Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na karshe taje gyaran Radio din tata ne. Fitilar ma haka, dan ya shigo mata sallama da daddare cewar da sassafe zai wuce ya same su cikin duhu, Ummi ma bata nan.

"Nidai bana so... Babu godiya a tsakanin mu ai"

Duk da haka sai da tace

"Nagode sosai. Allah ya saka da alkhairi yabar zumunci"

"Kije kar Beena ta tashi"

Murmushi tayi tana wucewa. Ranta wasai, zuwan Tariq a koda yaushe na kawo mata sauqi. Ko Yaya ne saiya bar mata abinda zata kara jin kewarshi duk idan ya tafi kamun ya dawo. Tana shiga gida daki ta nufa ta fara adana battery din.

Ta bude radio din, da battery a ciki. Rungumeta tai a kirjinta hadi dayin dariya. Tasan sosai an wuceta a shirye shiryen duk da take bi, amman samun Radion zai rage mata kadaici, su Azrah ma zasuji dadi, dan tare suke ji da daddare, tunda ba kayan kallo suke dashi ba.

Kunnawa tayi kuwa, ta koma gefen Sabeena ta kwanta

"Allah ya kawo muku sauqi kaman yanda kake kawomun da duk zuwanka Ya Tariq"

Ta tsinci kanta da fadi. Koda Sabeena ta tashi zamansu sukai a daki. Bata fito ba sai da taji kiran Sallah. Sannan tasan su Azrah na gab da dawowa. Dan haka ta dafa musu taliyarsu yar kullum. Zubawa tayi a kwanon silver ta rufe taba Sabeena takaima Tariq.

Dawowa tayi da ledoji har biyu a hannunta, dayan kuma a dumtse ta mikama Tasneem duka biyun.

"Wai a kawo miki"

Karbar ledojin tayi ta ajiye sai kudi a duqunqune, budewa tayi, dubu biyune. Dan dafe kai tayi tana rasa abinda take ji.  Jakar makarantarta ta janyo ta saka kudin a ciki. Sannan ta bude ledojin, awara ce sai dankalin Hausa soyayye.

Dariya Tasneem tayi, kamun kewar lokuttan da ita da Tariq din kanje siyan dankalin da awara su danne ta. Diba tayi sukaci ita da Sabeena ta ajiye ma su Azrah nasu suma.

*

Da La'asar sakaliya Ummi ta shigo gidan, da buhunnan bakko har uku ta ajiye, Tasneem kawai ta samu a gidan da Radion ta tana ji. Ta amsa sannun da Tasneem tai mata. Kallo daya tai mata ita da Radion da take ji ta dauke kanta tana shiga daki ta fito da tabarma.

Shimfidawa tayi ta shiga zazzage kayyakin dake cikin buhunnan da fadin.

"Su Azrah su zo, kwana biyun nan kamun Abban ku ya dawo su zagayamun da gwanjon nan"

Ba shiri Tasneem ta mike tana kashe Radion.

"Gwanjo kuma Ummi?"

"Eh gwanjo na saro, na gaji da zama haka nan. Gara kamun dan bakin cikin Abban ku ya dawo su zagaya mun dashi. Kema da zaki dauka ai ba daga nan ba"

Cike da tashin hankali Tasneem tace

"Wai talla Ummi?"

Kafeta Ummi tai da idanuwa.

"Eh talla. Akwai wani abu ne a ciki?"

"Abba fa ya hana maganar tallar nan tun tuni"

Tasneem ta fadi muryarta can kasa, dan ranar da Ummi ta dorama Azrah tallar gyada ne ranar farko da zata ce taga bacin ran Abba. Marin Ummi ne kawai baiyi ba, duk fadanta shiru tayi dan ita kanta ta tsorata. Bata kuma sake gwadawa ba sai yanzun da baya nan.

"Uban me Abban naku yake tsinanamun? Eye? Nace uban me yake tsinanamun da zan haifeku yace bazan mora ba? Ku duka kunfi son shi akaina. Ba zamu taru mu rufa ma juna asiri ba? Harda ke Tasneem? Kina zaton in aurenki ya tashi Abban naku zai iya tsinana wani abin kirki ne?"

In akwa abinda yafi batama Tasneem rai bai wuce taji Ummi na ma Abba irin wannan tozarcin ba. Zuciyarta har zafi-zafi take mata saboda qunar da take.

"Ni dai Ummi dan Allah kiyi hakuri kibar maganar Tallar nan..."

A hasale Ummi tace

"Sai inyi me da kayan? In zauna ina kallon su? To wallahi badani za ai wannan asarar ba. Ko ke ki dauka ki zagayamun dasu ko su Azrah su dauka"

Tashi Tasneem tayi tana shiga daki. Idanuwanta cike taf da hawaye har dishi dishi take gani, ta bude jakarta ta lalubo dubu biyun da Tariq ya bata ta fito. Mikama Ummi tayi.

"Meye wannan din?"

Ummi ta tambaya a fusace, ware kudin Tasneem tayi, ganin dubu har biyu yasa Ummi saurin kawo hannu ta karba, fadan da take na juyewa da fara'a.

"Yar albarka..."

"Dan Allah kibar maganar Tallar nan"

Murmushin Ummi ya fadada

"Da muna haka ai da ba aji kanmu ba. Dan zancen nan Tasneem kin biyema Abbanku bakya fita. Ke bakya ganin Su Dije yanda samari ke musu hidima"

Juyawa Tasneem tayi, bata son Ummi taga hawayen da suka sami damar zubo mata. Ta dauka Ummi zata tsareta da tambaya akan inda ta samu kudin ne, sai taga bata damu ba sam. Asalima tafi damuwa da yanda zata samo wasu. Radio dinta ta dauka ta shige daki.

Kuka marar sauti har ta kware akanshi. Tana jin Ummi na hidimarta tsakar gida. Kamun ta juyo muryarta da fadin

"Kin fanshi su Azrah. Ni bari in fita in zagaya dakaina kamun Magriba tayi"

Dafe kanta Tasneem tayi da hannuwanta duka biyun tana girgiza shi. Neman dalilin da yasa Ummi take daban da sauran iyaye mata takeyi ta kasa samu. Kuka take sosai har idanuwanta sun kumbura, taji Sallamar Tariq. Da sauri ta goge fuska tana kakaro murmushi ta dora a fuskarta ta fito.

Kallo daya yaima fuskarta yace

"Waya saki kuka?"

Girgiza mishi kai tayi tana kasa magana.

"Tasneem..."

Yanda ya kira sunanta nasa zuciyarta sake yin rauni. Kuka ta fashe dashi wannan karin mai sauti. Tsaye Tariq yayi yana kallonta, har saida tai mai isarta, da kanta ta wuce ta dauki buta ta wanke fuskarta ta dawo ta zauna kofar daki.

Kujera yaja ya zauna yana kallonta dake fassara ta dauki duk lokacin da take bukata zai jira ta nutsu ta fada mishi meke damunta.

"Ummi... Nagaji da matsalar Ummi Ya Tariq"

Sauke numfashi yayi

"Me tayi?"

"Hmm..."

Kawai Tasneem ta furta, dan bata san ta inda zata fara ba. Meye ma Ummi batayi ba. Juya kujerar Tariq yayi ya fuskance ta.

"Dazun kike tambayata tabbaci kan wahalar rayuwa Tasneem. Komai bazai dawwama a haka ba... Komai zaiyi sauqi in kika jure... Akwai wahala....amman kiyi hakuri zai wuce kinji?"

Kai ta daga mishi.

"Dan Allah kiyi hakuri. Ki rage yawan damuwa. Gobe da safe zan wuce"

Muryarta a dakushe tace

"Da sauri haka? Baka ce kwana biyu zakai ba?"

Girgiza mata kai yayi.

"Wani abune ya taso... Shisa"

Rausayar dakai gefe Tasneem tayi, dan ssauqin da zuwanshi  ya kawo mata na dishewa.

"Yanzun sai yaushe?"

Ta bukata idanuwanta na kawo hawaye.

"In shaa Allah bazan dade ba. Zan dawo... Ki kula da kanki"

Kai ta daga mishi tana share hawayen daya zubo mata.

"Zan sake ganin ka kamun ka tafi?"

Wannan karin shiya daga mata kai yana mikewa. Saida safe yai mata yana ficewa daga gidan. Bai jima da fita ba su Azrah suka dawo.

"Ummi ta dake ki ko?"

Hamnah ta tambayeta muryarta na rawa da alamar gab take dayin kuka. Murmushin Tasneem tayi tana girgiza mata kai

"Injiwa yace Ummi ta dake ni?"

"Kuka kikayi. Idanki yayi ja"

Hamnah ta fadi. Tasneem kan danganta kular Hamnah kan abubuwa da yawa da rashin yawan maganarta. Tafi bin komai da idanuwanta fiye da bakinta. Hakan yasa tana lura da duk abinda yake faruwa kusa da ita.

"Idona ne zaimun ciwo.... Yana zafi tun dazun"

Tasneem ta amsa, tana kin kallon Azrah dake mata kallon tuhuma. Tasan su duka ba yarda sukai ba. Sunkai matakin da wayonta baya tasiri akan su.

"Ku tsaya kugani"

Ta fadi da sauri tana shiga daki ta dauko Radio da fitilar da Tariq ya siyo tana nuna musu.

"Fitila... Mun samu fitilar karatu inba wuta... Waya siyo mana?"

Azrah ta fadi muryarta cike da farin ciki.

"Ya Tariq"

Tasneem ta amsa ta. Karbar fitilar Azrah tayi tana duddubawa. Rigar ta Sabeena ta kama tana son cirewa. Dan haka Tasneem ta ajiye fitilar tana kama mata rigar dan ta cire. Tsayin da take yi naba Tasneem din mamaki.

Ita da Azrah su suka biyo tsayin yan gidansu Abba. Su ukkun babu tazara a tsakanin su dan kuwa Ummi kwanika tayi, tsakanin Azrah da Hamna shekara daya da wata biyar. Ita da Azrah ne shekara biyu. Sai Hamna da Sabeena akwai tazara sosai. Yanzun ita Tasneem shekaru cikin na sha bakwai take.

Azrah Sha biyar, sai Hamnah sha hudu. Duk da makarantar du Azrah da Hamna daya. Ita gwammaja take. Kasancewar lokaci daya aka saka su makaranta da Azrah dan harma tafita tsayi yasa matakin karatun su daya.

Sai bayan ta cire ma Sabeena rigar ne ta kula Hamnah bata nan.

"Ina Hamnah?"

Ta tambaya. Dan daga mata kafada Azrah tayi alamar itama bata sani ba. Tasan su dukansu babu inda suke zuwa. Tasan Hamnah bazata wuce shiga tayi su gaisa da Tariq ba. Aikam gidan su Tariq din ta shiga. Tana sa hannunta ta shafi katangar gidan.

Tanajin kamar ace tana da ikon dawo musu da komai yanda yake. Sallama tayi a hankali tana kwankwasa kofar dakin duk da a bude take.

"Waye?"

Tariq ya tambaya da razana a muryarshi.

"Nice..."

Ta amsa a taqaice.

"Shigo"

Ya amsa. Labulen ta daga taba dora shi kan kyauren kofar duk da akwai fitila data cika dakin da hasken, tunda magriba ta doso kai. Kwalaben dake gabanshi ta soma kallo tukunna ta kalli fuskarshi da idanuwanshi da sun fara sake launi.

"Hamnah..."

Ya kira da wani yanayi a muryarshi. Jin muryarta yasa baiko kokarin boye kwalaben ba. Ya dauka Tasneem ce dayaji kwankwasawa.

"Baka daina ba. Baka daina sha ba"

Zame jikinshi yayi kan katifar dakin yana kishingida hadi da lumshe idanuwanshi.

"Muryoyin dake cikin kaina...ina son jin shiru. Surutu yai yawa a duniyata"

"Me yasa shi kadai ne hanya? Me yasa babu wata hanyar?"

Bude idanuwanshi yayi da suke wani lumshewa da kansu.

"Na gaji da jin tambayoyin da basu da amsa..."

Juyawa Hamnah tayi tana kama labulen zata sakar mishi.

"Baki ce komai ba... Ba zaki fadamun yanda da duk kwalba nake nisa da hankalina ba"

Batare data juya ba tace

"Me zan fada maka daba ka sani ba Ya Tariq?"

Maida idanuwanshi yayi ya rufe gam. Dan bakin shi yayi nauyi bayajin zai iya magana. Yana jin yanda yake bacewa zuwa wata duniyar ta daban. Labulen dakin Hamnah ta sakar mishi tana ficewa ta koma bangaren su.

"Ina kika je?"

Tasneem ta tambaya badan bata sani ba, sai dan tana son tabbaci.

"Gaisawa da Ya Tariq"

Hamnah ta amsata tana wucewa daki dan ta cire uniform dinta. Tasan rashin maganarta na kara zama dalilin da suke ganin kamar bata san abinda take ba, kamar shekarunta sunyi karanci ta fahimci abubuwa da dama.

Saidai har a zuciyarta bata son magana kan abinda ba zata iya canzawa ba. Shisa tafi binsu da kallo akan tai magana. Banda Tariq ko su Tasneem basu cika jin maganarta ba. Shima din tun tashin ta inta ganshi ne kawai tana son mishi magana. Ko da ba zatai magana ba zata tsinci kanta da zuwa inda yake ta tsaya.

Tasan yanda fuskar Tasneem take in tayi kuka, ba tun yanzun ba, tun tana yar karamarta wayon Tasneem bai taba tasiri akanta ba. Shiru kawai take yi mata.

*

Ranar Ummi ma bata dawo ba sai bayan Isha'i. Suna zaune sun fara jin shirin Inda Ranka a gidan radiyon Freedom wani yaro ya shigo da Sallamarshi hannun shi riqe da baqar leda.

"Wai gashi aba Tasneem"

Ai kamun Tasneem din tace wani abu tuni Ummi ta taso ta karbi ledar hannun yaron tana fadin

"Inji wa?"

"Alhaji Madu kuma wai tazo"

Ware idanuwa Ummi tayi, Alhaji Mado tsohon sanata ne, bayan unguwarsu yake da tanqamemen gida, amman ance iyalanshi na zaune a unguwar rijiyar zaki. Yaron ya juya yana ficewa. Kankance idanuwa Tasneem tayi da suke a kumbure har lokacin saboda kukan da taci.

Tun kwanaki da take dawowa makaranta ya dinga binta a mota. Taki sauraren shi, dan tasan tsoho dai mai shekarun shi inda mutunci bazai bita ba. Dan a haife ya kusa jika da ita.

"Tasneem kinga arziqin Allah ko?"

"Tun rannan ya dinga bina na dawo makaranta. Ashe saida ya gano gidan nan... Bari Abba ya dawo wallahi in fada mishi yai mai magana"

Da hanzari Ummi ta karasa inda Tasneem din take tana riqo mata riga

"Kiyi me? Ke baki da hankali ne wai? Yaushe zaki nutsu? Kina dai fita kin kuma ga girman gidan shi dake bayan mu. Wallahi tun kamun inyi kasa-kasa dake ki tashi kije ku gaisa"

"Cikin daren nan?"

Azrah ta fadi tana bin Ummi da wani kallo da Tasneem din bata so. Dan haka ta mike, tasan kaunar kannen nata, bata son ransu na baci da Ummi akanta, daman dazun suna dauka Ummi ta daketa. Hijab din datai Sallah dashi na jikinta dan haka ta saka a jikinta, ta kama hanya.

Ummi nacan na bude ledar da aka kawo cike da kaji da fresh milk Hamnah ta faki idonta ko takalmi bata tsaya sawa ba balle hijab tabi bayan Tasneem din da tana fita Alhaji Madu ke washe mata hakoranshi.

"Tasneem?"

Kallon shi tayi, yanayin yanda yake kallonta yana wani kyafta idanuwa yasa dan sauran mutuncin shi da take gani ya karasa zubewa. Bude baki tai zata amsa shi taji an fisgo hannunta. Juyawa tayi cike da mamaki take kallon Hamnah dake maida numfashi.

Tunda take da Hamnah ko fada da yara kanyi bata taba ganin tayi ba, a Islamiyya da boko lokacin da take Primary, amman yanayin dake shimfide kan fuskarta a yanzun ya tsorata Tasneem din. Gaban Tasneem ta shiga tana son zama katanga tsakanin ta da Alhaji Madun.

Tana jin daya daga cikin yan ajinsu na cewa Mamanta tace koya kirata karta sake taje. Ta ruga gida, dan iska ne, bata gama sanin cikakken abinda kalmar take nufi ba, amman yanayinta sam ko dadin ji bai mata ba, bakuma tason ko kusa da Yayarta ta gifta balle ta rabe ta.

"Banda girma sosai, amman ina da kawaye da yawa kuma dukkan mu munsan inda kake ajiye motarka, inka sake zuwa wajen yayata sai mun kunna ma motarka wuta. Kuma Wallahi sai nayi Addu'a Allah ya kasheka"

Ware idanuwa Tasneem tayi tana kallon Hamnah kamun wata irin dariya ta kubce mata. Shi kanshi Alhaji Madu mamaki ne bayyane kan fuskarshi. Kama hannun Tasneem dake dariyar data jima batai irinta ba Hamnah tayi tana watsa ma Alhaji Madu harara.

"Yaya zo mu tafi"

Binta Tasneem tayi, ta kasa daina dariya da take har lokacin. A soron farko Hamnah ta tsaya, ko ina jikinta bari yake yi, rungume Tasneem din tayi a jikinta.

"Yaya gabana faduwa yake Wallahi..."

Riqeta Tasneem tayi a jikinta tana dariya har lokacin

"Haba jarumata... Ku da zaku kunna ma motar Alhaji Madu wuta ke da kawayen ki?"

Dariya Hamnah tayi, su dukansu dariya suke. Hamnah na riqe jikinta suna dariya suka shiga gida. Ummi ta kalle su

"Harkin dawo?"

Kai ta daga ma Ummi tana kokarin gintse dariyarta.

"Haka yace dare yayi"

Hamnah ta fadi. Sosai Ummi ta kalleta, kamun tace

"Kuzo ga kaza"

"Nidai bana ci"

Hamnah ta fadi tana zamewa daga jikin Tasneem zuwa daki, Azrah nabin bayanta dan itama bata jin zata iya cin naman indai ba Tasneem da kanta zata bata ba.

"Kizo ki karba ki basu...nasan zasu karba inke kika basu da kanki"

Karasawa Tasneem tayi ta karbi kunshin kazar guda daya da Fresh milk din. Murya Ummi ta sauke da fadin

"Tasneem ki rufa mana asiri kamun Abban ku ya dawo ki lallaba mu kwashi arziqin mu wajen Alhaji Madu"

Kai kawai ta daga ma Ummi da murmushi a fuskarta, hakan yasa Ummi washe baki

"Yawwa yar albarka"

Daki Tasneem ta wuce tana samun waje ta zauna. Labarin abinda ya faru taba Azrah, har tsakar gidan Ummi najin dariyarsu kamar tababbu. Ta wanni fannin zuciyarta na mata wani iri da rabon da suyi dariya haka a gabanta.

Wani lokaci ko hira suke a tsakar gida inta sa baki sai su duka suyi shiru. A hankali zasu dinga tashi suna bar mata wajen suna komawa daki komin zafin da akeyi kuwa. Sabeena ma yanzun bata nemanta. Ko da Tasneem na makaranta ma yarinyar zatai ta zama a daki tana jira saita dawo ta fada mata tana bukatar wani abu. Tashi tayi ta shige daki itama da sauran kazar dake cikin ledar.

*

Bacci ne ya dauketa bayan tayi Sallar Asuba, dan ta dade bata same shi ba daren jiya sabo da tunani dayai mata yawa. Dan haka a gurguje take hada komai tana taya su Azrah suka karasa shiryawa, dan tama haqurema ranta zuwa makaranta ranar.

Sai da taga fitarsu tukunna, da hanzari ta dauki Hijab dinta tana nufar sashin su Tariq. Kofar dakin data gani a rufe an maida labulen ciki ya fara sanar da ita ya tafi. Duk da haka taki barin zancen ya karasa zuciyarta saida ta karasa ta bude kofar taga baya ciki.

Zuciyarta taji tayi tsaye waje daya. Haka yace zasuyi Sallama kamun ya tafi, ko godiya bata samu ta kara mishi ba. Tasan zai iya watanni kuma bai dawo ba. Tana kewar lokuttan da katanga ce kawai tsakanin su, har makaranta tare suke fita.

Idanuwanta taji sun cika da hawaye. Ga tsoro daya cika mata zuciya, yanda komai yake canzawa lokaci daya na firgitata. Sai taji kewar Abba ta danne ta, inda yana nan ko ganin shi tayi sukai labari ranta zai sanyi.

"Allah ya tsareka a duk inda rayuwa takai ka Ya Tariq. Nagode da sauqin da zuwanka yake kawo mun... Allah ya dawo dakai lafiya..."

Ta ke fadi a tsakar gidan tana saka gefen Hijab dinta ta share hawayen dake cike da idanuwanta.

"Dan Allah karka dade da yawa... Kai kasan inda nake, ni bansan inda zan ganka ba...karka dade..."

Ta karasa muryarta can kasa, wani abu na tsaya mata a zuciya...!
[11/30, 10:17 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com
Alkalamin Kaddara.

05

Daki ta koma ta kwanta, jinta take kamar marar lafiya. Ta jima a haka kamun ta yanke hukuncin tashi. Sun tara wanki kwanakin nan biyu. Dan haka ta duba taga suna da sabulu, tattara wankin tayi ta fito dashi waje ta ajiye.

Ta dauki jarkoki, ruwa ta dibo ta ciccika ko ina, ta fara wankin kenan Ummi ta fito daga daki. Gaishe da ita Tasneem din tayi tana dorawa da

"In kina da wanki ki fito dashi Ummi, amman sabulun bazai isa ba, in kina da wani saiki karo"

Daki Ummi ta koma ta hadoma Tasneem kayan wankin nata harda zanin gado, sai sabulu guda daya da omo biyu. Sannan ta wuce bandaki. Tasneem batai mamaki ba, ganin Ummi na Alwala dai-dai wannan lokacin. Sallah kan lokaci bai dami Ummi ba sam. Tana kuma gamawa ta sa Hijab ta fice daga gidan batare da tace ma Tasneem din ga inda ta nufa ba.

Wanki tasha har wajen 12 tana fama. Dan wasu kayan ma basu samu wajen shanya ba sai gidan su Tariq ta shiga ta shanya sauran a can ta dawo. Tunanin abinda zata dafa musu ta somayi. Dan batason su Azrah su dawo makaranta babu abinda zasu ci. Kazar da Alhaji Madu yakawo ce sukaci da safe daman.

Kitchen din ta shiga, gawayinsu ko ruwan zafi bazai dafa ba. Ga yanayin sanyi ya fara shigowa. Har tausayin Sabeena taji da zatai mata wanka da safe, saboda ruwan yayi sanyi da yawa. Ledar taliyarsu ta duba itama tai kasa sosai. Gabaki daya ranta ya jagule, bata san yanda zatayi ba.

Addu'a take Allah ya dawo musu da Abba lafiya. Dan inbai dawo ba zasu sha wahala. Dabara ta fado mata data shiga dakin Ummi ta duba ko zata samo wani abin. Saidai tana zuwa taga Ummi ta kulle dakinta harda kwado a jiki. Tsaye tayi bakin kofar jikinta a sanyaye.

Sabeena ta fito tana kallonta

"Yunwa ko Beena?"

Kai ta daga mata a hankali kamar batason amsawa, hannu Tasneem ta mika mata, ta karaso tana kamawa. Rike yarinyar tai a jikinta tana jin idanuwanta sun ciko da hawaye. Bata san iya lokacin da suka dauka a tsaye ba, saida taji kafafuwanta sun gaji tukunna ta zame tana zama ta zaunar da Sabeena a jikinta.

Suna nan zaune taji Sallamar Ummi, da sauri ta amsa tanabin ledar da Ummin ta shigo da ita da kallo.

"Sannu da zuwa"

Kallon su Ummi tayi

"Lafiya kukai zaune anan kamar marayu"

Ta tambaya. Cikin sanyin murya Tasneem tace

"Beena ce take jin yunwa. Babu komai da zamu dafa a gidan"

"To me kuke so in muku? Ubanku nawa yabarmun dazai tafi? Kuna gani dai rana daya komai ya kare. Munafuncin banza ai nasan yabar miki kudi kika boye saboda bakin hali irin na ubanki"

"Wallahi kudinne na siyo mana filawa muka kai aka murza taliya dasu Ummi, sun kare kuma"

Tabe baki Ummi tayi

"Nidai banda wasu kudi a hannuna gaskiya"

Wani abune mai daci yai ma Tasneem tsaye a wuyanta. Tana rasa hali irin na Ummi, ita bata damu da yunwarsu ba, kome zasuci koma ina suke samun abincin da zasuci. Halin Ummi zuwa yanzun tasan shi tsaf, takuma san ba zata bata kudi ta siyi abinci ba.

"Ki ara mana dan Allah Ummi mu siyi wani abin. In Abba ya dawo sai in karbar miki"

Harara Ummi ta sake watsa mata. A hasale tace

"Da yake binshi kikai yace miki ya samo kudi ko? Satin shi nawa yau? Inda adalci ko aike ai saiyai mana. Tunda yasan ba wata tsiya yabari ba dayasa kafa ya fita. Banda su kinajina ko?"

Hawayen da Tasneem take tarbewa ne suka zubo. Tasa hannu ta share su kamun Ummi tagani kuma ya zama wani abin.

"Zan fita in Alhaji Madu yazo..."

Juyowa Ummi tayi

"Da gaske?"

Kai Tasneem ta daga mata. Washe baki Ummi tayi, fuskarta shimfide da fara'a kamar ba lokacin ta gama fada ba. Jikin habar zaninta ta laluba, ta zaro kudi da suke a cukurkude, ta warware, zasu kai dubu shidda. Dubu daya ta zaro ciki tana mayar da kudinta ta mika ma Tasneem din.

"Bawai kyauta na baki ba. Zaki biyani abuna wallahi, dan ubanku bazai tsallake yabarmun wahalarku ba. Bazan iyaba"

Mikewa Tasneem tayo da sauri tana karbar kudin kafin Ummi ta canza zuciyarta ta hanasu. Hannun Sabeena ta kama suka fice, shago sukace ta auni shinkafar hausa ta siyi farin mai da farin magi da yaji. Sauran canjin ta biya ta siyi gawayi. A hanyar dawowa ta tsinci ledojin da zata kunna gawayi dasu.

Bata sami Ummi a gidan ba, ta sake ficewa, sai baqar leda data ajiye musu kan kofar dakin su, hakan na nuna ma Tasneem cewar komeye a ciki nasune. Dauka tayi ta bude, miyace da nama a ciki. Kitchen takai ta ajiye ta hada gawayin ta fito.

Alwala tayi ta dora ruwa dan gawayin ya soma kamawa tukunna ta sa Sabeena tai Alwala itama. Sallah sukai ta Azahar tukunna ta zauna zaman tsince shinkafa dan tasan akwai tsakuwoyi sosai a ciki. Anan su Hamna suka sameta da sallamar su.

"Yaya wanki kikai? Ba zaki jira muzo muyi tare ba?"

Hamna ta fadi. Murmushi Tasneem tayi

"Kuda kukaje makaranta, ga Islamiyya kuma. Banaso wankin ya taru sosai shisa. Wani karin munyi tare ai"

"Sannunki da aiki"

Azrah tace tana ajiye ledar da litattafanta suke ciki ta shiga daki ta, tsaye Hamna tayi saida Azrah ta sake kaya ta fito tukunna ta shiga itama ta sake kaya. Tana fitowa jikinta da hijab wajen robobin ruwan su tayi.

"Hamna me zakiyi? Jarkar nan ta miki girma. Kibari kici abinci kuma saiki dibo ruwan"

Cewar Tasneem.

"Zan iya dauka fa wallahi, rannan ma na dauko ko Azrah?"

Girgiza kai Tasneem tayi

"Ai bansani ba. Karki sake daukar jarkar nan ko bana nan. Ki dauki bokiti inma ruwan zaki dibo. Kuma ki dawo ki zauna saikin ci abinci tukunna. Akwai na amfani yanzun ai"

Turo baki gaba Hamna tayi tana dawowa ta sami waje ta zauna. Tayata tsintar shinkafar suke. Kamun Azrah tace

"Ina kika samo shinkafa?"

"Ummi taban kudi"

"Alkawarin me kikai mata?"

Hamna ta tambaya tana tsareta da ido. Tiren da shinkafar ke ciki Tasneem ta dauka batare data amsa ba. Dan bata son yanayin dake muryar Hamna sam, batason yanda a hankali halayyar Ummi ke nisanta kaunarsu da ita. Ko da ta zuba shinkafa kitchen din ta zauna dan karta fita su sake tsareta da tambaya.

Bakin kitchen din suka dawo suka sa tabarma suka zauna. Sabeena tasa ta dauko mata Radio dinta a daki, dan tama manta da ita duk ranar. Kunna musu tayi ansa wakokin Hausa a Fm. Sunaji harta gama abinci suka ci, saida Hamna ta cika ko ina na gidan da ruwa tukunna sukai Sallar Asr suka shirya suna tafiya Islamiyya.

*

Washegari haka su Hamna suka tafi makaranta batare da ko sisi ba, har a ranta Tasneem take jin tafiyar da zasu ci yau. Fatanta kar a kwalla

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment