Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah a wattpad account ɗi na 000Azee)*


............

"Yakubu dan Allah ka nemo min super glue mai kamawa sosai wanda baya saurin bushewa"

"Yanzu dan Allah mi za ki yi da super glue? Ke ba mai gyaran takalmi ko radio ba"

"Ni bana son sa'ido, ka nemo min kawai. Harda gum na ruwa ɗin nan. Yau na ke so ba gobe ba"


"Ke wallahi case ce, na ji zan nemo"

Farida ta yi murmushi

Da wurwuri ta zo office yau. Tana daƙontar zuwan Najeeb dama ta gayawa security da zaran Najeeb ya ya shigo ya kirata.
Tana zaune kuwa security ya kira ya ce ga Najeeb ya shigo. Ta yi sauri ta shiga office ɗin sa ta samu kujeran sa ta fara matsa super glue ɗin da Yakubu ya kawo ma ta.
Za ta fito kenan ta yi kiciɓis da Najeeb zai shigo dama tuni ta sa tubes ɗin a jakarta.
"Good morning Sir"
Bai amsa ma ta ba ya wuce wajen zaman sa.

"Sir Ya Anas ya kawo flash ɗin da za ka yi amfani wajen presentation ɗin na ajiye a table ɗin ka" wannan magana shi ya ɗaukewa Najeeb hankali ya zauna ba tareda ya lura da kujerar sa ba.
Tana gani ya zauna ta yi murmushi.

"Ki tabbatar duk wanda ke cikin team ya isa conference room kafin ƙarfe tara"

"Ok Sir" ta fita tana murmushi.

Flash ɗin ya ɗauka ya sa a laptop na shi yana duba presentation ɗin da Anas ya sha wahala ya tsara.

Ƙarfe tara saura minti shabiyar ya gama bitar abin ya kira Farida. Ta san dole zai kirata domin ta ɗauka ma sa laptop da wasu files dama.

Ƙoƙarin tashi yai a kujeran ya ji ya ka sa tashi. Da ya tashi sai kujeran ta biyoshi.
"What's this" ya faɗi lokacin da ya ke ƙoƙarin raba takashinsa da kujeran amma hakan bai yiwu ba.

"Sir Najeeb ya dai?"

Farida ta faɗa kamar ba ta san mi ya ke faruwa ba.

Tsaki yai ya cigaba da ƙoƙarin raba jikinsa da kujeran.

"Sir idan ka ja da ƙarfi zai yaga ma ka wando ka ga anyi ba ayi ba kenan. Tsuliyar CEO Najeeb constructions a waje" ta sa hannu ta ɗau flash ɗin da ke kan table ta ce " tunda takashin Oga ya maƙale a kujera sai na kaiwa Ya Anas kawai yai presentation ɗin tunda dama shi ya kamata yai tun farko"

Sai da ta fara tafiya ya ƙwalla ihun sunan ta da ƙarfi "MISS SALIHUUU"

Ta waigo tana fari da ido ta ce " SIR NAJEEB YA DAI"


*difdifdifdif..... anan na kawo ƙarshen free pages. Na yi ƙoƙari ai har page 15. Well, za ka samu cigaban labarin idan ka biya 200 kacal. Stay safe and Allah ya mana albarka ya rufa mana asiri duniya da lahira ta ku AZIZAT*



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣1️⃣6️⃣


Tana fita daga office ɗin Sir Najeeb office ɗin Anas ta wuce. Ta sameshi ya yi wani jugum da shi. Tabbas abinda Najeeb ya ma sa ya mugun kashe ma sa jiki.
Ajiye flash ɗin ta yi a gaban sa ta ce "Yaya na ga shi ka je ka yi presentation ɗin"

"Roƙonsa ki ka yi? Ko kawai ɗaukowa ki ka yi?"

"Ko ɗaya, Yaya na shi da kan sa ya bani ya ce na kawo ma"

"Ban yarda ba, Najeeb ba ya chanja magana da wuri. Kar ki damu ƙanwata, Najeeb shi ke da kamfani yana da ikon hana ni ko ya sa na yi abu"

"Ya Anas da gaske na ke fa, idan ba ka yarda ba ka zo muje ka tambayeshi"


Da farko dai Anas bai amince ba daga baya da ta takura sai ya tashi su ka fita, har lokacin dariyan Najeeb na cinta.


A ɓangaren Najeeb kuwa yayi nasarar raba jikin sa da kujeran amma kamar yadda Farida ta faɗi sai da wandon shi ta farke, wasu daga cikin pattern na wandon suna manne da gum ɗin a jikin kujera, wandon ya koma har ana ɗan ganin boxers na shi.

Najdah ya kira akan ta kawo ma sa kaya daga gida, ta ce ma sa tana school ai kuwa ya fara babbaleta da masifa abinda bai saba yi ma ta ba, idan ba masifa akan Mom ba, normally ba ya taɓa ɗaga ma ta muryarsa. Ganin yadda ya ke faɗa ya sa ta san lallai akwai matsala, dole haka ta bar class ta wuce gida.
Yana ajiye wayar sai ga Anas da Farida sun shigo, yai saurin komawa ya zauna akan kujeran dan kar Farida ko Anas ɗin su ga yadda bayan wandon sa ya koma a rarike.

"Sir Najeeb ina kai ka ce Ya Anas ya je yai presentation ko?"

Sai da ya ma ta kallon banza sannan ya kalli Anas ya ce " ka je ka yi pitch ɗin nan, its already time"

Anas da mamaki ya ce " miyasa ka chanja ra'ayin ka?"

"Oh please, just go"

"Ya Anas, Sir Najeeb ba shi da ja fa, kai ɗin ne dai za ka yi presentation ɗin"

Anas yai shiru yana nazarin Najeeb, akwai ɓacin rai mai tsanani a tattare da shi amma yanzu bai da halin tambaya saboda chanjawar da abokin sa yai. Ya karɓi flash ɗin daga hannun Farida ya juya. Farida ta bi bayan sa tana gwada irin tafiyar Najeeb. Sai da su ka kai bakin ƙofa ta juyo ta ce " Sir Najeeb asha zaman kujera lafiya" sannan ta sa dariya.

Bayan fitan su da kusan minti arba'in Najdah ta zo mi shi da wasu kaya daga gida.

" Big B mi ya faru ka ke ta min tsawa ɗazu?"

"I'm sorry baby, i was just pissed off ne"

"Barin koma school muna da class"

Ok kawai ya ce ya jira sai da ta fita daga office ɗin sannan ya wuce banɗaki ya chanja kaya.
Lokacin da ya ga wandon wani haushin Farida ne ya zo ma sa har wuya. He's 100% sure ita ta sa wannan abun a wajen, kuma ta yi ne domin ta hanashi presentation ɗin nan.

"All because of Anas" ya furta a fili.

Ya kalli kan sa a madubin banɗakin ya ce " Did she really love him?"

Wanni ɓangare na zuciyar sa yana cewa miya shafeka idan tana son Anas, wani ɓangare kuma na cewa bai dace su yi soyayya ba, Anas is a good person amma wannan Ayshern, bai san ma ya zai kwatantata ba.

Shi dai abinda ya barwa ran sa shine dole ne ya hukuntata. Ya rasa miyasa ya ke kasa aiwatar da komai a kanta despite the fact cewa ta raina shi kuma tana karya dokokin sa son ran ta....


Najdah daga office ɗin Najeeb sai ta wuce office ɗin Anas. So ta ke ta sake tambayarsa ko da gaske ne yana son Farida, domin ranan ba ta barshi yai magana ba ta kashe wayar.

Ganin baya office ya sa ta yi yunƙurin tafiya idan ya so sa haɗu daga baya, sai hankalinta ya je kan wani hoton sa da ke kan table. Ta ɗauka hoton ta ƙura ma sa ido. A cikin tarihin rayuwarta tana son baƙin namiji, ita baƙin mutum na burgeta. Farar fata gareta amma many a times tana envying skin ɗin baƙaƙen mutane. Tun tana ƙarama ta san Anas, lokacin idan sun zo hutu Nigeria, su na tare koyaushe saboda tafi kowa kusa da Najeeb shi kuma shine kaɗai abokin Najeeb. Wani lokacin ko da Najeeb bai zo hutu ba to kullum tana tareda Anas, wannan ya sa ta shaƙu da shi tun a yarintar ta, shekaru uku da su ka wuce kuma ta fara jin wasu baƙin lamura game da shi wanda ita kan ta ba za ta iya fassara su ba. Ta ɗan shafa hoton sannan ta ajiyeshi.

Tana fitowa ta yi kiciɓus da Anas da Farida, da alama office ɗin na sa za su shiga amma maganar da su ke yi ya sa su ka tsaya a wajen. Dariya Anas ke yi sosai harda riƙe ciki. "Farida you are too much wallahi, abinda ki ka yiwa Najeeb kenan"

Doguwar tsaki Najdah ta ja wanda ya ja hankalin su.

"Najdah" Anas ya faɗa lokacin da ya juyo ya kalleta.

"An dai ji kunya" ta faɗa sannan ta bar wajen. Da sauri Anas ya bi bayanta yana kiran sunan ta.
Ta shiga lifter amma kafin ƙofar ta rufe Anas yai saurin sa hannu ya tare sannan ya shiga lifter ɗin shi ma.

"Najdah wai miya faru ne?"

"Dont pretend kamar ba ka san abinda ya faru ba. Sakatariyar Big B fa ka ke so. Sakatariyar sa"

A wannan dama da Allah ya bashi yau, dole ya cire tsoro kamar yadda Farida ta ce.
A hankali ya furta " to miye a ciki? Ita sakatariyar Najeeb ba mutum ba ce?"

Wannan karan kaman za ta yi kuka ta ce "Yaya yanzu duk faɗin garin nan ka rasa wanda za ka so sai ita, that cheap girl"

Ƙwarai ya gane kishi ta ke amma bashida 100% assurance cewa kishin sa ta ke, sai dai dole ne ya tabbatar wa kan sa domin shi ta ke kishin.

"Najdah wa ki ke so na so? Wa ki ke ga zai so ɗan Maigadi"

"Yaya you know we love you, ka riga ka zama ɗan uwan mu yanzu"

Matsowa yai kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya ya ce "so idan ɗan Maigadi ya nemi 'yar masu gida za ta amince?"

Jikinta yai sanyi haka nan kuma kusancin su da hannunta da ya riƙe ya sa ta fara jin wani baƙon yanayi ajikinta, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri.

Zuciyar sa ce ta ce 'Anas is now or never'

A hankali ya kai bakin sa dai-dai kunnenta ya ce "i love you Najdah, only you"

Maganar yai dai-dai da tsayuwar lifter dan haka ta wafce hannunta ta fita da gudu. Bai bita ba, sai ma murmushi da ya fara yi saboda jarumta da yai yau, finally he said it...


Farida na zuwa office ɗin Najeeb ta tadda ya chanja kaya.

"Manyan mutane kenan, Allah ya ja zamanin ka CEO"

Fiskar nan ba fara'a ko kaɗan ya ɗago ya kalleta ya ce "your two weeks suspension starts now, Miss Salihu"

"Suspension"

Sai kuma ta yi shiru.

"Two weeks suspension is not all, bayan kin dawo za ki serving punishment na ki"

"Hutarere wallahi. Hutun sati biyu ai gaba ta kaini, ka ga zan fara azumi a gida kenan dan Jos zan wuce. Na gode Sir Najeeb Allah ya ƙara daraja"

"Leave" ya faɗi da ƙarfi

"Sir Najeeb ina da magana" ba ta jira ya ce komai ba ta ce "tsakani da Allah abinda ka yiwa Ya Anas bai dace ba, ka san yadda mutumin nan ke ganin girma da darajarka amma ka walaƙantashi. Irin walaƙancin kun nan na ma su kuɗi ya sa ya kasa furtawa ƙanwar ka kalmar so, kaima kuma da ke ba ka damu da shi ba, sai ba ka gano son da ya ke yiwa ƙanwar ka ba"

Ɗago ido yai yana mamakin maganganun ta.

"A rage girman kai Sir Najeeb. Shi girman kai rawanin tsiya ne"...

Bai san lokacin da ta fita daga office ɗin ba saboda ƙwaƙwalwarsa da ta tafi duniyar tunani.

Anas na son Najdah, how when,why?. Kenan ba Aysherh ya ke so ba?

Da sauri ya miƙe ya bar office ɗin...


Wasu takardu Anas ke dubawa lokacin da Najeeb ya shigo, da ka gan shi ka san yana cikin farin ciki.

"You love my sister?" Ya tambayeshi lokacin da ya shigo.

"Najeeb..."

"Idan har kana son Najdah, why Miss Salihu again"

Dariya yai ya ce "tsaya Najeeb, waya gaya ma ka akwai abu tsakanina da Farida? I love your sister, ita kaɗai na ke so"

Ɗan ƙaramin tsaki ya ja sannan ya bar office ɗin.

Nan zuciyar Anas ta ɗauko kan zan cen.

"Najeeb kishi ya ke da ni. Haba, dole biri yai kama da mutum ai. I suspected this tuntuni, Najeeb is inlove"

Murmushi ya biyo bayan maganar da yai wa kan sa, duk wani abinda Najeeb ɗin ya ma sa sai ya ga ya washe ko kaɗan baya jin haushin sa. The fact that Najeeb has feelings for someone else bayan Sabreen ai abun farin ciki ne. After 8yrs of loneliness.


Cikin kwana biyun nan abubuwa sun chanja. Najeeb ya koma yana jin kunyar Anas saboda abinda ya ma sa duk da kuwa Anas ɗin ya nuna komai ya wuce. Shi kan sa Najeeb ba zai iya faɗan dalili ɗaya da ya sa yai ma sa haka ba domin haushinsa ya ke for no reason amma kuma yanzu ya washe.

"Yau zan fara zuwa hira officially, sirikina ka gaya min tips wanni irin kaya Najdah ta fiso namiji ya sa"
Najeeb ya dundeshi ya ce "ɗan iska, ta fi son gwanjo"
Kalmar gwanjo da ya faɗi ya sa sunan Aysherh ya zo ma sa, kwana uku kenan da ba ta nan.

" abokina dan Allah kar ka manta a shigemin gaba wajen Daddy"

"Fuck you, Daddyn ne sai ni ne zan ma sa magana, kai ma ai ɗan sa ne you can talk to him about it"

"Ni ba marar kunya bane irinka ai"...

Anas na fita daga office ɗin sa ya tura wa Farida text akan an janye suspension ɗin ta resuming aiki gobe. Lokacin da text ɗin ya shigo Farida na bacci so ba ta gani ba.

Shigowar Khalidah office ɗin ne ya sa shi deleting ɗin text ɗin da ya ke shirin tura wa Farida ta ɗaya layinsa.

"Kwana na biyu da dawowa banga sakatariyar ka 'yar gold ba. Ko ka koreta ne?"

" get out"

"Maida wuƙar Najeeb. Na zo maganar project da ake yi a Kaduna ne"

Ya nuna ma ta kujera akan ta zauna...


Farida na ganin text ɗin Najeeb ta yi tsaki ta tura ma sa reply kamar haka

*Sir Najeeb ni ba zan dawo ba sai sati biyu sun cika, kana gani za a fara azumi nanda kwana biyu ka ce na dawo, gaskiya sorry*

Lokacin da ya gama karanta text ɗin yai ƙaramar tsaki.


...................

Sati biyun dai ba ta yi shi ba, sati ɗaya ta yi ta dawo saboda yadda Anas da Yakubu su ka takura akan ta dawo.
Duk da an rage awa ɗaya cikin lokacin aiki, hakan bai sa ta jin haushin aikin ba yanzu saboda watan azumi da aka shiga.
8-3pm ba wasa ba ne a wajen Farida ga ɗan karen zafi da ake yi a garin na Kano, ga ruwan sama ma dai har lokacin da azumi ya kai goma ba wani alamunsa sosai dan sau ɗaya aka yi ruwa. Daga ƙarfe shabiyu za ka ga Farida ta yi laushi. Da ƙyar ta ke kaiwa lokacin tashi.

Yau ma wani aikin da za ta yi Najeeb ke ma ta bayani.
Burping ta fara yi akai akai har sai da Najeeb ya fusata ya ce " Miss Salihu will stop sounding like a frog"

(Burping kaman ƙwanafi kenan, ban san Hausa word na shi ba. Irin dai abinda ma su ulcer su ke yi ɗin nan ko kuma idan mutum ya cika cikinsa da abinci dayawa za ka ga daga maƙoƙoron ka kana fitar da sautin irgh irgh irgh )


"Sir Najeeb ba fa da gangan na ke ba, ulcer na ne ya tashi..." ba ta ƙare maganan ba ta kuma yi ya ce "Gosh! Miss Salihu get out"

Ba ta musa ba ta fita dan dama a gajiye ta ke...

Ya dawo daga sallar Azahar ya shiga office ɗin sa sai ya ji ƙanshin abinci. Abinci in his office a watan Ramadan? Ya juya inda ya ke jin ƙaran sokali and there he sees her. Ta barraje a ƙasa tana cin jollof ɗin taliya da macaroni.

"Since when did my office become your dining room?"

Ɗago ido ta yi ta kalleshi hannunta ɗauke da sokali totse da abinci.

"Ni ban ɗauka za ka dawo yanzu ba"

"Miss Salihu"

"Dan Allah Sir Najeeb ka barni, ka ga office ɗina kowa na shigowa ƙarangatsau, na ka office ɗin akwai privacy"

Zuwa yai ya zauna bai ƙara cewa komai ba. Lokaci zuwa lokaci yana ɗaga ido ya kalleta. Shi mamakin yadda ta ke cin uban abincin nan ya ke. Ko za a matse shi ba zai iya cinye abincin nan ba amma ita ya san zuwa anjima kaɗan za ta take shi.

Wata rana ana azumi goman ƙarshe, ranan anyi tsananin rana. Ƙarfe biyun rana sun je wani site Farida tana tsaye tana jin maganganun su har ta koma ba ta jin komai sai yijib ta faɗi ta suma. Najeeb da mutanen da ke wajen su ka yi kan ta.
Wanni Emmanuel na shirin kai hannu zai taɓa ta Najeeb ya daka mi shi tsawa "dont touch her"....



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣1️⃣7️⃣





Bayan ta farfaɗo ya sa aka kawo ma ta ruwa, maltina da madara akan ta karya azumi.

"Kai za ka biyamin ai idan na karya" abinda ta faɗa kenan lokacin da ya miƙa ma ta maltinan.

Ranan daga wajen ma ya maida ita gida ba tareda sun koma kamfani ba.

Haka dai a dararance ta cigaba da azumi har aka ƙare. Ana gobe Sallah aka ba su hutun kwana uku akan rana ta ukun sallah za a dawo. Farida kam cewa ta yi ba ta san zance ba sati ɗaya za ta yi. Ta wuce Jos ta yi sallan ta achan, duk da Kano za ta ga hawan sallah amma wannan baya gaban ta ta fiso ta ji ta jikin Umminta. Ƙila ma daga wannan sallah ita da sallah a Jos sai ta Allah.


.................

Lagos


Sati uku Maijiddah da angonta su na kwasan amarci, ba ta da matsala dan yaransa ba ma su hayaniya sosai bane.

Iya Bose ke mu su girki, amma tana kwana uku da zuwa ta fara shiga kitchen tana taya Iya Bose sarrafa abinci duk da kuwa Iya Bosen ba ƙarya ta iya girki sosai. A wajen ta ta san favourite na mijinta ta kuma koyi yadda ake sarrafa su. Shi ba bayarabe ba amma yana son cin amala da sakwara, dan haka ta dage tana koyon su a wajen Iya Bose. Miya kam ta ga ikon Allah, domin ita dai a gidan su idan ba kuka, kuɓewa, ko alayyaho ba to ba wani special miya da ake yi. Akan yi miyar egusi wani lokacin saboda Baffa na so amma a wajen Iya Bose sai ta ga miyar egusin ma ba kala ɗaya ba ce. Haka ta dinga ɗaukan darasin girki a wajen 'yar tsohuwar matar nan.


Daren Jumma'a da ya cika sati uku da auren su sai ga Aneesa ta zo.

Suna zaune su na kallo da yara a falo ta shigo, yaran suna ganinta su ka fara ihun mommy mommy.
A hankali Maijiddah ta fara satan kallon Aneesan duk da kuwa ta taɓa ganin hoton ta, amma ganinta a fili sai ta ga ta ƙara zama ma ta wata Madam. A ƙalla Aneesa za ta kai 36yrs ko 37yrs, amma jin daɗi da kuma samun mayuka ma su tsada sai ya ɓoye shekarun ta.

Sai da ta raba su Baby da Alizah a jikinta sannan ta kalli inda Maijiddah ke zaune sanye da doguwar riga ta atampa ɗinkin ya amshi ɗan jikinta ɗas-ɗas da ita.

Sai da Aneesa ta ƙare ma ta kallo sannan ta ja tsaki ta ce "ashe househelp Sweetheart ya kawo min"

"Sannu da zuwa" Maijiddah ta ce da ita.

"Nonye, Nonye" Aneesa ta fara ƙwalla sunan nannyn su Alizah.
Matar ta fito da sauri.

"Welcome ma"

"Je ki gyara min ɗakin Seeetheart, na san by now it most be stinking of filth"

Nonye ta haura sama ɗakin AbdulWahab. Dama ita ke gyarawa sai dai zuwan Maijiddan ne ta hanata ta ce ta dinga gyara ɗakin yaran kawai da sauran wajen.

Kallon kirki Maijiddah ba ta samu daga wajen Aneesa ba. Aneesa ta haura sama don ta je ta shirya kafin AbdulWahab ya dawo.

Maijiddah kam sai duk jikinta yai sanyi. Tsoron Aneesan ne ya kamata ganin wannan kallo da ta ke ma ta. Ta na da ƙuruciya amma Aneesa ta fita wayewa da komai. Ba za ta iya haɗa kan ta da ita ba.

Ƙarfe tara saura sai ga AbdulWahab ya dawo daga office. Yaran su ka fara sanar da shi gameda zuwan Aneesa. Bai yi mamaki ba dan rabon sa da magana da ita tun ranan da aka ɗaura aurensa da Maijiddah.

Maijiddah ba ta yi yunkurin raka shi ɗaki ba kamar yadda ta saba tunda Aneesa ta dawo.
Ɗakin sa ya je ya cire kaya ya watsa ruwa sannan ya fito bayan ya sa kayan gida.

"Hauwerh yau na yi laifi ne ko ya hanya ba a min ba?"

Rasa mi za ta ce ma sa ta yi dan gaba ɗaya zuwan Aneesa ya birkita ma ta lissafi.

Sai da ya zauna sannan ta fara serving na shi dama yara sun riga sun ci abinci, ita ɗin ma saboda zuwan Aneesa ta ci abincin tareda yaran dan ba ta son hayaniya.
Da ta gama ta juya za ta tafi ya riƙe hannunta " gimbiya ta zauna"

Ba ta musa ba ta zauna amma hankalinta ba a kwance ya ke ba. Ƙanshin turarukan Aneesa shi ya sanar da su isowanta falon. Irin kayayyakin da Farida ta bata a matsayin gudunmawa, irin sa ke jikin Aneesa yanzu. Wata arniyan riga ce ta saka wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyar ta, rigan ba ta da hannu, rabin nonuwan ta a waje. Tana catwalking har ta iso wajen su.

Kai tsaye ta mannawa AbdulWahab kiss a kumatu tana faɗin " Sweetheart sannu da zuwa. Shine har ka fara cin abincin ban da ni"

Da ƙyar Maijiddah ta sauke wani wahallen numfashi sannan ta tashi ta bar wajen. Ashe rashin ganin Aneesa a kusa ne ya sa take ganin kaman ita ba ta da kishi.
Kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta ja ƙofa ta sa key. Maimakon bacci ya ɗauketa kamar yadda ta so sai bacci ya ma ta ƙaura. Ta ga yadda idon AbdulWahab ya chanja lokacin da ya ga Aneesa, to irin wannan shiga ai ko ita da ta ke mace ma ta yaba. Sai dai anya ita Maijiddah za ta iya saka irin waɗannan kaya kamar yadda Farida ta yi ta ja ma ta kunne?...



...............

Satin da Farida ta ce za ta yi shi ta yi duk da kuwa Yakubu ya kira ya ce Sir Najeeb ya yi faɗa akan wanda su ka ƙara hutu. Ita kam ba damuwarta ba ne.

Ranan da ta resuming aiki Najeeb bai yi faɗa ba, kodan ta ga kamar hankalinsa na kan wani aiki da aka damƙawa kamfanin na su satin da ba ta nan. Sati biyu bayan sallah aka kawo sadakin Farida sannan aka sa rana uku ga watan december wanda yai dai-dai da wata uku ma su zuwa.
Farida ta so Baffa ya sa bikin irin wata biyar ɗin nan, dan ta samu ta haɗa wasu kuɗaɗe wanda za ta yi hidiman biki da su.

Sai da aka tashi daga aiki ta shigo office ɗin sa, lokacin ma shi duba wasu zane da aka submitting ma sa ya ke.

"Sir ga goron sa ranan aurena da akayi, na kawo ma"

Ɗago ido yai ya ga baƙar ledar da ta ajiye akan table.

Ƙura ma ta ido yai yana son gano wani abu a tattare da ita. She was excited as she talked to him.

"Sir idan ka ɗan ƙara haƙuri da ni, nan da wata uku zan bar aiki da kai"

Still bai ce komai ba
"Ka san anguwan da zan zauna ɗan karan nisa ne da kamfanin nan, ga kuma aikin ku 8am-4pm. Ina matan aure kam ba zan iya ba"

Duk maganganunta ba wanda ya tanka a ciki a dole da ta ga ba shi da niyyan yin magana ta haƙura ta ce "Sir Najeeb tunda ko fatan alkhairi ba za ka min ba. Sai da safe" ta gyara zaman jakarta ta fita daga office ɗin.

Certainly Anas ya ce ma sa Farida is engaged tuntuni, amma shi bai ɗauki abin serious ba. Tukunna ma wani mahaukacin za ta aura da zai iya zama da ita. Ya kalli ledar da ta ajiye ya ji wani takaici ya shigeshi. Haka kawai ya tashi ya ɗau ledar ya je ya jefa a dustbin da ya gama ya shiga banɗaki ya wanke hannun sa. Da ya dawo ya zauna, ran sa ya riga ya dagule, aikin da ya ke son yi ma kasa yi yai dole sai tattarawa yai ya bar office ɗin shima.


.........

Its like tunda Farida ta yi maganan sa ranan ta sai Najeeb ya rasa kan sa. Mafiya lokuta idan Farida ta zo sai ya ji wanni haushin ta fiye da da, haka nan kuma ba shi da abinda zai ma ta. A da tana ɗan tsoron masifar sa amma yanzu kam kamar ma ta maida shi

Please Login or Register in order to submit comment