Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kauce masa ba, ko da Aunty Hannatu ta lura da su, fad'a tayi musu sosai tace.
"Wannan ai cin amana ne, ya yarda da kai, ya amince da kai ya baka amana, sannan kaci masa amana, bazai yihu ba wallahi.”

Hakanne yasa Muhammad ya k'auracewa Umaimah, ita kuma Umaimah hakan bai mata dad'i ba sam, domin wata iriyar soyayya ta afka mai zafi² ashe da ba soyayya take ba, kawai don ta k'agu ta bar gidansu ne shiyasa ta amincewa D'ahiru, Muhammad shine ya dace da zama mijinta, shi ta dad'e tana mafarki a duniyar auranta, wani irin tsagwaran so take masa mai tafiya da shauk'i zalla.


*****

Wata ranar talatane, talatar da ba tayi musu dad'i ba, talatar da suka ji dama ba'a yota a cikin jerin talata ta duniya ba, talatar da tazo musu da sabon yanayi cikin rayuwarsu.
Sun wayi gari a wannan rana babu Aunty Hannatu, daga yin sallar asuba ta koma, shikenan aka zare ran, Allahu Akhbar, Allah mai iko kenan.

Hankulan jama'a da dama sun tashi, bare kuma mai gidanta Zaidu, da Muhammad, mutuwar ta kad'asu, ta girgizasu ta kad'a musu zuciya da ruhi, ta dake su duka na musamman.


Sunyi kuka da idaniyansu da zuciyarsu, har sai da suka daina jin wani d'and'ano a cikin duniyar gaba d'aya, saboda an yi musu wani babban gib'i a cikin rayuwarsu.

Rashin Hannatu ya zame musu babban rashi, domin Hannatu garkuwa ce a garesu, ta zame musu bango majingina, domin tamkar uwa take garesu, amma Alhamdlillah Allah yasa musu dangana da juriya sosai, Umaima tasha kukan rashin Hannatu ita da zaman nasu ma ba wani me nisa bane.


****
Bayan share makoki , gida ya zame musu tsit, ya zamo Umaimah ce ta zamo tamkar matar gidan, don itace take musu girki da komi² da zasu buk'ata, a haka har aka ci 'yan watanni.

Abinda yasa magulmata basu yo musu ca ba, saboda duk an d'auka Umaimah k'anwar Zaidu, amma duk da haka ba'a rasa masu fad'ar zamansu bai dace ba, ita kad'ai mace a tsakiyarsu, ko babu komi akwai shaid'an, maganganu suna ta yawaita har suka fara damun Zaidu, kuma dama ya lura da Umaima da Muhammad wani salo da suka fito da shi kamar ma soyayya suke, kullum sai kusan k'arfe d'aya kowa yake tafiya makoncinsa, suna falo suna hira, ganin haka ne yasa Zaidu ya nemi shawararsu akan su amince ya d'aura musu aure, in yaso idan D'ahiru ya daho sai ya fahimtar dashi.

Dukkaninsu soyayya ta rufe musu ido, babu wanda yayi tunani kawai suka amince da shawarar Zaidu, nan da nan aka fara shirin biki.


Sanda labari yajewa Sulaiman, baiji dad'i ba kwata² gashi tun tafiyar D'ahiru ba'a samun layinshi kuma shi bai kira ba, bare ya sanar masa, takanas yazo yayiwa Muhammad cin mutumci, kamar bai sanshi ba, yana ta neman ya fuskantar dashi amma Sulaiman sam yak'i fuskanta, nan yayi fata² kuma yace yanzu suka d'aura da shi, tunda har ya shigo da cin amana tsakaninsu, kuma ya jirayi dawo war D'ahiru, domin dawo warsa baza tazo da kyau ba.


Hankali kwance aka sha bikin Umaimah da Muhammad, suna zaune cikin kwanciyar hankali, soyayya suke yi ta mutunta juna, Umaima ta bashi labarin gidansu itama, sosai ya tausaya mata, hakan ya kuma janyo soyayyarta gareshi, sosai yake tattalinta, yana karb'o mata rubutu tana sha, saboda matsalar gidansu itama.

Watan su tara da aure cif Umaima ta santalo 'yarta kyakkyawa, a take Muhammad yayi mata hud'uba da Hannatu.

Ansha bidirin suna sosai da sosai, Zaidu yayi farin cikin sunan da aka saka mini, hakanne yasa ya d'auko duk wata soyayya ya aza bisa kaina, shine ainihin wanda ya fara kirana da SUHANAH, ko yace mini HANAH.

Ina wayo kyahuna yana fitowa, tsabar farina har wani yellow² nake, ga dimples da suka k'ara mini matuk'ar kyau, eye lashers d'ina irin me gazar² d'in nanne, ina da sumar kai wadatacciya, Allah yayi mini farin jinin masoya birni da k'auye.

Auncle Zaid yana matuk'ar nuna mini gata, gatan da ban tab'a ganin anaiwa wani ba, ya shagwab'a ni sosai, saitin gwala gwalan da yake siyomin Ammi har gurin rasa ajiya take, komai ya samu ni, yana nuna mini soyayya mara misali, hakanne yasa Abii yace duk sanda yayi aure zai mallaka mini shi gaba d'aya, hakanne yasa Auncle Zaid ya fara shirin yin aure, don da bashi ma da niyar yi.







_______________

D'ahiru ko da yaje Lagos, cigaba yayi da neman mata don dama sana'ar shi ce, Ammi ma dan Allah ya kareta ne, kuma ta nuna mishi ba ta sha'awar hakan ya bari suyi aure.

Ganin neman matanshi ya had'u da Hadiza (Amma) ta zamo masa dadiron sa, ana haka har ta samu ciki, ko da suka lura tana da ciki, hankalinsu yayi mugu mugun tashi, nan suka shiga neman zub da cikin amma ciki yak'i zubuwa.

Subai'ah ta rantse sai ta shak'i iskar duniya hhhhhh.

Ganin sunyi² ciki yak'i zubuwa, kawai sai suka yanke shawarar d'aura aure, amma tuni ya sanar mata da labarin Umaimah, yace kuma yana komawa zai aureta, tsabar son da take yimishi nan da nan ta amince da zancen Umaimah.


Amma irin gogaggun 'yan barikin nanne ta san yadda take tafi da Abba, nan da nan suka samu waliyai aka d'amrah musu aure, watansu takwas da aure ta haifi 'yarta mace, aka saka mata Subai'ah.

Shekarar Subai'ah d'aya, Abba ya had'o kayansa yayo gida, amma bai taho da su ba, yace mata zai dawo ya d'ebesu idan komai yayi masa dai².

Gidan Sulaiman ya fara dira, don yana son su tattauna wata magana, ko bari ya huta Sulaiman baiyiba ya zayyana mishi abinda ya faru bayan baya nan.

Hankalin Abba yayi k'ololuwa gurin tashi, a fusace ya nufi gidan Muhammad, Sulaiman yana tsai dashi amma ko ta kansa bai biba.



*****
Muna falo, ni ina ta wasana da kayan wasa, ina gwaranci, don a lokacin ban fi shekara d'aya ba, amma ina tafiya, ga wayo kamar 'yar shekara biyar.

Abii da Ammi suna ta wasan 'yar birin² fuskar Abii ce a kulle Ammi tana b'uya , ganin haka ne yasa ni mik'ewa na kamo hannun Abii na zaga ta bayan Ammi, na kaishi gurinta ina dariya, rungumota Abii yayi, yana dariya yana cewa.
"Na kama ki”

Dariyar itama ta saka, nima ganin suna dariya yasa ni na dinga washe wawulon bakina, k'arar bud'e k'ofa ce ta saka su tsayawa da dariyar da suke.

Ganin mutum tsaye fuska babu annuri, ga idanuwansa jajur ya zubo mini su, hakanne ya sani b'uya a bayan Ammi.

Ammi kuwa fad'uwar gaba ce ta ziyarce ta, gaba d'aya jinin jikinta ya daskare, cire k'ullin idonsa Abii yayi don yaga me ke faruwa, nan sukayi ido hud'u da Abba.........
[12/10, 14:48] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

~Ummu Isma'il, Ummi moi mada, MAMAN MASHKHUR, nd Sis Feedy, na baku wanga page kyauta kuyi yadda kuke so dashi, saboda yadda kuke son Abba Hhhhhhhhhhhhh~


__________________
*THERTEEN*

Wani irin shock ne ya kama Abii, ruwan jikinsa ya tsaya cak.

Da jajayen ido Abba yake kallonsa, hawaye na zirara bisa kuncinsa.

"Kaci amanata Muhammad, kafi kowa sanin yarda na k'wallafa rai akan Umaimah, amma ka take kaci amanar abokantaka.
Ku sani dukkaninku babu wanda zan bari wallahi, sai na d'and'ana muku bak'in cikin da kuka d'and'ana mini, daga kaina kun daina cin amana.

Kinci amanar k'auna Umaima, kin yaudare ni, kin azabtar da zuciyata, ban tunanin zaki yimin haka ba, amma ku jirayi abinda zai biyo baya, domin bazai muku kyau ba. ” Daga haka yasa kai ya fice.

Bin bayanshi Abii yayi yana k'walla mishi kira.

D'ahiru ka tsaya ka fiskanceni, wallahi ba da cin amana na auri Umaima ba. ”

"Babu wata fuskanta da zan maka, sai dai ku sani, yarda kuka tab'an zuciya, wallahi kuma sai na tab'a zuciyarku. ”

Daga haka yaja motasa ya bad'e Abii da k'ura, jiki a sanyaye Abii ya shigo ciki ya d'auki key d'in mota, rik'o hannunshi Ammi tayi.

"Kar ka bishi yanzu, ka bari zuciyarsa tayi sanyi tukun, in ba haka ba baza ku kwashe ta dad'i ba, ka kwantar da hankalinka insha Allah zai fuskan cemu. ”

Dawo wa yayi da baya, ya koma kan kujera ya zauna dab'as, hannu ya mik'awa Ammi, ma'ana tazo gareshi, sanya hannunta tayi cikin nasa ya janyota jikinsa, a tare suka sauke sanyayyar ajiyar zuciya.

" Ji nakeyi kamar wani sabon al'amari zai faru damu, aduk sanda wani abu zai tunkaro ni ina jin hakan a jikina.

Nasan halin D'ahiru, babu abinda bazai iya aikatawa ba, don ya d'au fansa a kanmu, shiyasa nake son nake son fuskantar dashi, bamuyi aure don cin amanarsa ba, aurena da ke muk'addari ne ga ubangiji, Allah ya rubuta ke matata ce, matar mutum kabarinsa ce, kuma kowa akwai ta silar da zasu had'u, Allah yayi da rabon Hannatu a tsakaninmu.

Idan har yanzu yana sonki, zan iya sawak'e miki, kije ki aureshi, nikuma Allah ya raya mini Hannatu na san zata wanke mini zuciya.”


Shigewa jikinsa tayi, ta fara shashshek'ar kuka.
"Wallahi a duniyar nan babu me rabani da kai sai mutuwa, itama da da hali bazan bari ta fara d'aukar ba, sai dai ta fara d'aukana, ina matuk'ar sonka, ko shi ban masa kwatan kwacin soyayyar da nake maka ba, bazan tab'a rabuwa da kaiba, domin kaine rayuwata, kai ka san mutumcina, a duniyar nan banga wanda ya soni tamkarka ba, ko shi jikina yake so ba ni yake so ba, yaje ko me zaiyi yayi Allah ya fishi, ka kwantar da hankalinka, komai zai zo da sauk'i insha Allah. ”






"Sulaiman a yau zan juya Lagos, banga amfanin zamana a garin nan ba, don haka bazan kwana a garin nan ba wallahi, na san Muhammad zasu biyo bayana, nikuma ba na son k'ara saka su a cikin idona, don tabbas babu makawa sai na d'auki fansar abinda suka mun.”

"Nima ba na son ka barsu haka, na fi son ka d'auki fansa a kansu, don nima tun daga lokacin hanyar da Muhammad yake bi ban kuma bi, don ya b'ata mini rai sosai da sosai, amma haka zaka tafi ba ka jewa su Inna ba?”

"Zanje mana, domin ina son zan sanar musu nayi aure a can har da 'ya, zan koma ne domin na taho dasu, na san zasui farin ciki. ”


"Tom shikenan, sai ka dawo d'in, Allah kiyaye, idan kaje ka kirani, don mu san ta inda za'a b'ullo musu.




***"""
Sai da D'ahiru yayi wajen kwana nawa yana jiyar zuciyarsa, Amma tana bashi baki, a haka har ya samu ya wartsake.

"Hadiza ina son d'aukar fansa a gurin mutanen nan, amma kaina ya kulle, na rasa ta ina zan b'ullo musu, ki taimaka ki gaya mini, ina son na tab'a musu zuciya kamar yarda suka tab'a mini tawa. ”

Shiru Amma tayi, can tace.
"Abu d'aya zamuyi mu tab'a zuciyar Umaimah, mu kashe Muhammad, sannan mu mallake zuciyarta, ka aureta, yarda zamu mallake dukiyarta da mijinta zai bari, ba kace me kud'i bane, ga kuma dukiyar da yayar shi ta bari? ”

"Eh hakane ”

"To kaga in ka aureta munyi arzik'i, sai kace zaka rik'e 'yarta ta, kaga yarda dukiyar zata fi zuwa hannunmu kenan, bayan mun cinye dukiyar kuma sai ka saketa. ”

"Good idear, dole na jinjina miki, amma to ta yaya hakan zai kasance?”

"Ka bari zuwa gobe insha Allah zamuje gurin wanda zai mana aikin.”

Farin ciki ne ya dabaibaye Abba, sai yaji ya k'ara son Amma, ashe had'uwarsu da ita alkhairi ce, waya ya d'auka ya kira Sulaiman, ya gaya mishi shawar da suka yanke da Amma, Sulaiman yace.

"Gaskiya ban goyi bayan a kashe Muhammad ba, a dai yimusu farrak'u nasan hakan zai tab'a zuciyoyinsu sosai. ” Cike da b'acin rai Abba yace.

"Ba shawara na bugo ka bani ba, na gaya maka ne don kaji shawarar da muka yanke ba wai don ka bani wata ba, ka bari sanda na kira na nemi shawararka ka bani.” K'it ya kashe wayarsa, ya juya ga Amma, ya zayyana mata abinda Sulaiman yace, Amma tace.
"Gaskiya to zai bamu matsala, ya zama dole shima mu rufe bakinsa. ”





*****

Su Ammi bari sukayi sai washe gari suka je gidan su Abba, suka tafi tare da Uncle Zaid, ko da suka je anan ake sanar musu ai a ranar da yazo a ranar ya juya, haka suka juyo, sam ba suji dad'in jin hakanba, gidan Sulaiman suka huce, Uncle Zaid ne ya shiga ya anso number D'ahiru, don ko Abii ya shiga da kansa bazai saurareshi ba.


Da suka koma gida, Uncle Zaid ya kira Abba da kansa ya gaya mishi yarda lamarin ya kasance, anan Abba ya nuna masa babu komi, komai ya wuce, don har waya sukayi da Abii da Ammi, hakan da yayi sai yasa hankalin dukkaninsu ya kwanta.
Hmmmmm Abba makiri kenan, muje dai zuwa maga k'arshen makirai.




****"
Gurin wani k'ungurmun boka anan Lagos d'in Amma takai Abba, nan da nan Abba ya zayyane mishi abinda ke tafe dashi.

Wata ashariya boka ya lailayo, sannan yace.
"Ku ajiye mak'udan kud'i, kuga biyan buk'ata, nan da sati komi da kuke buk'ata zai wakana”

Kud'i suka zazzagewa boka, nan boka ya kuma antayo wata ashariyar ya d'aukko k'asa a cikin baho, yayi zurfi da ita, ya saka wani abu a ciki ya binne.

"Wannan da kuke gani shuka ce nayi, nan da sati zata fito, a ranar kuma zan gille kanta, ina me tabbatar muku da a ranar Muhammad zai rasu, a ranar ku kuma zaku tattara ku tafi, zan baku magun gunan da zakui amfani dashi wa Umaima, mutuwar zata baku damar da zaku aiwatar da aikinku ba tare da zargi ba. ”
Magun gunan ya basu, wani na turare wani na abinci, cike da farin ciki sukaiwa bokan sallama suna k'iyasta cikin wadatar da zasu shiga, dan akwai wani sirri da yake so ya sani game da Muhammad tun tuni, amma yanzu gashi zai sani ta hanya me sauk'i......



~Kuyi hak'uri da wannan, wallahi bani jin dad'i, masu son na dad'a musu tsayin typing idan na samu damar hakan zaku gani insha Allah~
[12/10, 17:52] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


~Fashuna nd Maman Aseef na baku wanga page kyauta, sai kun amince sannan za'a karanta shi, inma saidawa zakuyi na amince Ku saida shi. Hhhhhhh.~

_A gaskiya ina matuk'ar farin cikin yarda kuke suburbud'a mini addu'a especially Rabin Jiki, addu'arki takan sa wani zubin naji kamar na zubar da hawaye tsabar farin ciki da nishad'i._
_Yarda kuke faranta mini da addoin ku Allah kuma ya faranta muku da abubuwa na alkhairi, ku sani zuciyata da ruhina cike suke da tsantsar k'aunarku, kamar yarda kuke k'aunata, k'aunata ce tasa kuke karanta littafina, Allah Ubangiji ya bar k'aunarmu har darus salam_

*Hudah A Yusuf, Auntyna ta kaina kenan, barka da dawowa online, nayi rashinki sosai don akwai masu tab'ani don anga baki nan, irin su.......hhhh. Ta bani hak'uri, duk mai shirin kuma tab'ani to ya sani Auntyna ta dawo, zanci gaba addumsa sunana na 'YAR GATAN HUDDAH*



__________________
*FOURTEEN*
Rashin lafiya matsananciya Abii ya kwanta, sunje Asibiti duk wani bincike da doctor yayi bai gano komai da yake damunsa ba, haka suka tarkato suka dawo gida domin gwada na hausa.

Magun gunan hausa aka dinga karb'o mishi yana sha, amma duk da haka sauk'i sai a gurin Ubangiji, yau idan nan yayi masa ciwo, to gobe wani guri da banne zai masa yana matuk'ar shan wuya sosai da sosai.

Gaba d'aya nutsuwar Ammi da farin cikinta, walwalarta sun d'auke, kullum addu'arta Allah Ubangiji ya bawa mijinta lafiya, domin tana hango tashin hankali da rikici, gami da damuwa mai tarin yawa idan har Abii ya tafi ya barta cikin duniyarsu ita kad'ai, hawaye ne masu d'umi suka biyo kuncinta, a can k'asan zuciyarta addu'a takeyi.
Ya Allah ka jarabceni da barin mahaifana da mahaifa'ta, wacce nake alfahari da ita, da nayi yunk'urin komawa gareta sai hakan ya gagara gareni, Allah kai ka san me ka b'oye cikin Rayuwarmu ni da 'yar uwarta, Allah Ubangiji ka bamu ikon cinye Jarabawar K'ADDARAR RAYUWARMU, Allah kar ka jarabceni da mutuwar Muhammad, mutuwarshi zata tab'a mini zuciya, rayuwa babu shi tamkar ba rayuwa nake a doran k'asa ba, mutuwarshi zata zo da babban rikici cikin rayuwata, Allah ka duba maraicin da HANAH zata shiga, kar ka jarabceta da rashin mahaifi, ka barta mahaifinta ta rayu dashi ta san dad'in uba......

Matsa hannunta da Abii yayi, shi ya dawo da ita daga zancen zucin da take, wanda shima d'igar hawayenta kan hannunshi ne ya fargar da shi cikin halin da take.

Kuma matsa hannunta yayi, ya kalli fuskarta da har lokacin hawaye na sintiri bisa kuncinta.

"Ko wani bawa baya wuce K'ADDARARSA, kuma ko wani bawa yana da K'ADDARA a cikin RAYUWARSA, ki zamo me juriya da karb'ar lamarin rayuwa a duk yarda yazo miki, kar ki zamo d'aya daga cikin masu butulcewa Ubangiji.
Ita rayuwa tana zuwarwa mutum ne a yarda ya d'auketa, kar kiga kamar ke kad'ai Allah yake jarabta ta fannin abubuwa da dama, kowa na duniya Allah yana jarabtarsa, kuma Allah yafi jarabtar salihan bayi, yana sane da ke, ki dage sosai gurin cigaba da karb'ar rubutu kina sha, insha Allah da k'afarki zaki taka zuwa mahaifarki, naso naje na gano miki mahaifanki, sai dai kawai kiji nazo miki da labarin suna lafiya, amma Allah baiyi zanje ba.
Cuta ba mutuwa bace, amma wannan ciwon nawa ina ji a jikina ciwon Ajali ne, ba ciwo ne na tashi ba, Allah ya rubuta gajeriyar rayuwa zamuyi da ke tun fil'azal, amma ina me rok'onki kada ki manta dani a duniyarki, ki dinga mun addu'a, sannan ki dinga bawa Hannatu labarina, da irin soyayyar da nake mata, naso na rayu da ita, amma ina jin kamar rayuwata tazo k'arshe. ” Hawaye ne masu matuk'ar d'umi suka kwaranyo bisa kuncinsa.

Fadawa jikinsa Ammi tayi, ta saki kuka me ban tausayi.
"Baza ka mutu ka barni ni kad'ai cikin Duniyarmu ba, domin ni da Hannatu muna buk'atarka cikin RAYUWARMU, insha Allah, Allah ya rubuta tun Fil'azal Rayuwarmu me matuk'ar tsayi ce, bana son naji kana zancen mutuwa ko kad'an, yayiwa k'wak'walwata nauyi, bazan iya d'auka ba. ” Ta fad'a tana k'arawa kukanta k'arfi, murmushin yak'e Abii yayi, yace.

"Mutuwa ai ta zama dole Umaimah ko da ciwo ko babu ciwo dole sai an tafi, bare ni da nake cikin matsanancin ciwo, ni kad'ai na san irin azabar da nake sha, bakina ma bazai iya fad'arta ba.
Ko da kuna buk'atata a duniyarku, nima ina matuk'ar buk'atarku a duniyata, amma Allah baya barin wani dan wani, da yana bari da baisa an d'auke uwa daga haihuwarta ta tafi tabar jaririnta ba, kuma da baisa an raba soyayyar masoya ba, kuma da baisa an mayar da yara marayu ba, idan rayuwarmu ba ta zamo me tsayi ba anan, to Allah Ubangiji ya d'orar mana da ita a Jannatul Fiddausi. ”

Kasa magana Ammi tayi, sai sheshshek'ar kukanta kawai ake ji, rintse ido Abii yayi ya kira sunanta.
"Umaimah”

"Na'am” Ta amsa muryarta har ta fara dashewa saboda kuka.

"Dan Allah ki daina wannan kukan yana tada mini da hankali.”

"Na daina, Allah Ubangiji ya baka lafiya, ka dawo muci gaba da soyayyarmu mu yowa Hannatu k'anne tara, insha Allahu rayuwarmu me matuk'ar tsayi ce, mutuwa baza tayi mana yankan k'auna ba. ”

"Insha Allah Umaimata.” Abii ya fad'a yana kallon tsakiyar idonta, murmushi me sanyi ne ya kufcewa Ammi, har sai da dimples d'inta sukai matuk'ar lotsawa.

(Chaii Ashe dimples d'in Ammi Hanah tayo,ku baku ganshi ba kamar kwa zira yatsa ciki Hhhhh.)

"Kiyi mini al'k'awari Umaimah”

"Al'k'awarin me mijina?”

"Idan ta Allah ta kasance a kaina, kina yaye Hannatu zaki cika mini alk'awarin da na d'aukarwa Auncle Zaid, bi ma'ana zaki bashi Hannatu halak malak, domin ina tausayinshi wallahi, tunda har Aunty Hannatu ta rasu ba'a gane me matsala a tsakaninsu ba, naci burin ko da Aunty Hannatu na da rai 'yata ta fari takwara zan mata, kuma na basu ita, sai gashi sai bayan ranta hakan ya kasance. ”


"Nayi maka al'k'awari, insha Allah ma da kanka zaka cika wannan alk'awarin.
Nima ina tausyin Auncle....... ”

Sallamar Auncle Zai ce d'auke da ni a kafad'arsa nayi bacci ce ta katse Ammi daga fad'ar abinda zata ce, ta mik'e ta karb'eni ta kwantar dani a kusa da Abii, tana yiwa Auncle Zaid sannu da zuwa.

Yaje rano ne ya karb'owa Abii magani, mak'ale masa nayi akan sai na bishi, hakanne yasa yacewa Ammi ta shirya ni mu tafi tare.

Abii sannu da hanya yake masa, shikuma ya k'arfin jikin nasa, yace.

"Alhamdlillah, don tunda ka tafi ka barni bai motsa ba, hira ma muke tayi da Umaimah. ”

Fuskar Auncle Zaid ce ta fad'ad'a da murmushi saboda jin dad'in abinda abi ya fad'a, yace.

"Allah mun gode maka, Allah Ubangiji kasa warakar ce tazo.”

Amin dukkaninsu suka ce, yacewa Ammi ta kawo masa cup, ko da ta kawo mishi cup d'in rubutu ya tsiyaya aciki ya mik'awa Abii, karb'a Abii yayi, yasha da bismillah a bakinsa ya shafe ragowar a dukkanin ilahirin jikinsa, a take wani k'arfi da nutsuwa suka zo mishi.


Wani akwatin k'arfe Abii yacewa Ammi ta mik'o masa, ko da ta mik'o masa sai ya d'aukko wata doguwar takadda fara tas da abubuwa a cikinta a nannad'e, ya mik'awa Auncle Zaid, karb'a Auncle Zaid yayi yana cigaba da kallon Abii, yana san bayani kenan.

"Kaine mahaifin Hannatu, ko ina da rai ko bana da rai, naso sai randa zan dank'a Hannatu gareka na baka, to amma ina ji a jikina kamar bazan kai lokacin ba shiyasa na dank'ashi gareka yanzu, bayanan komai yana ciki, kyauta ce ga d'iyarka Hannatu, a ranar da ka aurar da ita ka yarda da nagartar mijin da ta aura, a ranar zaka dank'a kyautar gareta, kace inji k'aramin ubanta.

Akwai key a ciki, na wannan gidanne, babu wanda yasan da zaman gidan daga ni sai kai sai Aunty Hannatu, saboda yarda da aminci sunyi k'aranci a cikin duniyar nan, don haka daga ita sai mijinta na amince su san da zaman gidan, shima idan ka amince da nagartarsa.
Idan kuma Hannatu Allah yayi ba me tsawon rai bace, to na barmuku abinda ke ciki kai da Umaimah halak malak.”

"Insha Allahu dukkaninmu sai munga auran Hannatu, Allah kuma ya bani ikon sauke wannan nauyi da aka bani. ”

Amin suka ce dukkaninsu, sannan suka cigaba da hira, Abii yana shafa fuskata, yayin da nake cikin duniyar bacci.





____________________
Ranar juma'a da sanyin safiya jikin Abii ya kuma rikicewa, Ammi da Auncle Zaid hankalinsu yayi k'ololuwa gurin tashi domin Abii ko magana baya iya yi, bakinsa dai sai motsi yake, yana ciccige leb'e.

Ko wace addu'a idan tazo bakin Ammi da Auncle Zaid tofa masa suke, hawaye yana zuba bisa kuncinsu.

Jikin Abii ne ya saki gaba d'aya ilahirin jikinsa ya daina motsi, idanuwansa suka k'ak'k'afe, hakan yayi dai² da sanda boka ya yanke shukar da ta tsiro a cikin robarsa.

Ammi tana lura da haka jinin jikinta ya tsaya cak, zuciyarta ta daina harbawa, ta kifa kan Abii numfashinta ya

Please Login or Register in order to submit comment