Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miki fad'a, amma saboda ke kunnen k'ashi ne da ke har ya warware ko”
"Baffa fa Uwata ta zaga. ”
"To ke wace da baza a zagi uwarki ba? Naga ke yanzu uwar wasu kika kama kina jibga, sa'ar kice, ai in kina da mutumci mahaifiya zaki d'auketa, amma tunda raini da rashin mutumci ne abin yinki fice ki barmin gida, kar ki kuma tako k'afarki cikin gidana tunda baki d'au macen gidan da k'ima ba, in gaisuwa ce ma dinga yi a waya ko kuma kije office d'ina, za'a biyoki da komi naki, tunda baki da mutumci babu wanda zai rakaki kije dangin uwar taki su rakaki gidan mijin. ” Yana gama fad'in haka yabar gurin, Aunty ta rufa masa baya farin ciki fal ranta.

Kukane sosai yaci k'arfin Rumanah saboda jin furucin da Baffa yayi gareta, musamman kalmar nan tashi ta k'arshe, dak'yar ta iya d'aga k'afarta, ta d'auki jakar kayana ta fita daga gidan tana zubar hawaye.
"Kuma ki gayawa wannan d'an iskan da ya mareni ya tab'owa kansa tsuliyar dodo, domin na shiga rayuwarsa kenan har sai ya daho tafin hannuna. ” Cewar Shukhura, ko waiwayowa bata yiba bare ta nuna ta jita tai ficewarta.



Da gudu wanda ya d'auki hoton ya biyoshi yana mik'a masa hoton, wani kallon banza yayi masa, tunani kuma yayi, idan yabar hoton baisan iyakar inda zaije ba, karb'a yayi ya zaro dubu biyar ya bashi.
"Kayi delete. ”
Yana tafe ina binshi a baya har muka isa gurin motarsu, Hisham yana ganinmu ya shiga tambayar. "Lafiya?” Mota kawai ya bud'e ya shiga ya had'a kai da stiaring in motar bai bashi amsa ba, kaina ya maida idonsa yana kuma tambayata, bansan amsar da zan bashi ba hakanne yasa na kuma fashewa da kuka, iska ya busar me zafi tare da cigaba da kiran wayar Rumanah, wayar kuma na cikin jakar hannuna a silent take hakanne yasa bansan ana kira ba.

Bai hak'uraba yaci gaba da kiran wayar hankali a matuk'ar tashe, ni kuma na bud'e gidan baya na shiga na had'a kai da guiwa ina cigaba da kukana.
Tafiya take tana hawaye, zuciyarta tana yimata d'aci, wannan wata iriyar rayuwace? Yaushene zasui rayuwar farin ciki, yaushene farin ciki zai d'auru cikin rayuwarsu ita da Yayanta? Tunda suka rasa mahaifiya farin ciki ya ruguje a sahun rayuwarsu, lallai uwa itace abu mafi girma a cikin rayuwar mutum, tabbas mutum baya sanin halin rayuwa sai bashi da mahaifiya, ita Hanah mahaifiyarta tana raye shiga tsakaninsu akai amma kalli yarda K'ADDARAR RAYUWA take wala gigi da ita, wayyo mutuwa meyasa kikai mana haka, kin d'auke mna mahaifiya daga cikin RAYUWARMU kin barmu cikin k'uncin rayuwa.
"Rumanah ”
Taji muryar Hisham ya kirata, zata wuce ta gabanshi bata sani ba, d'ago da idonta tayi cike da hawaye tana kallonshi, bud'e mata hannuwa yayi da gudu ta k'arasa jikinsa ya rungumeta a tare suka saki wani kuka me ban tausayi.
"Yaya inama ana siyan dangin uwa da wallahi yau sai na siya, domin baki mafi girma ya furta mini gori, wanda ban tab'a tunanin zai furtan ba, kuma shine silar komi tunda da bai aureta ba da bata haifemu ba.
Har abada bazan tab'a da na sanin kasancewar Mami mahaifiyata ba, kasancewarmu mara asalin uwa ba siya mukayi ba haka K'ADDARAR RAYUWARMU tazo ba siya mukayi da kud'i ba me yasa su suka kasa fuskantar hakan? ” Ta fad'a tana k'arawa kukanta k'arfi, bubbuga bayanta.
"Ba zasu tab'a ganewa ba Rumanah, hak'urin nan shi zamu cigaba da yi komai me hucewa ne, gashi yanzu zaki bar gidan wa zaki gani bare yayi miki gori, me ya faru?”
Labari ta kwashe ta bashi duk yarda abin ya faru, rintse ido yayi cikin b'acin rai.
"Nine nan dangin mahaifiyarki Rumanah, ni zan kaiki gidan mijinki da kaina, ni na gaya miki akwai randa Baffa zaiyi nadamar abinda ya aikata mana, ba yin kansa bane makirci ne na mace, shiga mota muje.” ya saketa shima ya zaga ya shiga.

Duk naji labarin da ta bawa Hisham, hakanne ya kuma saka kukana tsananta, da ta shigo motarma rungume juna mukayi muka saki marayan kuka, ina jin kamar ni na janyo mata matsalar.
Jan motar Haisam yayi idonshi yayi jajir alamun shima yaji abinda yake faruwa........
[12/10, 17:55] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

______________
*TWENTY TWO*
Momy da taji abinda ya faru ranta ya matuk'ar b'aci sosai, abinda ya hanata zuwa gidan bikin kenan don tasan muddin taje baza su kwashe ta dad'i ba da Aunty, lallashinmu ta dinga yi don har lokacin dukkaninmu kuka muke yi, ina matuk'ar tausayawa rayuwata bansan abinda zai faru dani nan gaba ba, zamewa nayi na kwanta akan kujerar da nake ina tunanin rayuwata da abinda yake zagaye da ita.

Cikin drower ya jefa hoton ya rufe, ya daho da baya ya d'auki bottle d'in giyar dake kan center table yayi cilli da murfin ya kafa a baki, shigowa Hisham yayi ya taddashi a haka, kau da kansa yayi cikin k'unar rai, ya fad'a kan doguwar kujerar dake kallonsa ya rufe idonsa yana tunanin KADDARAR dake zagaye da RAYUWARMU.


"Kinyi nesa da idanuwana amma kina nan kusa da zuciyata, ko za'a shekara million d'ari matsayinki a raina baza ya tab'a canjuwa ba, na kasa rayuwa babu ke, kullum tunanina ya kike, a ina kike rayuwa, wata iriyar rayuwa kike? Duk babu me bani amsa, ina mutuk'ar sonki my Hanah na dad'e ina gaya miki soyayyarki itace K'ADDARAR RAYUWATA, kuma ina jin kamar itace zata zamto ajali na, fatana ko da babu raina ki dinga yawan tunawa da ni, kar ki manta dani a cikin zuciyarki ki dinga sakawa dani.”

"Baza ka tab'a barin Rayuwata ba Hamid, kaine mutumin da ya zame mini majingina a yayin da nake tangad'i zan fad'i, kaine ka nuna mini soyayya da k'auna wanda suka amsa sunansu ba na gaibu ba, ka soni a sanda duniya take yayina, ka kuma soni a lokacin da duniya ta juya mini baya, kowa yak'ini ya k'yamaceni kaine kad'ai wanda nake ganin soyayyata da k'aunata a cikin k'wayar idonka, dan Allah kar ka mutu ka barni CIKIN DUNIYARMU” (Littafina me zuwa in Allah ya yarda)
Na kai k'arshen maganar ina fashewa da kuka, kukan da ya sakani farkawa daga barcin da ya kwasheni anan ne na gane ashe mafarki nayi, kuma k'ara k'arfin kukana nayi domin a kwana biyunnan mafarkin da nake yawan yi kenan, kuma bansan abinda hakan yake nufi ba Allah ne kad'ai masani.




Misalin k'arfe takwas Rumanah tayi wanka ta shirya, Ya Hisham zai kaita gidan angonta, da Momy tace ya bari a taro mutane a had'u a kaita gidan mijinta, yace a'a hakan zai zamo kamar tonon asiri, zai kaita kawai da kanshi ya bawa Sadiq amanarta, cewa tayi to hakan babu laifi, tayi mata fad'a sosai na tsakanin 'ya da mahaifiya wanda hakan sosai ya tadawa Rumanah tsumin rashin Mami.
Duk da sakamakon kukan da na sha ya tayar mini da ciwon kai da zazzab'i hakan baisa na kasa juriyar shiryawa ba domin rakiya wa Sahibatina ba.


Haisam har lokacin barci yake yi, don yana gama shan giyar ta kayar da shi, don haka daga ni sai Ya Hisham muka tafi raka Sahibati, dukkaninmu a gidan gaba muka zauna tunda ba wani auki ne damu ba, shiru dukkaninmu mukayi kowa da abinda yake sak'awa a zuci har muka k'arasa Lamid'o cristent.
Gidan Sahibati ya had'u dai² gwargwado, duk kushen me kushi babu abinda zai kushe, tsarin gidan ya had'u matuk'a gwanin sha'awa.

“Sadiq ga amanar Rumanah nan, ka dai san marainiya ce, ka rik'eta amana, a yanzu kaine kad'ai zaka fi kusanci da ita, fatana ka rik'eta da zuciya d'aya ka da d'ad'a rayuwarta kasanyata farin cikin da ta rasa a baya, abu d'aya zaka yi wanda zai tab'an zuciya shine ka wulak'anta mini Rumana.”
Cizan leb'e yayi, yaci gaba. "Allah ma dai ya kiyaye."

"Amin, insha Allahu baza ka sameni da yin hakan bama, zan zame mata MIJIN MARAINIYA, zan jiyar da ita farin ciki mara misaltuwa, fatana Allah Ubangiji ya bamu zaman lafiya me d'orewa.”

"Amin²” Ya fad'a yana maida idonshi kan Rumanah. "Toh K'anwata mu zamu huce, Ubangiji ya kad'e fitina, yasa gidan zamanki ne, insha Allahu mutuwa ce kad'ai zata miki katanga da wannan gidan. ” amsawa tayi da amin cikin ranta, tana d'an k'arawa kukanta sauti, mik'ewa nayi don ganin Ya Hisham zai fita, rik'o hannuna tayi.
"Habibati yanzu tafiya zakui ku barni? ” D'aya hannuna na saka na d'auke k'wallar da ta tarar mini a ido, cikin san fashewa da kuka nace. "Ina yimiki fatan alkhairi cikin rayuwar auranki. ” Daga haka na salub'e hannuna na fice, har ya shiga mota yana zaman jirana don haka da sassarfa na k'arasa na bud'e na shiga, rintse idona nayi hawaye yana gangarowa bisa kuncina na janyo mayafina na rufe fuskar, a hankali ya fara jan motar muka fara tafiya akan titi.
Driving d'inshi akwai dad'i akan na Haisam, domin a hankula yake tafiya shi kwa Haisam da gudun tsiya yake figarta, mun kusa isa gida wayarshi tayi k'ara, alamun sak'o ya shigo cikinta, da kamar bazai bud'a ba, sai kuma yaga Rumanah ce.

_"pls nd pls Yaya ka binciki damuwarta, tabbas akwai abinda ke damun zuciyarta, daga ni har ita zuciyoyinmu bamu jin dad'insu shiyasa na kasa bincikar tata zuciyar, ni yanzu akwai me bincikar tawa zuciyar ita kuwa na tabbata babu domin yayi nesa da ita, don haka gata nan, dukkaninmu Amanarmu ce, kaima ka kulamin da ita kaji Yayana.”_ Yana kai k'arshen aya ya ajiye wayar yana furzar da iska me matuk'ar zafi.
Ko da muka isa gida, ban san mun isa ba, barci ne mara dad'i ya samu nasarar saceni, ko da yayi perking yaji shiru² ban motsaba sai ya janye mayafin dake kan fuskata yana lek'oni, bud'e idona nayi suka wad'a cikin nasa, maida su nayi na rufe cike da jin kunya na yunk'ura zan fita daga motar don naga a lamun mun iso gida, dakatar da ni yayi da cewa. "Tsaya mana kiji. ” Komawa nayi na zauna sai ji nayi yace.
"Meye yake damun zuciyarki? ”
Shiru nayi na kasa bashi amsa, a raina ina mamakin to ta yaya ma yasan ina da damuwa a raina?
" kimin magana mana Hanah”
Kallonsa nayi saboda jin yarda ya ambaci sunana da wani irin salo.
" Wani abune ke damun zuciyata, magance shi kuma sai Allahn da ya dasa mini shi. ” Meye shi? Kika sani ko Allah ya bani ikon magance miki shi.”

"Soyayya ce ke damuna. ” Na fad'a cikin kar yar² murya. “Soyayya kuma, to soyayyar wa?”
"Soyayyar Yaya Hamid, bansan wani hali yake ba, kullum sai nayi mafarkinshi, ina son jin wani abu daga gareshi amma bansan ya zanyi ba ” Na fad'a ina yin rau² da ido.
"Kina so na jiyo miki labari a kansa. ”
D'aga mishi kai nayi, murmushi yayi yana cizan leb'ensa na k'asa.
"Amma fa sai kinmin alk'awari. ”
"Alk'awarin me?”
"Alk'awarin bazan kuma ganin damuwa akan fuskarki ba. ”
Murmushi nayi nace. "Nayi ma alk'awari. ”
"Tom shikenan bani cikakken address yarda zanji dad'in jjiyo miki news akan masoyinki ko” yakai k'arshen maganar yana kallon cikin idona, kau da idona nayi cike da kunyarsa na bashi address mafi sauk'i.
"Insha Allahu zan binciko miki komi game da shi, jeki ciki to dare yana kuma yi.” Ya fad'a yana lakace mini hanci, murmushi nayi nace. "Amin, na gode, Allah ya saka da alkhairi ” Ban jira amsawar sa ba na fito daga motar na nufi cikin gida, yayin dashi kuma yabi bayana da kallo yana lumshe ido, ta cikin hasken gen domin hutar lantarki tayi wuya a zamanin nan, kai tir da irin wannan mulki.




___________

Hankalin su Umma yayi mugu²n tashi ganin har kusan kwana biyar babu su Abba babu labarinsu, gashi Hamid tunda yazo ya kwanta kashirb'an bashi da lafiya, har sai da aka danganta shi da asibiti, Umma ji take kamar ta d'ora hannu aka tai ihu, Suby kuwa duniya tayi mata zafi, iyaye babu labarinsu ga masoyi babu lafiya zuciyarta gaba d'aya ta tsaya cak da aiki, idaniyanta kuwa har sun k'ek'ashe saboda kuka.
Ammi baiwar Allah, sanin halin da zuciyarta take ciki Allah ne kad'ai masani, domin akwai tarin damuwa a cikin zuciyarta, wanda suka kusan yiwa gurbin zuciyarta kad'an.

Sai a randa suka kwana biyar aka kira Umma, akan sukai million ashirin, idan suka kai k'asa da haka to za'a kuma k'wamushe wanda yakai kud'in, ragowar million goman da aka sayi gidan ta ciro a banki, ta ciri million goma a Accaunt d'in Hamid wanda sai da ya girgiza sosai da sosai, ga ciwon Hamid yana mugun cin kud'i kuma har yanzu likitan bai gaya musu abinda ke damunsa ba.

K'anin Umma ne ya karb'i kud'in ya kai a lokacin kuwa aka sake su, dukkaninsu sunci uwar wuya an wahalar dasu sosai, Amma sai dakace take yi dama bata saci jakar ba da duk hakan bata faru ba, gashi babu ribar da ta samu sai uwar wuya da ta janyo musu, Abba kuwa asibiti aka nufi dashi domin jininsa ya hau sosai.




___________
Ya Hisham ne yace nazo na rakashi unguwa, hijabi kawai na d'ora kan riga da siket d'in dake jikina na atamfa na fito muka tafi, tunda muka tafi babu wanda yayi magana har muka k'arasa bakin wani privet hospital, perking yayi, ya d'ora mini nik'af akan cinyata, d'agowa nayi ina kallon fuskarshi, bai bari mun had'a ido ba yace.
"Saman bene d'aki na goma, kije ina jiranki. ”..........
[12/10, 17:56] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


_______________
*TWENTY THREE*
Ji nayi gabana ya yanke ya fad'i, na kuma kallon fuskarshi a gain dai yak'i bari mu had'a ido kuma yak'i bani fuskar da zan tambayeshi, d'aura nik'af d'in nayi na fita daga motar, ina fita yabi bayana da kallo yana sauke nannauyar ajiyar zuciya.
Ban samu kowa a harabar gurin ba, na tura k'ofar a hankula k'irjina yana bugawa fat², a hankali na bud'e idona dake a rintse, babu kowa cikin d'akin sai majinyaci akan gado, rufe k'ofar nayi na k'araso gaban gadon ina sauke idona kan mahad'insu, fuskarshi tayi fayau ta k'ara wani annurin kyahu, jikinsa babu riga sai wasu k'arafuna da aka jajjona masa a k'irjinsa, wasu zafafan hawaye ne suka biyo kuncina na mugun tausayin masoyina, ya dad'e yana gaya mini soyayyata itace k'addararsa kuma gashi a yau na kuma gasgatawa da maganarsa domin na tabbata soyayyata ce ta sakashi shiga wannan halin.

Durk'usawa nayi gaban gadon na kama hannunshi na rik'e k'am ² na fashe da siririn kuka me fitar da sauti d'an kad'an.
"Hubbina kaine farin cikina, kaine rayuwata, dukkanin wata walwalata tana tare da walwalarka, farin cikinka shine nawa rashin lafiyarka kuwa tashin hankaline gare ni, dan Allah ka tashi gani na dawo gareka bazan kuma tafiya na barka ba, muyi tafiyarmu can nesa da gari muyi rayuwarmu, dan Allah ka tashi.” Na kuma fashewa da kuka, motsa hannunshi yayi sannan ya sauke ajiyar zuciya me nauyi, ji nayi alamun za'a bud'e k'ofa, diri² na fara yi ina neman gurin b'uya, da dai naga alamun za'a shigo a ganni sai nayi wuf na fad'a toilet, muryar Umma naji tana cewa.
"Ki shiga toilet ki wanke fuskarki kizo ki tafi gida kici abinci, insha Allahu zaiji sauk'i idan kina k'in cin abinci ai sai azo ayi biyu ai. ” Ko da bansan wace ba nasan da Suby take, a hankali naji alamun tafiyarta ta tunkaro toilet d'in, bugun da k'irjina yake yine akan nada ya k'aru, na rasa gurin da zana b'oye, a hankali na tsuguna daga bayan sink na rakub'e harbin da zuciyata ke yi yana tsananta, har ta shigo ta wanke fuskarta Allah bai bata ikon ganina ba.

"Muje to ki tafi, zani phermacy na siyo magani, idan Papa ya fito daga gurin doctor zai zo ya zauna da shi. ” Ina jin fitarsu nima nayi sauri na fito, zama nayi gefen gadon ina k'urawa fuskarshi ido, sai da na tabbatar sun fita daga Asibitin sannan na mik'e na shafi fuskarshi a hankali na furta. "Allah ya baka lafiya” Hawaye na cigaba da tsiyaya a idona, sauri nayi na fita saboda kar Papa yazo ya taddani.


Kansa kife bisa stiaring in motar, ya k'ure sanyin A.C in motar na taddashi, bud'e motar nayi ina me had'a kai da guiwata naci gaba da risgar kukana, bai mun magana ba yaja motar a hankula muka soma tafiya.



" Yaronka zuciyarsa ce ta tab'u tun yana d'an shekara 22 a hankali take tab'uwa duk baku san da haka ba, a haka kuma ya kamu da ciwon so me tsanani, kuma da alamu ya kasa samun abinda yake so d'in shiyasa ya shiga wannan mawuyacin halin, dan zuciyarsa na gab da bugawa, sai dai Allah ya kiyaye kawai, kuma muma zamu cigaba da yin iya k'ok'arinmu don ganin ya samu lafiya, amma kuma dole ku nemo masa abinda yake so, idan har kuna son rayuwar d'anku ta inganta. ”

Zufa ce ta kecowa Papa ta tashin hankali k'irjinshi yana wani mugun bugu, jiki a sanyaye ya yiwa Doctor in godiya ya fito, ko da ya gayawa Umma abinda ke damun Hamid kuka ta fashe da shi wiwi ² shi kenan yaronsu namiji kuma Allah ya saka musu mugun soyayyarshi amma suna yin alkunya kasan cewarsa d'an fari, duk soyayyar da suke masa amma suka kasa taya shi son abinda yake so saboda son faranta ran wasu.
"Tir da zuciya irin tamu da muka kasa bawa yaranmu farin cikinsa tunkan dama ta kufce mana, wayyo Allah! Yanzu ina zamu ga Hannatu? Allah ya Ubangiji Allah ka kawo mana d'auki” Cewar Umma tana me kuma fashewa da kuka sosai da sosai.


****

Abba sai da yasha ruwan leda 12 sannan ya daho hayyacinsa, sai da yaji sauk'i sosai aka sallame shi, tunda ya daho hayyacinsa yake tsinewa Hanah, yace sanadinta ne ya shiga wannan halin gashi ya janyowa ma wasu shiga, ai tunda ta janyo masa asarar millioyin kud'i shima sai ya maida finsa a kanta muddin k'udirin da ya k'udirta ya tabbata, yaji takaici sosai da yaji labarin gidansa aka sayar aka karb'oshi.
Police d'in da yasa aka tafi da Hanah yaje amma bai samu ko da labarinta ba, Amma tace.
"Ai duk inda kake tunani Hamid yaje amma ko labarinta bai samo ba. ”
"Allah yasa ma yanka kan tsinanniya akayi don ko ni da na same ta yanka kan shegiya zanyi ta mutu, a yau nayi da kacen sanin Umaima da Muhammad tunda suka shiga rayuwata nake ganin matsalu iri da ban² to wallahi akan uwarta zan wuce takai cina. ”



Abba ya sha tsinuwa da Allah ya isa a gurin Papa da Umma, domin suna ganin duk sanadinsu ne Hamid ya shiga wannan halin, don haka suma Subai'ah ko zata mutu baza su bari ya aureta ba, baran² sukayi sosai kowa na zagin kowa, Papa yace ya tattara matansa da 'ya'yan shi ya bar masa gida, haushin haka yasa Abba ya kwashe su suka cala Abuja, (yana da gida a can) Suby na kuka sosai kamar ranta zai fita haka ta bisu don babu yarda zatayi amma zuciyarta na mata zafi da rad'ad'i.

Dan wulak'anci da tozarci sai da sukaje Abujan ya rattabawa Ammi saki uku, domin ramuwar gayyar abinda suka yimasa tunda dai bai samu nasarar cinye duka dukiyar da Muhammad ya bari ba da kuma abinda yake kwad'ayin sani, amma ya k'udiri niyar nemo Auncle Zaid domin bazai barshi yaci shi kad'ai ba, yarda ya k'wallafa rai akai sai yaci, ita kuwa baiga amfanin cigaba da zama da ita ba tunda yarinyar tata tabar hannunsa k'ilama ta mutu tunda bai san a wace duniya take ba.

Ammi taci kuka sosai, yasan bata da kowa a garin nan, ba ta san ina zata nufa ba, gashi ya rabata da komi nata, shine yaje ya barota da mahaifarta, shine kuma da yasan sirrinta da dalilin barinta gida, gashi kuma shi ya zamo dalilin rushewar farin cikin da ta samu na d'an lokaci kad'an, Abii ya tafi ya barta, shi kuma ya rabata da 'yarta, yasa ta ciwa mutumin da ya d'auketa a matsayin k'anwarsa mutumci, yasa taci amanar alk'awarin da ta d'aukarwa Abii, sannan ya rabata da dukkanin dukiyarsu, gashi ya rabota da cikin mutane ya kawo ta gurin da bata san kowa ba, ba ta san ya suke rayuwa ba, lallai D'ahiru shima K'ADDARA ne cikin RAYUWARSU ita da d'iyarta, gashi yanzu ba ta san duniyar da iyayanta, 'yan uwanta, 'yarta, Uncle Zaid, ga kuma 'yar uwarta da suka zo duniya tare suke ba, tsakaninta da D'ahiru Allah ne kad'ai zai bi mata hak'k'inta, yanzu ko wace K'addara ce ke yaho da ita kuma, ko ina kuma zata dosa oho, kukane ya kuma cin k'arfinta sosai da sosai.





______________
Tunda naga Ya Hamid cikin wannan halin nutsuwa ta bar zuciyata, murmushi ya k'auracewa fuskata sai dai nayi yak'e kawai, sam bani da wata walwala, kullum ina cikin d'aki don raban da naga Ya Hisham tun randa muka dawo bare kuma Ya Haisam, Momy tana yawan kwantar mini da hankali, tana nuna mini in karb'i K'ADDARATA hannu bibbiyu, bani kad'ai ce ke cikin matsala ba, kowa Allah yana jarabtarsa ta abubuwa da dama.
Muryar su Ya Hisham naji a falon Momy, kuma na san Momy tace mini zata gurin Malam Jafar ta dawo, kamar an tsikareni na mik'e na d'auki hijabina na saka na fito, da Haisam muka fara had'a ido nayi saurin kawar da idona ina mai da shi kan Hisham, shi kuwa dama ni yake kallo, narkar da idona nayi cikin nasa idon ina me nuna masa key d'in da na gani kan center table don da alama daga unguwa suke suka yada zango anan.

Kawar da kanshi yayi, ya nuna kamar bai san me nake nufi ba, cikin muryar san kuka nace "Kaji”
D'agowa yayi yana kallona.
"Me naji?” Kuma nuna mishi key din nayi da hannuna ban magana ba, kawar da idonshi yayi daga kaina, ya mik'a hannunsa zai d'au Key d'in ba tare da ya tashi ba, Haisam yayi saurin riga shi d'aukar key d'in yana me mik'ewa.
"Babu inda zashi, ki koma ciki baya jin dad'i.”
Rau² nayi da idona kamar zan saki kuka nace.
"Pls Ya Haisam ka taimaka. ”
"Nace ki b'ace ki bani guri baza shi ba, haka kawai saboda damuwarki sai ya takura kansa?.”
Ya fad'a cikin daka mini wata uwar tsawa wacce rabon da amun shigenta ma na kwana biyu, hawaye naji zir sun fara bin kuncina na girgid'a masa kai na juya zan koma d'aki, sai ji nayi Hisham yace. "Tsaya ” Tsayawa nayi ina me cigaba da kukana.
"Bani key d'in muje.”
Tsaki yaja me sauti yayi

Please Login or Register in order to submit comment