Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata yarinya da uniform a jikinta? yace.
"K'warai naga fitowarta, to sai naga ana mata magana a cikin wata mota sai taje ta shiga suka tafi. ”
Sulalewa tayi a gurin ta sume, tsorata mutumin yayi, yaje ya gayawa me gadin gidan, sanin halin da gidan yake ciki sai bai je ya gaya musu ba, ruwa ya d'auko suka zuba mata, a firgice ta farko, tayi cikin gida da gudu gurin Abbu ta nufa ta zube a gabanshi ta saki wani irin kuke me ban tausayi.
"Abbu sun tafi da Khadijah............”







A matuk'ar gajiye nake, saboda Rabin Jiki na d'an sammuku.
[12/10, 18:20] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


_________________
*THIRTY THREE*
"Me ya samu Khadijan, su waye suka tafi da ita?” Abbu ya tambayeta cikin rud'ewa.
"Nima ban san su waye ba Abbu, ance dai ta shiga cikin wata mota sun tafi.”
Salati da sallallami Abbu ya shiga yi, yace.
"Garin ya hakan ta faru? Nine fa da kaina na d'aukota daga makarantar kuma har bakin k'ofar ku na kaita, sai da naga shigarta sannan na wuce.”
"Launch box inta tace mini ta manto a mota ta dawo d'auka.”
"To kuma ina shigowa Fadi tace mini na bata aron motata zatayi aike da ita, bara na tambayeta naji wa ta aika? ”
Abu kamar wasa fa an nemi Khadija an rasa, don motar tana nan ba ma tayi aiken da ita ba, fad'ar irin tashin hankalin da su Baffi, Abbu, Innai suka shiga b'ata lokacine, cigiya babu inda ba suje ba, hatta da gidan Radio, kullum cikin addu'a suke suna kai sadaka makarantu a kan Allah ya bayyanata amma shiru kake ji har yau Allah bai bayyana ta ba, ciwo sosai Innai ta kwanta wanda har sai da yakaisu ga asibiti, anan suka gane tana d'auke da ciki na tsawon wata hud'u, sunyi matuk'ar farin ciki da ni'imar da Allah ya saukar musu, suna kuma fatan Allah yasa Khadija ta bayyana garesu ba jima ko mu dad'e.
Watan cikinta tara cif, ta haifo tagwayenta duk mata masu tsananin kyawu, tsabar farin ciki sai da sukayi kuka, ansha murna ansha shagali wanda ba'a tab'a yinsa ba a tarihin gidan Fulani, su Fadi da Inno bak'in ciki kamar ya karsu, don Asiya (Umma) tun daga haihuwar Fiddausi ba ta kuma haihuwa ba.
Hassana suna kiranta da Umaimah, Usaina kuma Ummeetah, gatan da suke samu gurin mahaifansu da kakansu ba'a magana, a haka Allah yayi ta rayasu har kawo girmansu.
Yayin da suka zama 'yan mata ainihin kyahunsu ya kuma bayyana, sun zama cikakkun 'yan mata gwanin ban sha'awa, sun kammala secondary insu, ana shirye²n tafiyarsu Adamawa a can zasu cigaba da karatun su, kasancewar Kakannin Innai acan suke, asalin fulanin Adamawa ne, a lokacin har anyi bikin Nusaiba ta haihu ma.
