Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufo shima, tukunna yace

"Ko ina banda nan"

Kai kawai Muneeb din ya daga mishi yana jan motar baya ya samu ya juya yana hawa titi. Rafiq kam jingina jikinshi yayi sosai da jikin motar. Ya rasa tambayar daya kamata ya fara yima Muneeb. Yana son sanin yanda akai yagane Tasneem ba budurwa bace ba. Sai dai babu yanda za ai kalaman su fara fitowa kan su gauraya da iskar da zata gifta ta kusa da Muneeb ma ballantana ya sani.

Sirrin shi nada muhimmanci a wajenshi. Ballantana sirrin daya shafi gidan aurenshi, sirrin daya shafi Tasneem. Baisan lokacin daya suka dauka ba. Kawai ji yayi Muneeb ya tsayar da motar. Dagowa Rafiq yayi yagansu tsaye bakin Blue Cabana. Kallon Muneeb yayi

"Haka nace wani waje, saika kawoni restaurant"

Dan daga kafadunshi Muneeb yayi yana zare mukullin motarshi.

"Nan ya fara zuwa raina"

Bai jira amsar Rafiq dinba ya bude ya fito, hakan yasa shima ya fito yana rufe murfin. Mukullin Muneeb yasa ya kulle motar tukunna suka jera suna shiga wajen tare da Rafiq. Bangaren manyan mutane da akafi kira da VIP Muneeb ya nufa dan ko basu da maganar da zasuyi nan suke zama.

Kuma bayason wani a wajen yagane Rafiq. Komai zai warware in wani ya gane Rafiq din, duk da ba karamin kallo zakai mishi ba kamun kagane shi. Daga shiga har yanayin askin shi, amman mutane basa gajiya daba Muneeb mamaki. Lemuka yasa a kawo musu duk da yasan da wahala Rafiq din yasha.

Daukar Cup daya Muneeb yayi yana kurba dan ya jiqa makoshin shi. Rafiq na zaune da wani nisantaccen yanayi a tare dashi. Sake kurbar lemon Muneeb yayi yana shirin hadiyewa Rafiq yace

"Na taba aure a baya?"

Lemon Muneeb yaji yabi wata hanya ta daban yana sarqeshi, lokaci daya ya fara tari, babu shiri ya kwankwade duka abinda ke cikin cup din yana kara zuba wani, ko motsi Rafiq baiyi ba, kallon Muneeb din yake har tarin ya tsagaita mishi yana gyaran murya. Hannu yakai yana goge idanuwanshi da suka kawo hawayen wahala.

"Me yasa kake mun tambayar nan? Inka taba aure kai baka sani ba, ni ne zan sani?"

Gyara zama Rafiq yayi, ba saiya karanci ilimin gane yanayin dan adam bane zai fahimci yanayin Muneeb ya nuna alamun rashin gaskiya. Sai dai ya rasa dalilin dayasa zai mishi karya.

"Saboda babu abinda yake dai-dai a rayuwata Muneeb, zan iya tuna har yarinta ta, abotarmu, in ba na fara samun tabin hankali bane, nasan lokuttan da muke fita kuma nine nake tuqin, lokaci daya na tashi na fito na shiga mota na kasa tuqawa? Me yasa? Banyi magana ba saboda Nuri da kanta tacemun sai dai in na manta dama can driver gareni...sai nake dauka a tunani nane kawai... Abubuwa da yawa suna faruwa dana kejin akwai tushen su, amman na rasa... In su Nuri sunqi fadamun, me yasa kai ba zaka fadamun ba?"

Wasa Muneeb yake da cup din hannunshi yaki dago dakai, zufa yakeji tana taruwa a bayan wuyanshi, basan yanda zai kalli Rafiq yai mishi karya ba, bai kuma san yanda zai fada mishi gaskiya ba, saidai baya tunanin zai yafe mishi lokacin nan idan ya gane karyar dayai mishi. Bayan haka akwai alkawarin da su duka suka daukar ma Nuri na ganin sun kare Rafiq din daga gaskiyar.

Kallon shi Rafiq yakeyi, shirun shi na kara tabbatar mishi da cewar akwai abu mai girma da su duka suke boye mishi. Yawo yake da tunanin shi, amman ya kasa tuna komai, baya ganin komai a wannan bangaren sai katon filin da babu komai a ciki. A bangare daya kuma ya fara tunanin wani abu na damun kwakwalwarshi, ko cutar mantuwar da yake ganin tana kama tsofaffi a fina finai na kasar waje ce ta tsallako Nigeria ta fara sauka akanshi.

"Ni Engineer ne ko?"

Ya tambaya yana son tabbatarwa, a hankali Muneeb ya daga mishi kai batare daya kalli fuskarshi ba.

"Ka yi soyayya da Zafira?"

Da sauri Muneeb ya dago kanshi yana kallon Rafiq din.

"Kunyi soyayya ko bakuyi ba? Ina son sanin tabin hankali bai sameni ba"

Rafiq ya karasa, dan badan Tasneem tabashi labarin da ta bashi ba, a yanzun da suke zaune daya fara tunanin ko darensu na farko ba gaskiya bane, a tunanin shine kawai.

"Munyi"

Muneeb ya fadi yana kurba lemonshi, kaman yana son wanke kalmar daga harshen shi.

"Tayi aure, shekaru biyu kenan, me yasa ba zaka manta taba? Me yasa ba zaka hakura da ita ba?"

Girgiza mishi kai Muneeb yakeyi

"Karkai haka Rafiq, ba saika raba radadin da kakeji tare dani bane zan san kana jinshi. Ba saika famamun tabon da nake fama dashi ba..."

Dafe kanshi Rafiq yai cikin hannuwanshi, yana jin da gaske wani abu na damun shi ko da ba tabin hankali bane ba. Dagowa yai yana kallon Muneeb da idanuwanshi da suka sauya launi yace

"Dan Allah ka fadamun gaskiya, kasan wani abu dani ban sani ba"

Jinjina mishi kai Muneeb yayi.

"Nasani, amman bazan iya fada maka ba"

Muneeb yace yana gyara zamanshi kan kujerar da yake. Amsar dayaba Rafiq din itace dai-dai a yanzu. Bai mishi karya ba, bai kuma karya alkawarin dayai ma Nuri ba. Kallon shi yake cike da tausaya da wani abu daba yafi karfin fassara.

"Kabar gaskiyar nan inda take Rafiq, shine kwanciyar hankalin kowa..."

Numfashi Rafiq ya sauke yana mikewa. Dan ji yake kanshi zai iya tarwatsewa saboda tunanin da yai mishi yawa. Muneeb dinma tashi yayi yana sa hannu ya zaro wallet dinshi a aljihun bayan wandonshi. Kudi ya kirga ya ajiye kan table din wajen yana bin bayan Rafiq din da harya fita daga bangaren da suke.

Tafiya kawai Rafiq yake baya kallon gabanshi, kawai so yake yaji shi a waje, dan iskar dake wajen ta mishi kadan. Bai kula da yan mata hudun da suka shigo wajen ba sakai karo da daya, har jakar dake rike a hannunta ta fadi kasa.

"Ya Salam..."

Ta fadi tana tsugunna.

"Yi hakuri dan Allah..."

Rafiq ya fadi, dago kai tayi tana bude baki, da alama magana zatayi amman ta kasa cewa komai, yanayin da sau daya ya tabajin shi ya kuma manta dashi yana barin wajen ya dawo sabo, yagane budurwar, ya taba ganinta a KFC kwanakin baya. Akwai wani abu tattare da ita da yake ganin yasani, yanajin yasanta da dadewa, amman ya kasa tuna a ina.

"Dan Allah na sanki?"

Ya tambaya. A hankali ta girgiza mishi kai, jakarta ta dauka tana mikewa. Dakuna fuska Rafiq yayi, koma a ina ne ya santa.

"Ke kin sanni?"

Ya sake tambaya dai-dai lokacin da Muneeb ya karaso yana fadin

"Rafiq? Lafiya?"

Girgiza mishi kai Rafiq yayi har lokacin fuskarshi a daqune. Ganin kallon da yarinyar take ma Rafiq dinne kamar ta gane shi yasa Muneeb tura shi

"Muje..."

Tafiyar kuwa sukai, amman saida Rafiq ya juyo ya sake kallonta, yana da tabbacin yasanta koma a ina ne, har cikin kasusuwanshi wani irin kusanci a tsakaninsu dabai taba ji a tare da wani ba.

"Nasan ta Muneeb, ko a ina nema nasanta"

"Baka santa a ko ina ba"

Muneeb ya fadi da tabbaci a muryarshi. Rai a bace Rafiq yace

"Ban santa a ko'ina ba, ko kuma tana cikin gaskiyar da ba zaka iya fadamun ba?"

Mota Muneeb ya bude ya shiga, fada Rafiq yake nema yaga alama, yana kuma da duk wani dalili dazai yi hakan, amman bazai bashi abinda yake so ba, bazai biye mishi ba. Da yasan abinda yake son tsokanowa daya hakura da sanin gaskiya, komin hargitsin da rashinta yake haifar mishi a yanzun. Yakai mintina biyar da zama kamun Rafiq ya shigo yana jan murfin motar kamar shi yai mishi laifi.

📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

IN THE LOVING MEMORY OF SAIFULLAHI (Allaahummaghfir li SAIFULLAHI warfa' darajatahu fil-mahdiyyeena, wakhlufhu fee 'aqibihi fil-ghaabireena , waghfir-lanaa wa lahu yaa Rabbal-'aalameena, wafsah lahu fee qabrihi wa nawwir lahu feehi. Amin thumma amin)

09

TUNA BAYA (RAYUWAR RAFIQ MUSTAFA SHETTIMA)

Alhaji Mustafa Shettima shine babban da ga Justice Shettima da Kuma Hajiya Hajara. Daga Mahaifiyar Alh. Mustafa har mahaifinshi yaren Kanuri ne yan asalin garin Maiduguri. Zamane ya mayar dashi garin Kano. Su takwas ne 'ya'ya ga Justice Shettima. Mustafa, Abida, Nazir, Sadiya, Amina, Jabir, Kabir sai Autarsu Khadija.

Asalin kakanninsu masu haline, hakan yasa bawai da aikin shi aikinshi kawai Justice Shettima ya dogara ba, harma da rassa na kasuwanci da kamfanoni har hudu daya gada daga wajen mahaifinshi kasancewarshi da daya namiji. Su Alhaji Mustafa sun taso cikin wadata. Inda a cikin yaran Justice Shettima, Alhaji Mustafa ne kawai yai sha'awar karantar fannin da babanshi yayi wato bangaren shari'a.

Yana shekararshi ta farko Allah yaima Justice Shettima rasuwa. Hakan bai girgiza karatunshi ba tunda akwai wadata. Bayan kammalawarshi ne ya samu aiki a garin Abuja. Daman tun lokacin da yake makaranta soyayya mai karfi ta kullu tsakanin su da matarshi Hafsatu wadda itama yaren Kanuri ce. Dan haka da auren shi zama ya mayar dashi garin Abuja.

Allah ya azurtasu da yara biyar. Rafiq, Fawzan, Zafira, Aroob, da Nadir. A zuciyar Alhaji Mustafa Shettima bayan zama cikakken alkali yana da sha'awar siyasa, dan haka duk wani taku nashi da hangen abinda gobe zata haifar mishi a cikar burinshi yake yinshi.

Bayan kalubale da dama daya fuskanta a lokacin daya fada harkar siyasa za'a iya cewa ya shiga da kafar dama, inda yai kwamishinan ilimi a lokacin mulkin fashola. Daga nan ne ya tsaya takarar gwamna inda tun a zabane primary aka kayar dashi, dayake shugaban kasar lokacin nasu ne aka sake bashi kujerar kwamishina ya riqe. Yanzun kuma yana kan neman tsayawa kujerar mataimakin shugaban kasa.

Ta ko ina ana damawa da Alh. Mustafa, ta fannin kasuwanci inda yake da hannun jari da manyan yan kasuwa, yake kuma da gidajen mai sama da guda goma. Da wahala ka shiga gari a cikin najeriya ka kira Mustafa Shettima ba'a samu wanda yasan shi ba.

*

A ko ina Rafiq ya samu kanshi zai iya cewa baisan menene rashi ba, kalmar bata taba karasowa taku hamsin kusa da inda yake tsaye bama. Idan akwai abinda gabaki daya rayuwar shi data kannenshi ta ta'allaqa akai bai wuce kinyin kuskure ba, a cikin rayuwarsu ta makaranta, data yau da kullum. Ko da yaushe cikin yin abinda Alhaji Mustafa zai yaba sukeyi. Komai ya fara bayan Rafiq na da shekaru Ashirin da takwas a duniya.

A lokacin banda yan uwanshi da suke ciki daya, mutane shidda ne suke da kusanci dashi. Abdallah, Faruk, Zaid, Muneeb, Arfan sannan Samira. Ita kadaice macen da take cikin rayuwarshi take kuma da kusanci dashi wadda babu alaqa ta jini. Itama dalilin babanta, Alhaji Habibu daya kasance babban aminin Alhaji Mustafa, kuma abokinshi a kasuwanci da siyasa.

Zai iya cewa abokantakar shi da Samira ba zabi bane ba. Babu yanda zaiyi ne kawai.

*

Sauri take tana nufar hanyar kitchen ta ci karo da Zafira dake shirin fitowa, hannun ta daya rike da plate din dake dauke da plantain da soyayayyen dankali, dayan kuma lemo.

"Wai me yasa hankali ya kasa samun waje tare dake?"

Zafira ta fadi rai a bace tana yin sama da abubuwan dake hannunta da kadan ya rage tai bari. Dariya Aroob tayi

"Na dauka kun daina daga burin ku akan maganar hankali na?"

Hararta Zafira tayi tana shirin wucewa, da sauri Aroob ta riko hannunta.

"Dan Allah zo ki taimaka ki hadamun coffee, yanda Yaa Rafiq yake so"

Gira zafira ta daga mata duka biyun tana mata kallon dake fassara 'Rashin hankalin ki yakai har haka?'

"Please, tun dazun ya sani dazai shiga wanka, ni banma ji ya yace in hado ba, hankali na yana kan Jhalak da akeyi a bollywood... Please please"

Kallonta kawai zafira take har lokacin.

"Yaa Rafiq zai kasheni, pleaseee..."

"Har fatalwarki bazai bari ba in ya fito daga wankan nan babu coffee dinshi"

Zafira ta karasa tana dariya, sake ware idanuwa Aroob tayi

"Inalillahi...ki taimaka dan Allah. Duk aiken da kike so zanje, duk me kike so in miki na kwana biyu"

Girgiza kai tayi tana shirin wucewa, da sauri Aroob ta sha gabanta.

"Come on, kwana uku"

"Kalli fuska ta sosai... Kin ga alamar na damu? Matsa ki ban waje, abincina nayin sanyi"

"Sati daya... I promise kome kike so"

Wani murmushi Zafira tayi hadi da mika mata cup da plate din dake hannunta.

"Kai mun falo, ki shiga dakina ki mayar mun kayan dana fito dasu kan gado"

"Da na bari Yaa Rafiq ya kashe ni zaifi sauqi"

Aroob ta fadi kasa-kasa.

"Magana kike?"

Hannu tasa ta karbi plate din tana ficewa tabar Zafira a kitchen din. Bata dauki wani lokaci ba ta gama hadawa ta dauko mug din tana fitowa falo.

"Aroob!"

Ta kira,da sauri Aroob ta fito tana mata murmushi, karbar mug din tayi.

"Thank you. Kinsan ina son ki ko?"

Ta fadi tana wucewa da sauri, kai kawai Zafira ta girgiza tana samun waje ta zauna. Saman benen gidan Aroob ta nufa tana hawa, hadi dayin hanyar dazai kaita bangaren Rafiq.

Bakin kofa ta tsaya tana kwankwasawa. Ta kusan mintina biyu kamun taji muryarshi ya amsa da Yes. Turawa tayi hadi da yin sallama. Yana tsaye jikinshi sanye da kaftan, dinkin da samarin zamani ke yayi.

Gajeran hannu ne, yadin dark blue ya kamashi kadan, yana daura agogon shi.

"Gashi... A ina zan ajiye maka?"

Sai lokacin ya dago idanuwanshi cike da yanayin dake nuna gajiyar da yake ji har cikin kasusuwan shi.

"Saman kai na"

Ya amsa yana tsare ta da idanuwa, fuskar shi babu alamar fara'a. Dariya ke son kwace mata, ko kadan Aroob bata raina abin dariya.

"Yi hakuri... In ajiye nan?"

Ta bukata tana nuna mishi kan mirror din dakin, hannun shi ya mika mata, ta taka tana sa hannuwanta biyun ta bashi mug din. Karba yayi yakai zuwa fuskarshi yana dan busa iska a ciki kamun ya kurba.

Kai kawai ya jinjina mata alamar yayi mishi, ta juya abinta tana ficewa daga dakin

"Aroob..."

Da gudu ta dawo tana raba mishi manyan idanuwanta.

"Haka kika samu kofar?"

Dan dukan goshin ta tayi tana ja mishi kofar. Kamun ya samu damar tunanin ko yaushe Aroob zatayi hankali an sake turo kofar hadi dayin sallama, takalmanshi ya cire yana karasowa ya wuce Rafiq din dake tsaye ya fada kan gadon da yake a gyare tsaf.

"Oh my God..."

Fawzan ya fadi yana kai hannu ya lalubo pillow ya daga kanshi ya dora yana wani maida numfashi. Sai da Rafiq ya sake kurbar coffee din, ya samu waje ya ajiye mug din tukunna ya kai hannu yana janyo kafar Fawzan daga kan gadon.

"Dan Allah Yaa Rafiq ka kyaleni... Kasan daga inda nake? Ba kaji yanda jikina ke mun ciwo ba"

"Na aike ka? Sakko ka gyaramun gadona yanda kaganshi, ka fice mun daga daki kuma..."

Ya karasa maganar yana janyo kafafuwan Fawzan duka biyun daga kan gadon yana shirin janyo shi gabaki dayane ya mike babu shiri yana ture hannuwan Rafiq din, sakkowa yai daga kan gadon, fuskar shi a shagwabe ya ke fadin

"Fine! Na tafi daki na..."

Daga mishi gira Rafiq yayi yana nuna mishi gadon daya ya mutsa da baki.

"Gyara shi tsaf"

Tsaye yai saida Fawzan ya gyara gadon tsaf tukunna.

"Zo ka sauke ni gidan su Abdallah"

Rafiq ya fadi cike da umarni yana saka takalmanshi dake ajiye, ya dauki wayoyin shi duka biyun, sai mug dinshi ya fice daga dakin yasan Fawzan din zai biyo bayan shi.

Sauka yai falon kasa inda ya samu zafira na danne-danne wayarta tana cin plantain.

"Yaa Rafiq..."

Ta fadi da fara'a a fuskarta.

"Zaf... Ya school din?"

"Ga ta nan babu dadi... Sannu da dawowa"

"Exams ko? "

Kai ta daga mishi. Tana shekararta ta karshe a Nile University dake nan garin Abuja

"Allah ya taimaka, focus akan abinda ya kaiki ok?"

"In shaa Allah. Yaa Fiq.... Anty Samira fa?"

Zafira ta tambaya tana kallon fuskar shi.

"Gata nan cikin mug dina"

Dariya take sosai. Tasan da wahalar gaske ya amsa mata daman. Indai zaka tambayi Rafiq wani abu zaka sha baqar magana. In baka ci sa'a ba zai banza ya kyale ka ne.

"Kwana biyu ban jita bane ba, kuma bata leqo mu ba. Ko dan baka nan ne shisa..."

Dan daga mata kafada yayi, in Samira take son gani ko magana da tana da number dinta, zata iya zuwa gidan su, baiga dalilin da zaisa ta dame ta ba.

"Fawzan!"

Ya kira a qagauce.

"Yaa gani nan fa a bayan ka"

Fawzan ya fadi yana daquna fuska. Saida yadan kara shan coffee din tukunna, da kanshi ya taka har kitchen ya karasa, cika mug din da ruwa yayi ya zubar a wajen wanke-wanke, dauraye wa yayi ya mayar wajen zamanshi, ya dauki karamin towel din dake ajiye ya tsane hannun shi tukunna ya fito.

Gabaki daya fuskarshi ta sauya, farin ciki bayyane har a idanuwan shi.

"Nuri..."

Ya fadi muryarshi dauke da dadin da yake ji a zuciyarshi. Shi kam indai a gaban mahaifiyar shi ne jinshi yake kaman yaro dan shekara biyu. Ita ma murmushi take yi, jikin ta sanye da lifaya da kallo daya zakai mishi kasan yana da tsada sosai.

"Tun dazun na dawo bakya nan"

Ya karasa maganar yana sauke muryarshi kaman zai mata kuka.

"Na leqa ma Haj. Ruqayya wani suna ne, ya gajiyar tafiya?"

Rausayar dakai yayi. Dan ganin Nuri ya tafiyar mishi da gajiyar. Yasan akwai shakuwa mai karfi tsakanin mahaifiya da yaranta. Amman bayajin akwai irin kaunar dake tsakanin shi da tashi mahaifiyar, dan ko yan uwanshi sukan ce Nuri tafi sonshi akan su, ba suna fada bane dan suna kishin hakan, dan kaunarsu a gareshi mai girma ce, suna fadane dan shi kanshi yasan hakan ne.

"Alhamdulillah..."

Ya fadi yana karasawa ya karbi jakar dake hannun Nuri.

"Banma karasa ba, Daddy ne yasani dawowa, wai zamuyi magana..."

Kamun Nuri ta bashi amsa Fawzan yace

"Yaya kaifa nake jira..."

"Na fasa..."

Dakuna mishi fuska Nuri tayi

"Ba fita zakai ba Rafiq?"

Girgiza kai yayi.

"Ba mai muhimmanci bane, na dauka zaki dade shisa..."

"A'a nasan zaka dawo shisa na fita da wuri..."

Takawa suke shida Nuri zasu nufi sashinta. Sai lokacin Zafira tace

"Sannu da zuwa..."

"Yawwa Zafira..."

Nuri ta fadi suna wucewa ita da Rafiq din, a falonta tabarshi tana shiga ciki, kan kujera ya zauna. Kayan jikinta ta sake zuwa doguwar riga mai kama da malun-malun ta less ruwan hoda sannan ta fito. Tun kamun ta karaso yaji kusancinta, zai iya rantsewa a zuciyarshi yake ji idan Nuri na waje koda idanuwanshi basu ganta ba.

"Yunwa nake ji sosai... Banci komai ba tun safe"

"Rafiq ban hanaka zama da yunwa ba? Nace ka dinga samun wani abu kana ci ko?"

Bude baki yayi zai magana ta dakatar dashi tana ci gaba da fadan zaman da yake da yunwa sai ulcer ta kamashi.

"Nuri mana...kiyi hakuri....kamun ince zan nemi wani abu Daddy ya kirani, kuma dole saina karasa wasu abubuwan kamun in taho shisa..."

Bata kula shiba ta wuce zuwa bangaren da suka baro. Da kanta ta shiga kitchen ta zubo masa dambun shinkafar da sukayi ita da Aroob, dan bata taba yarda yaranta sunci abincin yan aiki ba, da kanta take kula da komai ta wannan bangaren. Sai kunun Aya data zuba mishi. Bata san yana bayanta ba, ba karamin tsoro ya bata ba.

"Ya Salam!"

Ta fadi da karfi, dan da akwai kaya a hannunta saita barar dasu, dariya Rafiq yake sosai

"Nuri tsoro..."

Yake fadi yana ci gaba da dariya. Hararshi tayi

"Inda zuciyata ta buga da bakai dariya ba..."

Plate din yasa hannu ya dauka da kofin kunun Ayan yabi bayan Nuri suka koma falonta. Kan kujera ta zauna, shikuma ya zauna kan kafet yana ajiye plate din a gabanshi. Abincin ya nutsu yana ci, kallon shi Nuri take tana tunanin ta inda zata fara fada mishi dalilin daya sa Daddy ya kirashi ya dawo.

"Ki fadamun kawai Nuri, nasan Daddy bazai kirani haka kawai ba..."

Rafiq ya fadi yana ture plate din abincin dayaci rabi, ya dauki kofin kunun Ayar da sanyin shi yake ratsa shi, saidai sikari ya mishi yawa, dan ba ma'abocin abubuwa masu zaqi bane, indan ta bakinshi ne kar a saka mishi sikari a ciki ma zai sha.

"Menene kuma wannan karin? Babu wanda yai wani kuskure da Fawzan ya fadamun..."

Girgiza mishi kai Nuri tayi, tana hadiye wani abu daya tsaya mata a makoshi. Mikewa Rafiq yayi yana komawa kan doguwar kujerar da take zaune, fuskarta yake nazari, kawai sai yaji zuciyarshi ta soma dokawa, dan yasan wani abune babba tunda tayi shiru, tana tunanin ta yanda zata fara gaya mishi ne.

Tana so ya fara ji daga bakinta ne, kamun Daddy ya dawo zuciyarshi ta dan nutsu, dan bata son abinda zai biyo baya.

"Kimun magana dan Allah Nuri... Aikina yake so in bari ko?"

Kai Nuri ta sake girgiza mishi.

"Dan Allah karki cemun akan Fawzan ne, wallahi Nuri yana son asibitin nan, na dauka ya hakura..."

Rafiq ya karasa yanajin wani daci akan harshen shi, Daddy bazai taba barinsu su huta ba, da rana daya ace sunso yin wani abu dayake zabinsu ne ya amince kai tsaye, bai taba ba. Abinda yake so dole shi za'ayi indai ana son zaman lafiya. Tunda karancin shekaru Rafiq ya san cewa yana da banbanci da sauran yaran dake ajinsu.

Daddy yake gaya mishi cewar dole ne yafi kowa kokari a ajin, abokanshi ma dole su zama masu kokari, harya fara hankali hakan bai canza ba, haka ya ga ya faru da duka kannen shi, babu wanda yasha wahala kamar Fawzan, dan kwakwalwar shi bata ja yanda Daddy yake so. A littafin Daddy babu wani abu mai kama da rashin nasara.

Baya fahimtar meye kuskure koda ya ratso ta cikin kaddararka ne, bazaiji uzurinka ba, indai nasara ce a littafin Daddy zabin samuwarta na hannun ka ne.

"Duk ba wannan bane ba..."

Nuri ta fadi tana katse ma Rafiq tunanin da yakeyi. Duka hankalin shi ya mayar kanta yana jiran yaji ko menene.

"Ya samar ma Zafira miji ne daman..."

Dariya ta kubce ma Rafiq da baisan daga inda ta fito ba, da alamun rashin yarda yake kallon Nuri, itama kallon shi take, bai daina dariya ba har lokacin daya ce

"Miji? Zafira?"

Wata sabuwar dariyar na kubce mishi saboda abinda yasan bazai yiwu bane ba. Duk da yana sane da haqqin Daddy ne ya samar mata mijin da zata aura, sanin halin Daddy yasa shi kin yarda da hakan.

"Rafiq..."

Nuri ta kira cike da damuwa. Mikewa tsaye yayi yana kai kawo cikin dakin, kamun yai tsaye yana watsa hannayen shi hadi da girgiza ma Nuri kai, lokaci daya girman maganar da ta fada na danne shi.

"Kice mun Daddy bai amfani da rayuwar Zafira wajen siyasar shi ba, Nuri kicemun baki barshi ba wannan karin, kice mun kin zabi rayuwar ta akan son Daddy wannan karin..."

Rafiq yake fadi yana karasawa ya tsugunna gaban Nuri ya riqo hannuwanta, da duk wani abu da yake dashi yake roqanta da tace mishi bata amince da wannan rashin adalcin ba.

"Nuri dan Allah... Wannan karin kawai..."

Dauke idanuwanta da takejin sun ciko da hawaye Nuri tayi daga kan Rafiq. Bata san yanda zatai musu da Daddy ba ko kadan, dan duk wani abu dazaiyi yana mata bayani yanda zai gamsar da ita. Taso musa mishi maganar auren Zafira din, yazo mata da hujjojin da suka gamsar da ita. Ta kuma san koma waye gidan da zata huta ne. Kuma bawai tana soyayya da wani bane ba, dan haka abune mai sauki.

"Bata soyayya da kowa Rafiq, abin zai zo..."

A karo na farko a rayuwarshi da ya daga hannuwanshi duka biyun yana hade su waje daya alamar roqon Nuri da tai shiru, bai tabajin bayason abinda zai fito daga bakinta ba sai yau. Kallon shi take, tana ganin yanda ranshi yake a bace ta cikin idanuwanshi da suka kankance. Mikewa yayi

"Ta sani?"

Ya tambaya, Nuri ta girgiza mishi kai. Dariyar takaici mai sauti ta kubce mishi.

"Ni Daddy yake so in fara gaya mata... Shisa ya kirani... Ni yake so in fada mata..."

Ya karasa yana dafe kanshi dayake jin ya fara ciwo. Yakai mintina biyu a tsaye dafe dakai, kamun ya juya yana ficewa daga dakin batare daya cema Nuri komai ba. Jingina kanta tayi da kujera tana lumshe idanuwanta, yaranta ne komai nata, farin cikinsu nada muhimmanci a wajenta musamman Rafiq, saidai farin cikin Daddy dashi zuciyarta ta bude ido. Bata tunanin ko kaunarsu zata fi hakan girma.

*

Murmushi tayi ganin Aroob ta mayar da duka kayan data fito dasu kan gado, bude wardrobe din tayi, komai a shirye yake tsafe, ta sake shirya mata komai, atamfa ta hadasu complete waje daya. In tanan bangaren ne kuma Aroob bata da ha'inci, saboda babu wanda yakaisu tsafta ita da

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment