Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi ba.

"Saida na tambayeki ko akwai abinda ya kamata ki fadamun kikace babu, ke kika amince Zafira?"

Fawzan din ya karasa tana dago kanshi ya tsare ta da idanuwa.

"Ni na amince dakaina. Bawai zai zabi abinda zai cutar dani bane ba..."

Mikewa tsaye Fawzan yayi yana kai kawo cikin dakin.

"Me kike so in fadama Yaya Rafiq? Zafira me kike so ince mishi? Karo na farko daya bude bakinshi yace in kula daku...me yasa zaki amsa Daddy baki sanar dani ba?"

Kallon shi Zafira take yanda yake jan numfashi kamar yana dandana iskar.

"Ni dai dan Allah karka daga hankalin ka. Zan fadama Yaya nice na amince dakaina ba dole akai mun ba..."

Jinjina kai Fawzan yayi

"Yeah kin kyauta sosai. Gobe daurin aurenki, za'ai sauran abubuwan bayan jarabawarki ta karshe..."

Ya karasa maganar yana ficewa daga dakin hadi da doko kofar kamar zai karyata. Kafafuwanta Zafira taja ta mayar kan gadon tana kwanciya. Zoben dake hannunta take wasa dashi. Zoben Muneeb da takejin dole ta cire shi daga gobe take wasa dashi. Zuciyarta ta riga ta gama bushewa, ta karbi kaddarar datazo mata da hannuwa biyu.

BAYAN SATI DAYA.

Kallo daya zakai ma Zafira ka tabbatar babu kwanciyar hankali a tare da ita. Dakyar ta gama jarabawar da take da ita a ranar ta dawo gida. Inda Allah ya taimake ta bata barin karatu ya tarar mata, da babu abinda zata iya rubutawa. Kuma jarabawar tazo mata da sauqi fiye da yanda ta fahimta. Kwance take cikin daki, dan yanzun ko abinci Aroob ce take kawo mata dakin.

Batason fita. Nuri batai mata magana ba, dan tana tunanin bata san abinda zata ce mata ba. Hakan kuma ya mata dadi. Wayarta kuwa tun ranar take a kashe har yau bata kunna ba. Ta roqi Aroob da karta fadama Fawzan. Tabarshi tukunna, yanda aka bankado kofar tasan ba lafiya ba. Mikewa tayi babu shiri.

"Kinsan lefenki ake karba a falo yanzun haka?"

Fawzan ya tambaya yana tsare ta da idanuwanshi da suka canza launi saboda bacin rai. Bata ce komai ba, idanuwanta ke zafi saboda babu sauran hawaye a cikinsu. Tayi kuka harta godema Allah. Cikin dakin ya shigo sosai yana samu waje gefen gadon ya zauna hadi da dafe kanshi da hannuwa.

"Ya Fawzan dan Allah karka wani damu... Kaga kar ciwon ka ya tashi..."

Zafira ta fadi hankalin ta a tashe. Karshen abinda zata so a yanzun bai wuce ciwon Fawzan din ya tashi ba.

"Saida na tambayeki ko akwai abinda ya kamata ki fadamun kikace babu, ke kika amince Zafira?"

Fawzan din ya karasa tana dago kanshi ya tsare ta da idanuwa.

"Ni na amince dakaina. Bawai zai zabi abinda zai cutar dani bane ba..."

Mikewa tsaye Fawzan yayi yana kai kawo cikin dakin.

"Me kike so in fadama Yaya Rafiq? Zafira me kike so ince mishi? Karo na farko daya bude bakinshi yace in kula daku...me yasa zaki amsa Daddy baki sanar dani ba?"

Kallon shi Zafira take yanda yake jan numfashi kamar yana dandana iskar.

"Ni dai dan Allah karka daga hankalin ka. Zan fadama Yaya nice na amince dakaina ba dole akai mun ba..."

Jinjina kai Fawzan yayi

"Yeah kin kyauta sosai. Gobe daurin aurenki, za'ai sauran abubuwan bayan jarabawarki ta karshe..."

Ya karasa maganar yana ficewa daga dakin hadi da doko kofar kamar zai karyata. Kafafuwanta Zafira taja ta mayar kan gadon tana kwanciya. Zoben dake hannunta take wasa dashi. Zoben Muneeb da takejin dole ta cire shi daga gobe take wasa dashi. Zuciyarta ta riga ta gama bushewa, ta karbi kaddarar datazo mata da hannuwa biyu.

Aroob ce ta shigo dakin jikinta sanye da doguwar riga ta material, sai wata irin hula saman kanta, fuskarta tasha kwalliya marar hayaniya.

"Ki tashi, ba su Asma sunata kiran wayarki a kashe tun jiya. Zasu shigo ba sai kowa yagane me yake faruwa ba..."

Can kasan makoshi Zafira tace

"Dan Allah ki kirasu kice suyi zamansu. Ba sai sunzo ba. Daurin aure ne kawai gobe in Allah ya kaimu. Kome za'ayi ku bari sai na gama exam dina"

Zafira ta karasa maganar tanajin kamar ba ita ba. Kamar wata ce daban duk wannan abubuwan suke faruwa da ita.

"Bansan me zance musu ba. Ki tashi ki shirya. Inajin Faiza na maganar wani party ko meye....sanda kika cema Daddy eh bakiyi tunanin duk wannan ba ai..."

Tashi Zafira tayi ba sai Aroob taci gaba da fada mata kuskuren datai ba, kamar yanda takanyi a duk satin nan. Gani take kamar laifinta ne duk abinda yake faruwa yanzun. Sai lokacin ta kula da wata milk din riga a hannun Aroob din da yanayin da take ciki bai hanata ganin kyawunta ba. Gefe Aroob ta ajiyeta tana fadin

"Ki sake watsa ruwa. Ga riga nan..."

Mikewa tayi, batai mamakin ganin rigar ba. Tunda daman sune abinda Aroob take dinkawa, tun tana aji uku secondary tace tana son koya, Rafiq kuma ya goyi bayanta, shekara biyu da yake tana son abin ta zama kwararriya sosai, tana da bangare a cikin gidan da take da keku nanta. Sosai take ciniki a family dinsu, duk da saita ga dama dinkin nata.

Wanka tayi ta fito. Ta shafa mai, Aroob tai mata kwalliya mai nauyi saboda ta boye duk wani alamu na rashin bacci da damuwa. Sannan ta fice tana barinta dan tasa rigarta. Dawowa tayi da hular da tafi tata ado tana tayata gyara gashin kanta da ba wani yawan kirki gareshi ba, dan haka basu dauki lokaci ba. Ta saka hular. Ita kanta saida ta yaba da kyawun da tai, akwai wani gyale daga kafadar rigar ya dauka zuwa baya cikin yanayi na kayatarwa.

Waje ta samu ta zauna. Tana jin yanda kirjinta yai wani irin nauyi, sai dai nauyin baisa ta daina jin rashin wani bangare na zuciyar ta da zai kasance tare da Muneeb har abada. Sama-sama take jin ihun su Asma'u da suka shigo, dariyar su da duk wata magana da sukeyi. Murmushi ne kawai ta dora saman labbanta, idanuwanta da wani irin nisantancen yanayi.

Tanajin in wannan ya dafa ta sai wancen ya rikota, hasken da take gani yana gilmamawa ta cikin idanuwanta kawai yake tabbatar mata da hotuna ake dauka. Bata san waya kamata ya mikar da ita tsaye ba, sama-sama take jinta, hasken camera dai taci gaba da gani cikin idanuwanta, kamun taji kamar anason saka mata wani abu a kafafuwanta.

Daga kafafun tayi Aroob ta taimaka mata tasa takalman. Kamun suja ta, ko gani batayi sosai, har lokacin murmushin da ta dora yana kan fuskarta, tana jin suka shigar da ita mota, Aroob d Asma na zama gefenta. Akaja su inda batasan ko ina bane ba. Amman sanin zuri'arsu bazai wuce gajeran taro na tayata murna ba.

*

Basu dawo gidan ba sai bayan isha'i, abinci ma Aroob ce ta matsa mata taci shi. Bawai dan taso ba, ranar a dakin suka kwana ita da Aroob. Washe gari da sukai sallar Asuba ita bata koma ba, nan ta zauna kan kafet din tana dora kanta gefen gadon ta. Jikinta ya mata sanyi, juyawa tayi ta bude drawer din gefen gado ta dauko wayarta dake ciki tana kunnawa.

Karfe takwas da rabi na safiya, ance daurin auren ta karfe goma ne na safiyar ranar. Dubawa tayi wani bangare na zuciyarta na fatan ko da saqo dayane na Muneeb tagani. Ga tarin saqonni daga mutane dake nemanta a kashe suna fatan lafiya amman babu nashi ko daya.

Inda hotunan kan wayar suke ta shiga, tana bude folder din da hotunan shine kala-kala. Zuciyarta ta numfasa da wani yanayi da ko ina na jikinta sai da ya karba, dan yatsa tasa tana shafar fuskarshi.

"Allah ya baka farin ciki fiye da wanda nake tunanin zan iya baka..."

Ta furta kamar yana ganinta, hawayen da ta kwana biyu bataji alamarsu ba suna cika mata ido da zubowa kan kuncinta da wani irin dumi, tanajin zafinsu tun daga zuciyarta ne. Bankwana take son mishi amman ta kasa furta kalaman ko a zuciyarta. Tanajin agogon dake mata yawo cikin kai, agogon da yake qure mata.

Kamun wani lokaci har goma saura, duka takai ma Aroob dake bacci, a firgice ta mike tana kallon Zafira.

"Saura minti sha biyar Aroob.....Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, wallahi saura mintina sha biyar..."

Zafira take fadi wani irin tashin hankali da bata taba sanin shi ba yana lullube ta, asalin abinda auren wani ba Muneeb ba yake nufi a tare da ita yana zauna mata a zuciya. Gunjin kuka ta saki da yake fitowa daga karkashin zuciyarta. Sakkowa daga kan gadon Aroob tayi tana riqw Zafira dako ina na jikinta ke kyarma.

"Allah yasa hakan ne mafi alkhairi a duniyarki da lahirarki...."

Aroob ke fadi hawaye masu dumi na zubo mata. Inda zata iya ko yayane zata daukema Zafira wani ciwon da take ji. Girgiza mata kai Zafira takeyi tana kuka kaman zata shide.

"Bazan iya mishi bankwana ba, bansan ya zan rufe wannan kofar ta rayuwata ba...."

Zafira take maganar cikin kuka. Riqeta Aroob tayi sosai, tana rasa ta inda zata gaya mata basaita yi kokarin rufe kofar rayuwar soyayyarta da Muneeb ba, ALKALAMIN KADDARArsu ya riga ya rubuta musu yanda komai zai faru, lokaci kawai suke jira. Wayar Zafiran dake rike a hannunta ta fara kuka, da sauri ta duba, Muneeb ne.

Dagawa tayi ta kara a kunnenta tana sakin wani irin kuka.

"Duk yanda naso kar in kira na kasa Zafira, yau kawai kamun goma ta cika ina son sake jin muryarki kamun ki zama mallakin wani..."

Muneeb ya karasa tanajin dacin dake tattare da sautin muryarshi ta cikin wayar, yanayin dake kara gudun kukanta.

"Kice mun wani abu dan Allah, saura mintina uku kacal halaccin magana dake ya tsayamun.... Ki mun magana..."

Girgiza kai take tana jan numfashi cikin son koyayane muryarta ta fito, amman abin ya faskara, kuka take da bata taba irinshi a rayuwarta ba, batama taba zaton zata iya irin shi ba sai yau. Ta dauka ta hakura ta gama kukan, amman muryarshi ta dawo mata komai sabo.

"Yaa Mu... Muneeb.... Muneeb...."

Ta samu furtawa numfashinta na wani tsai-tsaiyawa.

"Nagode da komai. Nagode da soyayyarki duk da bata kaimu inda na hango mana ba. Saura minti daya...."

Kuka ta sake rushewa dashi muryarta na sarqewa take fadin

"Ina sonka sosai.... Wallahi ina sonka. Allah ya baka farin ciki..."

Tana jin numfashin da yake ja yana fitarwa a kunnenta. Muryarshi a sarqe shima yace

"Allah ya sanya miki alkhairi da albarka. Ki kasance cikin farin ciki..."

Ya karasa yana kashe wayar, dawo da ita Zafira tayi saitin fuskarta tanajin kamar ta bulla ta ciki ta ganshi na karshe. Lokaci ta gani, karfe goma dai-dai. Cilli tai da wayar tana haduwa da bango, kararta na ruguza sauran abinda ya rage a zuciyarta, da sanin cewa ta zama matar wani dako sunanshi bata kai da sani ba, wani irin numfashi taja fitar dashi na mata wahala. Kamun wani duhu ya gilma ta cikin idanuwanta.

Can sama-sama taji Aroob ta rikota tana fadin

"Zaf! Zafira!!"

Kamun gabaki daya duniyar tai mata wani irin shiru....!

ALHAMDULILLAH...!!! KARSHEN KASHI NA DAYA. YANZUN TAFIYAR TA FARA. NAGODE DA DUKKAN KAUNARKU.

#AnaTare
#TeamAK
#FWA


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment