Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ɗau brief case na shi ya fita.
Agogo ta duba ta ga ƙarfe bakwai saura minti ishirin. Kai dole Sir Najeeb ya dinga zuwa da wuri, duk da kamfanin sa ne amma ba ya wasa da zuwa da wuri.

Bayan fitan sa sai da ta mori bacci sosai kafin ta tashi wajen ƙarfe goma ta fara gyara ɗakin...


....................


"Dan Allah wa ya ke zuwa wajen aiki ranan ukun auren sa. Haba Najeeb ko a week break ba za ka ɗauka ba"

"A week break? Bayan asaran da Miss..." " i mean Mrs Jibo ta jawo min"

Anas ya kwashe da dariya " Mrs Jibo, haba nawan, ba wani sweet pet name da za ka sa ma ta sai Mrs Jibo"

"Mrs Jibo ma ai matsayi ta samu"

"Akwai lokacin da za ka kirata sweetheart, my love..."

"Oh please Anas"

"Allah Wallahi. Yanzu dai akwai wani Korede da zai fara aiki da kai yau, i hope you'll like him"

"No need, Mrs Jibo za ta resuming monday"

"Wait, Farida za ta dawo nan?"

"She has no choice"

"Ka san mi ka ke faɗa kuwa? Yanzu fa Farida matar ka ce"

"So what?"

"Wallahi ba ka ma ta adalci ba Najeeb. Ita da ya kamata ya zama tana zaune a gida, ana treating na ta kamar queen, sai ka kawota nan, nan ɗin ma a matsayin secretary"

"Ba na buƙatar shawaran ka, hold it to yourself"

"Amma Daddy ya sani?"

"Anas ba ruwan ka da al'amarin rayuwata. Dont meddle with my family affairs"

Anas ya sa dariya ya ce "sannu Mr Family man"










*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣2️⃣5️⃣







Bayan fitan Anas da jimawa sai ga Khalidah fuuuu ta shigo office kamar wadda aka korota.

"Najeeb why?, why her?"

"Excuse me"

"Najeeb all this while da na ke zuwa wannan wajen ka ɗauka dan kuɗi na ke zuwa, ko an gaya ma ka ina son aikin wahala ne. Saboda kai na ke aiki a nan. Only for you"

"So?"

" Najeeb ka rasa wadda ta dace da kai sai Farida, miye ta ke da shi"


"Idan kin gaji da aiki za ki iya forwarding resignation letter ɗin ki, zan yi farin ciki da ƙarɓan sa"


"Najeeb dan Allah ka fahimce ni, Ina son ka, ina son ka fiye da yadda ka ke tsammani"

"Get out"

"Najeeb please"

"Out"

.......................


Bayan ta gama gyara ɗakin ta yi wanka ta shirya cikin atampa riga da skirt, ta sauko ƙasa dan yunwa ta ke ji. Gidan shiru sai ƙaran TV da aka bari a kunne. Zuwa ta yi wajen dining ɗin ta zauna ta zuba abinci ta fara ci.
Adama ta fito daga kitchen za ta haura sama Farida ta kira ta.
Sai da su ka gaisa sannan ta ce " mutanen gidan sun fita ne?"

"Eh"

"Ayya sannu da aiki"

"Na gode Anty"

"Anty kuma, ai sai ki sa na ji kunya. Ki kira ni Aisha ko Farida"

"Anty Farida dai"

Farida ta sa dariya.

"Dama na ce daga yanzu ba sai kina gyara ɗakin mu ba, zan dinga gyarawa"

"Na gode" Adama ta faɗa tana murmushi.

Da rana tareda Adaman su ka yi girkin rana, su na aikin tana ma ta tambayoyi gameda gidan. Su biyu ne ma su aikin ita da Tasallah. Tasallah kuma ta je gida an mu su rasuwa. Ita Adama matar Iliya dreba ne ita kuma Tasallah bazawara ce wanda aƙalla za ta kai shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar.

Da su ka gama ta haura sama ta duba wayar ta ta ga miss call ɗin Maijiddah da text ɗin ta, inda ta ke sanar da ita ta isa gida lafiya. Kiran Maijiddan ta yi amma ba ta ɗauka ba sai ta kira Ummi. Sosai su ka yi hira da Ummin wanda ta ke ta ƙara ma ta nasiha akan haƙuri...

Ƙarfe uku saura Mom ta dawo, bayan ta kimtsa ta ci abinci ta sa Adama ta kira ma ta Farida.

Farida na bacci ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa kamar daga sama, ta tashi da ƙyar ta zo ta buɗe.

"Anty Farida Hajia na kiran ki"

"Ok tana ina? Tana falon sama"

"Ina zuwa"

Sai da ta wanke fiskarta sannan ta fito.

A ɗan kishingiɗe ta sameta kan kujera ta yi nisa cikin tunani.

Farida ta ɗan yi gyaran murya ta ce " Mom barka da yamma"

Mom ta ɗago kai ta kalleta tareda ƙaƙaro murmushi.

"Sannu da zuwa Aisha"
Sai da Farida ta gyara zama sosai sannan ta ce "you're lucky Aisha, Kin san, Najeeb yana son sunan Aisha sosai"

"Ayya! Amma bai taɓa kirana da shi ba kuwa"

"He likes you. Na san bai gane hakan ba amma nan gaba zai gane"

Farida dai shiru ta yi tana sauraron wannan mata wadda ta ke uwar miji gareta.

Mom ta ɗauki wanni takarda da ke gefen ta ta miƙawa Farida ta ce " na rubuta mi ki abubuwan da ya ke so da wanda ba ya so. Zai taimaka mi ki wajen ganin kun fahimci juna da wuri"

"Na gode Mom"

Ta miƙa ma ta wani ƙaramin jewelry box ta ce "wannan kyauta ne da na ke son bawa duk matar da Najeeb ya aura"

Farida ta ƙarɓi box ɗin tana godiya.

"Open it"

Tana buɗewa ta ga sarƙa ce ta dimond sai walwali ya ke.

"Its pure dimond" Mom ta faɗa tana kallon yadda Farida ke kallon sarƙan

"Mom na gode, Allah ya saka da alkhairi. Haƙiƙa banida ma bakin godiya, this is too much Mom"

"Ba komai, just make him happy"

"Insha Allah zan yi ƙoƙari Mom"...


Farida na shiga ɗaki ta ɗau sarƙan nan ta gwada sawa a wuyan ta, tana duba kan ta a madubi. Wannan duk taron da ta je ta sa ka shi sai ta zama topic of the day. Tana cikin dubawa sai kuma ta ji jikinta yai sanyi tunowa da ta yi wanda aka bata sarƙan domin sa ba wai ya damu da ita ba ne.

Ta maida sarƙan inda ya ke sannan ta ɗauko takardan da Mom ta ba ta, ta fara karantawa.

- ya fi son kala baƙi
- ya na son cin fruits (musamman apple, inabi da lemu)
- ya na son coffee
- ya na son ƙanshi
- ba ya son wari
- ba ya son ƙazanta
- ba ya son hayaniya
- ba ya cin doya
- ya fi son kifi akan nama
- ba ya son jan abu....

Wayar ta da ya fara ringing ne ya sa ta tsaya da karantawa. Ta ɗauko wayan sai ta ga Rayyan ke kiran ta. Har wayan ta katse ba ta ɗauka ba.

"Mi kuma zai ce min" ta faɗa a fili yayinda kiran sa ya sake shigowa. Sai a kira na uku ta ɗauka.

"Rayyan lafiya ka ke kirana?"

Daga ɓangaren Rayyan ya ce "My Farida ban san ya zan yi ba, yanzu na ke jin wai hotunan nan haɗa su aka yi, wai Alhaji Jibo ya zo ya samu Baba ya nemi a maida zancen auren mu. I'm sorry dear, ki bani lokaci mu zauna mu yi magana"

"A ina za mu zauna? A saman kwano ko a saman bishiyan mangoro. Look Rayyan, kar ka ƙara kira na, ni matar aure ce"

Ta na kashe wayar ta cillata kan gado ta cigaba da karanta takardar da Mom ta ba ta.
...........................

Kusan ƙarfe biyar wa su baƙi su ka zo Adama ta zo ta kirata ta sauko ƙasa. Su biyu ne, ɗaya ta ganeta domin jiya ta zo, ƙanwar Daddy ce da su ke kira Hajia Fatima. Ɗayar kuma ba ta san ta ba.

Sai da su ka gaisa Hajia Fatima ta gaya ma ta sun zo ƙarɓan sizes ɗin ta ne saboda lefe da za'a haɗa ma ta.

Hajia Salma da su ka zo tare wadda ta ke amaryar Uncle Sulaiman ne ta ɗauko Tab ɗin ta ta na rubuta sizes ɗin, tundaga na inner wears zuwa general measurement na ta.
Bayan sun gama aka buge da taɗi, su na haka sai ga Najeeb ya shigo.

"Yawwa ango dama kai mu ke jira"

"Ni kuma?"

"Yes, mun zo karɓan kuɗin haɗa lefe"

"What's that?"

"Ɗan iska, dan ka yi ƙwacen mata sai ba za ka ma ta kayan lefe ba. To ba zai yiwu ba"

Hajia Salma ta ce " Najeeb bar Hajia Faty da tsokala. Check za ka rubuta ma na za mu haɗawa Farida kayan lefe"

Sai da yai kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "how much?"
Hajia Fatima ta ma sa daƙuwa ta ce " ungo na ka da how much ɗin, blank check za ka bamu"

"Hell no, there's no way i'm giving you a blank check. Ki samu daman zuba jari a shagunan ki ko?

"Zan ci ƙaniyar ka Najeeb"

Najeeb ya zauna ya ciro check book na shi ya fara cikatawa Hajia Salma da Hajia Faty idon su ƙyam akan abinda ya ke rubutawa.

Hajia Fatima ta ce "Allah ya sawwaƙa Najeeb, mi wannan zai yi? Ka san ina da ina zamuje kuwa? Kai ka na sa kaya designer ba ka so matar ka ta sa designer ne?"
Farida kam dai kallon su ta ke yi dan ba ta ga nawa ya rubuta ba. Ƙarshe dai dole blank check ɗin ya ba su...

Yana shiga ɗaki ya ji wayar Farida da ke kan gado yana ringing haka kawai sai ya tsinci kan sa da ɗaukar wayan wanda kafin ta yanke ya ga sunan nan dai da ke tada ma sa hankali *My Ray* tsaki yai ya maida wayar ya ajiye.
Ya na cire kaya amma sai tsaki ya ke shi kaɗai.

Lokacin da ta shigo yana kan gado, ya kunna TV da ke ɗakin yana kallon tashar Aljazeera.


"Sannu da dawowa, ya aiki"

" your Ray ya kira ki"

Dam ta ji gaban ta ya buga. Ita wallahi ta manta ba ta goge numbar bane ɗazu.

"Sir Najeeb ba wai abinda ka ke tunani ba ne, Allah mantawa na yi ban goge numbar ba"

Bai ce komai ba sai ma remote da ya ɗauka ya fara chanja tasha.

Ganin yai shiru ta ce " Sir Najeeb ka yiwa Mom godiya ta min kyautar girma. She gave me a dimond necklace"

"Mrs Jibo" ya faɗa da sigar jan hankali.

"Kar ki ƙara yi min maganar matar nan"

Farida ta zaro ido "mahaifiyar ta kan"

"Idan ki na so mu zauna lafiya, to ki dena kawo min zancen ta"

" yau na shiga uku, Sir Najeeb...."


"Shhhhhhh"

Haɗiye maganar ta yi dan yadda ta ga ran sa ya ɓaci.

Zama ta yi a gefen gadon ta ce "Sir Najeeb zan yi aikin, amma sai ka amince za ka bani dama na wanke kai na daga zargin da ka ke min"

" good for you"


..........................

Zuwa yanzu ta gama gane yanayin gidan. Mom ba ta da matsala ko kaɗan hakan ya sa ta rasa gane dalilin da zai sa Najeeb ya dinga ma ta abinda ya ke yi. Najdah kam ƙiri da ƙiri ta ke nuna ba ta son ta. Ita kam ko ajikin ta, dan ba wannan ba ne a gaban ta.
Ranar asabat da ta cika sati ɗaya 'yan gidan su su ka zo ma ta gaisuwa. Ta ji daɗi sosai kuma ta karrama su, gayya guda su ka zo dan duka matan Baffa Musa ne su ka zo da yaran su kusan su goma. Da za su tafi ta haɗa mu su tsaraba...

Anas tun ranan da Najeeb ya ma sa zancen zai dawo da Farida aikin t, ya kira yana ma ta faɗa akan miya sa za ta amince da haka, ta nuna ma sa ba komai ita ke son komawa aikin...

"Sir Najeeb wai haihuwa ka ke a banɗakin ne? Tun ɗazu fa" ta cigaba da ƙwanƙwasa banɗakin.
Haƙura ta yi ta je ta zauna tana jiran sa, dama fitsari ne ya matseta.

Yana fitowa ta tashi da sauri ta shiga banɗakin.

Tunanin ko lafiyarta lau ya ke. If she's really pressed mi ya sa ba za ta je guest room ba.

Lokacin da ta fito ɗaure da towel ya riga ya shirya takalmi kawai ya ke sawa.
"Sir Najeeb ka jirani mu tafi tare dan Allah"

" i'm not your driver"

"Sir Najeeb ya ka ke so na yi, anguwar kun nan ba lallai mutum ya samu abin hawa da wuri ba"

"Akwai mota a gidan"

"Motan tuƙa kan ta za ta yi ne. Ni ban iya tuƙi ba"

Ya miƙe tsaye ya ce "good for you"
Har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya juyo ya ce "idan kin je office ki yi aikin ki kamar yadda ki ka saba, cause our relationship is strictly professional"

"Na ji Mr professional"

...........

Ta ci sa'a da ta fito lokacin Mom za ta fita ta ce ta shiga ta kai ta. Da suna tafiya ta ce idan sun dawo ta zo ta karɓi key ɗin mota. Farida ta ce ba ta iya tuƙi ba, mom ta ce za ta sama ma ta dreba.
Lokacin da ta shigo kamfanin kowa kallon mamaki ya ke ma ta tunda dai kowa ya san ita Sir Najeeb ya aura. Kai tsaya office ɗin ta ta je, yana nan yadda ya ke ta ajiye jaka ta shiga office ɗin Sir Najeeb.

Yana waya lokacin da ta shigo dan haka ta samu waje ta zauna maimakon da da take tsayawa a gaban sa. Sai da ya gama wayar ya kalli agogon hannun sa ya ce "8:44am Mrs Jibo"

Ta langwaɓar da kai ta ce "na tsaya na karya ne kuma kai ma ka san..."

"Shhhhhh, kin san ba na son latti. Today should be the last time da za ki zo min office a makare. Sannan ba na son personal excuses na ki a nan. Here, our relationship is..."

"Strictly professional na sani" ta ƙarasa ma sa.

"Good, akwai wassu saƙo da zan tura mi ki ki printing na su ki distributing na su according to their respective specification"

"Ok" ta tashi za ta tafi sai ya ce "ɗauko min wancan green file ɗin" ya nuna ma ta shelf ɗin da ke office ɗin. Ta je wajen sai ta ga file ɗin yana ta ƙasa ne ta tsugunna za ta ɗauka dai-dai idon sa ya kai wajen dan ya tabbatar file ɗin za ta ɗauka. Wandon jeans ta saka baƙi sai shirt mai dogon hannu ash color, ta yi rolling da baƙin gyale. Ɗan tsugunnon da ta yi sai rigan ya ɗan ɗaga. Ya rintse idon sa saboda wani abu da ya ji ya tokare ma sa maƙoƙoro.
Farida ta ɗauko ta ajiye ma sa.
Gyaran murya yai ya ce "Mrs Jibo, akwai dokar da ta ba da dama wa duk wata matar aure da ke son saka hijabi a wannan kamfani da ta sa, ba matsala"

"So?" Ta faɗa tana harɗe hannayen ta a ƙirji.

"It means, za ki iya saka hijabi ko mayafi babba tunda ki na da aure"

"I see, amma ka sani ko nawa mijin bai damu da sa hijabina da rashin sawata ba"

"Still Mrs Jibo, ya kamata..."

"Shhhhhh, Sir Najeeb our relationship is strictly professional" ta kwaikwayi muryan sa.

Ya ɗan ji zafi a ran sa amma ya dake da ce wa "ok get back to work"

Har ta buɗe ƙofa idon sa na kan bayan ta. Irin kayan da ta ke sawa ne tun da, amma ya rasa dalilin da ya sa yanzu bai son ganin ta da wannan kayan...


Tana zaune tana typing Anas ya zo zai shiga office ɗin Najeeb sai kuma ya tsaya su na gaisawa. Labarin marukan da Najeeb ya sha a kan ta ya fara yi ma ta wanda ya sa ta fara dariya. Dai-dai lokacin kuma Najeeb ya fito, ba yau Anas da Farida su ka fara hira su na dariya ba amma yau gani yai dariyar ta yi yawa.

"Ango wajen ka na ke son zuwa amma tunda za ka fita barin jira ka a nan, idan ka dawo sai mu yi maganar"

Najeeb bai ce komai ba ya fita, bai yi nisa ba sai ya dawo, har lokacin magana su ke.
Yai gyaran murya ya ce "Mrs Jibo ki tuna min ina da meeting ƙarfe goma"

Ba tareda ta kalle shi ba ta ce to.
Ya sake fita amma ko taku biyar bai yi ba ya dawo.
"Mrs Jibo follow me"

"Ina zuwa"

"Follow me, now!" ya daka ma ta tsawa. Shi kam Anas ya gane kishi ke ran sa, tun ɗazu da ya fito ya ga irin kallon da ya ke ma sa kaman zai mangareshi.

Farida ta tashi da sauri ta ce " ina zuwa Yaya na"

Sai da su ka fita Anas yai dariya ya ce "muje zuwa Najeeb, da kan ka za ka hanata aikin nan"










*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣2️⃣6️⃣



*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi*




Har su ka isa second floor bai ce ma ta komai ba. Bin shi kawai ta ke yi amma har su ka dawo ba abinda ta ma sa. Su na dawo wa ta ce "Sir Najeeb dama ba abinda zan yi shi ne ka hana mazauna na su samu hutu"

"Dama hutu ki ka zo yi ne?"

"Sir Najeeb its not fair, ina zaman-zamana kawai ka zo ka tasheni ,na yi ta bin ka kaman wanda aikin bodyguard ka ɗauke ni"

Kafin ya ba ta amsa wayarta ya fara ringing.

"Your Ray?"

"To ba shi ba ne, Yakubu ne" ta faɗa tana picking call ɗin ta yi waje.

Shi ma ɗin ɗaukan waya yai ya kira Anas. Lokacin da Anas ya zo ya ce "ango-ango, ka gama yawo da amaryar ta kan. Can we discuss business"

Najeeb ya ɗan gyara zama ya ce "wannan Architect Yakubu ɗin whats his surname?"

"Yakubu Musa Wase"

"Ok"

Anas ya kalli reaction ɗin Najeeb ya kwashe da dariya yace " ba dan ka ma sa ƙwace ba da yanzu shi ne angon Farida"

"Kar ka ƙara cewa na yi ƙwace. You and Dad force me into this marriage"

"Ayya! Ashe abinda ya faru kenan ko. Sorry Najeeb angon Aisha"

"Cut this bullshit, ya ake ciki?"

"Dama maganar hutun ƙarshen shekara ne, ta ya za'ayi a gama duk wasu major project da mu ke da su a ƙasa kafin lokacin?"...

Tana duba wasu takardu sai ga mutum ya shigo ma ta office da sallama. Ɗagowar da za ta yi sai ga Rayyan.

Ta miƙe tsaye da sauri. "Rayyan lafiya?"

"Kin ƙi ɗaukan waya ta Farida kuma na ji labari kin fito aiki"

"Wato stalking ɗina ka ke yi?"

"Farida ki zauna ma na mu yi magana"

"Wanni maganan za mu yi?, ni fa matar aure ce Rayyan"

"Exactly, matar Rayyan ya kamata ki zama ba ta Najeeb ba. Duk abinda yai ya yi ne da sanin kan shi dan ya raba mu. Idan ba rashin sanin darajan mace ba, ta ya zai auri mace kamar ki just one week ya dawo da ke aiki, aikin secretary"

"Rayyan dan Allah ka tafi. Ka ga miji na na nan"

"Miji? My Farida miji fa ki ka ce. Ina ki ka saka alƙawurran da mu ka yiwa junan mu. Tun yanzu har kin fara cin amana ta kenan"

"Yau na ga ta kai na, Rayyan duk alƙawarin da na ma ka ba wanda na saɓa aciki, Na yi alƙawarin mallaka ma ka zuciya ta da duk soyayyata idan mu ka yi aure. Kuma ba mu yi aure ba mi ya kawo maganar cin amana a nan?"

"Saboda yana da kuɗi ko?"

" yes, saboda ina da kuɗi"

Su ka jiyo muryan Najeeb a bayan su.


"Daɗin abin ma sai dai mutum ya bi gefe yai zagon ƙasa amma bai isa ya tunkari mace ya nemi soyayyarta ba" Rayyan ya faɗa yana yiwa Najeeb kallon banza.

Najeeb ya ƙaraso kusa da shi ya ɗan buga kafaɗar sa ya ce " mutumina ka ɗan je ka ɗauki darasi a kan virtual reality ka ji"

Ya miƙawa Farida hannun sa guda ɗaya ya ce " Mrs Najeeb Jibo shall we"

Farida ta haɗiye miyau saboda kan ta ya ɗaure amma indai dan ta yi abinda zai sa Rayyan ya fita a rayuwar ta ne to za ta yi. Duk da ta so Rayyan a baya, amma yadda ya shure watannin da su ka yi tare ya fasa auren ta ana saura kwana biyu ɗaurin aure ya sa tana jin ko da akwai burbuɗin son shi a tareda ita to za ta kaɗe shi ta huta. Ko da ba ta auri Najeeb ba Rayyan ya dawo, to ba za ta iya auren sa ba bayan ya riga ya watsa ma ta ƙasa a ido.

Ta sa hannun ta cikin na Najeeb tareda matsowa ku sa da shi, maimakon ya tsaya a haka sai ya jawo ta jikin sa sosai. Ya kalli Rayyan da yai mutuwar tsaye a wajen saboda kishi ya ce " please feel free to visit Najeeb constructions some other time, yanzu Mr and Mrs Jibo za su huta. So get out"

Yadda ka san an sace balon-balon (balloon) haka gwiwar Rayyan ta yi sanyi. Yana son Farida sosai tun ranan da ya fara ganin ta a Keke kuma har yau yana son ta, hotunan da ya gani su suka birkita ma sa tunani ya rasa gane kan sa, musamman da ya kasance dama mahaifiyar sa ba son Faridan ta ke ba, ta dai haƙura ne a lokacin dan ba yadda za ta yi.

Juyawa yai zai fita dan bashida ta cewa a wajen. A yadda ya ke ganin su zai iya shaƙe Najeeb a wajen.

"One more thing, dont ever call Mrs Jibo again"
Rayyan ya ji wani abu ya suke shi a ƙirji. Ya haɗiye miyau da ƙyar sannan ya sa kai ya fita.

Rayyan na fita Najeeb ya ture Farida gefe.

Ta ɗan yi ƙara ouch.

"Sir Najeeb za ka karya min ƙafa"

Fiskar nan ba wasa ko kaɗan ya ce " kar ki sake kawomin tarkace office"

Ta gyaɗa kai saboda yadda ta ga ya ci serious.

Har aka tashi ranan Najeeb ba shi da walwala. Tana ganin ya fito zai wuce gida ta yi saurin bin bayan sa. Bai ma ta magana ba har su ka isa gida itama ba ta ce komai ba dan yunwa ta ke ji.

Shi ne ya fara shigewa ciki ita kan zuwa ta yi ta ɗebi abinci kafin ta haura sama da tray a hannunta.

Tana shiga ta gan shi tareda Najdah, Najdah na nuna ma sa hoton abu a wayarta wai ya zaɓa ma ta.

Sallama ta mu su amma ba ta ji an amsa ba, ko da kuwa an amsan to aciki su ka yi.

"Amsa sallama yana daga cikin haƙƙin musulmi akan ɗanuwansa musulmi"

Najdah ta ɗaga ido ta kalleta sai kuma ta sauke ido. Shi kam Najeeb bai ce komai ba ya san fitina ta ke nema and he's not ready for that.

Ta ajiye tray ta shiga banɗaki ta watsa ruwa, lokacin da ta fito Najdah ta fita. Ba ta san mi ya sameshi ba amma ta ga ko kayan jikin sa bai cire ba ya miƙe akan gado yana kallon sama.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?" Shiru

"Sir Najeeb ka tashi mu ci abinci"

Ta gama duk surutun da za ta yi amma bai ce komai ba sai daga baya ya tashi ya shige banɗaki...

.....................


Sati ɗaya kenan da fara zuwa aikin ta, ba za ta ce komai na tafiya dai-dai ba ba za kuma ta ce akwai matsala ba. Yawanci ma Najeeb ba ya zama a office ya kan fita supervising ayyukan da kamfanin sa ke yi kuma ya ke so a ƙarasa kafin hutun ƙarshen shekara.

Safiyar yau da ta shiga kitchen ta samu Mom na decorating wani chocolate cake, sai ƙanshi ya ke yi.
"Mom wa ke birthday?" Ta tambaya.

"Ya kamata a ci taran ki tunda ba ki san birthday ɗin waye gobe ba" Mom ta faɗa tana murmushi.

"Najdah?"

Mom ta girgiza kai, Farida ta leƙa cake ɗin ta ga shekarun da aka rubuta "wai-wai ashe na babban mutum ne"

Mom ta yi murmushi ta ce " he likes chocolate cake"

Farida ta ce "Ayya, cake ɗin ya yi kyau kuma"

"Akwai surprise family dinner da za ayi gobe da yamma. But dont tell him, idan ya sani ba zai zauna a gida ba"

"Allah ya kaimu gobe Mom"

....................

Safiyar asabat bayan ya iddar da sallah bacci ya koma. Haka kawai ta tsinci kan ta da kallon kyakykyawar fiskar sa, ta jima tana kallon sa, she cant believe he's 35yrs. Gaskiya jindaɗi da hutu na ɓoye shekarun mutum...

Da ta ɗan tattare ɗakin sai ta fita dan ta taimakawa su Adama da aiki.

Lokacin da ta dawo ɗakin kusan azahar ya riga ya fita. Ta buɗe akwatin kayan ta tana duba kayan da za ta sa. Mom ta ce iyalen gidan Uncle Sulaiman za su zo ga su Hajia Fatima, dole ta yi shigar da ba za a raina ta ba. Tana cikin duba wannan ta ajiye

Please Login or Register in order to submit comment