Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


"Amin ”
Matar tace, har lokacin tana bina da kallo, ni kuma na bi bayan Ya Hafiz da na hango sa tsaye da wani.
A dawowa sai da Ya Hafeez ya biya ya saya mini pop corn, saboda a mota naci wanda Baby ta bani nayi ta santi, yayi birgima cikin madara sosai don ni duk inda harkar kwad'ayi take nan naga gurin zama.

Tsaye muke da shi muna yin sallama, ya cikani da surutu yak'i barina na tafi, Ya Haisam naga ya nufo gurinmu fuskar nan tasa a murtuke.
"Ke shige mu tafi dare yayi. ”
"Haisam” Hafiz ya kira sunansa, d'aga masa hannu Haisam yayi yace.
"Dare yayi da safe mayi ko wata irin magana ce. ”Daga haka ya tisa k'eyata muka shige ciki........
[12/10, 18:21] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


__________________
*FOURTY*
Zan shige d'aki ya daka mini tsawa, ba shiri na mik'i hanyar d'akinsa gabana na bugun tara².
Hanya na bashi ya shige, fuskar nan tasa a murtuke har lokacin, bakin gado ya samu ya zauna, ni kuma na sunkui da kaina k'asa, shiru na tsayin mintuna babu wanda yace komi, jin shirun yayi yawa yasani d'ago kaina na dubeshi, sai idona cikin nasa, wata shegiyar harara ya watsomun nayi saurin kawar da kaina daga kansa, d'an siririn tsaki yaja, ya d'auki wayarsa ya danna kiran Sadiq, don tun misalin 9 yake kiransa Rumanah ta damesa ya had'ata da Sahibatinta, amma hakan ya gagara, don a lokacin yana kwance cikin ciwo, zuciyarsa tanai masa k'una, a duk sa'ilin da ya tuno mugayen kalaman da Daddy ya gaya masa zuciyarsa tana masa wani irin ciwo mara misali.
Cewa Sadik' yayi ba ta nan, amma in ta dawo zai kira, da suka ji shiru bai kira ba shine misalin 9:45 ya kuma kira, k'in d'agawa yayi ya fito nemanta, Baby ce take cemasa sun fita da Ya Hafiz, shine dalilin da yasa ya zauna zaman jiran su dawo cikin b'acin rai.
Picking Sadik' yayi ya mik'awa Rumana da ke gefensa, yana ganin anyi picking ya mik'o mini ansa nayi na zauna a k'asa, kallonta kawai na tsaya yi na kasa magana sai itace cikin sanyi tace.
"Sahibati lafiya? ”
Ji nayi wani kuka me d'aci ya taho mini kuma na kasa tsayar da shi, cikin son fashewa da kuka itama tace.
" Tom bari na kashe wayar tunda ba zaki mini magana ba. ”
Murmushin yak'e na k'ak'alo na share hawayena nace.
"Yaushe zaku dawo?”
"Naji yace sai k'arshen wani watan da zai kama, lafiya? ”
"Ammi, ni dai zanje gareta ko da Abba zaiyi sala² da naman jikina. ”
"Hanah.”
Zuba mata ido nayi, don tunda naji ta ambaci sunana na san magana zata mun me muhimmanci.

"Kiyi hak'uri b'oye mikin da nayi, nayi hakanne don a lokacin bai kamatu a k'ara miki damuwa cikin damuwa ba.
Tun bayan da Hamid ya rasu, naje muyi magana da Ammi, anan naji zancen Abba ya kwashesu sun koma Abuja, hankalinmu ya tashi ni da Yaya Hisham yarda ba kya zato, amma muka yanke shawarar kar a gaya miki saboda kina cikin rad'ad'in mutuwar Hamid, amma Yaya Hisham tun daga lokacin ya saka a bincika inda suke zaune a Abuja, kwanan nan ya kirani yace mini an samu inda Ammi take, amma ko da yaje sai akace masa wai ta tafi gidansu. ”
Kukane ya taho mata amma ta dake, don ganin yarda hawaye ke gudu a kumatuna, taci gaba.
"Kiyi hak'uri, komi na duniya k'ararrene, duk abinda yayi farko zaiyi k'arshe, kuma babu wata damuwa me d'orewa face komi yana da lokaci, ki kwantar da hankalinki yanzu gurin da kike zaune babu wata damuwa cikinsa, insha Allahu zamu juyo labarin Ammi, gara ma ke kina da Ammin, kuma muna saka ran bayyanarta, mu kuwa da tamu ta rasu, bamu da wani bayani a kanta sai dai kullum tace mana tana da iyaye ba, kuma tana da asali, ta taso ne kawai a gidan marayu, munyi² ta fad'a mana inda mahaifanta suke amma ina har sai da me rabawa ta raba, tun da ranta muka taso cikin gorin asalin uwa har wa bayan ranta ba'a daina goranta mana ba, muna da mahaifi amma da mu da wanda bai dashi duk d'aya, to ki gaya mini muyi ya da rayuwa Hanah? Hak'urin nan dai shi zamu cigaba da yi tunda babu yarda zamuyi da K'ADDARAR RAYUWARMU.
Ke kina saka ran zakiga naki dangin, tunda ance Ammi ta tafi danginta, kuma na san dole zata nemeki, kuma muma zamu cigaba da nemanta, mu kuwa fa? Haka zamu k'arashe RAYUWARMU babu dangin uwa bare na uba, tunda da su da babu duk d'aya. ” Hannu ta saka ta cire k'wallar idonta, zuciyarta na mata zafi tana son yin kuka, amma ba ta son kuma karyawa Hanah zuciya.
Share hawayen da yak'i tsaya mini nayi nace.
"Ba kince akwai abinda Umma ta baku ba da zata rasu, tace ku rik'esa may be ta silarsa ku samu asalinta? ”
"Bar wannan batun Hanah, bayan ba musan daga wani gari take ba. ” Hawayen da take ta mak'alewa ne ya zubo bisa kuncinta, dariya ta hau yi don kar Hanah taga hawayenta ta damu tace.
"Habibati, ina da ciki na wata uku ”
Dariya nima nayi nace. "Kai Alhamdulillahi, Allah Ubangiji ya raba lafiya ya kawo mana Babynmu lafiya, amma nayi farin ciki wallahi.”
Dariya tayi tace.
"Amin Habibati, kije ki kwanta dare yayi."
Dariya muka yiwa juna hawaye na zuba a idonmu mukai sallama, mukayi hanging up in wayar.
Idanuwan Haisam suna kaina har na kammala wayar na tashi na mik'a masa wayar, rik'ewa yayi tare da hannuna ya mik'e yana kallon yarda hawaye ke sintiri a kumatuna har lokacin, jan hannuna yayi ya jingina da jikin bango ya janyoni jikinsa, ina jina jikinsa na fashe da wani irin kuka, don dama abinda nake buk'ata, to nayi rashin Ya Hamid, shi kad'aine yake rungumata nayi kuka a jikinsa, sai Rumanah, ita kuma tayi nesa da ni. Lumshe idonsa yayi ya zame da mu k'asa, k'ara shigewa jikinsa nayi, nayi kukana me isata daga bisani na fara k'ok'arin ta shi, cikani yayi yana mini wani irin kallo.
"Ya isheki?” D'aga masa kai nayi. ”
"Dukkaninmu muna fuskantar K'ADDARAR RAYUWA, kici gaba da hak'uri duniya babu wani hali me d'orewa, yau in ta sakeka gobe waninka zata kama, mudai muna fatan Allah yasa mu gama daita lafiya, Amin.
Ki mini alk'awarin baza ki kuma kuka ba. ”
Kai na kuma d'agawa yace.
"Um um nidai magana zaki min. ”
"Na yima alk'awarin ba zan kuma ba” nace, cikin sanyin murya.
"Tom tashi kije ki kwanta. ”
A tare muka mik'e, ya bud'e mini k'ofa na fita, juyowa na kuma yi, yana tsaye be koma ba, muka had'a ido, ya sakarmini murmushin da ban tab'a ganin yayi irinsa ba, nima murmushin na masa ya d'aga mini hannu.




_________________

Ashe tun tafiyar Yaya aka kira Daddy akan yazo yayi hatsari, a kansa ya bugu sosai, tun zuwan Daddy Yaya ya dinga ya kira masa Haisam a waya, amma sai Daddy yace ya kira a kashe, ganin ciwo yana ta gaba yana jin kamar bazai tashi ba, ya gayawa Daddy duk inda kadarorinsa suke, da takardar da ya rubuta ta mallakawa Haisam komi nasa, da takardun asibitin da ya bud'e masa a ithopia, shine dalilin da yasa yace yazo k'arshen wata ya samesa, a k'arshen watan za'a bud'e asibitin, kuma suprice yake son bashi shiyasa.
A ranar da ya gayawa Daddy komi a ranar ya amsa kiran mahalicci, gashi har anyi kwana biyu da rasuwarsa amma bai gayawa su Haisam ba, ita kuma Mama sai k'ok'ari take ta karb'e takardun da suke hannun Daddy.

Shi kuma Haisam ganin kwana biyu basui waya da Yaya ba, tun yana kira ana k'in d'auka har ya zamto in ya kira a kashe, kawai sai ya shirya ya tafi ithopia ya fasa jiran k'arshen watan yayi, don hankalinsa ya tashi sosai Mommy ma ta goya masa baya......


To fah masu karatu anan na kawo k'arshen littafin K'ADDARAR RAYUWARMU na d'aya.

To shin Mama zata samu nasarar karb'ar takardun hannun Daddy kuwa?
Ya Haisam zaiyi idan yaji Yaya ya rasu?
Ammi zata ji sauk'i ta koma ga danginta, akwai sake rabon had'uwarsu da tilon 'yarta kuwa?
Meye abunda Umman su Rumanah ta basu? Ko zaiyi sanadiyar ganin asalinsu kuwa?
Daddy zai dawo hayyacinsa ya nemi tilon d'ansa da matarsa,
Ya makomar Mama zata k'are?

Amma da Abba ko zasu kuma ganin Hanah a rayuwarsu?

Asirin jikin Baffa zai karye ya nemi 'yay'ansa, ya makomar Aunty take?
Ya zasu karb'i Hanah idan suka san ba k'anwar Haisam bace?

Hisham, Haisam, Hafiz, wa zaizamo miji ga Hanah? Ga kuma Halisah shin kuna ganin zata samu soyayyar Haisam?

Duk ku biyoni amsoshinku suna cikin littafin K'ADDARAR RAYUWARMU KASHI NA BIYU.


My Readers ina matuk'ar alfahari da ku.

Allah Ubangiji ya bani ikon rubuta muku shi.......

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment