Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyarta kamun ta cigaba da jero 'Inalillahi wa ina ilaihi raji'un' babu tsayawa. Suna nan zaune tsakar gidan Sabeena ta fito, yanda tagansu kwance jikin Tasneem haka ta samu waje itama tana kwanciya, dan bata san me yake faruwa ba. Anan makota da suka fara shigowa suka same su.

Babu irin maganar da ba'ayi musu ba kan ko basu koma daki ba, su tashi daga kasa, dan rana harta fara samun su, amman ko motsi basuyi ba. Wata mata data zo ta kama Tasneem tureta tayi da fadin

"Kuyi abinda ya kawoku ku kyalemu muji da rayuwar mu"

Aikam kyalesun sukayi. Duk wanda zai shigo sai yayi magana. Tasneem bata damu ba. Ba lallai wasu su kara damuwa da halin da rayuwarsu take ciki bayan yau ba, kamar yanda babu wanda ya damu da halin da suke ciki kamun yau, bata ga dalilin da zaisa su fara damuwa dasu yanzun ba.

BAYAN KWANA UKU.

Kasancewar waya bata yawaita ba, sai tangaraho (Telephone) da tsirarun mutane masu wadata suka mallaka, ga rashin nutsuwa, kuma yan unguwa babu wanda yasan inda yan uwan Abba suke, randa Abba ya rasu ba'a samu fadama wasu cikin yan uwanshi ko daya ba. Har sai washegarin mutuwar tukunna.

Kullum sai matansu sunzo, suma haka. Har akai sadakar ukku. Da yake su biyun da suka rage sunada wadata haka sukaita kawo buhunnan shinkafa ana dafe ma yan zaman makoki. Da ido Tasneem take binsu, dan ya zamar mata dole taci ko zata samu su Hamna ma suci, amman wannan shinkafar baqiqirin take a idanuwanta.

Basu kawo lokacin da Abba yake da rai ba, lokacin da sukafi bukatar taimako, sai yanzun da kasa ta rufe mishi ido. Su dukkansu kallo daya zakai musu kasan babu nutsuwa tare dasu. Musamman Tasneem da tayi baqi tai wata irin ramewa. Rabon jikinta da ganin ruwa kwana uku, tama manta da wani abu waishi wanka.

Haka kawai take jin duniyar na wuce mata da yanayin da ta kasa fahimta. Sabeena ta zame daga jikinta tana mikewa dakyar.

"Ina zakije?"

Hamna ta bukata idanuwanta na cikowa da hawaye. A kwanaki ukun nan ko bacci zai daukesu a jikinta sukeyin shi. Ko bandaki zataje suna biye da ita, haka zasuyi tsaye bakin kofar bandakin saita fito su sake binta.

"Bandaki zanje Hamna. Ku zauna yanzun zan dawo. Dan Allah ku zauna karku biyoni"

Ta karasa a gajiye, saida ta tabbatar ba zasu bita ba tukunna ta fice daga dakin. Ko takalmi bata damu dashi ba. Da sauri ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga gidan. Babu bandakin da zataje, iska take so ta shaqa daban data cikin gidan, numfashi take so tadanyi ita kadai ko kanta zai dan rage mugun nauyin dayake mata. Bama ta ganin hanya sosai, bata kuma san inda zata nufa ba.

"Tasneem...Tasneem..."

Ta ji muryar Tariq kamar daga sama. Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi da ke dauke da wani irin yanayi data kasa fahimta.

"Sai yau naji Tasneem, wallahi ban sani ba... Bansani ba da nazo tuntuni..."

A yanayin muryarshi kawai tagane ya fahimta, tagane duka taron mutanen dake cikin gidan bata tunanin akwai wanda ya fahimci halin da suke ciki fiye dashi.

"Ina zakije?"

Ya tambaya. Muryarta kamar batata ba ta amsa shi da

"Ban sani ba. Inason inyi numfashi ne, ina numfashi amman inason yin wani daban..."

Kai ya daga mata alamar ya fahimta, hanyar gidansu ya kama, tabi bayanshi, kamar jira take kafafuwanta su taka tsakar gidan, anan ta baje. Numfashinta take kokawa dashi, dan sai yanzun komai yake danneta, sai yanzun kukan dayaki zo mata yazo. Nan kasa ta kwanta tana sakin wani irin gunjin kuka dayasa Tariq jingina jikinshi da bangon wajen yana zamewa ya zauna.

Ba kukanta bane yasa hawayenshi zuba, ba tausayin yanayinta bane yasa shi kukan dake fitowa daga zuciyarshi. Saidai famin da yanayinta yai mishi, ba kuma ita kadai bace, ko wucewa yazoyi yaga ana zaman makoki sai yayi kuka.

Dagowa Tasneem tayi tana saka hannu ta goge hawayenta wasu na sake zubowa.

"Ya kukayi? Ya Tariq ya kuka wuce wannan yanayin?"

Muryarshi a dakushe yace mata

"Bake zaki wuce yanayin ba, shine zai miki sauki. Yanzun? Wannan lokacin bakuji komai ba Tasneem, sai babu kowa a gidan tukunna. Zakiyi numfashi kirjinki kamar zai bude, ciwon ba yanzun zakuji shi ba..."

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Tasneem ta fadi tana sake rushewa da wani sabon kukan. Jikin Tariq bari kawai yake. Yanajin yanda komai yake son dawo mishi sabo. Hannun yasa a aljihu yana zaro wata takarda a duqunqune.

Dakyar ya warwareta yana daukar wasu fararen kwayoyi guda biyu yasa a bakinshi yana tsotsa kamar duka nutsuwarshi na tare da hakan. Runtsa idanuwa yayi yana hadiyewa yana jiran su fara ratsa mishi jijiyoyin jikinshi, yanason muryoyin da suka soma ihu cikin kanshi suyi shiru. Duhun ya gama mamaye shi duka, yana son boyewa daga duniyar nan zuwa wata da duhunta bazai bari komai ya tabashi ba.

Lokacin dayaji muryar Tasneem sama-sama ya daina gane abinda yake faruwa a wajen duniyarshi.

"Na tafi kamun su Azrah su biyoni"

Dakyar ya iya daga mata kai. Hijab dinta tasa tana goge fuskarta, taja wani dogon numfashi kamun tabarshi anan tana nufar hanya ta koma cikin gida.

BAYAN WATA SHIDDA

A watannin nan Tasneem ta kara jinjina ma duk wani maraya, dan tana tsakiyar dandana maraici, zuciyarta bata sake tsinkewa saita kalli su Azrah, musamman Hamna da duk tafisu fari, yanda tai duhu, sun rame duk sun fita hayyacin su.

Sai yanzun take jinjina maganganun da Tariq ya fada mata. Sai yanzun tagane ma'anarsu. Komai bai danneta ba sai da aka watse aka barsu su kadai, ranar tai kuka kamar ranta zai fita. Maraicin na danne su da duk rana.

Da suna zuwa makaranta a kafa su dawo a kafa, saidai suna matukar wahala dan wata rana haka zasu dawo ga rana ga yunwa kuma su samu gidan babu komai. Yanzun haka suke yini, Ummi inta fita sai dare take dawowa, dan abinda ta samo ta basu haka zasuci, su rage wani da zasu ba Sabeena dan ita ba sanin halin da ake ciki tai ba.

Zullumin fadan Ummi da babu abinda yai banda karuwa ma kawai ya ishe su. Musamman randa ta dawo bata samo abinda kirki ba. Akansu zata huce da zagi da gorin yanda Abba ya mutu bai bar musu komai ba. Musamman Tasneem zatace ita tasan yanda tai Alh. Madu ya daina zuwa.

Yauma kamar kullum, su dukansu a kwance suke bayan sun idar da Sallah. Yunwa tasa ko Islamiyya sun kasa zuwa. Kallonsu Tasneem tayi, dakyar ta dafa kasa ta mike, wani haske taga ya gilma mata, kamun kanta yaci gaba da sarawa da tasan yunwa ce kawai ke dawainiya da ita.

Daki ta shiga ta dauko hijab dinta. Ta saka silifas din dahar sun huje daga tsakiyarsu saboda jikin da suka ji.

"Ina zaki je?"

Hamna ta tambaya tana tsareta da idanuwa.

"Yanzun zan dawo. Karku fita ko ina"

Tasneem tace bata jira komai ba ta nufi hanyar fita daga gidan. Hanya ta mika da zata kaita gidan Anty Asabe, yar uwar Ummi. Ba rokonta abinci zatai ba, dan tun kamun rasuwar Abba ta fahimci halin mutane, yan uwanshi ma sun watsar dasu ballantana kuma Anty Asabe dabawani kusanci suke dashi da itaba. Mutane basa taimako saboda Allah, zata roketa ne ko wanki ta dinga bata tana biyanta lada suna rage wani abin.

Dakyar ta iya kai kanta gidan saboda galabaita. Dan ko da suka gaisa, ruwan da aka kawo mata kurba daya tai mishi amman tanajin yanda cikinta ya tattare waje daya.

"Anty Asabe zuwa nai daman. Dan Allah ko wankin kune ku dinga bani saiki biyani lada, wallahi abubuwa sun mana yawa sosai. Dan Allah..."

Tasneem ta karasa muryarta na rawa. Kallonta Anty Asabe tayi, dan inba aike ba, Tasneem bata taba wanko kafa tazo gidanta ba, kuma sam yarinyar batai halin mahaifiyarta ba, ga hankali da Anty Asabe ta kula Tasneem din nada shi. Ba taimaka mata bane batason yi. Suna da mai musu wanki, mijinta yake hadawa duka yakai a wanko a goge.

"Tasneem muna da mai wanki wallahi, duk shekarun nan babansu Muhsina can yake kai mana"

"Ya Allah..."

Tasneem ta fadi idanuwanta na cika taf da hawaye, bata san ya zatai ba, tadai san tagaji da ganin kannenta cikin halin da suke. Yanayin ta da Anty Asabe tagani yasata fadin

"Sai dai akwai kawata da take neman mai aiki, tun rannan tai..."

Bata ma bari ta karasa ba ta katseta da cewa

"Zanyi wallahi, komun yawan aikin zanyi"

Dan murmushi Anty Asabe tayi

"Bansan kota samu ba, saboda wajen sati kenan da taimun maganar. Sai dai kidan jira na aiki Muhsina, inta dawo yanzun sai in aikata gidan muji"

Jinjina kai Tasneem tayi batare da tace komai ba. Mikewa Anty Asabe tayi tana dawowa da plate din abinci ta ajiye ma Tasneem, cikinta wata kara yai da idanuwanta suka sauka kan abinci.

"Nagode. In kina da leda kiban dan Allah, zan juye a ciki"

Dan ba zata iya ci ita kadai ba. Zaifi musu albarka ko yayane in suka hadu ita dasu Azrah. Anty Asabe batace komai ba ta dauki abinci, a ledar ta juye mata tana kara mata wani. Har a ranta taji tausayin Tasneem din, girma ya kamata da karancin shekaru.

Dayake gidan Haj. A'i kawar Anty Asabe nan bayane, Muhsina na dawowa ta aikata. Aikam akayi sa'a bata samu yar aiki ba. Dan haka ta sake hadasu da Muhsina kan cewar taga Tasneem din, in yaso sunyi magana daga baya. Sosai Tasneem tai mata godiya tukunna suka wuce.

Tun kamun su shiga gidan Tasneem take ganin girmanshi. Balle ma da suka shiga wani tankamemen falo. Muhsina na rakata ta tashi ta juya abinta. Kallonta Haj. A'i tayi a wulakance.

"Anya zaki iya kuwa?"

"Zan iya wallahi"

Tasneem ta fadi a kagauce

"Share-share ne da wanke-wanke,sai kuma zaki dinga kamamun girki, banason lalaci ko kadan, ba kuma nason kazanta da ha'inci, zan dinga baki dubu biyar duk wata. Na kori yar aikina ne saboda tanamun sata, ba zamu shirya ba inhar naga abubuwa sun fara bacewa"

"In shaa Allah duk zan kiyaye. Yaushe zan fara zuwa? Ina layin Mai agwagi ne"

Tasneem ta fadi, dan da yar tafiya ba laifi. Wani kallo Haj. A'i ta sakeyi mata

"Gobe ma zaki iya fara zuwa. Kizo da wuri saboda wanke-wanken safe. Ki jirani ina zuwa..."

Ta karasa maganar tana mikewa. Tadan jima kamun ta dawo, kudine ta mikama Tasneem din yan naira dari-dari guda biyar.

"Ki hawo mota goben dan karki zomun latti"

Godiya Tasneem tai mata. Sanda ta fita daga gidan wani sabon karfi takejin yazo mata. Murmushin dake fuskarta yaki dishewa. Koba komai dubu biyar ba karamin kudi bace a wajenta. Su Azrah zasu koma makaranta, rashin makarantarsu na tsaya mata, Abba na sonsu da karatu ba kadan ba.

Anan shago ta tsaya ta siya musu garin kwaki da sugar ga kuma ledar abincin da Anty Asabe ta bata. Da sallamarta ta shiga gida, suka amsa mata. Ta karasa kan tabarmar tana ajiye ledojin ta zauna tace Azrah ta dauko musu faranti a kitchen. Ba musu ta tashi ta dauko, abincin ta juye

"Kuzo muci..."

Sabeena ta fara sa hannu, sai Azrah, Hamna kallon abincin tayi, tana komawa kan dayar ledar gari da sugan da Tasneem ta ajiye sai dari biyun daya rage, kamun ta kalli Tasneem, cike da rashin yarda tace

"Ina kika samo abinci? Ina kika samo dayar ledar nan da kudin?"

Sai lokacin hankalin Azrah ya dawo mata na basu san inda Tasneem ta samo kayayyakin nan ba. Itama hannunta ta tsame daga abincin tana kallon Tasneem din

"Gidan Anty Asabe naje, na roketa ta dinga bani wankin su inayi dan mu dinga samu abinci, ita tabani abincin nan, gari ne a ledar nan da sukari dana siyo. Na samu aiki a gidan kawarta dake bayan gidan Anty Asabe, gobe zan fara zuwa in shaa Allah, matar taban dari biyar"

Murmushi Hamna tayi mata

"Dan Allah? Zan biki sai in dinga tayaki ayyukan"

Murmushi itama Tasneem tayi ganin Hamna tasa hannu cikin abincin.

"A'a basai kin bini ba. Zakuyi zamanku a gida. In shaa Allah da anban kudin farko zan saka Sabeena makaranta. Kuma saiku koma"

"Ke ba zaki koma ba?"

Azrah ta fadi. Numfashi Tasneem ta sauke, dan ta riga tasan ita da makaranta sunyi bankwana. Wanda ta samu Allah ya amfana, indai su zasu ce ya isheta, zatai duk wani kokari dan ganin karatunsu bai tsaya ba, zata kula dasu. Ba saisun san ita tata rayuwar zatayi tane kawai dan kula dasu ba

"Zan koma nima a hankali"

Ta fadi, maganar ta zauna musu, abincin suka gama ci, tace in basu koshi ba su kara da garin, har Sabeena kai ta girgiza mata. Hira suka ci gaba dayi cikin jindadin canjin dayazo musu na farko tun rasuwar Abba.

Sai da sukai isha'i tukunna Ummi ta dawo.

"Sannu da zuwa"

Hamna ta fadi. Kallon ta Ummi tayi, dan bawai ko yaushe Hamna ke mata sannu da zuwa ba. Gaisuwar safe kawai take hadasu in sunga juna kenan.

"Ba wata tsiya na samo ba da kike saurin mun sannu. Nima banci ba, babu wanda yaban kudina, jummai sai gyada na sungomo da na samu an siyo mata"

Mikewa Hamna tayi ta shige daki, batayi magana bane dan wani abu, tayima Ummi sannu da zuwane kawai saboda tana cikin jin dadi, amman saida Ummi ta rusa mata dan farin cikin da take ciki. Azrah ma bayan Hamna tabi da hannun Sabeena cikin nata. Suna barin Ummi da Tasneem.

"Wannan gyadar zan soya su Hamna su zagayamun da ita, dan bazan asara ba wallahi"

"Talla Ummi?"

Tasneem ta tambaya muryarta can kasa. A tsawace Ummi ta amsa da

"Eh tallar, dan banda abinda zan ci daku dashi. Wallahi in kika zugasu sukaqi zuwa ku zaku zauna da yunwa. Dan in ba'a jemun tallar nan ba, babu wanda zanba abinci a cikin ku, kuna ganin wahalarku da ubanku yabarni da ita, danginshi ba shegen daya tuna damu balle yace zai kawo mana wani abu..."

Runtsa idanuwa Tasneem tayi tana jin wani abu yai mata tsaye a wuya.

"Na samu aiki. Ba saisun fita talla ba, Abba bayason tallar nan"

"Kin samu aiki? Yaushe?"

Kallonta Tasneem tayi

"Dazun Ummi, Anty Asabe ta samarmun a gidan kawarta"

Jinjina kai Ummi tayi

"Asabe munafuka ce wallahi, dan bakin munafunci nan naje tace bata da inda zata samomun aiki, shine ke harta samo miki ko? Ya mata kyau"

Shiru Tasneem tayi, ledojinta Ummi ta kwasa tana shigewa daki. Itama Tasneem dakin ta wuce, kamun Ummi ta dawo ta sake sauke mata wani fadan. Indai kan abincin da take basu ne dako isarsu bayayi sau daya a rana zata dorama su Azrah talla ta rike kayanta. Tasneem ma tayi mamaki da sai yau Ummi tai maganar, dan kullum ta basu jininta kan farce take karba, tasan Ummi ba zata dinga basu abu haka kawai ba, sai sun mata wani abin.

**

Bata koma bacci ba bayan tai Sallar Subh, saida ta share ko ina da ina, tai wanka, ta kunna radio tana jiran taji bakwai tayi saita fita. Aikam karfe bakwai nayi tasa hijab dinta ta tafi. Hankalinta a kwance yake saboda akwai sauran garin kwakin da zai ishi su Azrah har rana.

Mota tahau kuwa. Kamun wani lokaci harta isa maigadin gidan tsohone, cike da ladabi Tasneem ta gaishe dashi, ya amsa fuskarshi babu yabo ba fallasa. Data shiga cikin falon da suka zauna jiya taita sallama babu wanda ya amsa, waje ta samu ta zauna a kasa ta rakube, tana jinta wani irin. Babu motsin komai sai Tv da takeyi da sauti dan kadan a falon.

Agogon dakin ta zubama idanuwa, lokaci zuwa lokaci takan karayin Sallama amman shiru, saita sakama ranta bacci suke, batason yin ba dai-dai ba, tunda batasan ko ina na gidan ba, dako share-share ta fara yi dan ta rage aiki, ganin babu mai fitowa yasa ta mayar da hankalinta kan Tv tana kokarin fahimtar film din da akeyi amman ta kasa.

Haj. A'i bata fito ba sai wajen takwas da rabi, jikinta sanye da rigar bacci doguwa sai wasu takalma da kallo daya zakai musu kasan suna da laushi a kafarta.

"Ina kwana"

Tasneem ta fadi a sanyaye. Kallonta Haj. A'i takeyi kamar tana son gane inda ta taba ganinta maimakon amsa gaisuwar da tai mata. Ganin hakan yasa Tasneem fadin

"Kince inzo da wuri. Inata sallama banji kowa ba"

Dan ware idanuwa Haj. A'i tayi.

"Oh, ai da kin fara aikinki baki jirani ba. Bacci nake"

"Bansan inda komai yake ba"

Kai Haj. A'i ta daga

"Biyoni in nuna miki"

Mikewa Tasneem tayi tana bin bayanta, har suka karasa wani kitchen mai girma daya qawatu, tunda Tasneem take bata taba ganin irinshi ba.

"Ya sunanki?"

"Tanseem"

Ta amsa a sanyaye

"Tasneem kinga kitchen dinmu da mukafi aiki a ciki, akwai wani a dayan bangaren. Yarona dayane a gida yanzun, sauran duk suna makaranta sai karshen sati wasu suke zuwa, wasu kuma karshen wata ko insun samu hutu. Amman zaki share kowanne dakunansu kullum ki goge saboda kura..."

Kai Tasneem take daga mata, haka suka zagaye gidan da duk da babu bene, babbane sosai, Haj. A'i na nuna mata ko ina, tana mata bayani, wani daki suka shiga, dayasha banban da sauran dakunan baccin, dan shi da aka tura maimakon gado datagani, falo suka fara cin karo dashi.

Numfashi taji Haj. A'i ta sauke da fadin

"Haidar anan akai bacci kenan..."

Inda idanuwan Haj. A'i suke Tasneem ta kai nata, kwance akan kujure wani matashin saurayine da Tasneem bata iya ganin fuskarshi ba, saboda kanshi a juye yake, kafarshi daya a kasa, kusan rabin jikinshi ma bakan kujerar yake ba. Juyi daya zai ya fado kasa.

"Sai nan ma, kullum zaki share ki goge, akwai karamin kitchen ba wani girki ake a ciki ba. Can kofar dakin baccin shi yake da bandaki a ciki. Akwai kwandon dana nuna miki ciki zaki zubo kayan wankin saiki kaisu dakin wankin da nakai ki..."

"Mummy...go away"

Haidar ya fadi muryarshi can kasan makoshi, yana jan jikinshi yahau kan kujerar sosai, hadi da juyowa ya bude idanuwanshi a hankali

"Ba inda zani, ka tashi kai sallah"

Sosai Tasneem take kokarin boye mamakin dake fuskarta, na tiqeqen kato kamar wanda Haj. A'i ta kira da Haidar bai Sallah ba har lokacin, abin ya mata wani iri. Har suka juya suka fice daga dakin bai kara motsawa ba. Bata kuma sake tashin shi ba.

Wanke-wanke Tasneem tayi, tana jinjina yawan kwanonin da tukwanen da aka bata, dan a bayanin Haj. A'i basu da yawa a gidan. Sai ta sama ranta ko na kwanaki ne aka tara, kamun wani lokaci ta gyara kitchen din ta goge ko ina, dan Allah bai dora mata qwiya ko ha'inci ba. Hakama ko ina ta share tas ta gogge.

Haj. A'i tace banda nata bangaren. Dan haka dakin Haidar kawai ya rage mata. Takai minti biyu a bakin kofar tana tunanin shiga, kwankwasawa tayi har sau biyu amman shiru,sake kwankwasawa tai a karo na ukku, da ba'a amsa ba ta yanke shawarar shiga, duk da haka da Sallamarta.

Tai mamakin ganinshi zaune ya kafeta da idanuwa, sai da zuciyarta ta doka. Ganin ta da tsintsiya da mopper a hannu yasa shi gane sabuwar yar aikin da Haj. Ta kawo ce.

"Bakuwace ke, zan fada miki sau dayane kawai. Ba'a kwankwasamun daki, in wani abu zakiyi ki turo kiyi ki fita, saboda in bacci nake zai iya samun ciwon kai..."

Tunda ya soma magana kai kawai Tasneem take daga mishi, akwai wani abu tattare da idanuwanshi da yanda yake kallonta da bataso, zuciyarta ba ta sake dokawa ba sai da yace

"Ki kullemun kofa"

Hannunta dake kyarma tasa ta tura kofar, zagayawa tai daga bayanshi tana soma sharar duk da dakin babu wani datti, banda gwangwaneyen lemuka dake tsakiyar dakin ajiye da tagani tun shigowarsu da Haj. Ko da tazo share wajen jikinta na mata wani iri, sau biyu suna hada idanuwa da Haidar amman bai daina kallonta ba.

Ya sake kayan dazun dake jikinshi, wani wandone duk kafafuwanshi a waje, sai riga mai yankakken hannu, itakam jikinta na mata wani iri, dan bata saba ita kadai da wani namiji a daki ba. Tanason tace ya janye kafafuwanshi ta sharo wajen dan akwai gwangwaneyen lemo amman bakinta ya mata nauyi.

Saima kara matso da kafafuwanshi da taga yayi wajen.

"Zan share"

Ta tsinci kanta da fadi

"Na hanaki ne?"

Ya tambaya a hasale, hannunta na rawa tana kara takure jikinta dan karta tabashi, inda Allah ya sota da hijab dinta duk aikin da take bata cire ba, tai dabara ta sharo wajen da sauri tana tattarawa. Sai nishi take kamar wadda tai gudu, ga zuciyarta dake dokawa, ga Haidar daya kafeta da idanuwa.

Dakin baccin shi a hargitse yake, ko ina kayane kaca-kaca, kan gado da kasa, banda zube suke ba zatace kayan wanki bane dan harda kamshin turare a jikinshi, haka ta tattara su waje daya. Ta share, ta gyara gadon, dakin yai fes dashi, tana saka kayan cikin riga daya dan ta kulle ba saita dawo dakin ba taji shigowar Haidar dakin.

Juyawa tayi, sai lokacin ta kare mishi kallo sosai, dogone, bakine saidai fuskarshi nada cika, ko kuma girmanshi ne yasa yai mata haka bata sani ba, da sauri ta ke tattara kayan, ta bayanta ya wuce kafafuwanshi na gogar jikinta.

"Auzubillah"

Ta fadi da karfi tana runtsa idanuwanta kamar ta goga mata wuta, da sauri ta tattara kayan ra mike tana daukar abin sharar ta fita daga dakin zuwa falo, da gudu ta dauki mopper ta fice, kirjinta na dukan ukku ukku, dakin wanki taje takai kayan. Kitchen ta koma ta samu Haj. Ai ta fito da dankalin turawa mai yawa.

Kasa Tasneem ta sakko dashi ta zauna kan tiles tana ferewa. Ta jima da yake da yawa, kuma tana bi a hankali karta kwashe shi, itama Haj. A'i hidimarta ta shigayi, duk da ta yaba da aikin Tasneem din, komai ya fita tsaf-tsaf bata fada ba. Da yawansu haka suke farawa daga farko.

Ita ta nuna ma Tasneem yanda take so a yayyanka tukunna, ayyukan da yawa, Tasneem ita ta soya dankalin, harda su farfesun nama Haj. A'i tayi. Sai yanzun taga yanda ake kwanoni ja baci. Koda suka gama ayyukan tsaf, suka zuba a kuloli saida ta sakeyin wanke-wanke. Ta goge kitchen din.

Wani babban kwano Haj. A'i ta zubama Tasneem farfesun nama a ciki, ta cika mata plate da dankali da soyayyen kwai, ta kuma ce mata ta hada shayi ga ruwan zafi nan da kayan shayi. Kallonta Tasneem take cike da mamakin, murmushi kawai Haj. A'i tayi, tabarma Tasneem kayan shayin ne ta hada da kanta saboda tanason taga hankalinta.

Ita ba irin mutanen nan bace masu rowa, ko masu kudin da zasu dauki yan aiki, su suci mai dadi su hana wanda suka tayasu aiki. Ba haka halinta yake ba. Abinda duk sukaci shi duka yan aikin dake gidan suke ci harda maigadi, bata iya halin tsiya da rashin wadata ba. Lipton kawai Tasneem ta saka a ruwan zafin da sugar, dan yunwa takeji jikinta harya soma bari. Dankalin da kwai taci, ko rabi bata iyaci ba. Naman ma yanka biyu taci, sosai yai mata dadi.

Leda tagani ta dauka ta juye dankali tana tsame naman daga cikin romonshi ta juye ciki shima ta kulle tana ajiyewa gefe. Anan kitchen din tai zamanta. Ta dade sosai har Haj. A'i ta dawo ta sameta.

"Tasneem anan kika zauna. Taso akwai dakin masu aiki, tunda ke ba kwana zaki dingayi ba. Saiki zauna ki huta kamun ki gama aikin ki"

Mikewa Tasneem tayi da ledar ta a hannu. Ganin Haj. A'i tabi ledar da kallo yasa Tasneem saurin fadin

"Dankalin dana ragene da nama. Bazan iya cinyewa ba, zan kaima kannaina"

Kai kawai Haj. A'i ta daga mata. Tasneem tabi bayanta tana sauke numfashi. Dan batason ta dauka ta dibar mata wani abune. Dakin babbane harda Tv a ciki da fanka.

"In zakiyi kallo ga remote din can. Inma bacci zakiyi to, in zakimun wani abu zanzo in kiraki"

"Nagode.."

Tasneem ta fadi, dan bata zata akwai kalarsu Haj. A'i ba. Karamcin matar ya tsaya mata. Duk da haka batason ta zaqe a kasa tai zamanta.

*

Aikin ranar ma bamai yawa bane, abincin darene ma kala-kala, shima karfe biyar sunyi komai sun gama. Wata kula Haj. A'i ta samu ta cika ma Tasneem abincin daren a ciki. Ta saka mata a leda, dari biyar ta sake bata tai mata sallama. Har hawaye tai a hanya, dan bata taba zaton hanyar samun abinci zata zo musu cikin sauki haka

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment