Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi loosing memoryna, sosai taji tausayina hakanne yasa tazo ta dubani.
Bayan naji sauk'i an sallameni Abbakar ya d'aukeni ya kaini gidansu, bayan ya tambayeni labarina na gaya mishi, ya tambayeni wani gari ne na kasa gaya mishi, ga sunan ina fad'a a raina amma na kasa furtawa, daga k'arshe ya bani biro na rubuta, shima na kasa sai kuka kawai da nake, tausayina da soyayyata su suka sashi ya d'aukeni ya kaini gidansu.
Abbakar ne sanadiyar barina bariki, ya kankane rayuwata gaba d'aya ya hanani sukuni ko kad'an, zamana cikin gidan su Abbakar ina matuk'ar jin dad'insa babu tsangwama bare hantara, a gurin Lamrah ne kawai ban jin dad'i k'ara² take nuna mini tsana, don ganin irin kulawar da Abbakar yake bani daga k'arshe muka b'ige da soyayya, wanda ya tayar da hankalin Lamrah, wai ashe sonsa take kamar ta mutu, kuma Ba'ba ta lura da hakan shine tace mata.
"Wallahi muddin ta cewa Abbakar tana sonshi, in ba shine yace yana sonta ba, ba ta yafe mata ba duniya da lahira.”
To hakanne ya hana Lamrah tunkarar Abbakar sai kwandon tsana da ta juye mini.
Ko da Abbakar yace zai aureni Baba bata hana shi ba, sai albarka da ta sakawa abin ta tsaya masa a gaba.
Rana d'aya akai bikinmu da Lamra da wani tsohon saurayinta da ta amshi tayinsa don ganin Abbakar bai ma san tana yiba, amma ta k'udur tarwa ranta abubuwa da dama, soyayya sosai muke sha ni da Abbakar da tattalin juna har Allah ya azurtamu da samun d'a namiji, ya sakhawusa sunan babansa Farouk (Haisam). Sati guda Ibrahim (Yaya) da shi da matarsa Kubrah (Momma) suka zo sukayi, Allah ya saka musu soyayyar Haisam don Momma cewa tayi idan zan yaye shi zata karb'eshi, tunda su har yanzu Allah be kawo musu haihuwar ba.

Allah yayiwa Haisam farin jini ta koina, tun yana yaro yake da wani asirtaccen khawu me d'aukar hankali.
Watana d'aya da haihuwa Lamrah itama ta haihu, ta haifi namiji aka saka mishi Harris, har yanzu babu wata jituwa tsakaninmu ni na rasa ma me na mata, satinta biyu da haihuwa Allah ya d'auki ran Ba'ba, dama mijinta ya bawa shekara biyu baya da rasuwa.
Munji mutuwar Baba yarda me karatu ba ya zato a haka har Allah ya saka mana dangana.

Tun daga yaye Momma ta d'auke Haisam ba su dawo mana da shi ba har suka sanya shi makaranta, mu kuma mukayi kara ba muce ya dawo ba, amma dukkaninmu munyi kewarsa, saboda jini da zuciyarmu ne, yana can yayi rashin lafiya kamar ba yayi ba, hankulanmu suka tashi, a nan aka gane yana d'auke da ciwon zuciya, sosai muka sare da lamarin, kwana nayi ina kuka Abbakar na tausata da yake ya fini k'arfin zuciya, su Momma sosai suka tashi hankalinsu.
Cikin ikon Ubangiji Haisam yaji sauk'i, tun daga sannan bai kuma irin ciwon ba.

Bayan kammala secondary insa ne Allah yayiwa Momma rasuwa, munji mutuwa yarda bakwa zato, Haisam suma ya dinga yi yana sank'amewa har sai da aka dangana shi da Asibiti, saboda Momma ta soshi iya so, don shi a da yayi zaton itace mahaifiyarshi ma, sai da take nuna masa nice mahaifiyarsa tukun ya gane, amma yafi sakewa da ita sosai.
Yaya ma yaji mutuwarta sosai da sosai, shiyasa har kawo yanzu bai sake aure ba, aurenma ya fitar masa aka tunda likitoci sun tabbatar masa bazai tab'a haihuwa ba, shiyasa ya maida hankali kan Business inshi, kuma tuni ya rubuta takarda idan har ya mutu dukka abinda ya mallaka na Haisam ne.


Tun daga mutuwar Momma Haisam ya dawo gurinmu, a lokacin Lamrah ta dawo gidanmu da zama, Allah ya amshi ran mijinta bayan ta haifi Hindu da tagwayenta Khalid da Walid, sai autarta Walida.
Dukkan wata d'awainiya tasu ta dawo k'ark'ashin Abbakar,saboda a lokacin Allah ya kuma bud'a masa samunsa, kud'ine suke shigo masa babu yankewa. Lamrah ta kwantar da kanta muke zaune lafiya k'alau, a kai² Yaya yana kawo mana ziyara, shine kuma ya tura Haisam da Harris Ithopia sukaje sukayi karatunsu a can, a canne Haisam da Hisham suka had'u, jininsu yazo d'aya, shiyasa abotarsu tayi k'arfi, kuma garinsu d'aya. A kai ² Yaya yana kai musu ziyara don ganin ya tarbiyarsu take, sai ya samesu a kimtse ba shashanci karatunsu kawai suka saka gaba, Harris ne ma me wasa, don tun yana gida yake shaye² ba'a sani ba, gashi kuma yanzu yana son fara bin mata, shiyasa duk zuwan da Yaya zai musu sai yayi ta masa nasiha, amma duk a banza, su Haisam ma suna iya yinsu sai ya fara zaginsu sai suka watsar da shi, amma abin yana wa Haisam ciwo sosai, ya tsani yaga Harris yana shaye² bare neman mata.

Yaya ne yacewa Mama.
"Naga Harris yana neman lalacewa shine nace ko a dawo da shi nigeria yayi karatunsa a gabanki? ”
Bud'ar bakinta sai cewa tayi.
"A'a ka barsa, Allah zai shiryasa, shi d'ayan aka san me yake yi. ”
Baice mata komi ba ya rabu da ita.
Tun daga sannan Mama tace wallahi d'anta bazai lalace shi kad'ai ba, sai ta san yarda tayi ta lalata rayuwar Haisam, kai sai ma ta d'auki fansar shiga soyayyarta da nayi,

Daga Haisam har Hisham Allah ya basu k'wak'walwa akwai su da matuk'ar k'ok'ari dukkaninsu sun fita da kyakkyawan sakamako, Harris ma result d'insa ba laifi yayi kyau, shima yana da kwanya ba a iya sha shanci ya tsaya ba, ba su dawo gida ba sai da suka kammala har masters d'insu, Daddy har pherty ya had'a musu bayan dawowarsu gida.

Kyahun Haisam ya kuma bayyana, cikar kamalarsa da kyan haibarsa ba'a magana, farine shi amma ba irin farin nan kar ba, ba ya aski amma sumarsa a gyare take, tana shan mayuka kala² yana da saje wand a ya taho sink'if har gemunsa suna bada shek'i tsabar gyara, baya barin gashin baki don shi a ganinsa muni yake saka shi, hancinsa bai da wani tsayi can, idanuwansa kuwa irin lumsassun nanne k'wayar idon tana bada shek'in bak'in, cikin kuwa farine tas, girarsa idan kika gani sai kice gyarata yayi, a gyare take kawa ta mace, kina dai ganinsa kinga kyakkyawan saurayi wanda dole yasa zuciyarki yamutsawa.
Allah yayi mishi farin jinin 'yan mata duk inda ya shiga sai an samu matan da ya yamutsawa zuciya, bare in suka had'u da Hisham ai kamar a cinyesu d'anyu.
na kance da su.
"Ku kuma so kuke ne na dinga gadinku kawa mace? ”
Saboda mata har gida suke zuwa nemansu, hakanne yasa ake cewa suna neman mata, ga kuma Hindu a gida da take mutuwar son sa, amma inda na fuskancesa shi sam ba ya sonta. kwatsam ba sai Haisam ya fara shaye² ba, mun shiga tashin hankali yarda ba kwa zato randa muka bud'i ido muka ganshi, tun Daddy na damuwa da hakan har ya daina ya tattara shi ya watsar, ya kama Harris ya samar masa aiki ga Asibiti nan yana bud'e masa, shine dawowar da Yaya yayi ya tadda Haisam cikin wannan halin yace na kaishi gurin Malam Jafar, to shine nima na gaya masa tawa matsalar, saboda Haisam yasha matsa mini akan sai na gaya masa inda dangina suke, to shine yake bani rubutu nake sha shiyasa har na iya furtawa Hisham ainihin sunan gidanmu da k'yar sailin da mahaifinshi ya kore shi.

Ban tab'a tunanin Mama ce ta saka hannu cikin al'amurana ba, saboda ganin yanzu babu wata tsana da take nuna mishi, ashe ha'inta ta take, ita taje tayiwa Haisam asirin da yake shaye² itace ta raba soyayyar Haisam da Daddy ta maida masa da soyayyar Harris yake ganinsa kamar Haisam, ita tayi silar da Daddy ya kori Haisam daga gidansa, sannan take son ya sakeni ya aureta, wannan duk fansace ta d'auka akan k'wacen soyayyar da na mata, yarda ta so ta maida rayuwar Haisam Allah bai lamunce ba sai ya tsaya a iya shaye² kawai.
Na samu wannan bayaninne a gurin Sahiba ('yar aiki) kuma tace mini gaba d'aya ta siye 'yan aikin gidan, sune duk suka ciyar da su Haisam asirin da aka musu.
Ni ragon azancin da nayi, na amincewa da Mama, shaf na manta duk mutumin da bai soka da safe ba, bazai tab'a soka da yamma ba.



*CIGABA*

_____________

Likitoci sunce Ammi sai ta ibi watanni hud'u zuwa biyar tana jinya kafin ta warke ras, saboda karaya uku ce a k'afarta, ga raunuka da ta jijji, don haka da suka biya kud'in da aka cagesu sai suka tafi akan zasu samo wacce zatai zaman jinyarta har tsawon wa'yannan watanni....
[12/10, 18:20] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

__________________
*THIRTY SEVINE*
Hisham daga Abujan juyawa yayi V/Island domin dama ba gama abinda yaje yi yayi ba, yanzu so yake ya sayar da Asibitin da ya fara gina musu ya dawo Ithopia dan yana matuk'ar son k'asar, tun tuni suka so rik'esu suyi musu aiki a can amma fir suka k'i yarda, ya samu wanda zai siya amma ba su gama magana da shi ba shiyasa ya koma ya gama harhad'a abubuwansa, daga nan sai yayi Ithopia, in yayi arranging in komai sai yayi Gombe, amma fa yaso yaje yaga Hanah don sosai yayi missing inta, ture ta Haisam shi suna yin vidio call, yankewa zuciyarsa yayi in ya samu lokaci zai kirasa yace ya had'asa da Hanah.



***
Gidan Fulani komai ya dai daita, kawuna sun had'u kowa ya gane an tafka babban kuskure a baya, don an watsa zumunci, Ummi ta dawo daga gidansu, tazo ta nemi yafiyar su Innai, har kuka tayi tace duk bak'in kishin Inno ne ya jaho musu 'yan ubanci, amma dan Allah ta manta komai ta rik'eta 'yar uwa suyi zumuncin da ba suyi shi a da ba.
Hakanne yasa kawuna suka kuma had'uwa guri d'aya, tunda kowa ya gane kuskurensa, sosai yanzu rayuwa take dad'i a cikin gidan babu ban banci tsakanin d'an kowa da kowa.
Gurin wani Malam Mujtafah aka kai matsalarmu ni da Haisam, yace k'warai kuwa sammu aka mana, amma insha Allahu komi zai warware da sannu, idan har anbi k'aida magani, za'a d'au tsawon wata guda ana aikin, ya bada magun gunan da za'a fara aikin da su, sai fatan Allah yasa ayi cikin sa'a.
Jininmu yazo d'aya da Haya da Baby da Hidaya, Halisah ce dai ba ta fiya jana a jiki ba, sai tai tamun wani d'anyen kai.
Ku san ko da yaushe muna tare da juna, tunda dama mune 'yan matan gidan, su Iklima da Ihsan sun bar gidanma gaba d'aya sun kama dabar karuwai, yarda ma naji zancen wai Iklima ce take da ciki har yakai tsawon wata bakwai, kuma an kusa bikin Baby da Hakim saura wata uku ma.



***
Bayan dawowar Hindu daga duniyar bacci tayiwa Mama tijara sosai, kuma tace tunda tayi sanadiyar barin masoyinta gidan itama sai ta bar gidan, ta had'a kayan ta kaf ta gudu gurin wata k'awarta, duk wani kayan maye da yake kore damuwa babu wanda ba ta sha amma ba ta iskanci mutum d'aya take so a cikin duniyar nan, Haisam shi kad'ai zata samu ta daina shaye².
An d'aura auran Daddy da Mama, Mama farin ciki kamar tayi me, ranar da aka d'aura auran ranar aka bud'e asibitin da Daddy yayiwa Harris, me Farouk privert Hospital, da Mama tace sai ya canja masa suna, sai yace mata shi ai sunan babansa ya sakawa asibitin, amma sai da ta san yarda tayi ta amshe duk wasu takardu da suka danganci asibitin.
Yaya da yazo ya tadda abubuwan da suka faru sai da yayiwa k'anin nasa fata² hatta Mama ma bai k'yaleta ba, kuma yayi mamakin da Haisam bai gaya masa ba don suna waya a kai². Bai koma ba sai da yazo Gombe ya bawa su Momy hak'uri akan kar su k'ullaci k'anin nasa duk sharrin Mama ne.
Sannan yacewa Haisam k'arshen watan nan yazo ithopia yana son ganinsa, sun rabu da shi dai akan sai yazo d'in idan Allah yasa da rai da lafiya

Harris kuwa duniya tayi masa dad'i, kud'i suna shigowa ko ta ina, ga kyawawan mata sai wacce ya zab'a zai kwanta da ita, ga kaya na nauikan maye kala², abubuwa dai sunci gaba sun k'ara ta'azzara....
[12/10, 18:20] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


__________________
*THIRTY EIGHT*
Innai tayi masifar iya girki, ita take mana nauikan girkuna kala², duk yarda na so ta sakar mini girkin ta huta k'i tayi, haka ma Momy tayi² ta daina girki amma tak'i yarda, randa naji zan iya na kan shiga kitchen in naga yarda take yi amma ba ta yarda na tayata da komi, sai dai girkinta akwai d'an karan dad'i, in ina ci nakan ce lallai girkin wasu tsofaffin akwai dad'i.
Ni nake kaiwa Yaya Haisam abincinsa har d'aki, tana gamawa ta zuba mishi zata k'wallo mini kira nazo na d'auka, ni kuma ina kaiwa zan dire nayi juyowata, sai dai sam Momy ba ta son mu kasance guri d'aya ni da shi, sai dai ba yarda zatai tunda duk gidan kowa ya d'auka ni k'anwar sace, babu damar ta hanani zuwa gurinsa, kuma itama tsakaninta da shi sai dai kallo, saboda kasancewarsa d'an fari, baza ta zauna tayi hira da shi ba sai ace tayi rashin kunya, duk wani abu da ya dangance shi nice a kai, to inda hankalinta ya kwanta da taga ba zama nake ba da na kai masa zan juyo na dawo.

Yau ne aka gama mana maganin da Malam Mujtafa ya bamu, ma'ana yaune wata ya cika, tun jiya Yaya Haisam yake kelaya amai bak'ik'k'irin ya jigata sosai wanda sai da ya saukar masa da ciwon kai da zazzab'i, a d'aki ya huni sir, sai zuwa duba shi ake yi, amma Momy sai waya sukayi Innai ta hanata zuwa, ita dai Momy wannan al'ada ta fulani tana ci mata tuwo a k'warya, ba ta san girman soyayyar da takewa Haisam bane, yanzu da taji bashi da lafiyar nan gaba d'aya hankalinta ya tashi,so take kawai ta ganshi amma ina.

Mik'ewata kenan daga gado zan shiga bayi na wanke bakina, naji Innai na k'walon kira kamar zata tashi gidan gaba d'aya, Hijabina na d'auka na saka har k'asa, saboda rigar bacci ce jikina, duk da doguwa ce kuma da d'an kaurinta, saboda yanayin sanyi.
"Maza d'auki kije ki gano mini jikin Haisam, girkine na masa na marasa lafiya, ki tabbatar yaci sosai. ”
"To” nace ina tsokanarta.
"Ke dai Innai kin fiya son jikan nan naki da yawa.”
"Ba dole na soku ba, bayan ku wa nake da su?”
Tausayinta naji ya matuk'ar kamani. 'Yanzu idan ta san ni ba jikarta ba ce, ai soyayyar da zata nuna masa sai tafi haka, hawaye naji ya siraromun na saka hannu na goge, ina tausayawa rayuwata, yanzu ni haka zan k'are a k'aryar dangi, kai bari na saka ya kira mini Rumanah, nace mata gaskiya zanje kano gurin Ammina, sai dai Abba ya sakani gabas ya yanka kaina, ko na huta da K'ADDARAR RAYUWA.'
K'arar bud'e k'ofar da nayi ce ta saka shi fito da kansa daga cikin bargo, don ganin waye, idanuwan mune suka sark'e, nayi saurin yin k'asa da kaina, na ajiye tiren abincin kan kujerar mudubin d'akin, na huce toilet, sai da na wanke band'aki sannan na had'a masa ruwa me d'an d'imi na fito, idonsa na kan k'ofar band'akin ina fitowa idanuwanmu suka gauraya guri d'aya, idanuwansa sunyi ja kuma sun d'an k'ank'ance saboda kansa da ke masa ciwo har yanzu, hannu ya mik'o mini, yana so na taimaka mishi, don ya san me nayi a toilet in, k'arasa wa nayi gabansa, na mik'a masa hannuna, wani sanyi naji gami da laushi ga yarda tsigar jikina ta wani tashi saboda kasantuwar hannunsa cikin nawa, yunk'urowa yayi da k'yar ya mik'e, sauri nayi na janye hannuna na matsa, bai kalleni ba ya fara takawa a hankula ya shi ga toilet in.
Kafin ya fito na gyare d'akin tsaf, sai bada k'amshi yake, na fito masa da kayan da zaiji dad'insu, ina jin motsin fitowarsa nayi saurin mik'ewa zan fita.
"Ina zaki? ”
Tsayawa nayi cak amma ban juyo ba.
"Um mm jira zanyi ka shirya. ”
Bai magana ba, sai zama da yayi bakin gado, jin shiru ni kuma yasa na k'arasa fita.
A k'alla ya d'auki kusan mintina 20 kafin ya gama shiryawa, naji yace.
"Zo ki bani abincin.”
Faten dankalin turawa tayi masa, sai farfesun naman kaji da sukayi laushi tub'us, tsabar dahuwa, yarda zaiji dad'in ci.
Bak'in ruwan tea na fara basa ya sha tukunna sannan na zuba mishi faten, mik'a masa nayi yak'i ansa, da hannu ya nuna mini bakinsa yana kallon tsakiyar idona, k'asa nayi da kaina cikin jin kunyarsa.
"Idan dai baki bani ba sai dai in ba zanci ba, don cokalin ya mini nauyi. ”
D'ago da kaina nayi, muka had'a ido ya d'age mini gira d'aya, ji nayi wani irin yanayi yana shigata.
K'i nayi mu had'a ido, har na gama basa, namanma yanka d'aya yaci, bayan na zame masa shi daga jikin k'ashin.
Ruwa na zuba masa cikin cup, na b'allo masa maganin ciwon kai da yace na b'allo masa, mik'a masa ruwan nayi ya had'a da hannuna ya rik'e, yana kallon cikin k'wayar idona, lumshe idona nayi, saboda jin yarda sanyin ruwan ke ratsa tafin hannuna ga wata kasala da ta saukar mini.
"Kurma kika zamane? ”
Idona na lumshe nace masa me ka gani?”
"Baki min magana. ”
"To me zance maka?”
D'an k'asa yayi da muryarsa yace.
"Baza kice mini ya jiki ba? ”
Kuma lumshe idanuwana nayi, don jin yarda na kuma tsunduma cikin irin wani yanayi, murya can ciki nace.
"To ya jiki?. ” Ina d'an turo baki gaba.
"Bar abinki sai da na rok'a. ”
Cika mini hannuna yayi, yasha maganin, ya jingina da jikin gado, ya lumshe idanuwansa.
"Zuba abincin kici. ”
"Ban goge bakina ba.”
Su Haya ne suka bud'e k'ofar suka shigo, gefen da yake Halisah ta nema ta zauna, su kuma suka zazzauna kusa dani, tana zama kusa da shi ya murtuke fuska sosai, don yarinyar ta fara matsa mishi, ya rabu da Hindu ala k'a k'ai, gashi yanzu yaga alamun yarinyar nan so take ta takura masa, ta saka mishi ciwon kai.
Tashi nayi zan fita yace mini koma ki zauna, yana kallona, ba musu na koma na zauna, gaishesa sukayi sukai masa ya jiki sannan suka tashi zasu fita amma banda Halisah, Baby ce ta kalleni tace.
"Shine jiya mukai ta zaman jiranki ba ki dawo ba, Ummee har tana ajiye miki d'an wake. ”
"Wayyo ai ban sani ba, jiya wani irin barci naji ina ji, idona har ruwa yake, amma yanzu in nayi wanka zan shigo, kinga Yayane ya hanani tafiya tun d'azu. ”
"To shikenan.” Baby tace suna k'arasa fita daga d'akin, Halisah ce tace.
"Kije ni zan zauna da shi. ”
Ban san sanda na jefeta da wata shegiyar harara ba, dariya ce ta kusa kama Haisam amma ya shanyeta yace mini.
"Tashi kije to, tunda ni na hanaki tafiya, gashi na samu wacce zata zauna da ni.”

Wani haushi ne ya kamani na mik'e zan fita, ita kwa Halisah sai sakin murmushi take zan basu guri, har na kusa kai bakin k'ofa yace mini.
"Dawo ki d'auki abincin. ”
Da kamar kar na dawo na d'auka, sai dai kawai na koma na d'auka na fita ko k'ofar ban rufe musu ba.
Ina fita itama yace mata ta tashi ta bashi guri, ba shiri ta tashi ta bar d'akin tana k'unk'uni. Kitchen naje na dangwarar da kwanukan na koma d'aki da gudu, zuciyata tayi mini wani irin nauyi sai kawai na saki kuka don shine kawai zai sassauta mini raina.


MAY BE KUGA WANI IN ANJIMA.
[12/10, 18:21] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


_________________
*THIRTY NINE*
Irin k'atun² d'in motocin nanne suka bi ta kan Janah da Jabir a can yawon bararsu, ko shurawa ba suyi ba suka amsa kiran mahalicci, Amma tayi kuka da idanunta har sai da taji kamar tayi me, duniyar gaba d'aya ta fitar mata a rai, kwatsam suka had'u da wata K'awarta da sukayi bariki tare a da, ai kuwa ta wanke jikinta ta koma bariki, tsofe² da ita tsabar masifa, nan ta fara zagayawa har k'asashen waje, likafa taci gaba.

Abba duniya tayi masa zafi sosai, rayuwa cikin prison in da yake yi ji yake dama mutuwa ta riskesa, domin wahalar da shi ake yi da ayyuka masu tsanani, gashi babu wanda yake zuwa gurinsa, dama shine me k'arfi a cikin gidansu, kuma a lokacin babu wanda yake saurare cikin 'yan uwanshi, gidansu ma sai yafi k'arfin wata bai doshi hanyarsa ba, ko sune suka zo gidan haka Amma zata zagesu tsaf kuma babu a binda zaice, hakanne yasa duk suka watsar da shi suka barshi da Amman.

Miftahu, wanda ya taimaki rayuwar Ammi kenan, k'annensa ya kawo Aisha da Faiza, suka zauna suna jinyar ta, babu laifi jikin nata yana samun sauk'i sosai.

__________
Tun daga wannan ranar ban kuma saka Haisam a idona ba, da naga Innai ta kusa sauke girki zan tafi gurin su Haya muyi ta shan hira sai kwanciyar bacci ce zata dawo da ni, da safe kuma nak'i fitowa da wuri na more baccina.
Har yaji sauk'i ya warware Innai ce da kanta take kai masa abincin, har sai yaci a gabanta sannan zata bar d'akin.
Misalin k'arfe tara da kusan rabi na fito daga gurin su Haya, Baby na hango da Ya Hakeem a jikin motarsa, d'ago mini hannu tayi na k'arasa gurinsu da fara'ata muka gaisa da Ya Hakeem, pop corn Baby ta bani da Ya Hakeem ya kawo mata.
"Ci kiji wallahi akwai dad'i, nima yau na tab'a cin irinsa.”
Karb'a nayi nace na gode, ban ci ba yana rik'e a hannuna muna ta hira da su cikin raha, duk don na kuma jan lokaci, Ya Hafiz ne ya iso gurinmu hannunsa rik'e da key in mota, Baby ce tace.
"Ya Hafiz fita zaka yine?”
" Eh fita zanyi abu zan ansa a Ummee plaza yanzu zan dawo, ko zaku rakani ne?. ” Yakai k'arshen maganar yana sauke idonsa a kaina.
"Murmushi Baby tayi, don ta gane nufinsa tace.
"Sai dai Hanah ta rakaka, ni baka ga a gaban wa nake ba?”
"Gaya masa dai, ina ga ya makance. ” cewar Ya Hakeem.
Murmushi yayi baice komi ba, ya rank'wafo yana kallon cikin idona.
"Zan samu alfarmar rakiyar Hanah? ”
Cikin sanyin murya nace. "Muje to ”
Murmushi yayi yace.
"Thanks ”

Yana gaba ina binsa a baya zamu shiga cikin plaza in naji ance.
"Suhanah”
Juyowa nayi a fusge da tunanin waye zai kirani da wannan sunan, wata yarinya na gani da ba ta huce shekara 8 ba tayo cikin gurin da gudu, nake to mahaifiyarta tace take kiranta, kallona matar tayi cike da mamaki tace.
"Sunanki ne kema? ”
Murmushi nayi gami da d'aga mata kai, murmushi itama tayi tace.
"Sunan yarinyata ne nima.”
Kallon yarinyar nayi, 'yar kyakkyawa da ita, nayi murmushi na d'anja kumatunta.
"Beauty girl Allah ya rayaki.

Please Login or Register in order to submit comment