Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kira Number din Fawzan, har tai ringing ta yanke bai dauka ba. Dan daquna fuska Rafiq yayi, yasan Fawzan sarai, in ya kwanta koda baccin rana ne to bashi da lafiya, balle kuma bayan Asr.

Ba wayarshi yake sakawa a silent ba. Sake kira yayi, wannan karin ma harta yanke bai daga ba, mikewa yayi yana nufar bangaren Fawzan din, harya kai kofar dakin shi, kwankwasawa yayi yaji shiru, dan haka ya tura yaji kofar a kulle. Baisan me yasa zuciyarshi ke mishi wani iri ba.

Wayarshi dake dayan hannun yai swiping, har ya soma saka number din Nuri, sai kuma ya fasa, Aroob ya kira, dokawa daga ta dauka.

"Hello Yaya..."

"Aroob, kina kusa da Nuri?"

Ya fara tambaya.

"A'a gidan Hajiya Turai mukazo, suna dakin ta. Ka kira wayarta ne? Ko in kai mata"

Girgiza kai Rafiq yayi kamar tana ganin shi, kamun ya dora da fadin

"Nazo gida ne, babu kowa sai Asabe. Tace Fawzan yana nan, kuma dakin shi a kulle. Ban san ko meye ba... Kawai bana jin yanayin namun dadi"

"Ka kira wayarshi to...amman yace babu inda zaije da zamu fita"

Dan dafe kai Rafiq yayi, yana maida numfashi.

"Shine damuwar, na kira sau biyu bai daga ba"

Da sauri Aroob tace

"Bari in gwada kira in gani"

Rafiq bai amsata ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana sakata cikin Aljihu. Hanyar da zata fitar dashi daga gidan ya nufa, motocin da suka rage ya kirga, yaga biyune kawai babu. Yasan Abba ya dauki daya, su Nuri sun fita da dayar. Lokaci daya zuciyarshi ta soma dokawa.

Wajen maigadi yaje ya tambaye shi ko yaga fitar Fawzan din.

"Tun bayan La'asar daya shigo gaskiya bai fita ba, su Hajiya ne kawai..."

Rafiq bai jira ya gama ba da gudu ya juya cikin gidan, zuciyarshi naci gaba da dokawa kamar zata fito daga kirjinshi. Yana shiga falo, wayarshi na soma kara, daukowa yayi ya daga kiran. Muryar Aroob cike da damuwa tace

"Wallahi bai daga ba, wajen kira biyar. Me yake faruwa ne yaya?"

Shi kanshi cikin damuwar yake, ga zuciyarshi da taqi daina bugawa, dakyar ya iya dai-dai ta muryarshi.

"Ban sani ba tukunna Aroob. Ki nutsu, ina kuke ajiye keys din gidan nan? Karki fadama Nuri komai tukunna... Kina jina?"

"Suna... Su... Su"

Dafe kai Rafiq yayi, jin yanda Aroob din take jan Numfashi, yasan tashin hankali ko bacin rai na saurin tasar mata da Asthma dinta.

"Aroob...Aroob! Ki nutsu dan Allah. Kinga gama Fawzan din na kira na...Kashe in amsa..."

Kashewar tayi kuwa, sai yanzun yake ganin shirmen kiran dayai ma Aroob din, baya son hankalin Nuri ya tashi ne shisa, to gara nata da Aroob din. Wayar Nuri din ya kira, tana shiga kuwa ta dauka.

"Assalamu alaikum. Rafiq kazo bama nan ko?"

Nuri ta fadi da murmushi a muryarta. Lumshe idanuwanshi yayi, muryarta na sama mishi yar karamar nutsuwa. Duk da bai iya ya amsa mata Sallamar da tayi ba.

"Nuri ina kuke ajiye spare keys dinku? Inajin Fawzan na dakinshi, kuma ya kulle, inata kira bai daga ba, na kwankwasa ma shiru.... Jikina namun wani iri..."

Ya karasa yana kai hannu da goge zufar da yake ji a goshin shi, har hannuwanshin ma sunyi zufa saboda tashin hankalin da yake ji.

"Ka duba a dakina, wajen drawer din gado, duka suna ciki"

Kai yake dagawa tunda ta fara magana.

"Rafiq... Ka nutsu... Ga munan zuwa muma"

Kan ya sake dagawa, baisan kafafuwan shi ma na daukar shi zuwa bangaren Nuri ba, bai cire wayar daga kunnen shi ba saida yaji ta kashe kiran daga can bangarenta tukunna, Aljihu ya mayar sanda ya tura dakin Nuri da ya shiga, inda tace mishi din ya nufa kuwa, yana janyo drawer din farko yagansu a ciki, daukowa yayi yana komawa bangaren dakin Fawzan.

Soma gwada mukullan yayi a jikin kofar, yasa sunkai guda goma, amman babu wanda ya bude mishi kofar, ga hannunshi da dukkan jikinshi dake bari, bai taimaka wajen nutsuwar da yake buqata ba.

"Damn it..."

Ya fadi yana dukan kofar da kafarshi.

"Fawzan... Dan Allah kar abinda ya same ka..."

Ya fadi muryarshi can kasa, zuciyarshi kaman zata fado, babu mukullin da bai gwada ba a jiki amman sunqi budewa.

"Asabe! Asabe!! Asabe!!!"

Yake kira cikin karaji da kosawa, ci gaba da kiranta yayi babu kakkautawa, kamun ta karaso da gudu. Mukullan hannunshi Rafiq ya mika mata

"Bude mun kofar nan"

Ya bukata muryarshi a dakushe da yanayin da yake ji. Tsayawa yayi yana kallon ta tana saka kowanne mukullin kaman yanda yagama yi babu jimawa, saida ta gwada kowanne tukunna ta kalle shi, muryarta a dan tsorace da yanayin da take gani a ciki

"Hajiya tace wani lokaci in anga haka, akwai mukulli a jikin kofar daga ciki"

"Damn it Fawzan..."

Rafiq ya fadi yana ja da baya, hadi da dukan kofar da kafadarshi. Amsawar da tai kamar kashin wajen ya karye na aikama kwakwalwar shi da wani irin radadi mai zafi gaske. Sake gwadawa yayi amman ko motsin kirki baiji kofar tayi ba. Matsawa ya sake yi da baya yana sa kafarshi wannan karin dai-dai inda wajen mukullin kofar yake.

Sau hudu yai hakan, wajen ya karye, kofar na budewa, Asabe na tsaye tana kallon shi dan bata san me ya kamata tayi ba. Da gudu Rafiq ya shiga dakin, kafafuwan shi suka tsaya cak, ganin Fawzan kife a kasa, hannun shi daya mike da alama yana son daukar wani abune, inhaler dinshi dake can gefe Rafiq ya hango.

Girgiza kanshi yake yana fadin

"Fawzan... No... No... No... Please No..."

Zuciyarshi na gaya mishi ya karasa ya taba Fawzan din, yanda yake ganin shi kwance ko alamun numfashi babu a jikinshi balle yai motsi na kara ma bugun zuciyarshi gudu cike da bayananne tsoron daya nuna har akan fuskar shi. Cikin karfin halin da bayaji sam ya karasa yana tsugunnawa.

Hannunshi na bari ya dafa kafadar Fawzan, kamun yasa dayan hannun yana juyo dashi, idanuwan Fawzan din rabi a bude, rabin su a lumshe, sosai ya jashi yana dorashi a jikinshi hadi da girgiza shi

"Fawzan... Fawzan... Dan Allah ka tashi. Karkai mana haka... Ba zakai mana haka ba... Ka tashi"

Fawzan bai ma san duniyar da yake ba, balle yaji me Rafiq yake fadi, dube-dube yake a dakin cikin tashin hankali ko zaiga wani abu dazai taimaka musu, mukullin motar Fawzan din ya hango. 'Asibiti' wata murya ta fada mishi. A hankali ya sauke Fawzan daga jikinshi yana dauko mukullin motar ya saka a Aljihunshi.

Dawowa yayi ya tallabi Fawzan da yake jin ya mishi nauyin gaske, dakyar ya kaishi waje yana maida numfashi. Wajen motar Fawzan din ya karasa dasu, yana jingina rabin jikin Fawzan da motar, rabi da jikinshi ya dauko mukullin ya bude bayan motar. Dakyar ya samu ya saka Fawzan a ciki tukunna ya rufe yana zagayawa ya zauna mazaunin driver.

Yana saka mukullin motar a jiki, ya murza, kanshi na bugawa kamar wanda aka dokawa wani abu, numfashi yaja da sauri yana fito dashi. Steering wheel din yake kallo, zuciyarshi na bugawa fiye da dazun. Hannu yasa a jiki, kanshi ya sake bugawa a karo na biyu. Runtsa idanuwanshi yayi, jan abu yake gani, ko ina cikin kanshi kamun ya fahimci jini ne, da sauri ya bude idanuwanshi yana kallon motar a tsorace.

Juyawa yayi ya sake kallon Fawzan dake kwance a bayan motar, yasan ya kamata yaja su tafi Asibiti, hannun shi ya kai jikin steering wheel din, kanshi ya sake dokawa, kamar zai rabu da gangar jikinshi. Dukan steering wheel din yayi da karfin gaske yana sakin karamar kara saboda ciwon da kanshi yakeyi har a ko ina na jikinshi.

Ya manta rabon daya gwada tuqi, ya manta azabar da yake shiga duk lokacin da ya gwada yin hakan, kaman yanda ya kasa tuna dalilin faruwar hakan. Dan sosai yake tuna lokutta da dama da yake kai kanshi ko ina a mota, harma da kannen shi.

"Fawzan na kasa.... Na kasa wallahi"

Ya fadi muryarshi na rawa kaman zai fashe da kuka. Jikinshi ko ina bari yake yi. Dafe fuskarshi yai cikin hannuwanshi biyu yana jin komai ya hade mishi waje daya. Yana rasa da abinda ya kamata yaji, sam baiji bude murfin motar ba, sai dafashi da yaji anyi.

Hakan yasa shi bude fuskar yana kallon kafadarshi kamun ya maida dubanshi inda Nuri take tsaye.

"Nuri..."

Rafiq ya fadi yana fitowa daga motar da sauri, ganinta nasa duk wata damuwa da yake ciki sake danne shi, rungumeta yai a jikinshi, zuciyarshi na ciwo, yana jin kaman ya cire ta ya ajiye a gefe.

"Na kasa Nuri..."

Yana jin tana daga mishi kai da yake fassara ta fahimta. Kamun ta zame jikinta daga riqon da Rafiq din yai mata.

"Shiga bayan muje.... Aroob koma tacan bangaren"

Cewar Nuri, su dukansu abinda tace din sukai, Rafiq na dago Fawzan zuwa jikinshi sannan ya zauna yana rufe murfin motar.

*

Da gudu aka shiga daya daga cikin dakunan dake ward B na King's hospital da Fawzan da aka sama oxygen mask kamun a shiga dashi. Binsu Rafiq yake shirin yi. Nuri ta riko hannunshi tana girgiza mishi kai. Kallon ta yake cike da tashin hankali.

"Da baku zo ba... Da sai dai ya mutu? Nuri me yasa ba zaku fadamun abinda yake damuna ba? Me yasa bana iya tuqi?"

Kallon juna Nuri da Aroob sukayi. Kamun Nuri ta maida hankalinta kan Rafiq daya daquna fuskarshi kamar zaiyi kuka.

"Munzo yanzun ai, babu abinda zai same shi..."

Girgiza mata kai Rafiq yakeyi, wannan karin yana son sani. Waje ya samu ya zauna cikin daya daga cikin kujerun silver din dake wajen jiran. Muryarshi can kasa yake kallonta.

"Ina son sani, ina son sanin koma menene Nuri"

Juyawa Nuri tayi bata son Rafiq din yaga hawayen dake cike da idanuwan shi. Ta fanni da yawa mantawarshi alkhairi ce, halin da yake ciki yanzun yafi sauqi akan wanda zai shiga in yasani.

"Nuri..."

Rafiq ya kira sunan ta, dakyar ta samu nutsuwar data juya ta kalle shi sosai cikin fuska. Damuwa ce shimfide cikin idanuwan shi, ta rasa yanda akai bata kula da ramewar da yayi ba, dan tafi karfin ta tashin hankalin da yake faruwa dasu yau din nan.

"Ba yanzun ba... Wani lokacin Rafiq"

Yanayin yanda tai maganar a gajiye ne yasa Rafiq din jingina sosai da kujerar yanayin shiru. Ko ba da Nuri ba, baya son jan magana. Aroob ce ta karasa gefen Rafiq ta zauna, a hankali ta matsa tana kwantar da kanta a kafadarshi, dan kallon ta yayi, hakan ya sata riqo hannunshi ta dumtse cikin nata tana fadin.

"Komai zaiyi dai-dai"

Sauke numfashi yayi, in da tasan yanda yake tsananin bukatar jin kalaman nan da ta sake maimaita mishi. Lumshe idanuwanshi yayi kawai yana ci gaba da maida numfashi.
[11/30, 10:16 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

02

LAGOS

"Kaifa kace zaka barni, ko bikin Yaya Rafiq banje ba... Haba dan Allah"

Zafira ta karasa maganar tanajin hawayen bakin ciki na cika mata idanuwa. Musamman yanda Omeed din ke daura agogo a hannun shi kamar bai tarwatsa mata farin cikin datai wata daya da kwanaki tana tarawa ba.

"Yanzun kuma na fasa, ko ban isa ba?"

Ya bukata batare daya juyo ba, asalima hular shi ya dauka yana karyawa. Hadi da zuwa ta gaban Zafira dake zaune bakin tanqamemen gadon dakin yana daukar daya daga cikin turarukan daya fiddo ya ajiye akai. Hawayen da take tarbewa ne suka zubo

"Amman inkai haka bakaimun adalci ba wallahi... Kai kace zaka barni, kai ka fada"

Sai lokacin ya juya ya kalleta, hawayen tana bata mishi rai, dan in akwai abinda ya tsana bai wuce hawayen rashin dalili ba, in yana son ganin su zai bata dalili mai karfi da zata zauna tana mishi kuka ba karamin abu irin wannan ba.

"Ke adalci zakimun? Duka jiya na dawo, bakyajin wani iri ki tafi har kwana hudu kibarni ni kadai? Sayrah fa?"

Hannu Zafira tasa ta goge hawayen fuskarta, wasu na sake zubowa

"Kai kace bazan tafi da ita ba, kace wajen Mami zaka kaita, sati biyu zakai Omeed, dan Allah karka hanani, kaine dalilin kin zuwana bikin Yaya, dan Allah, ko kwana biyu ne..."

Girgiza kai Omeed yayi alamar a'a duk da yanajin rashin kyautawar hakan, yasan tafi shi gaskiya, sai dai son kanshi bazai bari ta tafi ba. Ya rasa me yasa ita ba zata fahimci bayason kona kwana daya tai nisa dashi ba, balle har kwana hudu, ko yana wajen aiki ne kuwa, zuciyarshi na nutsuwa sanin tana gidan shi.

Ganin yaci gaba da shiryawarshi baice mata komai ba yasata kara magana

"Dan Allah ko kwana biyu ne, kaga har fada musu nayi nace zanzo cikin satin nan..."

Zafira ta fadi zuciyarta na mata kuna da kewar gida data yan uwanta, ta kusan wata takwas bata ga Nuri ba, gara ma Fawzan yazo ya kawo Aroob tai mata sati, shima an fi wata hudu. Shirun dai Omeed yasa ke yi

"Duk sanda kaso kake zuwa kaga naka 'yan uwan... Bansan me yasa kake hanani zuwa ganin nawa ba"

Ta fadi muryarta na rawa saboda bacin rai

"Bana son jan magana, kin kuma sani. Ba zaki ba"

Girgiza kai Zafira take, tagaji, sosai take jin gajiya da Omeed din har a kasusuwan ta

"Ba wannan karin ba Omeed...ba wannan karin ba, nagaji Wallahi..."

Hularshi a hannu yake shirin hanyar fita daga dakin, ta mika tasha gabanshi, hawaye na zubo mata

"Dan girman Allah kabarni, kwana daya kawai, dazan iya wuni daya ma zanyi, roqarka nake Omeed..."

Sauke numfashi yayi, hawayen ta naci mishi rai, haka nacin da take ya soma juya mishi kai. Rabata yazo yi ta sake tare hanyar, baisan lokacin daya dauke ta da mari ba, duk da ba bakon abu bane, marin ya mata bazata, har lokacin kunnenta na barin haggu dum take jinshi.

"Babu inda zaki"

Omeed ya maimaita, baisan sau nawa take so ya fada ba kamun ta gane. Ba marin ke kara gudun hawayenta ba, bata san me yasa fuskarta takasa sabawa da zafin ba, amman zuciyarta da alama ta fara sabo da hakan.

"Me yasa? Me yasa baka son barina zumunci da yan uwana?"

Ta tambaya muryarta can kasa, tana son sanin dalili, yau tana so ya fada mata ko da zai sumar da itane, inta farfado saiya fada mata dalilin shi, ganin yan uwanta ko ba komai zai sata shakar iska daban data gidanshi, zai bata karfin gwiwar sake ci gaba da jure zama dashi, ya kasa gane tana bukatar ganin su saboda dalilai da yawa.

Kanshi yaji ya fara juya mishi, in ranshi yai dubu ya baci, rabon da Zafira tai mishi gardama irin tayau tun farkon auren su, hannu yasa ya hankade ta gefe yana nufar kofa, yana da abu mai muhimmanci dayake bukatar yi, inya tsaya zata kara bata mishi rai ne.

Amman me bai kai kofa ba ta biyoshi da gudu, tana riqe hannun kofar, kuka take sosai wannan karin

"Ko me zakai mun kayi, dan Allah kabarni nidai, ina bukatar zuwa... Ina bukatar shakar iska daban data gidan ka, ina son wani ya fadamun ina da hankali da nake zaune dakai... Omeed ina son ganin mahaifiyata... A karo na farko a shekaru ukku ina son ganinta in fada mata damuwa ta.... Ina son in kalli fuskarta inji ko zama dakai ne abinda ya kamata..."

Tunda ta fara magana zuciyarshi tai tsaye waje daya. Jin dalilin dayasa take son zuwa gida na kara gudun bacin ranshi, yana saka tsoro a wani bangare na zuciyarshi

"Rabuwa kike shirin yi dani? Gida kike son zuwa dan ki rabu dani?"

Yake tambaya yana cilli da hular dake hannun shi hadi da dauke Zafira da wani irin mari da saida ta fadi kasa. Kuka ta saki mai cin rai tana kallon shi da wani yanayi da yake son ya batar daga idanuwanta da duka. Ko zata dawo hayyacinta, hannu yasa ya riqo mata kafada yana dago ta

"Baki isa ba wallahi... Babu inda zaki..."

Omeed yai maganar yana sake dauke ta da wani mari, kamun ya tureta ta fadi kasa, tana jin yatsun hannunta data fadi kansu sunyi kara, zafin hakan na kaiwa har kwakwalwarta, dayan hannunta tasa tana kama wanda take zaton yatsun shi sun karye saboda azabar da take ji yana mata, cikin wani irin kuka take bin Omeed da yake neme-neme cikin wardrobe din dake cikin bangon dakin da kallo

"Meye dalilin zama dakai? Ka fadamun dalili daya dazai sa inci gaba da zama dakai!!!"

Juyowa yayi yana sauke mata idanuwan dake cike da masifa a tsawace ya amsata

"Saboda ina sonki! Saboda kin koyamun son ki!..."

Ya karasa hannunshi na kaiwa kan belt din dayake nema ya fito dashi yana takowa inda Zafira take zaune, hakan nasata jan jiki tana matsawa cikin hanzari

"Karka dake ni... Wallahi karka tabani.... Wayyoo Allah na shiga uku.... Omeed dan Allah ka..."

Belt din daya zabga mata na sa sauran kalaman koma mata. Zafin nasata mantawa dana yatsunta tana saka hannayenta duk hadi da murza duk wani waje da belt din ya samu

"Babu inda zaki... Ba zaki barni ba"

Yake fadi yana sake zabga mata belt din, ko ta ina yake dukanta.

"Zaka kasheni ne zan zauna dakai?!"

Zafira take tambaya tana ihun dako a jikin Omeed din, dan bashi yake bukatar ji ba. Ci gaba yai da dukanta

"Ba zaki barni ba... Kina jina? Mutuwa ce kawai zata rabani dake..."

Azabar da take ji take son ta tsaya kona minti daya ne, sam Omeed yaki bari ko numfasawa tayi, gabaki daya ya gigita mata rayuwarta, jikinta babu inda bai dauki dumi ba, hawayenta kansu sun tsaya dan azaba

"Ba inda zani....wayyoo Nuri... Yayana... Omeed dan Allah kayi hakuri... Wallahi ba inda zani... Ba inda zani dan Allah kabari... Bazan sake ba"

Girgiza mata kai Omeed yake yana ci gaba, bata ji ba, yana son ta kwana biyu ko juyin bacci zatai tanajin tunin cewa ba zata barshi ba, duk ihu da magiyar da take mishi bai sa ya daina dukanta ba, yasan iya karfin da belt din yake sauka jikinta dashi, bazai fasa ba, zaibar tambari na kwanaki dai. Saida zuciyarshi ta fada mishi ya isa haka tukunna ya ajiye belt din.

Zama yayi kan kafet din gab da ita yana kamo ta jikin shi, a rikicen da take da azabar da take ji yasata fadawa jikin shi wani rin kuka na kwace mata, zata karbi lallashi ko da nashi ne tunda bata da inda zata je ta samu. Sai yanzun tasan yaudararta zuciyarta take data fada mata ta fara sabawa da irin azabar nan.

Dan satikan dayai baya nan, bai taba lafiyarta bane yasata sakin jiki, lokaci daya dana sanin jan maganar da tayi dashi yake lullubeta. Tanajin hannunshi kan bayanta yana rage mata radadin da take ji. Iska yake hura mata a gefen fuska

"Laifin kine...kin sani? Kinsan ke kikasa ni dukan ki ko?"

Kai take daga mishi hawayen ta na jika mishi gaban riga, sake riketa yayi gam yana lumshe idanuwanshi.

"Ina sonki... Me yasa kike tunanin barina? Me yasa kike tunanin zama dani kuskure ne?"

Bata son yin kowacce magana, bata tunanin kwakwalwar ta zata iya wani tunani a yanayin da take ji.

"Kina sona kema... Ki fadamun kina sona inji"

Omeed ya bukata yana gyara zamanshi da sumbatar gefen fuskarta. Sai ajiyar zuciya take saukewa.

"Ina sonka..."

Ta tsinci kanta da fadi, zuciyarta na wata irin dokawa, kaman tana son amincewa da abinda ta fada din. Yanda yake sata tana fadin tana sonshi har zuciyarta ta fara yarda da hakan. Ba zata iya wani dogon tunani ba, dan haka ta zagaya hannuwanta jikin bayanshi tana runtse idanuwanta hawaye naci gaba da zubar mata.

Duk yanda yake son fita zama yayi, bayason yabar mata dukanshi kawai a jikinta, hakan zai bata damar yin tunanin wani abu daban, baya so kuma. Dan haka ya zauna yana riqeta a jikinshi, yasan bata da wani karfin kirki ba zata jima ba zatayi bacci, inya mayar da ita kan gado saiya sauri ya fita ya dawo.

**

KANO

A gajiye Altaaf ya kalli Majida da hannunta daya yake rike da kwandon da yake cike taf da kayayyaki, dayan hannunta kuma rike da takardar datai list din kayayyakin da suke da buqata.

"Majee..."

Yaja sunanta, kaman yanda yake kiranta, dago idanuwanta tayi tana sauke su kan fuskarshi, tsaf ta karanci me yake son fadi tun kamun ya furta.

"Sai da nace hwa kai zamanka  gida, sayayyata da yawa... Kace sai ka biyoni"

Daquna mata fuska yayi.

"Tun dazun fa... Me zaki kara zubawa anan? Bazai dauka ba ma"

Kwandon Majida ta tura gaba tana fadin

"Nikau ka takura mani gaskiya, ka tai mota ka zauna in ida"

Girgiza kai Altaaf yayi yana ciza lebenshi na kasa yanda yakanyi in yanajin rikici da kuma dariyar hausar Majida da duk da sabon dayai da ita bata gajiya da sashi nishadi.

"Ya isa haka...kin dawo ke kadai ki karasa"

Bude baki tayi da shirin mishi musu, ya daga mata hannu.

"Gida zamu tafi Majee"

Turo baki tayi kawai, dan tasan bata lokaci ne musu da Altaaf, abinda yake so din dole shi za'ayi. Tana kallon shi ya kama kwandon yana juyawa hadi da nufar counter din dake cikin Mall din. Bin shi tayi a baya suka tsaya tare ana fitar da kayyakin hadi da lissafa kudaden.

Da gudu wasu yara biyu mace da namiji, dukkan su babu wanda yakai shekaru biyar suka shigo wajen, kamun matar da duk alamu mahaifiyarsu ce ta biyo bayansu tana riqo su duka biyun.

"Wallahi zamu koma in surutu zaku sakani..."

Ta fadi tana maida numfashi dake nuna da gudu ta biyo bayansu. Macen ce ta kalle ta kamar zatai kuka

"Mummy ni Ice cream"

"Noo cookies mummy"

Karamin ya fadi, dauke idanuwanta Majida tayi daga kansu tana mayarwa kan Altaaf da gabaki daya hankalinshi ya koma kansu, fuskarshi dauke da wani irin yanayi da yasata kai hannu ta riqo nashi tana matsawa cike da son nuna mishi tana tare dashi a kowanne yanayi.

Numfashi me nauyi Altaaf ya sauke yana riqe hannun Majida da yake cikin nashi sosai, dukkan zuciyar shi na tare da yaran da yake jin kamar ta bashi guda daya. Credit card dinshi ya zaro ya mika ma Majida, har lokacin yana bin yaran da ido saida suka bace mishi.

Ta mishi magana kusan hudu da su tafi dan har yaran wajen sun kwashi kayyakin su, amman bai jita ba, saida ta ja hannun shi tukunna ya juya ya kalle ta.

"Mu tai..."

Ta maimaita muryarta na rawa, baice komai ba har suka fita daga wajen. Mota ya bude ya shiga, ita tai tsaye aka gama saka musu kayan a mota, ta dauko jakarta dake ajiye a ciki ta basu dubu daya tukunna ta shiga ta zauna tana rufe murfin motar.

"Mi kake so inyi inka ci gaba da haka?"

Ta bukata idanuwanta kafe a fuskarshi, bai juyo ya kalleta ba, saida ya tayar da motar tukunna yace

"In naci gaba da me?"

Ya amsa tambayarta da wata tambayar, duk da yagane abinda take nufi, baisan yanda zai hana zuciyarshi ba, yana son yara tun tasowarshi, kuma yana da burin haihuwar nashi, amman yanzun yanda yake jin kaunarsu abin ya wuce duk wasu kalamai.

"In kana kallon kowanne yaro da zamu hadu dashi kamar zaka dauke shi, in kana kallon shi kaman ka cire rai ga samun naka..."

Majida ta karasa maganar muryarta na rawa, tun zuwansu asibiti na farko da aka tabbatar musu su duka biyun lafiyarsu kalau, hankalinta ya kwanta ta wannan fannin, tasan duk yanda suke son haihuwa in lokacinta baizo ba babu yanda zasuyi.

Duk da Altaaf yaki hakura, watannin nan yana karya mata zuciya, kullum cikin yawon sake asibiti sukeyi. Abin kara haukata yake da duk rana. Jan motar yayi yana juyawa dasu, suka hau titi. Wani abune tokare da makoshin shi daya hana shi magana.

Koda babu abin ma bashida kalaman dazai amfani dasu, baida kwarin gwiwar kallon Majida ya fada mata rashin dalilin rashin haihuwarsu, baida karfin zuciyar dazai furta ma kanshi dalilin a fili ko da shi kadaine, ballantana kuma tare da Majida.

Ganin yanda yake fisgar motar ya sa Majida jan numfashi da fadin

"Yi parking..."

Babu musu ya samu waje gefen hanyar yai parking din motar, baice mata komai ba ya fito suna masayar waje, dan yasan sam baida nutsuwar tuqi. Lumshe idanuwanshi yayi yana bude su a hankali.

*

"A-Tafida banga period dina bafa, na fada maka tun satin daya wuce"

Sigarin dake hannunshi ya kunna, yana mata wani irin ja, hadi da fitar da hayaqin cikin kwarewa.

"Me yasa kike abu kamar wannan ne karo na farko Anisa?"

Altaaf ya fadi batare daya juya ya kalleta ba, sigarin shi ya sake ja fuskarshi cike da alamun jin dadin ta da yake yi.

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment