ba. Gashi ita ba mai iya maida magana bane, haka ta gama zagin ta kashe wayar. Lokacin jimamin rashin Farida ya sa ba ta wani damu da abinda Aneesar ke ma ta ba.

"Matar AbdulWahab ce ta kira ki ko?"

Maijiddah ta gyaɗa kai.

"Ban wayar na bata amsar maganganunta"

Maijiddah ta langwaɓe kai ta ce " Anty dan Allah ki barta. Idan ta gaji za ta bari"

"Hmmm a tarihin rayuwata ba na gani in ƙyale dan haka bani wayar kawai"

Maijiddah ta miƙo wayar dan ba yadda ta iya.
Bugun farko ba a ɗauka ba sai a na biyu.

"Assalamu Alaikum Uwargida ran gida, da fatan kina ta shirye-shiryen zuwan amarya?"

Daga ɓangaren Aneesa ta ce " who's this?" Dan muryan bai yi kama da na Maijiddah ba wacce ranan farko da ta kirata haƙuri ta dinga ba ta.

"Aisha Farida ce, yayar Amarya Hauwa Maijiddah. Na kira ne in gaya mi ki kar ki kuskura ki sake kiran ƙanwata saboda naga alama ƙwaƙwalwar kifi ce a kwanyar ki"

"Ke! ƙaramar karuwa ki kiyayi bakin ki. Ki kuma ja wa ƙanwar ki kunne karta yadda ta shigo gidana"

"Ashe ke Jaka ce, daƙiƙiya, Tinkiya mai kamar Aladu. Har kin isa ki hana Jidda zuwa gidan ki. Idan ba kwartonci ba, mijinki na Lagos kin maƙale a Abuja wai ke sarkin aiki. To tunda ke bakisan yadda ake riƙe miji a tarairayeshi ba, shi ya samu wacce za ta zauna kusa da shi ta kula da shi. Kuma wallahi wallahi ki ja girman ki ki dena kiran ƙanwata ko kuma mazaunanki su yi tsami"

Yadda Farida ke magana da faɗa-faɗa ya ƙara tunzura Aneesa.

"Ke matsa chan jahila mai kama da...."

Farida ba ta bari ta ƙarisa ba ta amsa da cewa " ke ce jahilar ai. Kwartuwa mai bin gindin maza, Allah ya wadai da halin ki. Tir da ke Aneesa mai ƙaton baki. Hooooo ashewo....Hoooo ashewo" (ashewo- karuwa)

Aneesa ta yi saurin kashe wayar saboda zuciyarta da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
Wannan wace irin yarinya ce haka, lallai kuwa Maijiddah za ta ci ubanta idan ta shigo ma ta gida. Sai da ta gama banbamin bala'i sannan ta dubi screen ɗin wayarta ta sa hannu ta shafa lips ɗin ta.
"Ko wa yace ma ta ina da babban baki? Ba dai AbdulWahab ba"...


Farida na jin an kashe wayar ta sa dariya ta ce " ƙaramar 'yar iska, da ki tsaya ma na"
Ta kalli Maijiddah da ta yi zuru-zuru da ido
"Ke kuma ki cigaba da yin shiru-shiru har wannan matar ta sa mi ki ciwon zuciya. Gara ki ɗaure ɗamara dan wannan matar da alama 'yar tasha ce"

"Sannu Malama Farida, expert a ɓangaren rashin mutunci"

"Kai Yakubu ba na son iskanci fa"

"Ki fito Anas na jiran ki a waje"

Gyale kawai ta yafa ta fita bayan ta gayawa Ummi. Gaishe shi ta yi lokacin da ta shiga motar na shi.

" 'yar uwa ya jiki"

"Da sauƙi yaya na"

" ashe ba ƙaramin jin jiki ku ka yi ba. 'Yar uwa ya abin ya faru ne? Najeeb ya ƙi ya bani labari"

Dama abinda ta ke jira kenan ta fara karanto ma sa yadda abin ya faru. Labarin da tun safe ta ke faɗawa 'yan gidan su da maƙota da ke zuwa gaisuwa.
Abu ɗaya ta ƙi faɗa wanda ita kanta duk yawar maganarta ta rasa dalilin ƙin faɗar da ta yi. Ta ƙi faɗin cewa Joseph ya tofa wa Najeeb miyau.

Sai da ta gama ba da labarin Anas ya ba ta wani envelope ya ce "wannan daga Najeeb constructions ne. Kuɗin magani"
ya miƙa ma ta wani envelop ɗin ya ce " wannan kuma Dad ne ya baki, kuma ya ce na gaishe ki da jiki"

"Kai na gode sosai, ka miƙa godiyata wajen Daddy dan Allah. Najeeb constructions kuma sai mun zo mu ku sallama"

"A'a, 'yar uwa sallama kuma. Ba dai aikin za ki bari ba"

"Eh yayana, zan ajiye aiki da ku"

"Gaskiya ban yarda ba. Ai hutu kawai za ki yi na sati zuwa kwana goma ki dawo bakin aikin ki"

"Ya Anas Ummi na ba ta so, ta ce na ajiye aikin"

"No Farida, Najeeb needs you. Ki ba wa Ummi haƙuri ta barki ki dawo dan Allah"


" to bari mu ga ni dai. Na gode Yaya"

Sai da za ta fita daga motar ta ce " Ya Anas ya jikin Sir Najeeb?"
" da sauƙi ƙanwata" ya faɗi yana murmushi...

Ita ɗin ma da ta shiga gida sai ta ji kamar ba za ta iya haƙura da aikin ba. Musamman idan ta tuna bikinta da Rayyan zai iya kaiwa wata shida ma su zuwa...

Washe gari su ka wuce Jos ita da Ummi bayan ta yi welcome back ɗin layinta.


.....................



Yana zaune a kujerar sa yana duba wasu files amma hankalin sa na kan wayar sa, jira ya ke ya ga ko an turo ma sa saƙo. Sai yanzu yai da na sanin ƙin bin Anas da yai ranan. Ko ba komai da ya ganta ya tabbatar lafiyar ta ƙalau.

Duk da ya san ba ta da numbar da ya tura saƙon. Ya ja dogon tsaki ganin har awa ɗaya kenan da tura saƙon na shi amma ba amsa, saboda ka da ta gano shi ma ya sa ya ke rubuta saƙonnin da Hausa. Da ya gama duba files da takardun da ke gaban sa ya tashi ya fita a office ɗin. Ganin kujerarta wayam ba kowa ya sa shi jin wani abu a zuciyar sa, ba dai da gaske barin aiki za ta yi ba. Kai tsaye office ɗin Anas ya wuce wanda ba nisa da na shi office ɗin.

Waya ya samu Anas na yi lokacin da ya shigo, ya samu waje ya zauna yana kallon sa.

"Miss Salihu ta bar aiki ne?" Ya faɗa da harshen ko in kula lokacin da Anas ya gama wayar.

"Ka fara kewar ta ne?" Anas ya amsa ma sa

"Oh please, ka amsa min tambayata ba na son shirme"

Dariya Anas yai sannan ya ce " well, ta ce za ta dawo amma sai Monday"

"Monday is too far"

"Mutumina da alama ka ƙagu ka ganta ko?"

Tashi Najeeb yai ya ce " idan ba ta dawo Monday ɗin ba, ka nemo min wata sakatariyar"

Anas ya ɗan yi dariya ya ce " kamar da gaske"......


...........


Ghana-must-go manya guda biyu ne a gabanta tana faman jera kayan gwanjo da ta saro da za ta kai Kano.


Adiyya wata jikar Nanna ta miƙo ma ta waya wai ana ta kiranta tun ɗazu.
Amsa wayar ta yi ta ranƙwashi kan yarinyar wadda ba za ta wuce shekara takwas zuwa tara ba. "Na hana ki ɗaukan wayata ba kya ji ko. Yanzu jiba yadda kuka cinye min chaji"

"Allah Anty ba ni kaɗai bane har da Mubashshir, shi ne ya ke game, ni kallon hotuna kawai na ke yi" yarinyar ta faɗa tana shafa wajen da Farida ta ranƙwasa.

Duba wayar ta yi ta ga missed call ɗin Maijiddah ne da na sister Munibat sai saƙo guda ɗaya wanda wani number ya turo. Numbar na yawan damunta da saƙo tun lokacin da ta yi welcome back ɗin layinta. Ta buɗe saƙon ta karanta kamar haka.

*fatan ki na lafiya Aysherh? Ina so ki yadda da ƙaddarar da ta same ki, ki ɗauke shi

Please Login or Register in order to submit comment