Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta matse gefe daya dajin zafin rashin shi na shekarun nan, tanajin yanayin mantawa dayai da ita na danneta. Hakan ya kula dashi a fuskarta yasa shi fadin

"Ban manta dake ba, wallahi ban manta daku ba..."

Cikin idanuwa take kallon shi.

"Shekaru nawa? Ina kaje? Babu kalar tunanin da banba Ya Tariq..."

Tasneem ta karasa muryarta na rawa, tanajin kamar kuka ne ke shirin zuwa mata, abinda tajima bataji alamu ba, saboda ganin shi nason farkar mata da wani bangare daya dade dayin bacci a tare da ita. Hadiye yawu yayi dan makoshin shi ya bushe da yanayin da bashi da alaka da kishin ruwa.

"Akwai dalili..."

Ya fadi yana yin shiru, itama shirun tayi tana saurarenshi yaci gaba. Kome zai fada tasan bazai sake komai ba, lokaci ya riga ya kure mata, yazo a makare, daya zo lokacin da take neman wani koyayane ya fada mata akwai wata hanya banda wadda tabi, ya haska mata duhun dake mamaye da ita koyayane, kilan da bai zauna tare da ita har haka ba.

Jin bashi da niyyar kara cewa komai ya sa muryar Tasneem din can kasa tace

"Ka makara..."

Idanuwanshi ya ware a kanta yana son gane me take fada, jinjina mishi kai tayi

"Ka makara Ya Tariq... Abubuwa da yawa sun faru. Ka makara...."

Karar dataji na katse mata kalamanta, yana saka Tariq dauke idanuwanshi daga cikin nata, hannu yasa a bayan aljihunshi ya ciro wata karamar waya yana dubawa, runtsa idanuwanshi yayi yana bude su akanta da fadin.

"Zan dawo Tasneem, zan dawo..."

Murmushi tayi dake nuna alamar bata yarda da kalamanshi ba.

"Yaya Ashfaq ne, nasan yana tunanin ina naje ne saboda baisan na fito ba. Amman zan dawo..."

"Me yasa?"

Ta tambaya.

"Me yasa me?"

Ya amsa cike da rashin fahimtar tambayarta.

"Me yasa ka fito baka fada mishi ba?"

"Saboda in yasani bazai barni ba"

Ya karasa muryarshi can kasa. Shiru tayi na wani lokaci, wayar Tariq din ta sake daukar ruri

"Ka daga mana..."

Girgiza kai yayi yana fadin

"Zan dawo..."

Kai ta daga mishi. Bai sake cewa komai ba ya juya da sauri, tsaye tayi saida taga yasha kwana tukunna ta sauke wani numfashi da batasan tana riqe dashi ba, ta juya tana shiga cikin gida. Mayafinta kawai ta ajiye, Hamna tace

"Kin dawo da wuri"

Ba zata iya da Hamna ba da daren nan, batama jin karfin jan magana. Ganin Tariq nason hargitsa mata lissafi.

"Ya Tariq yazo. Amman ya koma yace zai sake dawowa"

Shiru Hamna tayi na tsayin lokaci, har saida Tasneem din tayi tunanin ko bata jita ba, buda baki tai zata sake maimaitawa Hamna ta rigata da fadin

"Ya yake?"

Dan daga kafada Tasneem tayi

"Ya canza..."

"Canji mai kyau ko marar kyau?"

Hamna ta tambaya, dan shiru Tasneem tayi, banda yanayin da tagani a idanuwanshi, zata iya cewa canjin shi me kyaune, kayan jikinshi tsaf suke, haka shima tas dashi harma da waya a hannunshi, duk yanda take tsada a wannan lokacin.

"Me kyau"

Jinjina kai kawai Hamna tayi tana sauke numfashin da ita kadai tasan tana rike dashi. Komawa tai kan katifa ta kwanta tana juya bayanta, wata irin kewar Tariq din na mata sallama. Sanin mintina kadan da suka wuce yana kofar gidansu yasa zuciyarta matsewa.

Ta daina maganarshi ne saboda shirun yayi yawa, saboda batason zuciyarta ta fara tunanin wani abu ya same shi. A duk fitar da zatai haka take kallon fuskokin samari ko zata ga tashi a ciki. Wasu siraran hawaye suka zubo mata masu dumi.

'Karka dade wannan lokacin Ya Tariq, dan Allah karka dade'

Take maimaitawa cikin zuciyarta kamar hakan zaisa sakon ya isa gare shi. Hannu tasa tana goge hawayenta hadi da kara gyara kwanciyarta tunda tayi isha'i batajin zata sake tashi. Komai ya tsaya mata waje daya, babu wani abu a cikin kanta banda fuskar Tariq da tunanin yanda Tasneem tace ya koma, hoton da zuciyarta ta hasko mata na sata yin murmushi. A haka bacci ya dauketa cike da mafarkin shi.

*

Sai da tai Sallar Asr tukunna ta shirya, yau banda hoda bata shafama fuskarta komai ba, atamfa ta saka dinkin doguwar riga sai ta dauki hijab din Hamna ta saka, har kasa yake ja mata dan Hamna tafita tsayi ta fito, Ummi na zaune tana tsintar wake da alama abincin dare zata dora.

Tasneem ta bita da kallo cikin jinjina yanda rayuwa ta canza musu, Ummi ce da zaman gida da girki, ita kuma da fita, girgiza kai tayi sannan tace

"Ummi zanje gidansu Kausar"

"Ki gaishe dasu. A dawo lafiya"

"Allah yasa"

Tasneem ta amsa tana ficewa. A ranta tana kudirtar zatai ma Alh. Madu magana ya siya mata waya ko wani daga cikin samarinta dan tagaji da zama shiru haka. Da tana da waya yanzun daya daga cikinsu zata kira yazo ya kaita ba saita shiga motar haya ba. Da tunanin a ranta ta taka zuwa titi.

Takalmane dogaye a kafarta, kawayen da take haduwa dasu suka koya mata saka dogoyen takalmi, aikuwa bata kula da wani dutse ba ta taka, gurdewa kafarta tayi, saura kadan ta fadi, saidai ba faduwar bace tasa zuciyarta dokawa, muryar dataji ance

"SubhanAllah..."

Dan ko kadan tunanin kiran Allah baizo mata ba. A hankali ta dago kai tana sauke idanuwanta cikin nashi, ruwan kasa mai haske, kalar da bata taba gani a idanuwan duk mutanen data sani ba. Da shadda ruwan kasa mai duhu sanye a jikinshi. Shima kallonta yake, kamun a hankali yace

"Baki ji ciwo bako?"

Kai ta daga mishi tana sauke idanuwanta daga cikin nashi, saboda yanda taji jikinta ya dauki dumi, kwarjinin shi ya cika mata zuciya, abinda bata tabaji game da wani da namiji ba. Muryarta da wani irin sanyi tace

"Nagode..."

Tana duba kafarta da gyara takalminta ta soma tafiya, duk da kafafuwanta sun mata nauyi na rashin dalili. Ji tayi kamar ana binta a baya hakan yasa ta juya, fuskarshi ya daquna mata.

"Baki fadamun sunanki ba"

Ya fada muryarshi da yanayin mamaki, kamar yana mamakin dalilin da zaisa yaso jin sunanta, ba kuma a muryarshi kawai taji ba har a fuskarshi da take a daqune har lokacin. Kawai sai taji ranta ya baci.

"In kana mamakin dalili me yasa ka tambaya?"

Sake daquna fuska yayi

"Excuse me..."

Ya ce yana kallonta.

"Sunana nake nufi... Me yasa ka tambaya?"

"Saboda ina son sani"

Ya amsa yana tsura mata idanuwan da yan mintina kadan da fara ganinsu sun samu waje a tare da ita sunyi zaune.

"Tasneem..."

Ta tsinci kanta da fadi, abinda ta sake jimawa batai ba, tun tana sabon shigar samari kamun ta waye.

"Anan unguwar kike?"

Ya sake bukata. Daga mishi kai tayi

"Kimun magana da bakin ki"

Kallon fuskarshi tayi wannan karin, yana da kyau dai-dai nashi, amman akwai samarin datayi da sukafi shi kyau, duk da akwai kwarjinin da take gani a fuskarshi da bata taba gani a ta samarin ta ba, hakan baya nufin zai dinga bukatar abu a wajenta kamar ya santa. Bude baki tayi tace mishi zai iya daukar fuskarshi da idanuwanshi masu kyau ya maidasu inda suka fito amman saita samu kanta da cewa

"Eh nan unguwar nake. Inka mike layin nan kwanar farko"

Kamun tagama mamakin abinda tayi ya dan daga nashi kan, hadi da juyawa batare dayace mata komai ba. Harta shiga mota tana ma kanta fada a zuciyarta. Dole ya tafi yabarta a tsaye batare dayace komai ba, daga tambayar ko nan unguwar take ta saki baki harda fada mishi inda gidansu yake.

Gidansu Kausar dinma da taje bata wani dade ba, dan gabaki daya hankalinta baya jikinta, fuskarshi ta mata tsaye a zuciya ta rasa yanda zatai. Har Kausar ta kula akwai abinda yake damunta. Da zata rakota tahau motar dawowa gida saida ta tambaya tace mata babu komai.

Haka ta dawo gida da sanyin jiki. Haka kuma tai kwanaki har biyar da tunanin shi, tasan zata bari na wani lokaci, dan mamakin shine kawai da abinda yai mata da babu namijin daya taba mata shi, in mayyar zuciyarta tagaji zata daina damunta da tunaninshi da idanuwanshi.

A ranar bayan magriba suna zaune a daki, Sabeena na kwance a jikinta yaro yai sallama ana kiranta.

"Sabeena dagani inga waye..."

Ta fadi ranta a bace tana daukar hijab din datai sallah da ita, dan a kwana biyun nan babu inda taje, bama tason ganin kowa, bata kuma son fadama kanta dalilin hakan. Fuskarta babu walwala ta fita, unguwar fayau dayake akwai hasken lantarki. Zuciyarta tai wani irin dokawa a kirjinta ganinshi jingine jikin motarshi da farin kaya a jikinshi, har hularshi fara ce, hannuwanshi nade a kirjinshi.

Takawa tayi tana zuwa inda yake, zuciyarta na ci gaba da dokawa musamman da taga fuskarshi kurkusa, rannan bata kula da kasumbar dake kwance a fuskarshi ba saboda idanuwanshi sun dauke mata hankali, bata kula da abubuwa da yawa a tattare dashi ba. Har lokacin bai kalleta ba, idanuwanshi na kafe a wani waje daban da inda take.

Zuciyarta na kara gudun dokawar da take ta jingina bayanta da motar da yake jingine a jiki shima, badan ta gama kallon shi ba, saidan tana ganinshi kamar wani katon kogi, data fara saka kafafuwanta a ciki, tanajin inta ci gaba da tafiya nutsewa zatai a cikin shi batare data san abinda zata samu ba koya zatai ta fito ba.

"Me nake anan?"

Ya fadi da alama a zuciyarshi yai niyyar maganar bai kuma san ta fito fili ba. Runtsa idanuwanta Tasneem tayi danjin maganar ta taba wani waje a kirjinta dayai maga ciwo. Tsintar kanta tayi dayi mishi Sallama. Sai lokacin ya juyo kanshi yana kafa mata idanuwa batare daya amsa ba. Tanajin yanda idanuwanshi ke yawo kan fuskarta kamar mai neman wani abu, kamun ya amsa sallamar a hankali.

Wani yanayi taji ya lullubeta data kasa gasgatawa, dan tasan sunyi hannun riga da kunya da jimawa, babu dalilin dazai sa ta ziyarce ta a wannan lokacin.

"Dare yayi ki koma gida..."

Ya furta muryarshi a dakile kamar ta mishi dole. Batace komai ba ta raba bayanta daga jikin motar datake zaton tashi ce, badan bata da abinda zatace ba, saidan wani abu ya mata tsaye a makoshi. Tunawa tayi ko sunanshi bata sani ba, inhar a gani na biyu yana saka zuciyarta gudu haka, yana saka jikinta daukar dumi yakamata ta samama fuskarshi suna a zuciyarta.

"Ya sunanka?"

Ta bukata batare data juyo ba.

"Rafiq Mustafa Shettima"

Ya fadi, ci gaba tai da tafiya, tanajin muryarshi nabinta, tana kuma jin yanayin daya fada mata sunan dashi, kamar a cikin sunan akwai sakon dayake son fada mata, kamar a cikin sunan akwai dalilin tambayar dayai ma kanshi ta 'me yake a wajen ta', a cikin yanayin akwai abubuwa da yawa data kasa fahimta saboda komai tare da Rafiq Mustafa Shettima na mata ihun banbancin da ke tsakanin su.

**

Tari ya sarqeta data soma ba kakkauta tana jin ciwon shi daga zuciyarta da yanda ta bude tsofaffin tabo suna zubda jini. Rafiq ko motsi baiyi ba har ta samu tarin da take ya tsagaita mata. Kallon shi tayi

"Kasan abin da ya faru daga nan.... Daga haduwar mu dakai zuwa yanzun..."

Ta karasa da wani irin wahaltaccen yanayi. Idanuwanta take so su sauka cikin na Rafiq ko zata fahimci kadan daga cikin abinda labarinta yasa shi ji, amman yaki yarda su hada idanuwa. A hankali ya mike tsaye yana juyawa da niyyar barin gurin.

"Sugar... Tsaya... Karka tafi... Kace wani abu dan Allah kace wani abu...karka tafi..."

Tasneem ke rokonshi hankalinta a bala'in tashe, kokarin mikewa take amman ta kasa, saboda batajin karfi ko kadan, tana kallon Rafiq ko alamar yaji me take cewa bai nuna ba ya bar falon yana nufar bangarenshi. Karar doko kofar shi na hadawa da wani bangare a zuciyarta...!

©
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

08

KANO

Sakin Tariq yayi yana mikewa da shirin fita daga dakin.

"Ina zaka je?"

Ashfaq ya buqata muryarshi can kasa, idanuwanshi dauke da wani nisantaccen yanayi.

"Zan kira likita ne..."

Dariya Ashfaq yayi sautin ta na mishi wani iri a jikinshi. Da dayan hannunshi ya nuna Tariq da ko ina na jikinshi ke bari, idanuwanshi sunyi wani fari, ya kalle shi tukunna ya maida kallonshi kan Yasir da fadin

"Ba Likita yake bukata ba...babu abinda likita zai mishi a wannan yanayin Yasir"

Ashfaq ya karasa muryarshi na sauka kasa sosai. Girgiza kai Yasir yayi

"Kasan hadarin, Faq kasan zai iya komawa gidan jiya..."

Cikin fuska Ashfaq ya kalli Yasir din dake girgiza kai cike da alamar rashin yarda.

"Meye bambancin? Bazan iya mayar dashi wajen nan ba.... Wallahi bazan iya ba"

Kofar Yasir ya daka da hannunshi kaman zai karyata, kamun ya tura hannun cikin sumar kanshi yana sake hargitsa ta.

"Ka bashi kawai... Nasan akwai a jikin ka..."

"Faq..."

Hannu ya daga mishi.

"Nasan baka daina ba...Kaman yanda nasan bai shima bai daina ba. Ka bashi kawai"

Batare da musu ba Yasir yasa hannunshi a bayan aljihunshi yana zaro takardar dake dauke da cocaine, nufo inda Tariq yake kwance yayi. A gefenshi yai layi biyu da cocaine din dogaye, a kasa kan tile yana sa hannu daya ya mirgino da Tariq ta wajen.

Tariq kam da yake jin kanshi na shirin tarwatse wa saboda surutan dake ciki, Yasir na mirgino ta gefen idonshi ya fara ganin layin cocaine din, ba sai an fada mishi ko menene ba, cikin bacci yana da tabbacin zai jita in tana kusa dashi. Hannunshi dake kyarma ya dago yana gyarata hadi da kai hancinshi wajen, ja daya yayi ya zuqe layin. Runtsa idanuwanshi yayi gam yana jin shigarta har cikin kwakwalwarshi.

Yakai minti biyu a haka kamun ya bude idanuwanshi ya sake zuqe dayan, sake runtse su yayi yana mirgina kwanciyar da yai hadi da dunqule jikinshi waje daya yanajin wata irin nutsuwa na saukar mishi, a hankali yake jin surutun dake cikin kanshi na ragewa, jijiyoyin jikinshi da suke rirriqe suna koma mishi dai-dai.

Duk abinda yake Ashfaq bai dauke idanuwanshi daga kan Tariq ba, kallon shi yake da wani irin ciwo a zuciyarshi.

"Ina so in bari... Da duk zuciyata ina so in daina amman na kasa. Ina ganin komai kaman yanzun ya faru... Tana dishemun wannan bangaren..."

Yasir yake fadi a hankali. Yana so Ashfaq din yagane, yana so ko yayane ya fahimce shi, ya fahimci Tariq, dan yanayin dake idanuwanshi yasa zuciyar Yasir din riqewa ta bangarori da dama. Bayaso ya kara mishi matsaloli fiye da wanda yake ciki, bayason ya dora mishi damuwar shi akan tarin wadda yake dauke da ita a kullum.

"Na dauka abinda ya samu Tariq ya isa yasa kabari, na dauka kagane da duk ja daya da yanda kake nisanta da hankalinka da lafiyarka...cocaine da kwayoyi ne zasu rabaku da hankalin ku, damuwar ku ce zatai sanadin nawa"

Ashfaq ya karasa yana gyara zamanshi kan gadon hadi da jingina bayanshi sosai. Yasir baice komai ba, badan bashi da abin fada bane, saidan yanayin Ashfaq daya nuna bazai saurara ba. Takawa yayi yaja kujera ya zauna suna zubama Tariq dayake shirin tashi zaune idanuwa.

Ba zaman yayi ba. Mikewa yayi gabaki daya, idanuwanshi sun sake launi, cocaine din dayaja na saka shi jin babu wani abu dazai iya taba nutsuwar dake duniyarshi. Hannu yasa yana danne hancin shi daya yaja. Kamun ya sauke yana kallon Ashfaq. Cikin muryarshi data kara budewa yace

"Kasan me? Banma san rashin hankalin daya sani dauka zaka yarda naga Ya Yasir ba... Kome zan sha, ko me zanqi sha bazai hanani gane shi ba... Nasan bambancin abinda nake gani a cikin kaina dana zahiri..."

"Ka samu wajen zama Tariq"

Ashfaq ya fadi cike da kashedi. Hannuwanshi Tariq ya nade a kirjinshi.

"Saboda me? Daka bishi ranar kilan da ka ganshi..."

Runtsa idanuwanshi Ashfaq yayi yana kirga daya zuwa goma cikin kanshi. Tariq baisan abinda yake ba, cocaine ke hura mishi kai, bazai bari maganganunshi su mishi tasiri ba.

"Bakaso ya dawo ko? Shisa yanzun ma baka yarda naganshi ba. Kai ya kamata ka bace a madadin shi... Halin duk da yake ciki kai ya kamata ka shiga bashi ba... Dashine bazai bar abu ya sami Arfa..."

Baiga dirowa da karasowar Ashfaq inda yake ba, saida yaji katsewar kalamanshi ta hanyar shaqar da Ashfaq din yai mishi. Kwata kwata bai damu da ciwon dake jikinshi ba, dan baikai wanda maganganun Tariq suka jefa zuciyarshi ba. Yasir ne ya taso yana kokarin kwace Tariq din daga hannun Ashfaq dake girgiza Tariq da fadin.

"Nasan ba zaka taba yafemun kan abinda ya sami Arfa ba...ban roqeka ba saboda bazan iya yafema kaina ba...hakan bashi zai baka damae boyewa bayan cocaine kana jefamun babban kuskuren rayuwata a fuska ba Tariq...karka gayamun abinda nake so ko banaso akan Yasir.... Karka fara..."

"Faq zaka ji mishi ciwo..."

Yasir ya fadi yana kokarin banbare hannun Ashfaq daga wuyan Tariq da harya soma tari. Tarinne yasa Ashfaq sakin shi da sauri yana kokarin kamoshi

"Tariq..."

Tunkude shi Tariq yayi yanabin bango ya nufi hanyar kofa, bayanshi zaibi Yasir ya riqeshi

"Ashfaq!"

Ya fadi a tsawace

"Karya fita Yasir, baya cikin hankalin shi"

Janshi Yasir yayi yana mayar dashi kan gadon ya zaunar.

"Bayau ya fara fita shi kadai cikin yanayi irin wannan ba. Allah kadai yasan ranakun daya hau titi da machine cikin maye...karka damu da Tariq baka da lafiya..."

Dafe kanshi Ashfaq yayi da hannuwanshi duka biyun yana neman hawaye ko zai samu sauqi a zuciyarshi amman ya kasa samun shi. Ko bai fadaba yasan jini ke fitowa daga ciwon dake jikinshi yana bullo bandejin da yake rufe dashi, amman bai damu ba.

"Nayi kuskure nasani... Me yasa Tariq zai dinga jifana dashi?"

Ya tambaya batare daya dago ba. Sauke numfashi Yasir yayi.

"Me yasa ba zaka daina dukan kanka akan abinda ba zaka iya canzawa ba? Ka daina saka maganganun Tariq a ranka... Bama cikin hayyacin shi yake ba. Zuwa dare bazai tuna abinda ya faru ba"

Shiru Ashfaq din yayi. Inama zai iya komawa baya, saidai haka rayuwa take, duk lokacin daya wuceka bazai taba dawowa ba, lokaci abune mai muhimmanci, zabin da zakayi a lokuttan daka gani nada hadari, ko kayi kuskure a cikin zabinka ba zaka iya kowa ka sake wani ba.

"Kagani ko? Jini ciwon ka yakeyi.... Karka motsa. Ina zuwa..."

Yasir ya karasa, yanajin fitarshi daga dakin, fadawa Ashfaq yayi kan gadon ta bayanshi yana maraba da ciwon daya ratsa kwanyarshi saboda ya dauke mishi hankali da wanda yake a zuciyarshi, ya kuma san zai tayashi danne abinda ke zuciyar na wani lokaci. Karar shigowar sako yaji a wayarshi da tunda Yasir din ya ajiye mishi ita gefen kanshi baiko bi ta kanta ba.

Ya dauka ma ya yarda a hargitsin daya faru, lalubawa yayi ya dauko yana dubawa. Bai saving number din ba, amman yasan ko wanene. Lumshe idanuwanshi yayi yana jin wani ciwon na daban. Yana kuma tuna yanda akai harya sami lambarshi

*

Jijiyoyin gefen kanshi sun tashi saboda bacin rai, wayar ya sake kalll da saqon daya shigo, kamun ya kalli Yasir da yake tsaye babu alamar razana a tare dashi, asali ma a nutse yake kallon Ashfaq din dan yaga kome zaiyi.

"Me yasa zaka bashi lambata?"

"Saboda dan uwanka ne, saboda ya tambaya"

Numfashi Ashfaq yaja yana saukewa.

"Da nace bana son ganin shi hakan bai fada maka bazan so ya samu lambata ba!"

Hannu Yasir ya daga mishi

"Kar kaimun ihu akai Ashfaq, zaka iya blocking dinshi, banga kana niyyar hakan ba..."

Badan Yasir yasan Ashfaq kamar yanda yasan kanshi ba da baiga tahowarshi ba balle hannu daya kawo saitin fuskarshi, hakan ya bashi damar kaucewa yana kaima Ashfaq din duka a gefen fuskarshi, yanda hannunshi ya hadu da fuskarshi yasan ko bai karya wani abuba ya dake shi sosai. Hankade shi yayi baya

"Bansan abinda ya faru tsakanin ku ba..."

Sake tahowa Ashfaq din yayi, Yasir ya sake tare shi, yana saka mai gwiwar kafa a ciki, girman jikinsu da karfinsu ba daya bane, Ashfaq din yasani dan bayau bane karo na farko da fada yake hadasu, amman yaga alama yau dukan yake bukata shisa yake haye mishi.

"Amman kana bukatar yan uwanka..."

Yasir ya fadi yana riqe da Ashfaq din dam.

"A shekarun da nasanka, babu wanda ya nace da son gyara kome ya faru a tsakanin ku sai Altaaf. Ka fadamun, ka fadama kanka yanda ka tsane shi bai dameni ba, amman duk zuwan dazai kaqi yarda ko ganinshi kayi ina kula... Ina ganin yanda abin yake ci maka rai fiye da yanda nake gani a fuskarshi. Zaka iya gogewa ba matsalata bace, zanyi bacci mai dadi sanin na maka zabin da baqar zuciyarka ta hanaka kayi..."

Yasir ya karasa yana sake kai mishi wani dukan da sai da gwiwoyinshi suka kai kasa, sannan ya fice daga dakin yana barin shi nan.

*

Yanda bai saving din lambarba, bai kuma yi blocking ba, sakon ya bude yana karantawa:

'Ko ba zaka yafemun ba, kaimun magana, ka zageni, ka ce wani abu komenene dan Allah'

Key ya saka wayar yana ajiyewa inda ya dauketa, miqewa yai zaune, yanajin ciwon shi ya sake budewa da wata irin azaba, hakan kuma yake nema dan baison ba kwakwalwarshi wani sarari da zata saka shi tunanin abinda bayason sake ziyarta.

**

KANO

A cikin falo ya daura agogon shi.

"Jawwad baka makara ba?"

"Ina kwana..."

Ya gaishe da Anty maimakon amsar tambayar datai mishi yana dorawa da

"Sosai ma, kuma meeting zamuyi wallahi"

"Yaya ina kwana"

Jawda ta gaishe dashi.

"Lafiya kalau. Ba zaki school bane yau?"

"Hutun tsakiyar zango muke"

Jinjina mata kai yayi yana karasawa ya karbi kofin da Anty ta bashi, a tsayen ya kurba yana yatsina fuska saboda bai dauka da zafi sosai ba.

"Anty zan ci wani abu a office...."

Girgiza kai tayi dan tasan halinshi.

"Kodai ka zauna kaci ko ka jira in hada maka ka tafi dashi"

Daquna fuska yayi yana tsugunnawa.

"A tsugunnen zakaci abinci?"

"Allah na makara sosai..."

Ya karasa yana zama, dankalin dake plate din gaban Jawda ya fara tsinta yana ci a hankali yana kurbar shayin dake riqe a hannunshi. Wainar kwai ya dauka ya tura a bakinshi yana ajiye cup din ya mike da sauri.

"Saina dawo..."

Ya fadi a bakin kofa yana zura takalmanshi dake ajiye a wajen.

"Jawwad..."

Anty ke kira, ina da sauri ya fice yana dariya. Girgiza kai tayi kawai. Yasan inya tsaya Anty na iya hadashi da kula da dankali a ciki sai kace karamin yaro, abokanshi har zolayarshi suke a wajen aiki, dan gatan Anty. Machine dinshi ya hau hadi dayin addu'a kamun ya tayar yana ficewa daga gidan.

Sai dai ko nisa baiyi ba ya kula mai na gab da kare mishi. Sauke numfashi yayi, yasan aikin Marwan ne, ba takaicin shi karar da man ba, makarar dazai karayi tsayawa zuba mai. Amman bashida wani zabi. Bazai iya tsayawa ya karasa gidan mai ba, baima san layin dazai samu ba, dan haka yana hango wasu yan bunburutu yai parking a gabansu yana saukowa daga machine din.

Na dari biyar yace a zuba mishi, ya basu dubu daya. Saidai babu canji.

"Kaga siyomun Mtn na dari biyar din in da masu kati a kusa. Dan Allah kai sauri"

Jawwad ya fadi a kagauce, da hanzari mai man yabar wajen yana barin Jawwad tsaye sai abokanshi dake zaune kan benci dake bakin titin. Lokaci-lokaci Jawwad yake duba agogon shi yana jan qaramin tsaki. Kallo daya zakai masa kasan a kagauce yake da yabar wajen.

Kaman daga sama yaji ance

"Jawwad?"

Muryar dauke da mamaki da shakku, zuciyarshi ta fara dokawa kamun wani abu cikin kanshi ya fada mishi bazai yiwu ba, saidai zuciyarshi na fada mishi a cikin mutane dubbu masu shigen muryar zai iya ganeta.

"Jawwad"

Aka sake kira, da duk wani karfi da yake ji yake son kin juyawa, amman jikinshi baisan wannan ba, a hankali ya juya yanajin makoshin shi ya bushe kamar ya kwana biyu baisha ruwa ba, kayan dake jikinta ya fara bi da kallo da suke a wulaqance, sai robar dake hannunta, kamun idanuwanshi su sauka kan fuskarta da yanayinta yasa zuciyarshi matsewa har yanajin iskar daya shaqa taqi kai mishi inda ya kamata.

'Mama'

Ya fadi cikin kanshi, bakinshi a bude amman kalma ko daya taqi fitowa, wahala da halin rayuwa da ke tare da ita baisa fuskarta ta canza mishi ba. Baya tunanin kuma kome zai samu fuskarta zai kasa ganeta.

"Jawwad..."

Ta sake fadi, wannan karin muryarta na karyewa, hawaye na zubo mata. Kare mata kallo Jawwad yake dan duk yanda bayaso ya furta ma kanshi kalmar yasan bara take. Runtsa idanuwanshi yayi yanason ya bude su yaga ta bace, ya bude su yaga baima sauko daga gadon dakinshi ba balle ya fito waje wannan yanayin ya tabbata.

"Jawwad baka son ganina ko?"

Muryarta tasa shi dole ya bude idanuwanshi yana tabbatar da ba mafarki yake ba. Ita din daice a gabanshi.

'Wallahi saika sakeni, kamal bazan zauna dakai ba'

Muryarta ta dawo

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment