Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su ka yi. Duk Jummu'a ita ke zama da su Adama su girka jollof rice da naman rago su sa a take away guda dubu a kai wa almajirai da mabuƙata. Kullum sun sa ana mu su sadakan kunu da ƙosai da Masa.
Mom ma ba a barta a baya ba wajen sadaka. Ranan su Adama su ka tayata fitar da kusan duka kayayyakin ta da ke closet, wassu kayan ma ba ta taɓa sakawa ba, ga su kaya ne ma su matuƙar tsada, ta sa aka rabar sadaka. Mutum goma ta biyawa Umurah da lokacin azumi. Shi Daddy kam ba irin sadakan da yai Allah ne kaɗai ya san adadin sa. Ba wai dama ba ya taimako ba ne, amma abinda ya faru ya sa ya ƙara buɗe hanyoyin taimakon al'umma...

A Desk ɗin sa da ya ke zama yai aiki idan yana ɗaki ta zauna. Wani brown envelope ta gani, ta jawo shi. Wayoyin Najeeb ne guda biyu a ciki. Sai yanzu ta tuna cewa ita ɗin ce ta saka a wajen ranan da Anas ya kawo ma ta. Anas ya sa an buɗe wayan domin a duba wassu saƙonni. Ko lokacin da za aje Bank da Court wajen authorizing signature ɗin ta ya zama bayan Najeeb da Anas har da na ta signature ɗin wajen sarrafa abubuwan Kamfani har da wayan nan aka je. Ta tuna sai da ta yi rantsuwa a kotu sannan aka gama haɗa komai, abin tausayin ma maimakon signature ɗin Najeeb dole thumb print na sa aka sa.
Ranan da Anas ya kawo wayan tunda ta ajiye su a kan table ɗin ba ta sake bin kan su ba.

Ta ɗauki babban wayan ta kunna. Hoton sa ne a screen ɗin duk da ma screen ɗin ya ɗan tsatstsage. Ta ƙurawa hoton sa ido, ta sa hannu tana shafa kyakykyawan fiskar sa. Ta shiga gallery tana kallon hotuna wanda yawanci hotunan zane-zane ne, sai wani folder wanda hotunan Najdah ne da hotunan sa wanda su ka ɗauka da Anas wassu kuma da Daddy. Allah sarki ya yi hoto da yawancin 'yan uwan sa amma ba hoton Mom ko guda ɗaya a wayan da ta gama ta koma kan text messages ta ga duk yawanci alerts ne sai saƙonni na ma'aikata ko clients.
Ɗaya wayan ta kunna, wannan kam da ta shiga gallery ɗin hotuna biyar kacal ta gani aciki. Hoton farko na Mom ne tana budurwa kaman ma ranan aure ne dan ta sha ado na gwalagwalai da dimond ga shi kayan da ta sa wani kaman bridal dress ne kalar pink. Sai ɗaya hoton kuma Mom ne da wani ɗan yaro a gaban cake. Ta zooming hoton sosai sai ta ga a jikin cake ɗin an rubuta *Najeeb is one*. Dariya ta fara tana ganin yadda Najeeb ya ke so cute har da murmushin sa a hoton.
"Ayya! Miji na yana ɗan yaro"

Ta jima tana kallon hoton kafin ta tura zuwa hoto na gaba. Wannan hoton family picture ne kaman a Birthday ɗin Najma ne lokacin tana shekara shashida. Mom, Daddy, Najma, Najeeb da kuma wata budurwa wanda ba ta gane ko waye ba ce. Hoto na huɗu ma na wancan budurwan ce, tana murmushi ta sa graduation gown ta ɗaga hulan sama. Cikin ranta ta ce kowaye ce wannan tana da muhimmanci a rayuwan Najeeb, cikin ran ta ta ke tunanin ko budurwan nan babban yayar su Najeeb ɗin ce? To amma kuma Anas ya ce 'ya'yan Daddy uku ne. Hoto na biyar da ta gani sai da ta miƙe tsaye. Ƙwaƙwalwanta ne ya shiga tunani, jijiyoyin jikinta suka fara guje-gujen kai saƙo domin su taimakawa ƙwaƙwalwar ta yi bincike cikin gaggawa.

"Na tuna, Wallahi na tuna" ta faɗa da ƙarfin ta...

Watarana sun fita supervision aiki wani waje. Tana gefen Najeeb yana magana da wassu sai ga wani mai saida cucumber a wheelbarrow. Wassu ma'aikata su ka nufe shi su na siya. Yadda mai cucumber ke yanka ta yana zuba yajin ƙuli sai ta ji yawun ta ya tsinke.

"Sir Najeeb ina zuwa" ta faɗa tana barin wajen da sauri. Zuwa ta yi aka yanka ma ta cucumber ta ɗari, ga albasa da aka yanka siri-siri da shi abin gwanin sha'awa. Tun a wajen ma ta ke ta haɗiyan miyau. Ta ƙarɓi ledan ta bi bayan Najeeb da ɗan sauri-saurin ta saboda ya nufi wajen da motar sa ta ke. Tana shiga motar ta buɗe ledar, ƙanshin albasa da ƙarago ya cika motar. Maimakon ya tada motar sai ya tsaya yana kallon ta yadda ta ke sa hannu tana cin cucumber.
"Kai! yajin nan ba ƙaramin maggie ya ji ba" ta juyo ta kalli Najeeb da ya zuba ma ta ido.
"Sir Najeeb za ka ci ne?"

"Miss Salihu..." sai kuma yai shiru ya tada motar

"Sir Najeeb ka san ba na iya juran yunwa, ga shi tun ɗazu mu ke ta yawo cikin rana"

Bai kulata ba ya maida hankalin sa ga tuƙi da ya ke yi.

"Sir Najeeb Allah ka ci, kasan ance maza su dinga cin cucumber saboda yana ƙara mu su ruwa" ta yi saurin riƙe bakin ta jin abinda bakin ya riga ya faɗa

Ɗan juyowa da yai ya kalleta ya sa ta ce "Sir Najeeb ka ji mi na ce ne?"

"Wani irin ruwa?" Ya faɗa ba tareda ya kalleta ba.

"Nima ban sani ba, kai namiji ne ai ka san irin ruwan ai"

"Ke kuma mace da ki ke ci mi zai ƙara mi ki?" Ya faɗa yana kallon ta.

Basar da zancen ta yi ta ce "tunda ba za ka ci ba shikenan"

Wajen traffic light da su ka tsaya ta cigaba da cin abinta. Hoton da ya ɗauka daidai ta kai cucumber baki ne.

Rungume wayan ta yi tana dariya. Wani daɗi takeji a duk ilahirin jikin ta, rabonda ta ji daɗi haka tun ranan da su ka ci gasa. Kai ya ma fi. Hoton ta a wayan Najeeb, duk da ma ta san ya ɗau hoton ne dan ya dinga dariya saboda ga bakinta cike da abu kuma ga shi ta kai hannu tana son ƙara cusa wani cucumber.

"I love you Najeeb, I love you" yanzu kam ta yadda ko ba so bane to Najeeb yana jin wani abu gameda ita...

Wajen message ta shiga tana duba saƙonnin wayan wanda ba su da yawa kaman ɗaya wayar.
Text ɗin da ta ci karo da shi an tura wa wani number da aka saving da *Aysherh* ne ya tsaya ma ta a rai. Duka texts ɗin sai da ta bisu ta karancesu. Ta gane text ɗin amma kanta ne ya ɗaure. Numban Ayshern ta duba wanda ya sa numfashin ta ya tafi hucin gadi na 'yan daƙiƙai.

" N-J, Sir Najeeb shi ne N-J" ta faɗa tana dafa ƙirji.
Sai yanzu ta gane shirmenta na baya. Tana ta neman ma su suna da ya fara da N a kamfani bayan ga mai Kamfanin nan da ke da sunan NJ
"N-J, Najeeb Jibo" ta furta tana dariya kaman wata zararriya.

Its true kenan abinda Anas ke faɗa. Najeeb has feelings for her. Zama ta yi tana tuno abubuwan da su ka faru tsakanin su tun daga farkon fara aikin ta da shi har ƙarshen haɗuwar su. Duk wani abu da zai yi hinting feelings ɗin Najeeb sai da ta zaƙulo shi...

Tana cikin mota ma sai murmushi ta ke wani lokaci kuma sai ta yi dariya. Hatta Dreban ta Abdullahi sai da ya tsargu ko Madam ɗin na sa ƙalau ta ke yau ɗin.

"Hajiya amma dai lafiya?"

"Lafiya Malam Abdullahi" ta amsa tana sake duba hoton da Najeeb ya ɗauketa.

Ba su yi nisa da gida ba Daddy ya kirata akan ta zo gidan Hajiya Mama. Ta so ta ƙarasa asibiti ta ga mijinta ko da na minti ɗaya ne amma dole ta bari ta gama da komai dan ƙilan idan ta je wajen sa ba za ta iya barin gefen sa ba yau.
Cewa ta yi Abdullahi ya kai ta gidan Hajia Mama...


Ta san Hajia Mama ba lafiya tun kwanaki to amma kusan sati kenan da aka sallamota daga asibiti. Rabonta da 'yar tsohuwan ma kusan kwana takwas, tun tana asibiti rabon ta da ita.

Gaskiya 'Yar tsohuwa na jin jiki dan yadda ta ganta ba ƙaramin bushewa ta yi ba. Tana kwance akan gado su Mom, Daddy, Uncle Sulaiman da Hajia Fatima su na kewaye da ita.

Har ƙasa ta tsugunna ta gaida su, kafin Daddy ya ce "Mama ga Aishatun na ki ta zo"

Hajia Mama ta ɗan miƙa hannu tana yiwa Farida alamar ta zo. Farida ta ƙaraso ta tsugunna a bakin gadon tana riƙe hannun Hajia Maman.

"Aishatu ce ko?"

Hajia Fatima ta ce "e ita ce, ba kin ce a kira mi ki matar Najeeb ba"


"Najeebullahin ya tashi ne?"

Farida da idon ta ya ciko da hawaye ta ce "zai farfaɗo Insha Allahu Hajia"

Hajia Mama ta ɗan yi murmushi, ta san Allah bai bata haihuwa ba amma ya bata 'ya'ya da jikokin da za su tuna da ita bayan rai yai halin sa.

Akwai wani awarwaro kaman bangle na zallan azurfa da ke hannun Hajia Mama. Ko su Daddy da shi su ka tashi su ka gan ta. Ba su taɓa gani ta cireshi ba.

Hajia Mama ta sa hannunta ta cire awarwaron azurfan ta miƙawa Farida.
"Mutane dayawa sun nemi na bar mu su wannan awarwaron amma na ƙi, kin san miyasa na baki?"

Farida ta girgiza hawaye na zubowa a idon ta.

"Na yiwa Najeebullahi alƙawarin zan bawa matar sa awarwaron nan..."

Tari ne ya ƙwace ma ta. Ta jima tana yi kafin ta cigaba.

"Kyautar budurci ne, tundaga ran da Alhaji ya sa mi ni a hannuna ban taɓa cire shi ba sai yau. Ki riƙe shi da daraja"

"Insha Allah Hajia" ta faɗa tana sa awarwaron a hannun ta.

"Allah Sarki Najeebu na. Allah ya tashe ka"

Kowa a wajen sai hawaye.

Mom ta taso ta durƙusa gefen Farida da ke sheshsheƙar kuka.

"Hajiya" Mom ta faɗa cikin raunatacciyar murya

"Nabilatu ce"

Mom ta gyaɗa kai.

"Ki yafe min dan Allah. Najeeb ya yi gaskiya ni ba uwa ta gari ba ce, ranan da Aisha za ta rasu ta kira ni sau biyar, kuma daga jin yadda take nishi na san tana jin jiki amma kishi ya rufe min ido ban je na taimaketa ba, ban kuma kira an je an taimaketa ba har ta haihu ita kaɗai ta rasu ba kowa a wajen ta. Ki yafemin"

"Allah Sarki Najeebu ashe dai dalilin da ya sa ya ke gudun ki kenan. Na yafe miki, ai dama sababin mutuwar Aisha rubutacce ne tun kafin ta zo duniya. Allah ya yafe mu gaba ɗaya. Na yafe wa kowa"


..................

Duk wani ɗokin zuwa asibiti da ta ke sai ta ji ya fita a ranta. Tana so ta tsaya da tsohuwar nan wanda ta ke cike da tarin barkwanci.
Ranan ba ta bar gidan ba sai taran dare. Da ta je ma kuka ta dinga yiwa Najeeb tana nuna ma sa awarwaron da Hajia Mama ta bata...

Da asuba bayan ta yi sallah ta yi azkar ta ɗau alƙur'ani ta zo saitin kunnen Najeeb tana karanta ma sa kamar yadda ta saba. Da ke asabar ne ba za ta je aiki ba. Kusan ƙarfe shida da rabi sai ga kiran Mom akan Allah ya yiwa Hajia Mama rasuwa tsakar daren jiya, tun daga wajen ta fara hawaye...


Tareda ita aka yi karɓan gaisuwa har na kwana uku. Cikin kwanaki ukun nan sau ɗaya ta ke zuwa duba Najeeb...

7days later

Daren ranan jummu'a tana zaune akan kujera tana karatun ƙur'ani bacci ya sace ta. Tana bacci ta yi mafarki Najeeb ya farka yana kiran sunan ta. Da murmushi ta buɗe ido lokacin da ta farka. Haka kawai sai ta tsinci kan ta da zuwa dubashi ko dai da gaske mafarkin ta zai zama gaskiya.
Ƙura ma sa ido ta yi, kaman a mafarkin sai ta ga gashin idon sa yana ɗan rawa, chan kuma sai idon ya buɗe, ido ta zaro ganin idon sa ya buɗe. Sake rufe idon yai ya sake buɗewa a karo na biyu a karo na uku kam da ya buɗe bai sake rufewa ba.

Farida da ta yi suman tsaye na ɗan daƙiƙai ka sa yarda da abinda idon ta ga gani ta yi ta fara murza idon ko dai har yanzu bacci ne a idon ta. Ganin idon sa a buɗe ta mari kumatun ta da ƙarfi dan ta tabbatar dai ba mafarki ta ke ba. Bakin sa ta ga yana motsawa kamar zai yi magana amma bakin ya ma sa nauyi. A hankali ta ƙarasa wajen sa hannun ta na rawa ta kai yatsar ta kaman za ta sa a idon sa sai ta ga ya fara ƙyafƙyafta idon.

"Sir Naj..." maganar bai ƙarasa fitowa ba ta faɗi wajen a sume...



*Team Najeeb ku sha rawan shoki wannan page na ku ne*





*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣3️⃣9️⃣





Yana son ɗaga hannun sa amma hannun ya mai nauyi banda yatsun sa da su ke motsi ya kasa ɗaga hannun sama. Da farko baƙi ya ke gani daga baya kuma ya ci karo da idon mutum. Ba zai iya cewa ya san mai idon ba hakanan kuma ji ya ke kaman ya jima yana kallon mai idon. Ƙaran na'ura da kuma abubuwan da ya ga an jona ma sa a ƙirji ya tabbatar ma sa a asibiti ya ke. Ƙoƙarin tuno dalilin da zai kawo shi asibiti ya ke amma ya kasa. A hankali ya fara ƙoƙarin tursasa ma ƙwaƙwalwar sa domin ta gano abinda ya kawo shi asibiti. Yana so yai magana amma ya kasa, haka ya cigaba da kallon sama still yana ƙoƙarin gano miya faru da shi da kuma inda ya ke.

Tun ƙarfe huɗu na dare sai ƙarfe biyar da kwata ta farfaɗo. Initially ƙwaƙwalwarta bai tuno ma ta miya faru ba, amma cikin rabin sa'a da ta tuno abinda ta gani sai ta yi wuff ta tashi.
Har lokacin idon sa a buɗe ya ke.
"Da gaske Sir Najeeb ka farfaɗo?" Ta faɗa tana shafa fiskar sa.
Da yana da bakin magana da zai tambayi dalilin taɓa shi da ta ke.
Dariya ta ke, murmushi da kuma kuka duk a haɗe. Ta jima tana kissing kumatun sa duka biyu kafin daga bisani ta ankara ko Sujudish shukri ba ta yi ba.
Ta gyara ɗaurin ɗankwalin ta sannan ta yi kabbara ta yi sujjada. Bayan ta ɗago da gudu ta je wajen jakarta ta fito da waya, ba za ta iya barin ɗakin nan ba. Idan ta fita zai iya rufe idon sa ya ƙi buɗewa.
Numban Daddy ne a kusa dan haka shi ta kira, har wayan ya katse ba a ɗauka ba. Ba ta yi ƙoƙarin sake kira ba sai ta kira numban Mom. Sai da ta kusa yankewa kafin aka ɗauka.

"Hello Mom ya tashi, ya tashi mom. Idon sa a buɗe har yanzu, Mom ku zo ya tashi" wassu maganganun ma ba ta san ta yi su ba dan abin na ta har da shirme.

"Najeeb ya buɗe ido?" Mom ta tambaya da mamaki

"Yes Mom wallahi idon sa a buɗe ya ke har yanzu"

"Muna zuwa yanzu ki kira likita" har za ta ajiye wayan sai ta kuma cewa "Aisha dan Allah ki turomin hoton ɗana na gan shi"

"Yanzu ma kuwa Mom"

Tana katse kiran ta shiga camera ta fara video ɗin Najeeb.
Shi kan kallon ikon Allah kawai ya ke yi yana ƙyafta ido. Bai san me wannan matar ke yi ba, ihun da ta ke ma ya sa bai gane maganganun da ta ke faɗa.

38sec video ta turawa Mom wanda ta ke saukowa daga stairs. A ƙasa ta haɗu da Daddy daya dawo daga masallaci.

"He's awake, our son is awake" ta faɗa tana fashewa da kuka.
Karɓan wayar da ta ke nuna ma sa yai ya kunna video ɗin, and there it is, idon ɗan sa Najeeb a buɗe har yana ƙyafta ido.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah" ya faɗa yana mai sujudi. Mom ma ganin haka ita ma ta bi shi ta yi sujjadar...

Tana turawa Mom video ta fara kiran numbar Dr Sadiq da ke shima na masallaci bai ɗauka ba, sai ta kira Dr Johnson, shi kam ya ɗauka amma ya sanar ma ta baya asibitin ta kisa Dr Usama. Duk ma su kula da Najeeb tun daga doctors zuwa nurse tana da numbobin su. Hatta cleaner da ke zuwa gyara ɗakin musamman idan bata nan tana da numban su...

Kusan minti shida sai ga Dr Usama ya shigo.

"Doctor ka gani ko, ka gani idon sa a buɗe ko?"

Wanni na'ura ya ɗauko mai kaman torchlight ya fara haska idon Najeeb da shi. Farida na gefe tana sauke numfashi.
Duk wani response na ido Najeeb ya yi. Ya ci first step a cikin glasglow coma scale da ake yiwa wanda su ka farfaɗo daga coma.

"Ka na jina?, are you hearing me?" Dr Usama ya faɗa

Najeeb sai motsi ya ke da baki amma maganar ta ƙi fitowa.

"Idan kana jina ka motsa hannun ka" ya faɗa yana kallon hannun.
Najeeb ya fara motsa hannun sa a hankali.

"Alhamdulillah" Dr Usama ya faɗa.

"Dr Usama ya baya magana?"

"Malama Aisha kenan watanni fa yai a kwance ba magana ba motsi, a hankali komai zai dawo dai-dai. Alhamdulillah ma tunda har ya fahimci mai na faɗa"

"Allah ya baka lafiya miji na" ta faɗa tana goge hawaye.
Ƙarfe shida ta gota kafin su Daddy su ka iso.

Har lokacin Dr Usama na wajen tareda Dr Wunmi. Duk abinda su ke a kan idon Farida. Ta ƙi matsawa ko nan da chan.

Daddy dai ya yi ta maza bai yi kuka ba amma Mom kam kuka ta fara ganin yadda ake Ƙoƙarin juya kan ɗan ta saboda wuyan da ya riƙe. Ƙwanciya waje ɗaya tsawon watanni ba wasa ba...

Su ukun suna tsaye a kansa sun ƙura ma sa ido, yadda su ke kallon sa ka ce jaririn yaro ne sabon haihuwa.
Ƙarfe takwas aka ce za'a ma sa Computerize Tomography Scan (CT-scan)
saboda a gano ko akwai matsala a ƙwaƙwalwar. Najeeb ma idon ya zuba mu su. Daga ya kalli Daddy sai ya kalli Mom da ke hawaye sai ya kalli Farida da ta kasa rufe baki.

Yanda ya ke jan numfashi ma ka san a wahale ya ke yi.
Duk cikin su ba wanda ya matsa daga gefen sa har aka zo aka fita da shi. Sai da aka tafi da shi tukunna Daddy ya kira Najdah ya faɗa ma ta sannan ya kira ƙanin sa...

Kafin a gama yi ma sa komai 'yan uwa sun cika wajen. A kwance aka turo shi aka dawo da shi ɗakin. Kowa sai tausayi yadda ya ke abin tausayi. Ga baki amma ba magana.
Likitan ne ya kira su gefe yana briefing na su akan abubuwan da za su yiwa Najeeb saboda taimakon sa har ya warware. Kafin result ɗin scan ɗin sa ya fito kar a dinga hayaniya a wajensa kuma mutanen da su ka fi kusa da shi ne kaɗai za su tsaya kusa da shi dan idan yana ganin baƙin fuska zai confusing ɗin sa...

Kwana biyu kafin aka fara ɗaura Najeeb akan wheel chair, har lokacin baya magana sai dai wani lokaci idan likitoci na tambayar sa yana gyaɗa mu su kai tunda kan ya fara motsawa yanzu. Da ke an hana hayaniya, banda wanda su ke kusa da shi ba wanda ya ke zuwa wajen sa.
Farida kam duk da yanayin da ya ke ciki na rashin magana da rashin iya motsa jiki tafi kowa farin ciki saboda yanzu idon Najeeb a buɗe su ke, zai kalleta za ta kalle shi.
A rana na biyar ya fara iya ɗaga hannun sa har ana bashi abu yana iya riƙewa kuma har lokacin ba magana.

Bayan CT scan da aka ma sa sai da aka kuma yin MRI wanda aka tabbatar mu su Najeeb yana da severe traumatic brain injury. A yadda su ka mu su bayani Najeeb zai jima kafin ya iya yin komai da kan sa hakanan kuma zai iya manta wasu abubuwan gaba ɗaya, wasu abubuwan kuma sai a hankali zai dinga tuno su.
Farida kam ta dena zuwa office, ko da abu ya taso sai dai Anas ya kawo ma ta ta yi cike-ciken da za ta yi a asibitin. Yanzu kam ita da Mom su ke kwana da shi. Har gara itama ta dena kuka yanzu, amma Mom idan ta ga ana ma sa neuropsychological assessment ko excercise sai abin ya dinga sa ta kuka. Hatta juya kai sai da aka koya ma sa.
In every theraphy section da aka yi ma sa Mom da Farida su na manne da shi. A kwana na sha uku aka fara koya ma sa tsayuwa. Sai a bashi abu ya dafa ya tsaya idan ya daɗe sai a zaunar da shi kafin a kuma ɗaga shi a haka ake yi har sai an ga ya gaji kafin a bar shi haka nan.

Ranan da aka fara bashi abinci, amai ya dinga kwarawa ƙarshe jikin sa ya fara jijjiga da ƙyar aka samu jikin sa ya dawo normal. Sai da ya kwana biyu ana bashi maganin da zai sa shi iya cin abinci kafin da ya ci bai amayar ba. Mom ce ke bashi abincin amma yana ci kaman wani ɗan koyo.

A rana na goma sha tara ya fara magana. Mom na sallah ita kuma Farida na zaune a kujera tana karanta ma sa labari taji kaman magana. Maganar ta fito kaman mai koyon magana ko na ce irin maganar wawaye.
"Yuu a yuu?"

Ta yi saurin ajiye littafin ta kai kunnen ta saitin bakin sa dan ta ji da gaske Maganar yai.

Maganar ta sake fitowa kaman ta da. Da farko ba ta gane me ya ce ba sai a na biyu da ya maimaita ta gane cewa "who are you" ya ce.
Dam ta ji ƙirjin ta ya buga.
"Sir Najeeb ba ka gane ni ba?, Aisha Farida, Miss Salihun ka"

Mom ta dafa kafaɗarta ta ce "Aisha ki kwantar da hankalin ki, kin ji dai mi likita ya ce" sai a lokacin ta ji zuciyarta ya yi sanyi.

"Whhhhere...Whhha" sai yai shiru saboda maganar da ta maƙale ma sa.

Mom ta fara shafa kan sa tana cewa " its ok son, a hankali maganan zai fita"

Da therapist ɗin da ya ke ma sa rehabilitaion theraphy section ya zo su ka gaya ma sa ya yi magana. Sai ya fara ma sa wassu tambayoyi, wassu ya amsa da ƙyar wassu kuma shiru yai.

Tambayar farko sunan sa ya tambaya. Bawan Allah Najeeb kam da ƙyar ya iya furta "YaaJeeb" Najeeb ɗin ya ke son faɗa amma saboda bakin sa da be koma dai-dai ba maimakon N to Y ne ta fito.

A kwana na ashirin da shida ya fara gwada tafiya da taimakon sanduna biyu. Yanzu maganan sa ta ɗan fara kyau ba kaman ranan da ya fara magana ba...

Fiskar Daddy Dr Kenneth wanda ya ke shi ne rehabilitation therapist ɗin sa ya nuna ya tambaya ko ya gane shi.

"Dad" ya faɗa a hankali.

Ya nuna Mom ya tambayeshi, ya jima yana kallon ta kafin ya ce "Mom"
Hawaye da Mom ke ƙoƙarin ɓoyewa ne su ka fara zubowa. Shekara nawa rabon da Najeeb ya kira ta da wannan sunan.
Najdah aka nuna ita ma ya furta "baby"
Ƙirjin Farida bugawa ya ke da ƙarfi-ƙarfi yadda ka san zuciyar ta ne zai fito.

A karo na uku ya sake tambayar shi ko ya san Farida amma bai yi magana ba. Najma ya nuna ita ma ya kira sunan ta Najma.

Wannan karon hawayen da Farida ke ɓoyewa kan su ke zirya a idon ta.
Najeeb ya zuba ma ta ido yana son gane a ina ya san ta amma ya kasa, kuma idon na ta ya ma sa kama da idon da ya ke yawan gani cikin baccin sa.

Hannu ya ɗaga ya nuna Farida da yatsa ya ce "who is she?"






*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣4️⃣0️⃣




*jiya na ga comments ɗin ku na kuma sha dariya. Princess Salma shugaban 'yan team Farida, ina mai ban haƙuri😀. No brain injury is the same haka healing process ɗin ma ba ɗaya bane. Normally waɗanda su ka farfaɗo daga coma su na shiga wani yanayi da ake cewa traumatic brain injury. Ya danganta idan aka gwada mutum a samu ko mild ne ko acute ko kuma severe. Ko da wanda aka yiwa induced coma ba sa farfaɗowa a take su dawo normal. Wassu idan su ka farfaɗo manta komai su ke tundaga magana zuwa tafiya zuwa duk wani abu

Please Login or Register in order to submit comment