Haka kawai Ummeetah ta tsiro da yawo, idan ta fice tun safe sai tsakiyar dare zata dawo, hakan ya mutuk'ar d'agawa su Innai hankali sosai,duka babu irin wanda ba ta sha, amma duk a banza, ana gama dukan zata kuma ficewa, ganin abin ya ta'azzara sai suka had'a da rok'on Ubangiji.
Akwai randa Innai ta kulle k'ofa tace baza ta fita ba, tace mata wallahi muddin bata bud'e mata k'ofa ba, to wallahi zata kashe kanta, jin haka yasa Innai ta bud'e mata k'ofar tana kuka wiwi² Umaimah na taya ta.
Wannan rayuwa da Ummeeta ta samu kanta a ciki, itace tayi sanadiyar fasa tafiyarsu Adamawa, Abbu kanshi baiji dad'in wannan lamari ba, sai dai babu yarda mutum zaiyi da K'ADDARARSA sai hak'uri, amma hawaye kam ya zubar da su sau ba adadi sanadiyar Ummeetah, shi gani yake ma yafi su Baffi shiga tashin hankali don soyayyar da yakewa tagwayen nan daga Allah take, ko soyayyar da yayiwa Khadija sai dai ta biyo bayan tasu.
Ana haka ciki ya b'illo jikin Ummetah, tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, Abbu fad'uwa yayi, shurawar da bai kuma yiba sai ranar tashin alk'iyama, ita kuma Ummeetah ta had'a kayanta ta gudu, wannan shi ake kira tashin hankali cikin tashin hankali.
Fad'ar halin da Baffi, Innai da Umaimah suka shiga b'ata lokacine, idanuwansu gaba d'aya sun rine sun koma ja tsabar kuka, sunyi wani kumburi na ban mamaki.
Bayan lafawar al'amura sai Umaimah ma ta tsiri yawo irin na Ummetah,ita daga k'arshe ma had'a kayanta tayi tace baza ta zauna a gidan ba, saboda takura ga saka ido, rik'eta Innai tayi tana kuka tace.
"Ki taimakeni Umaimah, a yanzu ke kad'aice sanyin idaniyata, ke kad'ai nake gani naji dad'i zuciyata tayi sanyi ta samu nutsuwa, idan kika tafi kika barni ban san wani hali zan shiga ba, na rok'eki da Allah kar ki tafi ki barni Umaimah.”
Fusge hannunta tayi tace.
"Idan ina zaunai cikin gidan nan ji nake yi kamar na kashe kaina, na kashe ku ke da Baffi, na rasa me yasa hakan. ” Share k'wallar idonta tayi ta saka kai ta bar gidan, tsabar shiga tashin hankali Innai har kusa sab'o tayi ta gigice ta zauce ta fita hayyacinta, ta kira mahaifiyarta Hajiya ta gaya mata,bata kira Baffi ba, don ba ta san wani irin hali zai shiga ba, a sume Hajiya ta zo ta tadda ita ta yayyafa mata ruwa bata farfad'o ba, asibiti kawai ta nufa da ita,bayan ta kira Baffi ta gaya masa, shima Allah ne kawai yasa bai fad'i ya sume ba, sai da ta kwana uku sannan take gane wanda yake kanta, domin jininta ne ya hau sosai wanda ya haddasa mata ciwon kai me azaba.
Duk wannan Al'amura da suka faru su Fadi babu wanda suka jajantawa, hatta Asiya da take 'yar u war Innai tari ba tayi mata ba, haka zalika Abbakar ma (Kawuu) baiyiwa Imam ba.

Duniya sabuwa ta dawowa su Fadi, ji suke kamar su zuba ruwa a k'asa su sha, yayin da duniya take shud'awa zamani yana tsawo, Fadi a yanzu jikokinta 5, Maimoon na da 'ya'ya uku duk mata, Aysha ma biyu duk mata, dukansu kuma sun aurar dasu suma sun hahhaihu, tattab'a kunnen Fadi kenan Hafiz shine babban tattab'a kunnenta, babban jikan Maimoon kenan (Ummee) kuma shi kad'aine namiji hakanne yasa take matuk'ar k'aunarsa, don gidan ya daho da zama gaba d'aya.
Cikin tattab'a kunnanta Allah ya bata fitinannu, Iklima da Ihsan, kamar 'yan biyu haka suka taso, babu abinda basa sha na game da maye, dabar karuwai kuwa guda suka tara ta, sun gagaresu gaba d'aya sun rasa yarda zasui da su, daga k'arshe gaban Fadi suka zo suka zube su.



Nusaiba da Fiddausi suma sun haifi 'ya'ya uku² Nusaiba na da Hakeem, Hidaya Halisah, Fiddausi kuma na da, Asiya takwara tayiwa Asiya (Umma)sai Haya, sai autanta Haidar, haihuwar Asiya da suke kira da Baby, da kuma haihuwar Haya kwainika tayi shiyasa suka taso kansu d'aya, kuma dukkaninsu suna gurin Kakarsu Umma, ma'ana dukkaninsu suna zaune ne cikin gidan Fulani, an tura su Innai gefe babu me hurd'a da su, abu yayiwa Innai zafi ya had'u ya mata yawa, hakanne yasa ta manta da mutane a cikin gidan suke rayuwarsu daga ita sai mijinta, suka fauwalawa Allah lamuransu domin shi ya K'ADDARO musu irin wannan RAYUWAR, ga Hajiya a gefe tana tausarsu, domin itama Innai kad'ai ta haifa a duniya, kuma danginta gaba d'aya suna Adamawa, Baffi ya maidata tamkar mahaifiyarshi itama kuma tana jinsa a ranta kamar ita ta haifeshi.
Batun Khadija, Umaimah, Ummeetah har yau babu wanda suka kuma jin labarinsa.

*CIGABAN LABARI*........
[12/10, 18:20] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

_________________
*THIRTY FOUR*
Rik'ota Haisam yayi jikinta, yana jin k'aunarta har cikin mashin zuciyarsa, Baffi ne ya samo ruwa ya mik'a masa ya shafa mata a fuska, nannauyar ajiyar zuciya ta ajiye, ta bud'e idanuwanta da suka mata matuk'ar nauyi, cikin dashash shiyar murya tace.
"Allah Ubangiji yasa ba mafarkin da na saba yi bane a ko da yaushe.”
Hawaye ne ya zubo bisa idon Baffi yace.
"Ba mafarkinmu bane wannan gaske ne, muma yau Allah ya nuna mna jikokinmu tunkan mu tafi.”
Lumshe idonta tayi tace.
"To Alhmdlillh, Yaro kamani mu bar bak'in gurin nan. ”
Kama ta Haisam yayi, mun kusa fita da falon Fadi ta fara wani irin ihu.
"Sai da boka yace mana muddin jininsu ya bayyana cikin gidan nan, zamu had'u da wani bal'ai.mu mukayi asirin da Aysha ta mutu, sannan muka raba soyayyar Abbakar da Imam,
Da ni da Inno muka je mchargiasirin da Khalil ya mutu, sannan muka saka aka sace Khadija aka kaita k'ofar gidan marayu, mukaiwa su Umaimah asirin da zasui iskance kuma su bar gida kar su kuma waiwayen gida, muka kulle zuciyarsu yarda bazasu tab'a tuna gidansu ba, kawai saboda Imam yak'i karb'ar k'udirinmu na auran Zainab, shine muka salwantar da duka 'ya'yansa, yarda gidan Fulani zai zamo k'ark'ashinmu gaba d'aya. ”
Sai tai wani irin ihu ta kunce hannunta da aka d'aure, taci gaba da cisgar naman jikinta tana ci, daga Baffi har Innai kuka suke, yayin da nima hawayen tausayi ya wanken fuskata ina me jin muguwar tsanar matar ina wadaran da halinta, kad'an ma ta gani sakamakon duniya kenan ina ga na lahira, k'arasa fita mukai daga falon baki d'aya.
Duk baya nan nan da Fadi tayi, a gaban 'ya'yanta da jikokinta da tattab'a kunnenta tayi, Hafiz ne kawai baya nan, kuka dukkaninsu suke yi, basu tab'a tunanin zata iya aikata irin wannan mugun abu, fita daga falon Kawu yayi shima ya biyo bayanmu, yana shigowa gurin Baffi yayi ya rungume d'an uwansa, dukkaninsu sai suka saki kuka kamar wasu yara.
"Ka yafe mini Imam, hak'ik'a Fadi ta cuceni ta cuci rayuwata, tsakaninmu da ita sai a gaban Ubangiji, domin shi kad'aine zai mana sakayyar abinda tayi mana. ”
"Ko kad'an ban rik'eka a raina ba Abbakar, Baffu har ya rasu yana gaya mini kar na k'ullaceka ba yin kanka bane, akwai ranar da zaka dawo kan turbar gaskiya, lallai wasu matan sharrin su yayi musu yawa dole ne aji tsoransu, ta kashe mana mahaifiya, ta rabamu da kai, sannan ta salwantar mini da duka yarana uku, me mukai mata a duniyar nan dan Allah? ” Yakai k'arshen maganar yana fashewa da kuka, zuciyarsa tana masa ciwo.
" Yanzu cikin duniyar nan ba sai ka yiwa mutum abu ba yake k'ullatarka, wani ma giftawarka ba ya son gani ko kad'an, bak'in ciki ne kawai ta sakawa ranta da k'aunar abin duniya, ta manta komi na cikin duniyar tafiya zatayi ta barshi, yarda tazo haka zata koma sakayyarmu kawai da wannan matar sai a gaban Ubangiji.”

Kiran Hajiya Innai tayi ta gaya mata abinda ya faru, wani irin farin ciki ne ya ziyarceta, tace.
"Kinga Inno ma anan ta haukace sai bige ² take tana ta fad'ar mugun abinda suka aikata, Malam ya saketa saki uku ya koreta daga gidansa, yanzu ba'a san inda tayi ba, ga 'ya'yanta sun shiga nemanta, amma ina jin ta nan gidan naku ba ta san me ya samu mahaifiyar tata ba. ”
"Ina zata sani suna kan Fadi, ai wallahi kad'an suka gani, cuta dai sun riga sunyi mana sakayya kuma sai a gaban Ubangiji."
"To dai Allah ya kyauta, Allah kuma ya bayyana mana su Umaimah idan har suna raye, gani nan yanzu zanzo gidan. ”
"Amin, to sai kinzo.”

Sai da Hafiz ya dawo sannan yaje ya bud'e Fadi, kowa yak'i zuwa ya bud'e duk sunyi jigum² masu kuka nayi, Ummee kuwa ta tafi gida bayan 'yan uwanta sun kirata sun gaya mata abinda ya samu Inno mahaifiyarsu, Kawu kuwa yana can gurin d'an uwansa suna murnar bayyanar jikokinsu.
Hafiz na bud'e k'ofar ya tarar Fadi ta riga ta cika, duk ta yayyage naman jikinta ta cinye, durk'ushewa yayi a gurin ya fashe da kuka.
"Me yasa² Fadi kika d'auki irin wannan rayuwar bayan ba me b'illewa ba ce, duk wani abinda Allah bai baka ba, wallahi babu wani wanda ya isa ya baka, , banso kika zo a banza kika tafi a banza ba Fadi, Allah ba ya tab'a yafe laifin wani akan wani, sannan kuma baya tab'a yafe laifin shirka idan har ka mutu ka nayi, ya Allah ba don halinta ba ka dube mu kayi Rahama ga wannan baiwa taka. ” Kukane yaci k'arfinsa sosai.

" K'alu bale gareku masu yawon bin malamai, yawon bin malami ba wata riba bace ko fa'ida, idan har baki kaiwa Allah kukanki ba, to kwa ba kya kaiwa wani k'aton gardi ba, bayan shima Allah ne yake bashi s'aa, to ke dan me yasa baza ki tashi ki nemi sa'ar a wajen Ubangiji ba, har sai kinkai kanki da dukiyarki ga halaka, wallahi duk abinda Allah bai baki ba, babu wani k'aton banza da ya isa ya baki, in zakiji tsoron Allah ki daina zuwa indai har kina zuwa d'in to, don wallahi yanzu tun daga duniya ake fara girbar abinda aka shuka, fatanmu dai Allah ka tsare mana imaninmu jinmu ganinmu zuciyoyinmu ga fad'awa ga sab'onka, Allahuma Amin.)



Hafiz ne kawai, sai wasu abokanansa biyu sukaiwa Fadi sallah, don duk wanda yaji mugun abinda ta aikata sai yace baza shi ba, Baffi da Kawu kuwa babu wanda ya fito ko da sukaji an fasa kukan mutuwarta, bare mu da muke wutawarmu sai nan² ake damu cikin kulawa.
Gaisuwarta ma babu wanda ya shigo yayi sai iya su isu, Inno ma an ganota, amma mota tayi daga² da ita, itama irin ta Fadi ce ta same ta, babu wanda yayi mata salla sai wanda ta shafa, Kawu ma k'in zuwa yayi duk da kasancewarta surukar sa, don da cewa ma yayi sakin Ummee in zaiyi, Baffi ne ya hana shi don ganin meye amfanin sakin, bayan sun ruga sun tara jikoki?


______
KANO
Bayan barin su Haisam gidan, Daddy sosai ya rufe Momy da fad'a ba ji ba gani, yace kuma aure zaiyi, ba kowa zai aura ba face Mama, ko kad'an hakan bai tayar mata da hankali ba, illa kayanta kawai da ta shiga had'awa don zuciyarta da ruhinta gaba d'aya sunyo garin Gombe, ko da ta gaya masa gobe zata tafi Gombe bai hanata ba, sai ma kud'in mota da ya bata, sunyi waya da Haisam ya gaya mata sun isa Gidan Fulani, amma be gaya mata abinda ya faru ba, sai dai yace mata sun had'u da abokinsa da sukai karatu tare wato Hafiz, ashe d'an uwansane, sannan yace mata ya gaya musu har Hanah ma 'yarta ce ko da ta zo ta amsa akan hakane, saboda yana gudun kar Hanah ta samu tsangwama a cikin gidan, shiyasa yace k'anwarsa ce kafin bayyanar mahaifiyarta itama.



**
Baffa ya manta ma yana da wasu 'ya'ya, rayuwarsu suke tayi me dad'i, Aunty tana jan linzaminta, ta raba shi da kowa nasa, daga ita sai 'yan uwanta, sai Nihal suke zazuwa da dukiyar Baffa, nace Hmmmm su Aunty abi a sannu.



**
Hisham sunyi waya da Rumanah, ya sanar mata an gano inda Ammi take da zama a Abuja, a gobe zai taho ya sauka a Abujan zai taho tare da ita.
Murna sosai Rumanah tayi ta dinga shiwa yayanta Albarka, itama tana musu addu'ar Allah ya bayyana musu ahalin mahaifiyarsu.

Haisam ya kira, bayan gama wayarsu da Rumanah, don sun kwana biyu basui waya ba, don sosai ya shiga busy, kansa ya d'auki chargi, anan yaji dukkanin abinda ya faru, yayi farin cikin bayyanar ahalin Mommy, amma baiji dad'in korar da Daddy yayi musu ba, bai gaya masa anga Ammi ba, amma yace masa nan da jibi yana nan tahowa.




ABUJA
Hankalin Ammi sosai ya koma ga mahaifarta, ba ta da wani buri yanzu da ya huce ta tafi gida, don haka batai k'asa a guiwar tunkarar matar gidan ba akan zata tafi gida, sam ba ta ji dad'in tafiyar da Ammi tace zata yiba, amma kuma ba ta hanata ba, ta bata dubu goma, ta saka driver yakaita gurin da zata shiga mota, sukai sallama ya taho.
A nan gurin jejikan Kaduna motar su Ammi tayi hatsari.




_______
Ko da Hisham ya sauka Abuja, direct gidan ya nufa yasa aka masa magana da matar gidan, anan ya sanar mata abinda ke tafe da shi, ta gaya masa cewar ta riga ta tafi, rasa abinda yake masa dad'i yayi, ya kira Rumanah ya gaya mata, rasa abinda zata yi tayi kawai ta saki kuka...............
[12/10, 18:20] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

_______________
*THIRTY FIVE*
Ranar da Fadi ta cika kwana uku a k'asa da yamma Umma ta tara duka ahalin gidan fulani, a matsayinta na wacce ta zamo babba yanzu a cikin gidan, saboda da jimawa mijinta ya rasu ta dawo gidan da zama.
Bayan kowa ya hallara ta fara da bawa su Baffi hak'uri akan abinda mahaifiyarsu tayi musu, ta saka kowa sai da ya basu hak'uri akan irin rayuwar da akayi a da, sannan ta d'ora da.
"Kar ku dubi abinda mahaifiyarmu tayi ku yanke zumunci da mu, idan har kuka yi haka, Abbu kansa da yake cikin k'asa bazai tab'a jin dad'i ba, ku dubi girman Allah ku manta komai da ya faru, ku yafena ku yafewa mahaifiyarmu, ku barta da zafi abu guda d'aya na shirkar da ta Aikata."
Gefe Innai tayi da kanta tace.
"Manta abinda ya faru ai bazai tab'a yuyuwa ba,sai dai kice kar mu dubi hakan, da ace kwa zamu dubi hakan da baki ganmu zaune a nan ba, banda zuciyar musulunci da ni da duk wani wanda ya had'a jini da Fadi har a badan duniya wallahi, mu kad'ai muka san irin ciwon abubuwan da muka d'iba a cikin gidan nan, mun kurb'a da yawa wallahi, Allah ne kawai zai mana sakayya ”
"Na san kun kurb'a da yawa Innai amma ki duba zuciyar musuluncin da kika ce ki yafe mata, Allah Ubangiji ma da kansa yana son me yafiya, ta sanadiyar yafiyarma sai kiga wasu al'amuran suna warwarewa.”
"To Allah ya yafe mana baki d'aya ya rabamu da sharrin zuciya.”
Ga baki d'aya falon suka amsa da "Amin” dan dama ita ake ji, su Baffi tuni suka ce sun yafe.
A ranta kwa cewa tayi.
'Ai dama sai angama cutar mutum sannan za azo ana bashi hak'uri, nikwa ba zan gaji da fad'in sakayya sai a gurin Ubangi ba.

Haisam ne ya tashi ya fita, Momy ce ta masa waya akan gata tazo bakin get in gidan shine ya tashi ya fita, tunda ta baro gida take kuka har ta iso gidan fulani, rayuwar da sukai a cikin gidan ita da 'yar uwarta, da abubuwan da suka faru suka dawo mata.
'Allah sarki Umaimah, ko 'ya'yanta nawa, na san zatai mutuk'ar farin ciki da dawowata.'
Hawaye ne ya kuma biyo kuncinta, me gadi sai kallonta yake, Haisam na fitowa ya ganta tana kuka, rik'ota yayi yana bata baki suka shiga cikin gidan.
Mak'alk'ale Innai Mommy tayi kawa wace yarinya, ta saki kuka me ban tausayi.
"Innai ina Umaimata?”
Kukan itama Innai ta fashe da shi musamman da taji tambayar da Mommy ta mata.
"Bayan tafiyarki itama ta tafi ta barmu."
Barin jikin Innai tayi, ta koma jikin Baffi ta saki kuka me ban tausayi.
Allah yasa yarda hankalinta yayo gida yasa na 'yar uwarta ma yayo gida.”
"Ya kikai da cikin da kika bar gidan nan da shi?”
Innai ta jefo mata wannan tambayar wacce ta dad'e tana cinta, amma ba ta san wa zata tambaya ba, ita ba abin ta tambayi Haisam ba, shima ba sani yayi ba, don ta san halin Ummetah da barin abu aciki, kuma tana tsoran ta tambayeshi taje kuma tambayar ta dangan ceshi.



____________
Allah ya amshi ran Suby, bayan ta jigatu da ciwuka kala ² kuma babu kud'in magani bare na Asibiti, a wani kango ma suke kwana, abinci ma sai Jana da Jabir sunje sunyo bara suke samu su yafa wani abu a cikinsu.
Amma taji mutuwar Suby, duk da dai wata wahalarce Allah ya raba ta da ita, tun daga sannan itama ta fara fita bara, da ita suke ci su sha, tunda ina ita ina komawa bariki? Ga 'ya'ya har biyu gabanta ina kuma taga kuin da zata gyara jikinta?.

Anyi nasarar cafke Abba, yayin da suka mik'a shi court, daga k'arshe aka jefashi prison, ko ya biya mutane kud'insu, ko kuma ya k'arashe rayuwarsa cikin gidan yari.

Umman Hamid sun dangana da rashin Hamid, amma suna fatan Allah ya had'asu da Hannatu ko don su nemi yafiyarta.



________
Ammi kuwa cikin ciyayi ta gangara, hakanne yasa ko da aka kawo musu d'auki ba'a ganta ba, sai wani matafiyine da ya shiga cikin ciyayin yin fitsari ya ganta, a rud'e ya kira abokinsa da suke tafe tare ya kama masa ita don ganin tana motsi, suka nufa cikin garin kaduna da ita, suka kaita wani privert Hospital.




KO YA MOMY TAYI DA CIKIN DA TABAR GIDA DA SHI, KO KUMA CIKIN YA DANGANCI HAISAM KAMAR YARDA INNAI TAKE HASASHE?

ME YA FARU DA AMMI, SHIN ZATAJI SAUK'I TA KOMA MAHAIFARTA?
DAMA MAMA BA KISHIYAR MOMY BACE, TO MEYE DANGANTAKARSU?


Duka amsoshin suna page Thirty six, ku biyo alk'alamin BEBE'ART ta warware muku tambayoyin amma ku taho tare da ruwan comment.
[12/10, 18:20] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

_________________
*THIRTY SIX*
"Bayan barina gida kano na nufa, dan ji nayi gaba d'aya garin yayi mini zafi, don ko kad'an bana son shak'ar iskar garin, ji nakeyi kamar mutuwa zanyi.
Bayan isata cikin garin kano anan na nemi dabar karuwai naci gaba da shek'e ayata, sosai bariki take yayina , ake gurzawa dani a kuma dama dani,ko ta kan cikin jikina ban biba, don har ga Allah na manta da shi, tunda bai bani matsala, kuma yabi jikina ya kwanta in ba sani kai ba baza kace ina d'auke da ciki ba.
Kwatsam Abbakar ya shigo cikin rayuwata, munsha had'uwa da shi a gurare da dama, amma bai tab'a yimin magana ba, sai dai ya kamu da soyayyata, amma ya rasa ya akai ya kamu da soyayyar karuwa?
Da Faisal mukai zamu had'u a Santana Hotel bayan me keke nape ya saukeni zan tsallaka titin Allah ya kawo tsautsayin da mota ta kwasheni nayi sama na dawo k'asa, ba kowa ne ya kad'eni ba face Abbakar, d'aukata yayi kawai yayi Asibiti dani.
Naji ciwo sosai a bayana sannan cikin jikina ma ya zube har sai da aka mun wankin ciki, Abbakar ne yake kula dani ya samo kuma wacce take kwana muke kwana tare.

Abbakar su biyune mahaifansu suka haifa, daga shi sai wansa Ibrahim, a gurin yayar mahaifiyarsu suka taso cikin kulawa, ta jima ba ta haihu ba, yarinyarta guda d'aya Lamra ko Abbakar ya girmeta, cikin kwanciyar hankali suke rayuwarsu, daga Ibrahim har Abbakar Bussiness suka karanta, Ibrahim kasuwancinsa a k'asar waje yake yinsa, hakanne yasa rayuwarsa ta koma can gaba d'aya acan yayi aure yake zaune da matarsa har takai ya mallaki campanys da dama, shiyasa da wuya ka ganshi a Nigeria.

Har Ba'ba Abbakar ya kawo ta dubani, a kan hatsari mukai iyayena duka sun mutu, shine ya taimakeni ya kawoni asibiti, kuma bincike ya nuna

Please Login or Register in order to submit comment