Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine nake tunanin idan nayi aure wa zai dinga baka abinci, kullum saidai ka dinga yaho a titi, abinda yake damuna kenan, sai naji kamar na fasa auran wallahi. ”

Murmushi yayi yana jin soyayyar k'anwar tashi a cikin jininshi, yace.
"Kada ki damu, wannan matsalar bata isa ta hanaki aure ba, ina da guraran da zanje naci abinci, ko Momyn Haisam baza tab'a gajiyawa dani ba. ”

"To ai Yaya ni ba akan haka kawai nake son kayi aure ba, ina son mu'amalarka da Baffa ta koma kamar da, ina son naga Baffa yana nuna maka soyayya kamar sanda yake yimaka Ummi tana da rai, ace yaya kai da gidan mahaifinka baka isa kasa k'afa a koina ba sai gurin da aka keb'ance ka, kuma wlh da rashin auranka ne ta samu damar yimaka fanfo a gurin Baffa, har cewa takeyi mata kake kawowa gidannan, ko yanzu kafin na fito sai da mukayi da ita akan Kalmar mazinaci da ta jefeka da ita. ”

"Hmmmm Rumana kenan, ai aure lokaci ne, kuma komai Aunty takeyi lokacine, akwai sanda Baffa da kanshi zai gane makircin Aunty ne ya rabamu, akwai lokacin da zai gane ni ba mazinaci bane k'age ne kawai take mun. ”

"To Yaya yaushe ne lokacin zaizo, kullum haka kake cewa, hak'urinka yayi yawa Yaya, don taga kana da hak'uri shiyasa take wasu abubuwan wallahi.”

"Ai hak'uri shine ribar zaman rayuwar duniya, akwai lokacin da ribar hak'urin nawa zata zo, tashi maza ki koma, kar a samu damar k'ulla wani sharrin. ”

Tashi tayi tana zunb'uro baki a ranta tana cewa. "Shi kullum yace akwai lokaci, to yaushe ne lokacin zaizo? ” Babu me bata wannan amsar, kawai tasa kai ta fita.

Murmushi kawai yayi, yasan halinshi da na k'anwarshi ba d'aya bane, shi yana danne duk abinda za'ayi masa, amma Rumana bata iyawa, ko sanda Umminsu na da rai irin cin zarafin da dangin babansu suke mata Rumana me ramawa Ummi na kwab'arta, daga shi har Mahaifiyar tasu wani irin sanyin hali garesu.
Janyo tiren abincin yayi ya zuba yaci ya k'oshi, ya d'auro auwala ya gabatar da sallarsa ta azahar, sannan ya shiga ya kwanta.




*****
Haisam bashi ya farka ba sai isha, bud'e idonsa yayi ya sauka a kan Hisham da ke zaune kan sallaya yana karatun Al'Qur'ani me girma, bayan ya idar da sallar isha, abinda yasa baya zuwa masallaci baya k'aunar had'uwarsu da Baffa, kuma ya san muddin ya fita sai sun had'u.

Idonsa ya kai kan agogo ya nuna masa Takwas saura, ji yayi kawai hawaye na wanke masa fuska, k'ank'ame jikinsa yayi ya saki kuka mara sauti don kar Hisham yaji shi, gani yayi tsayawa kukanma kuma b'ata lokacine, don haka ya durgo daga gadon ya shiga toilet, sai a sannan Hisham yasan ya farka.

Wanka ya soma yi, sannan ya d'auro auwala, bayan ya goge jikinsa da tahul, ya d'aukko jallabiya maroon calour a goge sai k'yalli take, ya k'arasa jikin mirro ya fesa turare ( turarenma iri d'aya suke amfani dashi.)

Sallaya shima ya shimfid'a ya kalli gabas, sai da jero Azahar, La'asar, Magariba da Isha, yana zubar da hawaye sosai har ya idar, ya fara tasbihi, hannu ya d'aga sama yana kuka wiwi² yace.
"Allah ya Ubangiji Kaine ka jarabceni da wannan rayuwa, ba wai don baka sona ba sai don ka jarabceni, Allah Kana gani nafi kowa tsanar rayuwar da nake ciki amma babu yarda zan iya, Allah na rok'eka don isarka, don tsarkin mulkinka don soyayyar da kakewa Annabi Muhammad ka fitar dani daga wannan rayuwar.” Yana kaiwa nan kuka yaci k'arfinsa, kuka yake abin tausayi.

Rufe Qur'anin yayi, ya tazo yazo inda yake ya rungumeshi, shima yana zubar da hawaye, rungumeshi Haisam ya kuma yi, yace.
"Hisham a duk sailin da na dawo hayyacina na kanji na tsani kaina, ina sanya Mahaifana kuka da idanunsu a kan rayuwar da na jefa kaina, wallahi ba laifina bane nima bansan sanda nake sha har na bugu ba wallahi. ”

Rungumshi Hisham yayi cike da tausayin abokin nasa.
"Kayi hak'uri, Allah yana sane da kai, Allah zai amsa addu'armu bajima ko mu dad'e, komai yana da lokaci, wata rana hakan zai zamar mana tarihi kamar ba'ayi ba, kowa yana da k'addararsa a rayuwa mu K'ADDARAR RAYUWARMU kenan Allah kuma ya bamu ikon cinyeta Amin. ”
[12/10, 10:12] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

*Hoho Suhanah baiwar Allah, tun kan akai nisa da jin k'addararki har an fara tausayinki, harda masu zub da k'wallah, Hmmm My Readers kenan ba kuji komai ba a k'addar Suhanah, Hamid, Haisam, Hisham ba, yanzu aka soma gashi, ku dai ku bini a hankula har mukai ga inda muke so, na gode da supported.*

*Tunatarwa*
_Idan har Hannah ta baki tausayi, me yasa idan har kinga me irin halinta a gaske baki tausaya mata? Sai dai a k'anjameta duk abi a tsaneta, kowa ya dinga kyararta, bayan ba ita ta sakwa kanta ba, tabbas sata akwai ra'ayi, akwai kuma matsi na rayuwa, akwai ribatar k'awaye, akwai kuma sihiri, haka zalika kuma ana gadon ta, amma duk me, sun had'u a k'ark'ashin k'addara, kowa yana da k'addararsa a rayuwa, fatanmu Allah ka rabamu da mummunar k'addara, Allah ka shiryi dukkanin masu hali irin wannan, ka bamu zuri'a d'ayyiba, Amin, fatan shiriya shine ya dace dash ba kyara ba, Allah kasa mu dace Amin._


~GORON SALLAH~
____________________
*FIVE EPISODE*
Sai da suka yi me isar su, daga bisani Haisam ya mik'e zai tafi, sai a sannan na lura jallabiyar jikin su ma iri d'aya ce.

"Ka bari Rumana ta kawo mana abinci mu ci sai na kaika gida. ”

"Um um kazo muje can, na san Momy ta ajiye mana. ”

Bai magana ba, ya d'auki key d'in motar da ke kan mirror suka fice.



****

Suna k'aton falo suna cin abinci a kan dainin, irin dainin d'in nanne me kujeru goma sha biyu, Yaya ne ya kafa dokar hakan tun usuli, indai za'a ci abinci sai an had'u gaba d'aya a falo za'a ci, sai dai in mutum baya nan, a cewar sa hakan zai k'ara shak'uwa sosai tsakanin su.

Yaya ne a farko, sai Daddy, Harris, Mama, Momy, Hindu, Khalid, Walid, sai auta Walida, sun nutsu suna cin abincinsu cikin kwanciyar hankali.

Suna zuro kahunansu falon sukai karo da su, d'auke kai Haisam yayi ya d'auki hanyar da zata sada shi da phart d'inshi, shi kuma Hisham ya nufi gurinsu.

"Haisam” Yaya ya kira shi, amsawa yayi shima ya nufo gurin nasu, lokacin har Hisham ya ja kujera ya zauna Hindu na saving d'inshi, shima kujerar yaja ya zauna, tana gamawa da Hisham ta dawo kanshi, wani sanyayyen kallo take binshi da shi, shikuma ya d'aure fuskarshi tamau, kamar ba'a halicci murmushi a jikinta ba, k'afarta ta saka tana shafa lallausar k'afarshi, saka k'afarsa yayi ya murje mata d'aya k'afar da takalmi ba ta san sanda ta saki gigitacciyar k'ara ba, Daddy yace. "Lafiya ”
Cikin shagwab'e fuska tace. "Wani abu ne ya cije ni ”

"Kai duba ka gani meye ya cijeta, ka tsaya kamar gunki. ”

Kuma tamke fuskar shi yayi a kan ta da, ya sunkuya ya sakar mata mintsini a k'afa, ya d'ago yana ciccin magani da k'yar ya furta "Babu komi ”

Daddy zaiyi magana Yaya yayi saurin katse shi da. "Ja abincinka kaci, kaji Babana iskancin tane kawai. ”
Jan abinci yayi gabanshi ya soma ci, ita kuma cike da takaici ta koma gurin zamanta.

"Abbakar (Daddy) da Ummee (Mommy) Babana (Haisam) in an gama cin abinci ina son ganinku.” Cewar Yaya (Ibrahim) dukkanin su suka amsa da tom, yayin da takaici ya ishi Mama da Harris, wani munafincin kuma za'a kitsa da za'a ware su, to wallahi sai naje, sai dai a fasa maganar da za'ai, cewar Mama.

Ana gama cin abincin Hisham yayi musu sallama ya tafi, su kuma suka haye sama falon Yaya, don nanne gurin tan tannawa rsu. Kallon Mama Yaya yayi shak'e² yace. "Lamrah na kira sunanki a nan? ” Zata marai raice fuska, ya daka mata tsawa, ba shiri ta fice daga d'akin don tana mugun shakkarshi, amma duk da haka sai da ta lab'e a bakin k'ofa.

" Naji wani labari da baimun dad'i ba, ka samawa Harris aiki, kuma sannan kana gina mishi asibiti,sannan kuma na d'ora shi a kan dukkan harkokinka shikuma Babana ka k'wace takaddun sa meye dalilinka na yin haka?”

Numfusawa Daddy yayi yace. "Bayan dawo warsu daga makaranta ne alamarin Haisam gaba d'aya ya lalace, kullum cikin shaye² yake, ance ma har da neman mata, don halayyar abokinsa ce Hisham, nayi wa'azin, nayi nasihar nayi iya k'ok'arina Haisam ya bar abinda yake amma yak'i ji sam, sai daga baya nake ji ashe tun yana can yake yi, b'oye mana yake, shiyasa nak'i samar mishi aiki, saboda aikinshi ba na masu hali irin nasa bane, saboda shi dare da rana a buge yake, takaddunsa na kwace ne don duk ya sauya halinshi amma ina, Haisam yak'i ji, kullum cikin zubar da hawaye nake a kansa daga ni har mahaifiyar shi. ” Yakai k'arshen maganar yana d'auke k'wallar idonshi.

Hannu Yaya yasa yana shafa kan Haisam, yace. "Babana garin yaya hakan ta faru? Bayan ban tab'a kama ka da mugun hali ba a duk ziyarar da nake kai muku, dan har d'an uwan naka yafi ka shashanci.”

Sai da ya d'auke k'wallar idonshi da ta tarar masa sannan yace. "Yaya k'addara ce ta fad'omun, wallahil azimu ban sanda nake sha ba, sai dai na farka na ganni cikin halin, a duk duniya babu abinda na tsana illa naga d'an uwana yana shaye² sai gashi abin ya fad'o kaina, amma wallahi Yaya bana neman mata, daga ni har Hisham, asali ma mata basa gabanmu kawai k'age na mutane. ”

"Ni nasan da haka Babana, na san sharri ake muku da kai da Hisham duk na san halinku tsaf, sannan kuma ka kwantar da hankalinka ka kuma tashi da addu'a babu dare babu rana, domin akwai mutane mugaye a zagaye da mutum bai sani, wanda ko giftawar ka baya son gani, bance wani abin akai maka ba, illa babu abinda yafi k'arfin addu'a, inma sharrin mutum ne Allah ya mayar mishi kanshi, nima zan tashi da addu'a sosai, zan saka malam Jafar ya dinga ma rubutu ka dunga zuwa can kana sha. Kema Ummee sai kin mik'e tsaye sosai gurin yimasa addu'a , bakin uwa bashi da hijabi ga 'ya'yansu, shi mugu bashi da kama, akwai wanda ya tsani ya bud'e ido ya ganka, wannan duniya sai dai fatan dacewa. ”


Ummee har da k'wallarta tace. "Mun gode sosai da tunatarwa Yaya, Allah ya bar girma da lafiya, insha Allah zamu mik'e sosai a kanshi.”

Daddy kwa shiru yayi, don duk bai yarda da abinda Yaya yake cewa ba, ba wata k'addara kawai dai Haisam ya lalata kansa ne da ya wulak'an tasu ya tozarta su, don yaga sun k'wallafa duk wani buri a kansa.

"Yauwa Ummee,na gode da kika fahimceni, kija d'anki a jiki sosai, ki kula da zuwansa gurin malam Jafar yana karb'ar rubutun, zan masa waya insha Allah, don ni gobe nake son juyawa insha Allah, kar ki biye ta Abbakar shi an riga an juyar mishi da tunani, ki kula sosai, ki kuma dage da addu'a, nima ina can zan tayaku da addu'a insha, Allah Ubangiji ya shirya mana zuri'a gaba ki d'aya. ”

Amin dukkaninsu sukace, ya shafa kan Haisam. "Allah yashi maka albarka Babana, tashi kaje ka kwanta, insha Allah komai zai huce.”

"Amin Yaya na gode sosai, Allah yasa ka gama da duniya lafiya, ya k'ara tsawon rai me amfani. ”

”Amin Babana ”

Ummee ta mik'e ta kama hannunshi suka fita, suka bar Daddy anan, don suyi ganawarsu ta 'yan uwa. Mama dake lab'e a bakin k'ofa tayi saurin lab'ewa a inda ba za'a ganta ba, sai da ta bari suka sauka, sannan itama ta sauka, taja Harris d'aki ta zayyana masa abinda aka ce, Harris yace.
"Kaji Yaya kamar me aiki da aljanu, maganarsa kamar lauje cikin nad'i yake yinta. Kuma na lura fa tun tuni Yaya yana mini bak'in ciki. ”

"Nima haka na gani wallahi, amma ka rabu dasu gaba d'ayansu, in sun san wata ni basu sanni ba.”
"Yauwa Uwa ta gari, me son farin cikin d'anta, shiyasa nake sonki. ” ya bata hannu suka kashe, suka kwashe dariya.
[12/10, 10:12] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


~GORON SALLAH~
____________________
*SIX EPISODE*
Da jan jiki ta samu ta k'arasa d'akinta, kwanciya tayi a tsakar d'akin ta fashe da kuka me sosa rai, wai har yaushe ne kuka zai k'auracewa idanuna, ni dashi na tabbata mun zamo hanta da jini, rabuwarmu sai ranar da numfashi ya bar gangar jikina, a binda zuciyarta take ta sak'a mata kenan, tana cikin wannan halin bacci mara dad'i yayi nasarar sace ta.


***

Washe gari da ciwon jiki ta tashi, goshinta ya haye sintim, ko yaya ta motsa k'afarta zafi take mata, a daddafe ta samu tayi shirin makaranta, don tana son kaiwa juneaner Assignment d'in da ta basu, kuma in tayi zaman gidanma ba dad'inshi zata jiba, da bin bango kamar b'era ta samu ta fita bakin get, a lokacin su Suby har sun gama shiga mota za'a tayar, Ammi ce ta kirata ta bud'e mata gidan gaba tace ta shiga ko tausayinta taji ne oho mata.

Da shigarta Class, zazzab'i kamar jira yake ya sauka jikinta me matuk'ar zafi, gurin zamanta ta zauna ta rakub'e tana ta rawar d'ari, a haka Rumana tazo ta sameta, tab'a ta tayi, taji uniform d'in jikinta kanshi ya d'au zafi.

"Subhanallah Hanah, ya akai kika zo makaranta a haka?”

Cikin matsanancin ciwo tace. "Idanma banzo ba waye zai kula da lamurana? ” Hawaye ya biyo k'arshen maganarta, girgiza kai kawai Rumana tayi ta mik'e ta fita.

Tana fita ta hangi Auncle Amin a kusa da lambu ta k'arasa gurin da yake, bayan sun gaisa tace. "Dan Allah Auncle wayarka zaka aramun. ” Ba musu ya mik'a mata wayar ansa tayi tana godiya, number Hisham ta saka ta kirashi.
"Hello Yaya”

"Hello Rumana ya akayi? ”

"Dan Allah Yaya kazo makaran tarmu yanzu. ”

"Me ke faruwa? ”

"Kaidai Yaya kazo dan Allah ”

"To aini yanzu kinga saura mintina talatin na shiga theater. amma bara na turo miki number Haisam ki kirashi.”

"A'a nidai Yaya ka kirashi, kasan doguwar magana bata tab'a had'amu dashi ba. ”

"Tom shikenan, bara na kira miki shi.”
"Yauwa Yayana godiya nake. ”
K'it ta kashe wayar, ta kaiwa Auncle Amin wayarsa ta juya zuwa class.


*****
Yana ciki mota, ya kwantar da kujerar shima ya kwanta, ya d'ora hannunsa a kansa yana tinanin halin rayuwa, wayarshi dake gefensa ce tayi ringing, hannu yasa ya d'auka, My Blood na gani jikin wayar, d'agawa yayi ya kara a kunne.
"Hello Blood dan Allah kajemun makarantar su Rumana, ta kira akan naje nikuma theater zan shiga.”

"Tom shikenan Blood bari naje a fito lafiya, Allah yasa ayi a sa'a.”

"Amin Bloody.” k'it ya kashe wayar.

Suna gama wayar ya tada motar ya nufi makarantar.


****
Tana shiga class d'in ta d'ago ta, sai a sannan ta lura da yarda goshinta ya kumbura, a sanyaye tace. "Abbane ya dake ki ko?”
Bata iya bata amsa ba, sai hawaye da ya biyo bisa kuncinta.

Da taimakon Rumana ta iya takowa suka fito bakin get, suna jiran zuwan Haisam.

Ba jimawa kad'an sai gashi ya iso, da su ya fara karo a bakin get d'in, don haka sai yayi parking a gaban su, bud'e gidan gaba Rumana tayi ta shiga.
"Ina kwana Ya Haisam.”

"Lfy lau Rumana. ”

"Yaya dan Allah k'awar nan tawa zaka kai asibiti, tana buk'atar taimako. ”

D'ago da idonsa yayi yana kallonta. "Kamar ya nakai ta asibiti, ita ina 'yan uwanta ”

"Ya bata da kowa me lura da lamarinta. ”

Kamar ya bata da kowa, iyayanta mutuwa sukai, bata da kowa kuma take wannan makaranta mai matuk'ar tsada, abinda yake sak'awa a zuciyarsa kenan, amma sai ya tab'e baki saboda ba shirginsa bane.

"Ta shigo to mu tafi. ”

"Ai babu ni za'a, zamui test kuma za'a anshi Assignment d'in da aka bamu. ”

Sakin sitiaring d'in motar yayi ya tsaya yana kallonta.
"Aikwa sai dai a fasa zuwan, kinsan dai a zargin da muke daga ni har yayanki, taya za'ai na d'auki mace a motata daga ni sai ita? ”

"Yaya taimako zakayi, babu ruwanka da zargin mutane, wannan zargi babu me fitar daku sai Allah, Allah yaga zuciyarka, idan akace za'a biye ta mutane babu abinda za'a aikata, Ya pls nd pls ka taimaka tana buk'atar taimako.”

Rintse idonsa yayi, daga bisani ya bud'e , "Ta shigo”

"Yauwa Ya, thank u .”

Fita tayi, ta kamota ta sakata gidan gaba, ta rufe, yaja motar tana d'aga musu hannu, har suka je asibitin ko kallon gefen da take baiyiba, hankalinshi yana kan hanya.

Fita yayi baice mata k'ala ba, ganin haka yasa itama ta fito, rufe motar yayi, yayi gaba abinsa, bin bayanshi tayi tana d'ingisawa a hankali, sai da yayi nisa sosai, sannan ya juyo, yaga wayam babu ita babu alamunta, tsaki yaja cike da b'acin rai......


Kuyi hak'uri da wannan...





Masu buk'atar group kuna iya tuntub'ar number kamar haka👇🏼

08096781351
[12/10, 10:12] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

*Akwai wa'yanda suka mun magana akan group ban samu na basu amsa ba, sakamakon what's upp d'ina da ya samu matsala, bawai wulak'anci ne yasa haka ba, domin mu writer's ba ma fita a gurin reader's.
Ku tuntub'i number kamar haka👇🏼
08096781351


~GORON SALLAH~
____________________
*SEVINE EPISODE*

Hamid gangar jikinsa ce kawai a Sudan, amma zuciyarsa tana Nigeria, duk wani tunani nasa da farin cikinsa da walwalarsa suna ga Suhana, tun tana yarinya ya rayu da sonta, duk wani bugu da zuciyarsa zatayi da sonta take bugawa, ko wani numfashi idan ya shak'a da sonta yake shiga, duk abinda ake masa a kanta, dai² da rana d'aya bai tab'a jin sonta ya ragu bama, sai ma dad'uwa da yake.

Idan har ya zauna sai ya kammala karatunshi zai koma Nigeria yana iya rasa rayuwarsa, don muddun ya sake sukayi candy ana iya had'a wani tuggu da zaiyi kokawa da numfashinsa, ya tabbata idan ya rasa Suhana a duniyarsa to ya rasa rayuwarsa, a duniya babu abinda ya nema ya rasa illa mallakar Suhanah da ake k'ok'arin hanashi. Itace jinsa, ganinsa, farin cikinsa, walwalarsa, itace komai nashi, soyayyarta da k'aunarta sune suka zamo k'addararsa a rayuwa, kuma yana ji a jikinsa sune zasu zamo ajalinsa muddin akayi yunk'urin hanashi mallakarta.




*****
Tana komawa class taji Subai'a tana labartawa k'awayenta yanda alamarin ya kasance, ta d'ora da cewa. "Muddin mutum bazai daina halin da yake ba, to wata rana yana iya rasa ransa gaba d'aya. ”

Murmushi mai ciwo Rumana tayi, ta janyo littafi tana karatun test d'in da za'ai musu, don baza ta iya sauraran yarda suke aibata mata Hanah ba, don idan zuciya ta ciyota za'ayi b'atacciya.





****
Yana tafe yana jan siririn tsaki har ya tadda ta a zaune tana ta sharb'ar kuka, tsayawa yayi a kanta ya kasa magana saboda b'acin rai.

"Kee kukan me kikewa mutane? ”

Kanta yana k'asa tace "Na kasa tafiyar ne, k'afana zafi yake mun, ga juwa da nakeji. ”

Tsaki yaja, "Mtsss Rumana ta had'ani da matsala wallahi.”

"To yanzu ya kike so na miki? ”

"Ka maida ni gida kawai. ”

"Na maida ki gida, kuma ki zauna cikin ciwon?”

"Eh dama kullum cikin ciwon nake ”

Shiru yayi yana nazarin maganarta, daga bisani ya mik'a mata hannu, d'agowa tayi tana kallon hannun nasa mai matuk'ar kyau, agogon da ke hannunshi sai k'yalli yake, hannunta ta zira cikin hannunshi mai matuk'ar laushi, a hankali ya mik'ar da ita tsaye, yana rik'e da hannunta suna takawa a hankula saboda raunin k'afarta, gani yayi zasu jima basu k'arasa ba, indai a haka zasu, ga Momy na jiransa zasu je gurin Malam Jafar, kawai sai ya yanke shawarar d'aukarta, ai Allah yaga zuciyarsa a cikin hali na ciwo ne.

Kawai sai ji tayi anyi sama da ita, rufe idonta tayi, ta d'ora tafukan hannunta akai, saboda kunyarsa da taji ta dabai bayeta, siririn tsaki ya ja gami da tab'e baki, mamaki ya kama shi saboda yarda yaji ta shafal kamar bai d'auki komai ba.

Gurin Dr Salim ya kaita, ya barta a can akan yayi mata duk abinda ya kamata zashi ya daho, domin Momy sai kiran shi take a waya, yana barin asibitin gida ya nufa, yana zuwa ya tadda Momyn a shirye shi take jira, don haka ba b'ata lokaci suka nufi gidan Malam Jafar.

Ko da suka je, bayan sun gaisa, ya d'aukko rubutun ya bashi, Yace "Maza yi bismillah kasha, ka shafe ragowan a fuskarka.
"Toh” Yace ya karb'a da bismillah ya kafa kai yana sha a hankula, sai da ya shanye shi, sai amai kuma, yadinga kwarara shi, yi yake ba k'ak'k'autawa kamar zai amayar da kayan cikinsa, yana gama aman sai juwa ta 'yebeshi ya tafi luuuu ya kwanta, sai da ya samu hutu na second biyu sannan ya mik'e da hanzari.
"Gurin wani mugun mutumi kika kawoni Mommy, ki tashi mu tafi, wallahi bazan kuma zuwa gurinsa ba, ya bani abinda zai cuceni, Yaya bai san halin sa bane shiyasa. ”

Momy tsayawa tayi tana kallonshi cike da alajabi, sai jan hannunta yake kamar zai tsinka mata, wai sai ta tashi sun tafi, Malam Jafar yace wa Mommy" Tashi ku tafi, amma kar ki barshi yayi tuk'i, idan kunje ki yayyafa mishi wannan, ya bata ruwan magani, idan kika yayyafa mishi zaiyi wajen awa uku yana bacci, in ya farka zai tashi k'alau insha Allah, sannan kuma sai kin matuk'ar dagewa gurin zuwa yasha rubutun, da alamu rubutunne ba'a so yasha.”

Tom shikenan Malam mun gode Allah ya saka da alkhairi, ta ajiye masa sadaka tai masa sallama suka tafi, har lokacin jan hannunta yake.

Gurin tuk'in motar ma tubrewa yayi shi zai ja, da lallami tana adduoi ta samu ya barta ta jasu suka tafi, don ta lura ba lafiyanshi lau ba, haka kawai yaje ya runtumasu wani waje.

Suna zuwa gidan, tunkan ta daidaita parking d'in motar yake k'ok'arin fita, kafin ta fito ta rufe motar shi har ya fito ya runtuma ciki da gudu, ai a gurin ta wullar da key d'in motar tabi bayanshi da gudun tsiya,

Please Login or Register in order to submit comment