Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kakanta ne.

Yau ya dawo a gajiye ya tarar da Mom ta dawo. Kamar ko yaushe bai kulata ba, ita ne ta ma sa sannu da zuwa amma bai kula ta ba.

"Sabreen asked about you"

Tsayawa yai da tafiya ya juyo ya kalli mahaifiyar ta sa.

"Dont you dare, kar ki ƙara min maganar ta"

Juyawa yai ya wuce ɗakin sa. Yana cikin banɗaki ya kunna shower ruwa na zubo ma sa ya fara tuno rayuwar sa da Sabreen.

Sabreen ta kasance 'yar uwar sa ce, Mahaifinta da Mahaifiyar sa cousins ne. Ita ɗaya ce a wajen iyayen ta kuma mahaifinta yana da mahaukacin kuɗi. Shekara uku ya bata amma tun suna raya su ka shaƙu, duk lokacin da su ka je hutu ƙasar Bahrain to su na tare. Ko lokacin da ya ke fama da matsalar rasuwan Aisha, Sabreen ta kasance macen da ya ke son kasancewa da ita a wannan lokacin. Duk da alaƙarsa da Mom ya ruguje hakan bai hana shaƙuwar sa da Sabreen ya lalace ba. Shaƙuwa ce tun da ga yarinta ta girma ta zama soyayya. Saboda Najeeb Sabreen ta dawo America da zama wanda ya zamo musabbabin komai.

Sabreen tana da kyau kuma tana ji da kan ta. Bayan ta yi karatu a Newyork Film Academy ta nuna sha'awarta na acting film maimakon directing da ta ce za ta yi da farko. Sun riga sun tsara yadda rayuwar su za ta kasance idan sun yi aure. Matsayin mai bada umurni da ta ce za ta zama, Najeeb bai da ja akan haka, kuma tun kafin a sa ranan auren su ta riga ta fara aiki da Hollywood inda ta zama assistant director a wani romantic film da yai tashe a lokacin.

Shirye-shiryen biki ake yi wanda iyayen biyu ke ta sake kuɗi kamar ba su san wahalan neman sa ba. Mom a wannan lokaci tana so ta yi abin gwaninta ko Najeeb zai yafe ma ta amma kash abu bai yiwu ba.

Saura sati biyu a ɗaura aure Najeeb ya koma Bahrain saboda anan za a fara hidima kafin daga baya a wuce Dubai daga Dubai kuma a wuce Italy sannan a ƙare hidiman a Singapore.

Lokacin Najeeb yana ji da kan sa matashi ɗan shekara ashirin da bakwai. Sai dai kash! Saura kwana biyar a ɗaura aure Sabreen ta gudu bayan ta ajiye wasiƙa akan Najeeb yai haƙuri tana son sa amma ba ta shirya aure yanzu ba. Wannan shi ya ƙara birkitar da al'amarin Najeeb. Cikin ƙanƙanin lokaci ya lalace ya koma mara haƙuri mara fara'a kwata- kwata.
Wannan dalilin ne ya sa ya dawo Nigeria ya buɗe kamfanin sa, kuɗin da ya ke da shi da kuma aron kuɗi da ya ƙarɓa a wajen Daddy da su ya haɗa ya tada Najeeb constructions har ta zama abun da ta zama a yanzu. Shekaru bakwai kenan da su ka wuce ana cikin na takwas. Ba abin da ya ƙara ɗasawa Najeeb tsanar Sabreen irin bayan wata takwas da guduwa da ta yi sai ga shi an saki film ɗin da ta yi cikin turawa har tana kissing ɗin wani ƙaton kafiri a cikin film ɗin....


*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣1️⃣8️⃣




Farida na zaune a office wani babban mutum ya shigo office ɗin. Cikin fara'a ta gaida shi saboda irin su ne idan sun zo wajen Najeeb su ke ba ta alkhairi idan za su tafi.

"Barka da zuwa ranka shi daɗe"

"Yawwa beauty, sannu da aiki"

"Wa za ace ya zo?"

"Alhaji Matawalle"

Ta ɗau phone ta kira Najeeb. Yana ɗauka ta gaya ma sa ga Alhaji Matawalle ya zo.
Tana ajiye wayar ta ce " ka shiga"



Sun ɗan gaisa kafin su ka fara tattaunawa kan abinda ya haɗa su. Kusan 30mins suna magana kafin su ka cimma matsaya ɗaya. Najeeb ya ƙarɓi takardun hannun Alhaji Matawalle yana dubawa kafin yai signing.

"Na ce ba, wannan sakatariyar kan nan..." bai ida maganar ba Najeeb ya ɗago ido ya ma sa wani kallo.

Maganar da Alhaji Matawalle ke son faɗa daban amma dole ya haɗiyeta ya buge da cewa

"matar aure ce?"


"Alhaji Matawalle ka zo waje na ne ko wajen sakatariya ta ka zo?"

"Kai Allah yarinyar nan tana da kyau ga fara'a ga...."

Najeeb ya ture takardun hannunsa gefe ya ce " idan ka shirya aiki da ni sai ka dawo"


"Haba Najeeb, wanni irin magana ne wannan?"

"Ka jini da kyau Alhaji Matawalle, now leave"

"Shashashan banza shashashan wofi. Har ni za ka kora a office ɗin ka. Za ka gani"

Alhaji Matawalle ya ɗau takardun ya fita fuuuu...


............

Ranan Jumma'a bayan an dawo daga sallar jumu'ah Najeeb ya kira ta.

"Ki shirya, za mu je Lagos ranan monday"

"Haba yallaɓai ai ko ni buhun gawayi ce iya ka ci. Haka kawai ka ce in shirya mu je Lagos ba tareda na san abinda za muyi ba"

Ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙai kafin ya ce " akwai 2days bid da za'ayi a Lagos and its important for this company"

"Zan tambayi Baffa, idan ya barni to idan bai barni ba shike nan sai ka je kai kaɗai ko ka ɗau wani ku je tare" daga haka ta fita daga office ɗin.

Da dare ta samu Baffa Musa da maganar amma ya ce ba za ta je ba.

"Baffa ni da Oga na ne fa"

"Ogan na ki mijin ki ne da za ki bi shi har Lagos da sunan aiki, ku je kuna kwanan hotel"

"Baffa daɗina da kai gidadanci"

Daƙuwa ya ma ta ya ce "zan ci uban ki Farida"

"Yo Baffa ai kai ne Uban nawa, sai ka ci kan ka, kawai"

Baffa ya taso zai mangareta ta fita daga falon da gudu tana dariya.

"Wannan yarinya wannan yarinya, Allah dai ya shirya min ke"

Baffa bai amince da tafiyar ba sai ranan Lahdi bayan ta ma sa alkawarin a gidan Maijiddah za ta kwana ba a hotel ba.

Ranan monday Najeeb da Farida su ka wuce airport da sassafe, wanda dreban Daddy ne ya kai su, ba su jima ba jirgin su ya lula sama.
Wannan karan ne farkon hawa jirgin Farida, ta dinga surutu tana cewa " dama ance albarkacin Kaza ƙadangare kan sha ruwan kasko, Sir Najeeb na gode Allah ya samu a damshin ku, irin wannan matsayi haka. Wa ya ga Aisha Farida ta shiga jirgi"

As usual bai tanka ma ta ba dan ba ya da abinda zai ce. The girl talks too much...


Kamar yadda aka tsara ɗin su na gama taron na ranan dreban gidan AbdulWahab ya zo ɗaukan ta.

Da za ta tafi ta ce "Sir Najeeb ka zo mu je a rage ma hanya"

Idon sa ne ya ba ta amsa ba baki ba. Ta san ma'anar Kallon na sa dan haka ta ce "Allah ya ba ka haƙuri, sai gobe"...



Gidan Maijiddah ya ma ta kyau ɗakuna shida ne a gidan. Uku a sama uku a ƙasa, ɗakin AbdulWahab Aneesa da kuma yara su ne a sama ita Maijiddah kuma na ta na ƙasa.

Saboda traffic ba su isa da wuri ba duk sai da ta gama gajiya kafin su ka iso.
Maijiddah a ɗakin ta ta sauketa, tana tsananin farin cikin ganin ta.

"Barin kawo miki abinci Anty Farida, kafin nan ki ɗan watsa ruwa, ga banɗakin" ta nuna ma ta ƙofar banɗakin da ke cikin ɗakin.

"O'o su Jiddah Amarya, muma dai za mu zo wajen"

Har Maijiddah ta kai bakin ƙofa ta ji Farida na salati. Ta juyo da sauri "Anty miya faru?"

"Jiddah ashe duk jan kunnen da na miki duk a banza. Dan Allah a ina kika samo wannan bujen kayan"

Maijiddah ta kalli kan ta, pakistan ta saka riga da wando amma wandon irin mai buje ɗin nan ne.

"Anty a cikin kayan lefe na ne"

"Ki na amarya auren wata biyu da 'yan kai, ki ɗauko wannan bujen wandon ki saka, dan Allah dan Annabi. Wallahi ko ni budurwa ba zan sa bujen wando haka ba balle ke matan aure, ga pakistan ma su pencil wanduna ba ki sa ba sai ki sa mai bujen wando. To maza ki cire kuma idan ba wai kin kai an shaping wandon ba kar ki ƙara saka kayan nan"

"Anty na ji, ki shiga ki yi wanka ina zuwa"...


'Yan kwana biyu da Farida ta yi a gidan Maijiddah ta sha faɗa kaman ba gobe, musamman da Jiddan ta ba ta labarin irin kayan da Aneesa ke sawa idan ta zo.

"Ke me ya hanaki sa irin kayan?"

"Anty Farida, a gaban yaran sa sai insa ƙananan kaya 'yan ficil-ficil ɗin nan. Idan uwar su ba ta da kunya ni inada shi"


"Lallai ke jaka ce Jiddah, dama ustazan nan yawancin ku sai a hankali. Wacce ayar ce ta hana ayiwa miji shiga ta ado da jan hankali"

"Anty Farida ba fa mukaɗai ba ne a gidan"

"Maza na shigowa ne?"

"A'a"

"To wallahi ki shirya zama boyi-boyi a gidan nan, very soon idan kin gama amarcin nan za a ajiye ki gefe saboda ƙauyanci da gidadanci da ya mi ki yawa"

Maganganun Farida shi ya ke ta yawo a ƙwaƙwalwarta lokacin da ta ke dudduba ƙananun kayan da Faridan ta ba ta lokacin auren ta.
Ranan laraba su Farida su ka tafi ita kuma Aneesa ta zo ranan Alhamis da dare. Duk cikin weekend ɗin nan a takure ta yi shi. Dama tsarin AbdulWahab ɗin ko na Aneesan ne ma oho, duk lokacin da Aneesa ta zo to yana ɗakinta har sai ta tafi, ita kuma sauran ranakun na ta ne.

Yau da safe Aneesa za ta koma Abuja. For once a rayuwarta tana so ta cire kunya da tsoro.

Ta tuno faɗan Farida lokacin da ta ce kunyan saka kayan ta ke ji.
"Shegiya kunya ya ƙare a abinda kukeyi da dare. Miye bai ganiba ajikin na ki da za ki dinga ɓoye ma sa"

Ta ɗauko micro mini skirt na blue denim jeans ta saka, cikin tops ɗin da Faridan ta haɗo da shi ta ɗauki wata fara wanda ta fi kama da vest amma V-neck gareta. Ta tsaya jikin madubi tana kallon kan ta, da ke guntuwa ce sai ƙananun kayan su ka amsheta sosai. Ta tufke gashinta da ta sawa ribbon ta nannaɗe shi kamar doughnut. Idan akwai abu ɗaya da ta san mijinta na so kuma ya ke ja ma sa hankali bai fi gashin ta ba. Dama Farida ta gaya ma ta kowanni namiji akwai abinda ya fi attracting na shi a jikin mace. Wa su ƙirji, wa su hips, wa su ƙafa wa su gashi da sauran su. To itakan ta san dogon gashin ta ne, AbdulWahab ba ya gajiya da shafa gashinta yana sa fiskarsa ciki yana shaƙar ƙanshin sa.
Takalmi mai ƙasan wedges ta saka dan ba ta iya tafiya da heel ba...

Su na cin breakfast a dining ta fito. Alizah ce ta fara hangota ta ce " Wow! Anty you look beautiful"

Ta ɗan yi murmushi ta ce "Thank you dear"

Sai da ta zauna Baby ta ce " i love your hair Anty"

Maijiddah ta yi murmushi, ta sa hannu tana wasa da gashin na ta ba tareda ta yi yunƙurin ɗiban abinci ba.

Normally idan Aneesa na nan ba ta zama ta ci abinci da su amma yau tana so ta rama abinda Aneesan ke ma ta ne.

Shi kam AbdulWahab tunda ya ɗaga ido ya kalleta bai iya saukewa ba. Sandwich da ya riƙe tuntuni shine bai sauke ba kuma bai ci ba. Sai da Aneesa ta yi magana sannan hankalin sa ya dawo jikin sa.

"Sweetheart za ka dropping ɗina a Airport ko?"

" No Anny, zan makara idan na kai ki"

Ta gama gane mijin na tan ya ɗan bircike akan Maijiddan. Ta san mijinta na son ya ga mace ta sa sexy ƙananan kaya, shi ya sa duk lokacin da ta zo ta ke sawa dan hankalin mijinta ya tsaya a kanta, sannan a tunanin ta Maijiddah ba za ta iya saka irin waɗannan kayan ba dan tun day one da ta ganta ta ke ma ta kallon local girl. Sai ga shi kuma yau ta proving na ta wrong.


Nonye ta zo ta tafi da yaran bayan sun karya saboda makaranta da za su je. Su ma su Aneesan sun gama karyawan amma ta ƙi tashi saboda AbdulWahab ya ƙi ya ƙare cin abincin.

"Sweetheart time fa ya tafi"

Ya ɗan yi gyaran murya ya ce "yanzu zan gama. Yau na tashi da muguwar yunwa ne"

"Namiji munafiki" Aneesa ta faɗi a zuciyarta. Ta san dalilin Maijiddah ya sa shi ka sa ƙarasa abincin akan lokaci.
Ala dole ya tashi saboda Aneesa da ta tsaya a kan sa. Tare su ka fita daga gidan amma minti shabiyar kacal sai ga AbdulWahab ya dawo. Maijiddah na kan tattare dining ɗin ta ji an rungumeta ta baya. "Princess yau ba kya so na je office ko?"

" Yaya ni a su wa, ka je Allah ya kiyaye hanya"

"Wasa ki ke yarinya, wani office kuma bayan ban gaisa da gimbiya ta ba" ya ɗauko wayansa ya ma ta hoto kafin nan ya ɗauketa cak su ka shige ɗakin ta wanda shine mafi kusa.


............


Wannan weekend ɗin ta je Jos kuma ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba domin weekend ɗin ƙarshen wata ne, kaso mai tsoka ta ware cikin kuɗin ta ta tafi nemo sexy gwanjuna a kasuwa, tanaɗin biki takeyi tun kafin abin ya matso daf ta rasa lokacin zuwa Jos.

"Kin gaya ma sa kin taɓa aure?" Maganar da ta sa Farida ta ka sa kai lomar tuwon da ta yanko kenan.

"Ba na so a samu matsala kin san 'yan gulma, gara ki gaya ma sa tun kafin ya ji a waje"

"Ummi na ga ban tareba ai"

"Duk da haka, Farida ba na son a samu matsala a bikin ki irin na wancan karan. Gara duk wa ta ƙofa da zai kawo fitina a toshe ta tun kafin lokacin.

Da wannan zance ta koma Kano, zuciyar ta na tsoron abinda Rayyan zai ce idan ya ji wannan ba tu.

Sai da ta kwana biyu tana tunanin yadda za ta faɗa ma sa kafin daga baya ta yanke shawaran komai ta fanjama fanjam.


Tun kafin ya zo dama ta gaya ma sa tana da magana da shi. Dan haka da ya zo hira yau sama-sama su ka gaisa ya ce yana sauraron maganar ta.

"My Ray akwai abinda ya kamata ka sani gameda ni. It will come to you as a shock amma ka yi haƙuri"

"Ina jin ki"

"Na taɓa aure"

Ya zaro ido yana jiran ƙarin bayani.

"Yes, shekaru uku da su ka wuce an ɗaura aurena da Lukman, sai dai ko tarewa ban yi ba aka raba auren saboda matsalar da ta taso"...

Lokacin da ta gama bashi labarin Lukman yai shiru yana nazari daga ba ya ya ce " kin ga ke rabona ne, shi ya sa komai ya wargaje a lokacin"

Ta yi mamakin maganar sa dan ta ɗauka zai yi fushi saboda rashin gaya ma sa da ba ta yi ba da wuri.


*waye Lukman?*....





*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



0️⃣1️⃣9️⃣





Khairat Ilyas Magaji ta taso cikin gata da jin daɗi a gaban iyayen ta. Iyayen ta ita kaɗai su ka haifa wannan ya sa su ka ɗaura dukkan ƙaunan su a kan ta. Mahaifinta da Mahaifiyar ta dukkan su mutanen Kebbi state ne.
Tana ƙare secondary school mahaifinta ya turata karatu ƙasar South Africa inda anan ta haɗu da Lawrence su ka fara soyayya.

Lawrence Schneider asalinsa Bayahuden ƙasar Germany ne amma a South Africa aka haifeshi.

Rashin isashshiyar ilimi na addini,rashin tarbiya mai kyau da kuma son zuciya su suka sa Khairat ta sakamar Lawrence ragamar rayuwarta har ta koma ko Sallah ba ta yi saboda idan Lawrence ya ganta tanayi yana fushi da ita.
Gidan da iyayen ta su ka kama ma ta, ya koma tamkar gidan ta da na Lawrence, domin kusan koyaushe anan ya ke kwana. A wani hutun dogon zango da ta zo Nigeria, lokacin shekararta na uku kenan a makarantar ta fara rashin lafiya. Aka ma ta treating ɗin shi sai kwana biyu kuma zazzaɓin ya sake dawowa. Wannan karan da su ka je asibiti aka ma ta gwajin ciki, sai ga shi result ya fito tana ɗauke da cikin wata uku.
Alhaji Magaji da matar sa ba su shiga tashin hankali ba sai da Khairat ta ce ai cikin na Lawrence ne.

"A Jew! Khairat ba ma Christian ba Jew. Wanda sun fi kowa tsanar musulmai" Alhaji Magaji ya faɗa cikin masifa.

Sun yi ƙoƙarin zubar da cikin aka ce mu su akwai haɗari saboda Khairat ta jima tana shan maganin hana ɗaukan ciki kuma ya sa mahaifarta yai rauni.

Lokacin komawa makaranta yai Alhaji ya hana Khairat komawa. Shi da kan sa ya je har South Africa neman Lawrence. Abin takaici a gidan da ya kamawa Khairat anan ya samu Lawrence yana hutawa da wata baturiyar karuwar sa.

Ko da ya shaidawa Lawrence Khairat na ɗauke da cikin sa dariya yai ya ce "who wants to have a baby with a moslem whore"

Alhaji dan takaici bai san lokacin da ya mari Lawrence ba. Abu kamar wa sa sai ga shi an kama Alhaji Magaji saboda ya mari Lawrence. Kasancewar sa baƙar fata ya sa abun ya kuma sawa kotu ta ɗau tsauri akan al'amarin. A ƙalla Alhaji Magaji sai da yai wata kusan uku a ɗaure kafin aka fitar da shi nan ma bayan ya biya tara wa Lawrence.

Wannan ya ƙunsawa Alhaji da matarsa baƙin ciki. Itama Khairat ɗin tunda ta ji abinda Lawrence yai sai jikin ta yai sanyi.

Duk min lalacewar ɗa dai na ka ne. Haka Khairat ta raini cikin shegen ta a gidan su har lokacin da ta cika watannin haihuwa. Wata rana da tsakar dare ta tashi da naƙuda iyayen ta su ka kaita asibiti. Ta jima tana labour kafin ta haifi ɗa namiji.

Nurse ɗin da ta sanar da su haihuwar Khairat ita ta cikata maganar da cewa Allah ya yiwa Khairat rasuwa.

Bayan an yi bakwai ɗin Khairat Alhaji ya fara shirye-shiryen barin Kebbi saboda gulmace-gulmace da ake yi akan mutuwar Khairat.

Garin Jos Alhaji ya dawo da iyalin sa, inda su ka cigaba da rainon Lukman tamkar ɗan cikin su. Tarbiyan da ba su bawa Khairat ba, shi su ka duƙufa su na ba wa Lukman.

Lukman Ilyas Magaji ya taso cikin tarbiyya mai kyau, ga shi dama yaron mai biyayya ne. Tun yana shekara shahuɗu yai haddar ƙur'ani, yana da ilimi na boko da addini. Alhaji Magaji da Hajia Zainab su ya sani a matsayin iyayen sa har ya girma ya zama ƙwararren Likita.



Wata rana a asibitin Juth inda ya ke aiki aka kawo wata yarinyar cikin uniform mota ya bigeta. Wasu couples ne Mr and Mrs Owulum su ka kawota saboda su ne su ka bigeta da mota.
Yarinyar tun kan a fara duba ƙafarta ta fara ihu tana kuka tana faɗin Allah ya isa.

Lokacin da aka fara stitching kuwa tana kuka tana lissafta abinda Mr Owulum za su kawo.

"Wallahi Kaji goma za ku kawo, na gida biyar na Agric biyar. Kuma wallahi luƙa-luƙa dan ba na son ramammu"

Dr Lukman bai san lokacin da ya fara dariya ba. Ƙarin dariyan ma, Mr Owulum da matar sa ba sa jin Hausa. Ita kuma ta dage sai lissafo abubuwan da za a kawo ta ke yi.

Sai da a ka gama ya kalleta ya ce " Aisha duk lissafin nan fa ba su gane ko ɗaya ba, ba sa jin Hausa."

"Kan Uban chan! To wallahi chicken, 10 big chicken Mr Igbo man"

Lukman mi zai yi ban da dariya. Kafin su tafi da ita sai da Lukman ya kusa fitsari a jiki saboda dariya. Ko da ya je gida sai da ya bawa Mom da Dad labarin Aisha mai Kaji goma.
Washegari ma Mr Owulum ne ya kawota amma wannan karan har da Ummi da Nanna. Anan ya ke tambayar ta ko an kawo ma ta Kajin.

Ummi ta ce "ashe a gaban ka aka yi ko?"

Dr Lukman ya ce "na ga alama Aisha na son kaza"

Da za su tafi ya ce "Aisha Kaji nawa su ka kawo"

"Dan uban su shabiyu, shabiyu su ka kawo"

Dr Lukman yai murmushi.

Duk zuwan da za su yi sai Dr Lukman ya tabbatar shi ya duba ciwon Aisha. Bayan sati biyu da haɗuwar su wata ranan Jummu'a sai ga Dr Lukman a gidan su ya zo gaisheta. A wajen Mr Owulum ya samu
address ɗin ta.
Har cikin gida ya shigo ya gaida Baba da su Nanna da zai tafi Farida ta rakashi har wajen motar sa.
Ya shiga mota ya miƙo ma ta ledoji guda biyu.

"Dr green eyes har da wahala haka to an gode"

Dr green eyes ta ke ce mishi tun ranan da ta fara ganin shi, kasancewa ƙwayar idon sa green ne, wanda ya samo asali daga mahaifinsa Lawrenc.

A hankali Farida da Dr Lukman su ka shaƙu har soyayya ta shiga tsakani. Ko da ta zana WAEC da NECO Lukman ne ya ƙara ma ta ƙarfin gwiwa akan ta ci gaba da karatu. Da ba ta samu university ba ya ƙarfafa ma ta gwiwa akan kar ta zauna haka.

Lokacin da Farida ta ke aji biyu na diploma aka bayar da ita wa Lukman da zimmar tana ƙarewa za su yi aure.

Kowa ya san Alhaji Ilyas Magaji dattijon arziƙi ne, haka nan ɗan sa Lukman shima saurayi ne da aka ma sa shaida mai kyau a ko ina.

Rana ba ta ƙarya Farida ta gama diploma, aka fara shirye-shiryen bikin ta da Lukman.

A Wase za'ayi auren dan haka sati ɗaya kafin ɗaurin aure Farida ta koma chan. Mutanen Kano da Dukku duk sun hallara a wannan biki. Ba wanda ya fi jin daɗi ma kamar Baffa Musa saboda shi bai so har ta kai harka ba tareda an aurar da ita ba. Shi Mutum ne da bai yarda da karatun mace a gidan su ba.

Anyi kamu, anyi walima komai ya tafi lafiya. Ranan Asabat aka ɗaura auren Lukman Ilyas Magaji da Aisha Farida Salihu. Bayan an ɗaura aure ana ɗan gaggaisawa cikin 'yan uwan Alhaji Magaji da su ka zo daga Kebbi, wani ya fara magana da Alhaji Magaji bayan ya tabbatar a kusa da Baffa Musa su ke kuma maganar ta su ba a hankali su ke ba.
"Allah ya jiƙan Khairat, yau da kun ma ta tarbiya kaman yadda ku ka yiwa Lukman da Lukman bai zama ɗan shege ba"

Alhaji Magaji ya haɗe rai yana hararan ɗan uwan na sa wanda su ke 'yan uba.

Cikin rashin fahimta Baffa Musa ya ce " ban gane ba Alhaji Magaji. Wani irin ɗan shege?"

"au ba ku san Lukman ɗan shege ba ne? Lallai! Ai Lukman jikan Alhaji Ilyas ne, wadda 'yar sa ta haifa ma sa shi shege. Ance ma saurayin na ta ma wani bayahuden bature ne" Alhaji Kamalu yai wa Baffa Musa bayani.

Lokaci guda Baffa Musa ya hau faɗa yana masifa, kafin ka ce me wajen ɗaurin aure ya hautsine. Alhaji Magaji ba abin da ya ke sai hawaye.

Lukman na wajen masallaci su na hotuna da abokan sa aka zo ma sa da wannan mummunan labarin. Da farko bai yarda ba sai da ya shiga masallacin ya ga Alhaji Magaji yana hawaye. Shi kuma Alhaji Kamalu yana ƙara zuba bayani kan yadda Alhaji Magaji ya sakalta 'yar sa Khairat har ya kaita ga karuwanci a ƙasar waje.
Lukman dai a take a wajen ya suma.


Amarya Farida tana cikin ƙawayen ta ana hira ana ma ta kwalliya. Sai tsokanarta su ke wai yanzu kam an ɗaura aure ta zama Mrs Lukman Ilyas Magaji.

Wajen ƙarfe sha biyu ta gota kaɗan labarin abinda ke faruwa ya iso mu su gida.

Wassu cikin 'yan uwan su mata su ka fashe da kuka ana ta kururuwa ciki har da Inna Tabawa.
Wannan hayaniya ya sa Farida da ƙawayen ta su ka fito daga ɗaki su na tambayar abin da ke faruwa.

"Wai ashe Lukman ɗan shege ne" wata ta faɗa da ƙarfi.

"Ɗan shege kuma?" Farida ta faɗa cikin rashin fahimta.

"Wallahi, ance uban sa ma kafiri ne. Yanzu haka su Baffa Musa sun ce sai ya sake ki dan ba za ki auri ɗan sheg..." ta tsaya da maganan lokacin da Farida ta yafuto ta tana dukan ta ta ko'ina.
Da ƙyar aka raba Farida da matar nan. Farida sai zage-zage ta ke tana faɗin ita ko Lukman ɗan Alade ne za ta aure shi.

Gidan biki fa sai ya zama tamkar gidan makoki. Zuwa ƙarfe tara na dare kafin su Baffa Musa su ka

Please Login or Register in order to submit comment