Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'auke gaba d'aya.

Auncle Zaid rikicewa yayi, ya rasa abinyi, ya zauna dab'as kafin ya fashe da matsanancin kuka.

Nikuma ina gefe ina ta kuka, yahu da majina da hawaye duk sun had'e kamar nasan me yake faruwa......



Al'k'uran mutuwar Abba ta tab'a min Zuciya, sai zuciyata ta warke zanci gaba, wayyo Abii d'inmuuu.


Mrs Aminu na gaisheki kyauta, ina matuk'ar jin dad'in addu'arki, Allah ya bar k'auna.
[12/10, 17:53] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


__________________
*FIFTEEN*
Allahu Akhbar duniya ba matabbata ba, wanda ya d'auketa matabbaciya to gashi ga tanan, irin su Abba kenan, burinsa ya cika Muhammad ya tafi ya bar masa duniyar, gashinan sai yaje ya cita da tsinke mu gani.

Ammi sai da aka dangana ta da Asibiti, domin numfashinta yak'i daidaituwa,a hannun Nurse Auncle Zaid ya barota ya daho domin a sitirta Abii akaishi makwancinsa.


Mutuwar Abii ta zaga ko wani k'etare na anguwar, Auncle Zaid ya kikkira 'yan uwa da abokan arzik'i ya gaya musu, harda 'yan uwansu na Damaturu.

Ko da mutuwar tazo kunnen Sulaiman, ya shiga tashin hankali na misali, waya ya kira Abba, ringing d'aya ya d'aga.

"Hello, D'ahiru Muhammad ya rasu, kuma wallahi kaine..... ”

Ruf kike ji kamar an rufe masa baki, ya kasa k'arasa abinda zaice, wani d'an iskan murmushi Abba yayi.

"Hello Sulaiman ina jinka, me kace. ”

Jiki a sanyaye yace masa.
"Dama cemaka zanyi kaji mutuwar Muhammad kuwa. ?”
Salati Abba yayi har da dafe k'irji, yana mai maita, Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
"Yanzu Muhammad d'inne ya rasu, wayyo mutuwa kin mana yankan k'auna, kin d'auke mana abokinmu.” Sai ya fara kukan k'arya har da shashshek'a.
"Bari to yanzunnan zamu taho Allah Ubangiji ya jik'anshi. ”
"Amin"Sulaiman yace ya ajiye wayar.
Abba kuwa daga shi har Amma babu wanda ya d'auki komi nashi a cewarsu daula zasu shiga komi a banza zasu sameshi, Subai'ah ma kala d'aya aka d'aukar mata, wai ai Ammi na da k'aramar yarinya in yaso a dinga saka mata nata.





_____
Alhamadlillah Abii ya samu dubban mutane da sukayi masa jana'iza, don filin anguwarsu kad'an yayi musu har sai da aka fita filin masallaci sannan akayi, an kaishi gidanshi na gaskiya aka baroshi daga shi sai halinshi, ayyukan alkhairin da ya aikata su kad'aine zasu kub'utar dashi.


A hannun Umman su Hamid nake, sai ihu nake da kururuwa ta rasa yarda zatai dani, sai bayan su Auncle Zaid sun dawo daga jana'iza sannan yazo ya ansheni yana lallashina, mak'ale masa nayi sai waje yafita dani, gurin shimfid'ar da ake karb'ar gaisuwa, a gefensa ya kwantar dani kaina a kan cinyarsa, duk wanda yazo gaisuwa sai nayi matuk'ar bashi tausayi, ga Auncle Zaid har lokacin hawaye d'iga yake a idonsa.


Ammi sai a washe gari aka sallameta, har lokacin ba ta um ba ta um² ga ko ruwa tak'i ta sakawa cikinta, Umma da Amma ne suke lallashinta har ta d'an samu ta saka wani abin a cikinta.
da wannan damar Amma ta samu take saka mata magani a abinci, turaren ma tana yimata sai tacewa mutane na dangana ne domin a samu ta warware, cikin ikon Allah kafin bakwai Ammi ta saki jikinta sosai, ni kuwa d'awai niyata dama ta koma kan Amma, gaba d'aya take had'emu tai mana wanka, a cikin kayana zata sakawa Subai'ah, ita kuwa dama kayan Ammi ne suka zamo kayan sakawarta.


Abba yacewa Auncle Zaid zai bar Amma ta zauna tare da Ammi, kafin ya samu inda zai ajiyeta, Auncle Zaid yace.
"Ai kuwa naji dad'i, dama tunanin zamanmu daga ni sai ita nake, saboda akwai munafukai, inmu zuciyarmu babu komi akwai masu saka ido. ”


Nan kusa da su Sulaiman Abba ya tanfatsa gida mai kyau, kwata² baiji kud'in da ya fitar ba, saboda yana hango daular da zai shiga nan gaba.

Bayan ya kammala ginin yacewa Auncle Zaid zai d'auke Amma saboda ya kammala gininsa, shikuma yace yayi masa hak'uri zuwa sanda Ammi zata gama takaba, in yaso sai a d'aura musu auren su tare gaba d'aya, saboda shi kad'aine a yanzu yafi dacewa da auran Umaima, wani sanyin dad'ine ya dabaibaye Abba saboda samun hanya da yayi cikin sauk'i, dama tuntuni yake son tunkararshi da maganar to amma kuma sai ya bari ta kammala takabarta tukunna.


Bayan Ammi ta kammala takabarta, ta yaye HANAH, aka d'aura auranta da Abba, sosai Abba ya shiga kula da Ammi da nuna mata k'auna, bayan auran Ammi da 'yan satittika aka raba gadon su, Auncle Zaid ya dank'awa Ammi nata da hannunta, amma bai bata na Hannatu ba, yana bata Abba ta dank'awa, yana karb'a ya kalleta.

"Ina na Hannatun?”
"Ai nata yana hannunsa, tunda shine zai riketa, tariyar tasa wani satine me zuwa, amaryar tasa na tarewa zan dank'ata gareshi, domin cika alk'awari. ”
"Akan wani dalili zaki d'auki 'yarki ki bawa wani?,nine nan ni nafi cancanta da na rik'e Hannatu, ba don komai yake son rik'eta ba saboda dukiyrta ne ni nasan da haka. ”

"Nima dai tunanin da nake tayi kenan, a gaskiya bana son rabuwa da 'yata ko kad'an, duk abinda zai rabani da ita bana sonshi ko misk'ala zarratin, nima gaskiya nafi tunanin saboda dukiyar Hannatu yake son rik'eta, don haka na fasa bashi ita, nice nan zan rik'e yarinyata, kuma abinda Muhammad ya bayar yace sai ranar auranta za'a bayar to shima sai nasan yarda nayi yazo hannuna. ”
"Meye abinda Muhammad d'in ya bayar?” Nan Ammi ta shiga labarta masa, wani shu'umin murmushi ya saki yana ciza leb'e, ya shiga zancen zuci.
Abinda na dad'e ina son sani kenan, sai gashi zan sameshi ta hanya me sauk'i, amfanin auranki kenan Umaimah bayan haka babu abinda zanyi da sauran da Muhammad ya bari.
Cizan leb'e ya kuma yi,kana ya shiga zizziga Ammi akan taje ta anso gadon 'yarta.


Ko da Ammi tajewa da Auncle Zaid da maganar gadon Hannatu, sai cewa yayi bazai bata ba, bud'ar bakinta sai cewa tayi.
"Dole ka bani gadon 'yata, inma don haka kake son na baka Hannatu to wallahi kayi kad'an, don ni bazan iya rabuwa da 'yata ba. ”
"Kar muyi haka dake Umaimah, kada ki manta girman alk'awari, indai don gadon Suhanah ne zan baki, amma kada ki hanani ita, na riga na k'wallafawa raina ita, inai mata soyayyar da bakya zato, zan iya jure rashin komai, amma banda hanani Hannatu, kada ki manta alk'awarin da kikaiwa Muhammad. ”

"Oho ni ina ruwana da wani alk'awari, nidai na riga da na canja, a yanzu dai babu ni babu bada 'yata, ka bani kayana na huce. ”

K'wallar da ta tarar mishi a ido ya d'auke ya durk'usa guiwoyinshi a k'asa.
"Haba Umaimah, ke da kanki fa kikayiwa Muhammad alk'awarin zaki bani Hannatu, ki tuna fa ke zaki iya haihuwar wasu, nikuma bani da tabbacin hakan, kiyiwa Allah da Manzonsa ki bani Hannatu, duk wani buri nawa da soyayyata na d'orashi a kanta ki taimakeni ki taimaki halin da nake ciki.”

"Naga ni nad'au alk'awarin dai ko? To yanzu kuma nace na fasa, don banga wanda ya isa yasa ni na bada Hannatu ba, tunda banga wanda yazo ya tayani zama da cikinta ba, don ko shi Muhammad d'in da yayi maka alk'awari sanda nayi nak'udarta bazuwa yayi ya tayani ba, don haka ka sanyawa ranka salama babu ni babu baka 'yata Hannatu. ”

Bai kuma magana ba, sai k'wallar idonshi da ya kuma d'aukewa da hannunsa, ya d'aukko duk wata kadara da take ta Hannatu ya bata, yace.
"Kud'in zakiji su a Account d'inki. ”

"Ai ba su kenan ba. ”
Wani kallo ya jefeta dashi ya koma kan kujera ya zauna rik'e da saitin zuciyarsa da take masa matuk'ar zafi.......


Kyan alk'awari cikawa, wallahi kaina ne yake tamun ciwo, to saboda nayi alk'awari shiyasa na daure nayi muku wannan.
[12/10, 17:54] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


__________________
*SIXTEEN*
Ammi ta takurawa Auncle Zaid akan sai ya bata abinda Abii ya bada a bawa Hanah ranar auranta, kuma ba kowane yake zigota ba face Abba, shikuma Auncle Zaid yace, baiga wanda ya isa ya sashi yaci amanar da aka basa ba, da yaga suna neman takura masa, har suna son suci galabarshi, don zuwa suke suyi masa tijara daga ita har Abba, harhad'a kayansa yayi kawai yabar k'asar gaba d'aya, don aurenma ya fasa yi, dama saboda HANAH zaiyi auren, yanzu kwa da aka fasa bashi ita baiga amfanin auranba.
Ya k'udirewa ranshi baza su kuma jin labarinshi ba, bare gurin da yake zaune, har sai sanda yaji labarin auren Hannatu, ko kuma ya daidaici lokacin da ta isa aure, a lokacin zaisa a dinga jiyo masa labarinta, don yasan baza ta huce candy ba, don sun saka ido sosai akan abinda mahaifinta ya bata, kuma duk saka idonsu baza su tab'a sanin wannan sirrin ba.

Abba da Amma babu inda basu shiga sun fita ba don Auncle Zaid ya kawo musu da kanshi amma Allah bai basu sa'a ba ko kad'an, ganin hakane yasa suka hak'ura har zuwa sanda HANAH zata yi candy sai ya samo miji ya aura mata, idan mijin yasan wannan sirrin suma tamkar sun sanine, muk'ullin na zuwa hannunsu shikuma Abba zai saki Ammi, itama HANAH yasa mijin nata ya saketa, yasan hakan zai matuk'ar tab'a zuciyar Ammi yarda baya zato.



________
Ina girma kyahuna yana dad'a fitowa ainun, Ammi tana matuk'ar kulawa dani, tana sona tana tarairaya ta, gashi mak'otansu suna aikowa a d'aukeni, in biki zasu ko wata unguwa duk dani suke zuwa.
Hamid ma yawancin kullum ina hurinsa mun matuk'ar shak'uwa dashi, har takai dukkanin abokanansa sun sanni, haka zakiga ana kahomin ledojin biscuit da caculate kala².
Allah yayi mini baiwa iri ² ga farin jinin masoya ta koina, duk inda aka shiga dani to sai mutanen gurin sun soni, kuma ba kyahuna ne ya jaho hakan ba kawai dai farin jinine daga Allah, domin Subai'ah ta fini kyahu sosai, kawai dai yaluwar fata zan nuna mata, sai kuma adon da Ammi kan yimin ko da yaushe.

Ko kad'an Allah bai had'a jinin Yaya Hamid da Subai'ah ba, gashi ita kuma tana son yarda yake mun shi da abokanansa itama su dinga mata, yana shigowa gidanmu zata tafi gurinsa da gudu, haka dai zai d'auketa amma baya sakar mata kamar yarda yake mun, gashi daga Abba har Amma Allah ya d'iga musu son Hamid,don har sunyi magana da Sulaiman (Papa) da Umma akan zasu had'a auran Subai'ah da Hamid.
Abinda Hamid kemin duk sun d'auki hakan cikin yarinta, idan ya girma ya mallaki hankalinsa me zaiyi da ni sai dai Suba'ah, Amman kuma Amma tana bak'in cikin yarda kowa yake nuna soyayyarsa gareni, don hatta Abba baya tab'a banbanta mu ni da Suba'ah, ita kuma Amma hakan sam baya mata dad'i, yayin da Ammi ita kuma hakan yake matuk'ar faranta mata rai.
Da muka isa sakawa a makaranta, privet mai matuk'ar tsada da k'ok'ari Abba ya sakamu, komai iri d'aya yayi mana.


A haka rayuwa take ta tafiya, komai na cikinta yana juyawa shekara ta zamo tamkar ka rufe ido ka bud'e domin gashi har mun gama junior candy mak'erin budurci ya fara k'eramu duk da dai bamu fi 15 years ba, Yaya Hamid a lokacin shikuma yana Adamawa yana cigaba da karatunsa akan Bussines, amma yakan lek'owa wani lokaci zuwa lokaci, game da shak'uwarmu kuwa babu abinda ya ragu, sai ma wanda ya dad'u, don duk sanda akace miki yazo to ko da yaushe muna manne da juna, babu duba wai yanzu na soma girma.
Amma ta sake haihuwa, ta haifi 'yan biyu mace da namiji ake cemusu Janah da Jabir.



Bayan munyi junior candy sai Abba ya sauya mana wata makarantar muka soma daga sss 1, Allah Ubangiji ya bani baiwar k'wak'walwa sosai, wanda Subai'ah take bak'in ciki da haka, ajinmu d'aya amma kowa k'awayensa da ban, k'awayenta dukkansu 'yan anguwan mune, Sumayya wacce suke kira da Sumy, sai Surayya (Sury) sai Safiyya (Sufy) sai ita kanta Subai'an wacce ta koma Suby, duk cikin su hud'un nan babu me k'aunata ko kad'an saboda k'ok'arina ya kuma jahomun farin jini mai matuk'ar yawa, k'awata d'aya ce Rumanah, Rumanah tana matuk'ar k'aunata ainun, duk inda zaki ganmu muna tare a ko da yaushe.


Duk dawowar da Yaya Hamid zaiyi sai yayomun tsaraba wacce ta ninka ta kowa, hakan yana matuk'ar sosa ran su Amma, har sai da takai akaiwa Hamid maganar karfa ya sake soyayya ta shiga tsakanina dashi domin Subai'ah ce matarsa, shikuma yace musu shi a gaskiya ni zuciyarsa take matuk'ar so, don bai tab'a jin sha'awar kasancewa da Suby ba ko kad'an, aikwa iyayanshi suka tada mishi k'wanji, aka d'auki matakin rabani da shi.

Abinda ban sani ba ashe nima na rayu da soyayyar yaya Hamid, ban farga da hakan ba sai da Yaya Hamid ya koma makaranta kuma aka hanashi dawowa, ashe Suby ma tana matuk'ar k'aunar Yaya Hamid saboda iyayanta sun ginata akan hakan, kuka taje ta sakawa Ammi akan nafita k'ok'ari, na fita farin jini, kowa ni yake so ba ita ba alhalin ta fini kyau nesa ba kusa ba, sannan kuma ita da gidan mahaifinta a dunga musu abu kai d'aya da ita.

(Hhhh Suby kenan, baki san dukiyar Hanah bace mahaifinki yake zazuwa da ita, har yake hank'orar wata?)

Rarrashinta Amma tayi akan ta share hawayenta, don sai ta maida dariyar fuskarmu kuka, ba Ammi tana farin ciki ta haifi yarinya me farin jini ba, to sai ta maida wannan farin jinin ya koma bak'in jini, sai ta saka kowa ya tsaneni, hatta shi kanshi Hamid d'in sai yaji baya sona.


Amma ta samu Abba akan maganar dole sai an raba soyayyata da Ammi da dukkanin wata shak'uwa tsakaninmu sannan burinsa zai cika, don haka sai yace ta shirya taje yabar komai hannunta.......
[12/10, 17:54] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


__________________
*SEVINETEEN*
Amma ce sanadin d'auke duk wani farin ciki da walwala na kan fuskokinmu, ta maida murmushin kan fuskokinmu k'unci da bak'in ciki, kuka ya zamo shine abokina a ko da yaushe, har ya zamto sai da na manta yaya ake jin farin ciki da nishad'i domin na zamo abokiyar gabar su.
Sai da ta shiga ta fita ta sanya k'iyayyata a zuk'atan mutane, bak'in k'irin suke ganin fuskata kamar hadarin kaji, ba ta barni haka ba sai da ta saka aka turo mini bak'in aljanin b'arawo, duk inda yaga kayan mutane sai ya d'auka, sai dai kawai naga abin a jikina, hakan sai ya kuma jahomun tsana mai tsanani a zuciyar kowa, saboda duk inda na shiga sai nayi sata har mutane suka lank'aya mini Suhanah B'arauniya, ko daga bakin titin anguwarmu aka ambaci wannan sunan nawa sai an kawo mutum gidanmu.
Ammi ma kanta ta ta tsani nazo gurin da take, kyara da tsangwama shine tsakanina da ita, duk abinda za'a yimin a gidan bata magana sai ido, an riga da an d'aure mata baki.
wani zuwa da Ya Hamid yayi ya taddani cikin wannan halin yayi matuk'ar bak'in ciki da hakan sosai, kuma ya d'ora zargin hakan akan Amma, me makon ya gujeni sai ya kuma d'aukko dukkanin wata kulawa ya aza bisa kaina, kullum cikin nasiha yakemun, ya tsani ya ganni ina zubda hawaye ko kad'an hakan da yakemun sai ya kuma ninka soyayyar da nake masa a da, amma ban tab'a fito da ita fili ba saboda gudun matsala, saboda a lokacin na shiga tarko a cikin gidan kowa ya tsaneni babu gurin wanda nake jin dad'i, daga gurin Ya Hamid sai gurin Rumanah, su kad'ai ne suka damu dani suka kuma damu da damuwata.

Abinda yafi damuna kullum mukaje makaranta sai na d'auki abin Subai'ah ita kuma bata fasa tara mini mutane ba, haka zasu had'u ita da k'awayenta su dinga zageni tas suna dungure mini kai, Rumanah ce me k'arfin halin tare mini, ko kuma suje su had'ani da Ittale ya farfasa mini jiki na dawo gida Abba da Amma su d'ora, a haka rayuwata ta kasance gida babu dad'i makarantu babu dad'i har gwara boko nakan samubiyuanah ta kwantar mini da hankali.
Haka na addabi duk makarantu da nake ciki da sata, har ya zamto ana guduna, kuma duk satar da zanyi sai an kamani haka nake cin duka da farfasa baki, abinda yasa makarantun basu koreni ba, Allah yayimin baiwar k'wak'walwa sosai, duk divert d'in da za'ayi ko musabak'a dani ake fita, hakanne ya zamo garkuwa a gareni.


A cikin wannan rayuwar har muka shiga SSS 3, mun kuma zama 'yan mata, kyahunmu ya kuma bayyana, a lokacin Ya Hamid shikuma ya tafi Sudan yin course na shekara d'aya, har yama kusa cinye shekara d'aya, zuwa na musamman yayi don ya ganni, kewata tayi mugun addabar ruhinsa, tsaraba yayomun ta ban mamaki wacce bai tab'a yimin irinta ba kuma daga gidansu har gidanmu babu wanda ya san ya bani kuma a lokacin ne ya gaya mini yana sona, domin gudun a barshi ya huce, kar ya koma kuma Allah ya kaho rabon wani, hakanne yasa ya mik'omin duk wata soyayya tasa, nima kuma banyi k'asa a guiwar mik'a masa tawa soyayyar ba, a lokacin ya zira mini zoben azurfa mai kyau me harafin sunanmu.
Soyayya muke sha sosai ni da Yaya Hamid, amma a b'oye babu wanda ya ankare damu Subai'ah ce ta fara d'ago jirginmu aikwa anyi babban rikici sosai, iyayanshi suka cimin mutumci yarda bakwa zato harda cewa d'ansu bazai auri B'arauniya ba wacce bata da asalin Uwa bare na Uba, Abba da Amma kuwa karyani ne kawai basuyi ba amma sun jijjimin ciwuka sukamun kashedi da babbar murya, hakanne yasa na k'udirewa raina ko da soyayyar Ya Hamid zata kasheni na hak'ura da shi insha Allah, hakanne yasa duk inda na ganshi nake neman kauce masa, amma shi har zuwa lokacin nan bai hak'ura dani ba, har sai da yayi sanadiyar da iyayanshi suka korashi Sudan d'in, kuma suka yanke shawarar muna yin candy za'a d'aura auranshi da Subai'a ta bishi Sudan d'in, in yaso in ya kammala sai su juyo tare.

Cigaba tayi da basu labarin har zuwa yau, ita kuma Rumanah ta basu labarin yarda sukayi da Ammi, ta rok'i Momy akan ta rik'e HANAH a gurinta kafin lokacin da Ammi zata nemeta, saboda itama babu halin ta tafi da ita gida itama saura kwanaki biyar tabar gidan.
Momy sosai ta tausayawa HANAH, tace wa Rumana babu damuwa zata rik'eta insha Allah ta dinga d'ebe mata kewa, sosai labarin HANAH ya tab'a Momy, lallai mak'iyinka babu abinda ba zai iya aikatawa gareka ba, ashe basu kad'ai suka ga k'addarar rayuwa ba irin yanda mak'iyansu suka maida su abin kwatance sai gashi itama wannan yarinya haka aka maidata, share k'wallar idonta, a hankali ta shiga tashin Haisam domin jin ana kiran sallar la'asar, shikwa yayi likimo, ashe ba bacci yake ba duk ya gama jin labarin da HANAH ta bayar, ya tausaya mata sosai domin an cuci rayuwarta an mata tambarin da bazai gogu ba, banda baisan shiga shirgin da ba nasa ba da sai ya k'watar mata 'yancinta.

A hankula ya mik'e daga cinyar Momy cikin yanayin barci ya nufi d'akinshi domin ya d'auro auwala, suma mik'ewa sukayi suka shiga d'aki don sauke farali.




Nagode matuk'a ga wa'yanda suka mik'o addu'arsu gareni, da masu kirana da masu min message duk godiya nake gareku, Alhamdlilah naji sauk'i sosai, kwana biyu biki muka sha shiyasa.
[12/10, 17:54] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

*Maman Mash hud sak'onki ya iso gareni, nayi matuk'ar jin dad'in addu'arki ina fatan Allah ya amsa tare dake kuma, nima ina matuk'ar sonki har tsakiyar zuciyata.*
*Na gaisheku masoyana*
__________________
*EIGHTEEN*
A 'yan kwanakin nan wasu mugayen mafarkai yake mara dad'in ji, gaba d'aya zuciyarsa tayo Nigeria, hakanne yasa ya biyo jirgin Azahar yayo k'asarsa Nigeria.
Bayan saukarsa daga jirgi taxi ya biyo ta saukeshi gida, gidan su HANAH idonsa ya fara sauka yayi ido biyu da ka'ton kwad'o lokaci d'aya k'irjinsa ya fara bada wani bugu, dafe k'irjinsa yayi ya fara takawa a hankula kamar wanda aka zarewa laka ya shiga cikin gidansu.
Da Ammi ya fara cin karo a tsakar gida, suna had'a ido dashi taji hawaye ya biyo kuncinta wanda bata shirya zubarsa ba, ganin hawaye a kuncin Ammi ya kuma jefashi cikin matsanancin tashina
hankali, dafa bango yayi saboda jin juwa na neman kayar dashi, lasar lab'b'anshi yayi ya bud'e baki zaiyi magana Umma ta fito daga d'aki.
"Me ya dawo dakai Hamid, Watakan kai baka jin magana duk abinda ake gaya maka ta gefen kunnenka yake hucewa tsabar ka raina mutane ko?”
Bai tanka mata ba ya maida idonshi kan Ammi da ta sunkui da kai.
Tana matuk'ar tausayawa Hamid, tasan irin tsananin soyayyar da yakewa Hanah, yanzu idan yaji HANAH bata tare dasu wani irin hali zai shiga?

"Ammi me ya faru naga hawaye akan fuskarki?”
"Abba ne ya tafi Abuja yau kusan fin sati babu waya bare labarinshi.”
Umma tayi saurin bashi amsa, b'oyayyar ajiyar zuciya ya saki kana yace.
"Toh kuma ba abi bayanshi ba? ”
"Tun safe Papa yabi bayanshi, to kaji shima har yanzu shiru bai dawo ba.” Umma ta kuma bashi amsa.
"Toh Allah Ubangiji dai yasa lafiya. ”
Amin suka amsa da ita dukkaninsu.

Subai'ah na ciki tana sallah, Allah² take ta idar ta fito, aikwa tana yin sallama tayo tsakar gida da gudu, daga bakin k'ofar d'akin ta tsaya tana k'are mishi kallo, Amma kuwa tana band'aki tana sakin kashi duk abinda yake faruwa tana jiyo su.
Idonshi ya kuma maidawa kan Ammi, domin zuciyarshi ta gaza hak'ura mahad'inta kawai take buk'atar gani a kusa da ita, don haka ya yakice kunya ya tambayeta.
"Ammi ina HANAH? ” Domin yasan a gurinta kad'ai zai samu cikakkiyar amsar da zata kwantar mishi da hankali, Ammi har ta fara motsa baki zatayi magana, Umma ta daka mishi wata iriyar tsawa.
"Ka b'ace mini da gani daga gurinnan Hamid tun kafin na sab'a maka, tsabar mara hankali ne kai ana gaya maka ba'aga iyayanka har biyu ba kai ta wata banza b'arauniya kake yi, wacce duk ita ta janyo wannan bala'in. ”
Baki ya bud'e zai magana, Ammi tayi mishi alamu da ido, ya tafi kawai, a hankali ya fara d'aga k'afarsa da yake jin tayi masa matuk'ar nauyi ya shiga d'aki.
Tsaki Umma taja, ta shiga sababi.
"Haka kawai yaro duk yabi ya susuce akan wata kod'ad'd'iyar yarinya, karatu ma yak'i tsayawa yayi ya gama kullum shi kenan a tafe, anbi kawai an susuta mini yaro, ni banga abin so a gurin b'arauniya ba ita ba kyau ba, ba kyan hali ba kawai dai kod'ad'd'iyar fatarta ce ke d'ibarshi, amma ga santaleliyar budurwa tana binka kai

Please Login or Register in order to submit comment