Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abu zan gaya mata ba,tambayarta kawai zanyi, na ma yarda kisa wayar a speaker.”

"Tom shikenan bara na kai mata. ” ta kashe wayar ta nufi d'akin Hanah.


Mumushi yayi a ransa yace.

"Lallai na yarda mata k'aramar k'wak'walwa ce da su, banda haka ta ya za'ayi Subai'ah ta yarda zan iya daina son Hanah? Soyayyar Hanah da ita aka halicci zuciyata na kuma tabbata da ita zan koma ga mahaliccina.




*****
Bata da wani aikin yi in ba bacci ba, yanzunma bacci takeyi.
Mafarkin Hamid take yi, dama kuma da tunaninshi ta kwanta.
Wai ya taho da gudu ya bud'e mata hannaye, yana kiran sunanta, da gudu itama ta nufosa, yana gudu tana gudu, saura kad'an ta k'arasa ga faffad'an k'irjinsa da take son yin masauki a nan, wani abu kamar iska yazo yayi sama da shi, ya lullub'a masa wani farin yadi kamar likkafani, kamar daga sama taji muryar Subai'ah tana tashinta, da salati a bakinta ta mik'e zufa tana keto mata ta koina.

Mik'a mata wayar Suby tayi, don a lokacin har ya sake kira, ita kuma ta manta ba tasa a hand's free ba, amma tana tsaye a kanta.

"Hello My Hanah”

"Na'am Yaya Hamid” Ta fashe da kukan da tak'e mak'alewa tun d'azu ”

"I love u Hanah, ina sonki sosai, ki daina kuka, ranar farin ciki tana nan zuwa, ranar da zan sanyaki dariya, dimples d'inki sui ta lob'awa ina jin dad'i.”

Dariya tayi, hakanne ya ankarar da Suby, kafin ta fisge wayar tace masa.

"I love u two Yaya Hamid” Sai ji tayi an fisge wayar, shikuma yaji an kashe, murmushi yayi, ko babu komai nayi amfani dake na samu abinda ya kwantar min da hankali.


Mari ta wanke ta da shi, tsabar takaicin yaudarar da Hamid yayi mata, da gudu ta fice daga d'akin tana kuka, itama Hanah kukan ta fashe da shi, daga bisani taje ta d'auro auwala, ta kalli gabas, tana kaiwa Allah kukanta.






____________________
Wasu mak'udan kud'ine Abba ya shigo da su wanda shi kansa bai san iyakarsu ba, kuma a gobe ne za'a karb'i kud'in daga hannunshi, Ammah ya bawa ta saka masa a siff ta kulle, babu wanda ya san da zaman kud'in a gidan, daga shi sai Amma.


Washe gari ko da Amma taje d'aukar kud'i, sai kud'i suka ce d'aukeni inda kika ajiye, kallon kallo akai tsakanin Abba da Amma, d'akin Hanah dirrect suka nufa suna huci, tana toilet lokacin da suka shiga, idon Amma ne ya fad'a kan wani key ajiye akan mudubi, iri d'aya ne sak da na sif d'inta, d'auka tayi tana nunawa Abba.
"Ka gani ko” Girgid'a kai kawai yayi, ya kasa magana, a lokacin ita kuma ta fito daga bayi, kallonsu tayi tana tambayarsu lafiya, Abba sai cewa yayi.

"Lafiyar kutumar ubanki, fito mun da kud'in mutane.”

"Wani kud'i Abba ”

Marin da ya kifa mata shine ya zamto amsarta, ya buga kanta da bango.
"Billahil lazi ki fitomun da kud'innan don zan iya kasheki a kansu.”


Cikin kuka tace.
"Wallahi Abba bansan wani kud'i kake magana a kaiba, ni tashina kenan ma na shiga wanka. ”

"Kar ki raina mana hankali, ga key d'in sif d'ita na gani kan mudubinki ya akayi yazo nan?”

"Wallahi Amma nima ban san da zamanshi ba sai yanzu.”

"Sharri za'ai miki kenan?”
Sai ji kike kau ta d'auketa da mari.

Sai da sukai mata duka, suka farfasa mata jiki, sannan ya kira 'yan sanda suka tafi da ita........
[12/10, 10:15] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


____________________
*EPISODE TEN*
Sai da suka birkita gaba d'aya d'akin nata basu ga komi ba, hatta toilet d'inta sai da suka bincika babu abinda suka samu.

Gaba d'aya Abba ya rud'e ya susuce, ya fita hayyacinshi, ya rasa inda zai tsoma ransa yaji dad'i, gashi sai kiran wayarsa ake tun d'azu akan shi ake jira ya kaho kud'in, amsa kawai yake basu da gashinan k'arasowa.

Kansa gaba d'aya ya kulle, yama rasa wani tunani zaiyi, zufa ko ta ina tana kwararo masa, sintiri kawai yake yana shafa kansa.

"Wayyo, wannan yarinya ta jefani cikin bala'i, yanzu ya zanyi da kud'in mutane? Kud'in dukkaninsu sunma ninka rabin dukiyata, shikenan asara ta hauni, Hannatu ta illata mini rayuwa, wallahi muddun bata fitomun da kud'innan ba sai na saka an gana mata azabar da bata tab'a gani ba a rayuwarta, inma zaiyi sanadiyar mutuwarta ita ta sani.” Sai ga hawaye shar yana bin kuncin Abba. ”

"Cikin lallashi Amma take kwantar masa da hankali, tana nuna masa insha Allah in taji matsi zata fad'i inda takai kud'in.

Kamar sabon kamu ya mik'e ya shige d'akinsa, ya birkita d'akin, duk wata kadara tasa sai da ya kwashe ta, sannan ya afka d'akin Amma a nan bai samu komai ba, d'akin Subai'ah ma bai samu komi ba, a d'akin Ammi ne duk wani gwala gwale nata sai da ya kwashe, tana zaune tana kallonsa k'ala bata cemasa ba.

"Zan tafi Abuja, zuwa gobe insha Allah zan daho, zan har had'o musu kud'insu, don kud'ina na nan ba sukai ko kwatan kud'in ba, na kashe wayata, kuma ku kulle gidan ku shiga gidan su Hamid, don na san tabbas sai anzo nemana. ” Yana kaiwa nan yasa kai ya fice, ya shiga motarsa ya tafi.


Yana fita, suma suka fice, suka kulle gidan, suka shiga gidan su Hamid.


A hanyar Abujan kidnerpers suka kama Abba, suka tafi da shi.






*****
Kwanan Hanah uku a hannun police Abba baibi baya ba, don haka suka tarkata sukayi prison da ita, domin k'aidar cell kwana ukune, shiyasa suka mik'ata prison ajiya.

Tsabar kukan da takeyi idanuwanta gaba d'aya sun kumbura sumtum, zagayensu sunyi jajur, har takai yanzu hawayen baya zuba, sai dai tayi na zuci, idon ya bushe k'ark'af.

Taga rayuwa iri² a cikin gidan prison, mutane ga sunan kala² kowa da k'addarar da ta kaho sa, wani da hak'k'insa, wani babu hak'k'insa, ga sunan dai, wasu zaman gidanma ya zame musu jiki, wasu kuma sababbin kahowa ne kamar ita, abinda ta lura da shi, kusan rabin gidan duk ba da hak'k'insu aka kahosu ba, yawanci duk k'aharu ne, ga masu aikata laifin a waje ba'a kama su, sai dai wa'yanda basu jiba basu gani ba, indai akace kana da kud'i kuma kana da hanya duk mugun aikin da ka aikata, to zaka fita salin alin, gaskiya k'asarmu akwai gyara sosai.

(Allah ya Ubangiji, duk wanda bashi da hakk'i aka kaishi wannan gida mai muni, Allah ka fitar da shi, ka wankeshi ka bi mishi hak'k'insa duniya da lahira, Allah ka tona asirin wa'yanda sukayi masa sharrin, ya Allah kar ka barsu ka d'ora musu azabar da ta huce wacce suka jefashi, Allah duk wani mugun d'an sanda, me karb'ar cin hanci, me yiwa mutum sharrin da baiji ba bai gani ba, Allah Ubangiji ka kaho mana k'arshensu, ka tagaiyara su, Amin ya Allah, Allah ka tausayawa wa'yannan bayi naka ka fiddasu daga wannan gida, wanda babu dad'in ji bare Ambato, ko mak'iyina bana fatan ya shiga gidan nan bare kuma masoyina, Allah ka kaho mana k'arshen mugaye ka rabamu da mummunar k'addara Amin.)


Wani bak'in tuwo ne a gabanta, da wata iriyar miya, tafashi kad'i, tsululu take, kamar ruwan da aka wanke kai, a hankali take bin mutanen d'akin da kallo, wasu sun d'aukko dunk'ule suna barbad'awa a miyar, don miyar babu d'and'ano, dunk'ule shine ya zamewa d'an prison nama, don da ki basu nama gara ki basu dunk'ule, wasu kuma haka suke ci, wa'yanda basu da dunk'ulen kenan, wasu kuma kwaki suka jik'a, wasu kuma indomie, wasu kuma abinci ne aka kaho musu daga gidan su, a hankali ta maida kanta kan cinya tana kukan zuci, a hankali wata daga ciki ta mik'e ta isa inda take, dafata tayi tace.
"Sai fa kinyi hak'uri, muma duk a haka muka saba, idan har aka kahoka gidan nan dole sai kayi hak'uri, kin ganni nan, Makah zamu tafi ni da k'awata, ashe ta saka mun coken a cikin kayana ban sani ba, mahaifina babu dukiyar da bai fitar ba don na fita daga gidannan, amma har yau ban fita ba, Allah bai yanke ba, kema na san bazai huce sharri ba, don haka sai kinyi hak'uri, mui ta kaiwa Allah kukanmu, har zuwa sanda lokacin fitarmu zaizo.”

Tuwon ta janye daga gabanta, ta mik'a mata abincin da aka kaho mata daga gidansu, tana ta lallashinta akan taci.


***
Khausar itace ta zamo me kula da Hanah, bata bari taci abincin gidan bare ruwan gidan, yadda bata ci itama ta hana ta taci, abincin da ake kaho mata shi suke had'uwa suci, kayan sawama nata take sakawa.


Tun ana kwana d'aya har zuwa sati su Amma basu ga k'eyar Abba ba, sannan babu Kira, bare suji halin da ake ciki, su kuma in sun kira swhich up, hankalinsu yayi mugu mugun tashi, gashi har yanzu suna cikin gidan su Hamid, ba shiga ba fita, domin ance wasu mutane suna ta zuwa suna shawagi a k'ofar gidan, da gani Abba ake nema.
Ammi gaba d'aya hankalinta yana kan Hanah, ko wani hali take ciki itama ba ta sani ba, police citation d'in da aka kaita ma ba sani tayi ba, gashi kuma babu damar fita, kar su fita a cafkesu ace sai sun fad'i inda mijinsu yake.




*****
A kwana biyun nan gaba d'aya Rumanah mafarkin Hanah takeyi, wai tana cikin mahuyacin hali, tana kuka tana buk'atar taimakonta, kuma kwana biyu daga ita har Subai'ah babu wanda yake zuwa makaranta, hakanne yasa washe gari ta shirya ta nufi gidansu, ko da taje ta tadda gidan a kulle, har zata juyo wata zuciyar ta yanke mata ta shiga gidan su Hamid.

Ko da ta shiga gidan, babu Wanda ya kulata, Amma sai huci take yi, Ammi ce ta salallab'a ta biyota har soro ta zayyana mata abinda ya faru, tana kuka, tace.
"Idan har kin gano inda Hanah take, rok'on da zan miki kar ki barta ta daho gidannan, domin basa k'aunarta burinsu kawai suga bayanta, in lokaci yayi ni da kaina zan nemi inda take, na barta Amana a hannunki. ”


Kasa cewa komi Rumana tayi, sai kuka, ta fice daga gidan, har taje gida kukan take yi.

Kanta gaba d'aya ya kulle, ta rasa ta ina zata fara neman Hanah, dole sai da mataimaki, baza ta iya ita kad'ai ba, gashi Sadiq baya gari.
Hisham ta kira, tana kuka ta zayyana masa komi, shima yaji tausayinta, yace bari ya had'ata da Haisam.

Haisam ko baya son abu, Hisham ya nemi yayi masa sai yayi, tun suna yara a haka suka taso, don haka ba musu ya amince, suka fara neman police sitation d'in da Hanah take, sunci uwar wuya kafin su gano inda case d'in nata yake.
Kud'i Haisam ya sakar musu, nan da nan suka rubuta takadda aka kai can gidan prison d'in.

A washe garin ranar aka saki Hanah, rungume juna sukayi da Rumanah suna kuka.

"Wai me kikaiwa mutanan nanne basa k'aunar rayuwarki, shin anya kwa Abba mahaifinki ne? Yau na rok'eki dan Allah ki bani labarin gidanku, nasan irin sark'ak'iyar da ke cikinsa,wannan wata iriyar rayuwa ce. Ko mu da matar uba ta rusa mana farin cikinmu bamu shiga rayuwa irin taki ba. ”

"Zan baki labari Rumana, amma ina buk'atar nutsuwa kafin haka.”......
[12/10, 14:45] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


____________________
*EPISODE ElEVEN*
Haisam tsayawa yayi yana kallonsu, zuwa can kuma ya janye idonshi daga kansu, janyota tayi zuwa bakin motar, ta bud'e mata gidan gaba, tace ta shiga, nok'e kafad'a tayi, tayi mata rad'a a kunne.
"Wari nake yi ”

"Yasin ba wani wari da kike, sharrinki ne kawai ”

Harara ta zabga mata, saboda gani tayi mata rad'a don kar aji, itakuma ta fallasa, dariya ta fashe da ita.
"Oh sorry, yasin na manta. ”

Duka su biyun suka turmutsu gidan gaba, ke kice babu gurin zamane, yana kallonsu kanzil bai cemusu ba yaja motar yayi gaba.

"Ni kad'ai zaka sauke gida, Baffa ne yake jirana tun d'azu, kaga ba damar na tafi da ita gidanmu, tunda nima ba gashin kaina nake ciba, don Allah ka tafi da ita gurin Momy, kace zuwa dare ko gobe zanzo na mata bayani. ”

Kai ya gyad'a, zuciyarsa tana kai kaho, wai shin me ke bibiyar rayuwar yarinyar nan ne? zuciyarsa na san sanin hakan, amma bazai iya tambaya ba, saboda ba shirginsa bane.

Kiran Hisham ne ya shigo wayar Haisam, peking yayi ya ajiyeta a saitinsa, saboda vidio call ne.
"Hello, ya ya an dace ne?.”

"Eh yanzuma haka muna hanyar gida, yaushe zaka dawo ne, maraicin fa yayi min yawa sosai. ”

"Nan da jibi zan dawo insha Allah, na tsaya yiwa Rumanah siyayya ne, yau ina jin bikin saura kwana biyar. ”

"Ok, kun fasa bari tayi candyn kenan?”

"Tuk'i kake, idan kun k'arasa na kiraka, sai mu k'arasa maganar, sai anjima. ”

"Ok, tom, sai anjiman. ”

K'it, suka ajiye layin, dai² lokacin suka iso k'ofar gidan su Rumanah, sai da Hanah ta fita, sannan Rumanan ta fita, saboda Hanan ce a farko, bayan Hanan ta koma ciki, Rumanan ta rufe mata k'ofo.
"Toh, Habibati, sai nazo, kar ki damu, nasan Momy zata kula da ke. ”

"Tom shikenan, na gode Sahibati. ”

Jan motar ya fara yi a hankula, har yabar harabar anguwar.


Ko da suka isa gida, a harabar gidan suka tadda Hindu da Harris, wani tuk'uk'i ne ya tsayawa Hindu a mak'ogaro, yayin da Harris yayi wani mugun murmushi, kallon sama da k'asa take wa Hanah, me ma'anar da me kika fini?

Atamfa ce a jikinta, ba wata sabuwa bace, sai Hijabi iya guiwa, kayan Khausar ne ta saka, Haisam ko kallon gurin da suke baiyiba yasa kai ciki, yanda bai kalli gun da suke ba, haka itama Hanah ba ta kalli gurinba tabi bayanshi, suna barin gurin Harris ya juyo da kallonshi kan Hindu.

"Yau dai kin gasgata abinda nake gaya miki da idonki ko? Ki kalli ma tsabar ya raina kowa na gidan nan, har cikin gida ya shigo da karuwa, kuma ya rasa wacce zai kula, sai wannan wacce bata waye ba. ”

"Mtssss” Hindu taja tsaki, don ta kasa magana, mik'ewa tayi ta shiga ciki, tana faman kumbura fuska kamar fanke, mik'ewa yayi shima, yana sakin shu'umin murmushi yabi bayanta.

Suna shiga ciki sashinsa kawai yasa kai, itama ba tayi k'asa a guiwar bin bayanshi ba, muk'ulli yasa ya bud'e d'akinsa ya shige ya turo k'ofar, tsayawa tayi a bakin k'ofar tana yanke shawarar shin ta shiga ko ta tsaya?

Hindu kasa hak'ura tayi tabi bayansu zuwa sashin Haisam, Harris ma yabi bayanta da ya gasgata zargin da yake, a tsaye suka tadda ita, tana ganinsu tayi k'asa da idonta, tana wasa da zoben azurfarta, wanda kyauta ne ga babban masoyinta Hamid, a tsakiyar zoben an saka H².

Gabanta Hindu ta k'arasa, tasa hannu ta d'ago kanta, tana jifanta da wani shegen kallo.
"Wace ce ke, meye had'inki da shi?”

Shiru tayi, ta kasa furta ko da Kalma d'aya, wata iriyar tsawa suka daka mata, nan da nan jikinta ya hau kyarma, hawaye ya fara cika idonta, ba ta san ta yaya zata yi musu bayani ba, wani irin duka k'irjinta yake, wannan shine an rabu da Bukhar an haifi Habu, wani gidan masifaffun aka kahota kuma?

Tsawar Haisam yaji, ya mik'e ya bud'e k'ofar ya fito, jin k'arar bud'e k'ofarne yasa su d'auke idonsu daga kan Hanah suka maida shi kan sa, yana tsaye yana jifansu da wani irin kallo, hannu yasa ya fisgo Hanah gabanshi, zuba mata ido yayi yana kallonta, karo na farko kenan da ya tsaya ya kalli fuskarta sosai, hakanma yayi ne da gayya, idonta a rintse yake hawaye na d'iga ta gashin idonta, d'auke idonshi yayi daga kanta ya maida kansu.
"Meye dalilinku na jin sanin ita wacece? Ai ba sai kunji ba, duk abunda ranku ya gaya muku hakanne.” Daga haka yaja hannunta zuwa ciki, ya rufe k'ofar, k'wafa dukkaninsu sukayi suka juya cikin gida.

Suna shiga ciki ya saki hannunta ya koma kan kujera ya zauna, dafe kansa yayi yana busar da iska ta bakinsa.
"Dole na takawa Harris birki, yana shigarmin rayuwa da yawa. ”

Janyo cup d'in dake gabansa yayi had'e da bottle d'in giya, ya d'aga zai tsiyaya yaji ana buga k'ofar, murya a kausashe yace.
"Waye ”

"Ban sani ba. ”

Yaji muryar Momy ta fad'a.

D'an murmushi ya saki, yace.
"Shigo a bud'e take. ”

"Murd'a k'ofar tayi ta shiga, Hindu ta biyo bayanta. ”

"Wata yarinya ka shigo da ita gidan nan?”

Me makwan ya bata amsa, sai ya kalli Hindu ya daka mata tsawa.
"Ficemun daga d'aki. ”

Jiki na rawa ta fice daga d'akin, yabi bayanta da harara a hankali yaja tsaki.
"Mtsss, mutum bai damu da damuwarku ba, amma duk kunbi kun shiga tasa rayuwar.”

Juyowa Momy tayi cike da masifa, sai a sannan ta lura da Hanah, tun shigowarsu d'akin tana tsaye jikin bango, tana kuka k'asa².

Mai da dubanta tayi kan Haisam.
"Wace ita. ”

Kallon Hanah yayi, yace.
"Kee yimata bayani. ”

"K'asa tayi da kanta, tayi shiru, a ranta tana.
"Kijimu da d'an rainin hankali, ni zan mata bayani, to nace mata me? Naga dai shi Rumana ta bawa sak'on.”

Daka mata tsawa yayi.
"Ba dake nake magana ba?. ”

Nan da nan ruwan hawaye ya kuma cika idonta, ran Momy ne ya kuma b'aci.

"Haisam, wai wasa nake da kai ne, ita ta kawo kanta ko kuma kai ka kahota har da zata mun bayani? ”

"Sorry Momy, Rumanah ce tace na kawo miki ita, zuwa anjima zata zo tayi miki bayani. ”

B'oyayyar ajiyar zuciya Momy ta saki, tace.
"To shine tsabar ka raina mutane ana tambayarka kayi shiru, gashinan ka kuma jaza mana wata maganar, maimakon ka fara kawota gurin nawa shine kayo nan da ita.

"Wallahi Momy kaina ne ya kulle tunda na shigo gidannan, ji nayi kawai shegiyar abarcan nake son sha, na d'auko kenan zan sha naji hayaniyarsu da Hindu, shine na fito na jahota d'aki, yanda zasu fi fad'e da kyau na kawo karuwa d'akina, don na san bazai wuce hakan ba. ”

"Baka gudun magana Haisam kai dai, zo ka shige mu tafi, muje kema, kinji yarinya. ”

Kallonta yayi, ya marai raice fuska..
"Daurewa zakayi kaji, in ba haka kakeyi ba baza ka rabu da ita ba. ”

Ranshi be so hakanba, ya shige yana tuturo baki, momy kuma ta d'auke giyar taje ta zubar, sannan taja hannun Hanah suka tafi.

Wanka Hanah tacewa Momy tana son yi, don haka sai ta kaita d'akinta, ta nuna mata band'aki ta fito, abinci taje ta zubowa Haisam, ta bashi da kanta, daga bisani ya kwantar da kansa kan cinyarta, tana shafa kansa har bacci ya sureshi, Rumanah ce tayi sallama ta shigo hannunta nik'i² da kaya, gaisawa sukayi da Momy, bayan sun gaisa Momy tace.
"Shiga tana d'akina ”

Lokacin da ta shiga, a lokacin ta fito daga wankan tana goggoge jiki, murmushi suka sakarwa juna, Rumanah ta ajiye kayan hannunta.

"Kayana ne na 'yebo miki kafin muje a siyo naki, gashinan sai ki zab'i d'aya ki saka ina jiranki a falo. ”

Ba ta jira amsarta ba, ta fice, domin ta samu damar shiryawa.


Bayan Hanah ta shirya taci abinci, ta huta, Rumanah tace.
"Ina saura ranki Habibati, ki warware mana komi a gaban Momy. ”

Murmushi Hanah ta saki me ciwo.

"Na san idan nace miki, Ammi itace mahaifiyata, zaki mamaki, to Ammi itace wacce tayi sanadiyar zuwana duniya, an raba soyayyar dake tsakaninmu tun ina yarinya, domin a cinma wani buri.
Asalin sunan Ammi Umaimah...........


Rabin jiki kice yayi hak'uri da wannan babu chargi🤩 dama Ummee tace mu kanawa bamu samun huta.

Sannan kuma babu wanda naji ya tausayawa Abba, domin har yanzu yana hannun kidnapers🤩🤩🤩🤩
[12/10, 14:48] HAJIYA DUDUWA MEKAN BARI🤣: *BEBE'ARTH*


*K'ADDARAR RAYUWARMU*

*2019*
*Cweat novel*

® *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Sadaukarwa ga Suhanah (Rabin jiki)

Jinjina ga Aunty Maryama (Kwaise)


__________________
*EPISODE TWELVE*

"Zan baku labarin gidanmu kamar yadda naji daga bakin Yaya Hamid, aduk fad'in duniyar ne daga shi sai Rumanah, su kad'aine nake ganin soyayyata da tausayina a idanunsu, bacin su babu wanda ya soni, ya nuna mini k'auna, sai k'iyayya da kyara.

Asalin sunan Abba D'ahiru, kamar yarda na gaya muku asalin sunan Ammi Umaimah.

Umaimah haifaffiyar garin Gombe ce, D'ahiru ne yaje wani aiki Gombe ya taho da ita, Yaya Hamid yace, har yau basuga wani d'aya daga cikin dangin Umaima sunzo ba, kuma itama ba taje ba, ba'a san meye silar rabuwarta da danginta ba, ita ba ta fad'a ba haka zalika D'ahirunma bai fad'a ba.

Ko da yazo da ita garin Kano, sai ya kaita ajiya gurin yayar abokinsa Muhammad, me suna Hannatu, domin baya da inda zai ajiyeta, kuma ba aure sukai ba, amma dai suna tsananin son junan su, bari yayi sai ya kama aiki tukun, sai suyi aure.
abinda yasa yakaita ajiya gurin Hannatu, saboda Mahaifinsa ne, don zai tuhumi wace ce ita, kuma sannan ba zai barshi ya aureta ba, idan kwa ya barta gidan Hannatu in ya tashi auranta sai yace 'yar uwar mijin Hannatu ce .

Muhammad, D'ahiru da Sulaiman, abokanai ne tun suna yara har wa girmansu, mahaifan su Muhammad sun rasu tun Muhammad na yaro, daga shi sai Hannatu suka haifa, hakanne yasa ya taso a hannun Hannatu, domin 'yan uwan mahaifan nasu duk suna Damaturu.

Mahaifin nasu ya bar musu dukiya me tarin yawa, sannan kuma Hannatu ma shahararran me kud'i take aure, sai dai bata tab'a haihuwa ba, kuma a haka yake zaune da ita domin yana matuk'ar sonta.

Shi Sulaiman da D'ahiru mahaifan su suna nan a raye, kuma duk a cikin garin kano suke.

Sulaiman duk ciki ya riga su yin aure, ya auri matarsa Rayya, shekarar Rayya d'aya da aure ta haifi d'anta na miji, aka saka masa suna Abdul Munaf, suke kiranshi da Hamid, daga nan kuma haihuwa ta bud'e mata.



******
Umaimah tana zaune gidan Aunty Hannatu lafiya lau, tana matuk'ar jin da'din zaman gidan ainun, D'ahiru kusan tarewa yayi a gidan, ko da yaushe suna manne suna gurzar soyayyarsu.

A duk sailin da Muhammad yaga Umaimah sai ya dinga jin gabansa yana fad'uwa, zuciyarsa tana wani irin bugu tana yamutsawa, yayi tunani don ya gane dalilin da yasa hakan yake faruwa, amma ya kasa, don haka sai ya nisanci had'uwa da ita.

Ga b'angaran Umaimah ma hakanne, a duk sanda taga Muhammad tana jin wani sabon yanayi yana kamata, ga wani shauk'i da takeji, zuciyarta ta dinga wani zillo tanai mata tsalle, ga wani kwarjini da yake mata, fuskarshi tana bada wani annuri.

Muhammad kyakkyawa ne sosai, yana da kyan haiba da kwarjini, don ya ninka D'ahiru sau dubu a kyahun fuska da na hali, D'ahiru da Sulaiman sunfi abokan taka, saboda halinsu yafi zuwa d'aya.

Ana cikin haka D'ahiru yayi musu sallama zai tafi service a Lagos, bayan dawo warsa daga Lagos kuma zai fara maganar auransu, ya k'ara jadda dawa Muhammad ga amanarsa nan ya kula masa da ita, kar ya barta ta kula ko wani namiji don zaiyi kusan shekara d'aya da rabi.

Bayan tafiyar D'ahiru, Muhammad da Umaimah suka afka soyayyar juna, sunyi k'ok'arin kaucewa hakan amma ina, abinda Allah ya k'addara baka isa ka

Please Login or Register in order to submit comment