Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciwu a ga reiki ba kisha abu me d'umi sannan kiyi sallolin dake kanki. ”
Cikin dashash shiyar muryata nace masa. "Na gode ” na tashi na fito yabi bayana da kallo cikin tausayawa, sunkui da kaina nayi, don na san yana falon saboda sam bana son mu had'a ido da shi, shima kuma ko kallon inda nake bai yiba har na fice.

Ban tadda Rumanah ba tun magariba Sadik' yazo suka tafi akan gobe zata dawo, Momy ce ta had'a mini ruwan wanka me d'an zafi da kanta na shiga wanka, dunk'ule hannuwana nayi na rintse idanuwana na shiga rera kuka a hankula yarda Momy baza taji niba.
Ya dinga cemini nayi hak'uri ashe tafiya zaiyi ya barni tafiyar da bazai kuma dawowa ba,duk mafarkan nan da nake ashe hakan zai zo a gaske, wayyo ni HANNATU babu Abii babu Ammi babu Uncle Zaid gashi Ya Hamid shima ya bar RAYUWATA.
Ba zan tab'a mantawa da kaiba Ya Hamid kullum cikin addu'oina sai na sanyo ka, amma me yasa ka tafi ka barni CIKIN DUNIYARMU? ka tafi ka barni da d'unbin kewarka, ina sonka⁴ bazan tab'a daina sonka ba har k'arshen numfashina, kuma nayi alk'awarin idan har d'a namiji na fara haifa to sunansa ABDUL HAMID.





_______________


Kwanan Rumanah uku a jere Sadik' yana kawota sai magariba yazo su tafi, a washe gari taje gidan su Ya Hamid neman Ammi, domin washe gari zasu tafi America, shine taje taji yaushe ne lokacin da zan dawo gida, anan kuma take jin labarin sun koma Abuja, hankalinta ya tashi sosai ta gayawa Sadik' yace ai ba'a k'aran wani zafin ba ta barni kar ta gayan a gayawa Hisham ya saka a binciko inda suka koma a Abujan, shawarar sa ta d'auka shiyasa washe gari da suka zo yimana sallama sam bata gayan ba, ta dai gayawa Ya Hisham.

Munyi kukan rabuwa kamar ance baza mu rabu ba, bayan tafiyar su Rumana ya Hisham da Momy ne suka dinga d'ebi mini kewa, sam basa barina cikin damuwa, har fita yaho ma muke da Ya Hisham hakan yasa sosai na saki jiki da shi, bayan sati biyu da haka shima yace zaiyi tafiya ji nayi kamar na d'ora hannu a ka nai ihu, lallashina ya dinga yi yace ba wani jimawa zaiyi ba a can.
Ko da Ya Haisam zai tafi kaishi filin jirgi mak'alewa nayi nace sai naje, wani kallo ya watso mini da ba shiri na bar gurin ina k'un k'uni, ina kallon Hindu a tsaye ta kafe shi da idanuwa kamar ta cinye shi d'anye, don ba k'arya sosai kayan jikinsa suka kuma fito mishi da zallar kyahunsa.





*****
Yau gidan an tashi da tarb'ar Daddy, Mama sai rawar jiki take yi, nidai na k'agu na san wai Maman nan kishiyar Momy ce, ko kuwa?
Jinta nayi tana waya daga bayan kicthen.
"Eh mana yana matuk'ar son kunun gyad'a don haka a ciki zan bar bad'e shi ya saki tsinanniya su bani guri daga ita har bugaggen d'anta da shegiyar karuwar da ya ajiye.”
Nikuma abinda ya kawoni kitchen in, zuwa nayi na dama kunun gyad'a ji nayi kawai ina son shansa, ba tayi tunanin wani zaizo gurinba, tunda Momy ba zuwa kitchen in take ba 'yan aiki ne suke yin komi kuma Mama ta riga duka ta siye su, juyawa kawai nayi d'aki sai da na tabbatar ta bar kitchen in sannan na dawo na dama kunun gyad'a me d'an yawa a plask nayi d'aki da shi,ina k'udurta abinda zanyi a raina, tsiyaya nayi na sha, Momy ma ta sha muka bar ragowar a plask kuma Momy bata tambayeni dalilin dama shi da yawa haka ba.



Ko da Daddy ya dawo be nemi Momy ba, don dama be sanar mata dawowarsa ba sai ji tayi, ko d'aukkosa ma Harris yaje yayi,
Mama ce take ta rawar kan dire abin ciccika kala² ta d'aukko jug in kunun gyad'yar ni kuma na fito, karo mukayi da. ya Haisam a raina na furta Alhamdlillah! Murje mishi k'afa nayi na kwasa da gudu shima ya biyoni da gudu ina zuwa na daki hannun Mama wanda ta rik'e jug in da shi aikwa yayi k'asa duk ya fallatse mana jiki, cike da huci ta d'ago ta fella mini wani gigitaccen mari.............
[12/10, 17:56] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

Page d'in nan naki ne Hafsat Muhd, Haisam yace ya baki shi kyauta saboda dad'in addu'ar da kika masa, amma fa yace shi sam ba son Hanah yake ba, domin shi sam soyayya ba ta cikin tsarinsa, a ganinsa b'ata lokaci ne da bada kai a gurin mace.

_________________
TWENTY FIVE
Zafin kunun da ya zubo mini a k'afa da zugin marin da Mama tamun a lokaci d'aya suka kaimun ziyara cikin K'wak'walwata na tafi luuu zan fad'i k'asa Haisam yayi saurin taro ni jikinsa, kallon k'afata yayi da kunun ya zubo mini na tsayin lokaci kad'an, sannan ya d'aukeni ya nufi fanfo da ni ya tara k'afata a kai.


"Mtsssss” Mama taja tsaki. "Duk wuyar da na sha na dama kunun nan yanzu shikenan yarinyar nan ta cuceni tayi sanadin da ya zube mtssss” ta kuma jan tsaki. ”

"Wani irin kuma wahala kika sha bayan muna da ga'sara da gyad'a a fridge? Ko da yake ina ga kin saka masa wani kayan da zai k'ara mishi armashi ko? ” Momy ta fad'a tana nufo gurin Daddy da flask d'in da na zuba kunun gyad'a a ciki, shiru Ammi tayi cike da tsoron kad dai an gano abinda ta zubawa kunun amma kuma ai kunun sam kalarshi bata sauya ba, banda ita da ta zuba maganin a kunun babu me cewa an zuba masa wani abu sai dai idan wani ya ganta tana zubawa, to amma kuma ai tayi ta ka tsan² kafin ta zuba.

"Ko da yake shima kunun kansa ya san Daddy bai kamaci ya sha shi ba sai wanda matarshi ta dama shiyasa ya b'are, don haka ki daina k'ok'arin k'watar daddawa a bakin b'era, domin k'watar ta ba abu ne me sauk'i ba don haka gara ki sayi taki daddawar. ”

Maganar Momy ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, barin falon tayi kawai zuciyarta tayi sama, ajiye flask in Mommy tayi ta tsiya yawa Daddy kunun gyad'ar a cup, ansa yayi yana sakar mata murmushi, ai duk da lafinki kema idan b'era da sata ai daddawa ma tana da wari, tunda na tafi ko waya ki kirani kiji ya nake baki tab'a ba sai dai ni na kira shiyasa da na gaji da kiranki nima na watsar, naga kin barwa Lamrah ni har tana k'ok'arin k'wace miki ni.”
"Na san nima ina da kuskure amma hakan bazai sake faruwa ba, kayi hak'uri dan Allah.”
"Ay ya huce, ana samun cigaba a al'amuran Haisam? ”
"Eh Alhamdilillah ba kamar da ba. ”
"Toh Allah yasa a dace, na kammala ginin asibitin na zuba k'wararrun likitoci, ranar lahadi za'ai walimar bud'e shi. ”
Babu nuna damuwar komi Mommy tace.
"Allah ya nuna mana, yasa a bud'e a sa'a.”
"Amin, ita wannan yarinyar da ta b'arar da kunun wace ita? ”
"Amanar Rumanah ce. ” Ta bashi labarin dalilin zamana a gidan, sannan tace yaci abinci tukun sayi hirar.




*
Tun zuwanta gidan a kulli yaumun sai ta tsaya ta k'urawa wani hoton yarinya da bata wuce shekara takwas ba ido da aka bud'a shi aka k'awata shi, daga k'asan hoton an saka SUHANAH BIN ZAID.
Kuma mai maita sunan tayi a k'asan zuciyarta, zuciyarta na zargar mata wani abu, sai dai kuma idan ta tuna bai tab'a haihuwa ba kuma bai da burin sake aure wanda zaiyi da ma zaiyi ne domin ya rik'e Suhanah, to in ta tuna hakan sai ta k'aryata zarginta.

Tana jin dad'in zama da matar gidan sosai da sosai don zasu kusa sa'anni da ita, don haka suna mutunta junansu, ya'ranta biyar uku maza biyu mata, dukkanin su suna girma ma Ammi, suna bata girmanta, amma duk cikin 'ya'yan babu wannan yarinyar me suna Suhanah Bin Zaid.


*
Subai'ah ciwo sosai ta kwanta wanda har sai da aka dangana ta da asibiti, gwajin farko da likitoci sukai mata sun tabbatar da tana d'auke da ciwon k'anjamau, hannu Amma ta d'ora aka tana kururuwa, Abba kuwa sumewa yayi ya dawo, kallon iyayen nata tayi tana ambaliyar hawaye cikin murya k'asa² tace.
"Ai duk ku kuka cuceni, ku ka cuci rayuwata,kun d'ora zuciyata akan bak'in ciki da hassada, tabbas hassada mugun ciwo ne dake addabar zuciya , kuma dukkanin me hassada baya tab'a yin gaba sai dai ya tab'e, kaico da rayuwa irin tamu, ina zan ganki Hannatu? Na nemi yafiyarki, tabbas hak'k'in ki da mahaifana da suka d'auka shi ya hujujjuga rayuwata na afka soyayyar wanda yake matuk'ar sonki garin nemo soyayyarsa na gamu da ciwo illata garkuwar jiki. Tana kaiwa nan ta kuma fashewa da marayan kuka, Amma tace.
"Wani mugu azzalumin ne ya saka miki mugun ciwon nan?” ta fad'a hawaye suna rankayowa bisa kuncinta.

"Sumy.....”



Kuyi hak'uri da wannan nayi typing ya goge ne kuma ban jin dad'i.
[12/10, 17:56] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


__________________
*TWENTY SEVINE*
Ashe bayan Mama taga hucewata harara tabi bayana da shi daga bisani tayi kyakkyawan murmushi, bi ma'ana k'udirinta na gab da cika, tashi tayi ta nufi d'akin Hindu ta bata k'ullin maganin da boka ya bata.
"Magani na karb'o miki wanda Haisam zai soki matuk'a har fiye ma da son da kike masa, na gaji da ganinki cikin damuwa shiyasa na yanke shawarar baki abinda kike so. ”
Rungumeta Hindu tayi tana tsiyayar da hawayen farin ciki.
"Na gode matuk'a Mamanmu, sai yanzu na san ina da matsayi babba a zuciyarki. ”
Murmushi Mama tayi tace.
"Naga Hanne ta tafi gurinshi kije maza ki hura musu maganin, dama yace sai suna tare za'a hura, kina hura musu kiyi saurin barin gurin kar ki bari wani yazo ya ganki, in ba haka ba aiki zai lalace mana. ”


Tana hura mana tayi saurin barin gurin da gudu ta isa gurin Mama tana ta haki, lemo Mama ta bata a cup ba tunanin komi ta karb'a ta kafa kai ta shanye tas tana gama sha taji kanta ya fara jujjuyawa kan kice meye bacci ya kwasheta a 360 Mama ta kalleta tana sakin murmushin mugunta.


Wani irin abu muka ji yana yaho a jikinmu, wani irin yanayi yana shiga ta k'ofufun jikinmu, sai jin bakin Ya Haisam nayi cikin bakina ba musu na anshe muka fara musayar yahu.
Gaba d'aya mun fita daga hayyacinmu idanuwanmu sun juye sun canja colour tuni yayi cilli da hijabin dake jikina ya fara k'ok'arin zame hannun doguwar rigar dake jikina ni kuma ina b'alle wuyan rigarsa.



Ina fita Momy itama ta fita taje d'akin Daddy, ta dawo d'aukar abu ta tarar har lokacin ban dawo ba, a ranta tace.
'To me yarinyar nan take yi a d'akinsa har yanzu bata dawo ba?'
D'an tsaki ta ja ta nufi d'akin Haisam ranta a matuk'ar b'ace.
'Sau nawa zata cemasa bata son mu keb'e a guri d'aya saboda gudun magana, shi sam bai gudun zargin mutane ko kad'an wallahi.

A yanayin da ta samemu da ba dan tayi da gaske ba tana iya fad'uwa a gurin, saura k'iris ya k'arasa zame rigar dake jikina bakinmu a had'e muna tsotsar juna kamar ba ma rabu ba, hawaye ne ya siraro bisa kuncin Momy ta fara k'ok'arin raba mu, mari ta zabga wa Haisam amma munk'i sakin juna ko kad'an, rufe shi tayi da duka, amma ina ba musan tana yiba ko kad'an.

Muryar Daddy taji daga bayanta yana sakin salati, Mama ce tayi saurin zuwa kiranshi don taga sanda Momy ta nufi d'akin.
Bata san sanda wani k'arfi yazo mata ba ta fincike ni daga hannun Haisam, tayi saurin lullub'a mini d'ankwalinta, hannu nake mik'a mishi shima yana mik'o mini hannu hawaye na tsiyaya bisa kuncinmu, da k'arfin tsiya Momy ta jani ta fice da ni daga d'akin, maruka uku Daddy ya wanke Haisam da shi daga bisani ya rufe shi da duka ko ta ina.
"Banga amfanin haihuwarka ba, na tsaneka³ Allah ya tsine maka albarka, duk bak'in cikin da ka k'unsa mini kaima sai ka haifi wanda zai maka finsa, duniya ce baka yiba ma anai maka bare kuma kayi, tunda ni har iyayena suka mutu suna saka mini albarka, Allah yayi wadaranka wallahi, a cikin gidana ka ajiye dadironka duk ban sani ba, ka had'a baki da munafukar uwarka, Allah ya isa cutar da kukai mini bazan tab'a yafe muku ba, ka tattara kayanka ka barmin gida kaje na yafeka dama kai kad'ai na haifa to zan sakawa raina ban tab'a haihuwar d'a ba sai Harris.”
Yana kaiwa nan ya juya ya bar d'akin yana goge k'wallar idonsa Mama na binsa tana tausar shi akan ai ba ya yanke hukunci cikin fushi ba, ya dakatar da ita alamun baya son jin komi.

Shikuwa Haisam baima san me Daddy yake ba, yakai k'ololuwa gurin buk'atuwa kawai Hanah yake so yaji a cikin jikinshi, juyi kawai yake a tsakar d'akin yana tsiyayar hawaye.

Ni kuwa Mommy na jana ina tirjewa har muka isa d'aki ta jefani kan gado, kuka naci gaba da yi ina.
"Momy ki maidani gurinsa wallahi zan mutu idan har ban jini jikinsa ba. ”
Kuka Mommy ta fashe da shi don ta fuskanci akwai matsalar da ta faru, maganin barci ta bani na sha da k'yar, ai kuwa cikakken minti uku ban yiba barci yayi awon gaba dani a gurin, tana ganin nayi barci ta fita ta barni a gurin.

A k'ofar d'aki ta tsaya, tsaf taji abinda Daddy yace, ko gurin da ya tsine mishi rintse idonta tayi zuciyarta tana wani irin tafar fasa, a zuciyarta tace.
'Ni kuma nace Allah yashi maka albarka ya kareka daga dukkanin wani bala'i, Allah duk me son lalata rayuwar tilon d'ana Allah ka tagayyara shi, Amin'

Sai da ta bari ya fita Mama tabi bayansa tukunna ta shiga d'akin ta taddasa yana ta juyi, maganin da yake sha ta d'aukko ta basa ta had'a mishi da na barci ya sha, yana sha shima ya b'ingire a gurin, tana ganin yayi barci ta fice gurin Malam Jafar, don ya zama dole ta karb'a mana rubutu tunda barin gidan zamui kuma dole zamu kasance guri d'aya domin sam bata k'aunar wani abu ya shiga tsakaninmu.




Sai la'asar muka farka, shima badan barcin ya ishemu ba, hayaniyar Daddy naji yana sai ya kashe Haisam, muddin bai bar masa gida ba, kulle d'akin Mommy tayi tana kuka, ta harhad'a mishi dukkanin kayansa na buk'ata har da takaddunsa da ta sato a d'akin Daddy don tana saka ran inda zaije zai samu waraka har ya soma aikinsa rayuwarsa ta nutsu guri d'aya.

Da kanta takai masa dukkanin kayan cikin mota, sannan ta dawo ta bashi rubutun da ta karb'o gurin Malam Jafar, ba musu ya karb'a ya sha da bismillah.
Bayan ya sha ta saka mishi key cikin hannunsa tace.
"GOMBE STATE, GIDAN FULANI. ”

Matse hannunta yayi yana zub da hawaye ya yi mata kiss cike da farin cikin gaya masa abinda ya dad'e yana nacin sani, zame hannuwanta tayi daga nasa ta nufo d'akin da nake,ina kwance ko motsi ban yiba sai hawaye dake ta tsiyaya ta gefinan idona, rubutun nima ta bani na sha, sannan naga ta harhad'a mini 'yan kayana ta fita da su.

Da kanta ta saka mini hijabi ta ja hannuna har bakin motar Haisam yana ciki yana jirana, bud'e motar tayi, ta sakani gidan gaba ta juya baya tace.
"Allah ya kaiku lafiya, ka rik'e amanarta. ” sannan tayi ciki da gudun tsiya kamar yarinya, domin yau zuciyarta ta famo abubuwa da yawan gaske.



Da gudun tsiya yaja motar ya fice daga gidan, sai da mukai tafiya me nisa sannan ya juyo da jajayen idanuwansa ya dubeni ya daka mini wata uwar tsawa yace na fice daga motarsa, wasu sabbabin hawaye naji sun kuma biyo mini kuncina, na kalli yarda gari ya kuma murtukewa don tun fitowarmu daga gida hadari ya had'o ko ta ina, tsawa ya kuma daka mini ba shiri na fice daga motar shi kuma yaja ta da gudun gaske.

Tafiya na soma yi ina kuka, ni duk duniyar ta isheni, ko kad'an bata birgeni, yanzu ina zanje, da wa zanje, ina zan saka kaina, wa zan kaiwa kukana ni Hannatu?'
Na durk'ushe a gurin na saki kuka me matuk'ar tab'a zuciya a dai² lokacin ruwa ya kece da gudun tsiya..........
[12/10, 17:56] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Sweet Novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)

Wannan page d'in naki ne ke kad'ai Ramlat kiyi yarda kike so da shi inji Hanah.
____________________
*TWENTY EIGHT*
Shi kenan bani da kowa, ni kad'ai zan ta rayuwa, inama² mutuwa tazo ta riskeni a wannan yanayin domin ita kad'ai nafi buk'ata a wannan yanayin, kukana ne ya kuma tsananta ina durk'ushe agurin ruwa yana sauka a jikina.

Birki yaja ya tsaya ya kifa kansa jikin stiarine in motar yayi kukansa me isarsa, zuciyarsa tanai masa k'una tana tafar fasa, watakan shi so ake aga rayuwarsa gaba d'aya ta lalace, me yayi musu ne da suke son illata mishi rayuwa? Duk yarda suka so su durk'usar da shi idan hakan baya cikin littafin K'ADDARARSA hakan bazai tab'a yuyuwa ba,duk me son ganin d'an wani ya lalace to tabbas sai dai yaga nasa ya lalace, tun yana yaro aka so maida rayuwarsa abin kwatance Allah baiyi hakan ba sai bayan da ya kammala karatunsa, tun k'uruciyarsu Harris ne ya taso da rashin ji har kawo yanzu ba'a rasa shi da shaye² da neman mata amma mahaifiyarshi bata sani ba ita burinta kawai ta lalata tawa rayuwar, sunyi nasarar saka mini shaye² shine suke son yanzu na haikewa yarinyar da rayuwarta take cikin garari me muka yi musu ne suke juya RAYUWARMU kamar abin gare²?
Kuka ya kuma fashewa da shi, zuciyarsa na tuno masa da Hanah yanzu da ya baro ta gurin wa ya barota, wata iriyar rayuwa ya barota tayi? Amanarta fa Momy ta bashi amma yace ta fita daga motarshi, ko da yake zuciyarsa ce tayi zafi baya son kowa ya kasance kusa da shi idan ya kasance cikin wannan yanayin, ribas yayi yai kwana da motarsa ya fisgeta da gudun tsiya.

A durk'ushen ya sameni ruwa yayi mini dukan tsiya, k'arfina gaba d'aya k'are, hon yayi mini ina jinsa na share don wani mugun haushin sa naji ina ji, na tabbata babu me zuwa gurinnan idan ba shi ba, hanyar gaba d'aya sahu ya d'auke mata.

Baya son ruwa ya tab'a shi amma haka ya bud'e motar ya fito domin wani mugun tausayina yaji ya kama shi.
"Hanan taso mu tafi kinga ruwa yana ta dukana. ”
Banza nai masa a raina ina.
'To ni da ruwan ya saukko a jikina har yake neman d'aukewa fa, ai wallahi kaima sai ya tab'aka'.
Ganin nayi masa shiru kuma gashi ruwa sai dukansa yake, durk'usowa yayi ya d'agoni daga durk'uson da nake cike da tsoratar ko lafiya?
"Hanan me ya sameki? ”
Ku jimu da d'an rainin hankali ya tafi ya barni ruwa ya k'are mini duka amma yake tambayata wai lafiya, rintse idona nayi hawaye suka satato bisa kuncina, d'aukata yayi cak tausayina yana kuma kwaranya cikin zuciyarsa, ya nufi mota da ni, da k'afa ya tura murfin motar ya sakani ciki sannan ya zaga ya shiga, juyowa yayi yana kallona, na kwanta lamo ina ta rawar d'ari kau da kansa gefe yayi ya tashi motar muka tafi.
Bakin wani camist ya gangara yayi parking, juyowa yayi ya kuma ganina har lokacin ina rawar d'ari, fita yayi ya shiga camist din can sai gashi da ledoji da alamun magun guna ya siyo, kallona yayi muka had'a ido nayi saurin kawar da kaina, idonsa yayi jajir sun kumbura, wani irin tausayinsa naji a can k'asan zzuciyata, jan motar yayi a hankula abin ya bani mamaki don bai tab'a jan mota a hankula ba sai dai ya fisgeta da gudun gaske.
"Idan nace zamu d'auki hanyar Gombe a yanzu zamui dare tunda gashi a yanzu shirin kiran sallar magariba ake, bari mu kama Hotel gobe da safe idan Allah yayi mana yawan rai sai mu d'auki hanya.”
Banyi magana ba shima kuma bai damu da sai nayi maganar ba ya maida hankali kan tuk'insa.

Gari har ya fara duhu muka isa Fishma Hotel, d'aki ciki da falo ya kama mana yasa aka d'aukko mana jakar kayanmu, shi ya shige ciki ni kuma na zauna a falo, yana shiga toilet ya fad'a ya had'a ruwa me zafi ya shiga ciki, ya jima a ciki sannan yayi wanka ya fito yana jin hancinsa yana neman toshewa saboda ruwan da ya d'an dakesa, jallabiya ya saka, ya lek'oni don yaji alamun ban motsa ba, d'ago da kaina nayi muka had'a ido.
"Sai ance miki ki raba kanki da wannan kayan? ”
Cike da son yin kuka nace.
"To ai banga toilet ba ”
Wani labule naga ya d'aga mini sai ga wata k'ofa ta bayyana, sakin labulen yayi ya juya ciki bai magana ba.

Ruwa na had'a me zafin gaske na gaggasa jikina da shi, na d'auro auwala na fito, sauri nayi na zira doguwar riga don kar ya fito, duk da bai zama lallai ya fito ba, na saka hijabi na tada salla, had'e da isha'i nayi don mukutarinta ya shiga, bayan na Idar yunwa tana ta sakulata naji ana nocking, ji nayi bazan iya tashi ba in na tashi juwa zata iya kayar da ni sai shine ya fito yazo ya bud'e, abincin da yayi order ne aka kawo, ansa yayi ya rufe k'ofar, leda d'aya ya ajiye mini ya shiga ciki da d'aya, yana ajiye mini na bud'e na hau ci don wata mitsiyaciyar yunwa nake ji, k'irjina har amsawa yake, tas na cinye na sha ruwa, ban sha lemon ba don bai cika damu na ba.

"Zaki k'ara abincin ne? ”
Banji fitowarsa ba sai muryarshi naji, k'asa nayi da kaina don wata iriyar kunyarsa naji ta kamani, nace."A'a”
Magun guna ya b'allo ya bani na sha, sannan naga yana had'a allura.
"D'aura zani kizo na miki allura saboda gudun zazzab'i.”

Rau² nayi da idona, amma fuskarsa sam babu alamun wasa cikinta, zanin na d'auka na shiga ciki na d'aura na fito a d'ad'are, d'agowa yayi ya kalleni don ya gama had'a allurar ni yake jira.
"Juya” Yace dani, rau² na kuma yi da ido don ina mugun tsoron Allura, da dai yaga bani da alamar juyawa sai yasa hannu ya fisgoni na fad'o jikinsa, da kansa ya d'aga rigar tawa ina ta faman mutsu ² ya zame zanin kad'an,ya kuma matseni jikinsa sannan ya tsikara mini allurar, ruk'un k'umeshi nayi na saki k'ara kad'an.
"Sauka jikina ki shiga ciki ki kwanta, ki ta lailaya allurar ”

Cike da kunya na sauka jikinsa na nufi hanyar d'akin sai ji nayi yace.
"Ki sakawa k'ofar key ”

Kwanciya yayi jikin kujera ya lumshe idonsa, d'ora hannunsa yayi saitin zuciyarsa da take masa mugun ciwo sosai, kalaman da Daddy ya jejjefesa yake

Please Login or Register in order to submit comment