Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai korafin kasawar Abba akan su. Yanzun haka Asaben da take magana kanwar mamansu ce, itama ba wani halin suke dashi ba, saidai wadatar zuci.

Hijab din ta Tasneem ta mayar tana ce ma Azrah

"Zoki siyo mana manja da farin magi shagon Mudi"

Murmushi Azrah tayi har hakoranta suka fito, ko dariya take haka takeyinta da duka fuskarta.

"Me zaki dafa mana? Daman yunwa muke ji fa, ko Hamnah?"

Kai kawai Hannah ta daga mata, karbar Hamsin din Hamnah tayi tana ficewa. Ummi ta tabe baki ta fice daga dakin da fadin

"Gara in tafi inda zanci mai dadi...Sai kuyita fama kukam"

Babu wanda yace mata komai, su kansu su Hamnah sun fahimci shiru shine mafi alkhairi a lamurran Ummi. Hamnah bata wani jima ba ta dawo. Nan da nan Tasneem ta kwaba filawar ta hada komai, albasa tagani a kitchen har wajen biyar, ganin tabi Albasar da kallo yasa Hamna fadin

"Karki taba ma Ummi kayanta, ina da Naira Ashirin da Abba ya bamu kudin makaranta, a kafa muka je muka dawo"

Ware idanuwa Tasneem tayi

"Hamnah da kun hawo mota wajen dawowa akwai rana yau fa"

"Ni nace mu dawo a kasa Ya Tasneem, mu da yawa fa muka taho, har da su Zahra"

Jinjina kai kawai Tasneem tayi zuciyarta na mata nauyi. Daki Hamnah taje ta dauko kudin ta wuce ta siyo musu albasa. Haka sukai ta maneji da manjan Tasneem ta soya musu wainar filawar. Addu'a take Abba ya dawo daga Masallaci kamun ta karasa.

Tunda babu yaji intai sanyi ba zatai mishi dadin ci ba, karta saka mishi a kular Ummi taja mishi wata tijarar inta dawo tagani. Aikam tana gab da gamawa yai sallama.

Da gudu Sabeena ta tashi tana tarbarshi.

"Beena karki shafa mai manja a kaya mana.... Abba sannu da zuwa"

Cewar Hamnah

"Sannun ku Hamnah.... Me aka samu haka"

Abba ya fadi yana riqo hannun Sabeena suka karaso tare, matsa mishi sukai kan tabarma ya zauna a kofar kitchen din da suka shimfida tabarma.

"Sannu da zuwa"

Tasneem ta fadi tana samun plate ta zuba mishi a ciki, ta fito tana ajiye mishi.

"Azrah dibo ma Abba ruwa, ki dauraye cup din"

"Yaya ruwan yayi kasa sosai fa... Tunda nagama bari in dibo ko bokiti biyu"

Girgiza kai Tasneem tayi

"A'a Azrah banaso kina daukar bokitin nan wallahi. Zoki karasa soyamun inje dakaina"

Mikewa Abba yayi da fadin

"Naga yara nata dibar ruwa fanfon kofar gidan Malam Musa kuwa. Ki zauna ki karasa aikin ki bari in dibo"

Sosai Tasneem ke girgiza kanta wannan karin

"Abba dan Allah ka zauna kaci wani abu, ko karyawa bakai bafa....zanje in dibo"

Jim yayi, ya kalli wainar filawar kamun ya kalli Tasneem dan sosai yunwa kecin shi, tun ranar jiya rabon shi da abinci, har jiri-jiri yake ji da yana hanyar dawowa daga masallaci.

"Ku harta ishe ku ne? Naga an zubamun da yawa"

Murmushi Tasneem tayi

"Wallahi kuwa Abba... Akwai saura ma in zaka kara, filawar da yawa ashe... Bari in dibo ruwan inzo dai.... Ka zauna kaci dan Allah Abba kar ya huce"

Tasneem ke fadi tana nufar hanyar kofa da daukar farin bucket din fenti, dauraye shi tayi ta dawo ta dauki hijab tukunna ta fice. Sawu biyar tayi ta cika ko ina tukunna ta dawo tana maida numfashi.

"Sannu"

Saida ta janyo kujerar da Azrah tagama soya wainar filawa akai ta zauna tukunna ta ce

"Yawwa Azrah... Kai ana rana yau"

Abba kam ya cinye wainar filawar da Tasneem ta zuba mishi tas, ya zauna shiru, da alama yai nisa cikin tunanin da yake.

"Abba a kara maka ne?"

Ta tambayeshi, dago kanshi yayi hadi da girgizawa

"Alhamdulillah, ban san na koshi bama saida nasha ruwa, cikina har wuya nake jinshi. Nagode Tasneem, Allah yai muku albarka"

Su duka suka amsa da

"Amin..."

"Ina Umminku?"

"Ta fita"

"Ta fita?"

Ya maimaita da alamar baisan da fitar tata ba. Shiru Tasneem tayi dan bata san me zata ce mishi ba. Shima jinjina kai yayi da fadin

"Allah ya kyauta. Tasneem bakya ganin giccin su Tariq ko?"

Sunan su Tariq din da Abba ya kira na saka zuciyarta jagulewa da wani irin yanayi mai hade da kewarsu da damuwar halin da suke ciki. Makoshin ta taji ya bushe, ga hawaye nason cika mata ido, jitai ba zata iya magana ba dan haka ta girgiza ma Abba kai

"Oh Allah... Allah ka kare yaran nan duk inda suka shiga"

Abba ya fadi a fili, a zuciyarshi yana kara tsorata da rayuwa, musamman yanzun da nashi yaran suke zagaye dashi, su kadai yake gani ya samu sauqi, wata shida cikakku baiji dadin zama da Bara'atu ba, tun a farkon auren su har izuwa yanzun. Inda ya biye zuciya da rabon yaran ma bazai gifta ba.

Ya kuma san duk da ba wani karfi gare shi ba, kasancewar shi dasu sauqi ne a fanni da yawa na rayuwar su. Saidai mutuwa bata sanarwa. Sai dai addu'ar shi Allah ya bashi tsayin rayuwa harsai sun girman da zasu tsaya da kafafuwan su.

Ganin inya zauna tunani zai haye mishi yasa shi mikewa yana tattara takalmanshi da har tsakiyarsu ya kusan hujewa saboda jin jiki hadi da fadin

"Ni na fita Tasneem..."

Addu'ar tsari da dawowa lafiya sukai mishi. Tasneem na mikewa ta zauna inda ya tashi

"Azrah kinyi Sallah kuwa?"

"Yaya kefa kisa mukayi kamun ki fara soya wainar filawa. Kin manta?"

"Au..."

Dariya Azrah tayi, Hamnah sarkin son jiki harta matsa tana kwanciya a jikin Tasneem din data ke kallon kan Sabeena

"Beena kanki ya kwana biyu. Azrah daukomun abin taje kai da kibiya. Kuma anjima ku kwance naku kan in muku kitso, kunga gobe in Allah ya kaimu akwai Islamiyya..."

Mikewa Azrah tayi ta shiga daki ta dauko mata. Ita ta kwance ma Sabeena, Azrah ta soma kwance nata. Ganin Hamnah na bacci yasa ta kyaleta tai ma Sabeena, itama ko rabi ba aiba tai bacci, dan haka tana karasawa ta kwantar da ita.

Kasancewar Azrah akwai son kitso kanana, saida Tasneem ta sa ta matso danta tayata kwancewa. Suna yi suna hira abinsu.

*

Har bayan Magrib Ummi bata dawo ba. Sauran wainar filawar da suka rage da rana taba Hamnah da Sabeena suka ci. Ita da Azrah suka zauna suna Tilawar Qur'an.

Karatun su shiya fara dukan kunnen Abba tun daga soron gidan. Musamman muryar Tasneem dinma. Wani irin sanyi yaji da nutsuwa ta saukar mishi. Yafi mintina biyar a bakin kofar bayason yin Sallama ya katse musu karatun, kamun ya shigo, Hamnah ta amsa mishi sallamar, kamun sukai aya.

"Ma shaa Allah, anata karatu ne Tasneem"

"Wallahi kuwa Abba, ina taya Azrah ne...sannu da dawowa"

"Yawwa... Ummin ku bata dawo ba har yanzun ko?"

"Eh wallahi"

Duk da yasan fitar Ummin bai wuce bin gidajen yan uwa zubda mutunci da ta saba bai hana hakan bata mishi rai ba. Ta wani fannin kuma yaji dadin dawowarshi bata nan. Dan sai suyi shawar su da Tasneem hankali kwance

"Dari biyar na samo Tasneem, bansan ko za a iya yin wani abu da ita ba, ko zaku siyo abinci ne gidan Mariya?"

Girgiza kai Tasneem tayi

"Siyan abincin nan baida albarka Abba, sai kaga bai ishemu ba. Tunda muna da filawa, bari in je da ita saita auni rabi, mu bata Naira hamsin zata bamu taliya yar kadi. A siyo manja da yaji sai muci dukan mu"

Dari biyar din Abba ya bata, ta kuwa dauki Hijab da filawar, nan da nan taje ta amso ta dawo. Abban da kanshi ya fita ya siyo manja da barkono da farin magi. Cikin mintina talatin sun dafa taliyar su. Tasneem bata zuba musu ba saida sukai Sallar Isha'i.

Sauran kudin ma ita yaba ta ajiye a hannunta ayi wani abun da safe. Suna zaune suna hirar su Ummi tai Sallama. Har ta Azrah saida gabanta ya fadi. Cikin dar-dar suka amsa mata. Hannunta da baqaqen ledoji, waje ta samu ta ajiye su tana cire hijab dinta ta rataye kan igiya.

"Da wuta kenan"

Ta fadi, babu wanda yace mata kanzil.

"Saida ka fita na tuna yau Alhaji Sani yake dawowa daga Cotonou. In fada maka zanje in mishi sannu da zuwa"

"Kinje ai ko?"

Abba ya fadi yana binta da kallo. Murmushi tayi da dagashi har su Tasneem kan jima basu gani a fuskarta ba.

"Wallahi kuwa, naje a sa'a na samo abin arziqi"

Mikewa Abba yayi batare daya ce komai ba ya fice daga gidan. Tasneem ma mikewa tayi ta dauki Sabeena dake bacci tana kaita daki ta kwantar kan katifarsu ta sakar mata gidan sauro. Ledojin Ummi ta janyo gabanta tana budewa ta dauko lemon zaqi.

"Azrah dauko mun wuqa in yanka mana"

Mikewa Azrah tayi ta dauko wuqar ta bama Ummi tana nufar hanyar daki.

"Ina zaki kuma? Zoki karbi naki mana"

"Na koshi"

Azrah ta fadi tana shigewa daki abinta. Hamnah Ummi ta kalla, suna hada ido ta bata fuska tana girgiza ma Ummi kai hadi dabin bayan Azrah. Cikin sanyin murya Ummi tace

"Tasneem ga Lemon zaqi"

"Na koshi Ummi, munci abinci"

"Me kukaci?"

Kallonta Tasneem tayi fuskarta dauke da yanayi mai nauyi kamun tace

"Taliya da manja"

"Abban ku ya samo kudi ne?"

Kai kawai Tasneem ta daga mata da fadin

"Sai da safe"

Bata jira amsarta ba ta shige daki itama. Lemon Ummi ta ci gaba da yankawa haka kawai taji ranta baya mata dadi. Musamman da ta juyo dariyarsu, da alamun hira suke ba bacci ba. Shan lemon take badan tana gane zaqin shi kan harshenta ba. Guda uku tasha ta mike tana daura Alwala dan batai sallar Isha'i ba.

Sauran kayan ta kwasa zuwa kitchen, harda kayan miya ta ajiye, ta koma nasu dakin. Bata sa ran shigowar Abba ba, dan ta riga da ta saba sai tayi bacci yake shigowa gidan.

*

Kasancewar safiyar ranar Asabar ce yasa suna tashi wanka suka fara yi. Tasneem taima Sabeena. Sosai take kewar Islamiyya, tunda sukai sauka, Tahfiz dinsu sai dubu daya kudin Term ga littatafan su da tsada, tasan Abba baida halin shisa bata ko yi mishi maganar ba.

Cikin kudin dake hannunta ta fita da kanta ta siyo sabulun wanki, dan dashi suke wanka suyi wanki taga ya kusan karewa. Ta siyo sugar na Ashirin da kosai na Hamsin ta dawo. Koko ta hada musu. Tasu su a gaba suka sha.

Saida Azrah ta matsa mata tukunna ta dauki kosai daya. Tafison taga sunci, akwai sauran taliyar jiya ita take son dafawa ta ishe su ita da Abba. Tana tunanin abinda zasuci ne da rana kawai.

Har lokacin Ummi bacci take. Kasancewar harda Sabeena za'a je yasa Tasneem saka Hijab dinta ta rakasu tunda sai an tsallaka titi. Malan Musa tagani, cikin ladabi ta gaishe dashi.

"Tasneem kinqi dawowa makaranta ko?"

Kanta a kasa tace

"Zan dawo Malam"

"Kullum haka kike cewa zaki dawo, amman har yanzun shiru, kinsa shiririta ko?"

Shiru tayi dan batasan yanda zata ce mishi ba.  Sosai tana son ta koma makaranta itama. Cikin sanyin murya tace

"Sai anjima Malam. Azrah dan Allah ku kula wajen tsallaka titi, ki riqe Sabeena sosai"

Ta fada musu tana juyawa. Sai lokacin data koma gida sannan Ummi ta tashi, alwala take, da kanta ta kwankwasa musu kofa da Asuba. Dan gajiya na damun Abba, da yawan lokutta ita take tashin shi Asuba. Hatta Sabeena da Subh take tashin ta tai Sallah, tun tana mata kuka harta saba yanzun.

Wani lokacin kamun ta tashe su sun farka, saidai su koma bayan sun Idar.

"Ina kwana"

Ta gaishe da Ummi din

"Lafiya... Ina kikaje ke kuma tunda sassafe?"

"Takwas fa ta wuce, su Azrah na raka Islamiyya"

Tabe baki Ummi tayi

"Dan gulma? Su Azrah din zaki raka Islamiyya, kindai so gantali kawai"

Maganganun Ummi sun sosa mata rai, ko tai mata bayani ba fahimta zatayi ba, dan haka ma bata bata bakinta ba. Hijabi ta je daki ta ajiye ta fito tana gyara kurfot din gawayi hadi da zuba dan sauran da ya rage

"Me zakiyi?"

"Taliya zan dafa"

Ta amsa tana daukar mafici da fifita gawayin dan ya kama sosai.

"Kinga ga cefane nan, harda soyayyen nama, kiyi mun miya ki juyemun a kula, sai kita shirmen da zakiyi"

Ummin bata jira amsarta ba ta shige daki, taliyar Tasneem ta fara dorawa dan garwashin ya kama. Koda ta gyara cefanen ma, jajjagawa tayi a turmi dan batason taje tambayar Ummi kudin markade ta sauke mata.

A kitchen din taci tata taliyar ta ajiye ma Abba tashi. Har Maggi akwai, bata fito daga kitchen din ba saida ta gama miyar, dai-dai fitowar Ummi daga wanka.

"Ummi nagama"

Kitchen din ta karasa ta shiga, ta dauki wani kwano da kular miyar ta zuba tana kirga nama yanka takwas ta saka a ciki taba Tasneem din

"Gashi nan kowa bibbiyu. Ga biredi nan ku dauki daya ki mikomun dayan"

Mika matan tayi, tana kirga naman da idanuwanta. Bude baki tayi zatai magana Ummi ta katse ta da fadin

"Ban niyya ba mai Uba, ya nemo ya kawomun ne?"

Maida bakinta Tasneem tayi ta rufe tana daukar kwanan miyar da biredin ta wuce daki, lokacin da takeyi har miyanta ke tsinkewa da ganin naman, amman sam yanzun ya fice mata a rai. Har miyar ji take ba zata iya ci ba. Da biredin ta rufe dan batajin zata iya sake fita kitchen dauko murfi.

*

Daga Sallar Asuba, a masallaci ya zauna yana gyangyadi har gari ya soma sha, tun jiya ya wuce ta wajen layin birji yaga an kawo motar bulo, saukewar da sukai nema yasa ya samu dari biyar din daya kawo gida. Ya roqe su koda dibar ruwane su bashi ya samu dan wani abu shima.

Shugaban maginan wajen yace yazo, dan da alama ya tausayawa ma yanayin Abban, dan haka gari na wayewa ya nufi wajen, aikam harsun fito, da alama shaguna ne za'a zuba a wajen. Dan fili ne babba, sai kuma wasu gidajen kasa da aka soma rugujewa duk za'a shigar ciki.

Abban akace ya fara aikin ruguje gidajen kamun wasu suzo su kama mishi.

"Indai ba akai da dauko su ba, zanyi ni kadai ma"

Kallon shi shugaban maginan yayi

"Anya kuwa Malam, aikin da yawa fa..."

Dan murmushi Abba yayi

"In shaa Allah zan iya, in na gaza sai a dauko wani"

Jinjina kai yayi kawai. Kayan aiki Abba ya dauka ya fara. Yanda yake ganin katangun a idanuwanshi ya raina su da, sai da ya fara aikin yaga suna da kwari, koya hannuwanshi suka gaji, in su Tasneem suka gifta mishi ta cikin idanuwanshi sai yaji ya sake samun karfin ci gaba da aikin.

Har sha biyu yana abu daya, ga rana ta soma takewa, ya hada zufa yai sharkaf, jikinshi yai futu-futu da jar kasa. Ga kishi daya addabe shi. Wani waje ya zabto, qura ta cika mishi hanci da ido, bai lura da katangar dake rawa gabanshi ba saida lokaci ya qure.

Ya matsa amman wani qaton bulo ya fado mishi a qafa, runtsa idanuwanshi yayi dan azaba, yana tsugunnuwa ya daga da sauri, a wajen ya zauna yana kallon wata farar tsoka ta fito kamun jini ya soma ambaliya, abinka da wanda yasha rana.

Kafar yaja yana fitowa daga wajen, ruwa ya hango cikin tanki wanda ake aiki dashi, da hanzari ya nufi wajen, baima damu da yanda kasa take kwance a ciki ba, diba yayi ya fara sha tukunna ya zuba yana kokarin tsaida jinin dake zuba a kafar tashi, amman sam abin ya faskara.

"SubhanAllah. Malam ciwo kaji haka?"

Shugaban maginan ya fadi yana mika ma Abba baqar ledar dake hannunshi da ruwa. Karba yayi cike da dauriya yace

"Abune ya fado, ban kula da wuri ba. Amman zanci gaba da aikin a haka"

Girgiza kai yayi

"Dan Allah kaje gida ka huta... Kaje kemis a duba kafar kuma. Gobe in Allah ya kaimu sai ka shigo. Akwai yaro daya dazai kama mana ginin, an mishi rasuwa bazai samu zuwa ba. Saika maye gurbin shi, ai kace kana sana'ar dama ko?"

Jinjina kai Abba yayi cike da farin ciki

"Sosai kuwa. Nagode kwarai. Allah ya dafa maka yanda ka duba mun"

"Amin..."

Ya fadi yana saka hannu a Aljihunshi, dubu biyu ya kirga yan dari bibbiyu yana mika ma Abba, duk da aikin dayai baikai hakan ba. Sosai Abba yai mishi godiya. Saida yadan wawwanke jikinshi tukunna ya dingisa zuwa gida. Da ledar abincin a hannu.

Da sallamar shi mai kwari ya shiga, Tasneem ta amsa mishi tana fitowa daga daki, kallo daya taima kurar dake jikinshi zuwa kafarshi ta ware idanuwanta cikin tashin hankali, idanuwanta na cika da hawaye. Da sauri ta karasa inda yake

"Na shiga uku... Abba jini... Jini a kafarka... Inalillahi... Garin ya kaji ciwo?"

Tasneem take tambaya a rikice, kujera taja ma Abba ya zauna, ta kama kafar tana hurawa da bakinta, tama rasa me ya kamata tayi. Murmushi Abba yayi

"Tasneem bawani ciwo bane babba, jinin ne kawai"

"Haba Abba... Garin ya kaji ciwon nan"

Janye kafarshi yayi

"Ke kam kibar ciwon nan, dauko mana kwano muci abinci..."

Ranta a jagule tace

"Ni banajin yunwa... Abba muje chemist a duba kafar nan... Akwai sauran kudi dari da goma a hannuna"

"Rabani da kemis din nan kinji"

"Abba..."

Tasneem ta kira muryarta na rawa. Yasan hankalinta bazai kwanta ba. Hijab ta dauko, jan kofar gidan kawai tayi, hakan na nuna mishi alamun Ummin su ta sake fita, ya manta rabon da ta tambaye shi zata je unguwa.

'Allah ka shirya Bara'atu ko dan yaranta. Na yafe mata Allah ka yafe mata'

Yake fadi a cikin zuciyarshi, kemis din Emma suka je, dan duk in basuda lafiya nan suke zuwa, kasancewar shi inyamuri kuma kirista bai hanashi zama mai kirki da tausayi ba. Koda Abba baida kudi yakan basu bashin magunguna in Abba ya samu a hankali ya biyashi.

Duba kafar Abban yayi, yai mishi dressing dinta, bai karbi ko sisi bama, sai maganin da suka siya Dari da hamsin. Suka dawo gida, faranti ta dauko ta zuba mishi abincin, shinkafa da miya ce, daki ta shiga ta dauko naman da Ummi ta basu ta zuba ma Abba nata yankan Naman guda biyu ta mayar da sauran.

"Ina kuka samo nama?"

"Ummi ce ta kawo"

Bai sake cewa komai ba ya dauki abincin yaci. Ruwan dumi Tasneem ta dora ta sirka takai mishi yai wanka. Harya shirya zai sake fita, kudin aikin daya samo duka ya dauko su, dubu daya ya ware gefe, ya dauki sauran daya taba aka sai magani ciki ya mikama Tasneem.

"Ki riqe a hannunki karki bari Ummin ku tagani..."

Tana shiga dakinsu ta boyo kudin ta fito Ummi na shigowa da Sallama. Abba ne ya amsa mata, binshi tai da kallo tana tsayar da idanuwanta kan kafarshi.

"Kai kuma ina kaje kaji ciwo?"

Bai amsata ba dan yasan ba damuwa tai ba. Dubu dayar dake hannunshi ya mika mata, ta karba fuskarta ba yabo ba fallasa ta kirga. Kallon shi tai a sheqe

"Me zan siya da dubu daya? Duk ciwon da kaji dubu daya ka samo?"

Numfashi ya sauke

"Ki siyi duk abinda dubu daya zata siya"

"Kamar me?"

"Nima bansani ba"

Ya amsa yana wucewa zai fita

"Karfa kasa ran dawowa kaga abinci dan bansan abinda zan da dubu daya ba wallahi, kuma sabuluna ya kare ga man shafawa zan siya"

"Yanda duk kikaga ya kamata kiyi"

Abba ya fadi yana sakai ya fita. Inalillahi yake ta jerawa dan ita kadaice tsakanin shi da hawan jini ko ciwon zuciyar da yasan Bara'atu zata iya saka mishi. Ya bata kudinne dan akwai haqqinta da Allah ya dora akan shi. Badan haka ba zaiba Tasneem duka kudinne, dan yasan ba tausayi Bara'atu ta cika ba, dan tabar su da yunwa ba matsalarta bane ba.

BAYAN SATI HUDU

Haduwar Abba da Alhaji Zanna saita zame mishi alkhairi, dan sosai ya kula Abba ya iya aiki, sannan shi ba mutum bane mai ha'inci. Dan yau kwana hudu kenan daya dauki Abban zuwa Gusau. Zasuyi aikin ginin wani kamfani.

Yan kudin daya samu ne yabarma Ummi dubu biyar. Yaba Tasneem dubu biyu ta riqe a hannunta suna hidimar makaranta. Sai dai Tasneem bata zaton kudin da Abba yabar ma Ummi sun kwana. Dan kaji ta siyo har biyu. Da kanta tai miya ta dafa musu shinkafa. Akai cin dare daya.

Badan kudin da Abba yabar m Tasneem ba, da yunwa ta galabaitar dasu ba kadan ba. Dabara tayi ta siyo filawa ta dari biyar takai aka kada musu taliya tazo ta ajiye dan suna da yaji da manja. Yanzun haka da ta tashi safiyar Naira hamsin ta rage a hannunta.

Su Azrah taba suyi kudin makaranta, ta shirya itama ta fito Ummi tace ba zata ce ba.

"Ni fita zan gaskiya, ki zauna da Sabeena"

Idanuwan Tasneem taf da hawaye tace

"Ummi mun fara jarabawa fa jiya, kuma ta canjen aji ce"

"Sai meyene matsalata da jarabawarki?"

Daki Tasneem ta koma ta cire uniform dinta tana ninke su. Dacin da take ji a makoshinta yama hana hawaye su zubo mata. Kwanciya tai gefen Sabeena. Tana jin Ummi ta fice daga gidan, karatun su ko rashin shi bai taba damunta ba. Abba ne dai yana matuqar daukar karatun su da Muhimmanci.

So take Allah ya dawo dashi lafiya. Indai yana da wata a dinkama Sabeena Uniform, tunda hutun karshen zangone, in an koma itama a sakata. Dan da yawan lokutta saidai ta hakura da zuwa makaranta ta zauna da Sabeena a gida.

Bacci ne ya dauke ta itama, su dukan su basu tashi ba sai wajen goma. Babu abinda zatayi, ta riga da ta gama gyaran ko ina na gidan tunda sassafe. Yar Radio din da take ji dan rage kewa ta lalace tun tuni. Takai a duba akace dari uku ta dawo ta ajiyeta.

Dari uku kudine masu daraja a wajenta, zasu ci abinci dasu. Ba zatai amfani dashi ta gyara Radio ba. Tana daki taji kamar Sallama ake, saurarawa tayi sosai taji Sallama ce da gaske. Amsawa tayi tana fitowa. Gabaki daya fuskarta ta canza da murmushin da tayi.

Dan tun daga zuciyarta ya fito.

"Ya Tariq"

Ta fadi. Shima murmushin yai mata, yanayin rayuwa yasa yai wani irin duhu, hasken nan babu shi, ga wata irin ramewa da yayi, saidai ya kara tsayi naban mamaki.

"Tasneem"

Dariya tayi cike da farin ciki.

"Ya Tariq"

Ta sake maimaita sunanshi har lokacin ta kasa yarda shidinne a gabanta.

"Na dauka ma kina makaranta"

Girgiza kai tayi

"Banje bafa... Ummi ta fita saina zauna da Beena"

Jinjina mata kai yayi

"Oh... Ko kujera ban baka ba"

Ta karasa maganar tana janyo kujera ta mika mishi. Kitchen ta shiga ta dauko cup ta dauraye ta kawo mishi ruwa. Kadan yasha ya ajiye.

"Oh Allah Ya Tariq..."

Murmushi yayi

"Kinata magana kaman kina mamakin zuwana"

"Sosai wallahi... Ai ban kawo a raina bane fa....Ya Faq ma baya zuwa kwata-kwata, kaima din yaushe rabo. Abba yana ta tambayarku"

"Allah sarki Abba... Mun gaisa ai, kamun in tafi"

"Yaje Gusau aiki... Yaushe zaka tafi?"

Dan jim yayi kaman yana tunani, kamun yace

"Kilan zuwa jibi in shaa Allah. Yaushe zai dawo?"

Dan daga kafada Tasneem tayi

"Nima ban sani bafa, yace dai bazasu shige sati biyu ba. Ko kwana bakwai basuyi ba kuma..."

Gyara zamanshi Tariq yayi

"Allah ya dawo dashi lafiya"

"Amin dai... Dan Allah me yasa ba zaku dawo gida ba? Me yasa kuka tafi?"

Yanayin da ya mamaye cikin idanuwa da fuskar Tariq din da tambayarta yasa ta dana sanin yinta. Ta sani, saboda Arfa ne, me yakaita sake tambayarshi ma. Muryarshi can kasan makoshi yace

"Me yasa ba zamu tafi ba Tasneem? Me ya rage?"

Jinjina kai tayi, zuciyarta na mata nauyi

"Rayuwa akwai wahala ko?"

"Sosai.... Fiye da zaton ki"

Fuskarshi take nazari nadan lokaci kamun tace

"Kun barmu da kewa"

Dan murmushi yayi mai sauti dake cike da fassara kala-kala, tana son ta fahimci kadan daga cikin nufin haka, na cewar baida kalaman dazai ganar da ita abinda yake ji.

"Ina Ya Faq?"

"Wajen aiki"

Ya amsata a taqaice.

"Allah ya taimaka... Gidan yai qura ko?"

Girgiza kai yayi

"Ba sosai ba. Tsintsiya ma nazo ara wajen Ummi"

Mikewa Tasneem tayi tana shiga daki taga Sabeena bacci ta koma. Tana jikinta tayi ko bata da lafiya ne, taji kalanta. Gyara mata kwanciya tayi tana daukar tsintsiya da ruwa a bokiti

"Muje in tayaka a share gidan"

"Beena fa?"

"Bacci take... Sai in dinga dawowa ina dubata ko da zata tashi"

Bokitin ya karba, aikam tare suka share ko ina na gidan tas, lokutta irin yau in Ummi bata nan, takan shiga ta share gidan. Dan kasancewa ciki kawai yana saka tata damuwar ta ragu. Dan duk halin da take jin tana ciki, ganin gidan kawai kansata jin ba komai bane ba.

Bokitin ta dauka da tsintsiya Tariq yace mata

"Ina zuwa"

Yar jakarshi dake ajiye ya bude, Radio karama ya ciro a kwali yana mika mata, kamun ta gama mamaki ya miko mata kwalin battery kanana sai torchlight.

"Ya Tariq..."

Ta soma ya katse ta da fadin

"Dan Allah karkice zakimun godiya Tasneem"

"Kasan godiya dole ne"

Ta fadi muryarta dauke da yanayin da take ji. Bai manta ba, zuwan dayai

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment