Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gindi. Shekararta uku a Najeeb constructions amma ba alamar nasara sai dai ta ƙi haƙura...

Ta gaji da cin abincin canteen kullum sai kashe kuɗi ga abincin a zuba ma ka kamar kana roƙo duk da ma mafi yawancin lokuta Engr Mathew ko Arch Hamza wani cikin abokan Yakubu ke siya ma ta. Ba ma wannan ba abincin ma bai ma ta yadda ta ke so ba.

Ta zuba faten doya da ya ji ganyen alayyaho da kifi a plate. Gaba ɗaya ƙanshi ya baɗe office ɗin, ta na ci tana korawa da zoɓonta mai sanyi a haka Najeeb ya shigo. Bai ma ta magana ba ya shige office ɗin sa, yana shiga ta ji kira. Tsaki ta yi ta ce " yana gani fa abinci na ke ci" haka ta ajiye ta shiga office ɗin sa.


"Miss Salihu. The next time you eat in the office, 10% zan cire a albashin ki. Is that clear?"

"Ok Sir " ta faɗi ta fita tana ƙunƙuni...

.....................

Farida ta zaunar da Baaba Sabuwa ta yi ma ta bayanin abinda ke faruwa tsakanin AbdulWahab da Maijiddah. Da kuma ƙudurin AbdulWahab ɗin na son turo iyayen sa.
Baaba Sabuwa ta ce idan dai da gaske ne za ta sanar da Baffa Musa sai ya basu lokaci.
Farida ta ce " yanzu Baaba Sabuwa ba ki yarda ba kenan?"

"Farida na fi kowa damuwa da rashin auren Maijiddah, sai dai maganar AbdulWahab ɗin ne ta zo kamar almara"

"Addu'arta ne ya ƙarbu. Kin san tunda na zo gidan nan kullum dare Maijiddah sai ta fi awa ɗaya tana sallah tana roƙon Allah ya bata miji. Ko ba ta sallah sai ta tashi ta roƙeshi. To Ubangiji mai jin ƙan bayinsa sai ya kawo ma ta wanda ba ta taɓa tsammani ba. Baaba Sabuwa ki godewa Allah kawai ki cigaba da yi ma ta addu'a"

Cikin satin Alhaji Bello Hassan Kachako da wa su wakilan AbdulWahab su ka zo. Bakin Baffa Musa kasa rufuwa yai, shi ba dan ya gani zahiri ba ko lokacin da Baaba Sabuwa ta gaya ma sa bai gama yarda ba. Su zuwan da su ka yi idan an basu Maijiddah su na so bikin kar ya ɗau lokaci.

Baffa Musa kam zani ne ta tadda muje. Dan haka ya amince da sauri.
Sati na zagayowa aka kawo sadakin Maijiddah, dubu ɗari da hamsin. Wata uku aka sa biki su ka nemi a dawo da shi wata biyu Baffa Musa ya amince. Duk da kuwa bashida kuɗi a ƙasa dan ya gama kashe kuɗi wajen bikin su Salima. Sai dai ba zai bari damar da ya ke nema tun da jimawa ya kuɓuce ma sa ba. Allah na gani ya so a haɗa bikin Maijiddah da Farida sai dai hakan bai yiwu ba. 'Yan uwan Rayyan sun ce Rayyan yana so ya haɗa ginin sa kafin ayi biki...

Wannan babban al'amari ya sa kishiyoyin Baaba Sabuwa kowa yai tsit dan abin ya ba su mamaki, duk cikin yaran da aka aurar ba mai sa'an Maijiddah. A gaba ɗaya yaran ma Yayar Maijiddah wadda ita Maijiddan ta biyo wato Bilkisu ita kaɗai ta auri wanda yai boko sosai kuma ya ke da hali yana aiki a kamfanin insurance, sai gara-gara mijin Kulthum wanda shima ma'aikacin Kamfanin Airtel ne.

Abu kamar mafarki fa yadda su ke tsokanarta da Matar Custom sai ga shi har sadakinta an bayar saura a ɗaura aure kawai.

......................

Tana kwance wayarta ya fara ringing tana ɗagawa ta ga Sir Najeeb. Mi zai sa ya kira a wannan lokaci? Ta dai ɗauki kiran.

"Miss Salihu, i asked you to send me a copy of the proposal before you leave. What happen?"

"Ya Allah! Na manta zan turo ma ka yanzu"...

Yana zaune yana sipping tea ɗin sa ta turo ma sa saƙon. Sai da ya duba ya ga aikin bai yi kyau ba akwai gyararraki. Nan ya sake kiran ta.
Tana amsa waya ya fara faɗa "Miss Salihu what is this? Mi ki ka turomin? Haka na ce ki yi?" Jin ƙorafin yai yawa ya sa ta ce

"Domin kai ƙorafi danna ɗaya, domin neman ƙarin bayani gameda aikin da aka maka danna biyu, domin magana da Aisha Farida kai tsaye danna uku...."

Ba ta gama ba ya kashe wayar.
Farida ta yi tsaki, " shi agidan ma ba za ka huta ba aiki, ya san da ya na yi wannan ɗin. Wallahi ba za ka kasheni da aiki ba"

Najeeb ya cillar da wayar yana cize leɓen sa na ƙasa. He's waiting for the perfect time ya aiwatar da ƙudurinsa, just a perfect time. Yarinyar nan sai ta raina kanta...



*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣8️⃣


Washegari a office Najeeb bai ma ta maganar shaƙiyancin da ta ma sa ba, iya kaci tana nuna ma sa proposal ɗin ya ce ta je ta gyara.

Tana aiki sai ga Sister Munibat ta shigo.

"Sister Farida ya aiki"

"Alhamdulillah"

"Sir Najeeb yana ciki?"

"Eh ki shiga"

Minti biyar sai ga ta ta fito har za ta wuce ta ce " Sister Farida ɗan bani ruwa mai sanyi ma na, fridge ɗin office ɗina ya ɓaci"

Farida ta miƙa ma ta satchet water mai sanyi.

"Na gode sister" har za ta tafi Farida ta ce " yawwa idan kina son zoɓo ko kunun aya, gobe zan fara zuwa da shi"

Sister Munibat ta ɗan yi dariya ta ce " a cafeteria za ki dinga ajiyewa?"

"A'a anan office ɗina, mai so sai ya zo ya siya"

"Toooo, ke da Sir Najeeb kunfi kusa, amma bana tunanin zai amince da haka"

"Sister Munibat ke dai ki sanar da 'yan wajen kun nan kawai"

Sister Munibat tace "Allah ya kawo kasuwa" Farida ta amsa da Amin...


Washe gari Farida ta haɗa zoɓo gora shabiyar da kunun aya gora goma. Tun kan ta shigo ta ɗan bibbiya wajen mutanenta ta sanar da su, wasu a lokacin su ka ƙarɓa dan wa ya ke da garajen zuwa har Office ɗin Sir Najeeb siyan zoɓo...

Tana aiki a computer Najeeb da Anas su ka fito.

" 'yar uwa sannu da aiki ko"

"Na gode Yayana"

Har zai shige ta ce " Ya Anas ga zoɓo fa, harda kunun aya"

" ƙanwata kenan, kina sha'aninki"

"Yaya ai mai neman kuɗi kam kowani ƙofar samu ya gani shiga ya ke"

"Well Hakane, Allah ya kawo kasuwa"

"Na kawo ma ka zoɓo ko kunun?"

"Ki bari anjima yanzu zamu fita wani waje nida mutumunki ne"

Kafin ya gama surutun sa Najeeb kam ya yi gaba...


.....................


Tana tsugunne gaban fridge tana duba sauran zoɓonta wanda na Anas ne da na Sir Najeeb da ta ajiye mu su, yanzu Yakubu ya zo ya ƙarɓi na sa.

"Miss Salihu"

A firgice ta juyo dan ba ƙaramin tsorata ta yi ba.
"Ya Allahu! Sir Najeeb ai sai ka sa hawan jinin mutum ya tashi. You scared the hell out of me"

"To my office, Now"

Yana shigewa ta fara mimicking na sa " Miss Salihu, to my office now nnnnnnaa. Mtsww"


Ta ɗau zoɓo ɗaya wanda yai sanyi sosai ta shiga da shi.
Tana zuwa ta ajiye ma sa akan table ta ce "Sir na san kafi son shan tea ko coffee amma wannan zoɓon one in town ne. Albarkacin haƙƙin maƙotaka za ka dinga samun kyautar goran zoɓo ɗaya"

Tunda ta fara magana ya zuba ma ta ido har sai da ta kai aya. Duk yadda ya ke jin tsanar yarinyar nan wannan quality na ta na rashin tsoro yana impressing na shi. Idan ka cire Anas duk girman Kamfanin nan babu wanda ke iya tsayawa gaban sa ya faɗi magana son ransa sai ita. People fear him, but this skinny girl idonta ƙyam ya ke duk lokacin da ta ke gabansa babu tsoro ko fargaba a tattare da ita.

"Sir ka taɓa zoɓon ka ji, Allah sai ka yi santi"

"Miss Salihu, duk wani rules and regulations na wannan Kamfani yana da muhimmanci. But na ga alama ba ki ɗauke su da daraja ba. You dont wear cooperate clothes, you eat in the office you... you... you and only you Miss Salihu"


"Haba Sir, tun ranan da kace na dena cin abinci a Office fa na dena"

"Oh really, and that yellow thing you ate in the morning yersterday?"

"Kai Sir ya akayi ka gani? Ban karya ba na fito shine na karya a office"

"I see. And this" ya nuna goran zoɓo da ta ajiye"

"Alakoro na kawo ma ka fa. Tunda dai Allah ya haɗamu maƙotaka"

"Look Miss Salihu, get this in to your dumb skull. Office ba wajen ciye-ciye ko kasuwanci bane, you keep on doing it i keep on cutting your salary. Now out of my office"

Ji take kaman ta make shi amma ba hali. Ta juya a hankali tana tafiya.
"Miss Salihu" dama a kufule ta ke ta juyo da sauri ta ce " Sir yanzu kuma mi na yi"

"Take this stupid thing out of my sight"

Ta kalli zoɓon ta kalle shi tace "idan ka ga dama ka wanke bahayarka da shi"

"Wait what?" Ai da sauri ta fice daga office ɗin...


Sana'ar zoɓo da kunun aya kam Farida ba ta fasa ba sai dai ta chanja salo. Duk mai so zai yi booking ne tana zuwa tun kafin ta shiga office za ta bi ta rarraba ta ƙarɓi kuɗinta wani lokaci kuma sai an kusa tashi ta biya ta karɓi kuɗi. Anas na ɗaya daga cikin ma su son zoɓonta kullum sai ya sha gora biyu. Najeeb bai sake ma ta maganar sana'ar da ta ke ba duk da ya san bata dena ba.

Yau wani ƙaton kula ta fito da shi daga keke saboda sana'ar zoɓo da ya ƙarɓe ta. Dan ko gora hamsin ta yi sai ya ƙare.
Tana faman ɗauka sauke da kular Najeeb ya zo wucewa, a lokacin ta sauke ta na ƙoƙarin murza hannunta saboda zafi, ya tsaya yana kallonta. Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Yarinyar nan da garaje ta ke ina ita ina wannan ƙaton abu. Ya wuceta ba tareda ta ganshi ba, yana zuwa bakin ƙofa ya ce da security da ke wajen ya je ya ɗauka ma ta kayan...


Yau ɗan wake ta zo da shi dan haka da su ka je Cafeteria ita da Sister Munibat ta wuce wajen su Anas.

"Yayana ban san ko kanacin ɗanwake ba?"

Anas ya ce " ci kai. Ai duk lokacin da mu ka je gidan Hajiya Mama sai ta sa an yi min"

"To barin zubo ma ka"
Ta je ta zubo ma sa a plate harda dafaffiyar ƙwai akai da ɗan ganyen lettuce da albasa sai ƙamshi ya ke yi.

"Gaskiya na gode sweet sister. Allah ya miki albarka"

Ta yi murmushi ta tafi. Ko kallon inda Najeeb ya ke ba ta yi ba.
Anas ya fara haɗa ɗanwake da shinkafa yana ci yana santi.

"Are you flirting with her?"

Anas ya ɗago da mamaki ya kalli Najeeb.

"Wannan shine dalilin da ya sa yarinyar nan ta ke abinda ta ga dama a office. Because of you"

"Dude are you....are you jealous?"

" im serious Anas stop flirting with her"

Tashi yai ya bar wajen ya bar Anas da baki buɗe.

Idan dai idon sa ya ga dai-dai to tabbas kishi ya gani a idon Najeeb. But why?.... ko dai.....
Ya juya ya kalli Farida da ke ta zuba uwa surutu cikin zuciyar sa ya ce " indai abinda na ke tunani ne to, Farida kin ciri tuta. I wish ke za ki maye gurbin Sabreen a zuciyarsa"...

.....................


Tana ɗaki tana cin abinci taji alert na kuɗi ya shigo ma ta daga wajen aiki. Sai dai tashi ta yi cikin sauri saboda abinda ta gani. Ba abinda aka ce za'a biyata ba kenan, kusan kaso sittin kawai aka biyata cikin albashinta.
Cikin tashin hankali ta fara kiran numbar Najeeb sai dai bai ɗauka ba.

Ta kira numbar Anas shima bai ɗauka ba.
"Lallai ma! Kan Uba. Wallahi ba zai yiwuba na yi uwa ayyukan nan ba dare ba rana ace wannan kuɗin za'a turomin. Ta tashi ta fara shiryawa.

Maijiddah da ta shigo ɗaki ta ce " Anty ina zuwa haka"

"Wajen aiki zan je. Yau Sir Najeeb ya taɓo ni"

"Anty ba yanzu ki ka dawo ba"

"Ke dai bari zamu yi maganar idan na dawo"

A hanya Anas ya kirata akan ta yi haƙuri ɗazu suna meeting ne shiyasa bai ɗau kiran ba.

"Yayana kuna tareda Sir Najeeb ne?"

"Eh tare mu ka yi meeting ɗin amma ni na fito na barshi a office yana ƙarasa wasu ayyuka. Lafiya dai ko?"

"Ba lafiya ba Ya Anas 60% na albashina kawai na gani"

"60% kuma?"

"Eh. Na san Sir Najeeb ne yamin haka, dan haka yau ni da shi, sai ya bani cikaton kuɗina ko yaga bala'i" ta kashe wayar tana huci.

Kamfanin yai tsit saboda an riga an tashi. ID card ta nuna aka bari ta shiga duk da kuwa ma su gadin sun santa. Ba ta wuce ko'ina ba sai office ɗin Sir Najeeb. Ba ya main office ɗin sa dan haka ta je wani ɗaki da ya ke yin ayyukan sa na zane acikin office ɗin. Ta ƙwanƙwasa ƙofar.
Yana tsaka da zane ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Who could it be? Dan ya san Anas ya tafi tuntuni.

Na'urar computer da ke gabansa ya danna nan da nan Farida ta bayyana. Yadda ya ganta ya san maganar albashi ne ya kawota. Wajen da ya ke waje ne da bayan shi sai Anas babu wanda ya ke da access na shiga, work place na shi kenan. Anan ya ke duk wani zane-zanen sa. Wajen zagaye ya ke da glass. Glass ɗin daga ciki za ka ga mutum amma daga waje mutum ba zai ga na ciki ba. Kana shigowa ɗakin idan ba ka da katin buɗe ƙofar glass ɗin to ba tayadda zai buɗu...

Tana tsaye ya buɗe ƙofar ya fito.
"Sir Najeeb ban gane manufarka ba. Me na yi aka cire 40% na albashina?"

Yadda ta ke maganar kamar za ta doke shi.

Bai kulata ba ya je ya zauna a kujerar sa.

"Sir Najeeb i demand an explanation"

"Ofcourse Miss Salihu. Ni na cire 40% na albashinki as a compensation for all your irrational behaviours in this company"

"Sir Najeeb idan ma yaren China ka ke gara ka dena dan ni banjin wannan yare. Ka tura min cikaton kuɗina kawai, abinda na sani kenan"

Murmushin yaƙe yai sannan ya ce " next month ma ki dinga take dokokin kamfani and i'll keep on cutting your salary"

"Cabɗi! Wallahi ba ka isa ba"

Tasowa yai ya nufi kanta ta fara ja da baya.
"Mi za ki yi idan na cire? Yau ma hugging ɗina za ki yi? Go ahead and i'll make sure you get what you are looking for"

Ganin ta kai jikin bango ya sa ta haɗiyi miyau.

"Come on hug me. Na san abinda ki ke so kenan, well yau ba Anas ba yayanki, nobody is here just me and you"

"Idan ma giyan wake ka sha. Wallahi na fika hauka. Kkkka matsa min"

Kallonta ya ke yi yadda take fitar da numfashi da sauri-sauri har yanajin bugun kirjinta.

"Scary bitch..."

Buɗe ƙofar da akayi ya sa yai saurin juyawa to his dismay sai ga Joseph biye dashi kuma wasu zaratan maza guda uku.

"What the hell are you doing here Joseph?"


Bindiga su ka fito da shi Farida ta ƙwalla ƙara ta ɓoye a bayan Najeeb jikinta na rawa tana salati.

"If you comply, nobody gets hurt" a cewar Joseph

Najeeb ya ce "Let the girl go"

"Shut up" ɗaya daga cikin guys ɗin ya daka ma sa tsawa

"Tie them both"

Farida na jin haka ta ƙwalla ƙara ta ƙara ƙanƙame Najeeb....



..........................

A yadda ya tsara sai ƙarshen wata idan Aneesa ta zo Lagos zai ma ta bayanin komai sai dai ko a ina Aneesar ta ji labari?.

Yana zaune a office su na waya da gimbiyarsa, Aneesa ta shigo fuuuu.

"You liar, sai yaushe ka ke son sanar da ni? Bayan an ɗaura aure?. You evil son of a bitch"

"Anny minene haka kuma"

"Munafuki, asirinka ya tonu ai. Wato har sadaki ka kai. To barin gaya maka Abdul wannan auren ba zai taɓa yiwuwaba"

"Aneesa kenan. Dama abinda ya taso da ke daga Abujan kenan. To ki sani aure babu fasawa tunda dama na gaya miki ai"

"Abdul Wallahi ba zai yiwuba. Idan ma wasa ka ke gara ka janye, i will never share you with anyone"

"Ina son ki Aneesa amma duk abinda ya faru ke ki ka jawo. Ba ni da ra'ayin mata biyu sai da ki ka zaɓi aikin ki fiye da ni"

"Wallahi sai dai ka zaɓa ko ni ko ita dan ba zan zauna da kishiya ba"

"Its too late Aneesa. Wata biyar da su ka wuce da na gaya miki saƙon Hajiyata what did you say?"

"Haka za ka ce ko. To mu zuba mu gani and i'm taking my kids with me"

"Tunda daga gidan ku ki ka zo da su ba"

Ficewa ta yi daga office ɗin kamar wata zararriya...


............................

Har ƙarfe tara na dare ba Farida ba dalilinta ga numbarta ba ya shiga. Maijiddah ta je ɗakin su Yakubu lokacin shima ya dawo daga hira kenan zai ci abinci.

"Amarya Amarya, ya akayi?"

"Yaya Yakubu Anty Farida ta kira ka ne?"

" Farida kuma. Ai ni tun da mu ka dawo daga wajen aiki rabona da ita"

"Yaya numbarta ba ya shiga kuma ta ce za ta je Kamfani wajen Oganta"

"Sir Najeeb"

"Eh"

"To barin kira Anas na ji"
Sai da ya sake gwada numbar Farida still baya shiga kafin ya kira Anas.
Anas ya sanar ma sa yadda su ka yi da Farida sannan ya ƙara da cewa shima ya yi ta gwada numbar Najeeb amma ba ta shiga.

Yakubu ya ajiye waya ya kalli Maijiddah ya ce " barin je Kamfani in dubata. Ko tana chan dan numbar Sir Najeeb ma ba ta shiga"...


Anas ne ya riga shi isa Kamfanin, lokacin da Yakubu ya iso a wajen motar Najeeb ya tarar da Anas da wasu securities su na magana.

"An ganta kuwa?" Yakubu ya faɗa a kiɗime

Anas ya girgiza kai ya ce " Yaks i think they have been kidnapped"

"What!"....



*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣9️⃣


"Wayyo Allah Ummi na. Wayyo Ummi naaaaa" abinda ta farka da shi kenan lokacin da ɗaya daga cikin mutanen da su ka sato su ya watsa musu ruwa.

"Shut up" ya daka ma ta tsawa. Nan kuma ta fashe da kuka tana cewa " dan Allah kar ku kashe ni, ni ɗaya ce a wajen Mahaifina kuma ko jika ban haifa ma sa ba"

Tare aka ɗauresu da Najeeb bayansu na gogan na juna sai dai tun da ya farfaɗo baice ƙala ba.

"Sir Najeeb ka ce su bar ni na tafi. Iyayena talakawa ne, ba su da kuɗin da za su basu, yanzu ma Baffa na cikin bashi yake saboda hidimar biki da yai..." saukar mari taji a fiskarta wanda ba shiri ta fashe da wani matsananci kuka.

"Chachachacha, you talk too much abeg"

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi Joseph da sauran su ka shigo.

"Well well well. The Almighty Sir Najeeb, the perfect man. Mr get out of my office" ya sa hannu ya murɗe kunnen Najeeb da ƙarfi.

"I will make sure you suffer before this is over"

"Untie him" ya faɗi yana yiwa Najeeb kallon tsana.

Kunce shi su ka yi ya ce su ma sa tsirara ai Farida na jin haka ta fara bada haƙuri.

Ɗaya daga cikin su wanda ya ke kamar shine Oga ya zuƙa wiwi da ya ke sha ya ce ma sa ɗan uwa ba haka akeyi ba, idan kana so su biya kuɗi to dole 'yan uwan sa su tabbatar yana cikin ƙoshin lafiya.
"Emeka why now?" Joseph ya faɗi cike da takaici

"Bros let me handle it" wanda aka kira da Emeka ya faɗi. Zuwa yai ya cirewa Najeeb takalmansa da agogo yace " so na designer you wear" naushin cikin Najeeb yai wanda sai da Najeeb ya wantsila.
Shi kuwa Joseph zuwa yai ya taka kafar Najeeb. Ba ƙaramin zafi ya ji ba amma haka ya shanye bai nuna ba.
Lokacin da za su tafi Joseph ya tofa wa Najeeb miyau a fiska. Har su ka fita daga ɗakin bai buɗe ido ba saboda tsananin ƙyanƙyamin abinda Joseph ya ma sa.
Ɗankwalin atamfar ta ta ɗan yaga ta zo ta goge ma sa miyau ɗin.
"Wai mi ka yiwa wannan guntun ne? Joseph ko me su ke kiran sa"

Bai buɗe ido ba kuma bai yi magana ba.

"Dalla buɗe idon. Ba na riga na goge miyau ɗin ba"

A hankali ya buɗe rinannun idanunsa ya ɗaura akan na ta. Itama ɗin shi ta ke kallo for some weird reasons sai ta ji ya ba ta tausayi. Wannan fa ɗan gata ne gaba da baya, CEO na babban kamfani amma Joseph ya ma sa wannan walaƙanci.

"Wannan bayan kuɗi da su ke so akwai bita da ƙulli tsakanin ku. Allah ya sa dai kar su kashe mu"

Ta kalli ƙafar da Joseph ya taka yatsun wajen sun yi jaa sun kumbura. Ta kai hannu za ta taɓa ya janye ƙafarsa da sauri.
" kaa! Dan ma zan taimaka ɗin, to ka ci kan ka"
Ta koma chan gefe ta zauna. Yanzu da aka kuncesu ta ɗan ji saƙayau.

"Ni wallahi yunwa na ke ji, ba dan kai ba da yanzu ina gida ina cin abinci. Ni daga mun kai gida lafiya ma ajiye ma ka aiki zan yi. Irin wannan aiki da kasada ba dani ba"

Tana cikin surutu aka buɗe ƙofa, abinci aka kawo mu su, take away guda biyu na shinkafa da satchet water guda biyu. Ko kallon inda abincin ya ke Najeeb bai yi ba. Farida kam jawo abincin ta yi ta fara ci dan Allah na gani ba ta iya juran yunwa. Abincin ba wani yawane da shi ba hakanan nan taste ɗin dai ba laifi da alama daga restaurant su ka ƙarɓo.

"Sir Najeeb ka ci abinci fa, da zafin sa kar yai sanyi"

Tashi yai ya ɗau ruwa ya shiga wani ƙofa da ke cikin ɗakin wanda ya ke tunanin banɗaki ne. Banɗakin ne sai dai gaba ɗaya a ƙazance ya ke da ƙyar ya kama ruwa yai alwala ya fito dan ba ruwa a wajen, famfom baya aiki.

Sai da ta ga ya je gefe ya tada sallah itama ta ankara ba ta yi sallar maghrib da Isha ba, gashi ta shanye ruwanta.
Dole sai taimama ta yi bayan ta leƙa banɗakin ta ga ba ruwa.

Tana zaune ta jingina da bango ta fara gyangyaɗi ƙarshe baccin wahala ya saceta....


..........................

Kafin ƙarfe goma na dare iyalen Alhaji Adam Jibo sun samu mummunan labarin rashin Najeeb da Sakatariyar sa. Abinda ya ɗaure mu su kai har lokacin ba a kira su gameda ransom ba. Bacci kam ƙauracewa iyalen yai bama kamar baby da ta dinga kuka wiwi da ƙyar Mom ta shawo kan ta ta yi shiru.


Gidan Baffa Musa ma dai hankulansu a tashe ya ke. Ba ma kamar Baffa Musa wanda ya ke gani kamar sakacin sa ne ya sa Farida ta faɗa wannan hali. Yadda Baffa ya hana a sanar da Ummi amma hakan bai yiwuba dan kafin yai maganar ma tuni Anty Hanne ta kirata ta sanar ma ta an sace Farida. Hankalin mutanen Jos ya tashi a wannan dare, a daren Ummi ta so ta zo amma Baba da Nanna su ka hanata, su ka ce ba abinda za ta yiwa Farida sai addu'a ta bari idan gari ya washe sai ta je.

Haka aka wayi gari gidajen biyu ba kwanciyar hankali. Ƙarfe tara na safe aka kira Alhaji Adam Jibo bayan an tura ma sa hoton Najeeb da Farida ɗaure. Miliyan hamsin su ke buƙata cikin awa ashirin da huɗu ko kuma su rasa su gaba ɗaya.

Anas ya sanar da Yakubu cewa kidnappers ɗin sun nemi ransom na 50million. Ya kuma kwantar ma su da hankali akan za a kuɓutar da su.

Baffa Musa da Yakubu su ka nufi gidan su Najeeb. Sun samu su Alhaji Adam su na meeting da wasu special police kan al'amarin sai da su ka gama sannan Dad ya saurare su.

"Alhaji dama maganan kuɗin nan ne. Ni dai a wajena idan na shiga na fita za a samu miliyan uku sai dai kaga ko rabin abinda su ke buƙata ba a kai ba"

"Alhaji Musa ka kwantar da hankalinka Insha Allahu komai zai zo da sauƙi. Maganar kuɗi kuma Alhamdulillah an fara arranging na su. Kar ka damu"


.......................


Da safe Emeka ya shigo ɗakin ya fara faɗa harda marin Najeeb wai 'yan uwansa ba sa son shi suna buƙatar 48hrs su haɗa 50million.

"I thought your parents are super rich. They better not play games with me"...

Emeka cousin ɗin Joseph ne, ya jima

Please Login or Register in order to submit comment