Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cilli da key d'in yana me barin falon, d'aukar key d'in yayi bai mun magana ba ya fice, bin bayansa nayi har lokacin hawaye na zirara bisa kuncina.




Yau ma naci sa'a ban samu kowa a d'akin ba, jikin nasa yayi sauk'i don an cire masa k'arafunan nan yana zaune ya sunkui da kansa, ko da na murd'a k'ofar ma na shiga k'arar hakan bai sa ya d'ago da kansa ba, jingina nayi da k'ofar na d'age nik'af in fuskata, dama zuciya a kusa nan naci gaba da kukana har da shashshek'a, kukan da yaji ne yasa shi d'ago da kansa kuma dama tun tuni yake jin bugun zuciyarshi yana sauyawa, d'an zabura yayi yana me gyara zamansa, mutstsika idonshi yayi ya bud'e a gain ya kuma ganina, saka yatsansa yayi a baki ya ciza don ya tabbatar gaske ne ko mafarki.

Bud'e mini hannuwansa yayi alamun na taho gare shi, da sassarfa na k'arasa gareshi na shige jikinshi ya rungumeni da duka hannuwansa yana me sauke mini numfashi me mutuk'ar d'umi a wuyana, shiru mukayi dukkaninmu na 'yan second.

"Ya Allah kasa ba irin mafarkin da na saba bane a kowani lokaci, Allah ka dauwamar mini da hakan a gaske ba dan halina ba. ”
Kuma shigewa jikinsa nayi sosai a hankula na furta.
"Da gaske ne Hubbina, Hanan kace a cikin jikinka ba a mafarki ba, nima ina fatan Allah ya dauwamar mana da hakan har k'arshen nnumfashi.”

"Amin My Hanah ” Ya fad'a cikin sauke sanyayyar ajiyar zuciya.
"Dan Allah kar ki kuma tafiya ki barni. ” Ya fad'a yana me d'ago da fuskata yana k'are mini kallo, jan hancina yayi.
"Wai ina kika tafi kika barni ne cikin tarin damuwa da kewarki? ”
Zamewa nayi daga jikinsa ina sakin murmushin da na jima banyi irinsa ba nace.
"Kafin nan bara ka fara cin abinci tukun, don na san baka ciba.” Baimun magana ba shima sai murmushin da ya kasa barin fuskar shi, bai ma san yana jin yunwa ba sai yanzun da yaji na fad'i abinci, flas d'in da na gani kan drower na bud'e, Sultan chip ne a ciki, dama kuwa Ya Hamid yana matuk'ar son sa, zubowa nayi a plate na ajiye a gefensa na bude'e d'an k'aramin pridge d'in dake gefen gadonsa na d'auko ruwa na tsiyaya a cup na kai masa bakinsa, don naga leb'ensa ya bushe, in yaci a bin in yana jin k'ishi bazai ji dad'insa ba, ba musu ya ansa yasha da d'an dama.

Tas ya cinye Sultan Chip d'in, kallona yayi yana murmushi yace.
"Ashe dai ina jin yunwar, bansan da haka ba sai da na ganki a gabana My Hanah kece komai nawa.” ya fad'a yana me lumshe ido

Murmushi nayi nima ina me lumshe nawa idon na bud'e su cikin nasa muka k'urawa juna ido na d'an lokaci.



Duk abubuwan da suka faru na gaya masa, har da inda nake zaune a halin yanzu.

"Ina fita daga asibitin nan auranki zanyi sai dai duk abinda zai faru ya faru, bai isa yayi mana a binda Allah bai rubuta a K'ADDARARMU ba.”
Murmushi nayi naci gaba da kallonsa sai naga ya k'ara mini wani annurin kyahu, d'aga mini gira d'aya yayi yace.
"Yane wannan kallon fa, kinga d'an Beautyn yaro ko?”
"Ba wani Beauty Ugly dai, ai kowa yasan nafi ka kyau. ”
"Ba wani nan kya dai fad'i gaskiya kinga Beauty kin mak'ale masa. ” Dariya kawai nayi ina me mik'ewa.
"Zan tafi kar wani yazo ya same ni. ” Rik'o hannuna yana mini sanyayyen kallo.
"Yanzu tafiya zakiy ki barni? ”
"To ya zamuiyi? ”
"Ina ji a jikina idan kika tafi kamar kin tafi kenan baza mu kuma had'uwa ba ”
"Hak'ik'anin gaskiya jikinka bai gaya maka gaskiya ba sam, ni da kai zamui aure za kuma muyi rayuwa me tsaho ni da kai.”
"To Allah yasa My Hanah, amma dai....”
"Amma dai me? kasa a ranka ni taka ce har abadan abadina, ina sonka. ”
"Nima ina sonki, ko babu raina ki dinga yawan tunawa dani.”

"Da ranka insha Allahu my Hubby, a ko da yaushe kullum ina kasancewa cikin tunaninka. ”
Ina kaiwa nan na salub'e hannuna zan fito daga d'akin yace. "Kinga” Jiyowa nayi ina kallonsa yace.
"Na gode, kiyi hak'uri, kiyi hak'uri, kiyi hak'uri⁴.”
Murmushi kawai na sakar masa shima ya sakar mini murmusmushi me tsayawa a rai, hannu kawai na d'aga masa alamun by by shima ya d'aga mini nayi sauri na fice don ban san wani ya had'u dani, amma hak'urin da Ya Hamid yake ta bani ya tsaya mini a k'asan zuciya, shin me hak'urin nasa yake nufi? Da wannan tunanin naje gida amma sam na kasa samun amsa kaina ya kulle gaba d'aya.............


TO SHIN ME HAKAN YAKE NUFI NE?
[12/10, 17:56] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


________________
*TWENTY SIX*
"Sumy ce tace mini idan har ina son Hamid ya soni to sai na yarda munje gurin wani boka ya san aikinsa sosai da sosai, da fari nak'i yarda da shawarar Sumy sai daga baya da naga muddin in ban aminta ba ciwon son Hamid zai zama ajalina, kuma naga ba wani abu bane tunda Amma ma tana zuwa.
Muka shirya muka je gurin boka, ya bamu bayanin tabbas Hamid zai soni so me tsananin gaske, don soyayyar da zai mini ko mahaifansa bai musu shigenta, amma fa kud'in aikinsa shine ya kwanta dani, hankalina yayi mugun tashi da naji wannan k'udirin na boka har na so na bijire amma Sumy ta kuma mun hud'ubar tsiya akan ai za'a kulle bakin Hamid sai abinda nace masa zai dinga yi zai zamo mini tamkar abun gare² na dinga garawa jin haka yasa ni na amince da k'udirin boka ashe yana d'auke da ciwo me karya garkuwar jiki. ”

Tana kawowa nan ta fashe da kuka, cikin kuka Amma tace.
"Amma Sumayya ta cucemu duniya da lahira da ta baki wannan muguwar shawara, tsakaninmu da ita Allah ya isa bamu yafe ba insha Allahu irin ciwonki ne zai zama ajalin ta. ”

"Amma, ni na tabbata hak'k'in da kuka d'auka ne na Hanah ke da Abba yake bibiyar RAYUWARMU dama masu iya magana sun ce ka so naka duniya ta k'ishi, ka k'i naka duniya kuma ta soshi, ga shinan soyayyar da kuka nunamun bata amfane ni da komi ba sai shiga halaka, garin neman gira naje na rasa idanuwa gaba d'aya, muddin kuna son RAYUWARMU ta dai²ta sai mun nemi yafiyar Hannatu, ni dai ko na mutu kuka had'u da ita kuce ta yafe mini kuskuren da nayi mata. ”

”Ki daina wani zancen Hannatu, bayan itace babbar matsalarmu cikin Rayuwa, ni har yanzu banyi da kacen yiwa Hanah abinda na mata ba. ”

"Ai baza ki tab'a ganewa ba Amma, ko sanda zaki d'auki jakarnan babu yanda banyi dake ba kar ki tab'a ga shinan abinda d'aukar jakar ya janyowa RAYUWARMU na tabbata da ba don haka ba da tuni muna cikin farin ciki kin sanadin talauta mu duk da duk rabin dukiyarma ta marainiya ce Abba yake zazuwa a kai. ”


Abba da ya had'a kai da guiwa duniya duk tabi ta masa zafi ya rasa inda zai tsoma ransa yaji dad'i, da zaiga Hannatu a halin yanzu tsaf sai ya kaita lahira. Tsayawa yayi yaji abinda Suby tace yace wa Amma.
"Wata jaka Suby ke magana a kai? ”

Suby maida idonta kan Abba tayi zata bashi amsa Amma tayi saurin toshe mata baki.
"Zafin ciwone yasa ta take ta fad'in magan ganu mara kan gado in kuma ka shirya jin abinda zai sanadiyar bugawar zuciyarka to? ”
Shiru Abba yayi bai cemata komi ba sai wani d'an iskan murmushi da yayi.
' Watakan ni zata mayar sauna,hmmmmm in ta san wani bata san wani ba, wallahi muddun naji ita ta d'au jakar nan to tsaf zan iya aikata lahira.'

"Nifa nace, naji zan tuttukan sun wuce hankali ” Yace mata haka don kawai a wuce gurin.




*
"Sun sanar mini abinda ke tafe dake me kuma kike so ayi? ”
Boka ya tambayi Mama dake tsugune a gabanshi kamar tana gaban wani Shaik.
"So nake Daddy ya kori Haisam daga gidansa tare da wannan shegiyar yarinyar sannan ya saki Ummeta ya aureni ya dawo k'ark'ashina, ni nafi son ma ya kama Haisam da wannan yarinyar suna iskanci yarda zaifi fusata sosai. ”

"Ki fara ajiye kud'in aiki tukunna. ”

Jaka ta bud'e ta ajiye mishi mak'udan kud'i a gabansa, hannu ya d'aga sama sai ga wani magani a leda mik'o mata yayi tasa hannu ta karb'a.
"Kinga wannan shi za'a busa musu a yayin da suka kasance guri d'aya amma kar a sake aga sanda za'a busa don muddin aka gani abin zai dawo kan wanda ya busa zaiyi iskanci da duk wanda ya samu, amma maganar saki babu ita don auransu mutu ka raba ne don duk wanda yace miki zai iya raba auran nan to kud'inki zai ci, sai dai kuma zai aureki bak'in cikin auranki da zaiyi da juya mata bayan da zaiyi shi zai saka ta bar gidan, kije idan wannan yarinyar ta bar gidan ki dawo ki karb'i abinda zaki saka masa a abinci da kansa zai miki maganar aure”.

Yana kaiwa nan ya b'acewa ganinta, ta tashi ta fita a karkace zuciyarta fari k'al.




*
"A duk lokacin da rayukanmu da zuciyoyinmu suka b'aci Yaya yace mini nayi hak'uri komi lokaci ne wata rana sai labari, ban tab'a tunanin lokaci da wannan ranar zasu zo ba sai yau, tabbas hausawa sunyi gaskiya da suka ce me hak'uri yakan dafa dutse har yasha romansa, gashi na gas gata hakan a kaina, na samu miji me matukar sona da k'aunata, me kulawa da ni, ga dangin miji masu k'aunata sun maye mini gurbin dangina da bani da su. Ya Allah ya Ubangiji kar kawo abinda zai shiga tsakanina da jin dad'in da na samu, Allah yarda na samu kwanciyar hankali ka samar dashi cikin Rayuwar Habibatina da Ya Hisham. ”

Takai k'arshen maganar hawaye na zirarowa bisa kuncinta. Sadik' dake gefenta ya zuba mata idanuwa cikin so da k'auna, ya saka hannunsa yana goge mata hawayen.
" Kin yarda komi lokaci ne, kuma duk tsanani akwai lokacin da zaizo sai dai a bada labarinsa don haka ki daina zubda hawayenki akwai lokacin da suma farin ciki zai dauwama a zuk'atansu.” Yakai k'arshen maganar yana danna kiran wayar Haisam, don yasan had'ata da sahibatinta ne kawai zai wanke mikin da ya taso mata.



*
Yana zaune a tsakiyar gado ya saka lap top a gaba yana danne²nsa kiran Sadik' ya shigo wayarsa.
D'auka yayi yai picking yana cigaba da danne dannensa.
Bayan sun gaisa yace.
"Dan Allah da Habibatinmu zaka had'amu.”
"Ok ba matsala in tazo zan kira. ”
Godiya yayi masa ya kashe wayarsa.


Kiran wayar Momy Haisam yayi yace ta turo masa Hanan, to Momy tace a ranta tace suna kuma ya canja mata, kallon gefen da nake tayi tace mini naje Haisam na kirana kar na sake na dad'e, to nace mata na d'auki hijabina na fita, a k'aton falo na tadda Mama a zaune nayi kamar bansan da mutum ba a gurin na huce na nufi sashen Haisam.
A falo na tadda shi, na shiga da sallama, kallo d'aya yayi mini ya d'auke kansa ya amsa sallamar da nayi ciki², a kan kafet na zauna ina sunkui da kaina.

Video call ya kira Sadik' shi kuma yana d'agawa ya mik'awa Rumanah ni kuma a lokacin ya mik'o mini, ai ina d'ago kaina naga Sahibati ban san ya akai wayar tazo hannuna ba, na bararraje na dargaje muka fara tik'ar hira har na manta a gaban wa nake shi kuma sai kallona yake yarda nake ta dariya kumatuna suna ta lotsawa, muna yin sallama na mik'a ma's a wayar har lokacin murmushi yak'i barin fuskata, karb'ar wayar yayi yana me d'auke idonsa daga kaina, na juya zan tafi yace mini kinga, dakatawa nayi da tafiya na tsaya ina jiran abinda zai ce.

"Me kika sani game da Mama?”

Ji nayi gabana ya yanke ya fad'i bakina har yana rawa gurin ce masa.
"Ban san komi game da ita ba. ”
Mik'ewa yayi yana me nufo inda nake, ja da baya na soma yi yana tunkaro inda nake har na had'e da bango.
"Ko ki gaya mini abinda kika sani ko mu kwana dake a cikin d'akin nan tare wallahi.”
A take tsoro ya bayyana k'arara a fuskata, shi kuma aransa yana a duk cikin yanayin da fuskata take yana mini kyau.
"Kin hana Hisham cin abinci, sannan kin b'arar da kunun da Daddy zai sha, duk me tunani ya kamata yasan da wani abu a k'asa, kuma kina sani kika murje mini k'afa dan na biyo ki ko? ”
Yakai k'arshen maganar yana kuma ware mini manyan idanuwansa masu matuk'ar firgita mace, rintse idona nayi hawaye na zirarowa a fuskata don na rasa wace iriyar amsa zan bashi,shi kuma ya tsaya yana kallon yarda hawaye ke sintiri bisa kuncina, a dai² lokacin Hindu ta bud'e k'ofar ta shigo tana ido hud'u da mu ta hura mana wani abu a hannunta
[12/10, 17:56] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


________________
*TWENTY FOUR*
Hak'uri da rashinsa mana, wata zuciyar ta bani amsa, ji nayi wani abu ya fara jijjuyani, na fara gani dishi² a hankula idanuwana suka rufe ruf, ni ba a mace ba kuma ba a raye ba.


Ammi wani gida ta samu ta shiga ta rok'esu arzik'in su d'auketa aiki ko basu biyata kud'i ba indai zasu d'auke mata cinta da shanta ta amince, cikin sa'a kuwa matar ta d'auketa aiki, don dama tana buk'atar me aiki kawo mata me aikin ne ya ga gara.

Abba kuwa ya had'awa gurin aikinsa kud'in nan zai kai musu b'arayi suka tare shi a hanya suka k'wace suka yimasa dukan tsiya, a lokacin sak'on kora daga aiki ya ziyarci wayarsa kuma sunce muddin ya shigo hannunsu sai sunyi shari'ah da shi.


A daren da na tafi na bar Ya Hamid a daren ciwonshi ya motsa sosai wanda likitoci suka kasa control in matsalar har sai da zuciyarsa ta buga a lokaci guda, Umma zubewa tayi ta sume, Papa kuwa Allah ne kawai yasa mishi k'arfin zuciya, ni kuwa dama haka na kwana gani nan ne ni ba raye ba, ba mace ba sai k'irjina ke ta faman bugu kamar ana dakan sakwara.

"Haisam Hamid ya mutu”
Hisham yake gayawa Haisam, kallonsa Haisam yayi yace. "Waye Hamid?”
"Hamid d'in Hanah mana”
"Oh, Allah yayi masa rahama, amma naji mutuwarsa ko da bansan shiba sai a bakinka. ”

"Nima ba saninshi nayi ba sai labarinsa da nake ji a bakin Hanah, idan har ina son ganin murmushinta sai na ambato mata sunanshi, wallahi ina mutuk'ar tausayinta, ban san wani hali zata shiga ba idan taji, ni na rasa ma ta yaya zanyi na gaya mata.”
Yakai k'arshen maganar kamar zai kece da kuka, dubanshi Haisam yayi kawai sai yaji yana tausaya musu domin da shi da Hisham da Hanah duk ababan tausayi ne, gara ma Hamid tasa ta k'are ya rabu da K'ADDARAR RAYUWA.
"Ka d'auketa kawai kuje k'ofar gidan da safe don na san a lokacin za'a masa sallah zata fuskanta da kanta, kar ka sake taji daga bakinka domin baza ta tab'a mantawa ba.”
Shiru yayi zuciyarshi tana aminta da shawarar Haisam, shi kuwa Haisam bai damu da ya amsa masa ba ya d'auki ta gadon ya fara shan kayarsa.


Kwata² banji dad'in baccin yauba, nayi shine kawai ga shinan, ni kaina jin jikina nake kamar ba nawa ba, wanka ma da brush da k'yar nayi na zira bak'ar doguwar riga na d'aura mayafinta a ka nayi kwanciyata, Mommy ce ta dubeni.
"Ki taso ki fito kici abinci, kullum ina miki fad'a akan saka damuwa a rai kin k'iji, wallahi Hannatu da ina saka damuwa a raina da na tabbata miki babu labarina a halin yanzu, Allah shi ya Kaddaro mana irin wannan rayuwar ba dan komi ba sai dan ya jarabci imaninmu don haka ina me kuma shawartarki da ki fawwalawa Allah dukkanin lamuranki a sannu zakiga rayuwarki ta fara warwarewa. ”

"Ina k'ok'arin ganin na cire damuwa a raina kullum, yauma yanayin da nake ji a jikina ne yasha bam² da na kullum, ina ji kamar zanyi rashin babban bigire a cikin rayuwata. ”

Kallona Momy tayi cikin tausayawa, domin Hisham ya gaya mata yanzun nan, bayan naci abinci ta turani akan nayi masa rakiya ta aikesa.
"Ki yawaita fad'ar Innalillahi..... taso muje maza kici abinci ki raka Hisham na aikesa ko kyaji dad'in jikinki. ”

Bansan me yasa ba tana fad'ar haka naji gabana yayi wani irin bugu ya fad'i, innalillahi... na shiga memetawa na mik'e na fita falon.
Saka abincin nayi a gaba ina kallo na kasa ko da loma d'aya, zuba mini ido Momy tayi cike da tausayawa tace.
"Ki daure kici ko da kad'an ne. ”
Tuttusa shi nayi da k'yar na iya cin guda uku sai ruwan tea d'in da na kurkurb'a.”
Ina k'ok'arin tashi Haisam ya shigo kallon farantin gabana yayi da cup yaga ban wani ci sosai ba, zama yayi kan kujera Momy ta tashi ta fita tana.
"Ki tashi kije yana jiranki. ” Jiki a sanyaye na mik'e zan fita sai ji nayi yace.
"Koma ki zauna.”
Zama na koma nayi ina sunkui da kaina.
"Cikin mintina biyar na baki naga babu komi cikin plate innan da cup.”
Da sauri na d'ago da kaina na kalleshi, cikin sa'a kuwa idanuwanmu suka gauraya, sauri nayi na janye idona daga kansa don sam fuskar nan tasa babu alamun wasa a cikinta, tea d'in na d'auka na kafa a baki na rintse idona, ban cire shi sai da na shanye shi tas na dire kofin ina matsar hawaye, janyo plate in doya da k'wan nayi na d'auki d'aya ina ci ina yatsina fuska hawaye na neman zirara bisa kuncina.
"Kin san Allah ko ki saki jiki kici ko kuma yanzu nazo na miki d'ura. ”
Jin hakanne yasa ni na fara tutturata ba don ina jin dad'inta ba har sai da na kuma cin yanka shida, kuma yankan babu laifi manyane gashi taji k'wai sosai, kallonshi nayi idona cike da hawaye taf nace.
"Na k'oshi ”
Kallona yayi na 'yan mintina yana daga kishin gid'e jikin kujera yace.
"Share hawayen to, ki sha ruwa kije yana jiranki .”
"In na sha ruwa amai zanyi. ”
Bai mun magana ba sai d'auke idonshi da yayi daga kaina yana me lumshe su, ni kuma ganin haka ya sakani na tashi na fita.

Tunda naga ya d'auki hanyar unguwarmu bugun da k'irjina yake ya kuma tsananta, kuma fuskarshi a tamke take sam babu annuri cikinta, ruwan jikina ne ya k'afe k'af yayin da na ga mun shiga layinmu mutane cike da layin, ji nayi zuciyata ta tsinke, ruwan hawaye har ya gama cikan ido yana k'ok'arin zubowa, kallonsa nayi bayan yayi parking a dai² k'ofar gidan su Ya Hamid, d'auke kanshi yayi yak'i kallona mai da kaina nayi k'ofar gidan a dai² lokacin ake fito da gawar za'a kaita babban fili a sallaceta, ban san ya akai na bud'e motar na fito ba kawai nidai na ganni gaban gawar bayan sun ajiyeta na bud'eta anan naci karo da fuskar Ya Hamid, zuciyata ce ta tsaya cak da aiki daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba.


Anwa Ya Hamid sallah an kaishi gidansa na gaskiya wanda ya samu nasarar rakiyar d'unbun mutane, har aka kaishi Umma bata san inda kanta yake ba, taci kuka kamar ranta zai fita gani take Allah sai ya kama su da hak'k'in Ya Hamid.
Kiran Abba Papa yayi ya gaya mishi mutuwar Ya Hamid kuma yace.
"Ka saka soyayya ta tab'a mini zuciyar yarona, to kaima in Allah ya yarda soyayyar d'ana ce zata kashe 'yarka. ” Daga haka ya kashe wayarsa, Suby tana jin mutuwar Hamid ta fad'i a gurin sumammiya dama tunda suka dawo ba wata isasshiyar lafiya gareta ba.


Ya Hisham ne ya kira Rumanah ya gaya mata halin da ake ciki, ba shiri Sadik' ya kawota domin ta kasance kusa dani.
Ko da na farka da ita na fara cin karo hannunta rik'e da nawa tana tsiyayar hawaye, ganinta tana kuka shi ya tuna mini da abinda ya sameni nan na saki kuka me k'arfi nace.
"Habibati ki taimakeni ki gaya mini mafarki nake ba'a gaske ba in ba haka ba nima zuciyata zata buga na mutu na huta da K'ADDARAR RAYUWA.”
"Kiyi hak'uri Sahibati, hak'ik'a babu wata damuwa me d'orewa ki yarda komai lokacine wata rana sai labari, kowa yasan mutuwa tana da ciwo a hankali kuma kowa zai tafi, gado ce me matuk'ar wahala babu yarda zamui da ita sai hak'uri domin ba'a tab'a sabo da ita addu'a kawai Hamid yake buk'ata a gareki tanan zai kuma tabbatar da kin cika babbar masoyiyarsa. ”

"Ya Hamid ne fa ya mutu Rumanah, mutumin da ya bani soyayya da k'aunarsa a lokacin da na rasata ga kowa hatta ga mahaifiyata sannan kuma kike cewa nayi hak'uri, lallai yau na san bakya k'auna....” Ban iya k'arasawa ba numfashina ya kuma d'aukewa gaba d'aya, rungumeni tayi tana kuka sosai.
"Wallahi ina sonki Habibati ina jinki kamar 'yar uwata ta jini, idan ban baki hakuri ba me kike so nace miki? Hak'uri shine ya zama dole ga wanda yayi rashi idan baiyi hak'urinba to me ya isa yayi? Kema na tabbata ba a hayyacinki kike ba kike wannan maganar. ” Shiru tayi yayin da ta lura bana numfashi da gudu ta tafi kiran Ya Hisham, bata same shiba sai Ya Haisam yana barci bata san ya akai ta tashe shi ba kawai sai gani tayi yana kallonta da jajayen ido.

Cikin kuka tace.
"Sorry Ya Haisam, Hanah ce numfashinta ya d'auke.. ” Bai bari ta k'arasa ba ya fice daga shi sai singileti da three quarter, don dama shine ya samu nasarar tayar da zuciyata taci gaba da aiki.

Yana zuwa d'aukata kawai yayi ya kaini d'akinsa ya kwantar dani bisa gado, nan ya shiga bani taimakon gaggawa, daga Rumanah har Momy suna daga falo d'insa suna jiran tsammani, ya d'au tsawon mintuna yana kaina sannan ya fito ya kulleni a d'akin yace musu ina buk'atar hutu daga yanzu zuwa dare.


Ban samu kaina ba sai bayan sallar isha'i, sanda na farka na jiyo hirar Haisam da Hisham a falo, shashshek'ar kukana ce ta tabbatar musu da na farka Hisham ya kalli Haisam yace.
"Paition inka ta tashi fa. ”
Shiru yayi masa bai bashi amsa ba, yasan me shirun nasa yake nufi don haka ya tashi ya shigo inda nake.

"Hanah. ” D'agowa nayi da rinannun idanuwana na dubeshi. "Dukkanin rai sai ta d'and'ani d'acin mutuwa, mutuwa tana da silkin d'aci amma meye maganin wannan d'acin? Shine hak'uri, duk yadda zaki ji zafin mutuwarshi ba kikai ga mahaifansa ba sune na farkon wayanda mutuwar zata fara dukansu kuma suma hak'uri zasu yi, don haka ki cire damuwa a ranki kiyi masa addu'a ita kad'ai yafi buk'ata yanzu a gareki, ki tashi kije kiyi wanka yanzu, nasan abinci yanzu bazai

Please Login or Register in order to submit comment