Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce yasa shi jefa wayar kan gado yana fita zuwa Masallaci abin shi.

Ciwon kai zata kara mishi ya sani, ko da aka idar da Sallah, zamanshi yayi a masallaci saida yayi Azkar din yamma tukunna ya nufi gida. Sai dai me yana shiga falo yagan su zaune ita da Fawzan suna hira a falo suna dariya. Numfashi ya sauke yana shiga da Sallama, su duka biyun suka amsa

"Sannun ku da gida"

Yace batare daya kalle su ba ya wuce yana nufar bangaren shi.

"Raafik..."

Samira ta kira, juyowa yayi fuskarshi babu walwala, yana kuma ganin yanda Fawzan ke murmushi, yasan yanda taja sunanshi ne yake ba Fawzan din nishadi, su duka suna kara mishi ciwon kan da yake ji.

"Bansan sau nawa zan gyara miki ba. Rafik, ki daina jan Raa din, kuma Q ne ba K ba... Rafik"

Ya fadi ta tsakanin hakoranshi. Saboda gab yake da daga musu murya su bar falon ko su kyale shi yaji da abinda yake damun shi. Yana kallon Samira ta taso daga inda take tana takowa zuwa inda yake. Jikinta sanye da doguwar riga ta farin less mai jar filawa, sai wata irin hula ja akan ta. Ya kuma tabbata a haka ta fito batare da wani mayafi ba.

"Me ya sami wayarka?"

Ta tambaya tana sauke idanuwanta cikin nashi.

"Siyarwa nayi"

Ya amsa yana tsare ta da idanuwa. Shagwabe fuska tayi

"Tun yaushe nake kiranka baka dauka... Na maka message yafi talatin baka mun reply ba... Ya kake so inyi? Kwana tara yau... Ban saka a idanuwana ba... Dan na damu da jin lafiyarka ya zama laifi Raafik?"

Idanuwanshi ta janye daga kanta yana kallon Fawzan dake zaune a falon ya zubo musu idanuwa. Tsare shi yayi da nashi idanuwan, babu shiri ya mike yana hade fuska.

"Ki kirani in kun gama..."

Yace ma Samira data daga mishi kai batare data juya ba tukunna ya fice daga falon. Hankalin shi Rafiq ya mayar kan Samira dake kallon shi idanuwanta cike taf da hawaye. Karshen abinda zaiso shine ta fara kukan ta da baya karewa.

"Hidimomi ne sukai mun yawa Samee, kina kira lokuttan da banda halin dagawa..."

Hannu tasa tana share kwallar data taru gefen idanuwanta tukunna ta sake kallon shi

"Ka kalleni... Ka kalli idanuwa, me kake so in zama akanka? Danne daraja da jifa da kunyata ta ya mace nace ina sonka kawai bai isa ba? Bai kai ka dinga mun sassauci ba?"

Runtsa idanuwanshi yayi yana bude su akan ta.

"Ina son ki"

Ya fadi. Lumshe idanuwa tayi ta bude su a hankali.

"Ba kalar son da nake maka ba..."

"Samee kaina namun ciwo. Kiyi hakuri ya kamata ko sau daya in bi duk kiranki. Happy?"

Dan guntun murmushi ne ya kwace mata duk da zuciyarta dake ciwo, son shi na mata yawo, ko ba komai yau nasara ce tunda ya amsa ya kamata ya kirata, hakuri ba wani abu bane a wajen Rafiq in har yayi kuskure. Akanta ne dai yake da wuyar sha'ani, kuma alaqarsu ta sake jagulewa ne daga lokacin da ta fada mishi zuciyarta na doka mishi ta wani fannin daban.

Ya bata hakuri nan take ya kuma ce bai taba mata kallon daya wuce kawarshi ba. Sam baya jinta kamar yanda take jinshi. Saidai ba zata daina binshi ba, wata kila ko tausaya matane yayi, tayi nisan da zata iya samun matsala in bata same shi ba.

"Tam ka rakani in tafi gida saika sha magani ka huta...kar in dameka..."

Bai ce komai ba ya fara tafiya yana nufar kofa, murmushi take, tabi bayanshi. Bayason wani surutu daban, inma catai ya rakata har gida zasu tafi sai Fawzan yabi bayansu ya dawo dashi. Bazai iya dogon surutu da Samira ba. Suna fita harabar gidan motar Daddy nayin parking. Saida zuciyar Rafiq tai wani tsalle kamar zata fito daga kirjinshi.

Da kanshi ya karasa yana bude ma Daddy murfin motar hadi da fadin

"Sannu da zuwa..."

Tun kamun ya fito, da kai ya amsa Rafiq din,tukunna ya fito, jakar dake hannun shi Rafiq ya karba, zuciyarshi babu komai a ciki banda ganin yayi wani abu dazai burge Daddy koya yake, ya manta yanda ya fara tunanin zaiyi musu dashi akan wani abu. Haka Daddy yake, yanayin shi kawai yana cika idanuwan mutane tun kamun su san kowanene shi.

"Sannu da zuwa..."

Cewar Samira da Rafiq ya manta tana tsaye a wajen. Murmushi Daddy yayi suna gaisawa cikin fara'a.

"Zan wuce Daddy. Allah ya huta gajiya..."

Hannu Daddy ya mika yana kama jakarshi dake hannun Rafiq.

"Bani ku tafi abinku..."

Sakar mishi Rafiq yayi yana murza hannunshi da yake jin alamar zufa a jiki yabi bayan Daddy da kallo.

'Allah kaban karfin zuciya...'

Ya fadi a zuciyarshi. Dan zabura yayi saboda Samira data tafa hannuwanta a saitin fuskarshi.

"Kana wacce duniya?"

Daquna mata fuska kawai yayi, tayi dariya kamun tace

"Na tafi, dan Allah ka daga in na kiraka"

Dakai ya amsata, ta juya tana tafiya, tsaye yayi a wajen gabaki daya gwiwoyinshi babu kwarin kirki. Cikin gida yake son shiga, amman ganin Daddy ya tuna mishi yanda musa magana dashi kawai ke daukarshi satittika yana tattaro duk wani karfi dayake dashi, balle kan abu babba har haka. Wani yawu ya hadiya, yasa hannu yana dafa zuciyarshi dake tsalle ya lumshe idanuwanshi yana maida numfashi cikin son samun nutsuwa ko yaya take. Ya kai mintina biyu a haka kamun ya bude idanuwan shi yana takawa zuwa cikin gida....!

©
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

IN THE LOVING MEMORY OF SAIFULLAHI (Allaahummaghfir li SAIFULLAHI warfa' darajatahu fil-mahdiyyeena, wakhlufhu fee 'aqibihi fil-ghaabireena , waghfir-lanaa wa lahu yaa Rabbal-'aalameena, wafsah lahu fee qabrihi wa nawwir lahu feehi. Amin thumma amin)

10

Ya kai mintina biyu a tsaye bakin kofa yana maida numfashi. Kamun dakyar kafafuwanshi sun mishi nauyi yaja su yana shiga babban falon gidan. Baiga kowa ba sai TV da take kunne, yasan Daddy na bangaren shi, Nuri ma tana can. Dakinshi yake son zuwa ko kwanciya yayi kamun Daddy ya gama hutawa yaje suyi magana.

Amman sam bayason ko motsawa daga inda yake saboda bayajin kwari a jikinshi, samu yayi ya karasa kan doguwar kujera ya zauna, kwanciyar na gagararshi. Kanshi da yake ciwo ya ci gaba da sarawa kamar zai fado, hakan yasa shi dafe shi da duka hannuwanshi. Baiji shigowar Aroob falon ba, sai maganarta da yaji

"Yaya? Lafiyar ka kuwa?"

Sauke hannuwanshi yayi yana kallonta, hadi da girgiza mata kai. Zai iya boyema kowa halin da yake ciki, banda su, wasu lokuttan in basu tambaya ba, yakan kyalesu dan bayason raba damuwarshi dasu, shiya kamata ya rage musu nauyin tasu duk sanda bukatar hakan ta taso. Amman indai suka tambaya, zai fada musu. Karya itace karshen abinda zai taba hadashi da kannen shi.

"Meya sameka? Menene? Nuri tace Daddy zai dawo. Shine ko? Me yai maka?"

Aroob ta karasa maganar muryarta na karyewa. Hannu Rafiq ya mika mata dan bayason yin magana, nata tasa cikin nashi yana janta ta karasa ta zauna kan kujera a gefenshi tukunna ya saki hannun nata.

"Me yasa Daddy yake haka? Duk inya dawo sai ya maka wani abin..."

Ware mata idanuwanshi Rafiq yayi cike da kashedi, hakan yasa tai shiru tana turo bakinta.

"In kawo maka ruwa?"

Ta bukata, tambayar nasa shi jin yanda makoshin shi ya bushe. Kai ya sake daga mata, ta mike tana dawowa da glass cup da ruwa a ciki ta mika mishi, saida ya karba tukunna ta zauna. Shanyewa yayi duka yana maida numfashi kamun yace

"Nagode..."

Jinjina mishi kai tayi. Tana kallon damuwa shimfide a fuskarshi da bata san yanda zata tayashi daukarta ba. Ta kuma tabbatar Daddy nada sa hannu cikin damuwar tashi. Tunda Nuri tace musu zaizo ranta yake a jagule. Lokutta da dama tafi son yai zamanshi, dan duk idan yazo saiya bullo da wani abin da tsantsar takura ce a wajen su.

Badan zuciyarta bata cike da kaunar Daddy ba, sai dan bata son yanda yafi takura Rafiq din da dawainiyar dake sakashi cikin damuwa, tasan kuma yana daukane harda tasu, dan takurar da yake shiga harda son karta karaso kansu.

"Yaya ina son zuwa gidansu Juwairiyya..."

Ta fadi dan janye tunaninshi daga koma menene kadai hanyar da take da ita. Dakuna mata fuska Rafiq yayi.

"Me ya hana?"

Ya bukata, dan tasan dagashi har Nuri basu taba hanasu ziyarar yan uwa ba. Zumunci na cikin manyan abubuwan da suke da muhimmanci a wajen Nuri.

"Ina so in kwana ne..."

Kai ya girgiza mata.

"Kije ki wuni ki dawo..."

Turo baki Aroob tayi

"Ba makaranta fa Yaya..."

Kai ya sake girgiza mata, hakan nasa shi runtse idanuwanshi saboda yanda hakan yasa kan ci gaba da sara mishi.

"Baya aiki Aroob, surutun na karamun ciwon kaine"

Rafiq yace yana dan dafe kan nashi. Ya gane bawai gidansu Juwairiyya take son zuwa ba, hankalin shi take son daukewa daga damuwar da yake ciki. Agogon dakin ta duba, biyar har tayi, da sauri ta dauki remote tana karo maganar TV din, kamun ta dauki dayan ta canza tashar zuwa star plus. Aikam sun saka shirin da take son kallo din na Saloni.

Yanda ta tattara duka hankalinta kan shirin ne yasa Rafiq fadin

"Yanzun meye dadin shiriritar nan?"

Ware mishi idanuwa Aroob tayi cike da mamaki.

"Hmm Yaya baka san dadin ba wallahi, ya hadu sosai. Kaga ita saloni din ko? Saboda kalar fatarta yasa bata samu miji da wuri ba, gashi iyayen suna musguna mata, to wani maikudi aka shirya yazo neman auren kanwar, amman basu fada mishi cewar yayarta bata da aure ba..."

Dakuna mata fuska yayi

"Saboda me?"

"Aisu abune marar kyau sosai kanwa tayi aure yayarta batai ba, to an shirya taje wajen addu'a ita saloni din, kamun suzo..."

Sauke numfashi yayi, ko kadan Aroob ba gajiya take da surutu ba yasani.

"Aroob yi kallon ki..."

Dariya tayi tana kyaleshi hadi da maida hankalin ta kan shirin da take kallo, shima idanuwanshi kafe suke kan TV din amman baya fahimtar komai, saboda nutsuwarshi bata tare da kallon sam. Baisan iya lokacin daya dauka zaune a wajen ko kuma ga asalin abinda yake tunani ba, sai dai ji yayi Aroob ta taba shi.

"Sallah ake kira..."

Ta fadi, sai da ya dan daga mata kai tukunna ta wuce, dakyar yaja jikinshi zuwa dakinshi ya dauro alwala ya fito ya wuce masallaci, ko daya idar da Magrib yai nafilarshi saya saba ta bayan Magrib, Qur'an ya dauka ya zauna ya bude yana karantawa da sautin da kunnuwanshi ne kawai suke ji. A nan ya zauna yanajin yanda nutsuwa ke shigar shi a hankali.

Baibar masallacin ba saida akai sallar isha'i tukunna. Saidai me kamar damuwarshi jira take ya fito ta sake samun wajen zama tare dashi. Ga zuciyarshi da gabaki daya ta karye lokacin daya shiga cikin gida. Bai kara jin faduwar gaba ba saida yaga Nuri zaune a falon. Sallama yai mata muryarshi da sanyi.

"Nuri..."

Ya kira a karo na farko da ganin ta ya kasa samar mishi kwarin gwiwar da yake bukata.

"Yana ciki..."

Nuri ta fadi muryarta na fin tashi sanyi. Numfashi yaja mai nauyi yana saukewa kamun ya nufi bangaren Daddy zuciyarshi na wata irin dokawa. Zufa yaji a tafin hannunshi lokacin daya dago dashi yana kwankwasa kofar.

"Yes..."

Daddy ya fada daga cikin dakin, muryar shi dauke da yanayin nan da yakan sa mutanen dake kusa dagowa su kalli wanda yake dauke da muryar duk sanda zaiyi magana. A hankali Rafiq ya tura kofar yana shiga hadi dayin sallama. Daddy yana zaune cikin shigar shadda ta alfarma, zaka rantse wata fita zaiyi babba, bawai zaune a babban falon gidanshi ba.

Kallon shi Rafiq yake yi daga nan bakin kofar ya kasa karasawa ciki, sam bayason jin ko wanne bayani ne Daddy yake son mishi, baya son jin yanda ya gama yanke hukunci akan Zafira, yanda babu wanda ya isa ya canza hakan. Runtsa idanuwa yayi yana ganin fuskar Zafira.

Farin cikin dake cikin idanuwanta lokacin da take gaya mishi abinda ke tsakaninta da Muneeb, fuskarta kawai ta nuna mishi yanda Muneeb yake da muhimmanci a wajenta. Girgiza kai yayi a hankali, saidai a madadin fuskarta, ta Muneeb ce ta cika mishi zuciya. Tashin hankali da tsoron dake bayyane akai nasa wani gashi mikewa a bayan wuyanshi.

Babu shiri ya bude idanuwanshi akan Daddy dake kallonshi a nutse, yana bashi lokacin da yake bukata kamun ya karasa cikin falon. Da sauri ya taka, yana zuwa gaban Daddy ya durkusa. Muryarshi can kasan makoshi yake soma fadin

"Dan Allah kar kai mana haka....Daddy karkai amfani da rayuwar Zafira a matsayin tsanin dagawar ka....a karo na farko farin cikin mu ya zo sama da naka....ina roqon ka ne Daddy... Dan Allah karkai haka..."

Rafiq ya karasa muryarshi na karyewa, bazai tuna lokacin karshe da hawayenshi suka zuba ba. Saboda raggontaka na daya daga cikin abinda Daddy baya so. Amman yau a shirye yake da ya zubda su akan Zafira, akan farin cikin kanwarshi.

"Ba karamin gida bane ba, yaro ne daya fito daga gidan mutunci..."

Daddy ya amsa cikin yanayin da babu kofar gardama. Murmushin takaici Rafiq yayi

"Gidan mutunci Daddy? Babban gida? Waye shi?"

"Dan gidan Alhaji Modibbo..."

Jinjina kai Rafiq yayi yana zama dirshan, fuskarshi cikin hannuwanshi, numfashi yake mayarwa a hankali, babu kalaman da zasu bayyana abinda yake ji. Bai kuma da karfin gardama da Daddy.

"Bama abinda na kiraka danshi kenan ba. Akwai abinda nake son siya a China, ina son kaje ka dudduba mun kamun in tura kudin..."

Sai lokacin Rafiq ya dago da kanshi ya kalli Daddy cikin rashin fahimta.

"Maganar auren Zafira din fa?"

"Sati biyu zakai, inka dawo sai muyi maganar da kyau"

Wani abune can kasan zuciyar Rafiq yake mishi wani iri, haka kawai bai amince da tafiyar ba, badan zai iya ce ma Daddy a'a ba, abune da bai taba faruwa ba, bakuma yajin daga yau za'a fara. Amman kawai bayason tafiyar.

"Daddy..."

Ya soma, katse shi yayi da fadin

"Kar kaja maganar nan. Saika dawo tukunna..."

Numfashi Rafiq ya sauke

"Yaushe zan tafi?"

"Gobe in shaa Allah. Da yamma... Nasa an gama komai tun last week"

Kai kawai Rafiq ya daga yana mikewa. Badan bashi da abinda zai fada ba. Sai dan yasan maganar su ta yau da Daddy ta kare, bakuma zai saurari komai ba. Hakan yasa shi ficewa daga dakin yana jan kofar.

*

Wayarta take ta kallo, tun karfe takwas ya kamata Muneeb ya kirata, lokacin wayarsu ne yanzun. Koda wani uzurin ya rikeshi yakan mata text ya fada mata. Yana gama abinda yakeyi kuma zai kira. Tun dazun take mamakin ko sakon shi bata gani ba.

Ba fada sukayi ko wani abun ba, koda ma sunyi shariya ba halin Muneeb bane. Yakan mata sakon cewar har lokacin fa bai hakura da laifin da tai mishi ba. Ta dauki wayarta tana ajiyewa da nufin kiranshi yafi sau biyar. Bata yanke hukuncin kira ba sai da taga har takwas da rabi tayi bata ji shi ba.

Saidai harta yanke bai daga ba. Zuciyarta da take a jagule ta sake jagule mata. Saida ta kira sau hudu bai daga ba tukunna ta tura mishi sako.

'Dan Allah ka daga...ina bukatar jin ko lafiyarka'

Sai da ya shiga, taga alamar ya bude tukunna ta tattara duka nutsuwarta kan wayar ko zata ga amsar shi amman shiru, zuwa lokacin wasu hawaye masu zafin gaske sun cika mata idanuwa. Hannuwanta biyu tasa tana share su. Kamun ta sake daukar wayar ta kira har sau biyar wannan karin batare daya daga ba. Tana ajiyewa qarar saqo na shigowa.

Da saurin gaske ta dauki wayar ta bude saqon

'Dan Allah ki kyaleni, zan kiraki dakai na in inason magana'

Tun kamun ta karasa karatun hawaye sun soma zubar mata. A karo na farko a rayuwarta da taji wani abu kamar yana budewa a kirjinta da ciwo marar misaltuwa. Da sauri takai hannu cikin rigarta tana tabawa ko da gaske tsagar har a wajene. Bataji komai ba, dakyar take jan numfashi saboda ciwon da take ji a wajen.

Ga hawayen sun sa dishi-dishi take ganin screen din wayar balle harta samu ta rubuta wani abu. Dakyar ta samu hawayen suka dan tsagaita mata. So take ta tuna kota mishi wani laifin ne amman ta kasa, mamakin da take shine ko da take mishi laifi bai taba fada mata maganar datai mata zafi har haka ba.

'Idan na maka laifi ne ka fadamun sai in baka hakuri, in kuma akan boye soyayyarmu ne, na fadama Yaya Rafiq dazun'

Ta rubuta tana turawa.

'Banda karfin maimaita magana daya. Ki duba sakona na farkon'

Ya sake dawo mata dashi. Wasu sabbin hawayen na sake zubo mata. Bata taba sanin haka tashin hankali yake ba sai yau. Ji take kamar babu wadatacciyar iska a dakin. Wani kuka mai sauti ya kwace mata. Wayar ta ajiye tana saukowa daga kan gadon, bata damu da cewar kanta babu ko dankwali ba. Asalima riga da wandone na bacci da akafi ma laqabi da Pyjamas a jikinta.

Fitowa tai daga dakin, tafiya take tana sa hannu tana share hawayen dake bin fuskarta, zuwa lokacin dalili daya ta samu da zaisa Muneeb ya datsa mata magana haka. Inba dai Rafiq ya same shi ya ce ya rabu da ita ba. Bata kuma ga dalilin dazai sa yai mata hakan ba. Ko gani bata yi sosai, bata ga Fawzan ba saida taci karo dashi.

"Hakora kike son ciremun ne da da..."

Fawzan ya soma, kallon dayai ma fuskar Zafira da kuma hawayen daya gani nabin kuncinta ya katse mishi maganar daya soma.

"Inalillahi... Zafira... Menene? Me akai miki? Me ya faru?"

Fawzan yake tambaya hankalin shi a tashe. Da duk tambayar da zai mata da yanda kukan ta yake tsananta. Gabaki daya ta daga mishi hankali. Hannuwan shi yasa yana tallabar fuskarta hadi da goge mata hawayenta. Amman wasu ne suke sake zubowa.

Zaice tun girmansu yaune karo na farko da yaganta tana kuka haka. Duka gidan babu mai hakuri da kawaicin ta. Bai taba ganin yarinya mai hankalin ta ba, bawai dan tazo a kanwarshi ba.

"Dan Allah ki daina kukan nan Zaf, ki fadamun ko menene..."

Kai take daga mishi, tana saka hannuwanta kan nashi dake fuskarta, numfashi take mayarwa. Cikin kuka take kokarin magana.

"Ya... Ya... Yayaa Rafiq...."

Taja kalmar tana sake fashewa da wani kukan. Fawzan bai jira wata kalmar ta sake fitowa daga bakinshi ba ya saki fuskarta yana kama hannun ta. Bangaren Rafiq yajata suna nufa, kwankwasa kofar yake kamar zai karyata. Ya daga hannu da shirin kwankwasawa aka bude kofar.

Baki Rafiq ya bude rai a bace, ganin Zafira yasa shi mayarwa ya rufe. Kallonta yai na yan daqiqai kamun ya maida hankalin shi kan Fawzan fuskarshi dauke da alamun tambaya.

"Ban sani ba wallahi. Ganin ta nayi tana ta kuka. Na tambaye ta kome akai mata, ta kira sunan ka tana ci gaba da kuka..."

Fawzan ya fadi cike da damuwa. Daga mishi gira duka biyun Rafiq yayi cikin yanayin dake fassara 'Me hakan yake nufi?'

"Na dauka ko kai take son magana dakai shisa..."

Sauke numfashi Rafiq yayi yana dan runtsa idanuwanshi ya bude su a hankali.

'Daddy bakai mun haka ba. Baka fada mata ba... Kace saina dawo zamuyi magana...'

Yake fadi a cikin ranshi, saidai kadan cikin aikin Daddy, zai fada musu abinda yasan suna sonji ne wasu lokuttan, yayi shi abinda yai niyyar yi, saboda babu wanda ya isa ya canza mishi ra'ayinshi. Hannu yakai ya riqo na Zafira dake cikin na Fawzan yana janta zuwa cikin falon yakaita kan kujera ya zauna.

Har lokacin kuka take da yake ji har bayan zuciyarshi. Cup ya dauko yana zubo mata ruwa ya bata, saida ta karba tukunna ya samu waje ya zauna. Sosai tasha ruwan tana ajiye cup din kan table din dake kusa da ita. Kallon Rafiq tayi da idanuwanta da suka rine saboda kukan da bata daina ba har lokacin.

"Me yasa Yaya? Ka fadamun dalili... Wallahi zan hakura dashi in har bai maka ba....amman ka fadamun dalili..."

Ta karasa muryarta na karyewa, wasu hawayen na sake bin fuskarta. Saboda yanayin shi ya nuna cewar yayi magana da Muneeb din, saidai tana son sanin dalilin da baya sonta dashi. Bai taba nuna mata wani hali marar kyau ba, ta yarda da Rafiq da dukkan rayuwarta, zata iya rabuwa da Muneeb koda shine karshen bugawar da zuciyarta zatai indai ya fada mata dalilin dazai gamsar da ita.

Mikewa tsaye Rafiq yayi. Ba Daddy bane yaima Zafira magana. Muneeb ne ya sata wannan kukan, in ranshi yayi dubu ya baci, ya dauka ba saiya roki Muneeb ba, zai bar yi mata magana sai shi ya fara tukunna, ya dauka hankalin Muneeb yakai nan.

"Me yace miki? Muneeb, meya ce miki Zafira?"

Rafiq ya fadi ta tsakanin hakoranshi saboda yanda ranshi yake a bace.

"Wanne Muneeb din? Me yake faruwa ne wai?"

Fawzan dake tsaye yana kallon su ya fadi. Wani irin kallo Rafiq ya watsa mishi daya sashi fadin

"Allah ya baka hakuri..."

Yana ficewa daga dakin gabaki daya. Hankalin shi Rafiq ya mayar kan Zafira.

"Me yace miki?"

Ya sake maimaitawa. Dan daga kafadarta tayi, tana jan hanci, kamun ta goge fuskarta da fadin

"Bayason maganar komai dani....baice mun komai ba..."

Tsugunnawa gabanta Rafiq yayi yana riqo hannunta.

"Nayi magana da Muneeb dazun... Kina jina... Akwai abinda yake faruwa, Daddy ya aikeni China, gobe in Allah ya kaimu zan tafi. Kiba Muneeb sararin da yake bukata har saina dawo....zanyi magana da Daddy. Ki daina kuka... Komai zai tafi dai-dai...."

Shi kanshi magana kawai yake badan yasan abinda yake fada ba. Gaskiya yake son fada mata batare daya fada mata asalin gaskiya ba a lokaci daya bai kuma san yanda zaiyi hakan ba.

"Ina sonki da Muneeb.... Kar wani abu ya fada miki akasin hakan... Ina sonki da Muneeb..."

Kai take daga mishi, hawayen da bayason ganin na sake zubar mata. Ta wani fannin tadan samu nutsuwar jin Rafiq din na sonta da Muneeb. Ta fannin da yafi dayan girma na cike da tsoron meye yake faruwa din. Amman ta yarda da Rafiq, ta yarda cewar zai gyara komai kamar yanda ya fada.

"Zakai magana da Daddy? Zaka fada mishi?"

Kai ya daga mata, yana son taga yanda zai iya komai dan farin cikinta. Kilan hakan tagani yasa ta goge fuskarta da dayan hannunta tana mikewa. Shima tashi yayi yana riqe da hannunta har lokacin. Tare suka fita ya rakata har bakin kofar dakinta yaga ta shiga ta turo kofar tukunna ya juyo yana nufar dakin Fawzan.

Kwankwasawa yayi shiru, hakan yasa shi turawa da Sallama. Fawzan din na zaune kan kujera da remote a hannunshi, ganin shigowa Rafiq din yasa shi danna remote din yana qure maganar tv din data cika gabaki daya dakin, tana karama Rafiq ciwon kan da yake fama dashi.

Baice komai ba, ya zagaya yana kashe switch din kayan kallon gabaki daya.

"Kallo nake..."

Fawzan ya fadi yana kin kallon Rafiq din.

"Aure Daddy yake son yi ma Zafira. Bashi bane babban tashin hankalina Fawzan. Tana soyayya da Muneeb..."

Girgiza mishi kai Fawzan yakeyi tunda ya bude baki yana magana harya kai karshe, kallon shi yake kamar wani bakon abu ya fito a fuskarshi da baisan dashi ba.

"Bai bani dariya ba ko kadan Yaya..."

Fawzan ya fadi yana sake girgiza kai.

"Saboda ba wasa bane ba..."

Shiru Fawzan yayi yana jin yanda hanjin shi suke kullewa waje daya saboda tashin hankali, numfashi yake ja a hankali yana jin yanda wucewar shi ta soma mishi wahala saboda ranshi a bace yake. Ba kuma na wannan lokacin bane ba, yana hadowa da wasu na baya ne suna kare mishi taron dangi.

Sai yaushe ne rayuwarsu zata zama fiye da tsanin takawa wajen nasarar Daddy? Sai yaushe ne zai daina musu haka, yaushe zai fahimci suma suna da bukatu nasu nakansu kamar shi. Kanshi ne ya soma daukar zafi kamun yaji kamar ana gobara cikin makoshin shi da take karasawa zuwa kirjinshi tana tsayawa.

Wani irin jan numfashi yake kamar zai shide. Da gudu Rafiq ya karasa inda yake, shisa bayason fada mishi wani abu dazai bata mishi rai, yanzun Asthmar shi zata tashi. Inhaler dinshi ya lalubo yana saka mishi a hannu, ya kai baki yana dannata.

"Fawzan dan Allah ka kwantar da hankalin ka. In ba so kike zuciyata ta buga ba yau...Shisa banso fada maka ba... Ya kuke so inyi?"

Ya karasa yana riqo Fawzan din hadi da dagashi ya ja shi zuwa inda gadonshi yake ya kwantar dashi. Har lokacin bai gama dawowa dai-dai ba. Nan gefen gadon ya zauna yana dafe kanshi dayake sarawa. Ko tunani ya kasayi, wani amai ma yakeji saboda rashin nutsuwa. Bai fita daga dakin ba

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment