Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saida Fawzan ya samu bacci.

Shima wayoyinshi yaje ya dauko daga dakinshi ya dawo dakin Fawzan din ya kwanta. Dan ko zai samu bacci sai da sanin koda wani abin zai faru da Fawzan cikin daren zai iya sani. Yana kusa dashi, shida Aroob ne kadai suke Asthmatic, saboda Nuri na dashi, amman ya manta lokacin karshe da ya tasar mata. Su kam ko ya ransu ya baci zasu iya samun matsala, musamman Fawzan.

Lambar Muneeb ya lalubo yana tura mishi saqo

'Idan ta sake kuka a kanka zan manta abokantakar dake tsakanin mu'

Amsa ya dawo mishi da ita

'Idan bakai wani abu ba, hawayen ta zasu zuba ne sanadin hakan Rafiq. Zuciyarta nada muhimmanci a wajena, tarwatsewar ta na hannun ka'

Jefar da wayar yayi, badan kujerar data fada kai ba data fashe. Banda ciwon kai babu abinda sakon Muneeb ya kara mishi. Kwanciya yai ya rufe idanuwanshi yana neman gafarar Ubangiji, saboda akwai samun sauki a cikin hakan, akwai kananun zunuban da kake tarawa batare da sanninka ba, in Allah ya yafe maka su hakan zai iya zama sanadin samun saukinka, hakan ya ci gaba dayi har bacci ya dauke shi.

*

Washe gari sam bai samu ya zauna ba. Tunda ya duba Zafira yaga lafiyarta kalau ya fita. Saboda akwai kayan abinci da zasu rarraba gidajen matan da suka rasa mazajen su na kananan hukumomi dake nan garin Abuja karkashin foundation din Nuri. Daddy yace yana bukatar yan Jarida su ganshi a wajen tunda shi bazai samu zuwa ba.

Gabaki daya zuciyarshi bata mishi dadi, da masu daukar hotuna zasu zuqo fuskarshi kilan da mutane da yawa sun fahimci akwai rashin jin dadi cike a kasan murmushin shi. Yana rabawa mabuqata abinci, yana kuma shiga asibitoci yakai taimako da kudin aljihunshi, batare da sanin kowa ba. Wannan dinma bawai bayason yi bane ba, yasan dai babu lada a cikinshi.

Saboda bawai anayi bane dan Allah, anayine dan idan duniya, anayi ne dan neman zabe, yana daya daga cikin yaqin neman zabe, ya kuma tsani duk wani abu dayake da alaqa da siyasa duk da kasancewarshi a tsakiyarta. Komai nata bai mishi ba. Sunayi yana fakar idanuwan mutane yana duba agogon shi. Yana bukatar zuwa Airport kamun karfe hudu na yamma.

Dan haka biyu da rabi dai-dai yabar komai a hannuwan wakilan Daddy yaja motarshi ya koma cikin garin Abuja. Ranshi na kara baci da Sallah daya rasa saboda aikin da babu ladar komai a cikin shi. Bai shiga gida ba sai uku da kusan kwata. A gaggauce ya sake watsa ruwa, danma ya hada jakarshi kamun ya fita.

Sallah ya samu yayi yana daukar jakar ya fito. Fawzan ya samu a falo yana jiranshi.

"Nuri fa?"

Ya tambaya.

"Tahau sama yanzun..."

Fawzan din ya bashi amsa yana dubar agogo

"Yaya zamu makara..."

"Nasani..."

Ya fadi yana mikama Fawzan din jakarshi, da gudu ya nufi kafar benen yana hada bibbiyu lokaci daya.

"Nuri....."

Yake kwala mata kira tun kamun ya karasa. Fitowa tayi cikin hanzari. Numfashi Rafiq yake mayarwa. Ya karasa yana sumbatar kuncinta.

"Na tafi... Zamuyi waya..."

Ya karasa yana juyawa.

"Allah ya tsare Rafiq. Ka kula sosai..."

"In shaa Allah"

Ya amsa yana sauka da gudu ya fita zuwa inda Fawzan yake tsaye jikin mota yana jiranshi. Shiga sukai su duka biyun, Fawzan yaja su zuwa Airport. Babu mai magana a cikinsu. Har saida suka karasa Rafiq ya dauki jakarshi zai fita tukunna ya kalli Fawzan da fadin

"Ka kula da ita dan Allah... Ka kula da kanka kuma..."

Kai Fawzan ya jinjina mishi.

"In shaa Allah. Kaima ka kula da kanka"

Batare daya amsa ba ya fice daga motar. Yanajin kamar akwai kuskure a tafiyar tashi. Kamar wani abin zai faru kamun ya dawo. Sai dai ya danne muryar dake mishi wannan radar da tunanin ba wannan karin bane yake jin kamar inya barsu Daddy zai musu wani abin kamun ya dawo.

A masallacin cikin airport din yai Asr. Tukunna ya dawo ya zauna. Yana danna wayarshi dan yaga ko karfe nawa. Text din Naadir ya shigo mishi.

'Yaya na ji ciwo a kafada, jiya akaimun surgery'

Wani yamutsi Rafiq yaji da baisan yanda zai misalta ba. Yanada tabbacin an fadama Daddy. Saboda babu yanda za'ai abu babba haka ya samu Naadir makarantarsu bata kira Daddy ba. Cikin kanshi yake kirga kwanakin daya dauka basuyi magana da Naadir din ba. Dan kar ya taso cikin takurar da suka taso yai tsaye saida Daddy ya fitar dashi England yana gama primary. Bama ya zuwa gida sai karshen shekara sam.

Yana kuma yin wasan kwallon Hockey ne, makarantar naji dashi, dan sunce akwai alamar nasara a tare dashi kan wasan. Hannunshi rawa yake yi lokacin daya kira number din Naadir. Bugu biyu ya daga, muryarshi can kasa

"Naadir..."

"Yaya zan ci gaba da wasa na nan da sati uku"

Naadir ya fadi cikin harshen turanci.

"Hausa Naadir..."

Dariya yayi daga dayan bangaren hakan nasa Rafiq din samun yar nutsuwa.

"Ya jikin ka?"

"Ya ji sauki. Zaka zo kaganni? Daddy yace yana busy bazai zo ba. Ina missing dinku sosai"

Naadir ya fadi. Kai Rafiq ya daga kamar yana ganinshi kamun yace

"Zanje China ne now. Amman zan kokarin gama abinda zanyi acan da wuri in shaa Allah. Then zan biyo in ganka..."

"Okay. Zan jira. Doc ya shigo muyi magana anjima. Love you"

"Love you more. Ka kula sosai"

Rafiq ya fadi yana sauke wayar daga kunnenshi. Ji yake kamar yai tsuntsuwa yaje yaga Naadir din. Amman koma menene zai sauri yaga yagama ya wuce England kamun yaga Naadir din. Yasan yana samun duk kulawar da yake bukata. Amman basa sonshi kamar yanda yake sonshi. In yana wajen hankalin shi zaifi kwanciya.

**

Wayarta ta dauka da niyyar fita daga dakin, jikin ta sanye da riga da zani na atamfa. Sakonni ne har hudu ganin Muneeb ne yasa zuciyarta matsewa a kirjinta. Kan mudubi ta ajiye wayar. Ba zatama bude ba ballantana ya sake dagula mata lissafi da safen nan. Rafiq dazun ya roketa karta saka damuwa a ranta, tabar komai a hannunshi saiya dawo.

Ta kuma yi mishi alkawari zatai iya kokarinta. Ba zata karya alkawarin ta ba. Ficewa tai zuwa babban falon gidan. Aroob ta samu ita kadai tana zaune kan kujera da plate din soyayyen dankali da wainar kwai a hannunta da cokali mai yatsu a ciki. Amman gabaki daya hankalinta nakan india din da take kallo.

Girgiza kai Zafira tayi tana wucewa kitchen din itama. Bawai dan tanajin yunwa ba sai dan jikinta na bukatar wani abu. Anan kitchen din ta hada ruwan shayi, ta kukkurba, tana dan cin dankalin cikin sauri kamun Nuri tazo taganta tana cin abinci a tsaye. Bata iya shanye shayin ba, dan haka ta cika cup din da ruwa ta zubar tana ajiyewa ta fito daga kitchen din.

Bata zauna falon ba ta wuce bangaren Daddy, dan ta gaishe dashi. Kwankwasawa yayi saida ya bata izinin shiga tukunna ta tura dakin da sallamarta daya amsa da fara'a.

"Ina kwana Daddy..."

"Zafira... Kamar kinsan ina nemanki"

Daddy ya fadi a maimakon amsa gaisuwarta. Karasawa tayi cikin falon tana zama a kasa gefen kafafuwan shi.

"Nace bari inzo in gaishe kane daman..."

Ta fadi cikin muryarta mai sanyi.

"Jarabawa an kusa ko?"

"Nan da Sati biyu in shaa Allah Daddy"

Ta amsa da jin dadi a muryarta. Dan ji take kamar wani nauyine zata sauke. Jinjina kai yayi yana gyara zamanshi, a nutse yace

"Kinsan komai da nakeyi akan ku dan shine yafi dacewa ko?"

Cike da rashin fahimta tace

"Nasani..."

"Da yawan lokutta kuna ganin kamar ina takura ku ne. Kuna ganin bana jin ra'ayinku nake yanke muku hukunci. Yayanku naganin farin cikin ku bashi da muhimmanci a wajena..."

Wani abune ya tsaya ma Zafira a makoshi. Haka kawai bata son yanda yanayin muryar Daddy take.

"Ba haka bane Daddy.... Ba haka muke gani ba"

Ta amsa da sauri. Kai Daddy ya girgiza mata, yana ci gaba da magana.

"Ba takura miki nake ba akan wannan. Ina son ki sani yana da matukar muhimmanci a wajena, zan rasa abu da yawa in baki amince ba, a karo na farko ina rokonki daki amince Zafira..."

Idanuwan ta cike suke taf da hawaye. Bata san menene Daddy yake so ta amince akai ba, bata son yanda yake rokonta kamar bai isa da ita ba, yanda yake tausasa murya kamar ba ita bace yar shi. Abin ya mata wani iri, muryarta na rawa tace

"Ka daina dan Allah... Ko menene na amince Daddy, kana da iko zartar da hukuncin da bai saba addini ba akaina..."

Numfashi mai nauyi Daddy ya sauke.

"Ina son ki auri dan gidan Alhaji Yusuf Modibbo ne..."

Takai mintina biyu maganar shi na mata yawo kamun ta samu wajen zama a kwakwalwar ta, ma'anar kalaman shi na zauna mata daram a zuciya. Cikin tashin hankali ta dago idanuwanta tana ware su akan Daddy.

"Auren ki dashi na da muhimmanci a wajena. Karki ce a'a Zafira. Na riga na amsa musu..."

Kai kawai ta iya daga mishi. Saboda jikinta yayi sanyi. Batajin karfi koda nayin magana ne. Kanta kamar an kwashe duk wani abu mai muhimmanci a ciki haka take jinshi. Zuciyarta tayi wani irin fili kamar an share.

"Allah yai miki albarka. Nagode"

Daddy ya karasa da alamar jin dadi a muryarshi. Saida ta dafa kafafuwan Daddy tukunna ta iya mikewa. Runtsa idanuwanta take yi tana bude su cikin sauri dan dishi-dishi take gani, kamun ta samu ta gane hanyar fita daga dakin shi. Dakin Aroob ne farko a bangaren su kamun nata, dan haka nan ta fada kawai.

Numfashi take ja tana mayarwa, tanajin kamar zuciyar ta zata fito waje saboda tashin hankalin da take ji, ta dauka jiya ne karshen tashin hankalin da zata sani a rayuwar ta, sai yanzun ta san jiya bataji komai ba, saboda hawayenta sun zuba. Yanzun nemansu take amman shiru. Kuka take so ta rusa mai sauti ta kasa.

Asalima ta rasa yanda akai ta amsa ma Daddy, bata san me yasa ta amsa mishi ba, dan a yanzun ji take kamar ana zare mata rai saboda tashin hankali, batajin zata kai ranar da zata auri koma wanene Daddy yake son hadata dashi a yanayin da takeji yanzun. Inama zata kai soyayyar Muneeb.

"Muneeb..."

Ta furta can kasan makoshi. Me zata fada mishi. Ta ina zata fada mishi ko kadan batai wani kokari wajen cikar burinsu ba, na minti daya bakinta baiyi rawa wajen amincewa da auren wani bayanshi ba. Jitai an turo kofar dakin, bata ko juya ba.

"Zaf? Lafiya?"

Aroob ta bukata tana zama kasa kusa da Zafira din. Cikin idanuwa ta kalli Aroob hadi da girgiza mata kai. Bata tunanin wani abu zai sake lafiya a tare da ita, komai ciwo yake mata.

"Daddy zai aura mun wani Aroob... Da bakina na amsa zan auri wani..."

Idanuwan Aroob da take jin sun ciko taf da hawaye ta ware kan Zafira cikin tashin hankali.

"A'a dan Allah kar haka ya faru... Kar Daddy yayi haka...."

Aroob ta karasa tana kwantawa jikin Zafira hadi da fashewa da wani irin kuka. Riketa kawai Zafira tayi tana jin yanda take mata kukan da ita ta kasa. Abu dayane takeji a yanzun. Muneeb take son gani, tana son ganin Muneeb a yau din nan, a yanzun ba sai anjima ba.

"Ina son ganin shi yanzun Aroob..."

Ta fadi muryarta a bushe. Dagowa Aroob tayi tana goge fuskarta data soma kumbura, tashi tayi ta dauko wayarta tana mikama Zafira, wani kukan na kwace mata, yama za'ai Daddy yayi haka, wayace mishi ana tarwatsa soyayya irin wannan, waya fada mishi anama so haka. Tasan yasan menene So akan Nuri, me yasa bazai bar Zafira da Muneeb ba.

Text Zafira ta tura ma Muneeb.

'Ka zo gidan mu yanzun. Dan Allah kazo, komai zai iya faruwa in baka zo ba. (zafira)'

Ta aika mishi tana ajiye wayar a gefe. Jikinta Aroob ta sake kwanciya tana ci gaba da kukan da take.

"Zaf ki fadama Nuri... Ki fada mata tai mishi magana..."

Dan murmushi Zafira tayi da bashi da alaqa da nishadi.

"Kin taba ganin yayi abinda bata sani ba?"

Girgiza mata kai Aroob din tayi

"Wannan karin kadai ya kamata Nuri ta zabemu akan Daddy..."

Zafira bata ce komai ba, in taga Muneeb ciwon sa take ji zai rage, haka take ta fadama kanta, yanda takejin duniyar na ruguje mata daga ciki zai dai-dai ta in yazo, inta ganshi komai zaiyi sauki.

"Shisa ya tura Yaya China...abinda Daddy yake so yayi kenan.... Bari in kira Yaya ya dawo...."

Aroob ta fadi tana kai hannu zata dauki wayarta dake gefen Zafira. Da sauri Zafira ta rigata dauka.

"Karki daga mishi hankali. Komai zai jagule in yazo. Kuma bazai hana Daddy yin abinda yai niyya ba. Karki kira shi Aroob, na roqeki karki kirashi..."

Mikewa Aroob tayi tana komawa kan gado ta kwanta. Kukan ta taci gaba dayi, dan tasan abinda ya faru da Zafira shine zai faru da ita nan gaba. Daddy bazai taba bari suyi abinda suke so ba. Son kanshi bazai barsu zaman lafiya ba.

'Ina kofar gidan ku...'

Text din Muneeb ya shigo. Wani irin matsewa zuciyar Zafira tayi.

"Aroob yana kofar gida"

Sakkowa tayi daga kan gadon tana goge fuskarta. Muryarta a dakushe tace

"Ki zagaya bangaren baqi. Bari in shigo dashi ta baya..."

Kai Zafira ta jinjina mata tana mikewa. Aroob kam ficewa tai daga dakin, hijab din Aroob na sallah ta dauka ta zunduma tana ficewa ta nufi bangaren baqin. Falon ta shiga ta zauna, zuciyarta kamar zata fito daga kirjinta saboda dukan da take.

Tanajin takun shigowarshi falon ta dago kanta. Fuskarshi ta fara kallo, tasan shi, tasan shi kamar yanda tasan kanta, idanuwanshi kawai ta kalla tasan akwai damuwa a tattare dashi, da rashin bacci, kallonta yake shima, yanayin shi yana kara bude sababbin ciwuka a zuciyarta daya sata jan numfashin da bata shirya ba.

Ta dauka ganinshi zai sata jin daidaito, sai dai ganin shi na fito da hargitsin da takeji a fili ne. Hannu takai tana dafe zuciyarta da take jin taba gab da fitowa waje.

"Aure za'aimun Love.... Daddy ya amsa su... Na amince... Ka yafemun.....dan Allah ka yafe mun..."

Ta fadi wani irin kuka na kwace mata, ciwon da take ji a ko ina na jikinta na sata sakkowa daga kan kujerar da take zaune. Kallon ta Muneeb yake yi, tun a daren jiya yakejin ya rasa ta, runtse bai iya runtsawa ba, alwala ya daura yana sallah, amman baisan abinda ya dinga karantawa ba.

Yanzun kam da take a gabanshi baisan me yafi tarwatsa mishi zuciya ba, sanin an bayar da ita, ko kuma kukan da takeyi. Bashida lafiya tun jiya. Zazzabi yake mai zafi, dakyar ya iya fitowa yazo yanzun ma ko aiki baije ba.

'Aure za'aimun Love'

Muryarta ta dawo mishi da wani irin yanayi. Kirjinshi ya dafe da hannunshi yana wani irin jan numfashi, saidai ciwon da yakeji yana rarrabuwa ne zuwa ko ina na jikinshi. Kallonta yakeyi, ta cikin idanuwanshi yake so ta fahimci yanda zuciyarshi ke tarwatsewa. Ya kasa yarda ita dashi ne a wannan matsayin, ya kasa yarda kaddara ta bude musu shafin rabuwa da junansu. Muryarshi can kasan makoshi yace

"Bazan iya ba, na kasa tuna yanda rayuwata take batare da soyayyarki ba, wallahi bansan ya duniyata zata kasance babu ke a ciki ba..."

Girgiza mishi kai da take yasa shi yin shiru, wasu irin hawayene masu dumi suke zubo mata, ganin shi kawai kara mata wani irin nauyi yake a zuciyarta, sanin lokuttan daya rage a tsakaninsu kawai nasata jin kamar ranar mutuwarta ce tasani saboda firgici. Na tsayin shekaru da soyayyarshi zuciyarta take numfasawa. Ko bacci take duniyarta cike take da mafarkinshi. Rayuwa zatai mata fili da girma mai cike da mawuyacin yanayi batare dashi ba.

Bata san yanda zata bude ido a matsayin mallakin wani ba.

"Ki fadi sunana ko sau daya ne..."

Ya bukata dan yasan da wahala ya sake ganinta bayan yau. Dariya ce ta kubce mishi da baisan daga inda ta fito ba. Wai shine yake tunanin ganin karshe yake ma Zafira a yau. Inda yasan ALKALAMIN KADDARA yai musu wannan rubutun da yaso ta daga nesa, da bai bari ya dandani yanda soyayyarta a kurkusa take ba tunda yasan zai rasa ta.

Kai Zafira ta sake girgiza mishi tana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Furta sunan shi zai zamar mata kamar bankwana ne take mishi. Ba zata iya bankwana dashi ba, bata taba sanin yanda dacin rashi na mutuwa yake ba, amman yau tana dandana yanda dacin rashi yake batare d a giftawar mutuwa ba.

"Bazan iya ba..."

Ta fadi muryarta can kasa. So yake ya karasa inda take. Amman bazai iya ba, daga nan dinma gaf yake da faduwa.

"Zaki iya. Allah bazai dora mana kaddarar nan ba in da ba zamu iya dauka ba. Allah ya sa miki alkhairi a cikin aurenki. Allah ya baki farin ciki a gidan kowanene fiye da yanda zan baki Zafira..."

Muneeb yake fadi yana jin kalaman kamar suna kona mishi harshe. Amman son da yake mata yakai ya taimaka mata tai ma mahaifinta biyayya. Ba laifinsu bane su dukansu, ita dashi sunzo a duniya daban-daban.

"Ban sani ba, komai bashi da tabbas, amman inajin labarin samun soyayya sau daya tak zai tabbata akaina. Bana jin zan sake soyayya kuma.... Amman zan cigaba da addu'a ke ki samu. Daya daga cikinmu ya cancan ci farin ciki..."

Numfashi yaja yana fitar dashi a wahalce. Jiri yake ji, ga zazzabi sabo ya sake lullube shi. Kukan ta na kara karya mishi zuciya.

"Ina miki fatan alkhairi. Nagode da dukkan kaunarki. Bazan manta ba..."

Ya karasa yana juyawa.

"Muneeb!"

Zafira ta fadi cike da tashin hankali. Tsaye yayi cik, tsikar jikinshi gabaki daya na mikewa da yanda ta kira sunanshi, yanayine da yasan fitar rai ne kawai zai mantar dashi. Bai juyawa ba yaja kafarshi yana ci gaba da tafiya.

"Muneeb karka tafi... Dan Allah ka tsaya tukunna... Wallahi bansan yazan yi ba. Inalillahi wa ina ilaihi raji'un.... Karka barni tukunna ka tsaya in sake ganin ka...."

Zafira ke fadi tana rarrafe dan ta karaso inda yake saboda kafafuwanta ba suda kwarin mikewa.

"Muneeb..."

Ta fadi lokacin daya fita daga falon. Kwanciya tai a wajen tana sakin gunjin kuka, tanajin yanda karshen duniyar ta yazo da tashin hankali marar misaltuwa. Kuka take kamar zata shide. Bata san shigowar Aroob ba sai jitai ta dagota, ruqunqume Aroob tayi tana wani irin gunjin kuka. Tana jin da wahalar gaske takai dare saboda yanayin firgici da tashin hankalin da takeji yana tabbatar mata karshen rayuwarta yazo.

*

Dakyar yakai wajen motar shi, ya bude ya shiga. Kanshi ya hada da gaban motar yana maida numfashi, kamun ya saki wani gunjin kuka kamar mace. Inda ance wata rana zaiyi kuka irin wannan dariya abin zai bashi, amman komai na duniya ya daina bashi mamaki.

Tsakanin jiya da yau ya shiga tashin hankalin da kalamai ba zasu iya misaltawa ba. Zuciyarshi yake ji tana ciwo kamar zata fado daga kirjinshi. Ta ina zai fara rayuwa da sanin duka burin shi akan Zafira yana cikane a tare da wani namijin daban. Tari ya soma yi yanajin kamar zai sume.

*

Tsaye yake bakin ajin su Zafira. Murmushin ta ya soma mishi maraba tana fitowa daga ajin. Farin mayafin da kanta yake nade dashi na sata yi mishi wani haske na daban. Da sallama ta karaso inda yake tana jingina bayanta da motar shi hadi da gaishe dashi.

"Kinyi kyau sosai..."

Dariya tai a kunyace

"Kaima kayi kyau..."

Tsayuwar shi ya gyara.

"Ina kirga kwanakin shekarun nan a cikin kaina fa...."

Dariya ta sakeyi sautin na dirar mishi a kunne da wani nishadi.

"Kai Love.... Duka yaushe aka shigo shekarar?"

Ta bukata cike da zolaya. Rausayar dakai yayi. Ba zata gane yanda yake son ganin magana mai karfi ta shiga tsakanin su ba.

"Kinsan akan kine na yarda akwai soul mate? Ina jin kamar an halittamun zuciyata ne kawai dan ta doka miki ke kadai.... Zafira da wahalar gaske in so wata macen bayan ke"

Dan kallon shi tayi kamun ta sadda kanta kasa.

"In baka same ni ba fa? Ka daina fadin hakan, zanso ka kasance cikin farin ciki ko da bana rayuwarka..."

Ware mata idanuwa yayi yana jin wani irin hargitsi a zuciyarshi. Yanayin shi nasata dariya hadi da hade hannayenta cikin alamun ban hakuri.

"Wasa nake..."

Numfashi ya sauke, har lokacin zuciyarshi na rawa.

"Karki sake mun wasan dazai zo da hasashen rayuwata babu ke a cikin ta. Kina sa inajin kamar ni kadai nake haukan sonki..."

Muryarta babu wasa tace

"Da soyayyarka zuciyata ta bude idanuwa, bansan me zanyi in babu kai a rayuwata ba, tun bansan menene so ba zuciyata take doka maka. Bakai kadai bane ba, bansan yanda kake ji a kaina ba, amman nasan yanda nake ji a kanka..."

Murmushin dayai mata har saida dimple din gefen fuskarshi ya loba ciki.

"Allah ya cika mana burin mu. Ina sonki wallahi. Sosai ina sonki..."

Dariya tayi.

*

Dariyar da yake jin sautin ta har cike da motar shi yanzun nan. Dariyar da wani zai dinga ji har abada. Wani irin kishi da bai taba sanin yana dashi ba ya turnuqe shi. Me yasa rayuwa bata da adalci ne, me yasa Daddy zai musu haka, kuka yake sosai. Jiyai kamar ana karar mota, dago kanshi yayi da fuskarshi a jike da hawaye, Daddy ne zai fita da motarshi kuma yanda Muneeb din yai parking din tashi bazai bari ba.

Da sauri Muneeb ya fito daga motarshi ko rufe murfin baiyi ba yana zagayawa ya kama glass din murfin motar Daddy, ganin shi yasa Daddy sauke glass gabaki daya yana son tuna inda yasan fuskarshi.

"Dan girman Allah Daddy ka taimaka mana.... Ka rufa ma rayuwar mu asiri kabarmu muyi aure...."

Muneeb yake fadi hawaye na zubar mishi. Kallon shi Daddy yake cike da rashin fahimta. Hakan yagani yasa shi fadin

"Muneeb ne, abokin Rafiq... Ni nake son Zafira. Wallahi ina sonta sosai kuma zan riketa tsakani na da Allah..."

Wani irin kallo Daddy yake mishi. Sai yanzun ya tuna inda ya taba ganin shi. Motarshi ya sake kallo tukunna ya kalle shi. Rafiq baya gajiya da kwashe-kwashe. Ko cikin motocin da ake zuwa cefane dasu a cikin gidanshi babu mai arhar ta Muneeb.

"Auren ta ran asabar ne. Ka nemi yarinya dai-dai kai. Kar kuma in sake ganinka a kofar gidan nan... Ka janye motarka ina da abu mai muhimmanci kamun insa security su janyemun kai da motar..."

Hannu Muneeb yasa yana goge fuskarshi. Koba komai bazaiji kamar baiyi wani kokari ba. Wucewa yayi ya koma cikin motarshi yana yin gaba abin shi. Ko hanya baya gani sosai saboda kukan da yake. Allah ne yakai shi gida lafiya. Sau hudu yana kusan haddasa hadari. Yana shiga daki kayanshi ya soma hadawa a akwati. Duk wani abu da hannunshi yakai sama kawai yake zubawa.

Har lokacin kuka yake mai cin rai, gida zai tafi, ko bakomai in yaga mahaifiyar shi zai samu sauqi-sauqi. Daman zai dauki hutun karshen shekara ne, zaiyi amfani da damar nan kawai ya dauka. Inya zauna a Abuja sanarwar daurin auren Zafira da zata cika garin zai iya zama ajalin shi. Yanzun ma sama-sama yake jinshi. Tasha zaije yahau motar haya. Dan bazai iya tuqi ba a halin da yake jin kanshi.

BAYAN SATI DAYA.

Kallo daya zakai ma Zafira ka tabbatar babu kwanciyar hankali a tare da ita. Dakyar ta gama jarabawar da take da ita a ranar ta dawo gida. Inda Allah ya taimake ta bata barin karatu ya tarar mata, da babu abinda zata iya rubutawa. Kuma jarabawar tazo mata da sauqi fiye da yanda ta fahimta. Kwance take cikin daki, dan yanzun ko abinci Aroob ce take kawo mata dakin.

Batason fita. Nuri batai mata magana ba, dan tana tunanin bata san abinda zata ce mata ba. Hakan kuma ya mata dadi. Wayarta kuwa tun ranar take a kashe har yau bata kunna ba. Ta roqi Aroob da karta fadama Fawzan. Tabarshi tukunna, yanda aka bankado kofar tasan ba lafiya ba. Mikewa tayi babu shiri.

"Kinsan lefenki ake karba a falo yanzun haka?"

Fawzan ya tambaya yana tsare ta da idanuwanshi da suka canza launi saboda bacin rai. Bata ce komai ba, idanuwanta ke zafi saboda babu sauran hawaye a cikinsu. Tayi kuka harta godema Allah. Cikin dakin ya shigo sosai yana samu waje gefen gadon ya zauna hadi da dafe kanshi da hannuwa.

"Ya Fawzan dan Allah karka wani damu... Kaga kar ciwon ka ya tashi..."

Zafira ta fadi hankalin ta a tashe. Karshen abinda zata so a yanzun bai wuce ciwon Fawzan din ya

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment