Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma kana lik'ewa B'arauniya.”
"Kema dai kya fad'a, ni wallahi banga abin so jikin Hannatu ba ga Subai'ah son kowa k'in wanda ya rasa. ”
Cewar Amma da fitowarta kenan daga band'aki.

Yana shiga d'aki kan katifa ya fad'a zuciyarsa tana masa wani irin zugi, to wani balai HANAH ta janyo da Umma take fad'a? Babu me bashi wannan amsar a yanzu, hakan yasa ya zurfafa cikin tunani.



*****


Abba kuwa ya sha duka gurinsu domin sunyi² ya basu number wanda ya haddace yace shi sam bai haddace number kowa ba hakan yasa suka masa dukan tsiya saboda wayarshi sam tak'i amsar chagi sai a yau suka samu wayar ta d'auka.
Tambayarshi sukayi akan wa zasu kira yace su kira Papa.


A lokacin shikuma yana hanyar zuwa gida, wayarshi ta d'au k'ara, ganin sunan wanda yake kiranshi kan screen d'in wayarsa yasa shi gangarawa bakin titi da hanzari yayi parking, kafin yakai ga yin picking har ta tsinke, yana k'ok'arin bin baya wani kiran ya kuma shigowa, ringing d'aya ya d'aga.
"Hello D'ahiru kai kwa ina ka shiga kwata².....”
"Dakata malam” Yaji muryar da ba ta d'ahiru ba an katse masa magana.
"Ba wanda kake zato bane, d'an uwanka yana hannunmu idan har kuna son shi da ranshi sai kun kaho mana million goma, idan kun shirya bayarwa kuna iya biyo layinnan.” K'it ya kashe wayar, daskarewa Papa yayi daga zaune ya kasa ko da motsi, Million goma, yanzu ta ina million goma zata fito? abinda yake ta sak'awa kenan a ransa, ganin zaman bazai masa ba yasa shi jan motarsa yayi gaba.



****
HANAH tana samun kulawa sosai gurin Momy a cikin kwana biyu rak da tayi cikin gidan, matsalar zamanta cikin gidan Hindu ce da Mama suke jifanta da karuwa ko kuma suce mata B'arauniya, saboda Momy da taga suna cemata karuwa, har suna cewa Momy ta goyawa Haisam baya ya kawo karuwa cikin gida kuma ta rik'eta, hakanne yasa ta zaunar da Mama ta bata labarin Hanah, me makon suji tausayinta sai sukace ai Momy aka rainawa hankali ya d'aukko karuwa zaice wani taimako yayi, don haka suka cigaba da jifanta da karuwa, ko kad'an bata tab'a kulasu ba bare ta nuna tasan suna yi, saidai kawai bata zuwa falo cin abinci sai dai Momy ta kawo mata d'aki taci. Amma kuma a k'asan zuciyarta tana son taji ya alak'ar wannan zuri'ah take? Domin tana ganin wasu al'amura suna faruwa a cikin gidan, abu d'aya ta sani da Rumanah tace mata Daddynsu baya nan.

Shirye ² bikin Rumanah kawai sukeyi gashi yau saura kwana uku bikin kuma har yanzu Hisham bai daho ba yace musu dai gobe zai daho.

Fitowa sukayi zasu je anso d'inkunan HANAH da na Rumanah na biki, a cikin mota suka ga Haisam, Hindu na jikin motar ta tsuguna tana tayi masa magana shikuma ya lumshe idonsa, yayi kamar baisan tana gurin ba, tana hangosu ta auna musu wata shegiyar harara, HANAH d'auke idonta tayi itakwa Rumanah ta zabga mata harara taja tsaki a ranta tana wahalalliya kawai, itama Hindu tsakin taja tace.
"Banzaye karuwai.”
Jin abinda tace yasa Haisam bud'e idonshi aikwa k'wayar idonsa ta samu kyakkyawan masauki cikin ta HANAH, yana sani ya sakar mata kyakkyawan murmushin da ba kowa ke samun irinsa ba, itama ba tasan ya akaiba ta tsinci kanta da maida masa da martanin murmushinsa, bud'e mata murfin motar yayi yayi mata alama da ido, ta shigo ciki, juya idonta tayi wanda ya bada damar ganin d'igon baki a tsakiyar farin idonta sannan ta shiga motar, wani irin abu yaji ya dakar mishi zuciya, rank'wafowa yayi ya janyo murfin motar ya rufe, lumshe idonta tayi saboda wani k'amshi da ya ratsa ta k'ofofin hancinta. Da kallo Hindu ta bisu dashi cike da b'acin rai tana wani irin huci, kallonta Rumanah tayi ta sakar mata murmushin mugunta gami da d'aga mata gira d'aya kana tace.
"Kinga irin salon karuwan ko?” Bata jira me zata ce ba ta shige gidan baya, tana shiga shikuma yaja motar ya buleta da k'ura, wani haushi ne da takaici yazo mata iya wuya, d'aga idon da zatayi sukayi ido biyu da Mama ta saman taga ta auno mata wani shegen kallo na ke kika kai kanki ba wani ba, ai ko soyayyar Haisam zata kasheki bazan bari ki aureshi ba bayan na gama illata mishi rayuwa.
Cikin gida ta shige da gudu tana fashewa da kuka.


Sai da suka hau kan titi suna tafiya sannan yace.
"Ina zaku je?” ya fad'a idonshi a kan hanya don tunda suka bar gidan bai kuma kallon inda suke ba, dama yayi hakanne don ya k'ular da Hindu, kuma Alhamdlillah ya hangi tashin hankali tsububu cikin k'wayar idonta.

"Fage zamu je anso d'inki. ” Cewar Rumanah, bai magana ba ya d'auki hanyar da zata sada shi zuwa fage........


Na samu ta d'auki chagi, muci gaba da lallab'awa kafin sabuwa tazo.

Mahaifina baya da lafiya ina neman tarin addu'arku, Allah Ubangiji ya bashi lafiya ingantacciya.

I love u Maman Mash hud na baki wanga page kyauta.
[12/10, 17:54] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


*Daddy's Girl naga sak'onki, kamar yarda kika ce akwai uzurirrika to tabbas uzurin ne ya hanani yimuku typing, k'anwar mahaifiya tace ta ràsu ina cikin alhinin mutuwa sosai, wa'yanda sukaimin ta'aziya ina matuk'ar godiya Allah yabar zumunci, ita kuma Allah ya jik'anta ya gafarta mata muma in tamu tazo Allah kasa mu cika da imani, Allah ubangiji ya dubi abinda ta bari, ya tallafi rayuwarsu, Allahuma Amin.*
*Ina matuk'ar yinki Daddy's Girl fiye da yarda kike yina.*
__________________
*NINETEEN*
Jin cewa kidnappers ne suka kama Abba kuma har sai an bada million goma sannan za'a sakeshi hakan yayi mugun d'agawa kowa hankali, gashi daga gurin aikinsa sai zuwa nemansa ake ba'a samunshi, sun saka an rufe Account d'inshi gaba d'aya.
Harhad'a kud'in aka shiga yi amma ko million biyu ba'a had'a ba hakanne yasa aka saka gidansu a kasuwa.


Hamid kuwa da Ammi ta bashi labarin halin da ake ciki hankalinshi yayi mugu mugun tashi, a ranar wuni yayi yana bin prison² neman HANAH amma har dare bai sameta ba, a wahalce ya dawo gida yazo ya tarar ana ta cuku cukun had'a kud'in fito da Abba, Papa ne yace.
"Hamid bani A. T.M d'inka zan ciri kud'i. (Saboda yana ajiye kud'i a account d'insa.”
Yasan me zaiyi da kud'in, tunda kud'in ciki suna da mak'udan yawa shi kansa baisan adadinsu ba, don haka sai cewa yayi.
"Banzo da shi ba, na mantosa a can.” Cikin ido ya kalli Ammah yace.
"Meyasa ita wacce ta saci jaka a d'akinsa baza ta fito da ita ba aje a karb'osa? Domin wallahi summa tallahi ba HANAH ce ta saci jakar nan ba, k'ullalliya aka k'ulla, kuma naci alwashin sai na warware wanna k'ullin da aka yiwa rayuwar marainiya, ko ta Allah ta kasance a kaina ban cika burina ba na tabbata akwai wanda Allah zai aiko ya share mata hawayenta ya zame mata mijin marainiya, hak'k'in marainiya yanzu ku ka fara saka k'afa tukunna dai. ” Yana kaiwa nan ya shige d'aki ya kullo, domin baya buk'atar amsar da zasu bashi.

Shiru kowa yayi kamar ruwa ya cinye, kowa ya shiga sak'a a zuci.

'Wai ni yaron nan bincike yake yimin ne, komai nawa ya sani, to shin ta ya yasan ni na d'au jakar?' Amma ta tambayi kanta wanda bata da me bata wannan amsar a kusa, ita tashin hankalinta ma tunda ta kira Buwaya ya ta bashi jakar bata sake jin d'uriyarsa ba, ko da ta kira wayarsa a kashe ake ce mata.

Gyaran murya Papa yayi yace.
"A cikinku waye ya d'auki jakar? ”
Kowa cewa yayi ba shi bane.
"Tom shikenan sai mu jirayi a sayi gidan tunda nima ba kud'ine a hannuna ba dama Hamid yazo da ATM d'insa ne da sai a cira a ciki to ya manta sa a can.”
yana gama fad'in haka ya tashi ya fita.

*
Zazzab'i me matuk'ar zafi ne ya rufe Hamid, sosai yake jin jiki amma haka ya nemi jirgi ya juya Sudan, dan ji yayi gaba d'aya garin yayi masa matuk'ar zafi, gashi dama ba hutu ya samu ba ya taho.




____

Yau har kusan 12 na dare Haisam bai shigo gida ba, raban da yakai dare a waje irin haka ya d'an jima, shiyasa hakan ya tada hankalin Momy ga matsanancin ciwon kai da ya addabe ta, magani HANAH ta b'allo mata ta bata tasha.
"Momy ki kwanta idan kika d'an samu bacci zaki ji kan naki ya saki da yardar Allah, ni zanje falo na zauna har ya shigo. ”
"A'a yi kwanciyarki Hannatu, zai shigo ai ba yaro bane. ”
"To ai Momy bai ci abinci ba, nidai zan jira shi har ya shigo, hankalinmu zaifi kwanciya gaba d'aya. ”

"Tom shikenan jeki tunda kin nace, idan kika d'an jima bai shigo ba kizo kiyi kwanciyarki, in na samu baccin ya d'aukeni to.”

"Tom shikenan Momy Allah ya sawak'e.” Tana fad'in haka ta juya ta fice."Amin” Momy tace tana binta da kallo cike da jin sabuwar k'aunarta a ranta.


Zama tayi a falo ta zuba uban tagumi da duka hannuwanta biyu tana tunanin rayuwa da abinda yake zagaye da ita, can ta d'an nisa ta mik'e tana hura iska a bakinta, zagaye falon ta shiga yi tana ta kaiwa da komowa, tazo wajen tagar d'akin Harris taji uwa magana, kuma nutsuwa tayi ta bada dukkanin hankalinta don taji me ake cewa, muryar Harris taji yana.
"Ai gobe Hisham d'in zai dawo, don haka dole ki san yarda kikai kika zuba mishi maganin nan yaci, tunda a nan zai sauka, naji labarin mahaifinshi ya koreshi.
Dama shine yake b'ata mana dukkanin wani shiri da zamui akan Haisam, yanzu ma zancen da nake miki a can k'asar da ya tafi asibiti yake gina musu shi da Haisam, kinga idan ya auri Hindu kakarmu ta yanke sak'a, zamu janyeshi daga jikinsu ya daho jikinmu hakan zai bamu damar cigaba da lalata rayuwar Haisam.”
Murmushi Mama tayi, tace.
"To k'arfe nawa zai sauka? ”
"K'arfe d'aya naji ance zai sauka, kinga k'arfe biyu muke yin Dinner.”
"OK to tun yanzu zan bawa Kulu maganin, ta tabbata ta zuba shi a gefen da zatayi Saving nashi. ”
Barin bakin window d'in tayi zuciyarta tana ta auno mata tambayoyi iri² wanda take matuk'ar jin amsarsu amma sam bata son tambaya saboda bata son shiga abinda babu ruwanta, kan kujera ta koma ta zauna bata jima da zama ba Haisam ya bankad'o labule ya shigo, idon shine ya fara sauka cikin na HANAH, janye idon shi yayi ya nufi hanyar d'akinshi.
Bakinta taji yayi mata matuk'ar nauyi ta kasa yimasa magana har sai da yayi nisa sannan ta iya bud'e baki da k'yar tace.
"Abinci fa?” Ta fad'a da d'an k'arfi yarda zai iya jiyota, wani kallo ya auno mata, wanda yasa jikinta b'ari, don sosai ta tsorata da yanayinsa don taga alamun baya cikin hayyacinsa, da azama ta juya ta nufi d'aki.
Ta tarar Momy tana barci don haka itama sai ta kwanta daga gefenta ta shiga tunanin rayuwa iri².



________

K'arfe d'aya da kusan rabi Haisam yaje ya d'aukko Hisham daga filin jirgi, suna zuwa gida wanka yayi ya sauke farali, sannan suka fito cin abinci, kowa ya hallara suna zama Kulu da Sahiba suka fara saving nasu.


Tana d'aki tunanin duniya ya addabeta, yanzu tana ji tana gani zata bari a cuci Yayan Rumanah da ta zame mata garkuwa a cikin rayuwarta, kuma ta dad'e da sanin k'aunar da Rumanah take yiwa Hisham ko mahaifinta bata yiwa irinta.
Mik'ewa tayi ta fita, ta kasa yankewa zuciyarta yarda zatai ta kub'utar da Hisham kar yaci abincin nan, kawai ji tayi ta k'walla masa kira.
"Yaya Hisham”
Tsayawa yayi dakai lomar abincin da zaiyi ya tsaya yana kallonta...........
[12/10, 17:55] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


__________________
*TWENTY*
Cigaba yayi da kallonta yayin da ita kuma gaba d'aya ta rikir kice ta rasa abinda zatayi, iska ce ta kad'a labulen window d'in falon ta hango Rumanah na tahowa da launching box a hannunta, hakanne yasa ta jin k'arfin guiwar k'arasawa gabanshi tana sakin murmushi, janye plate d'in gabanshi tayi, shikuma sai binta yake da ido.
'Bai santa ba, gashi ita har tasan sunanshi, to shin wace it a?'
"Rumana ce tace kar ka d'and'ana abincin kowa, ta yomaka girki na da ban”
Muryarta ta katse mishi tunanin da ya tafi, a lokacin Rumanah kuma tayi sallama, wani banzan kallo Mama take jifansu dashi tana ankare da ita, d'aukar plate din tayi ta nufi hanyar kitchen dashi tana sakarwa Rumana murmushi, murmushin itama ta sakar mata,babu wanda ya kula kowa tayi shigewarta kitchen, cikin dustbin na juye abincin nayi fitowata, ina fitowa mukai ido hud'u da Mama ta auno mini wani banzan kallo, d'auke idona nayi na nufi hanyar d'aki, ina kallon Rumana na Saving d'in Ya Hisham, tana gama saving nashi naji tana k'wallo mini kira nazo muci abinci, Mommy ce tace mata.
"Ki d'auka kuje d'akin kuci, don ita bata cin abinci anan."
Murmushi tayi ta d'auki plate ta zubo mana, tuwon farar shinkafa ne da miyar agusi da ganda, ( Abincin da take fara saukarshi dashi kenan a duk sailin da yayi tafiya.)

Mama da Harris takaici yazo musu iya wuya, Mama ji take yi kamar ta shak'oni tai ta jibgata, ina zaune bakin gado farin ciki fal raina nayi sanadin da Ya Hisham baici abincin nan ba, Rumana ce ta shigo tana. "To sai ki sakko muci” Ba musu na sakko muka hau ci, muna d'an tab'a hira, tana tambayata dalilin da yasa bana fita dining.

Bayan gama cin abincinmu Ya Hisham suka keb'e da k'anwarshi, anan yake tambayarta wace ce ni, tayi masa bayanina, murmushi kawai yayi suka cigaba da yin hirarsu wanda duk rabi akan shirye²n bikin Rumanan ne.




_____

An sayi gidan Abba akan 15 million, Amma ta bada shawarar a tafi da million biyar ko zasu ansa, papa yayi musu waya suka fad'a mishi inda zai kai kud'in, kuma suka ce ya taho da mace akan sharud'a.
Da Amma suka kama hanya suka tafi, ko da ogansu yaga kud'in yace bai kai million goma ba, ba musu papa yace.
"Eh million biyarne.”
Wata dariya yayi, yace. "A d'ad'd'aure su suma a basu matuk'ar azaba, sai nan da kwana biyar zan waiwayosu."

Yana fad'in haka ya b'acewa ganinsu, tashin hankalin wanda ba'a saka mishi rana, daga Papa har Amma sun tsure, Amma cikinta sai wata iriyar karta yake, d'ad'd'auresu yaran sukayi suka jasu cikin duhuwar wani guri.


Ammi da Umma suna ta jiran ganin Abba, sai gashi har dare babu Abba babu labarinshi, babu wayanda suka tafi fito dashi, hankalinsu idan yayi dubu ya tashi, sun kasa tsaye sun kasa zaune har zuwa dare babu labarinsu, kasa daurewa Umma tayi, ta kira wayar Hamid ta sanar masa, shima hankalinshi yayi mugun tashi, don tunda ya tafi ba wata isasshiyar lafiyace dashi ba, a lokacin ya ta shi ya nemi ticket d'in jirgi ya biyo jirgin asuba washe gari.


____________
Idan har aka sakawa abu rana, to tabbas ranar nan kamar k'ara mata gudu ake, dama dai wuyarta dai a saka.
Yau take Friday. Juma'atu babbar rana, yaune dinner d'in gidan su Sadiq, gobe kuma za'ai pherty da yamma wanda Baffa ya had'a, da daddare kuma ayi Dinner d'in da yayyanta suka had'a mata wato Haisam da Hisham.
Wani d'an ubansun less ta saka blue black har abun d'aurin tayi matukar kyau, shima Sadiq ya saka blue black din shadda, sunyi kyau sosai sun bada kala ainun, nima less din na saka blue, riga da zani aka yimin wanda ya anshi jikina sosai, nayi kyau dai ba laifi.
A motar da za'a d'auki amarya muka tafi, ina gaba ni da abokin Sadiq me suna Sadam, wanda ya mak'ale mun tun daga farkon fara bikin nan, ni besan zuciyata mutum d'aya take so ba, kuma shi zata cigaba da so har k'arshen numfashina.
'Allah sarki Yaya Hamid, ko ya yaji da ya dawo ya tarar bana nan?' Ji nayi k'walla na tarar mini a ido, nayi saurin mai data don kar ta b'ata mini kwalliyata.
"Sahibati lafiya?” Rumanah ta tambayeni da suke baya ita da angonta.
"Lafiya lau, me kika gani? ”
"Kawai zuciyata ce take gayan kamar zuciyarki ta motsa. ”

"Hmmmmm” kawai nace ina zamewa jikin kujerar yarda zanji dadin zaman, ina kallon Sadam yana d'an satar kallona na kuma d'aure fuska, itama bata kuma ce dani komai ba har muka isa gurin Dinner.
Anyi dinner sosai ta k'ayatar, dangin Sadiq sai ririta Rumanah suke yi, kakarsa ce ma tayi mata kamu.

Ko da muka dawo gida k'anwar Auntyn su Rumana ce ta dinga takalata da fad'a, don tunda aka soma bikin na dawo gidan su Rumanah da kwana.
Ashe wai ita so tayi so tayi Rumanah ita ta janyo ta zamo mata babbar k'awa, ita kwa Rumana ko kallo basu isheta ba mu biyu kawai muke sabgarmu, hakanne yasa take jin haushina, ga kuma Sadam da take so ya manne mini, ni kuwa dama ban bashi fuskar da zai kawo mini zancen so ba.


Washe gari da yamma aka yi pherty, yayi kyau sosai, shigar perpul Rumana tayi, ni kuma nayi shigar pink, k'arfe takwas dai² munyi shirinmu na diner, Rumana shigar goldin tayi nikuma nayi shigar black nd red, Sadiq ne Sadam suka zo muka tafi, shima yayi shigar golding.

Gurin diner yayi kyau, musamman ma da ba wani cika akayi ba, tunda kaf dangin su Baffa ba wanda yazo sai Shukura k'anwar Aunty, sai 'yan tsirarru daga dangin su Sadiq, sai k'awayen Rumana da abokanan su Ya Hisham.

Black d'in suit suka saka iri d'aya, tayi matuk'ar kyau sai k'yalli take da shek'i, ta anshi fatarsu ta fito misu da sirrin kyahunsu da samar takarsu, shigowarsu gurin tasa zuciyoyin 'yan mata harbawa, zuciyar Shukhura kuwa da taga Haisam tsayawa tayi cak da aiki.

Wak'a ta musamman DJ ya saka musu, aikwa nan suka shiga b'arin kud'i, Hisham yana yi yana rausayawa, ina gefe ina kallonsu ina murmusawa had'a ido mukayi dashi ya yafito ni da hannu, k'arasawa nayi kusa dasu, ya kawo bakinsa saitin kunnena.
"Kiyi rawa”
Murmushi kawai nayi, don ni a rayuwata ban iya rawa ba, kawai sai ji nayi ya rik'e hannuna yana rausayawa dani, zaro ido nayi ina kallonshi ya kashe mini ido d'aya, ina kallon Rumana tana mini dariya, Haisam idonshi dake sanye da gilas ya shiga yimana b'arin kud'i nan guri ya kuma hautsinewa bare DJ da yaga b'arin kud'i ko ta ina.

Yana gama lik'in fita yayi ya koma mota, don yasan yanzu 'yan mata mara sa aji zasu baibayeshi, duk da hakanma sai da wasu suka zo suka tsaya gaban motarshi, Allah yayi mishi farin jinin 'yan mata birni da k'auye, amma shi sam basa gabanshi, gani yake tsayawa yin soyayya ma b'ata lokaci ne, ko aure zaiyi, zaiyine dan raya sunna ba dan soyayya ba.
Diner tayi kyau sosai, anci me kyau an sha me kyau an kuma tafi da me kyau, abin ba'a cewa komi sai wanda ya gani.


Washe gari kuma misalin k'arfe goma sha d'aya na safe aka d'aura auran Rumanah da masoyinta Sadiq, bayan gama d'aurin aure daga nesa daga gidan su Hisham suka tsaya, yana kiran wayar Rumanah akan ta fito ayi musu hotuna amma sam batayi picking ba, Haisam ne yace.
"Bari naje na saka a kirata ”
"Ok” yace yana jin wani d'aci a zuciyarshi, tabbas rashin mahaifiya babbar musifa ne domin itace jigon rayuwar d'anta.

Riga da zani na grine d'in shadda Rumanah ta saka an mata adon pink din stone tayi kyau sosai, nikuma doguwar riga na saka ta yaluwar shadda da akamun storne work da red d'in stone, nayi kyau sosai, bayan an gama hotuna da angwaye Rumanah tace mun.
“Bari naje gurin Baffa yana kirina”
"Tom ” nace mata.
Tana barin gurin sai ga Shukhura a gabana ta zabga mini mari, hawaye da basu da control a idona tuni sun fara tsiyaya.
"Dama b'arauniya ce ke? Tun jiya nake neman zobena sai gashi yanzu na ganshi cikin jakarki, to billahillazi sai kin bar gidannan baza ki kassaramu ba tunda Allah ya toni asirinki.”
Kukana ne ya kuma k'arfi jin dalilin da yasa ta zabga mini, na zaci kwanciyar hankali tazo cikin rayuwata ashe zatona be zama gaskiya ba, kaico da zuciya mara imani da take janyo mini wannan k'ask'anci cikin jama'a.Jakar kayana ta d'aukko ta cillo mini, babu wanda ya hanata abinda take mun.
"Fita ki bar mana gida. ”
Ko yane na kasa motsa k'afata guda d'aya bare na iya tafiya sai uban kuka da nake risga,hankad'oni tayi gaba d'aya, dai ² lokacin Haisam ya bud'e get d'in gidan ya shigo, idonsa ya sauka a kaina zan fad'i, da azama ya isa gareni ya tallafoni jikinsa, wanda na riga da na sadak'ar goshina ya gama fashewa, d'ago da fuskata yayi yana kallon idona da yake a rintse yana d'igar da hawaye, sai ji kake k'yas an k'yasa mana photo.......



Barkanmu da sake saduwa.

Duk me docm na littafina RABEE'AH da kuma HEENAH pls send me.
09037093702
[12/10, 17:55] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama Kwaise

______________
*TWENTY ONE*
Cikani yayi daga rik'on da yayi mini na sunkui da kaina ina cigaba da d'igar hawaye, kyakkyawan mari Haisam ya bawa Shukura da ya sakata d'auke wuta lokaci guda, murza hannunshi yayi ya nunata da 'yatsa bai magana ba ya juya ya fita, nima bin bayanshi nayi ba tare da na d'auki jakar kayana ba.

Tana cikin azabar marin Rumanah ta fito daga b'angaran Baffa, akan jakar kayana idonta ya fara sauka, gabanta taji ya yanke ya fad'i da sarsarfa ta k'araso gurin tana bin mutanen gurin da kallo, musamman Shukhura dake rik'e da kunci.
"Me ke faruwa ne? ”

"Uwar kice take faruwa.”
Shukhura ta bata amsa tana k'ank'ance ido na azabar marin da bai saketa ba har lokacin, cizan leb'e kawai Rumanah tayi ta isa gurin jakar kayana ta d'auka ta nufi ciki, tsaki Shukhura taja.
"Mtssss anje an d'auko mana jaraba, ashe b'arauniya kika kwaso mana, wa ya sani ma ko a tsatson da uwarki ta fito kikaje kika kwaso....” Kan ta k'arasa Rumana ta dira gabanta ta kifa mata gigitaccen mari, ta rufeta da duka ba ji ba gani idonta a rintse, fad'ane ya kaure musu sosai, nan mutane suka shiga kiciniyar rabasu amma Rumanah tak'i sakin Shukhura sai jibgarta take, Aunty ce ta fito da gudu tayo kan Rumanah ta rifeta da duka, sakin Shukhura tayi ta koma kan Auntyn nanfa fad'a ya rikice mutane suna ta rabasu sunk'i rabuwa, su biyu sun had'arwa Rumana, da gudu Nihal taje ta kirawo Baffa.
Yana daka musu tsawa kowa ya shiga taitayinshi, suka tsaya suna maida numfashi, Rumanah ya kalla yana zabga mata wata muguwar harara.
"Yanzunnan na gama

Please Login or Register in order to submit comment