Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayin addu'a? Haka zaka hita..."

Tsayawa yayi sunayin addu'a tukunna suka fita tare har wajen mota ya bude ma Majida ta shiga. Shikam zagayawa yayi ya bude yana jefa jakunku nan a bayan motar tukunna ya zauna.

"Jikina nake ji a sanyaye..."

Altaaf ya fadi yana murza mukullin motar.

"Rasuwar nan ce, kayi ta Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Kai yadan daga mata, yana fita da motar daga gidan yahau titi kirjin shi yai wata irin dokawa, kamar zuciyar shi zata fito waje, da sauri sauri yake maimaita Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, bai fadama Majida ba, amman akwai wani abu tattare da tafiyar da yake mishi wani iri.

Bayajin akwai alkhairi a tattare da tafiyar, yana fatan sharrin zuciyar shi ne kawai. Shiru suke tafiyar har suka fita daga garin Kano suna soma shiga kauyukan ta.

"Mike damun ka?"

Majida ta tambaya tana korar shirun da ya cika motar. Muryarshi a sanyaye amsa

"Babu komai. Me kika gani?"

"Yau baka yin gudu, wanda suke tahiya da machine har sun wuce mu"

Tsoron taka motar yake ko dokawar da zuciyarshi take na da alaqa da titin da suka hau.

"Kina kewar gudun da nake da mota ne?'

Dariya Majida tayi.

"Wacce kewa? Addu'a ta Allah ya amsa"

"Oh wato Addu'a kika zauna kina mun ko? Dame-dame kike roka? Fadamun, hancina ya shige ciki kamar naki ko?"

Sosai Majida ke dariya

"Ka kyale man hanci, a haka dai kake so, har sumba kake manna mai"

Wannan karin shi yai dariyar.

"Allah ya shiryamun ke"

"Amin"

Ta amsa tana mishi dariya. Dan gudun motar Altaaf ya kara, Majida kam bacci takeyi, yasan hali, tafiya indai ta wuce ta awa daya da Majida a mota sai tayi bacci.

*

Suna gab da shiga Zaria Magrib tai musu, lokacin Majida ta tashi, yasan zata ce ya tsaya suyi Sallah, dan haka ya fada mata tabari su shiga zaria. Aikam haka akayi, wani gidan mai ya samu da yake da Masallacin mata dana maza, sukayi magrib, kamun nan suka sake daukar hanya.

Motar yake ji tana jerking dan haka ya samu gefen hanya yai parking.

"Tafdin, Allah ya kiyaye kar motar nan tai mana tsiya kuwa..."

Altaaf ya fadi yana fita, bude gaban yayi, ya dudduba iya abinda zai iya ganewa tukunna ya dawo cikin motar. Sai dai me, babu yanda baiyi ba amman motar taki tashi.

"Mi ya same ta?"

Majida ta tambaya.

"Bansani ba wallahi, shekaranjiya fa aka dudduba mun komai"

Altaaf ya fadi ranshi a bace yana sake fita ya kara duddubawa ya dawo, wannan karin ta tashi, amman daya fara takawa sai ta ci gaba da jerking, ga wani irin kuka tanayi.

"Bari in samu mu lallaba haka, kilan kauyen da zamu samu gaba ba za'a rasa mai gyara ba..."

"Allah dai ya ida kaimu lahiya, yasa karta sake macewa"

"Amin dai..."

A hankali yake tafiyar har suka karasa kauyen (      ) hango wani mai rake da mutane tattare a wajen yasa shi gangarawa da motar har wajen tukunna yai parking. Fitowa yayi yana musu sallama, bayan sun amsa ya dora da

"Dan Allah ko akwai mai gyara a kauyen nan, motata ke da yar matsala..."

Daya daga cikin su ne yace

"Wai, mai gyaran mota?"

"Tawfiq mana"

Dayan ya fada mishi ganin yana tunani.

"Tawfiq dan gidan Malam Bashari?"

"Eh shi"

Jinjina kai daya daga cikin su yayi.

"Aikam da wahalar gaske Tawfiq ya fito yanzun"

Da sauri Altaaf yace

"Dan Allah ko zaku dubo mun shi, ko nawane zan biya"

"Aiba dubo shi din bane wahala, sai dai ko muje tare, wata kila inya ganka yazo"

Dan jim Altaaf yayi, kamun yace musu

"Ina zuwa..."

Mota ya koma ya fadama Majida, hadi da bata mukullin motar.

"Ki kulle daga ciki, ki rufe glasses din duka..."

Karba tayi tana dariya.

"Sai kace yarinya"

"Majee..."

Altaaf ta ya fadi cike da kashe di. Rufe glasses din tayi da kofar daga ciki, tukunna ya juya yana komawa, biyu daga cikin matasan ne suka tafi dashi dan zuwa gidan su Tawfiq din da suke magana.

Kalle-kalle Altaaf yakeyi, dan akwai wuta a garin, ko ina tarau sai tsilli tsillin gidaje da basu da HASKEN LANTARKI (By dimples) a kofar gidajen su. Dakuna fuska yayi, akwai wani abu tattare da kauyen da ya zauna mishi. Yana jin kamar bayau bane karon shi na farko da kauyen.

"Ya sunan kauyen nan?"

"(       )"

Daya daga cikin samarin ya amsa. Tari ya kwace ma Altaaf, dan bugawar da zuciyar shi tayi wannan karon har cikin makoshin shi yaji tsallen, hakan na sawa makoshin ya bushe mishi kamar ya kwana bai sha ruwa ba.

'Kudin ka da matsayin ka ba zasu shiga tsakanina da illata ka fiye da yanda kai mana ba inhar idona ya sake sauka akan ka, ba dauri ba, kasa a batar dani, saina illata ka inka tako kafa hamsin tsakanin ka da gidan mu'

Wannan karin hanjin shine ya tattaru ya koma gefen cikin shi yana kullewa waje daya. Ga zuciyarshi dake ci gaba da dokawa. Girgiza kan shi yake, baya son tunawa, baya son gasgatawa. Babu yanda za'ai ALKALAMIN KADDARA ya rubuta mishi dawowa kauyen nan ta wannan lokacin.

'Allah ya dauke maka farin ciki kamar yanda kaimun, Allah ya tsayar maka da dukkan al'amuranka kamar yanda ka tsayar mana da namu, Allah ya tarwatsa maka rayuwarka ta fannin da baka taba zato ba, A-Tafida ko? In shaa Allah sunan ka kanshi sai ya zamar maka tashin hankali kamar yanda ya zamar mun, kaji ni? Wallahi ba zaka taba samun wadataccen farin ciki ba'

Zufa ce ke tsatsafo mishi ko ta ina, har cikin sumar kanshi, musamman tafukan hannuwanshi, shekaru bakwai da dori, amman jin maganganun su yake cikin kanshi kamar yanzun suke furta su. Ya dauke shi fiye da shekara uku yana kokawa da bangarori da dama na zuciyarshi kamun ya dishe addu'ar can, kamun ya yakice yanda duk sanda ya tunata sai tsoro ya kamashi.

Dan baya son yanda tasa yake duba rayuwarshi, yake duba kamar ta canza ALKALAMIN KADDARArshi. Musamman in ya duba yanda ko kadan baya son wani ya kira shi da A-Tafida. Suna ne dake tattare da abubuwan dayai rami ya binne, ramin da ko Majida baya so ta gifta ta wajen balle ta kula akwai shi harma tasan me yake ciki.

Baya son ya duba yaga yanda addu'ar ta soma tasiri a kanshi, sai yanzun da yake cikin kauyen dako a mafarki baya fatan ya sake takowa. Bai san ya tsaya da tafiyar da yake ba, saida yaji an dafa kafadarshi.

"Lafiya dai ko?"

Daya daga cikin samarin ya tambaya yana girgiza shi. Dan yai mishi magana ya fi sau hudu, amman zurfin da yai a tunani yasa baiji ba. Da sauri ya daga mishi kai, yana samun muryarshi da fadin

"Bana danjin dadi ne kawai, mun kusa?"

Jinjina kai sukai su duka.

"Ayya, Allah ya bada sauqi, eh mun kusa, nan kwanar kawai zamu sha"

Binsu kawai Altaaf yake, inda suka sa kafarsu yana mayarwa, amman bawai dan yana gane abinda yake faruwa a duniyar da take wajen shi ba. Ya tattara hankalin shine yana kokarin tsayar dashi kan samarin dake gabanshi.

Ganin sun tsaya yasa shi tsayawa shima, bangon gidan da suka tsaya din ya jingina dashi, yana neman nutsuwa komin kankantarta.

'Ka nutsu Altaaf, mai gyara kawai zaka tafi dashi, a duba muku motar ku wuce, babu abinda zai faru, babu abinda zai faru, yau zata wuce, zaka koma kamar kullum, kamar komai da kauyen nan bai faru ba'

Haka yake ta nanatawa cikin kanshi, amman zuciyarshi taki amincewa, sallamar da samarin suka rafka na sashi kallon su. Sai da sukayi har sau biyu, tukunna Altaaf ya ji alamar motsi.

Da gudu wani yaro da bazai shige shekara shidda ba ya fito yana dariya, wata yarinya na rufa mishi baya. Baisan me yasa idanuwanshi na sauka kansu yaji zuciyarshi tayi tsalle tana son fitowa daga kirjinshi ta bisu ba. Fuskarsu yake kokarin gani.

"Hassan! Hussaina!..."

Altaaf yaji an fadi dai-dai bakin kofar, kamun wani saurayi ya fito da a tsayi da girman jiki yafi Altaaf din, yabi bayan yaran dake wasan zagaye zagaye yana riqo hannuwan su.

"Ba zaku samun ciwon kai da daren nan ba, ku koma gida"

"Kawu ni tare dakai zan koma..."

Macen daya kira da Hussaina ta fadi, muryarta na dira kunnuwan Altaaf da wani yanayi da yasa zuciyarshi matsewa, idanuwanshi na fara sauka kan fuskar yaran da bakin shi ke motsi da alamar magana yake, amman sauti da duk wata kara ta daina isowa kunnuwan Altaaf.

Bama sauti kadai ba, duka duniyarshi ta tattaru ta tsaya cak kan fuskar yaron, har cikin kunnuwanshi yake jin dokawar da zuciyarshi take yi, hannuwanshi duka biyun ya kai yana shafa fuskarshi, yana son tabbatar ma da kanshi cewar tana nan tare dashi.

Sosai yake shafa fuskarshi, saida yaji daga bakinshi, ido, hanci duka suna nan jiki tukunna ya sauke hannunshi yana sake ware idanuwanshi kan yaron, duk da fuskarshi yajita a jikinshi, kuma ta yaron tafi tashi qaranta bai hana shi jin kamar tashi aka cire aka liqa a jikin ta yaron ba.

Ammi nason hoto, tunda can, dan tarin Albums dinsu kawai da hotuna tun suna yara da tasowarsu kawai zaka gani kasan haka. Yasan yanda yake yana shekarun yaron nan dake tsaye, kuma kamar shine aka ciro aka ajiye. Dakyar ya iya dauke idanuwanshi daga kan yaron yana mayarwa na yarinyar.

Dankwalin dake kanta ya kalla, cikin zuciyarshi ya hango yanda zaiyi in an daura mishi dan an saka mishi kayan mata, kuma kama zaiyi sak da yarinyar. Baisan kafafuwanshi sun karasa dashi wajen ba, saida yaji su cikin durqushe cikin kasa.

Kusancin dake tsakanin shi da Ammi mai girma ne, amman ba iri daya bane sam da kusancin da yake ji tsakanin shi da yaran nan. Ko Majida kusancin ta daban yake da abinda yake ji yanzun. Yanayi ne da babu kalaman da zasuyi mishi adalci.

Hannu yakai zai taba su ko zai tabbatar da gaske yana ganin su, yaji an hankade shi yana faduwa a zaune cikin jar kasar dake wajen.

"Malam lafiya? Meye haka?"

Saurayin da Hassan ya kira da kawu ya fada a tsawace, yana dawo mishi da sauti cikin kunnuwan shi, su kuma yaran na komawa bayan kafafuwan shi suka boye suna leqen Altaaf din.

"Tawfiq tare muke..."

Daya daga cikin saurayin ya fadi yana sa Tawfiq juyawa ya kalle su.

"Lafiya?"

Ya bukata dan har lokacin a harzuqe yake, baima jira amsar suba ya sake juyowa yana kallon Altaaf, wannan karin yana tsayawa kan fuskar shi. Sosai yake kallon shi. Kasumbar dake kwance a fuskarshi bai hana kamannin shi da Hassana da Hussaina kin fitowa ba.

Ware idanuwa Tawfiq yayi yana saka hannuwa duka ya ja yaran ya sake mayar dasu bayanshi cikin son kare su daga Altaaf. Mikewa Altaaf yayi yana kallon Tawfiq, ya bude bakin shi yana rufewa yafi sau biyar. Marin da Tawfiq ya dauke shi dashi na saka haske gilmawa ta cikin idanuwanshi kamun yaji wani tsuu cikin kunnen shi na gefen dama...!
[11/30, 10:16 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

03

**

ABUJA

Bayanta ne a riqe kamar zai karye haka take jinshi, ga zazzabi tun na jiya da yake jikinta har safiyar yau.

"Sugar..."

Ta kira Rafiq dake kwance akan cinyarta, dan da alama haka suka kwana, ganin bacci yake hankalin shi a kwance yasa ta saka hannunta cikin sumarshi tana yamutsawa. Bude idanuwa yayi da addu'ar tashi daga barci a bakin shi, ganin Tasneem yasa shi mikewa babu shiri.

Kallonta yake da mamakin me yake a dakin ta, kamun komai ya dawo mishi. Muryarshi da bacci a jikinta har lokacin yace

"Neem?"

"Lokacin Sallah yayi"

Shine abinda tace tana mikewa, wani irin jiri ya kwashe ta, cikin zafin nama Rafiq ya riqo ta

"Me yasa baki da hankali ne wai? Baki san ba'a so daga tashin ka daga bacci ka mike ba?"

Yai maganar yana kokarin saita bugun da zuciyarshi take yi har lokacin. Ta hannunta daya ke riqe dashi yaji zafin zazzabin dake jikinta daya tuna mishi cewar tana bukatar ganin likita, yana riqe da ita ya mikar dasu, hannunta rike cikin nashi yake janta zuwa toilet.

Muryarta babu kwari tace

"Zan iya zuwa da kaina..."

Dan har a zuciyarta take jin kusancin shi da tasan dan raunin dayaga tana dashine yake nuna mata, a hankali take kokarin zame hannunta da Rafiq ya sake rikewa dam yajata zuwa hanyar toilet din, da kanshi ya bude ya jata ciki tukunna ya sake ta, nazarin yanayinta yake, saida ya tabbatar zata iya alwala batare data fadi ba tukunna yace

"In zaki iya kiyi wanka, zanje Sallah idan na dawo nima shiryawa zan saimu tafi asibitin, Fawzan ma nacan"

Da mamaki Tasneem ta kalle shi, kamun ya juye zuwa wani yanayi daban, tun farko ma batasan meyasa ta mamakin rashin fada mata cewar Fawzan na asibiti da Rafiq baiyi ba. Ganin tayi shiru yasa shi juyawa ya na nufar hanyar data fita dashi daga dakin.

Har lokacin kanshi da nauyi sosai, yana nufa dakin shi, bandaki ya fada, alwala yayi ya fito yana sake kayan jikinshi zuwa doguwar jallabiya ya fita masallaci, duk saurin dayai raka'a daya ya samu. Ko da ya dawo saida ya fito wanka tukunna ya dauki wayarshi. Yana shirin kiran Nuri yaji ya suka kwana ne nata kiran ya shigo, dagawa yayi hadi dayin sallama.

"Yanzun nake shirin kiran ku"

"Nasan hali ai, shisa nace bari in kira in fada maka da sauki, ya farka amman ko mintina goma baiba ya sake komawa bacci, to har yanzun"

Sauke numfashi Rafiq yayi wata yar nutsuwa na shigarshi.

"Alhamdulillah. Ina kwana..."

"Lafiya kalau, ya kuka tashi?"

Numfashi ya sake saukewa, yanajin yanda zuciyarshi ke son fadama Nuri damuwar shi amman bazai iyaba

"Sai hamdala Nuri, Tasneem ma batajin dadi, zamu taho asibitin tare anjima kadan"

"SubhanAllah... Allah ya bada lafiya ya kaimu"

Nuri ta fadi ta dayan bangaren. Rafiq ya amsa da

"Amin thumma amin. Aroob fa?"

"Karatun Qur'an take"

Dan murmushi Rafiq yayi, Aroob itace ustazziyar gidan gabaki daya daman.

"Kice ta sakamu a addu'a"

"In shaa Allah"

Sallama sukai da Nuri akan sai sunje asibitin tukunna ya sauke wayar daga kunnen shi. Yanajin nauyin ranar akan kafadun shi tun kamun garin ya karasa haske. Mikewa yayi yana nufar wardrobe, yadi ya fito dashi ruwan kasa mai haske yasa ka a jikin shi, takalmi da hula ya fiddo yana ajiyewa.

Saida ya fesa collection din turarukan shi tukunna ya fita dan yaga ko Tasneem ta shirya.

*

Dakyar ta iya yin alwala ta fito, a zaune tayi Sallah dan ko kadan jikinta babu karfi, ko azkar din safe bata yi ba, da dafa bango ta koma bandaki, ruwa mai zafi ta hada ta samu ta watsa ma jikinta, hakan bai hana wani irin sanyi ratsa ta ba, har cikin kasusuwanta. Tana fitowa kan gado ta fada tana jan bargo ta rufa.

Amman ko ina na jikinta kyarma yake, sanyin da take ji har cikin hanjinta. Tanajin hakoranta na haduwa waje daya. Ga numfashinta da take ta faman kokawa dashi yana sa kanta daukar dumin gaske. Bata san lokacin data dauka a haka ba sai jin turo kofar Rafiq tayi, ba zata iya amsa mishi sallamar da yai ba.

Hangota kan gado rufe har kanta yasa shi karasawa da hanzari yana hawa kan gadon gabaki daya hadi da kama bangon ya bude fuskarta, idanuwanta a runtse suke sai rawa da duka jikinta yake

"Yaa Rabb..."

Rafiq ya fadi zuciyarshi na sake jagulewa, dan yanayin Tasneem din kawai zaka kalla kasan ta kwana biyu bata da lafiya. Ya ma rasa abinda ya kamata yai mata, kamota yayi yana mikar da ita zaune, hakan yasata bude idanuwanta

"Amai nake ji..."

Ta fadi a galabaice, sauka Rafiq yai daga kan gadon yana taimaka mata ta sauko, riqe da ita suka nufi bandakin, sai dai banda yunkurin aman babu abinda takeyi

"Me zaki amayar? Bayan cikin ki babu komai"

Rafiq ya fada cike da damuwa, haka ya kamata suka dawo dakin. Da kanshi ya dauko doguwar riga ta atamfa da hijab ya taya Tasneem din ta saka rigar ya kwantar da ita yana fita. Yoghurt ya samo a fridge din kitchen da cup ya dawo. Ajiyewa yayi ya tasheta yana jinginar da ita tukunna ya dauki cup din ya zuba, tun kamun ya miko mata tace

"Bazan iya sha ba..."

Dan ganin yoghurt din kawai daga mata hankali yake kara yi. Girgiza kai Rafiq yayi, Fawzan da Aroob sun saka zuwa asibiti ya zame musu jiki, ba ita dashi zasuyi rashin hankalin nan ba, yasan dokokin King's Hospital, dole tasa ma cikinta wani abu. Shi Doc din zaima magana

"Ko zakiyi amai kisha, wani zai zauna"

Karba tayi ta rufe ido tana kafa kai, tas ta shanye ta mika mishi kofin tana yamutsa fuska, nazarin ta yake. Saida ya tabbatar bata yunkurin amai tukunna ya sa hannu a Aljihunshi yana kiran driver dinshi daya fada mishi cewar yana gab da shigowa.

Kasancewar basu da nisa yasa Rafiq din bai damu ba, dan ko da cikin dare matsala ta tashi kiran shi kawai zaiyi.

"Tun yaushe ne baki da lafiya?"

Ya bukata, dan jim Tasneem tayi, tambayar shi na sata tunanin yaushe rabon da taji ta da lafiya, koda gangar jikinta bata amsaba, zuciyarta akwai ciwo a cikinta. Muryarta a sanyaye tace

"Kamun bikin mu..."

Ranshi yaji ya baci ba kadan ba

"Hankalin ki bai fada miki yakamata kije asibiti ko ki fadamun ba? Damuwar da kika sani ciki bata isheki ba Neem?"

Idanuwanta taji sun ciko da hawaye, ko da taso gaya mishi din yaushe ta samu dama, tun daren farkon su komai ya canza a tsakanin su, ta ina zata fara fada mishi bata da lafiya, zai ma iya dauka dan tana neman kulawarshi ne, bude baki yayi zai sake magana ringing din wayarshi ya katse shi. Isa ne, mikewa yayi yana fita daga dakin.

Baifi mintina biyar ba ya dawo kanshi sanye da hula, hijab din Tasneem ya dauka ya bata ta saka a jikinta tukunna. Hannu ya mika mata, yana kallon yanda motsi ma wahala yake mata amman kokarin tashi take da kanta.

"Na kusan daukarki a kafadata in ba zaki bari in taimaka miki ba..."

Tasan zai iya dan haka ta kama hannun shi tana rikewa gam ya taimaka mata ta sakko, a haka suka fita har wajen motar, gaisawa sukai da Isa tukunna suka shiga bayan motar yana jansu zuwa King's hospital.

**

KAUYEN KINKIBA

Ganin Altaaf ya jima, ga kuma zaman shirun ita kadai ya soma isarta yasata kunna Wa'azin Mufti tana ji, kirane ya shigo wayarta,  hakan yasa ta dagowa daga jinginar datai da kujerar ta dauka ta duba. Ganin Aslam ne yasata dagawa hadi da yin sallama.

"Anty ina wuni..."

Amsa gaisuwar tayi, tun tanajin nauyin Antyn da Aslam yake kiranta dashi kasancewar girmarta da yayi har ta saba.

"Wayar Yaya bata zuwa... Harkun karasa ne? Ni yanzun nake shiga Zaria ma"

Da mamaki Majida tace

"Na aza dasu Ammi kuka tahi"

"No ni ina wajen aiki fa, kamun in dawo harsun wuce..."

Aslam ya amsata, jinjina kai Majida tayi

"Motar mu ta lalace bisa hanya wallahi, mun tsaya wani kauyene, Altaaf ya tahi nemo mai gyara"

"SubhanAllah... Wanne kauyen?"

Dan daquna fuska Majida tayi dan batasan kowanne kauye bane ba

"Ina zuwa in duba"

Ta fadi tana kashe wayar, data dinta ta bude, saidai network din babu karfin kirki, hakan yasata sauke glass din motar ta tambayi wani saurayi ya fada mata. Sake kiran Aslam tayi tana gaya mishi sunan kauyen

"Okay... In an wuce Zaria ne, bazan fi mintina talatin ba zanzo wajen... Sai in duba motar mu wuce gabaki daya"

"Tau, Allah ya iso dakai lahiya"

Ya amsa da amin yana kashewa. Ajiye wayar tayi kan cinyarta tana komawa ta jingina da kujerar. Sosai take jin tagaji ga yunwa data fara damunta.

*

Marin da Tawfiq yai mishi na dawo da wani abu cikin kanshi. Da sauri samarin da suka rako Altaaf suka karaso suna riqe Tawfiq da fadin

"SubhanAllah... Tawfiq me yai zafi haka"

Ture su yayi, yana maida hannuwanshi baya yana sake boye yaran a bayan kafafuwan shi. Idanuwan shi cike da wani irin yanayi dan tsallen da zuciyarshi tayi da ganin Altaaf har cikin wuyanshi yajita. Yanzun kam kamar yana dandana dacin da take mishi kan harshen shi yace

"Kuskure na biyu da zakayi yau banda sake tako kafafuwanka kinkiba shine shiga ta gida in fito in sameka..."

Hannu Altaaf yasa cikin sumar kanshi yana harmutsawa kamun ya sauke shi yana yin tafiya da baya taku biyu, ya dora hannuwanshi duka biyun kan kugunshi yana sauke su, cikin shi da hanjin ciki sukeyin kamar suna tsinkewa ya dafe. Dariya ta kubce mishi da bata da alaqa da nishadi.

Kai da kake nesa da Altaaf yanayin daya shiga zaka iya cewa sabon hauka ne yake shirin kama shi, shi da kanshi yanajin kamar haukan dan lokaci ne ya same shi, dan yanda kanshi yake cunkushe da rashin yiwuwar abinda yaki yarda ko zuciyarshi ta furta mishi.

Wata dariyar ce ta sake kubce mishi dayaga yanda Tawfiq yaja yaran suna komawa kofar da suke fito, musamman dayaji shigar su ta tafi da wani bangare na zuciyarshi da bai taba sanin yana dashi sai yau ba. Samarin da basu san meke faruwa ba suka karaso inda Altaaf yake daya daga cikin su cike da rashin jin dadi yace

"Kayi hakuri dan Allah"

Kallon shi Altaaf yayi kamun ya sake kwashewa da dariya, cikin shi na yamutsawa yana fada mishi koda wanne lokaci abinda duk yaci dayai saura a cikinshi yana gab da fitowa. Juyawa Altaaf yayi yana nufar hanyar da suka biyo wajen zuwa.

Kaman wanda yasha wani abu haka yake hade hanya wajen tafiya. Ikon Allah ne kawai yasa yagane inda suka bi wajen zuwa, yanda jikin shi baya tare da nutsuwa ko kadan, bazai ce ga yanda akayi yazo ba, motar Aslam yake gani kusa da tashi. Sai Majida a tsaye da alama hirar da suke da Aslam din ta dauke musu hankali dan babu wanda ya kula da karasowar shi.

Ganin Majida ya kara hautsina mishi lissafi.

'Kasan anyi hwada sosai tsakanin dangin Innata dana babana kan auren mu, sukaita hidin baba ya amince ne saboda kudi, baka da halin kwarai'

Maganganun Majida suka dawo mishi, jikin shi ya dauki dumi kaman lokacin ne ta zagaya hannuwanta tana sake kwantar da kanta a kirjinshi

'Yanzun kau da babbar murya zan hidi ma kowa mijina mutumin azziqi ne, bani kadai nike alfahari dashi ba har yaran mu ma zasuyi'

Cikin shi ya sake jin ya yamutsa, zazzabin nan take yana kamashi

'A-Tafida kamata yayi ace duk garin da zaka sauka a dinga sanarwa kowanne gida su adana yaransu wallahi, ka soma bani tsoro, da gaske cikin ka Abida ta zubda last week?'

Maganar Jamal bata gama dawo mishi ba, Majida ta katse mishi da fadin

"Wai, har ina kukaje haka? Wayarka bata zuwa kuma?"

Kallonta kawai Altaaf yakeyi da wani irin yanayi a fuskarshi da yasata karasowa tana nazarin shi, hannun takai tana riqe habarshi da juyo da gefen fuskarshi, abinka da farar fata, yatsun Tawfiq ne kwance kan kuncin shi. Ware idanuwa Majida tayi, kamun tai magana Altaaf ya ture ta yana matsawa gefe.

Amai ya soma kwarawa, hakan yasa ita da Aslam sukai kanshi. A rikice take dafa shi tana fadin

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

"Daman bashi da lafiya ne wai?"

Aslam ya tambaya ganin yanda Altaaf din ke kwara amai kaman zai fiddo kayan cikin shi. Girgiza mishi kai Majida tayi idanuwanta cike da hawaye, muryarta na rawa tace

"Lahiyar shi kalau muka hito wallahi... Bansan miya same shi ba"

Ruwa Aslam yaje ya dauko a cikin motarshi yaba Majida. Altaaf ta mika ma ya karba ya kurkure bakinshi yana wanke fuskarshi, dakyar ya iya mikewa, Majida ta kama hannunshi, jin zafin ya wuce misali yasata saurin kai hannu ta taba wuyanshi da fuskarshi, zazzabin data ji yasata mantawa da shatin yatsun data gani kwance kan fuskarshi

"Miya same ka wai? Jikinka da zahi kwarai"

Ta tambayeshi, girgiza mata kai kawai yayi, dan bayajin zai iya magana, har lokacin cikin shi yamutsawa yake yi

"Sannu.... Aslam ma ya duba motar hwa, mu tahi kawai sai muje asibiti"

Majida ta fadi

"Gaskiya kam... Jiba yanda har fuskarshi ta kumbura"

Aslam ya ce cike da damuwa. Bude mishi kofar motar Majida tayi ya shiga. Ita ta zagaya mazaunin driver ta zauna tana ma Altaaf din sannu, shi kam hannu yakai yana sake sauke kujerar ya kwanta a jiki sosai ya rufe idanuwanshi.

Yanajin har Majida ta ja motar suka soma tafiya. Ba asibiti yake bukata ba, ba magunguna yake so ba, rashin lafiyarshi bata da alaqa da duk wannan, ALKALAMIN KADDARA ne yake son bude mishi shafin rubutun da yake zaton ya disashe, rubutun daya jima yana addu'ar kar ya gifta ko ta

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment