Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana k'ok'arin danno k'ofar d'akinshi Allah ya bata sa'a ta fad'a ciki, idon sane ya juye, ya daka mata tsawa. "Fitarmun daga d'aki.”
Jikin tane ya fara kyarma da hanzari cikin dakiyar zuciya ta yayyafa mishi ruwan maganin nan da Malam Jafar ya bata, ai kwa cikin 'yan mintina kad'an ya tafi luuu ya zube a gurin.



Tambayarta inda ke mata ciwo yayi, ta faffad'a masa, har da rashin k'arfin jikin da take fama da shi, yace"Kinci abinci?” Ta girgiza masa kai, don sai a lokacin ta tuna jiya ko abincin dare bata Ciba, waya yayi aka kawo mata abinci, aikwa taci ba laifi, sannan ya bata magunguna tasha, yayi mata allurar zazzab'i, yayi treatment d'in goshinta ya manna mata plasta, yace ta kwanta akan gadon da ke ofis d'in nasa ya jona mata ruwa, don tana buk'atar k'arin ruwa, aikwa bacci ne me matuk'ar dad'i yayi nasarar sace ta, wanda ta jima ba tayi irin sa ba, k'afar tace dai bai tab'a mata ba, don ba aikinsa bane, sai dai ya kira a duba mata.

Inda Allah ya taimake ta cikin bacci akai mata gyaran k'afar don tayi tsami sosai, gocewar k'ashi ne har sai da aka d'aure da bandeji.



******

Har aka tashi daga makaranta babu su Suhanah, don haka sai tai tunanin ko gida ya huce da ita, don haka sai ta nufi gidan nasu don takai mata jakarta, ta kuma tabbatar da ta daho.

Babu kowa a falon nasu, don haka sai ta nufi d'akin Suhanah, don ko da ace ta tadda mutane a falon babu wanda zai kulata, wayam ta tadda d'akin, har toilet d'inta ta duba shima ba ta nan, ajiye mata jakar tayi ta fito, sukai ido hud'u da Amma, aikwa Amma ta sakar mata wata uwar harara, Rumana ba tayi k'asa a guiwar ramawa ba, aikwa Amma ta lailayo wata ashar ta danna mata, murgud'a baki kawai Rumana tayi ta fice.
"Shegiya 'yar matsiyata, na kuma ganin shegiyar k'afarki cikin gidan nan sai na karyata ”

Da baya Rumana ta dawo don maida martani.
"Sai dai ki nemi 'yar matsiyata a gurin ki, don ni na shige gurin, ko makaho ya shafani yasan daga gidan girma na fito, kuma ba dukiyar haram muke ciba, idan kin sake gani gidan nan ba k'afa zaki karyamun ki birgeni ba, duka sassan jikin zaki karkarya ki watsar, shine na san kin cika muguwar mace.” mtsss taja tsaki ta fice abinta.

Wata iriyar Ashar Amma ta lailayo ta zuba mata, tana hargagi tana d'aga jijiyoyin wuya, tana sai taga k'arshen rashin kunya rta, don sai ta saka an canja mata kamanni, d'akin Suhanah ta afka da masifarta sai taga wayam.
"Hannatu” Ta shiga rafka mata kira kamar zata tashi gidan, amma shiru kake ji, toilet d'in ta bud'e nanma taga wayam.


Tana shiga gida, b'angaran Hisham ta nufa, tana shiga ta tadda d'akin shi a rufe.
Tana shiga d'aki waya ta d'auka ta shiga kiran Hisham aka sanar mata a kashe.




******
Bayan ya fito daga theater office d'insa ya shiga ya kwanta, ko takan wayoyinsa bai biba bare ya kunnasu don wani matsanancin bacci yake ji.


Hanah kuwa ba ita ta farka ba sai la'asar,sai da tasha ruwa leda hud'u, baccin yayi matuk'ar yimata dad'i, wanda raban da tayi tamkarsa har ta manta, ko motsi ba tayi ba, Dr Salim ya shigo, ya daho daga sallar la'asar, idanuwansu ne suka sark'e tayi saurin kawar da kai.
"Har yanzu bai dawo ba?”

"Eh bai daho ba, na kira layinsa kuma a kashe, na kira Hisham naji ko suna tare shima nasa layin a kashe. ”

"Tom shikenan bara na tafi. ” ta fad'a tana mik'ewa da k'yar sai a sannan ta lura da bandejin k'afarta.

"A'a bara na saukeki gidan, nima gidan na nufa. ”

Wani sanyin dad'i taji, domin kwa ba ta da kud'in mota, ga k'afarta da take jinta kamar baza ta iya taka ta ba.

Abu buwansa ya har had'a sannan yace ta sakko su tafi, da k'yar ta iya sakkowa daga gadon tana d'ingisa k'afa, bango ta dinga bi har suka fito, sai da ya taimaka da rik'e hannunta sannan suka isa gurin motar.


****

"Ammi ina Hannatu? Yau alhamis bare nace makaranta ta tafi. ”

"Nima ban ganta ba, rabona da ita tun jiya. ”

"Amma tunfa safe, wani yazo har makaranta ya d'auke ta a mota. ”Cewar Subai'ah.

"A mota ” ta fad'a had'e da dafa k'irji. "Yanzu bayan satar harda bin maza zata had'a, so take ta kashemu da bak'in cikin ta, to wallahi tayi kad'an, dole ayiwa tufkar hanci tun kafin ta fyand'are tafi k'arfinmu, bari Abba ya daho, ina zaune a nan naga ta inda zata b'ullo.



Ta gaya mishi unguwarsu, da kwatance yakai ta har k'ofar gida, yana parking ya zago ya bud'e mata ta fito, hannu ya mik'a mata ta rik'e tana takawa a hankula har ya kaita bakin get d'in gidan, sannan ya mik'a ledar magani yace "Ki kula da shan maganin. ”

"Tom na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi.”

Amin yace ya sakar mata murmushi ya juya, ita kuma ta kama get d'in ta shiga ciki, ashe Abba yana cikin motarsa shaho kwanarsa kenan ya gansu rik'e da hannun juna, tsayawa yayi yana kallon ikon Allah har sai da ta shiga ciki.............
[12/10, 10:13] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


~GORON SALLAH~
____________________
*EIGHT EPISODE*
K'arfe biyu Hisham ya farka daga baccin da yake, toilet ya fad'a ya d'auro auwala ya gabatar da Sallar Azahar, sannan ya d'auki wayoyinshi ya kunna, yana kunnawa kiran Rumana na shigowa, da hanzari ya d'aga ya d'ora bisa kunne.

"Hello Yaya ina ka shigane? Tun d'azu nake kiran wayarka swhich up.”

"Bacci na samu nayi ne shiyasa, ya akayi ne? ”

"Dama cewa zanyi ka kira Yaya Haisam kaji ko ya maida Hanah gida ne.”

"Hanah, wace kuma Hanah?”

"Oh sorry na manta baka san zancan ba, k'awar nan tawa ce da nake baka labari, to itace tazo makaranta ba lafiya, to dama don ka duba ta na kiraka, shine ka turo mna Ya Haisam, shine na rok'i arzik'in ya kaita Asibiti ”

Jinjina kai yayi, lallai ba k'aramin sa'a Rumana ta ciba, har da Haisam ya yarda ya d'auki mace a motarsa , ko da yake yayi hakanne saboda ni, duk abin da yadanganceni Haisam yana bashi matuk'ar muhimmanci ko da bai son hakan a ransa.

"Tom shikenan, bari na tun tub'eshi naji. ”

"Yauwa Yaya na gode. ”

Neman layukan Haisam ya shiga yi, amma ko wani layi sai ace masa swhich up, wani tunani ne yazo masa, ya san babu gurin wanda zai kaita da ya huce Dr Salim, don haka sai ya juya akala zuwa kiran layin Dr Salim, amma sam network ya hanata wucewa, kawai sai ya harhad'a kayanshi yayo gida.


Rumana na jin k'arar bud'e get ta fito da gudunta, don ta san Yayan tane ya daho, Aunty tana ganinta taja tsaki, itama kuwa ta ja tsaki har da murgud'a baki, ta fice.

Ita ta rik'o mishi jakarshi da wayoyinsa, tana tambayarshi yarda suka yi da Haisam, yake sanar mata duk ya kira layikan sa a kashe, wanka zaiyi yaci abinci sai yaje gidansu ya duba shi.

Sai da ta raka shi har d'aki sannan ta juya don ta had'o masa abinci, shikuma ya shiga wanka.

Tazo zata shiga kitchen Aunty ta daka mata wata tsawa.
"Ke dan kan uwarki me zakimun a kitchen? Bayan Kin gama ja mun tsakin.”

D'an razana tayi, saboda tsawar tazo mata a bazata, ta k'ifk'ifta idanu daga bisani ta galla mata harara.
"Kitchen d'inki kuma, ke dan Allah ko kunya baki jiba, naga daga kitchen d'in har kayan ciki na Baffanmu ne, don haka banga wanda ya isa ya hanani shiga ba wallahi. ”

Hannu Aunty ta saka ta fizgota daga bakin kitchen d'in ta had'ata da bango.
"Yau zanga k'arshen rashin kunyarki, in taurin kaine da rashin mutumci nafi ki iyawa wallahi, sai dai kizo a bayan bayana. ”

'Yar siriyar k'ara ta saki, saboda taji zafin bugata da bangon da tayi.
"Allah ya isana wallahi, ni dama bana fatan na kaiki bare har na biyo bayanki, kuma kitchen banga wanda ya isa ya hanani shiga ba. ” Ta kuma yunk'urawa zata shiga, ita kuma ta sanya mata k'afa ta hard'eta, zubewa tayi a gurin k'afarta ta lank'washe aikwa ta saki k'ara me k'arfi saboda azabar da taji, tana daga zaunen ta sanya hannuwanta duka biyu ta kwashi k'afafuwan Aunty ba zato ba tsammani itama taji ta yaf a k'asa, aikwa itama ta bugu a bayanta sosai, cikin azaba tayo kan Rumana ta rufeta da duka.


Yana cikin band'aki yana wanka ya juyo k'arar Rumana ta farko, kafin yakai ga gamawa ya kuma jiyo k'ararta, cikin hanzari ya k'arasa wankan ya zira jallabiya ya fito, dole ne naje na dubota naga lafiya, duk da Baffa yamun katanga da shiga gidansa, dole ne yau na shiga, don bazan iya jure jin k'arar Rumana ba, banje naga a wani hali take ba.

Yana shiga ya tadda Aunty kan ruwan cikin Rumana tana ta jibgarta, hannu yasa ya fincike Aunty daga kanta, yayi cilli da ita, goshinta ya bugi bango nan take ya fashe ya fara jini, aikwa tana ganin jini ta saki kuka wiwi².

"Na hanaki kulata tun ba yau ba, nace ki daina shiga shirginta kink'i ji, gashinan zata je ta kasheki a banza tunda ita ba asararta bace. ”

"Nifa ba shirginta na shiga ba, wai dan kawai... ”
Dakatar da ita yayi gurin d'aga mata hannu, yaja hannunta zasu fice, karo sukayi da Baffa zai shigo, ja baya sukayi cike da shan jinin jikinsu, saboda yanayin kallon da Baffan yake jifansu da shi, yana shiga ya tadda Aunty da fashashshen goshi.

"Hisham” Ya k'walla masa kira da babbar murya.
"Na hanaka shigomun cikin gida, shine tsabar ka raina ni ka maidani ba a bakin komai ba ka shigo, to ka tattara komai naka ka barmin gida, kar ka sake ka kuma danganta kanka da ni, ko da mutuwa nayi baka da gadona, domin na cireka daga sahun 'ya'yana. ”

Kuka Rumana ta saka tace. "Baffa wallahi ba.....”

Hannu ya d'aga mata.
"Bansan jin komai gareki, sau nawa nake gaya miki babu ke babu matata, saboda kunnen k'ashi ne da ke, bakya jin magana saboda yana zigaki ko, to na koreshi daga gidan, kema nan da sati biyu zaki barmin gida, don na fasa barima kiyi candy. ” Yana gama fad'in haka yaja hannun matarsa suka shige d'aki.

Nihal da shigowarta kenan ta share k'wallar idonta, cike da jin haushin halin mahaifiyarta, ta shige d'aki ta banko k'ofa.

A hankali ya fara jan k'afafunsa da yake ji sun masa matuk'ar nauyi, rik'oshi Rumana tayi ta saki kuka me sosa rai, janyota jikinsa yayi shima ya saki marayan kukan da yake mak'alewa tun d'azu.


Kuka suke abin tausayi gashi babu me rarrashinsu, sai da sukayi me isar su, sannan yaja hannunta zuwa d'akinsa, yace ta tayashi had'a kayansa, haka suka soma had'a kayan, suna yi suna zubar hawaye, ko wanne zuciyarsa tanai masa matsanancin d'aci.


****

Farkawar da Haisam yayi, sai ya farka cikin matsanancin ciwo, wata iriyar jijjiga yake hatta gadon da yake kai shima jijjiga yake kamar zai b'alle, a haka Momy tazo ta tarar da shi, kuka ta saka ta fice a gigice tana kiran mutanen gidan, dukkaninsu suka fito sukayi d'akin Haisam hankali tashe, Hindu kuka take kashirb'an , yayin da Harris ya k'arasa gurin da yake yana jijjiga shi yana hawaye, Amma a zuciya daga shi har Mama fad'i suke Allah yasa ya mutu, nace (Hmmm MUTUM A FUSKA kenan baka san meye cikin zuciyarshi ba.)

Cikin kuka Momy tace.
"Harris kama shi mu tafi asibiti. ”

Ciccib'arshi yayi yakaishi mota, Momy da Mama suka shiga, shikuma yaja suka nufi Asibiti da shi.





******"
Da bin bango ta samu ta shiga ciki, tana shiga falo kowa ya biyota da kallon tuhuma, d'auke kanta kawai tayi ta d'auki hanyar d'akinta.

Janyota Amma tayi, ta koma da baya ta fad'i k'asa dab'as, rintse idonta tayi, saboda azabar da ta ziyarci k'wak'walwarta.

"Tsabar kin rainamu bakya ganin mutumcinmu, muna zaune muna zaman jiranki kizo kiyi shigewarki, wani d'an ta tsinanniyar ne ya d'aukeki a mota? ”

"Salamu Alaikum”

Sallamar Abba ce tasa dukkaninsu suka d'auke kallonsu ga Hanah, don jin me zata ce, suka maida shi ga Abba suna masu amsa sallamar, Amma tace.

"Gara da Allah ya kahoka, ga tanan, bayan abin kunyar da take jaho mana na sata, gashinan zata had'a da bin maza, in bamu ankare sai dai mu ganta da cikin shege wallahi”

Zama yayi kan kujera, ya cire hular kansa ya ajiye, ya zare agogon hannunsa ya b'alle links d'in hannunsa daga bisani yace.

"Yanzu naga an ajiyeta a mota, hannunsu sark'e da juna, abin yayi matuk'ar bani mamaki, magana d'aya ce zanyi, domin na gaji da iskancinta, haka kawai baza ta d'ora mini hawan jini ba, na fad'i na mutu lokacina baiyi ba, don haka nan da sati biyu zan d'aura auranta da fasinja na, nasan bazai mun musu ba, zan had'a da auran Subai'ah tabi bayan Hamid in yaso ta zana WEAC DA NECO a can, saboda kar ace ita kad'ai na katsewa karatu. ”


"Hukuncinka shine dai² wallahi, muma mun huta, kunnenmu katsit ” tsabar farin cikin hukuncin da Abba ya yanke, ta manta da tijarar da Rumana tayi mata, taja hannun mijinta suka shige ciki.

Ammi kwa kanzil bata ceba, yayin da Subai'ah farin ciki ya ishi zuciyarta za'a d'aura mata aure da mutumin da tafi k'auna sama da kowa a duniyarnan hatta da iyayanta ma.


Ko kad'an maganar za'a aurar da ita bata tada mata hankali ba, dan auren tafi buk'ata a yanzu sama da komi, ita farin ciki ne ma ya dabai bayeta da basu tab'a lafiyar jikinta ba, da rarrafe ta samu ta k'arasa d'akinta, ta shiga toilet dan ta watsa ruwa.

Ko da tayo wankan, kimtsa kanta tayi ta haye gado ta kwanta, saboda tana fashin sallah, ba jimawa kuwa bacci me dad'i yayi awon gaba da ita.



******

A cikin Boot d'in motarsa ya zuba kayansa da ya d'iba, wanda ya san dole zai buk'acesa, duk wani abu me muhimmanci nasa sun had'ashi, juyowa yayi yana kallon Rumana da har lokacin bata daina zubar hawaye ba.

"Ki share hawayenki, komai na duniya k'ararre ne, tafiyata ba tana nufin mun rabu bane, ga waya nan zan dinga jin halin da kike ciki, duk yayin da kike buk'atar wani abu ki sanarmun, zuwa gobe insha Allah zan bar k'asar kafin zuwa sanda za'a soma bikin, kar ki tada hankalinki Nima nafi son na ganki a d'akinki hankalina zaifi kwanciya, na tabbata Sadiq zai rik'e mini ke amana. ”
Yana kaiwa nan ya shige motarsa yaja, saboda wani kuka da yake son fisgarshi, ita kuwa ta kasa firta ko da kalma d'aya saboda kukan da yake so yafi k'arfinta......


Barkanmu da Juma'a
[12/10, 10:13] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


____________________
*EPISODE NINE*
Da gudu ta koma d'aki, kan gado ta fad'a taci gaba da shan kukanta, can kuma ta janyo waya ta kira Sadiq ta zayyana masa abinda ke faruwa, lallashinta ya shiga yi, ya dinga gaya mata kalamai masu matuk'ar sanyaya rai, kuma yace mata ko da bayan auran nasu ne zata zana NECO da WEAC d'inta domin ta samu taci gaba da karatu, hakan sai ya kuma kwantar mata da hankali, ya zamto sai tunanin rabuwa da Yayanta mafi soyuwa a gareta ne yake damunta, shima kuma sai da yasan yarda yayi ya rage mata damuwa akan haka.


******
Derrect Gidan su Haisam Hisham ya nufa, ko da yaje Hindu ce ta sanar masa halin da Haisam ke ciki, hankali tashe ya juya ya nufi Asibitin.


An bawa Haisam taimakon gaggawa, inda da k'yar likitan ya samu ya shawo kanshi, bayan an kaishi d'akin hutu likitan ya kira Momy office d'inshi, da sauri Mama dake zaune ta mik'e tabi bayanta, Momy dad'in hakan taji, saboda ita a ganinta duk tana nuna kulawa ne ga tilon d'anta.

"Yaronki yana neman illata rayuwarsa, domin giyar da yake sha tayi over har tana neman tab'a mishi k'wak'walwa, sannan sanda kuka kawoshi bugun zuciyarsa ba a daidai yake ba, amma yanzu mun samu mun daidaita shi, don da bakui saurin kawoshi ba yana iya rasa rayuwarshi gaba d'aya, duk da dai rayuwa da mutuwa duk na Allah ne.”

Kati ya d'auka ya rubuta musu magun gunan da zasu bashi, Mama ji tayi inama basu kawoshi asibitin da huri ba, amma duk da haka ai rana bata b'aci ba, tunda ba daina shaye shayen zaiyiba, Momy kuwa cikin matsananciyar damuwa suka yiwa likitan godiya suka baro office d'in tana addu'ar Allah kada ya kawo mata ranar da Haisam zai haukace.

Suna fitowa Mama ta bawa Harris katin ya tafi siyo magun gunan, su kuma suka nufi d'akin da aka kwantar da shi, jikin gadon Momy taje ta zubawa kyakkyawar fuskar shi ido, hawaye na zirara bisa kuncinta, a haka Daddy ya shigo ya sameta, tafiya ce ta kamashi ma, yana ta zirga² akan asibitin da yake so ya bud'ewa Harris, Momy ce ta kirashi ta gaya masa, to don kar taga bai zoba, da sai dai ya kirata a waya ya huce kawai.

"Ummee ya kamata ki sakawa ranki salama, ki cire damuwar yaron nan a ranki, burinsa kawai shi yaga k'arshenmu, to ni Allah ya yayemun damuwar da nake a kansa, duk wani k'unci da yake saka ni na daina sashi a raina bare na kamu da ciwon da zai ajalina kwanana bai k'are ba, tunda rayuwar da ya d'aukarwa kansa kenan yaje yayi tayi ya kashe kansa a banza ko ya haukace, ga Harris nan Allah ya musanya mun dashi, tafiya ce ta kamani yanzun nan, ni zan tafi Allah ya k'ara sauk'i. ”

Tsabar takaici Momy kasa cewa komi tayi sai k'asa da tayi da kanta tana kuka k'asa².

Mama kuwa dad'i ne ya dabaibayeta tace.
"Damuwa ai ta zama dole, tunda ba'a son ranmu yake yiba, kawai dai dan ku maza kunfi mata juriya shiyasa, kullum add'uarmu gareshi Allah ya shirya shi, ya kimtsa mana shi, sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya, muje na rakaka bakin mota tunda naga Momy baza ta iya ba. ”

"Amin” Yace yana mai jin dad'in addu'arta gareshi, yana kuma mamakin yadda ko kallonshi Momy ba tayiba, suka jera da Mama, yana gaya mata cigaban da ake samu a harkar bud'e asibitin, ita kuma sai murna take da farin ciki, suna nan tsaye Hisham yayi parking d'in motarshi, tab'e baki Mama tayi tace.
"Kaga yaron da yake kuma jefa Haisam a halaka ko. ”

"Hmmmm to ya sanyi? Babu yadda zanyi na rabasu, da da akwai da tuni nayi, shiyasa kawai na zuba musu ido. ”

"Akwai yarda za'ayi, ka barmun komai a hannu na”

"Na barmiki, ni nari na huce ana can ana jirana.”

"Tom shikenan Allah ya kiyaye ”

"Amin” Yace, yaja motarsa yayi gaba.


D'auke kai Hisham yayi, yai shigewarsa, hankalinsa ya tashi sosai da ya tadda Momy na kuka, duk da shima hankalin nasa a tashe yake haka ya zauna ya dinga bata baki, yanai mata magana k'asa² wanda hakan yasa Mama da Harris da suka shigo suka taddasu jin haushi, tsanar Hisham ta kuma ruruwa a zuk'atansu.


******

Kwanan Haisam uku a asibiti aka sallameshi, jikinshi yayi kyau sosai kamar bai kwanta ciwo ba, Hisham ganin jikin abokin nashi yayi sauk'i ya tattara kayansa ya tafi V/Island, a zuwan yaje yin wani abu ne, don bai sanarwa da Haisam abinda Baffa yayi mishi ba, saboda kar ya tada mishi da ciwon zuciyarshi, ko kayansa ma a boot d'in motarsa ya barsu.

Sosai Momy take kula da shi, Malam Jafar yana aiko mata da rubutunsa, amma fir sai yak'i sha, akwai randa ta matsanta masa sai yasha aikwa ya birkice mata, don dole ta k'yaleshi.

Giyar dai an samu ya rage shanta da rana, amma da daddare wajibine sai ya sha ya bugu zai kwanta, Momy har mamakin inda yake b'oye giyar take, ta bincika d'akin sosai, amma har yau ba taga ma'ajiyarsa ba.


________________

A hankali ya fito daga makaranta iska na kad'a dukkan wani sassa na jikinsa, yau wani iri yake jinsa, burin gangar jikinsa ta isa inda zuciyarsa take, hakanne kawai zai kawo nishad'i da farin ciki cikin zuciyarsa.

A hankali ya zira muk'ulli ya bud'e d'akinsa, jingina yayi da k'ofar, ya hard'e hannuwansa a k'irji yana bin bangon d'akin da kallo.

Hotunan Hanah ne jikin bangunan d'akin, wasu tana yarinya, wasu da girmanta wasu kuma tare suka d'auka, k'arasawa yayi cikin d'akin ya fad'a bisa gado, lumshe ido yayi, yana jin wani tsagwaran soyayya na taso masa, a hankali lab'b'ansa suka furta *MY HANAH* k'arasawa jikin hotanta yayi yana shashshafa fuskarta.
"Allah sarki masoyiyata, ko a wani hali kike? Allah ne kad'ai masani, kuma shi kad'ai ne gatanki, na tabbata yana sane da ke, akwai rana tana zuwa, ranar da sai kinyi kukan farin ciki da idanunki, Allah Ubangiji yasa nine zan baki wannan farin ciki, na jiyar dake dad'i mara yankewa, ina sonki da gasken gaske Hanah, bani da wani buri da ya huce na kasance tare da ke. ”
A hankali yasa hannu ya d'auke k'wallar idonsa, ji yakeyi kamar yayi tsuntsuwa ya isa ga masoyi yarshi, jin muryarta ne, ko kuma jin wani abu daga gareta su kad'ai ne zasu fitar dashi daga shauk'in da ya shiga, amma to ta yaya? Ya jefawa kanshi wannan tambayar, kawai sai ya yanke shawarar kiran layin Subai'ah.

.
**"""
Tana kwance a d'aki, tayi zurfi cikin tunaninshi, wata iriyar soyayya take masa, wacce ita kanta ba tasan irinta ba ko a fim ko a littafi bare kuma a gaske, kamar da wasa taga kiranshi yana shigowa wayarta, da hanzari ta mik'e, hannunta har yana rawa wajen k'ok'arin d'agawa.

"Hello ” Ta d'aya b'angaran ya amsa da.
"Hello, My Suby, ya gida, ya su Abba da Amma?”

"Lafiyansu lau wallahi, ya makarantar? ”

"Alhamdlillah, kiyi hak'uri da abinda ya faru duk a baya, sai yanzu na gane tabbas kece wacce zuciyata take so ba Hanah ba, amma duk na kasa gane hakan sai yanzu. ”

Wani dad'i ne ya ziyarci zuciyarta, ji takeyi kamar ana yaho da ita cikin gajimare tsabar dad'i.
"Alhamdlillh, naji dad'i sosai da ka fuskanci hakan, no dama ban rik'eka da komi ba, soyayyarka ma baza ta barni naga laifinka ba. ”

Nan dai ya dinga janta da hira, ita kuma tana zayyana mishi yanda take mutuwar sonshi, can dai yace.
"Wani taimako nake so kimin, amma na san baza ki iya ba.”

"Ka fad'i ko meye, zanyi maka shi insha Allah.”

"Hanah nake so ki kaiwa wayar, zan tambayeta wani abu. ”

Shiru tayi, ta kasa cewa komi zuciyarta na k'una.

"Dama nace baza ki iya ba, kince zaki iya, ni ba wani

Please Login or Register in order to submit comment