Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su ta ke amma ita kaɗai ta san mi ta ke ji...

Washe gari tareda Yakubu su ka je wani classy restaurant da Mr Olabode ya ce su haɗu. Ɗan gefe da su Yakubu ya zauna.

Yadda su Yakubun su ka faɗa hakan ta ke Mr Olabode ya ce ma ta zanen kamfanin su na ɗaya daga cikin wanda ya burge su, sai dai idan tana so sun cinye komai gaba ɗaya to ta yi abinda ake yi.

Kai tsaye ta ce " ba kuɗin da zan bayar"

Mr Olabode yai murmushi ya miƙo hannun sa ya ɗaura akan na ta hannun yana faɗin "who is talking about money, when this heavenly beauty here is everything..."
Saukan mari da ya ji ya sa sauran maganan su ka kafe a bakin sa.

Ba ta tsaya haka ba ta ɗau juice ɗin da ke gaban ta ta watsa a fiskan shege. Ta ɗau jakarta ta fita ta bar Mr Olabode da buɗe baki.
Yakubu na jin ƙaran mari ya kalli wajen da su Farida ke zaune. Tana tashi ya bi bayan ta da sauri.

"Kuɗi ya ce ki bashi ko?"

"Wani kuɗi kuma, kana ganin baƙin kwarto a wajen"

Yakubu ya ce "Allah ya shige ma na gaba amma na karaya"

"Indai har sai mun ba da cin hanci da mu ci gasan nan to na haƙura. Mu koma gida kawai, ma san yadda za mu ɓullowa su Mr Vladimir"...

Yammacin ranan Lukman ya zo duba ta. Ya ji daɗin yadda ya ga ta murmure sosai. Da ya je ma ya samu tana ta masifan abinda Mr Olabode ya ma ta ne. Wai har Mr Olabode mai kaman angulu shi ne zai kalleta ya tsaya yana ma ta maganan banza. Uncle Abubakar ya ce " to ai yadda ƙasar na mu ta koma kenan. Give before taking ake yi"

Farida ta ce "dole ai ba za mu taɓa cigaba ba. Cin hanci da rashawa ya mana katutu"...

Sai da ta rako shi bakin mota sannan ya ce " so, yanzu gobe ba za ku jira ku ji result ɗin ba"

"Dr Lukman kenan, ka na ga bayan abin da na yiwa Mr Olabode za ma a saurare mu balle kuma ace mu mu ka ci gasa"

"You never know Aisha, ai ba shi kaɗai zai judging ba. Dan Allah ki je, ko da ba ku samu ba dai ya nuna kuna da jarumta you stayed till the end"

"Shi kenan" amma da ni na cewa su Yakubu gida za mu wuce gobe"...

Bayan Lukman ya shiga mota ya tafi sai ta ga Najeeb na tsaye ya harɗe hannun sa a ƙirji fiskar sa ba walwala.

"My champ lafiya ka haɗe rai? Ka min murmushi dan Allah"

"Aysherh ba na so, na ce ba na so" daga haka ta dena ganin sa ko na ce ya ɓace ma ta a idon ta...

Washe gari Jumma'a su ka je inda ake taron. Wassu ba su zo ba dan yanayin yadda ka ke jin kanada hope shi zai sa ma ka tsaya tunda dai mutum ɗaya ne zai ci.

Farida na zaune hankalin ta kwance ga Najeeb na gefen ta hannun su sarƙe cikin juna. Sai Yakubu da Hassan da kowannen su ya sha suit kaman a ranan za su yi pitching zanen su.

Mai gabatarwa ya gabatar tareda nuna jinjina ga duk wanɗanda su ka shigar da zanen su haƙiƙa kowannen su ya yi ƙoƙari. Amma akwai wani zane guda ɗaya wanda ya ɗau hankalin mu ba wai dan ya fi na kowa ba sai dan yadda tsarin zanen ya tafi da zamani kuma still its just simple tradional design. Haƙiƙa wanda su ka tsara zanen nan sun yi ƙoƙari. Mafiyawancin lokuta abun da bashida yawan ƙyale-ƙyale shi ke ɗaukan hankali. To mudai wannan zanen ya ɗauki hankalin mu. Harta baturen da ke cikin mu Mr Briston ya yaba da wannan zane matuƙa kuma a karan kan sa ya bada kyauta ta musamman ga wanda su ka yi wannan zane. Kafin na cika ku da surutu za mu kira Mr Briston ya faɗi kamfanin da su ka lashe gasan nan.

Duk yadda Farida ta so daurewa sai da ta dinga jin ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri.

Baturen Mr Briston ya hau stage ya fara bayani da turancin sa da ta ke kama da ta hanci ta ke fita.
Farida ba jin komai ta ke ba dan kunnen ta ya toshe a wannan lokacin.

Firgigit ta yi lokacin da muryan Mr Briston ya doki kunnen ta yana faɗin "we've selected the design presented by Najeeb Constructions company. I here by called on the team leader Mrs Farida Jibo of Najeeb constructions to come..."

Yakubu ne ya dafa kafaɗar Farida yana faɗin Alhamdulillah, 'yar uwa Alhamdulillah.

Ƙwaƙwalwarta ba abinda ke yawo ciki sai 'Najeeb constructions company'

"Farida ki tashi, ki tashi ana kiran ki" muryan Yakubu ya dawo da ita daga nisan kiwon da ta yi.

Sai da ta miƙe tsaye Najeeb da ke wajen ya kalleta ya ce "ni ba na son ƙauyenci, walk with class and elegance Mrs Jibo"

Hannun ta ya kama ya ce mu je na raka ki. Tafiya su ke tana jin kan ta a sama, ga shi sun lashe gasa ga Najeeb a kusa da ita.
Yakubu da Hassan kam kallon yadda 'yar batalikan nan ke tafiya su ke. Tana tafiya kaman wanda ta ke jin tsoron taka ƙasa...

Akwai daɗi fa ka representing mijin ka a wani waje, musamman wajen da ake ganin kaman matan aure ba su da wani daraja da ya wuce su zauna a gida su yi girki.

Yakubu da Hassan kuwa Mr Briston kyautar kuɗi naira dubu ɗari biyu ya basu.

Ba ta taɓa jin daɗin a kirata da Mrs Jibo ba irin yau. Ko ina ta juya sai congratulations Mrs Jibo ake ta faɗi. Su na barin wajen Daddy ta fara kira dan tun jiya da ya kirata ya tambaya ko akwai wani haske, ce ma sa ta yi ita ta haƙura za su dawo gida kawai.
Daddy ya ji farin ciki sosai. Na farko 5% zai dawo hannun Najeeb sannan ga yadda kamfanin za ta sake samun ɗaukaka a ƙasar...

Da dare text ɗin Anas ya shigo
*congratulations, ba ni da bakin magana Farida. Kin ƙara tabbatar min da maganar Najeeb da ya ke yawan gaya min cewa 'duk inda akwai tsoro to babu nasara a wajen' Allah ya dawo da ku lafiya*

Farida ta yi tsaki ta ce daga baya kenan, wai anyi sadaka da bazawara. Haushin sa ta ke ji yanzu ko da ace bai so ta shiga gasan ba amma tunda ta riga ta shiga sai ya sa hannu ya taimaka wajen ganin an yi iya ƙoƙari akan abin. Amma ya bar ta tana ta wahala ita kaɗai.

Ba su dawo ba sai ranan Tuesday saboda sai da su ka tsaya ranan monday aka yi cike-ciken contracts document.
Daga airport da aka zo ɗaukan su cewa ta yi a wuce da su asibiti, kafin ta ga kowa sai ta ga lafiyan mijin ta.

Tare su ka wuce asibitin dan su ma rabon su da Najeeb ya fi wata ɗaya.
Tana shigowa ɗakin ta ga Sabreen tana kissing goshin Najeeb har da hawayen munafurci a idon ta tana faɗin.

"Noory i have to go, i'm sorry, but this movie means alot to me. I've always wanted to work with Keanu Reeves and now i got the chance. Please forgive me. I'll come back for you after the shooting...."

Farida ta kama hannunta ta ja ta gefe. "Ba ya son jin komai daga gareki, so just go"

"If he wakes up Aisha, i'm going to do anything just to get him back. I promise"

"mtsssw aikin ɓur inji tusa. Ki wuce ki bamu waje karuwan banza karuwan wofi"

Sai da ta ɗau jaka ta tafi su Hassan su ka fara dariyan maganar ta.

Farida sai da ta goge wa Najeeb fiska kafin ta kissing ɗin sa tanajin haushin kissing ɗin da Sabreen ta ma sa.

"My Champ we got the contract, thank you for being with me"

Jin Farida ta manta da su a ɗakin ya sa su Yakubu su ka ma ta sallama su ka fita wanda ko iya amsawa ba ta yi ba dan hankalin ta gaba ɗaya na kan hiran da ta ke yiwa Najeeb...



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣3️⃣7️⃣



Tana tareda Najeeb, Anas da Daddy su ka shigo ɗakin.

"Masha Allah 'ya ta Allah ya mi ki Albarka" Daddy ya faɗa lokacin da ya ƙaraso.

Ta amsa da Amin tana murmushi.

"Son ka ga abinda matar ka ta yi ko? She is a fighter, she's a winner. Matar ka iron lady ce. Ka tashi ka ji, ka tashi ku gina rayuwar ku tare" ya kissing goshin sa yana shafa gashin sa.

"Daddy Mom ta dawo?"

"Sai next week" ya amsa ma ta.

"Allah ya dawo da ita lafiya"

Su ka amsa da Amin.

Anas kam kunya ta hanashi magana sai kau da kai ya ke. Daga baya Daddy ya bar su ya ce zai je yai magana da likita.

"Ya hanya" Anas ya katse shirun na su.

"Alhamdulillah mun je lafiya mun dawo lafiya. Sauro bai cize mu ba haka Cinnaka ba ta cize mu ba balle ayi tunanin mun wahala. Kuma dai girma ya faɗi"

"Farida dan Allah ki yi haƙuri. Na san ba ni da hujja akan abin da na aikata amma ki yi haƙuri ki yafe mun"

"Ya Anas a nan ka zo ka roƙe ni Allah Annabi akan na zama CEO amma mi ka yi bayan na zama CEO. Ka bauɗe min, ka ƙi goya min baya har ka na ganin gara ka bar aikin da zama na CEO ko?"

"Ba haka ba ne Farida, kawai dai ba na so kamfani ta shiga matsala ne"

"Da kyau, saboda ga Aisha Farida mai farar ƙafa ko?"

"Duk abinda ki ka ce i deserve it. Ban riƙe amanar abokina ba, i'm truly sorry"

"Ka san mi ake cewa namiji matsoraci? To Ya Anas kai matsoracin namiji ne kuma ragon namiji. Idan ba ka dena sa tsoro a lamurran ka ba to ba inda za ka je a rayuwa. Kuma ko a gidan ka za ka samu matsala. Kana ganin da ina da tsoro zan kai yadda na kai da Najeeb, ka san da ni matsoraciya ce da tun ranan da Najeeb ya koreni da na bar aiki a kamfani kenan. But i fight back, na nuna ma sa ni ba ƙwallo ba ne da zai dinga bugawa duk lokacin da ya ke so. Ka san miyasa Najeeb ya ka sa korata? Because he needs me. Najeeb na son mutum mai zafi, mutum da ba ya da tsoro ko kaɗan"

Ya ji haushin kiran sa rago da ta yi amma kuma gaskiya ta faɗa, sau tari ta inda su ke samun matsala da Najeeb kenan.

"Ki yi haƙuri dan Allah"

" na ji haushi kuma har yanzu ina jin haushin ka. Ka bani lokaci na huce tukunna"

"Ba komai, amma dan Allah ki yafe min"

"Na yafe"

Ba su sake wani maganan ba har Daddy ya dawo su ka tafi.


"My champ ka ga abokin ka ko, ka ganshi ko" ...

......................
Washe gari tana shigowa kamfani aka fara tafi, ana ma ta congratulations.
Duk wanɗanda su ke ma ta wani gani-gani to yanzu sun sha jinin jikin su. Madam Farida kamar yadda yanzu aka fi kiran ta ta zama Boss lady. Tundaga lokacin da ta ƙarɓi matsayin CEO kowa ya shiga taitayin sa saboda ita ma zafi gareta kamar Najeeb. Wani zubin ma gara Najeeb ɗin dan shi idan ya ma ka tsawa shi kenan amma wannan sai ta bika da baƙar magana wani lokacin idan ta yanko ma ka magana sai ka ji kamar ka kama kai ka rusa kuka.
Ga wanda ya bita sannu kuma tana da sauƙin kai...

Su Mr Vladimir bayan ya tabbata Farida ta leading team kuma anci gasa ba ƙaramin baƙin ciki su ka yi ba. Neman sulhu su ka fara yi dan kar su rasa 5% da au ka yi alƙawari amma kuma Farida ta ce bata san zance ba. Su su ka faɗi sharaɗi kuma dole su bi shi yadda ya ke. Haka dai ba tareda sun so ba su ma sa hannu a takardar da ke shaidar sun ba da 5% shares ɗin su a Najeeb. Ranan Farida sai da ta yi hawaye saboda hango farin cikin da ta yi a idon Najeeb idan ya farfaɗo ya ji abinda ta yi...


......................

Gidan AbdulWahab kam yanzu zaman lafiyan ba kamar da ba. Tunda Aneesa ta dawo Lagos da aiki sai komai ya chanja. Kullum cikin taƙalar Maijiddah ta ke yi, duk da ma yanzu Maijiddan ta dena tsoron ta kuma ta na ɗan maida ma ta magana amma still wassu lokutan shiru ta ke ma ta. Aksarin lokaci Maijiddah tana burin inama ace itama ta iya magana kaman Farida da za su dai-dai ta tsakanin ta da Aneesa.

Haka kawai ta hana yaran shiga harkan ta, duk da yaran na so amma abinka da uwa da ɗa sai ya zamana ta yi musu tsawa shikenan. Ɗan gara ma Alizah wani lokacin tana ƙin bin umurnin Maman na su.

AbdulWahab na iya ƙoƙarin yin adalci tsakanin su duk da ma yanzu Maijiddah ta fara ganin chanji a tattare da shi lokacin da Aneesa ta dawo. Tana renon cikin ta lafiya amma wani lokacin gani ta ke tunda Aneesa ta dawo kaman yanzu AbdulWahab ya rage ba ta kulawa da kuma ɗokin cikin da ta ke ɗauke da shi.
Cikin ta na wata bakwai Aneesa ta fara laulayin ciki. Ta gano hakan ne ranan su na zaune suna cin abinci ta fita da gudu tana amai a banɗakin da ke guest room.
Daga baya kuma Aneesan ta fara tsirface-tsirfacen abubuwa irin na ma su ciki.

Lokaci guda hankalin AbdulWahab ya koma kan Aneesa. Ranan su na cin abinci da ke Maijiddan ne ta yi girki, Aneesa ta fara kushe abincin akan an hana ta yawan cin mai a asibiti kuma ga shi abincin Maijiddan ya cika mai.

"Sweetheart ba ka gaya ma ta abinda likita ya ce ba ne?" Ta faɗa tana kallon Maijiddah.


"Anny zan gaya ma ta ba yanzu ba akwai yara a nan"

"Na san ba za ka iya gaya ma ta ba. To Malama Maijiddah ciki ne da ni kamar yadda ki ka sani, kuma likita ya ce saboda mahaifata tana da rauni na guji aikin wahala da yawan stress na kuma rage cin wassu abubuwa saboda kar cikin ya zube. Sai ki kiyaye nan gaba"


Maijiddah ta buɗe baki da hanci tana ganin wannan cin fuskan. Ƙarin haushin ma AbdulWahab bai yi magana ba.
Ajiye cokali ta yi ta bar wajen. Da ya ke kwanan ta ne AbdulWahab da ya zo sai ya ke ƙara gaya ma ta report ɗin da likita ya ce gameda cikin Aneesa.

Haushi ya kawo ma ta har wuya, ka sa shiru ta yi ta ce "amma Abban Alizah ni ma fa ciki gare ni kuma ko da babu likitan da ya gindayamin sharaɗi, dai a matsayin da na ke yanzu ina buƙatar kulawa ta musamman"

"Hauwerh dont get me wrong please, ba wai ina nufin ke baki buƙatar kulawa ba ne..."

"Sai yanzu na gane gaskiya. Dama saboda matar ka ba ta nan ka auro ni, to yanzu ta dawo ban da matsayi ko?"

"Shhhhh, kar ki sake faɗin haka Hauwerh ki na da matsayi babba a rayuwata"

" a rayuwar ka haka ne amma a zuciyar ka Anny ce kaɗai"

Kamo hannun ta yai ta wafce hannun.

"Plz Gimbiyata, ki yi haƙuri. Ki na da matsayi a zuciyata da rayuwata gaba ɗaya"

Ranan dai AbdulWahab da ƙyar ya shawo kan amaryar sa...

.....................


Ko mi zai ma ta ba za ta koma Lagos ba. Gara ya dinga zuwa yana dubata duk ƙarshen wata. Ta bar mu su waje su sakata su wala yadda su ke so. Sai da motar su ta ɗau hanya sannan ta jingina kanta da seat tana hawaye. Babbar motar Macapolo ta shiga da zai je Kano daga Lagos. Duk da kasancewa dare ne hakan bai sa ta ji wani fargaba ba. Su na tafiya tana tuno maganganun AbdulWahab...


Sai da su ka dawo daga asibiti sannan ya je ɗakin Maijiddah dan ya bata haƙuri tsawan da ya ma ta ɗazu. Ya sani sarai bai kyauta ma ta ba. Duk abinda ya faru bai kamata ya gaya ma ta magana haka ba.
Wayam ɗakin ba kowa. Ya duba ko ina ba ta nan. Mai aikin su dama ba ta nan ta yi tafiya. Fita yai ya je ya samu mai gadi inda ya sanar ma sa Maijiddah ta fita. Faɗa ya fara ma sa akan miyasa zai barta ta fita ita ɗaya da tsohon ciki. Maigadi ya ce shi ya je ya samo ma ta taxi ma domin kuka ta ke yi ta ce an musu rasuwa ne za ta je gida kuma kai ka ce ta tafi saboda kun fita da Madam Babba.
Tsaki yai ya koma ciki. Ya kira numbarta sau ba adadi amma a kashe. Ba dai Maijiddah gida ta tafi ba.
Aneesa na kwance sai nishi ta ke ita a dole ta yi ɓarin ciki kuma kishiyar ta ce sanadi. AbdulWahab ya shiga tashin hankali sosai ina ya san zai nemi Maijiddah da daren nan...

Washe gari da safe ya samu labarin ta shiga mota ta tafi Kano. Kiran Hajiyar sa yai dan ya ji ko ta iso sai ya ga Hajiya ba ta ma sa maganar ba sai ma tambayar sa da ta ke ina Maijiddah. Sai alokacin ya waske da cewa ai tana hanyan Kano ma yanzu.

"Ko kai fa amma ka ce wai ta zauna a chan ta haihu"

Dama Hajiya Yelwa ta nemi ya bar Maijiddah ta haihu a kano ya ƙi shiyasa ba ta kawo komai aran ta ba.

Ƙarfe goma na safe su ka isa Kano inda direct gidan su mijinta ta wuce. Yanayin yadda Hajiya Yelwa ta ganta ya sa ta gane ba tafiyar jirgi ta yi ba.

"Lafiya Hauwa na ga kin kumbura, duba ƙafafuwan ki"

"Ba komai Hajiya zama ne kawai ya sa yai haka"

Hajiya Yelwa ta kira AbdulWahab tana ma sa faɗa akan barin Maijiddah da yai ta zo ita ɗaya sannan a mota ba a jirgi ba.

Hamdala yai lokacin da ya ji Maijiddah ta isa gida lafiya. Ya bawa Hajiya haƙuri akan ayyuka su ka ma sa yawa.

"Hajiyata ki ɗan bawa Hauwa wayar na kira numbar ta baya shiga ina ga wayan ya mutu ne"

Hajiya ta miƙawa Maijiddah wayar wanda ganin idon Hajia ya sa ta karɓa.

"Haba Hauwerh kin min adalci kenan, idan wani abu ya same ki fa."

"Na isa gida lafiya a gaida marar lafiya" ta kashe wayan saboda Hajia ta fita a ɗakin...


Kwanan ta na uku sai ga AbdulWahab. Tana zaune tana cin abinci a ɗakin Hajia sai ga shi ya shigo.
Ganin sa da ta yi sai da ta ɗan yi jim amma ta dake.
Zuwa yai ya zauna gefen ta ya kamo hannunta ɗaya ya ce "Gimbiya ta haka kike da zuciya dama. Haba dan Allah, kin san ina son ki kuma ba zan taɓa yin abinda zai ɓata miki dai ba"

"Amma ai ka yadda ai lokacin da matarka ta ce na tureta ta faɗi. Na yi sanadiyar rasa cikin ɗan Lele ko"

"Na san na yi kuskure Gimbiyata a min haƙuri"

Namiji dai da daɗin baki haka ya gama kwantar ma ta da hankali da kalamai ma su daɗi. Dole dai ta miƙa wuya ta haƙura ƙarshe ma ita ta koma tana bashi haƙurin kan tahowa da ta yi cikin dare ba tareda ya sani ba...
Washegari ya tafi dan ya san tunda ta riga ta zo sai ta haihu tunda dama tun farko Hajiya Yelwa ta nemi hakan...



.......................

Sati biyu da zuwan Maijiddah kano ta haifo santalelen ɗan ta mai kaman uban sa. Haihuwan nan ya sa Aneesa ta tada daru akan AbdulWahab dole ya bi ma ta hakki tunda Maijiddah ce ta yi sanadiyar zubewar cikin ta. Shi kam bai biye ma ta ba dan sai a lokacin yake ganin wautarsa ranan. Domin ya san Maijiddah ba ta da faɗa kuma yadda ta ke ɗan jin tsoron Aneesa haka kawai ba za ta tureta ba dan dai maganar fatar baki. Balle Maijiddah na da tsohon ciki ita kuma Aneesa cikin ma wata biyu ne.
Ana saura kwana biyu suna ya tattaro yaran sa su ka zo Kano. Aneesa kam Abuja ta wuce ta ce ba za ta je sunan ba...


Daga gidan suna ta wuce asibiti.

"My Champ ka ga babyn Maijiddah kuwa? Wallahi kyakykyawa da shi. Ka tashi muma mu yi abubuwa na samu ciki na haifi Baby mai kaman ka. Ka ji miji na"
Ta ƙara kissing hannun sa tana faɗin "sunan Babyn na su Muhammad Al'amin, nima My Champ ina son suna Muhammad. Sunan ɗan mu na farko kenan Insha Allah"...


Ƙarƙashin jagorancin Madam Farida Najeeb Constructions ta samu cigaba sosai kuma an samu gyararraki kan abubuwa dayawa.
Yau ma wassu baƙi ta ke meeting da su da su ka zo daga Kaduna.

Tana shiga office ɗin ta Anas ya shigo.
"Farida ba ki sa hannu a wannan takardan ba"
Ya miƙo ma ta wani takarda. Ta ƙarɓa ta yi signing sannan ta miƙa ma sa.

Tana zama sai ga kiran sakatariyar ta.

"Hello Madam, Mr Rayyan Abdullahi is here to see you should i send him in?"

"Rayyan Abdullahi?"...

Mi Rayyan zai zo yi wajen ta. Rabon ta dashi tun ranan da ya zo office ɗin ta Najeeb ya ma sa kora da hali...






*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣8️⃣



"Faridah" muryan Rayyan ya doki kunnen ta. Ta ɗan ɗago ta kalleshi, kallonta ya ke yi mai cike da ma'anoni.
Da yatsar ta ta ma sa nuni da ya zauna ba tareda ta kalle shi ba. Har ya zauna bai ɗauke idon sa a kan ta ba. Ita kuwa tunda ta ɗago sau ɗaya ta maida kan ta ga takardun da ta ke dubawa.

"Farida" ya sake kira

Ta ɗago kai tana juya biron da ke tsakanin yatsunta biyu.
"Mr Rayyan what can i do for you?"

"Farida ni ɗin, ni ɗin ne Mr Rayyan" ya faɗa yana nuna kan sa.

" ok to Malam Rayyan mi zan iya ma ka"

"Lallai duniya!"

"As you can see aiki na ke yi. Idan ba ka da abin faɗi dan Allah ka ƙara gaba"

Jijjiga kai yai sannan ya ce "ya jikin Mijin ki?"

"Alhamdulillah da sauƙi"

"Stop pretending Farida, waye bai san halin da Najeeb ya ke ba a garin nan. He's being in coma for months now, ba alaman zai farfaɗo balle..."

"Balle me? Balle me?" Farida ta daka masa tsawa.

"Kwantar da hankalin ki Farida ba faɗa na zo ba. Ina so ki sani cewa har yanzu ina son ki kuma ina son auren ki. An sa aure na da mai sunan ki nan da 2 months. Amma na roƙi Umma ta bar ni na aure ki bayan na auri 'yar uwata Aishatu kuma ta amince. Kin ga by the time kin gama iddah sai mu maida auren mu"

"Ban san ka da shan giya ba Rayyan, ko dai ka fara ne bayan rabuwar mu?"

"Farida ke kan ki kin san har yanzu ina son ki..."

"Rayyan idan ba giyan wake ka sha ba ya kamata ƙwaƙwalwar ka ta gaya ma ka ni matar aure ce, ni matar Najeeb ce"

"Wanni Najeeb ɗin, Najeeb da ke chan kwance kamar gawa. How long has it being, kusan 8 months fa"

"Yes Rayyan. Yana chan kwance for 7months 9 days, kuma zan jira shi ko da zai ɗau shekaru kafin ya farfaɗo. I love him and i will wait for him till the end of my life. Get that into your thick skull Rayyan" ta faɗa tana miƙewa tsaye.

"Far..."


"Leave!" Ta daka ma sa tsawa

"Farida ki..."

"Get out! Ka fita na ce!" Yadda ta yi tsawan wannan karan sai da ya ɗan tsorata.

Ba tareda ya sake yunƙurin magana ba ya tashi ya fita.

Zama ta yi ta fashe da kuka. Miyasa kowa ke ganin Najeeb ba zai tashi ba, miyasa su ke ganin a haka zai ƙarasa rayuwar sa. Haka jiya da su ka yi waya da Ummi ta ke ce ma ta ance ba lalle Najeeb ya farfaɗo ba, ko za a raba auren su. Miyasa ita ba ta gaji da jiran sa ba amma su sun gaji. Akwai wanda ta farfaɗo daga coma bayan shekara ishirin, ko da Najeeb zai shekara ishirin a haka za ta jira shi. Balle ta san ya na chan ya missing ɗin ta yana ƙoƙarin dawowa gareta...

.....................

A gajiye ta shigo ɗakin na su saboda aikin abincin sadaka da

Please Login or Register in order to submit comment