Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inuwar Majida balle ta ganshi.

Da yaqinin da baita ba sanin yanada shi ba a rayuwarshi, zuciyarshi na zubda hawaye masu ciwo yake jero addu'o'i

'Allah karka tona mun asiri a wannan lokacin, Allah karka sa abinda nake zatone ya faru, Allah kasa abinda ya faru yanzun nan ya zama mafarkin dazan farka daga shi ina mai sake neman gafarar zunubaina'

Sai daime, da kukan motar da yake ji a hankali dana sauran motocin dake wucewa kan titin da yawan tsoron dake sake cika mishi zuciya, ga fuskokin yaran da suke son hargitsa mishi duniyarshi lokaci daya.

**

KANO

"Nikam da ansa wuqa an yanka lemon nan Tariq"

Ashfaq ya fadi, yana jan jiki da gyara zamanshi dakyar, Runtsa idanuwa yayi saboda azabar radadin daya ratsa shi, ta baki yake jan numfashi yana kokarin daidaita shi.

"Saboda me?"

"Saboda wahala kake tayi tun dazun"

Lemon dake hannunshi Tariq ya kalla, da gaskiyar Ashfaq din, yafi mintina goma yana kokawa da bare lemon zakin, baisa an yanka ba daya siyo, dan indai Ashfaq zai sha lemo bai taba ganin ya yanka ba, yafison ya bare da hannun shi. Bai taba sanin abin da aiki ba sai yau.

"Kaga miko mun nan"

Girgiza kai Tariq yayi yana daquna fuska.

"Ni zan bare fa"

"Bance ba zaka bare ba ai nima, kawai canai ka mikomun wani nima"

Ashfaq ya fadi yana kokarin boye murmushin shi, dan lemon dake hannun Tariq din ba karamar wahala yasha ba, duk kana ganin kayan cikin lemon. Jan kujerar shi Tariq yayi yana matsawa sosai gab da gadon Ashfaq din, ya dauki lemo daya yana miqa mishi.

Dan yatsan shi kawai yasa yai hanya, sai gashi ya soma bare lemon, ko mintina uku bai dauka ba ya gama, yana gyara shi. Baki a sake Tariq yake kallon shi.

"This is so not fair"

Dariya Ashfaq yayi, yana mikama Tariq lemon da ya gama barewa.

"Miqomun wani, sha wannan"

"Kai ka fara sha..."

"Bana son jan magana... Ka karba ka mikomun wani"

Karbar yayi, yana mika mishi wani lemon, dai-dai shigowar Yasir da sallama. Su duka biyun suka amsa, waje ya samu ya zauna.

"Kaman anyi wasan cikar shekara dakai a bakin sabon gari"

Tariq ya fadi yana kallon Yasir din dayai duhu, idanuwanshi sun canza launi, gajiya tattare a fuskarshi. Ga gashin kanshi a cukurkude. Hannu Yasir yakai ya dauki lemo daya.

"Ban dauka ma nakai haka yin kyau ba"

"Kanka kaman dambun yara"

Tari Ashfaq ya soma yi saboda lemon daya shaqe shi wajen dariya. Shi kanshi Yasir din murmushi ne a fuskarshi.

"Ba abin dariya bane Yaya... Yana bukatar taje kanshi"

Tariq ya fadi babu alamar wasa a fuskarshi. Ganin Ashfaq baida niyyar daina dariyar da yake yasa Tariq din mikewa.

"Kana nan? Ina son zuwa gida in dauko kayana"

Yai maganar yana kallon Yasir. Kai yadan daga mishi a hankali.

"Daka fadamun dana dauko maka, daga gida nake yanzun"

Tariq bai amsa shi ba ya mayar da hankalin shi kan Ashfaq, kamun yai magana Ashfaq din ya rigashi da fadin

"Kaje Tariq, ina nan, babu inda zanje"

Sauke numfashi Tariq yayi, yana wucewa ya bude kofar ya fita batare daya ce komai ba, kamar tura kofar shi kawai Ashfaq yake jira kamun yace ma Yasir

"Kaje?"

Girgiza mishi kai yayi a hankali.

"Na dauka har roqonka nayi, kafi kowa sanin muhimmancin cika alkawari a wajena Yasir, me yasa zakai mun haka?"

Sosai Yasir yake kallon shi.

"Me yasa ba zaka fadamun wacece ita ba? Me yasa ita din? Mahaukaciya Faq?"

Kauda kai gefe Ashfaq yayi, zai karya idan yace ranshi bai baci ba, bako da yaushe yake barin tunanin abubuwa na damun shi ba. Muryarshi can kasan makoshi yace

"Ba mahaukaciya bace"

Jinjina kai Yasir yayi

"Yeah, nagani ai, shisa take a gidan mahaukata, harda daki ko?"

"Nudra..."

Ashfaq ya fadi can kasa, daquna fuska Yasir yayi

"Nudra, sunanta Nudra, ba mahaukaciya bace ba..."

Shiru Yasir yayi yana jiran wani karin bayani. Ganin Ashfaq din bashi da niyyar sake cewa komai yasa  fadin

"Me kayi wannan karin? Ashfaq me kayi?"

Juyowa yayi yana saka idanuwan shi cikin na Yasir.

"Me kake zaton zanyi?"

Kallon shi kawai Yasir yake. Sauke numfashi Ashfaq yayi ranshi a bace

"Kasan komai..."

"Nasan abinda ka zabi ka fadamun, na gane wasu abubuwan dakaina, amman ita? Tun jiya da daddare kaina yake yawo na kasa zuwa ko ina da tunani, me yasa ita?"

"Tausayin ta nake ji..."

Yasir baisan lokacin da dariya ta kwace mishi ba, sosai yake dariya, idanuwan shi Ashfaq ya dauke daga kan Yasir, yasan me yake ma dariya, shi kanshi kalmar har lokacin nauyi take mishi kan harshe.

"Faq, tausayi? Tausayi fa kace, kai kake hada kanka da tausayi a jimla daya. Allurar baccin da akai maka ce bata gama sakin ka ba kome?"

"Idan ba zaka je ba ka fadamun kawai..."

Hankalin shi Yasir ya nutsar kan Ashfaq.

"Da gaske ka damu da zuwan nan har haka? Ashfaq me yake faruwa ne wai?"

Tambayoyin da Yasir yake mishi yanzun ne dalilin farko da yasa bai taba fada mishi ba. Bai kuma taba bari yasani ba. Dan idan za'a sake mishi sabon harbi bazai ce ga abinda yake faruwa ba.

"Da gaske ka damu da wani banda Tariq"

Yasir yake fadi da matuqar mamaki a muryarshi.

"Kana magana kaman hakan sabon abune"

"Gayamun waka damu dashi? Banda Tariq?"

"Kai...kudi..."

"Uhum... Ina jinka, sai me kuma?"

Yasir ya fadi, sosai Ashfaq yake tunani, zuciyarshi yake dubawa, me yai saura banda su da ya damu da, me ya rage mishi kuma? Rayuwa bata barshi da wani zabi na damuwa da wasu bayan Tariq, Yasir da kuma kudin daya fadi ba, sai kuma kanshi.

A yanzun in duniyar zata jirkice da kowa ba matsalarshi bane, inhar su kadai din nan zasu fita, wata qila inya samu dama zai fitar harda Nudra, inya samu dama kenan.

"Zan je..."

Yasir ya fadi yana katse mishi da yake. Jinjina kanshi kawai yayi, yana zame jikinshi ya kwanta kan gadon, hadi da lumshe idanuwan shi. Numfashi mai nauyi ya sauke, yana ganin yanda duniyar tai mishi duhu gabaki daya, babu komai cikin kanshi da zuciyarshi na tsayin lokaci banda duhu.

In ba idanuwanshi bane a bude, kuma ya nutsu kan duniyar dake faruwa a wajen shi, mantawa yake akwai wani haske a duniya, komai baqiqirin yake a tare dashi. Balle kuma wani abu waishi nutsuwa, yama manta ya ake jin abu mai kama da kalmar, ya kuma cire rai daga sake samun kusanci da kalmar.

Kamar yanda ya cire rai da faruwar abubuwa da yawa a rayuwarshi, kamar yanda ya fadana, ALKALAMIN KADDARArshi bai barshi da wani zabi ba.

*

Jin kafafuwanshi sunyi nauyi yakuma san zama waje dayane yasa bai nemi abin hawaba daya fito bakin asibitin. Ya yanke hukunci takawa ko yayane. Ko ba komai doguwar tafiya kan rage mishi tunanin da yakan cika mishi kai lokutta da dama.

Wasu yara yagani mace da namiji, da alama namijin ne babba, hannun shi riqe da na kanwar da ke dariya, kallo daya zakai ma fuskarta kasan tun daga zuciyarta take dariyar, hararta Yayan yayi yana jan hannunta ranshi a bace.

Tariq baisan murmushi ya kwace mishi ba, saida yaji bakinshi ya motsa

*

"Yaya Tariq ni yaushe zan koma makaranta?"

Arfa ta tambaye shi tana turo bakinta cikin yanayin da yaga kamananninta da Baba na kara fitowa, yana saka zuciyarshi matsewa. Dan murmushi yai mata

"Mu da muke hutawa Arfa.... Zamu koma ai, amman saimun kara hutu....ko bakyason hutun?"

Idanuwanta ne suka ciko da hawaye

"Ni banajin dadin hutun nan, saboda Su Mama basa nan, kuma in da makaranta ana dafamun abinci in tafi dashi, da biscuit"

Lumshe idanuwanshi Tariq yayi, yana rasa ta ina zai fara amsata, ko kuma me zai fada mata, karancin shekarunta sunyi kadan ta fahimci halin da suke ciki, a lokaci daya kuma shekarun sunyi karanci ta dinga fuskantar abinda take fuskanta tare dasu. Tashi yayi ya mika mata hannu, ta kama tana mikewa.

Fitowa sukai daga gidan suna nufar shagon Mahdi, akwai Naira ashirin a jikinshi, ita ya zaro ya siya mata biscuit ya bata. Wata irin dariya tayi

"Nawa ne?"

Kai ya daga mata, wannan karin ya kasa ko da murmushi ne, jinta yayi ta rike mishi kafafuwa tana dariyar jin dadi.

*

Birkin da machine din ya taka ne ya katse mishi tunanin shi, dan duk da kokarin kauce mishin da yayi saida ya dakar masa hannu da hannun machine din. Azabar radadin na saka Tariq jin hannunshi gabaki daya kamar bana shi ba

"Wanne irin marar hankali ne kai? Baka da kunnuwa ne?"

Mai machine din yake fadi rai a bace, muryarshi na sa Tariq sakin hannunshi daya riqe, kwakwalwarshi na daina jin komai lokaci daya, zuciyarshi ta soma dokawa da karfin gaske. Cikin tashin hankali ya dago kanshi yana sauke idanuwanshi kan fuskar saurayin dake kan machine din.

Runtse su yayi ya sake budewa, shekaru biyar, watannin cikin shekarun, ranakun cikin watanni, daqiqan dake cikin ranakun, duhun da yanayin rayuwa yasa shi yi, kasumbar dake fuskarshi harma da girman daya kara bai hana Tariq gane shi ba. Gwiwoyin shi yaji sunyi sanyi kafafuwanshi na soma rawa.

Lokaci daya ya runtsa idanuwanshi yana kara bude su, zuciyarshi ta kasa yarda da abinda yake gabanshi

"Ya... Ya... Yaya Yasir"

Ya fadi da nufin maganar ta fito fili sai dai ko labbanshi basu motsa ba, iya zuciyarshi kalaman suka tsaya. Bai san me yake faruwa a duniyar dake wajen shi ba, dan ta cikin shi a hargitse take da tashin hankali, sai da yaga yaja machine din yai gaba.

Zuciyar Tariq ta fara gudu tana bin bayanshi kamun kafafuwanshi su karba.

"Yaya Yasir!!!"

Yake kira yana bin bayan machine din da gudu, sai dai me, gudun machine dashi da yake a kasa ba daya bane, musamman yanda yake gudun kafafuwanshi na hardewa kaman zai fadi, ganin machine din ya mishi fintinkau yasa shi tsugunnawa a kasa, batare daya damu da mutanen dake harkokin su nayau da kullum a wajen da kallon da suke mishi ba.

Sosai ya durkushe cikin kasa yana maida numfashi, dafe kanshi yayi da duka hannuwanshi yana girgiza kai cikin alamar rashin yarda da abinda ya faru kamun ya mike tsaye yana juyawa, gudu da sassarfa yake hadawa dashi harya koma cikin asibitin, sama yahau yana nufar inda dakin Ashfaq din yake.

Kafafun wandon shi inda ya durkusa cikin kasa yayi budu-budu. Tunanin sallama baizo mishi ba, hannu kawai yasa ya bankada kofar. Jin bude kofar bana lafiya bane yasa Yasir juyawa. Ashfaq da bacci ya soma dauka shima saida ya bude idanuwanshi.

Bin Tariq da yanayin shi da kallo suke su biyun, an rasa wanda zai fara magana. Har Tariq din ya taka cikin dakin yana zuwa karshen bangon, jikin kusurwa ya hade fuskarshi da wajen kamar maison shigewa cikin bangon dakin.

Numfashi yake mayarwa a hankali saboda kanshi dayake ji a hargitse, ga jikinshi daya soma bari a hankali, makoshin shi ya bushe bada kishin ruwa ba, hannuwanshi dake bari yakai kan bangon yana dora fuskarshi akai. Da duk wani abu dake da rai a jikinshi yake bukatar ko da syrup ne.

Wani abu ya taimaka mishi wajen dai-dai ta hargitsin da yake faruwa cikin kanshi da zuciyarshi.

"Tariq..."

Ashfaq ya kira can kasa, muryarshi cike da fargaba da son sanin me yake faruwa. Yasir kam baice komai ba, yasan magana daya, muryarshi kawai zata iya karama Tariq din damuwa. Inda zai iya tashi zaiyi ya fice yabar musu dakin.

"Tariq menene?"

Ashfaq ya sake fadi a karo na biyu. Yana jinshi dan haka ya girgiza kanshi kawai, kokarin mikewa zaune Ashfaq yayi, sai dai kafadarshi tace batasan ya sauko daga kan gadon ba dan ciwon da take na saka numfashin shi daukewa na dan lokaci

"Kamun magana Tariq!"

Yanayin muryar Ashfaq din yasa Tariq raba jikinshi da bangon, yana juyowa a hankali, har idanuwanshi sun sake launi saboda kwayoyin da jikinshi suke bukata.  Ga jikinshi dake bari kamar maijin sanyi, karasowa yayi gefen gadon Ashfaq yana durkushewa.

Duk da karin ruwan dake hannun Ashfaq din daba babu ciwo bai hanshi saka shi yana riko kafadar Tariq daya dago ba, gefen gadon ya zauna yana dora kanshi kan kafafuwan Ashfaq din kozai samu sauqin abinda yake ji.

Saidai yana rufe idanuwanshi Fuskar Yasir yagani, muryarshi na rawa yake fadin

"Naganshi...Yaya naganshi wallahi..."

Girgiza kai Ashfaq yakeyi

"Ba yanzun ba Tariq... No... Ba zakai mun haka ba wallahi...ba zakai mun haka ba..."

Yake fadi cikin tashin hankali, babu yanda za'ai ciwon Tariq ya dawo, yana ganin yanda jikinshi ke kyarma, bubbuga bayanshi Ashfaq yakeyi

"Tashi ka kalle ni... Babu abinda zai sameka.... Babu abinda zai sake samun ka... Kana jina ko? Babu abinda zai sake samun ka Tariq!"

Ya karasa a tsawace, yana saka Tariq din dagowa. Kaman zaiyi kuka yake kallon Ashfaq, inda zasu bashi syrup, kwalba daya kawai zai dan samu nutsuwa, sai dai zuciyarshi bata da karfin rokar Ashfaq din

"Yaya Faq naganshi... Naga Yaya Yasir... Ba akaina bane wannan karin...Wallahi ba a tunanina yake ba... Shina gani akan machine..."

Sosai Ashfaq yake girgiza ma Tariq kai, yana amfani da hannunshi dake kafadar Tariq din shima yana girgiza shi

"Babu abinda kagani... Babu abinda zai sameka kuma.... Munyi sadakar mutuwar Yasir tuntuni"

Ture hannunshi Tariq yayi yana mikewa tsaye

"Naganshi.... Wallahi na ganshi!"

Yake fadi cikin hargowa yana jin kanshi na jujjuya kaman zai tarwatse saboda muryoyi yake ji a cikin kan da baya gane me suke nema, me suke so dashi, me suke bukatar yayi suyi shiru.

"Me yasa ba zaka yarda naganshi ba?!"

Ya tambaya cikin hargowa, ba Ashfaq din yake dagama murya dan ya yarda dashi ba. Yana daga murya ne ko sautin ta zaisa yaji sauqin hargitsin dake cikin kanshi. Girgiza kai kawai Ashfaq yake, yanajin yanda zuciyarshi take karyata cewar ya gina bangwaye masu karfin kare shi daga jin yanayi irin wannan. Muryarshi can kasan makoshi yace

"Saboda mun yi mishi sadaka....Saboda ya rasu Tariq.... Ya rasu..."

"Bai rasu ba!"

Tariq ya amsa yana tsugunnuwa ya riqe kanshi hadi da kurma wani irin ihu da yasa Ashfaq runtsa idanuwanshi, Yasir kuma yana saka hannuwanshi babu shiri ya rufe kunnuwanshi, kamun ya mike tsaye yana nufar inda Tariq din yake tsugunne yana rike da kanshi da yake jin kamar zai tarwatse.

Tsugunnawa yayi ya kamashi, duk da kokarin ture shin da Tariq din yake, sosai yasa karfi yana riqe shi, jikinshi ko ina kyarma yake, idanuwanshi na wani kakkafewa da yanda jikinshi ke bukatar kwayoyin da sukai mugun sabawa dasu.

Ashfaq bude idanuwanshi yayi yana kallon su, zuciyarshi na tsaya mishi waje daya, duhun dake cikin kanshi na yawatawa zuwa duk wani sassa na jikinshi. Baisan lokacin da rayuwa zatai mishi haske ba, na rana daya ya sake jin haske cikin rayuwarshi abin ya gagara.

**

LAGOS

"Mummy...Mummy..."

Zafira take jin ana kiranta sama-sama, buda idanuwanta tayi, motsin datai nasa jikinta gabaki daya daukar dumi,babu shiri ta bude idanuwanta gabaki daya.  Yusayrah tagani da uniform a jikinta.

"Mummy yunwa nake ji, pasta aka dafa mana a makaranta"

Kai Zafira ta daga tana kallon agogon dakin, shidda saura, kallon ta ta mayar kan Yusayrah dake turo bakinta irin na Omeed.

"Sayrah harkun tashi?"

Gani tai ta nutsa tana kallon hannuwanta, kamun takai dan yatsa daya tana taba shatin belt din dake kwance kan hannun Zafirar

"Papi ya dake ki ko?"

Yusayrah ta tambaya da wani yanayi a muryarta da Zafira bata so, idanuwanta cike da hawaye tai saurin mikewa tana fadin

"Zo muje in zuba miki abinci... Nayi meatpie kuma"

Bin bayanta Yusayrah tayi, sai dai maimakon tabi ta kitchen hanyar dakinta ta nufa

"Ina zaki je kuma Sayrah?"

"Zan sake uniform"

Ta amsa batare data juyo ba. Sauke numfashi Zafira tayi tana nufar kitchen din. Saida ta dago hannunta dantai amfani dashi taji ya mata mugun nauyi, gashi ya kumbure musamman yatsunta na tsakiya da gefe, da har naso suke saboda kumburi.

Hannun haggu tai amfani dashi ta zuba ma Yusayrah abincin, tana zuba mata Meatpie din guda biyu a waje daban, duk da tasan ba iya cinye biyun zatayi ba. Shigowa kitchen din tayi ta saka doguwar riga ta material a jikinta.

Inda taga plate kawai ta karasa tana dauka, kota kan Meatpie din bata bi ba ta wuce tana barin kitchen din. Zafira tasan shatin belt din da Yusayrah tagani ne ya bata mata rai. A shekarun yarinyar takwas da yan watanni tana fahimtar abubuwan da suka girmi shekarunta.

Ta gode ma Allah da bata gidan dazun. Omeed ba damuwar shi bane ya jibgeta gaban Yusayrah, in ranshi ya baci hankalin shi barin jikin shi yake. Falo ta fito ta zauna dan tasan halin Yusayrah inta gama fushin zata nemeta.

Da agogon dakin tai amfani wajen gane lokacin Sallah, dan ba masallaci suke dashi kusa dasu ba. Daki ta koma tayi Sallah, sai da ta nemi Panadol da bata rabuwa dashi ta hadiya dan tasan dukan da Omeed yai mata zai saka mata zazzabi tukunna ta sake dawowa falo ta zauna.

Kallo take amman sam hankalinta ba akai yake ba, ta kuma rasa tunanin daya kamata tayi, data tuna son zuwan da take gida sai gabanta yai mummunar faduwa, dan zuwan ya fice daga ranta, dukan data sha yasa taji ta hakura.

Omeed bai dawo gidan ba sai takwas da wani abu, dan lokacin ma tayi Isha'i. Da sallama ya shigo falon, sai da zuciyarta ta doka. Da sauri ta mike tana tarbar shi, hugging dinshi tayi, tanajin ya sumbaci saman kanta, kamun ya zameta daga jikinshi

"Sannu da gida..."

Ya fadi yana mata murmushi, hadi dasa hannu da shafar kuncinta.

"Fuskarki a kumbure..."

Murmushi takaici tayi, yana fada mata fuskarta a kumbure kamar bashi da alaqa da kumburin fuskar. Bata amsa shi ba, sanin Omeed bakowacce maganarshi take bukatar amsa ba. Cikinta ya kai hannu yana dafawa

"Kinci abinci?"

Girgiza mishi kai tayi

"Me yasa?"

Ya bukata yana kama hannunta daya sata ihu tana kwacewa hadi da rike shi, idanuwanta na cika da hawaye saboda zugin da yatsun suke mata. Da sauri Omeed yakai hannu zai kama nata, ta matsa baya tana girgiza mishi kai, hadi da boye hannunta baya.

"Meya samu hannun, kawo ingani"

Ya fadi yana kokarin hade space din dake tsakanin su, Zafira kam kara matsawa tayi nesa dashi. Kallon yayi fuskarshi babu alamar wasa

"Ki zo ingani"

Kai ta sake girgizawa wannan karin hawayen ta na zubowa. Takalma Omeed ya cire yana shiga cikin falon sosai ya samu kujera ya zauna yana cire hular kanshi ya ajiye

"Zafira zo..."

Tsaye tayi

"Kizo nace ko!"

Ya fadi a tsawace, babu shiri tana hawaye ta karasa inda yake, hannunta boye a bayanta. Riqo ta yayi tana zaunar da ita kan kafarshi daya hadi da sa hannu ya kamo nata da take boyewa. Ranshi yaji ya baci ganin yanda yatsunta suke a kumbure. Muryarshi can kasan makoshi yace

"Garin ya? Taya kikaji ciwo haka?"

Shiru tayi hawaye na zubar mata, ba zata iya jure wani dukan ba, kadan da aikin Omeed ya sake tusa mata wani sabo.

"Ban fada miki ki dinga bimun kanki a hankali ba?"

Da sauri ta amsa da

"Ka fadamun..."

"Taya akai kikaji ciwo to? In inason ganin ciwo a jikin ki zanji miki da kaina..."

Ware mishi idanuwanta tayi tana kokarin tarbe hawayen dake sake son zubo mata. Idan ta fada mishi lokacin dayake dukanta me taji laifin kanta zai koma, inta fada mishi faduwa tayi ma ba tsira tai ba. Har yanzun bata gane kan Omeed ko asalin abinda yake so daga wajenta.

Hannun yasa cikin nashi yana dubawa sosai.

"Targade ne a yatsunki har ukku..."

Yanda akai yagane bai bata mamaki ba, duk da babu abinda ya hada Pilot da aikin kanshi. A zamansu abubuwan da yasani ya daina bata mamaki, ya kuma koya mata yarda dashi ta karfi da yaji.

"Zan gyara miki, ba zakimun ihu ba saboda ban aike ki jin ciwo ba, bansan me yasa kike son batamun rai ba..."

"Kayi hakuri"

Ta tsinci kanta da fadi, sumbatar gefen fuskarta yayi da take jiqe da hawaye.

"Nasani..."

Ya amsa yana gyara mata zama a kan cinyarshi, kafarshi daya ya daga yana danne nata kafafuwan dasu.

"Karkimun ihu Zafira..."

Kamun ya rufe baki ya damqe hannunta ya soma jan yatsun, wani fitsari taji yana shirin zubo mata, ga mamakinta azabar bata sa ihu ya kubce mata ba, sai hawaye da zufa data hada, harya gama, tukunna ya mike da ita riqe a jikinshi. Bedroom dinsu ya jata yana zaunar da ita kan gado.

Da kanshi ya shiga toilet ya dauko ruwan zafi da towel ya gasa mata hannun dashi, kumburin harya fara ragewa, ta kuma soma jin dadin hannu.

"Sannu, bakya jin magana. Inba dukan ki nayi ba hankalin ki baya kwanciya"

Omeed yake fadi yana karasa gasa mata yatsun saida ya tabbatar ya isa tukunna ya je ya zubda ruwan daya dibo yana shanya towel din. Sake zuwa yai ya kamo hannunta, da kanshi ya zubo musu abinci a kitchen shida ita. Badan tanajin yunwa take ci ba, saidan gudun tashin hankali.

Laifin kincin abinci babbane a wajen Omeed, zaice ko batajin yunwa jikinta na bukatar abinci, sam baya wasa da abinci da kula da lafiya. Da suka gama shiya dauke plate din. Al'amuran shi na rikitar da ita. Platforms da yawa takan shiga, irin su Inside Arewa, Jaruma Magazine, Open Diaries, tana cin karo da labarai da dama.

Mazan dake dukan matansu, amman babu namijin da taji kalar Omeed, babu macen da taji in mijinta ya dake ta yake kula da ita haka, kuma basa fadar laifin da sukai ma mazan. Omeed na fada mata laifin datai mishi ya daketa, kuma har a zuciyarta tana jin wasu lokuttan kamar ta cancanci duk wani duka da yake mata.

Jin ya taba mata fuska yasa ta kallon shi

"Bana son tunani mai zurfi haka"

Ya fadi yana daquna mata fuska. Dan a irin tunanin nan ne takeyin na rabuwa dashi. Ko kadan bayason kwakwalwarta ta samu hutu ko nutsuwar da zatai tunanin wani abu mai zurfi.

"Sayrah fa?"

"Tana dakinta"

Ta amsa shi a taqaice, kama hannunta yayi suna nufar dakin Sayrah tare, bakin kofa suka tsaya, saida ya kwankwasa tukunna, sakewa yayi har sau uku tukunna ya tura hadi a sallama a hankali. Yana jan hannun Zafira ciki. Kwance suka samu Yusayrah kan gado, idanuwanta a rufe da alamun bacci, kunnenta da earpiece.

Gefen gadon Omeed ya zauna, yana jan abin rufa ya lullube Yusayrah, kamun a hankali ya zare earpiece din dake kunnenta yana dan dagata ya ciro Tablet din data danne rabinta. Dannawa yayi, murmushi ya kwace mishi ganin Karatun Qur'an take saurare har bacci ya dauketa.

Addu'a yai mata shida, da zasu fita daga dakin ya kashe mata wutar dakin hadi dajan kofa, Yusayrah na jin jan kofar su ta bude idanuwanta. A kwance take daman tana sauraren karin karatun da akai musu a Islamiyya da yammacin.

Taji kwankwasa kofa, tasan sune, tun bata iya baccin karya ba harta koya, in bata son magana dasu haka takeyi, cikin duhun ta lalubo wayarta ta mayar da karatun tana sake gyara kwanciyarta.

**

KAUYEN KINKIBA

Bai taba sanin duk wani abu da yake ji akan mutanen da sabani yakan hada shi dasu ba tsana bace ba, ko kusa da tsana bai taba kawai ba, saida A-Tafida ya shigo rayuwar su. Cikin shekara hudu babu abinda ya canza na daga yanda yake ji akan shi.

In akwai bai wuce yanda tsanar take karuwa da duk rana ba. Inda za'a bashi zabi cilla bomb a duniyar A-Tafida ya tabbatar bazai tsaya tunanin ko su waye bomb din zai shafa da suke kusa ko cikin duniyar shi ba, inhar zai tarwatse da A-Tafida batare da dana sani ba zai amince.

Yana jin yanda zuciyarshi ke girgiza har lokacin da ganin A-Tafida, baisan baiyi sallama ba, saida yaji Inna tace

"Waye nan?"

Muryarshi na fitowa a hargitse yace

"Inna nine"

"Tawfiq harka dawo... Banji sallamar ka bane shisa"

Inna ta amsa daga can cikin dakin

"Yan nema, wato duk kiran danai saida kuka bishi ko?"

Take ce ma su Hussaina da tun shigarsu gidan suka ruga dakin Inna, suna barin Tawfiq a tsaye anan. Yanayin da yake ciki yasa ya rasa abinda ya kamata yayi

"Inna Kawu ya mari wani"

Hassan ya fadi, da mamaki Inna ke kallon shi, yaron nada surutu, amman da wahalar gaske ya fadi abinda bai faru ba. Kuma tasan zafin zuciyar Tawfiq

"A ina?"

Ta tambaya

"A waje..."

Hussain ya bata amsa, babu shiri Inna ta mike tana barinsu a dakin ta fito waje, ganin Tawfiq din tayi a tsaye yayi zurfi cikin tunani, dan kira hudu tai mishi baima san tayi ba, saida ta taba shi tukunna

"Tunanin me kake haka?"

Sauke numfashi yayi, ta ina zai fadama Inna A-Tafida ne ya tako kafarshi kofar gidan su, shekara hudu yana kallo tana kokawa da warkewar ciwon da A-Tafida yaji mata, kullum yake kallon yanda take jinya da fama da tabon

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment