Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dawo masa a kwanyarsa, wai yau Daddynsa ne ya furta da bakinsa ya tsaneshi, Allah ya tsine masa, me yafi wannan ciwo ga d'a idan mahaifinsa ya furta masa?
Rintse idonsa yayi hawaye na shara ra a idonsa, wani irin numfashi ya fara fitarwa yana kuma danna hannunsa a saitin zuciyarsa, wani irin numfashi yaja me sauti wanda yakai ziyara har k'ofofin kunnuwana, har na rufe k'ofar kamar yarda yace mini, na bud'e na fito,
Kallonsa na tsaya yi numfashinsa yana sama da k'asa, tsugunawa nayi gabansa na fashe da kuka domin bansan wani taimako zan bashi ba, magani na gani a hannunsa da alamun sha zaiyi bai samu ya sha ba ya shiga wannan halin.

Da k'yar na iya d'ago kansa na bashi maganin, a hankula numfashinsa ya fara sauka har barci yayi nasarar d'aukesa.






*

Tun daga wannan ranar Amma bata barin Abba ya zauna daga shi sai Suby, shikwa duk yana sane da wayonta, sai da ya shammace ta tukun yace mata zaiyi tafiya, sai da ta bada amannar yayi tafiya tukunna, ta tafi gida ta kuma shishshiryo kaya tabar su Janah a gurinta shi kuma ya shiga ya tambayeta komi ta zayyana masa, ai bai bari ta dawo ba yabi ta can gida yayi mata dukan tsiya ya farfasa mata jiki ya saketa saki uku yace kuma kar su sake su dawo masa gida ya bar mata 'ya'yan duka.

Jikinta yayi mata mugun tsami taja jiki ta koma asibitin tana kuka sosai, Suby tace bata san Abba zaiyi haka ba da bata gaya mishi ba, ga dai abinda fad'ar ta janyo.

Sayar da gidan yayi ya k'ara tikitin gaba, Amma kuwa aka kore su daga asibitin domin dama Abbane ke biyan kud'in asibitin to ya sayar da gida yayi tafiyarsa basu san inda yayi ba, gashi yanzu sun rasa matsuguni sun rasa gur in zama.


_________________


Washe gari tun takwas muka d'auki hanyar Gombe kasancewar jikin nasa yayi sauk'i, da guzurin ruwanmu da abinci muka tafi.

A gajiye sosai muka isa cikin garin Gombe bare ma shi da yayi tuk'i, tambayar gidan fulani yayi, yana tambaya muka samu wanda ya rakamu har bakin get d'in gidan, daga bakin saman get d'in an saka.
*GIDAN FULANI*
[12/10, 17:57] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


________________
*TWENTY NINE*
Lek'o da kansa yayi yana wa me gadi magana, tasowa me gadin yayi ya nufo gurin motar.
"D'an samari wa kuke nema ne?”
"Gidan Fulani.” Haisam ya bashi amsa.
"Ai nanne gidan fulani, ba gashi a rubuce ba. ” Ya fad'a yana nuna gurin rubutun.
"Amma to daga ina kuke, wa kuma kuke nema?”
"Daga Kano muke”
"Kano?” Me gadi ya fad'a yana dafe k'irji, nan ya tuno da maganar Fadi.
“Duk wasu bak'i da zasu zo muddin suka cemaka daga kano suke to kada ka sake ka barsu su shiga idan ba haka ba zan saka a b'atar dakai a doran k'asa.”

"D'an samari idan har kana son kanka da lafiya ka bar k'ofar gidannan domin duk ahalin gidannan basu da ko tsinke a garin kano. ”
Mota ce ta fito daga cikin gidan tazo zata huce ta gefensu, kallon matuk'in Haisam yayi yace.
"Hafiz”
Juyowa Hafiz yayi ya kalli gurin da yaji an ambaci sunansa, wani kyakkyawan murmushi yayi yace.
"Hamid, kai me gadi ka bud'e mishi get ya shiga ciki, ka bani one hour thearter zan shiga bai fi three minute ya ragen ba.” Yana kaiwa nan yaja motar da gudu, saurin da yake yine ma yasa be nemi me gadi ba yasa k'aninsa ya bud'e masa get in.

Bud'e mana get d'in yayi muka shiga, da hannu ya nuna mana b'angaren Hafiz yace mu shiga mu jira shi, Haisam ne yace yayi mana iso gurin asalin mutanen gidan kafin Hafiz d'in ya dawo, amsawa yayi ya kutsa kai phart d'in da yake kallomu.
Durk'usawa yayi gaban wata 'yar dattijuwa, da ganinta kasan ta zuba mulki kuma har yanzu tana kan ganiyarta duk da manyance ya kamata.
" Allah ya huci zuciyarki, na karya dokar da kika kafa mini, Hafiz ne yace na shigo da su ciki bak'insa ne suka zo daga kano, kuma suna neman iso gurinki. ”

"Banda kace bak'in Hafiz ne da babu abinda zai hana na aikata abinda na firta maka ba, maza jeka ka shigo da su. ”
Da sauri ya mik'e ya fita, na jingina jikin mota saboda tsabar gajiyar da nayi, shi kuwa Haisam lumshe idanuwansa kawai yake.
“Ku shigo” Yace mana yayi gaba muna binsa a baya, da sallama muka shiga ta amsa mana tana d'ago kanta sakamakon jin wani fad'uwar gaba ya ziyarce ta, idanuwanta a kaina suka fara sauka, zumbur naga ta mik'e tayi cilli da d'ankwalin kanta ta saki wani mugun ihu da yakaiwa duka ahalin gidan ziyara, muna tsaye muna kallon ikon Allah har duka ahalin gidan suka bayyana domin ganin lafiya?
Wata shegiyar dariya ta hau yi tana cilli da kayan jikinta tana cisgar naman jikinta tana hullawa a baki, tsoro ne ya kama dukkaninmu, da k'yar wasu samari su biyu suka kama ta suka k'ulle hannuwanta ta baya suka jefata cikin d'aki suka kulle ta, tana wani irin ihu.
"Ku kwanceni na yagi naman jikina naci shine kwanciyar hankali. ”

Kowa jugum yayi cike da jimamin wannan al'amarin, ma's u kuka kuma suna yi, nan suka shiga kiran wayar Mahaifansu.

Wani farin dattijo ne, amma ba tsohone can ba yace.
"Garin ya hakan ta faru? ”
Me gadi ne ya nunamu akan bak'in Hafiz ne mu muka buk'aci da a kahomu ciki, da shigowarmu al'amarin ya faru, kallonmu dattijon yayi yana jin wani fad'uwar gaba a kanmu.
Zaro waya Haisam yayi daga aljihunsa ya nemo hoton da suka d'auka tare da Momy ya mik'awa wannan dattijon, karb'a yayi ya zubawa wayar ido hawaye na zuba a idonsa.
" 'Ya'yanta ne? ”
D'aga masa kai Haisam yayi.
"Innai ” ya shiga k'walawa matarsa kira da tace baza ta fito ba, babu yarda baiyi da ita ba akan tazo suje suga me ke faruwa tace wallahi ba zata ba, ai muryar Fadi ce kuma daga b'angaranta k'arar ta fito, babu yarda ya iya da ita shi ya taho, tunda ko babu komi a matsayin mahaifiyarsa take har yanzu shi sam bai duban k'iyayyar da take musu.”

"Innai kizo yau Allah ya amshi addu'armu jikokinmu sun bayyana a garemu, ko yanzu Allah ya d'auki raina na gode masa don ya cika mini burina duk da Khadijah Hassana da Usaina basu bayyana garemu ba.”

Da gudu matar da ya kira da Innai ta shigo, ya mik'a mata wayar hannunsa, nunamu ta shiga yi da hannunta yana karkarwa ta tafi luuu ta zube a gurin.


*TUNA BAYA*

KUYI HAK'URI DA WANNAN K'IRJINA KE MINI CIWO.
[12/10, 18:18] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


_________________
*TERTY*
Abdul Samad cikakken bafilatanine na garin Gombe, mahaifensa shi kad'ai suka haifa a doran k'asa, kuma familynsu basu da wani yawa na kuzo mu gani, kiwon shanu yake yi a cikin gidansa da aka bar masa gadonsa, kiwon sosai ya karb'eshi, har nono yake siyarwa da madarar shanu da man shanu, da Allah ya kuma bud'a mishi samun sa sai ya sissiyi gidajen kusa da shi ya had'e da nasa duk da nasan ma ba k'aramin girma ne da shi ba, ya ware gefe guda da yake zuba shanu sannan yayi gini a tsakiyar filin gidan inda zai zauna da matarsa in yayi aure, ragowar filin gidan ya k'udurtawa ransa idan Allah ya bashi tsawon rai iyalansa zai ginawa su zauna a ciki.

Abdul Samad yayi aure ya auri matarsa Hajjo wacce suke matuk'ar son junansu kamar su cinye juna,itama fillo ce gaba da baya, suna zaune lafiya abun su sai ya zamto Hajjo ce take sayar da su madarar Shanun yanzu.
Ana haka Hajjo ta samu ciki, murna da farin ciki gurin Abdul Samad ba'a magana , saboda yana matuk'ar son yara don yasha gayawa mahaifansa sanda suna da rai cewa.
"Kun haifeni ni kad'ai, to insha Allah ni kuma sai na tara muku jikoki 60” Sukan yi dariya idan ya fad'i haka suce.
"To Allah ya baka masu albarka, yasa kuma muna da rabon ganinsu. ” yakan ce. "Insha Allah da ranku da lafiyarku ” Sai suce. "To Allah yasa.”
Ashe dai basu da rabon ganin d'ansa ko guda, k'arshe auran nasa ma basu gani ba.
Cikin k'udirar Ubangiji Hajjo ta sauka ta haifi 'yarta mace, sosai Abdul samad yayi murna da samun wannan yarinya, ranar sunanta sa guda ya kayar, ansha bidiri sosai ya saka mata suna Maimuna, sunan mahaifiyarshi kenan.

Shekarar Hajjo guda da haihuwa k'anin baban Abdul Samad yayi kiran shi yace masa.
"Kaga mahaifanmu daga ni sai mahifinka suka haifa, sannan kuma shima kai kad'ai ya haifa nima kuma 'ya d'aya Allah ya bani a duniyar nan, yarinyata ta isa aure kuma babu wanda yafi can canta da na bawa auranta sama da kai, idan har ka aminta da kyautar da na baka, to ina jiran amsarka don nan da sati zan d'aura muku aure. ”
Zufa ce ta keto masa yayin da ya gama jin bayanin Baba Abbakar, a tsarin rayuwarsa bai da niyar yin mace sama da biyu, kuma girman soyayyar da yake wa Hajjo bai jin zai iya yimata kishiya, to amma ta ya zai kalli idon Kawu Abbakar yace baya son kyautar da ya bashi? Mutumin da ya d'auki soyayyar duniya ya aza masa tun yana k'araminsa, bacin haka ma ya za'ai ya d'auki 'yarsa sullu gudun ya bashi kyauta sannan kuma yace baya so? Bayan ba rasa manema tayi ba, tana da manema sosai da sosai kawai yana son k'ara k'arfin zumuncinmu ne.
Kansa na k'asa yace.
“Ya za'ai kamun babbar kyauta nace bana so? Na amince Kawu Allah ya sanya albarka a ciki, ai ko wata ka d'auko ka bani bazan k'ita ba bare 'yarka ta cikinka. ”
Albarka ya saka masa sukai sallama ya tafi, da k'yar ya iya tunkarar Hajjo da maganar auran da Kawu zaiyi masa, nanfa kishi ya rufe mata ido ta zage Kawu tas wai kwad'ayine yasa zai bada 'yarsa don kawai tazo suci dukiya, bar mata gidan Abdul Samad yayi don bazai iya zama yana jin mugayen maganganu daga bakinta ba don suna iya haurawa sama, duk da dole ne mace taji ba dad'i yayin da kace zaka mata kishiya, kamata yayi ka lallasheta idan baza ka iya ba to ka barta ta k'araci haukanta domin wasu matan akwai su da k'aramar k'wak'walwa, ni dai banga abin hauka ba don ance za'amun kishiya.
Kuka sosai Hajjo ta sha tana tsinewa Kawu Abbakar sau ba adadi, kuma ta k'udurtarwa zuciyarta abubuwa da dama.

An sha bikin Abdul Samad da Aysha cikin kwanciyar hankali, a washe garin da aka kaita d'akinta a ranar Kawu Abbakar ya amsa kiran mahalicci, sunyi kuka sosai kamar ransu zai fita daga bisani suka dangana suka mik'awa Allah lamuransu, shikenan itama Aysha ba Uwa ba Uba don mahaifiyarta tun a haihuwarta ta rasu, Hajjo tayi farin ciki da mutuwar Kawu Abbakar, a cewarta dukiyar da ya k'wallafa rai har ya kawo 'yarsa cikin gidan ga shinan ya mutu bai ci ta ba.
Zaman Hajjo da Aysha kadaran kadahan, a hankali soyayyar Aysha ta fara huda zuciyar Abdul Samad saboda ladabi da biyayyar da yake samu daga gareta, ga wasu qualities da take da su wanda Hajjo bata da su, kuma yanzu Hajjo kishi ya sakata ta tsiro da wasu mugayen halaye, a sannu a hankali Abdul Samad ya sakarwa Aysha ragamar rayuwarsa, domin ta riga ta gama siye zuciyarsa gaba d'aya da kyawawan halayenta a duk sanda ya kasance da ita yakan tainci kansa cikin matuk'ar farin ciki.
Ana haka Aysha ta samu ciki, a lokacin itama Hajjo tana d'auke da ciki don har ta yaye Maimuna, amma cikin Aysha sosai ya tsaya mata a rai, Allah ne kawai yake bashi kariya.
Aysha ta riga haihuwa, ta haifi 'ya'yanta tagwaye duka maza farin ciki gurin Aysha da Abdul Samad ba'a magana, bak'in ciki gurin Hajjo kuwa ba sai an tona ba, a ranar itama ta fara nak'uda ta haifi d'anta namiji amma bai zo da rai ba, a ranar kulle kanta tayi a d'aki ta hana kowa ganinta.

Ranar suna an sha bidiri sosai da sosai, shanu hud'u aka kayar aka sanya musu Abubakar da Imam, sunan mahaifansu kenan, Hajjo kuwa tsabar bak'in ciki barin gidan tayi gaba d'aya............
[12/10, 18:18] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: [11/25, 10:21 PM] : Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JeEtb40QgPwJtzZLAncIZG
*BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

_______________
*THiRTY ONE*
Haihuwar su Abbakar da Imam sai tazo masa da d'umbin alkhairai da dama, ya sayar da shanu sama da dubunnai hakanne yasa ya kuma siyan gidajen kusa da shi ya shigo da shi cikin gidan ya saka k'aton get, daga saman get in yasa aka saka Gidan Fulani.
Wani guri ya yanka a gefen gidan ya bud'e gurin sayar da Youghort da fura, da damammiyar fura me gyad'a, sosai ya k'awata gurin ya sakawa gurin Abubakar Imam Youghort nd Fura, a jikin jarkar Youghort in da robobin haka aka saka, sosai gurin ya janyo mutane da dama, hakanne yasa idan har kika sauka cikin garin Gombe kikace akaiki Gidan Fulani to har k'ofar gidan za'a kaiki.
Wannan abu ya tayarwa da Hajjo hankali sosai, nan maziga suka shiga zigata, wai ita da ta fara haihuwa bai saka sunan 'yarta ba sai sunan wa'yan nan yaran don an riga an gama shanye shi, tunkan zuwan Aysha gidan sai da aka samar mata dafai, nan fa Hajjo ta shiga bala'i ba ji ba gani, don kashe fitina sai ya bud'e wani gurin Youghort in akan titin layin ya sakawa gurin Maimoon Youghort nd Fura, duk da haka bala'i bai kwanta ba da ta jangwalo can sai ta jangwalo nan da ya gaji sai ya tattara ta ya watsar, dama Aysha ba kulata take ba sai dai tayi da mijinta, duk abinda zata ce sai dai ta toshe kunnenta ba wai don tana tsoranta ba sai don kawai bata son fitina ko kad'an.
Kalmar kuwa ta shigo cikin gidanta ta rabata da mijinta da yake matuk'ar sonta ta k'arfi da yaji, da yawon bin malamai da ta gada gurin mahaifinta, don kawai kwad'ayi da son cin dukiya, ta haddace ta a k'wak'walwarta saboda kullum ne sai ta yada mata ita, sau d'aya ne ta tab'a ce mata, Ai dama duk wani me aikata mugun abu, gani yake kowa ma aikatawa yake, da dai ba'a san asalin balbela bane da sai ta samu bakin magana.
Babu inda Hajjo bata shiga ta fita ba don kawai ta dawo da hankalin Abdul Samad kanta, ta raba su da Aysha amma hakan ya gagara, kud'inta kawai suke ci, ana cikin haka mahaifiyarta ta samo mata wani tantirin boka suka shirya suka je gurinsa, yace sam babu me iya raba soyayyar Abdul Samad da Aysha, duk wanda yace mata zai iya to kud'inta kawai zai ci, mafita d'aya kawai a kasheta, babu tsoron komi suka ce a kasheta, da yayi tsubbace tsubbacensa yace musu kasheta ma bazai tab'a yuyuwa ba, amma za'a saka mata ciwon kai me tsanani wanda zai sanadiyar mutuwarta, kud'i suka zazzage masa me d'umbin yawa suka komo gida.

Tun daga sannan Aysha ta kamu da ciwon kai me tsanani wanda har yayi sanadiyar mutuwarta, a lokacin shekarar su Abubakar biyu a duniya, Abdul Samad yaji mutuwar Aysha sosai da sosai, don ciwon da tayi fama da shi yarda ka san tare suka yishi, babu inda basu je neman magani ba amma Allah bai kawo warakar ba har sai da aka tafi, kwanansa biyu a asibiti bai san inda kansa yake ba, a washe garin da Aysha ta mutu aka aikowa Hajjo mahaifiyarta ta mutu sanadiyar gobarar da tayi a d'akinta ta k'one k'urmus sai toka ake gani. Allah kenan, murna ta koma ciki da ihu ta tafi gidan su.

Rayuwa ta tafi a hankali komi yake sauyawa, su Imam sun taso cikin maraicin uwa, amma mahaifinsu yana matuk'ar sonsu musammam Imam saboda yafi Abbakar sauk'in kai, shi Abbakar akwai shi da zafin zuciya, tsakaninsu su biyunma ba jituwa suke ba, Imam akwai shi da sauk'in kai sam bai son fitina, halinsa kamar na mahaifiyarsu sak, hakanne yasa Abdul Samad da suke kira da Abbu yake masifar sonsa, shikwa Abbakar Hajjo da suke kira da Fadi ta janyeshi ta cusa mishi k'iyayyar d'an uwansa, akan mahaifinsu yafi sonshi, hakanne yasa sam basa jituwa kullum cikin fad'a suke, haihuwa d'aya Fadi ta k'ara yi ta haifi mace yasa mata suna Aysha, anyi babban rikici sosai akan baza a sanyawa 'yarta sunan kishiyarta ba, da dai taga yafi k'arfinta dole tasa ta
hak'ura don har yau bata samu cikar burinta na mallake shi ba, har yau Allah bai basu sa'a ba, tun daga wannan haihuwar Fadi bata kuma haihuwa ba, a haka rayuwa taci gaba da juyawa har su Imam suka zama samari, sun kammala karatunsu akan harkar Business, Maimoon tuni tayi aure tun kammala Secondary inta har ta haifi yara biyu, Aysha kuma yanzu take 'yan matan cinta.

Da taimakon boka aka cusawa Abbakar soyayyar Asiya, 'yar gidan yayar Fadi ce, son ta yake sosai da sosai, kud'in da yake sakar musu kuwa ba'a magana, hakanne yasa suke ta k'ok'arin cusawa Imam soyayyar k'anwarta Zainab, amma shi sam yak'i, hakan ya yiwa Abbu matuk'ar dad'i don ba a son ranshi Abbakar yake soyyayya da Asiya ba, saboda ya riga da ya san ba domin Allah Fadi take rawar kai akan auran ba, amma ya fuskanci an riga an gama da shi, shiyasa kullum cikin rok'on Allah yake masa.
Abin da basu sani ba Imam tuni ya fad'a soyayya da 'yar kishiyar yayar Fadin, ma'ana k'anwar Asiyan da suke uba d'aya, yayin da suka fuskanci haka sun shiga matuk'ar tashin hankali su san samun su ya auri Zainab kinga gida ya riga da ya zama nasu, amma fir Imam yak'i yarda hakan sai ya kuma janyo mishi muguwar tsana gurin Fadi, harma gurin Inno mahaifiyar su Asiya kenan ita a gurinta cin fuska Imam yayi musu tunda zai auri 'yar kishiyarta, dama ba zaman lafiya suke ba, hakan sai ya kuma janyo musu rikici sosai, harma ta ziga mahaifinsu akan ya hana Imam fatiman, tunda dama ta riga ta gama da shi.

Ko da Abbu yaje kai kud'insu, k'in ansar na Imam akai, shikwa Abbu yace muddin ba za'a bawa Imam ba to shima Abbakar bazai aureta ba, jin hakan yasa da gudu ya anshi kud'in kar yaje yayi biyu babu uku ba ko d'aya.
Abbune ya had'a musu lefe kowa akwati shida² yayi musu gini a cikin gidan kowa da phart inshi, sai suka saka phart in su Abu a tsakiya.
An sha shagalin biki sosai da sosai, aka d'aura auran Abbakar da Asiya, Imam da Fatima akan sadaki dubu hamsin² lakadan ba ajalan ba, nan fa aka dinga zagawa da su a garin Gombe domin ba'a tab'a samun wa'yanda sadakinsu yakai haka ba, yayin da takaici ya ishi Inno da tuni duka 'ya'yanta ne zasu samu wannan 'yancin, kai Allah ya tsinewa Imam, abinda ya fito daga bakinta kenan tana me jan tsaki.........




Masu tambayata group na whats'up kuna iya biyo link innan, amma pls mata kawai, kuma kema idan kin san cika gidane zai kawo ki kiyi zamanki pls, nafi son ganin ruwan comment idan baza kiyi ba dan Allah kar ki shigo, don in kin shigo ma zan fidda ki.
[12/10, 18:18] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


_______________
*THIRTY TWO*
Zaman Imam da Fatima zamane na amana da k'aunar juna da kuma tsantsar biyayya, sannan kuma tana samun kulawa gurin sirikinta Abbu, don shi kad'aine a cikin gidan yake kulata, ko taje gaishe da Fadi ba ta amsawa kuma duk da haka ba ta fasa zuwa ba, kullum da safe sai ta shiga ta gaisheta, faccalarta, yayarta kuma harara ce tsakaninsu, hakan yasa Fatima ta tarkata ta gefe, dama ko sanda suna gida ba magana suke ba.

A kusan lokaci d'aya Asiya da Fatima suka samu ciki, Amma Asiya ta riga Fatima haihuwa ta haifi 'yarta mace aka saka mata suna Nusaiba, tsiran sati guda Fatima ta haifo tagwayenta mace da namiji, Abbu yayi matuk'ar farin ciki da haihuwar su, yarda ka san a kansu ya fara jikoki, ranar suna Shanu sunyi kuka, anyi bidiri sosai, bak'in cikin su Fadi da Inno k'arara suka nuna shi, an sakawa macen Khadija, namijin kuma Ibrahim Khalil, yaran sun shiga ran Abbu sosai, yayi musu kyautar gidaje saboda basu da gadonsa, kuma har ga Allah yafi son 'ya'yan Imam, saboda yafi jin dad'in shi, ya kuma fi masa biyayya, shi Abbakar ya mai da Fadi uwarshi da ubanshi, don yanzu tsakaninsa da Imam ma idanu ne ta shiga ta rabasu, ta cusa mishi bak'in ciki da Hassada.
Sati d'aya da suna Khalil ya rasu, ihu yayi tayi aka rasa abinda ke damun sa, kafin a tafi asibiti ma ya cika, sunji mutuwarsa sosai haka zalika sunyi kukan rashin sa, a haka rayuwa ta dinga ja da dad'i babu dad'i har su Khadija suka cika shekara 7 a duniya, har lokacin Fatima ba ta kuma haihuwa ba, Asiya dai ta kuma haifar mace Fiddausi,Aysha ma har anyi bikinta haihuwarta biyu ma, Faiza da Kabir.

Khadija tana ganin mugun gata gurin iyayanta da Abbu, duk cikin jikokin gidan Abbu yafi k'aunarta yafi ririta ta, babu shakkar uban kowa yake nuna mata soyayya, soyayyar da ta janyo mata tsana da bak'in jini, ko cikin jikokin gidan ta shiga yin wasa sun dunga dukanta da hattararta kenan, hakanne yasa Fatima (Innai) take kulle k'ofarta ta hana ta fita, Abbu kuma da kansa ya canja mata schl wacce ta kere ta 'yan gidan.
Yauma kamar kullum an taso su daga schl, da gudu ta shigo ta haye jikin Innai da ta k'urawa hotonsu da suka d'auka tun Khalil na da rai, Khadija na hannunta, Khalil yana hannun Imam (Baffi), fusge hoton Khadija tayi tana dariya, murmushi Innai tayi tace.
"Wlcm my Baby ”
D'an dafa kanta tayi tace.
"Auchh” sai kawai ta juya da gudu tayi waje hoton yana hannunta.
"Baby ina zaki?” Innai ta tambayeta, cikin d'aga murya tace Launch box ina na manto a mota zan auko. ”
Tun Innai na zuba idon shigowar Khadija, har ta gaji ta fito, me gadi ta tambaya yace shi dai bai ganta ba, tun da aka sauketa a mota baiga fitowarta ba, hankalin Innai ne yayi mugu mugun tashi, cikin gidan ta nufa ta tambaye su ko Khadija ta shigo? Idan sun mata magana bangon gurin yayi magana, hawaye ne ya siraro bisa kuncinta, ta fito daga gurin tayi waje, wani me d'inkin takalmi ta gani a bakin gurin ta tambayeshi ko yaga

Please Login or Register in order to submit comment