Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rafiq duk gidan. Basa son qazanta, kuma dakunansu ne ko takalmi ba zaka gani inda bai kamata ba, gado a gyare tsaf-tsaf.

Remotes ta dauka duka biyun tana zama kan gado. Ta kunna kayan kallon kamun ta ja kafafuwanta kan gadon ta kwanta, ganin ba'a samu wani abin kirki a duk tasoshin da take kallo yasata mikewa tana zuwa ta canza zuwa DVD. Sannan ta dawo ta kwanta, Merlin take kallo seoson 1, film din ya burgeta. Sai dai yana farawa tasa pause. Tun shekaranjia rabonta da kallo, a kagauce take kuma da taga ya za'a kare.

Karatun jarabawar yau ya hanata kallo jiya, sai dai tana da tsallaken sati daya kamun wata jarabawar. Matsalar Muneeb ne, tare suke kallo, kome take zai jirata saita gama su kalla tare, wani lokacin ma tana kallo suna waya suna tattauna abinda yake faruwa. Wayarta ta soma ruri, dauka tayi murmushi na kwace mata, ga daga da karawa a kunne, bayan ta amsa Sallamarshi tana dorawa da

"Kaman kasan kaine a raina..."

"Naji a jikina ne shisa na kira"

Tana jin murmushin da yakeyi a muryarshi, gyara kwanciyarta tayi, zata iya rantsewa tun batasan menene so ba Muneeb yake matukar burgeta, in yazo gidansu wajen Rafiq, yanda komai nashi yake a nutse.

"Ya exam din?"

Ya buqata ta dayan bangaren..."

"Alhamdulillah... Saura biyu amman nagaji, daman su mana ita a kwana biyu mu huta"

Zafira tai maganar cikin sigar tsegumi. Dariya yayi

"Kamar gobe ne in shaa Allah, zakiga kungama lafiya kalau..."

Kai ta dan daga cikin yarda da abinda ya fada.

"Allah ya nuna mana. Ya aikin ka?"

"Gashi nan sai gajiya..."

"Sannu..."

Saida ya sauke numfashin dataji cikin kunnenta, zuciyarta na nutsuwa waje daya tukunna ya amsa

"Yawwa"

Shiru tayi tana rasa abinda zatace saboda yanda son shi ke mata yawo, ko kwarin kirki bataji

"Zafira..."

Yanda yake kiran sunanta da muryarshi mai sanyi na sakata jin dadin sunan fiye da yanda zata iya misaltawa.

"Ya kamata su sani, nagaji da boyema kowa abinda ke tsakanin mu... Kallon Rafiq cikin ido koda yaushe da sanin ina sonki batare da goyon bayanshi ba yana mun wani iri"

Wannan karin ita ta sauke numfashi mai nauyi. Tafi shi son bayyana abinda yake tsakanin su, saidai tana jin tsoro, duk da itace mace babba a gidansu, har kasan zuciyarta tana da tabbacin ba za'a barta soyayya da kowa batare data gama makaranta ba. Shisa ta roqi Muneeb da subar komai sirri a tsakanin su har lokacin da zata gama makaranta. Bashi kadai bane yake jin wani iri, bazai gane babu sirri a tsakanin ta da Yayanta ba sai wannan karin.

Tana kuma jin nauyin abin na danneta da duk rana. Ji take kamar ta gaya mishi kawai ta sauke nauyin, amman duk lokacin data samu dan karfin gaya mishi, sai yai dai-dai da lokacin da zai sake jadadda mata karatu kadai yakaita makaranta, shi kadaine dalilin dayasa taje makaranta, abokan da zata zagaye kanta dasu a makaranta ya zamana harkar makaranta kawai take hadasu. Ba saiya furta mata kai tsaye cewar cikin kashedin shi harda soyayya ba, shisa take tsoron fada mishin.

"Kinyi shiru..."

Muneeb ya fadi da alamun damuwa a muryarshi.

"Na kusa, sauran sati biyu..."

"Shekaru biyu Zafira...a da muna ganin muna da dukkan lokacin da muke bukata, yanzun kullum da tsoron kar lokaci ya kure mana nake bacci...ko Rafiq ne yasani hankalina zai kwanta ta wani fannin....ba zamu taba wuce saurayi da budurwa ba indai basu sani ba..."

Kai take dagawa kamar yana ganinta.

"Nasani..."

"Bazan iya kara jira ba... Zan fada mishi da kaina..."

Tashi zaune Zafira tayi babu shiri, zuciyarta na dokawa.

"Love..."

Ta fadi.

"Bazai aiki ba wannan karin Zafira, nagaji sosai, na baki dukkan lokacin da kike bukata, ki nuna mun soyayyar mu na da muhimmanci a wajenki..."

Da sauri tace

"Ina sonka... Ina sonka sosai kasani kuma"

Sai da yadan yi jim tukunna yace

"Nasani, ki nunamun nakai matsayin da Rafiq zai iya sani..."

Runtsa idanuwanta tayi tana budesu a hankali, tasan dole Rafiq yasani daman, amman kullum tana ganin akwai sauran lokaci, kafin nan ta shirya. Sai dai yanzun take da tabbacin ba zata taba shirya fada mishi tana soyayya da babban abokin shi ba, ta ina zata fara, tunanin hakan kawai yasa kaman ta shige karkashin gadonta saboda kunya, ga kuma tsoro bayananne da take ji.

"Bari in baki lokaci kiyi tunanin da kyau..."

"Kwana nawa nake dashi?"

Ta bukata.

"Daga nan zuwa sanda zan hadu dashi..."

"Love ko yaushe zaka iya haduwa dashi fa.. Ina nufin ko yauma zaku iya haduwa"

Zafira take fadi a tsorace.

"Zabin nakine Princess..."

Muneeb yace yana katse wayar kamun ta samu damar bashi amsa.

"Inalillahi..."

Ta fadi tana ajiye wayar kan gado. Tasan halin Muneeb kaf, ya gajin kamar yanda ya fada, a muryarshi kawai ta fahimci hakan, kuma baya fada mata abinda bazaiyi ba, suna haduwa da Rafiq din zai fada mishi. Tana son ya fara ji daga wajenta, bataso Muneeb ya fara fada mishi, ko ba komai Yayanta ne, kuma yana fada musu ko yaushe suke buqatar abokin shawara a tare dashi zasu samu.

Bata taba wani bukatar kawa ba, tana dasu barkatai a makaranta, amman wanda zata kira kawaye sosai duk sun hada jini, yaran yan uwan Nuri ne kona Daddy. Suma ba wanda zaice wata hira banda ta duniya ta taba hadasu. In tanason shawara ko wani abu yan uwanta suna nan. Saukowa tai daga kan gadon tana fita daga dakinta zuwa na Aroob dayake jere da natan.

Sai data kwankwasa Aroob din tace ta shiga tukunna ta tura tana shiga, kan hannun kujerar Aroob din ta zauna, gabaki daya komai na dakin kalar pink ne mai haske da mai duhu. Haka kuma yake tun yarintarta komai na dakinta har zanin gado.

"Na kasa sabawa, kullum na shigo dakinki sai inga kamar na shiga duniyar Cartoon..."

Dariya Aroob take

"Da yake ma duk sanda kike shigowa ban gayyace ki ba..."

Juya idanuwanta Zafira tayi tana tabe baki.

"Naji... Ni ba abinda ya kawoni kenan ba. Kisa kanki a matsayina.... Kece kike boyema Yaa Rafiq wani abu babba, sai lokaci yazo da dole ya sani, zaki so yaji a wajenki ne ko a wani waje..."

Dan daga gira Aroob tayi tana kallon Zafira, kamun tace

"Wani abu babba kaman son Muneeb?"

Ware idanuwa Zafira tayi tana mikewa da sauri ta karasa inda Aroob take tana rufe mata baki, tureta Aroob tayi tana dariya.

"Wallahi ina mamakin yanda akai Yaa Rafiq bai gane ba, kalli yanda kuke kallon juna in yazo gidan nan..."

Sake kokarin rufe mata baki Zafira takeyi tanajin fuskarta nayin wani ja saboda kunya. Bata taba tunanin Aroob ta sani ba, ko da wasa kuwa.

"Wai ba zakiyi shiru ba sai wani yaji ki Aroob..."

Zafira tace tana murmushi cike da kunya. Matsawa Aroob tayi tana jingina bayanta da abin gadon, wannan karin babu alamar wasa a muryarta take kallon Zafira

"Ki fada mishi... Bansan me yasa kika boye ba tun da farko, in Yaya yasani komai zai miki sauki wajen Daddy..."

Ciza lebenta na kasa tayi

"Tsoro nake ji wallahi... In yayi mun fada kuma fa?"

Daquna fuska Aroob tayi

"Kice abokin shawararki kikeson magana dashi ba Yaa Rafiq ba... Kamun ki fada mishi, yana mana fadane kawai in yana Yayanmu"

Dan shiru Zafira tayi tana juya maganar Aroob din.

"Ki tashi... Kije ki fada mishi kawai..."

"Yanzun?"

Zafira ta tambaya tana ware idanuwa. Kai Aroob ta daga mata

"Me kike jira..."

Mikewa Zafira tayi, gudun zuciyarta na karuwa, tana jin shi a ko ina na jikinta. Har takai kofa Aroob tace

"Zaf..."

Juyawa tayi.

"Ya hadu..."

Girgiza kai tayi tana ficewa, dariyar Aroob din kamun ta rufe mata kofa na sakata murmushi. Kafafuwanta har kyarma suke lokacin da take karasawa bangaren Rafiq din. Sama-sama take jinta lokacin data kwankwasa mishi kofa, ta kusa mintina biyar a tsaye tukunna ta sake kwankwasawa, shiru, zata juya ta koma ne dan ta dauka ko ya fita taji yace

"Shigo..."

Zata rantse zuciyarta cikin hannunta data bude kofar dashi ta koma saboda zufar da yakeyi, tanajin ya dauki sanyi, murza shi take da dayan hannunta lokacin data shiga dakin, sai take ganin kamar ya kara mata girma yau. Falon da wajen bacci, harda karamin wajen cin abinci zaka iya ganinsu daga nan inda kake tsaye. Hawan bene biyu ya rarraba ko wanne bangare da dan uwanshi.

Yanzun zata iya cewa a falonshi take a tsaye. Yana zaune kan kujera ta mutum daya. Fuskarshi babu walwala, yanayin shi na kara mata tsoron da take ji.

"Zan iya dawowa wani lokacin..."

Ta fada tana shirin juyawa.

"Menene?"

Ya bukata a takaice. Makoshin ta taji ya bushe, wani yawu ta hadiye tana fuskantarshi, wasa take da hannuwanta.

"Naga kamar a gajiye kake..."

Sai lokacin ya dago yana sauke mata idanuwanshi.

"Yaushe na taba gajiyar da bazan saurareku ba?"

Duk da maganar ta fito da sigar tambaya, tasan ba amsa yake bukata ba.

"Bana son tsayuwar nan Zafira. Ki samu wajen zama..."

Ya sake fadi yana binta da kallo harta zauna. Zuciyarshi na matsewa waje daya da abinda Daddy yake so yai mata. Da abinda bazai taba amincewa dashi ba, idan Nuri ba zata nuna ma Daddy rashin kyautuwar hakan ba shi zaiyi.

"Yaya..."

Ta kira tana yin shiru kuma. Dafe kai yayi da hannuwanshi biyun yana sauke numfashi kamun ya dago ya kalleta. Daga yanda take wasa da hannuwanta zuwa yanayinta gabaki daya ya nuna a tsorace take da ta fada mishi ko menene.

"Me kike bukata?"

"Aboki..."

Ta fadi da sauri. Jinjina kai yayi, shi ya fada musu cewar duk sanda suke son fada mishi wata magana da suke tsoron zai musu fada, ko wata tambaya da suke ganin Yayansu bazai amsa ba, zai zama abokinsu, su fada mishi hakan suke bukata, sai suyi maganarsu lafiya kalau. Yana ganin yanda suke yawan amfani da hakan fiye da yanda ya kamata.

Musamman Fawzan dazai shigo ya daukar mishi abu, in yazo magana sai yace dakin abokinshi ne ya shigo, in ka dauki abin abokinka baya fada, haka abokai suke, dole yake kyaleshi. Zafira ce bata fiye mishi haka ba, to ko meye yanzun yasan yana da muhimmanci a wajenta.

"Ina jinki"

"Yaa Rafiq daman..."

Katse ta yai da girgiza mata kai, yana dora murmushin dayakan yima yan waje, wanda baida kusanci da zuciyarshi saboda bayajin nishadi ko kadan.

"Rafiq kawai..."

Kai ta daga duk da yasan ba zata iya kiran sunan shi kai tsaye ba. Hannuwa tasa tana goge fuskarta da takejin alamun zufa. Wani numfashi taja

"Yaa Muneeb muke soyayya!"

Ta fadi da sauri tana rufe fuskarta, tana kuma jin kamar wani nauyi ya sauka daga kanta. 'Yaa Muneeb muke soyayya' kalamai hudun da Rafiq yaji sun dira cikin kunnenshi suna yawata ko ina na jikinshi cike da neman inda ya kamata su zauna. Kamun su samu waje a cikin kashi suyi daram suna aikama zuciyarshi sakon girman da hakan yake nufi.

"Tun yaushe?"

Ya tambaya muryarshi can kasan makoshi. Bazai daga murya ba, bazaiyi komai ba

"Shekara biyu"

Ta amsa har lokacin fuskarta na rufe da hannuwanta, so yake ya girgiza ta, yaji dalilin dayasa bata fada mishi tun farko ba, maimaita ma kanshi cewar aboki tace tana bukata ba Yayanta ba. Amman kwakwalwar shi ta kasa tuna yanda aboki ya kamata yayi a yanayi irin wannan. Muneeb, dole yaji dalilin da zaisa ya boye mishi in Zafira bata fada mishi ba.

"Kina son shi?"

Ya sake tambaya yana kirga daya zuwa goma cikin kanshi, kamun ta daga kai a hankali.

"Zafira..."

Ya kira. Ba saiya karasa ba, yafi son tai magana da bakinta ta kuma san hakan.

"Yaya kunya nakeji wallahi..."

Ta fadi tana duqunqune fuskarta a jikinta. Runtsa idanuwanshi yayi yana bude su a hankali.

"Kina son shi?"

Ya sake maimaitawa.

"Eh... Sosai..."

Zafira ta fadi tana hade jikinta kan kujerar kamar zata shige ciki.

"Yana kula dake yanda ya kamata?"

"Yaya..."

Zafira tace tanajin kamar kasa ta bude ta hadiyeta saboda kunya.

"Abokin kine ni, na damune kawai, kawata nada saurayi shekaru biyu sai yanzun nake sani dole inji duka details din..."

Mikewa Zafira tayi da sauri tana rugawa da gudu tabar mishi dakin. Duk da abinda yakeji sai da dariya ta kubce mishi. Kamun lokaci daya ta dauke kamar yanda tazo babu sanarwa, a wata duniyar, a wani gidan, banda duniyarsu, banda nasu gidan, zaiyi farin ciki saboda Muneeb mutumin kirkine, kowanne Yaya zaiyi alfahari da kanwarshi ta samu Muneeb a matsayin mijinta.

Sai dai a tashi duniyar, abune da yasan bazai yiwu ba, abune mai wahala, a maimakon farin ciki, zuciyarshi cike take da tsoron da bai taba sanin kalarshi ba, tsoron yanda duniyar Zafira take gab da birkicewa. Zai dora gabaki dayan laifin akan Muneeb dabai fada mishi tun da wuri sanda zai iya tsayar da abin batare da su biyun sun shiga yanayi ba.

Tashi yayi yana kara shiga cikin dakin sosai zuwa bangaren baccin shi, mukullin motarshi ya dauka a gefen gado yana fita daga dakin zuwa hanyar data fitar dashi daga gidan gabaki daya. Yana tafiya yana tunanin yanda akai bai gane abinda yake faruwa tsakanin Muneeb da Zafira ba. Sai yanzun data fadane yake ganin alamomi da yawa. Akwai randa motar Zafira ta samu matsala ta kirashi suka tafi da Muneeb din dan ya duba mata.

*

Bayan ya dudduba ne ya dago ya kalli Rafiq din da fadin

"Dole sai na tafi da motar gareji..."

Shagwabe fuska Zafira tayi

"Yaa Muneeb har yaushe? Za'a gama gyarawa yau?"

"Zaf..."

Rafiq ya kira cike da kashedi, da baya tare da Muneeb dinma lokacin data kira da ba su taho tare ba, dan sam baya yarda sukai mishi gyaran mota tunda ba kudin yake karba ba, Rafiq najin wani iri, yafi yarda da duk kusancin dake tsakaninku in hidima ta shigo ta cikin sana'arka a baka haqqinka yanda ya kamata.

"Yaya zanyi fita da motar ne fa..."

Ta fadi tana turo labbanta. Idanuwa kawai Rafiq ya tsareta dasu. Dole ta dauke nata tana sadda kanta kasa dan tasan baya musu fada a gaban wani, amman dole zata sha fada in sukaje gida.

"Anjima zan kawo miki har gida in shaa Allah..."

Muneeb ya fadi yana murmushi. Kai kawai Zafira ta daga mishi tana zuwa ta gabansu zata wuce.

"Zafira..."

Rafiq ya fadi a gajiye wannan karin. Juyowa tayi ta kalli Muneeb tace

"Nagode..."

"Karki damu..."

Tana bude mota ta shiga, Rafiq ya matsa yana taka kafar Muneeb din daya ture shi da sauri yana durqusawa ya murza yatsun kafarshi tukunna ya dago yana watsama Rafiq din wani kallo.

"Ka gaji da idanuwanka a jikinka ne ko?"

Rafiq ya fadi shima yana harar Muneeb din

"Batun yanzun nasan kana bakin ciki da kafata da tafi taka kyauba, saidai ban dauka yakai har haka ba..."

Dariya Rafiq yayi

"Baka da hankali kai kam... Kanwata ce Muneeb"

Fuskar dake nuna alamun 'me nayi' Muneeb din yaima Rafiq.

"Kana kallonta fiye da na Yaya da kanwa..."

Dan daga kafada Muneeb yayi

"Tana da kyau..."

Duka Rafiq din yakai ma Muneeb ya kauce yana dariya

"Ka wuce ka kaita gida... Zan tafi da motar"

Kai Rafiq yadan daga mishi.

"Mungode..."

Girgiza kai kawai Muneeb din yayi batare dayace komai ba. Wucewa Rafiq yayi ya shiga tashi motar. Dan juyawa yai ya kalli Zafira, inda ta tattara hankalinta gabaki daya ya kalla, baiga komai ba sai Muneeb dake rufe gaban motarta. Dan daquna fuska yayi saboda ya kasa gane yanayin dake fuskarta, qarar tashin motar ne yasata juyowa tadan kalli Rafiq din.

Saida yai baya suka hau titi tukunna yace

"Ina tarbiyarki, ko kudi kika biyashi ya kamata ki mishi godiya ba saina tuna miki ba..."

"A gajiye nake shisa,bazai sake faruwa ba..."

Kai kawai ya daga mata batare daya sake cewa komai ba.

**

Sai yanzun abin ya fado mishi, bayan nan abubuwa da yawa sun faru, bai taba kawowa a ranshi ba, ba dan soyayya na baka zabin wanda zaka so ba, saidai ya dauka kawai Yaya da Kanwa Muneeb da Zafira sukeyi. Bai taba zaton yafi haka ba. Motarshi ya bude yana shiga. Saida ya zauna tukunna yai ma Nuri gajeran Text.

'Naje wajen Muneeb Nuri'

Ya sa wayar a key ya mayar Aljihu. Kanshi tsaye ma'aikatar su Muneeb din ta gyaran motoci ya isa. Yana parking din motarshi ya wuce ya shiga ciki har inda zai kaishi office din Muneeb. Yaron dake kula da shiga da fitar mutane a office din Muneeb dinma gaishe dashi yayi yana dorawa da

"Shi kadai ne yana ciki"

Dan haka ya karasa, ko kwankwasawa baiyi ba ya bude kofar yana shiga. Muneeb na kwance kan kujerar hutawar dake office din. Yadan dago da kanshi, kallo daya yaima Rafiq yace

"Ta gaya maka kenan!"

Dan kai kawo Rafiq yakeyi a office din Muneeb din yana rasa kalar tunanin daya kamata yayi. Daddy ya rigada ya samoma Zafira miji, da wahala matuqa wani abu ya canza ra'ayinshi, in har ya saurari cewa Zafira nada wanda take so in yaji Muneeb ne bazai amince ba, Rafiq nada tabbacin ko da ace Daddy bashida wanda zaiba auren Zafira da wahala ya yarda da Muneeb.

Ganin har lokacin Rafiq baice komai ba yasa Muneeb tashi zaune. Damuwa bayyane a fuskarshi

"Nasan ya kamata in fada maka, Zafira ce tace lokaci baiyi ba, ita ta roqeni da in bari ta gama makaranta tukunna..."

Girgiza mishi kai Rafiq yake tunda ya fara magana.

"Me yasa zaka biye mata? Me yasa baka fadamun ba Muneeb?"

Kallon shi Muneeb yayi

"Ina son ta, tun dana fara ganin ta nake sonta, nasan tayi yarinta a lokacin amman bai hana zuciyata doka mata ba, ban fada mata ba saida tana level 2 Rafiq...ya kamata in sanar dakai kamun in fada mata din... Shine kuskurena..."

Dariyar takaici mai sauti Rafiq yayi. Kin fada mishi shine kuskure na biyu da Muneeb yayi, na farko son Zafira ne. Ganin kallon da Rafiq din yake mishi yasa shi fadin

"Baka amince ba? Baka sona da kanwarka..."

Dan dafe kai Rafiq yayi, baisan ta inda zai fara ma Muneeb bayani ya fahimta ba.

"Kamun ka fada mata ya kamata in sani..."

Ya sake maimaitawa kamar hakan kawai ya isa ya fahimtar da Muneeb din abinda yake son fahimtar dashi.

"Nace maka nasan ya kamata in fada maka, banyi ba... Kayi hakuri ban fada maka ina son kanwarka ba kafin in fada mata...in so kake kullum in dinga rubuto maka text din hakuri har saika hakura zanyi...amman ina son ta, ko yanzun kukace in turo manyana zanyi wallahi... A shirye nake in aureta"

Karasawa Rafiq yayi ya zauna kan kujerar da Muneeb din yake, dan yanda ya karasa maganar kawai zaka iya jin yanda Zafira take da muhimmanci a wajen shi.

"Me nake dashi da baka sona da kanwarka? Kasan ko kawa mace banda ita Rafiq, kai kasani, itace mace ta farko da zuciyata ta dokama, kuma bata kara ba har yanzun..."

A rikice Muneeb din yake, gani yake Rafiq baya son shi da Zafira. Shikuma baisan ta inda zai fara mishi bayani ba, kamun yakai kan Zafira kenan, daya sani tun daga farko zai mishi bayani, in har yana sonta Rafiq din yake gani, zai haqura, bazai fara yarda ya janyota ta soshi har haka ba. Bazai so su duka biyun su wahala ba.

"Kai da ita... Ba zaku faru ba"

Mikewa tsaye Muneeb yayi yana kallon Rafiq dake fassara 'Ka ce mun wasa kake'. Ganin shima Rafiq din na kallon shi batare daya sake cewa komai ba ya tabbatar mishi da gaske yake nufin abinda ya fada.

"Me yasa? Banda duk wata halayya da aka shimfida a musulunci na sharuddan aure? Ina da ilimin addini, na fito daga gidan mutunci, ina da sana'a, ina da gidan kaina...me ya rage kuma?"

Shiru Rafiq yayi saboda baisan ta inda zai fara ba, saboda kanshi na mishi wani irin ciwo.

"Saboda me Rafiq... Ka fadamun ina jinka"

Muneeb ya ke fadi ranshi a matukar bace.

"Rafiq..."

"Saboda kudin ku bai kai ba! Saboda babanka bakowa bane a Nigeria!"

Rafiq ya fadi cikin daga murya. Dana sani na lullube shi saboda yanayin dayake gani a fuskar Muneeb din.

"Muneeb..."

Rafiq ya fara, hannu Muneeb ya daga mishi alamar baya son ji. Muryarshi dauke da mamaki, bacin rai, da abubuwa fiye da wanda kalamai zasu iya misaltawa yace

"Ko a mummunan mafarki ban taba tunanin zaka mun gorin arziqi ba Rafiq...ko baka fadamun ba nasan ni kadaine talaka a cikin ku, wallahi ba saika tunamun ba ina sane, ina sane da cewar karatuna dukkan shi kaine, rufin asirin dana samu har nake kula da kannaina da iyayena kaine... Ban taba zaton zaka goran tamun ba..."

Har a zuciyarshi Rafiq yake jin ciwon da Muneeb yakeji, kirjinshi har zafi yake mishi. Saida Muneeb din ya zagaya ya zauna kan kujerar office din nashi tukunna ya sake kallon Rafiq da fadin.

"Zaka iya tafiya, ka fadamun abinda kazo yi...sai dai ikon bayar da aurenta ba a hannunka yake ba, zan trying wajen Daddy, bazan ji kamar ban mana wani kokari ba..."

Kallon shi Rafiq yake yi sannan yace

"Na dauka ka sanni kamar yanda kake tunanin nasanka, na dauka zaka iya fadar abinda zan iya da wanda bazan iya ba..."

"Mutane na canzawa da duk rana, kuma zaka san abinda suka nuna maka ne kawai..."

Girgiza kai Rafiq yayi. Shi ba mutum bane mai yawan surutu, duk cikin abokanshi Muneeb yafi saninshi akan kowa. Amman bakowanne maganganu suke hadashi da Muneeb din ba. Yau ya zama dole yasan wani abu. Dole ya fahimtar dashi, bayan rasa Zafira, bazai bari Muneeb ya sake rasa abokin shi ba. Ko ba komai yana bukatar wanda zai taimaka mishi jinyar rashin Zafira.

"Gori shine karshen abinda zai hadani da kai Muneeb, inda zan iya mantar dakai duk abinda ka lissafa na taba yi maka zanyi... Saboda bana maka bane dan ka dinga tunawa koda yaushe, nayi ne saboda zumuncin dake tsakanin mu..."

Ganin yayi shiru yasa Rafiq ci gaba da fadin

"Matsayin babanka da kowaye shi a Nigeria ne abu na farko da Daddy zai fara dubawa, sai kai din da kanka, me kake dashi? Waye kai? Wanne mataki ka kai a rayuwa? Wannan sune abinda zai duba kamun addininka, kamun martabar gidan ku..."

"Rafiq..."

Muneeb ya soma muryarshi daban hakuri saboda ya fara fahimtar Rafiq din yanzun.

"Kabari in gama... Ko ca akai in zabar ma Zafira miji bazan iya zabo kamarka ba, Muneeb kana da halayen da ni dakaina nake son samu. Ina sonka da kanwata, wallahi ina son ka da auren Zafira... Na damu da me yasa baka fadamun daga farko bane saboda in maka bayanin nan, saboda kabar son da kake mata iya kai kadai ba saika janyota cikin abinda bazai faru ba..."

Dafe kai Muneeb yayi da hannuwanshi duka biyun

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Shine abinda yake fadi yana maimaitawa ko zai samu dai-dai to a duniyar da yake jin ta birkice mishi lokaci daya.

"Kayi hakuri..."

Rafiq ya fadi saboda baida wasu kalaman da zai iya fadama Muneeb din dan yaji saukin abinda yake ji.

"Rafiq... Ka taimaka mana..  Dan Allah kayi wani abu akai. Wallahi ina son ta..."

Muneeb yake rokon Rafiq din yanajin kaman zuciyarshi zata fado. Mikewa Rafiq yayi

"Kayi hakuri..."

Juyawa yayi yana nufar kofa, da gudu Muneeb ya taso yasha gabanshi kamar wanda ya samu tabin hankali.

"Kace mun zakai wani abu... Kace mun bazan rasata akan wannan dalilin ba..."

Rafiq kauda kanshi yayi saboda bayason ganin yanayin da Muneeb yake ciki ko kadan. Ya rabashi ya bude kofar ya fice daga office din. Yafi mintina goma zaune cikin mota batare daya san asalin abinda yake tunani ba, tukunna ya samu ya tayar da motar yana nufar gida.

Yana zuwa bangarenshi ya wuce ya sakama dakin mukulli. Dan karamin littafin da yakan rubuta matsalolin da yake dasu ya duba wanda ya kamata ya fara takai ya dauko. Ya rubuta Muneeb, yana sokewa dan ya riga da ya mishi bayani, ya kuma san zai fahimta. Tukunna ya rubuta Zafira, matsala biyu ne a tare da ita, yanda zai fada mata auren su da Muneeb bazai yiwu ba, sai kuma yanda zai samu ta koma dai-dai.

Sannan ya rubuta Daddy, shima abu biyu, yanda zai hakura da aurar da Zafira, da kuma yanda zai samu yabari ta zabi wani mijin da kanta, wanda zaiso, dan gidan wani babban dan siyasa ko hamshakin mai kudi. Littafin ya ajiye gefenshi ya kwanta yana rufe idonshi ko zai samu nutsuwar fuskantar Daddy anjima.

*

Wani wahaltaccen bacci ne ya dauke shi, karar wayarshi ta tashe shi, bude Idanuwa yayi baiko motsa ba balle ya cirota daga Aljihu, kanshi ciwo yake kamar zai rabe biyu, agogon dakin ya kalla, kowaye ya kira wayar ba karamin kyauta mishi yayi ba dan lokacin Sallah yayi, yanajin ana kira a katon masallacin dake nan cikin gidansu. Alwala yaje yayi ya fito yanajin wayar taci gaba da ringing ya ciro ta daga aljihunshi ya duba, ganin Samira

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment