Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hamna zamu tayata"

Daga kai Hamna tayi, alamar yarda da maganar da Azrah din tayi.

"Ki dauko waken yana kitchen, Hamna dauko turmi"

A tare suka mike, Hamna ta dauko turmin tana kawo mata ta ajiye, janshi gabanta Tasneem tayi tare da fadin

"Dubomun Beena bacci take kome, tun dazun ko motsinta banji ba"

Dakinsu Hamna ta nufa, ganin Sabeena tayi harta sakko daga kan katifa tana ta juye juye kan ledar tsakar dakin.

"Beena?"

Ta kira a dan tsorace kamun ta shiga cikin dakin gabaki daya, kamata tayi tana tsugunnawa ta dorata a jikinta, har idanuwanta sun juye sun wani yi fari.

"Beena..."

Hamna ta sake kira taja jijjigata.

"Cikin ki ke ciwo?"

Ta bukata dan tasan ciwon Sabeena baya wuce ciwon ciki, tana yawan yinshi akai-akai. Ganin Sabeena na wani irin nishi-nishi kamar ma batasan me ake a duniyar ba yasa Hamna kwala ma Tasneem kira. Jin kiran bana lafiya bane yasa Tasneem barin waken data fara zubawa cikin turmi ta mike babu shiri tana nufar daki, Azrah na rufa mata baya.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Tasneem ta fadi cikin rudani tana sa hannu ta dauki Sabeena tana duddubata.

"Me ya sameta?"

Ta tambayi Hamna hankalinta a matuqar tashe. Idanuwan Hamna cike da hawaye tace

"Nima bansani ba... Kawai naganta a kwance"

Hijab din dake qasa Tasneem ta sa hannu ta dauka batare data kula da cewar ta Hamna bace ba, a birkice ta saka Hijab din tana fitowa hadi da saka takalma. Kota kansu Azrah dake mata magana batabi ba, dan hankalinta ba karamin tashi yayi ba, lafiya kalau suka karya.

Kanta tsaye kemis din Emma ta nufa, su Azrah suka tsaya suka dauke waken suna mayarwa kitchen. Tukunna suka saka hijabai da niyyar binta.

"Mu duba ko da kudi, naga bata dauka ba"

Hamna ta fadi, inda suka san Tasneem na ajiye kudi suka duba, duka kudin da suka gani suka kwasa suna bin bayanta dan sun san ba zata wuce shagon Emma ba. Can din kuwa suka sameta a tsaye tana maida numfashi.

"Gaskiya kikaita asibiti zata fi samun kulawar data dace"

Emma ya fadi cikin hausar shi dake fida rangadam. Tasneem ko amsa bata bashi ba ta karbi Sabeena dake hannunshi tana sabata a kafada. Sai data juyo ta kula dasu Hamna. Muryar Hamna a sanyaye tace

"Mun dauko kudin da muka gani a jakarki"

Hannu ta mika ta amshi kudin a wajen Azrah, dakyar ta iya dai-daita muryarta da fadin.

"Ku koma gida, kunga asibiti zan kaita. Azrah ko taliya ki dafa muku. Dan Allah kubi a hankali wajen kunna gawayin"

Idanuwan Hamna cike da hawaye take girgiza ma Tasneem kai

"Nidai mu tafi tare"

Cike da damuwa Tasneem din ta amsata da cewa

"Kinga asibitin zana zan kaita, akwai nisa sosai Hamna, ga siyan kati da magani, kar kudin ko bazasu isa ba"

Hannunta Azrah ta kama tana girgiza mata kai. Hawayen da suka zubo ma Hamna ta goge

"Saikun dawo"

Ta fadi, kasa magana Tasneem tayi kawai ta juya tana nufar titi, ta dauka akan halin Ummi tasan menene tashin hankali, sai yau, sai yanzun da take jinta kamar duniyar ta tattaru waje daya. Bata taba zuwa asibitin Zana ba, tadai san can ne takeji ana cewa ana kai yara in basu da lafiya.

Batasan motar daya kamata ta shiga ba, ga Sabeena da takejin tana wani irin nishi a jikinta, bata san kuka take ba, dan ko saukar hawayen bataji a kuncinta ba, sai da taga hanya na mata biji-biji, ta runtsa idanuwanta ta bude su tukunna tasan hawaye ne cike da idanuwan.

"Tasneem!"

Taji an kwalla mata kira, bata damu dako waye ba, dan batashi take ba, sai da taji an sake kiranta a karo na biyu tukunna ta juya, batare data yarda da kunnuwanta ba. Dan babu yanda za'ai ta dinga juyo muryar Tariq bayan bai dade da tafiya ba. Gyarama Sabeena zama tai a kafadarta, tana sa dayan hannunta ta matso hawayen dake cike da idanuwanta.

Tariq ne, murmushi yai mata daya sa hawayen ta sake zubowa yana takowa ya karaso inda take.

"Duk sanda komai yaimun duhu sai Allah ya kawoka Ya Tariq"

Ta karasa muryarta na karyewa da ya dauke murmushin dake fuskar Tariq din, balle dayaga hawayen da sunqi tsayawa daga idanuwanta.

"SubhanAllah. Tasneem me yake faruwa ne"

Muryarta can kasa saboda kukan da takeyi tace

"Beena ce, bansan me ya sameta ba, wallahi lafiya kalau mukai karya da safe"

Karbarta Tariq yayi yana tallabeta a hannunshi.  Damuwa bayyane a fuskarshi yake kallon Sabeena dake hannunshi

"Yanzun ina zaki kaita?"

Fuskarta Tasneem ke gogewa duk da har lokacin hawaye baibar zubo mata ba

"Asibitin zana"

Ware idanuwa Tariq yayi

"Ai yayi nisa Tasneem, kuma rana tayi, ga su da wulakanci, akwai karamin asibiti nan kasanmu, muje sai mu fara kaita nan. Kinga kamun mu gano asibitin zana daga nan bachirawa ita kanta tasha wahala"

Kai ta daga mishi suna jerawa tare, a zuciyarta tana ma Allah godiya da duk sanda komai zai cakude mata sai Tariq yazo.

"Bansa ran dawowarka yanzun ba"

Ta fadi a sanyaye. Sauke numfashi mai nauyi Tariq yayi danshima bai tsammaci zuwan nashi nan kusa ba. Sai dai damuwarta ta danne tashi wannan karin.

"Na tafi ban tsaya munyi sallama ba ko?"

Ya tambaya maimakon amsa maganar datai mishi, dan kallonshi tayi, tana murmushi a wahalce kamun ta jinjina kai da fadin

"Ka dawo yanzun...ya wuce"

Shima murmushin yayi

"Nagode..."

Yace, basu kara magana ba har suka karasa asbitin. Komai yazo ma Tasneem da sauki kasancewar Tariq din, waje ta samu ta zauna tana rike da Sabeena. Shi yaje ya yanki kati da duk abinda ya kamata kamun su zauna bin layin ganin likita. Dayake wajen mata daban, na maza daban, sai dai murmushi kawai da suke mayarma juna duk in sun hada ido.

Nauyin da taji ya danne mata kirji dazun yai sauki kamar ganin Tariq din ya dauke mata shi. Ko da layi yazo kansu ita ta shiga da Sabeena, ba kamar sauran asibitocin gwamnati ba musamman kanana, sosai suka dudduba Sabeena, yana karawa da yima Tasneem din tambayoyi.

Magungunan daya rubuta yace taje ai kokari a siyo dan akwai allurai da ake bukatar ayima Sabeena din kamun su tafi. Tana fitowa Tariq ya taso

"Ya dai?"

"Magunguna da allurai za'a siyo"

Takardar ya karba da fadin

"Ki zauna da ita in fita in siyo. Yadan fi sauki a waje"

Kudin dake hannunta ta mika mishi, saidai dubu biyu ya zara a ciki da fadin

"Barsu haka, akwai kudi a hannuna ko bazai isa ba"

Kai kawai ta iya daga mishi tana samun waje ta zauna. Yakai mintina ashirin kamun ya dawo, da kanta ta sake komawa wajen likitan ya dudduba duka magungunan ya nuna mata ka'idojin shan kowanne tukunna yai ma Sabeena alluran. Suna hanya harta daina nishin da take, tayi luf a jikin Tariq da alamun bacci take.

"Da bakazo ba bansan yanda zan ba"

Tasneem ta fadi, har a zuciyarta tanajin dadin zuwan nashi. Murmushi kawai Tariq yai mata, har suka kai gida, da gudu su Hamna suka taso

"Ya jikin nata?"

"Me ya sameta?"

"Taji sauki?"

"An dubata?"

Su duka suke jero mata tambayoyin a tare, hannuwanta ta daga musu tana murmushi.

"To yan jarida. An dubata, kuma taji sauki, bacci ma take"

Kai suka jinjina. Sannan suka gaishe da Tariq, Azrah na dorawa da

"Yaushe kazo?"

"Ba dadewa Azrah. Hamna ya makaranta"

"Alhamdulillah..."

Ta amsa tana murmushi. Sabeena ya mikama Tasneem data kwantar da ita kan tabarmar a hankali tana gyara mata kwanciya. Hadi da ajiye ledar magungunan a gefe. Hannu Tariq yasa a aljihu ya dauko kudi yana mikama Tasneem.

"Ga kudin ki, na hannuna ma sunyi yawa"

Girgiza kai tayi.

"Ka rike Ya Tariq, hidimar tai yawa ai"

"Ki karba Tasneem"

Ya fadi da wani yanayi a muryarshi dayasata kasa yi mishi gardama. Karbar kudin tayi.

"Ni zan koma"

"Zaka koma? Ba kwana zakayi ba?"

Hamna ta jefe shi da tambayar da Tasneem din ta bude baki dan tai mishi. Su duka suna tsare shi da idanuwa.

"A'a amman zan dawo dana samu lokaci in shaa Allah"

"Allah ya kaimu. Ka gaishe da Yaya Ashfaq"

Azrah tai maganar. Hamna kuwa shiru tayi bata ce komai ba. Tasneem yake kallo, yana jiran tace wani abu, amman tayo shiru itama.

"Allah ya kara sauki. Ki kiyaye da bata magungunan yanda likita ya fadi"

Shirun dai ta sake yi. Ganin ba zatace komai ba yasa shi juyawa. Bin bayanshi tayi har cikin soron gidan kamun tace

"Me yasa?"

Juyowa yayi yana kallonta

"Me yasa zaka tafi? Me yasa komai bazai koma kamar da ba?"

Ta bukata tanajin wani sabon kuka na shirin kwace mata. Kewarshi na mata nauyi a zuciya. Idanuwanshi taga sun kara kankancewa

"Zan dawo..."

Girgiza kai take, hawaye na zubo mata.

"Tasneem... Ki kalleni"

Dago kai tayi tana sauke idanuwanta cikin nashi

"Zan dawo. Kina jina? Zan dawo, ki kula da kanki, ki kula dasu"

A hankali ta daga mishi kai tana kokarin mayar da hawayenta, a cikin idanuwanshi akwai gaskiyar da take karanta, akwai tabbacin cika alkawarin daya daukar mata, akwai gaya matan da yake ta zama mai karfin gwiwa.

"Ina bukatarki da karfin zuciyarki Tasneem, bani kadai ba, harsu Azrah, kina daga mana buri kan cewar komai zaiyi sauki"

Maganganun shi sun kara dakar mata da zuciya. Hannu tasa ta goge hawayenta.

"Ka kula da kanka, addu'a ta na tare dakai Ya Tariq"

Murmushi yai mata yana juyawa batare dayace komai ba, ta fahimta, bata bukatar yace komai. Saida ta daina ganinshi tukunna ta sauke numfashi mai nauyi, juyawa tai tana komawa cikin gida da kwarin gwiwar bama su Sabeena kulawar da suka kasa samu wajen Ummi.
*

Su Azrah basu dafa komai ba, dan ta basu karfin gwiwa alalen tayi musu. Cikin hukuncin Allah kamun Maghrib Sabeena ta warware, fura ta fita da kanta ta siyo mata. Da yake su Azrah kin zuwa islamiyya sukai. Bata matsa musu ba, dan kamun ma tai magana sun shirya da kansu.

Gidan suka tura sukai alwalar sallar isha'i suka shige daki abinsu. Ko da Ummi ta dawo ma Tasneem kadai ta fita tai mata sannu da zuwa. Su dukkansu kin fitowa sukai.

"Me kuka dafane Tasneem? Yunwa nake ji wallahi"

Cike da mamaki Tasneem din take kallonta dan bata damu da abincin su ba, ko Abba na nan takanyi wata bata ko kalli me suka dafa ba. Tun Tasneem na jagwalgwala musu harta fara iyawa.

"Alale mukai, akwai saura"

"Zubo mun"

Kitchen Tasneem ta shiga ta sakko mata guda ukkun data rage ta zuba mata mai da yaji ta kawo mata. Tsakar gidan ta zauna tana kallon Ummi cike da mamaki. Tas ta cinye alalen dan ta mata dadi ba kadan ba. Kamun tai magana Tasneem ta dibo mata ruwa ta kawo mata.

Tana ajiye kofin wani almajiri na shigowa. Sai da taji zuciyarta tai wata irin mummunar faduwa. Aikam kiranta ake waje

"Kaje kace bata nan"

Ta fadi, ummi har sauri take ta hadiye ruwan data kurba. Amman har yaron ya fice

"Wanne irin ace bakya nan? In Alh. Madu ne fa?"

Tasneem batace komai ba, ta wuce ta shige daki abinta. Mikewa Ummi tayi tabi bayanta

"Tasneem ki fito ki wuce kije nasan bai kai da tafiya ba"

"Nifa babu inda zanje Ummi"

Rai a bace Ummi take kallonta, dan yai haka tagama walagiginta bin bashin gwanjunan da mutane suka dauka, dakyar ta samo dari biyu, gidan yan uwa kuwa hade rai sukai tayi da suka ganta. Dan taga kwanakin nan biyu hade mata fuska suke. Asabe ma shekaranjiya taga shigewarta daki, yayan suka ce mata bata nan.

Shine Tasneem zatai mata bakin ciki, bayan tana da tabbacin in Alh. Madu bai kawo kayan ciye-ciye ba zai ba Tasneem din kudi.

"Wallahi baki isa ba....bazan haifi ya mai bakin ciki ba. Gaisawar da zakuyi?"

Muryar Tasneem na rawa tace

"Ummi rannan fa hannu ya rikemun. Kuma kinsan ba kyau"

Tafa hannaye Ummi take

"Oh Allah ni Bara'atu, Tasneem kiji tsoron Allah, ke dai kawai kice ba zakije ba, kin koyi karya ko? Alh. Madun ne ya rike miki hannu?"

"Wallahi ba karya nake ba..."

Ta karasa muryarta na karyewa, idanuwanta cike taf da hawaye. Dan ko Ummi zata daketa yau ba zata fita wajen Alh. Madu ba.

"Dan Allah Ummi ki kyaleta. Beena ma bata da lafiya yau har asibiti aka kaita"

Azrah ta fadi. Da sauri Ummi ta shiga dakin tana duba Sabeena da ke bacci.

"Asibiti kuma? Me ya sameta?"

Hawayen daya zubowa Tasneem ta goge

"Ciwon ciki, amman da sauki"

Sauke numfashi Ummi tayi, tana sake dubata, taga bacci take a nutse.

"Me yasa baki gayamun ba?"

Ta bukata tana kallon Tasneem din

"Gani nai taji sauki, kuma harmun siyi magungunan da komai shisa, kiyi hakuri"

"Allah ya kara sauki..."

Ummi ta fada tana dorawa da

"Amman in ya dawo gobe zaki fita ku gaisa. Bana son munafunci kina jina ko?"

Kai kawai Tasneem ta daga mata, ba tambayar inda suka samu kudin magunguna ko ma jikin Sabeena bane matsalar Ummi, ganin Alh. Madu ne. Ficewa tai daga dakin, ranar ko Radio basu ji ba. Haka suka kwanta. Tasneem tai musu addu'a.

Bacci mai karfin take, kamun ta bude idanuwanta, zuciyarta na wani irin dokawa kamar zata fado daga kirjinta. Ba shiri ta lalubi fitila ta kunna tana sa hannu a kirjinta ko hakan zaisa zuciyarta ta daina bugawa.

"Ya Tasneem na kasa bacci"

Ta ji muryar Azrah na fadi, ba karamin tsorata tai ba dan kamar daga sama taji maganar.

"Oh Allah Azrah kin bani tsoro"

"Nima tun dazun na tashi. Mafarki nai mai ban tsoro amman na kasa tuna kona menene"

Cewar Hamna data tashi zaune itama. Shiru suka zauna nawani lokaci kamun Hamna tace

"Ko dai muyi sallah sai muyi addu'a?"

Su dukansu yarda sukai da maganar Hamna. Tare suka fita tsakar gida suka daura alwala. Nafila sukai raka'a hudu hadi da gabatar da Addu'o'i. Jikin Tasneem Azrah ta kwanta nan kan dardumar ko Hijab bata cire ba, itama Hamna Qur'an ta dauka tana kwanciya jikin Tasneem hadi da budewa. A hankali suke sauraren kira'arta cike da fidda hakkokin tajwid har nutsuwa ta soma saukar musu...!
[11/30, 10:17 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

06

Sanin bawani baccin kirki suka samu ba su dukansu shisa bata tashi kowa ba. Tsaf ta share ko ina tai wanke-wanke. Wanka tayi, sanda ta fito a tsakar gida ta sami Sabeena, dan haka ta juye ruwan zafin itama tai mata sannan ta dorama su Hamna nasu.

Bata tashe su ba har saida ta tabbatar ruwan yayi zafi tukunna. Shirya wa sukai su duka fes dasu. Tasneem najin yanda jikinta yake a sanyaye har lokacin.

"Ko zaku siyo mana biredi ne da kosai, musha shayi?"

Ta tambaya tana kallon su Azrah.

"Rana batai ba? Za'a samu kosai kuwa"

Cewar Azrah.

"In babu saimu dawo ai, mu duba dai"

Hamna ta fadi tana mikewa tsaye da nufar inda jakar kayansu take ta dauko Hijab dinta. Itama Azrah tashi tayi. Kudin Tasneem ta basu da fada musu ko na nawa zasu siyo tana bin bayansu suka fito tsakar gidan tare, ita tana wucewa kitchen. Ruwan shayi ta dora musu ta koma daki abinta.

Aikam har kosan sun samu, ci sukai suka koshi har sukai Hamdala. Yanayin jikin kowa baya mishi dadi, dan haka suka sake komawa suka kwanta. Gyara kwanciya Hamna tayi

"Ni inason yin guga ne ma. Allah yasa su kawo wuta kamun lokacin Islamiyya"

"Amin dai, nima inason yi wallahi, amman kaina nakeson kwancewa kwiya ta hanani tun jiya. Yaya Tasneem zakimun kitso in kwance?"

"Ki kwance mana Azrah. Sai in miki kamun lokacin dora girki yayi, banason yin ranar abincin saboda zaku Islamiyya. Hamna kefa?"

Girgiza kai tayi

"Bayau ba, kaina namun nauyi tun jiya"

"Da kin koma bacci, Sannu"

Azrah ta fadi cike da kulawa. Dan daga mata kafada Hamna tayi

"Um um nikam, bana jin wani bacci, dauko kibiyar dai in tayaki kwance kan"

Ai bata ma karasa ba Azrah ta mike tana dauko abin taje kai da kibiya. Tana zama sunajin Sallama data gauraye dakin, wani irin dokawa zuciyar Tasneem tayi kamar zata fito daga kirjinta, karfin dokawar na sata runtsa idanuwanta gam da fadin

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Azrah ce ta amsa Sallamar muryarta na rawar data rasa dalilin shi, kamun ta mike ganin Tasneem bata da shirin yin hakan. Hijab ta dauka, sukaji kamar mutane a tsakar gidan su. Kamun Tasneem tajiyo muryar Ummi a gigice tana tambayar

"Me yake faruwa? Lafiya?"

Ai bata tsaya daukar Hijab ba ta mike zuwa kofa suna rige-rigen fita ita dasu Azrah. Mutane ne sunfi takwas, fuskokin su Tasneem take kallo, amman daga ciki mutane baifi biyu zuwa uku take tunanin tagane ba, take tunanin dukansu yan nan unguwarsu ne. Zuciyarta na bala'in dokawa take binsu da kallo, kamun taji Hamna ta riko mata hannu tana jijjigata.

"Ya Tasneem jini..."

Ta fada muryarta can kasan makoshi, sai da Tasneem ta kallo fuskar Hamna datai wani irin ja kamar tasha rana, da idanuwanta da suka fiffito waje cike da tashin hankali, kamun ta mayar da kallonta zuwa inda idanuwan Hamna suke a kafe. Kwakwalwarta ta fara gayama zuciyarta likkafani ne, badan farin zawwatin ba, sai dan yanayin yanda yake a qulle daga karshe alamar wajen kafafuwa da kuma kai, sannan kuma mutum ne a ciki, ko kuma gawa, kamar yanda wata murya ta fada mata.

Duk ba wannan ba, jini ne a wajaje da yawa jikin likkafanin, musamman ta wajen kan daya hudo har yana diga ta gefe alamar ya taru a wajen.

"Me yake faruwa wai? Lafiya? Waye wannan?"

Ummi ta tambaya tana karasawa inda suke.

"Waye a cikin abin nan? Ni ina tsoron abin nan Yaya Tasneem"

Azrah ta fadi idanuwanta cike da hawaye, tana boyewa bayan Tasneem kamar zata shige cikin jikinta. Bata su Tasneem take ba, amsa take jira mutanen da suke tsaye su bama Ummi.

"Wani bazai fara magana ba? Ya zaku shigomun gida da sanyin safiyar nan, ku ajiyemun gawa a tsakar gida kuma kuyi tsaye kuna kallona?"

Ummi tace ranta a bace, saboda bacci take mai nauyin gaske suka tashe ta, tama yi mamakin yanda akai taji sallamar su, dan hayaniya komin karfinta bata katse mata bacci, amman yau a gigice ta tashi zuciyarta kamar zata bar kirjinta saboda dokawar da take. Daya daga cikin mutanen da Tasneem bata gane bane ya kalli Ummi da wani yanayi a idanuwanshi.

Yanayin da yasa jikinta bari, wani abu na fada mata kome zai fada ba alkhairi bane, kunnuwansu ba zasu so jin abinda duk zai fito daga bakinshi ba. Tana kallo ya fara motsa labbanshi da maganar da zata canza musu komai, maganar da zata hargitsa musu duniyarsu gabaki dayanta.

"Hatsari aka samu wajen aikin su Alhaji Zanna, gini ne ya rugozo da ma'aikatan gabaki daya, da yawan sun jigata, mutum shidda Allah yai ma rasuwa, Mal. Muftahu na cikin su Shida Alhaji Zanna, yanzun haka shima an wuce da gawar gidan iyalanshi..."

A wani waje tsakiyar maganar da mutumin yake yi Tasneem ta daina fahimta, saboda komai ya mata shiru, bugun zuciyarta take ji har cikin kunnuwanta, tana jin shi a cikin budewa da rufewar da idanuwanta suke yi, bata san kafafuwanta sunyi sanyi ba saida tajisu a kasa, hannuwa take ji suna riketa, ture su take saboda bata son komai ya tabata ta, bata son komai indai ba abinda zai canza maganganun da kunnuwanta suka jiye mata bane ba.

Idanuwanta kafe suke kan gawar Abba, kan jinin daya taru gefen kanshi daya fara gangarowa tsakar gidan a hankali, ba zatace jan jiki ko rarrafe tai ba, tasan dai taganta gefen gawar Abba ne, hannuwanta duka biyun tasa a jikin likkafanin tana tabawa.

"Abba..."

Ta kira muryarta na fitowa dakyar, in tace iya kirjinta ke wani irin ciwo karya take, dan ciwon da take ji yawo yake a jininta.

"In shaa Allah wannan karin in na dawo kasuwa zamuje muyo siyayya da yawa. Duk abinda kuke so zan siyo muku"

Taji muryar Abba cikin kunnuwanta.

"Ki kula da kanku, dan Allah kuyita hakuri da Ummin ku har Allah ya ganar da ita. Ku dinga mata addu'a kinji ko?"

Ta sake jin maganganun shi kamar yana gabanta, jin kamar ta taba lema a hannunta ne yasata dauke shi daga gawar Abba da sauri. Dubawa tai, jini ne a duka hannuwanta biyun. A jikin zaninta take gogewa da sauri da sauri kamar wadda ta samu tabin hankali.

Dagowa tai ta kalli mutumin dayai ma Ummi magana lokutta kadan da suka wuce.

"Yaushe ya rasu?"

Ta tambaya. Tana kallon yanda yake kokawa da maganar dazaiyi kamun yace

"Cikin dare, bazance ga lokacin ba, amman biyu ta wuce. Kuyi hakuri dukkan mai rai mamaci ne in..."

Katse shi Tasneem tayi

"Inda yaje muma zamuje ko? Baiyi sauri ba, mu kuma bamuyi jinkiri ba"

Kai ya daga mata a hankali. Wani abu da yake tsaye a makoshinta ta hadiye.

"Ki kula dasu..."

Taji muryar Abba. Bata san inda karfi yazo mata ba, mikewa tayi tana juyawa. Ummi ce jingine da bango tana wani irin kuka kamar zata shide. Dauke idanuwanta tayi daga kan Ummi tana mayarwa kansu Azrah dake kallonta suna son ta tabbatar musu da gaskiyar abinda suka ji.

"Abba ne a cikin abin nan? Abba ya rasu?"

Hamna ta fada. Har cikin zuciyarta Tasneem taji zafin maganganun da Hamna takeyi, kamar tana zuba mata gishiri a sababbin ciwukan ta takeji.

"Shine Hamna. Ya rasu da gaske"

Dariya Hamna tayi tana girgiza ma Tasneem din kai hadi da karasowa, riketa Tasneem tayi, ture Tasneem din tayi tana tsugunnawa gaban Abba.

"Abba ka tashi, ka tashi Abba karmu zama marayu. Wallahi marayu wahala suke sha sosai Abba. Kaga yanda su Ya Tariq suka zama. Ai ba zakai mana haka ba ko? Ba zaka barmu kamar su ba... Waye zai siyo mana abinci? Abba waye zai bamu kudin makaranta? Wazai hana Ummi dora mana talla?"

"Hamna.."

Tasneem ta kira sunanta tana riko mata kafada, ture hannunta Hamna tayi, tana saka rigarta ta goge hawayen da suka zubo mata. Sai ta yarda Abba ya barsu ne zatai kuka. Bai barsu ba, bata ga dalilin dazai sa ta kuka ba.

"Abba dan Allah ka tashi...Abba..."

Ko alamar motsi bata ga yayi ba. Mikewa tsaye tayi hawaye na zubo mata. Kai kawo take tsakar gidan, wani mutum da yakejin bazai iya jurewa ba ya fice daga gidan. Kamun suma sauran subi bayanshi dan suba su lokacin yin bankwana da Abban, shisa suka shiryashi tun daga can. Ba zasu so iyalanshi suga yanayin raunukan dake jikinshi ba.

Azrah kuwa kamar an kafeta a inda take, kallon su take, numfashinta take kokawar nema ta rasa, kokawa take amman ta kasa numfashi tunda suka fara magana, wani irin dubu tagani ya gilma mata kamun komai ya dauke. Tasneem ce ta farayin kanta da gudu ganin ta suma. Dagota tayi tana jijjigawa.

"Itama ta rasu ko?"

Hamna ta tambaya tana tsare Tasneem da idanuwanta da har sun rine. Girgiza mata kai Tasneem tayi tana sakin Azrah ta dibo ruwa tazo ta shafa mata. Ajiyar zuciya ta sauke tana bude idanuwa. A firgice ta mike tana sake kallon su tukunna ta kalli inda Abba yake. Wani irin kuka ta fashe dashi, tana fadowa jikin Tasneem, rike ta tayi. Tana kamo Hamna da dayan hannunta.

Sunfi mintina sha biyar suna wani irin kuka su biyun tana jinsu, dan zuciyarta a bushe take jinta. Hawayen sunqi zuba, daga ciki suke mata quna mai ciwo. Dakyar ta iya mikar dasu tana nufar hanyar magujin su, ruwa ta zuzzuba a butoci tana fara alwala, suma hakan sukai duk da kukan su yaqi tsayawa.

Saida Tasneem ta sakko Hijab tukunna tazo ta kama Ummi dake wani irin kuka.

"Me yasa Abban ku zaimun haka Tasneem? Dawa zanyi fada yanzun? Yazanyi daku? Ya zan da rayuwata? Wallahi shi kadai ya ragemun, banda wasu yan uwa na kusa, shi kadai ne, shi kadai..."

Riqeta Tasneem tayi ganin yanda jikinta yake wani irin tsuma. Saida tadan samu nutsuwa tukunna ta kamata takai ta daki ta barota. Sukam gawar Abba suka zagaye suna mishi addu'a. Basu tashi ba har saida aka shigo daukar gawarshi. Nan tashin hankalin yake dan Hamna kamashi tayi ta rike gam tana kuka.

"Ina zaku kaishi? Dan Allah ku tsaya. Bamu shirya ba... Wallahi bamu shirya ba, Yaya Tasneem ki fada musu bamu shirya ba..."

Girgiza mata kai Tasneem tayi, zuciyarta na wani irin kuna.

"Ba'a shiryama mutuwa, Hamna bata Sallama balle baka damar kimtsawa. Ki mishi addu'a Allah yasa mutuwa sauki ce a gareshi...kaunar da ta rage tsakanin mu kenan..."

Tasneem din ta karasa tana riko Hamna, su duka biyun jikinta suka fada. Tana kallo aka dauki Abba aka saka cikin munkarar da aka shigo da ita. Kallon su take lokacin da zasu fita dashi. Sai lokacin ta lumshe idanuwanta.

'Allah ya sada fuskokinmu a Aljanna Abba, Allah ya haskaka kabarinki kamun akai ka cikin shi, dukkan wahalar kwanan yau Allah ya saukaka maka'

Ta fadi a

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

12 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment