Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gobe idan allah yakaimu,
Ahaka suka dawo gida karfe sha biyu da yan mintina gabaki dayansu har Dr zayyad kasancewar kawai manyan likitoci masu aikin dare kuma zasu kula da ita sosai kamar yana nan,
Sadda suka isa gidan shiru gabaki daya yan gidan sunyi bacci hakan yasa kowa Yakama bangarensa,
Su khadijama tuni sun shige day an dakin itada ummy da al'hussain kasancewar aunty maimuna fonitures dinta bibbiyu aka kawota dasu,
Hakan yasa koda baba isuhu yadawo yashige dakinsa baimasan suna part dinsaba,
Kasancewar khadija bata samu osasahen bacciba kuma ga kukanda tasha yasa tunda yayi sallar asuba bacci yasake dauketa akan daddumar,
Ita kuma ummy ganin khadijar ta samu bacci yasa bata tasheta ba tabarta tavigaba da baccinta,
Tanufi part din mamar,
Abba kadai ta iske Avalon ahima har yashirya zashi asibitin suka gaisa,
Agurguje ummy tashirya kasancewar zasu makaranta itada fateema tunda su suna da lectures kuma zasu biya asibitin su gaiaheda ammi,
Koda aunty maimuna ta leko taga khadija bata farkaba ita ma kyaleta tayi tacigaba da baccinta,
Karfe takwas da rabi gabaki daya mutanen gidan suka shirya zuwa asibitin,
Umma karama dasu aunty rukayya da aunty zainab mama karama da mama babba da ameenatu duk sun fito kasan cewar baba Iro yace tabar khadijan idan tatashi sa taho tareda su,
Duk sun hallara a farfakiyar gidan baba ummarune yace mazan su hau motar yaya munir yayinda yace hajiya da mama babba da umma karama su hau motar sa,
Yaya mamman akace yaje yacewa yaya zayyad inya shirya yazo yadauki sauran amotarsa,

Abangaren yaya zayyad kuwa tunda suka dawo daga asibiti yakasa samun sukuni abubuwa dayawane duke yawo akansa yama NASA tunanin me zaiyi,
Ba abinda yafiyimasa yawo a kwakwalwa sama da maganganun mama musamman ma akan waccan izzatun yarinyar,
Shin shi yaishema yataba magana da mamar akan cewar khadija tana likewa maza?
Sosai yaringa tunani akan abubuwa dayawa Wanda sanadin hakan ya haifar masa da ciwon kai hakannema yasa baiyi bacciba sai wajajen karfe biyu ahima bayan yayi alwalla tafara nafila daga bisani baccin ya kwasheshi Wanda yasa shi dakyar yatashi da wani masifaffen ciwon kai yayi sallar asuba kafin yakoma baccinda baitashiba har yanzu,
Ganin kofar dakinnasa arufe yasa yaya mamman bugawa Wanda hakan yatashi Dr zayyad daga bacci,
Cikin magagin bacci yace,
"Waye"
Daga waje yaya mamman yace,
"Yaya zayyad nine mamman dama Abba ne yace inka shirya kafito kadauki sauran mutanen muje asibiti"
"OK mamman kace masa wllhy na makarane yanzuma zantashi "
Yafada cikin muryar bacci17


"OK "
Yaya mamman have tareda komawa yasanarda abban sakon yaya zayyad,
Dole baba safiyanune yadauki motar sa shima tareda cewa sauran yaran su shiga,
Har kowwa yashiga amma mama babba tana hanga idanu kota hango khadija amma batagantaba kuma bataga alamun zata fitoba,
Lallai kuwa yarannan watakam sun hada meeting ne akan sai kowwa yatafi sannan su taho,itadama ba tun yanzuba take tunanin duk rashin jituwar munafurcine tsakanin khadija da zayyad din amma aboye akwai wani abin,
"Wai ina ita khadijan ne ko ita bazataba"
Mama babba tafada kamar bawani Abu azuciyarta,
Baba ummarune yacewa amima taje takirata abangaren hajiya,
Harzata tafi aunty maimuna tacewa baba ummarun ai khadijan tana part dinta tana bacci kasancewar jiya bata samu isasahen bacci ba yasa abban alhusaain yace abarta sa taho dashi da ita da hajiya,

Baba ummarunne yace
"badamuwa Ku kushiga muje"
Sosai wani mugun bakin ciki yatasowwa mama babba aranta tace,
"Lallai itama matar Iro ganinakefa kamar tafara wuce gona da iri tayi wata kwafa acikin ranta"
Azahiri kuwa sai ta wayance dacewa,
"Allah sarki ai khadija akwai sawa rai damuwa,totunda hakane ke aminatu kifito kije gurinta tunda dai taku tafi zuwa daya ki lallabata ta tashi taci abinci tayi wanka inyaso saiku taho tare"
Tafada tareda kallon aminatun takashe mata ido gamida cije lebe batareda kowwa yaganiba,
Sosai aminatu tadauki haske da maganganun mahaifiyar tata,hakan yasa tayi azamar fitowwa,
Sosai kowwa agirin ya yadda da maganar mama babba batareda sakawa ransa komaiba kasancewar babu Wanda ke kawo wani Abu aransa,
Saidai kuma aunty maimuna taga sum abinda mama babba tayi sannan kuma ranta yadarsa mata wani Abu amma kuma bata fahimci komaiba haka suka dauki hanya yayinda aminatu kuwa tawuce part din aunty maimuna,

To abangaren merry kuwa yau tunda sassafe ta tashi tadafa ingantaccen ruwan shayi tareda soyayyen dankalin turawa da kwai dakuma lafiyayyen bread,
Bayan yayi wanka tasaka wata wadatacciyar doguwar riga tareda daukar wani kyakkyawan zumbudeden hijab tasaka tadaura nikab afuskarta,
Bakaramin kyau shigar tayimataba kasancewar bata saba dayintaba hakan kuma bakaramin takurata yayiba,
Agsky badan soyayyar Dr zayyad data takurawa rayuwartaba da babu abinda zaisaka ta kunshe jikinta cikin wannan urban lafta laftan kayan,
To saidai kuma soyayya daban take musamman ma kaunar datakeyiwa Dr zayyad din wadda take junta har cikin bargonta,

Haka ta fito daga gidannata da basket din Mayan break din tahau motarta rayi hangar asibitin malam aminu kano,
Ahanya takira wata nmb bugu biyu aka daga ko sallama babu tafara dacewar,
"Kamal kudifa nake biyan ka Dan kayimin aiki amma bazaka taba kiranaba saidai ni nakiraka natambayeka Abu"
Daga dayan bangaren kuma akace,
Hajiya merry kiyi hakuri naso kiranki wayannawanefa ba kati sannan kuma kinga INA bakin aiki kamar yadda nafadamiki cewar adokar aikinmu bawanda ke sauka daga bakin aiki sai lokacin saukarsa yayi"
Tabe bakinta tayi tareda rausayar da murya tace,
"Naji,ya aka tsaya"
"Eh to har yanzu dai mutunen naki baizoba amma naga yanzu yan gidansu sun shigo"
"OK badamuwa"
Takashe wayarta tareda yin wani katsssss da cingam din bakinta days zamar mata kamar wata doka,

Koda aminatu tashiga part din aunty maimuna ta Tatarar da khadija na bacci,
Tsayawa tayi akan khadijar tana karemata kallo,
Anya kuwa hasashen mama gskyne akan cewar akwai wani Abu tsakanin yaya zayyad da khadijar,
Tabe baki tayi tareda samun gefen gadon ya zauna aranta tana saka cewar komaidai menen to yaya zayyad natane ita daya kuma tafi wannan alwashin,
Sosai ta tsare khadija da kallo batun yauba take tunanin wai me khadija ta fitane datake da nasarar da ita ba tada ita,
Hakadai tacigaba da yan sake2 da tunanin abubuwa daban2
Khadija CE tajuya da addu'a abakinta tareda mikewa tana salati,
Ahankali tafara murza manyan idanunta harta budesu tangaram akan aminatu datake zaune akan gado da wayarta ahannunta,
Ziro sambala2 kafafunta tayi kasa tareda saka silifas din daauke gefen gadon,
Da kasan ido aminatu Kebin kjafijar da kallo batareda ta San tanayiba ta Dan Tabe bakinta ahankali tareda dauke kanta kamar ma bata lura da khadijanba,
Duk abinda takeyi khadijan batama San tanayiba tunda ba ganinta tayiba,
Bandaki tanufa tayi wanka tareda daukar sabon brush din datagani tabare tazuba toothpaste ta wanke bakinta tareda dauro towel tafito,
Har yanzu aminatun na nan India tabatta,
Gaban madubi ta nufa direct ganin babu iron mandatake shafawa agurin yasa takoma India tavire hijabin datayi sallah ta daukr tasaka tareda kallon maryam tace,
"Nizan wuce part din hajiya"
Adan kufule maryam takalleta tareda cemata,
"Aikedama bakisan abin arzikiba,inba hakaba taya za'ace inzo gurinki inkintashi mutafi tare kuma kintashi amma kikasayimin magana sabosa tsabar ji da izza"
Tunda tafara maganar khadija take kallonta harsaida takai karshe sannan khadijar ta Tabe baki tareda sakar mata wani sakaran murmushi mai ciwo tayi gaba abinta,
Sosai ran aminatu yabaci kasancewar dama da akwai wani abin azuciyarta afusace ta taso tabiyo bayanta,
Afalo ta isketa tsaye ita da baba Iro yanacemata shima ankirashine kasuwa zai fara zuwa amma hajjaju tace taje,
Aminatu CE tagaisheda baba Iro ya amsa tareda cemata,
"Au dama kema baki tafiba,"
" eh dama Abba be yace inzo in khadija ta tashi ma tafi tare"
"OK badamuwa yanzu kuje bangaren hajiya in zayyad yagam shiryawa kwa tafi tare"
Sosai gaban khadija yafadi tunawa da abinda yafaru amotarsa tuni yanayinta yakara canzawa,
Aminatu kuwa wani dadine yafara lullubeta koba komai yanzu zata fara nunawa yaya zayyad soyayyarta agaban kowwa tunda ko baisotaba idan iyayensu sukaga yadda take sonshi dole su auramata shi sannan kuma ga mama datasan zata kara zuzuzta abin,hakan yasa taji wani sassanyan farinciki,
Khadija CE tace,
"Gsky nidai dady(sunan da take Kiran baba iron kasancewar ta ta hannun damansa)bazan hau motarsaba ni gwamma in hau adaidaita"
Dariya baba Iro yayi kasancewar yasan halin darun khadija yasa yace toshikenan in nafito zan biyo part din hajiya sai natafidake nasakaki Dan sahu,
Aransa kuwa cewa yayi kwa karata keda hajiyar,
Ahaka suka kama hanyar part din hajiya khadija na kuncin ance tahau motar yaya zayyad yayinda Amina kefarinvikin zata kasance da Wanda take kauna,
Hajiya suka iske zaune a part din har ta shirya tana zaune da radio ahannunta tanaji,
To dayake shirin yadauki hankalinta yasa sallamrsu kawai ta amsa tacigaba da jin abinta,
Khadijama direct daki ta wuce aminatu kuma tasamu kujera tazauna,
Ko minti biyar batayi da zamaba shahararren kamshinsa yadakammata hanci tuni jikin aminatu yayi likis duk wani kwarin gwiwa datake ji dashi yabar jikinta ko ido takasa dagawa takalli hanyar da kanahin yake fitowwa duk da kwadayinta nason kallon kyakkyawar fuskarta Dr zayyad,
Muryarsa CE tadaki dodon kunnenta cikin daddadan among sautinshi daya ida karyamata sauran garkuwar jikinta yace,
'Assalamu alaykum"
Hajjajuce kawai ta iya amsamasa tareda kaahe radion kasancewar angama shirin,
"Amin alaykumussalamu"
Dr zayyad yasamu guri yazauna akan kujera tareda jingina jikinsa da kujerar yace,
"Hajjaju antashi lpy"
"Lpy kalau zaidu yagajiya"
"Babu" yafada atakaice tareda jawo wayarsa yafara latsawa,
Saida aminatu tayi kokowa da zuciyarta dagaske kafin tayi nasarar rage fargabarda ke cikin zuciyarta ahankali cikin lankwasa murya tareda farrrrrr da ido tace,
"Yaya zayyad inakwana" tareda Dan dukadda kai,
"Lpy"
Shine kawai abinda yacemata,
Hajiyace tacafe zancen dacewa,
"Waini Amina ko wani abune yafadamiki a idon naga kinata marmarashi"
Sosai maganar hajjaju tabata ran Amina amma tadanne cikin sake kakalo wata kisisinar tasake lankwashe murya tace,
"Uhymmn wllhy kodaya hajjajunmu"
Hajiya tace,
"Waini meyasa kukeson zama da murane inmunje asibiti da allah Aidu kabata maganin mura mana,jifa yadda muryarta gabaki daya tafara zama irinta tsuntsaye ko fita sosaima batayi"
Hajiya takarashe zancenta tareda kallon zayyad da baima damu da me sukeyiba, yadaice to ne kawai jin an ambaci sunansa,
Aminatu kuwa jitake kamar ta fasa kuma saboda yadda hajiya tawani yarfa ta,
Watakam duk yadda take canza salo Dan birge yaya zayyad din amma abin baiyiwa hajiyaba barema Wanda tayidanshi data fuskanci ko kallo bata isheahiba,
Lakwas takoma ta lafe jikin kujera batareda ta sake koda kwakkwaran motsiba,
Khadijace tafito sanye da bakar riga mai fadi sosai tasaka mayafin rigar tayi rolling kanta gashin ta data daurene da ribom tayi donout dashine yayi das ajikin rolling din bawata kwalliya tayiba amma tayi masifar kyau,
Blue din jakace karama arataye akafadarta sai blue din plate shoes,
Sosai tayi kyau matuka,
Tunda tafito sassanyan kamahin turarenta yadaki hancinsa baiji alamun takuntaba amma ya tabbatarwa da kanshi izzatuce,
Samun kwayar idonshi yayi da zalamar son ganin yarinyar amma Sam zuciyarsa taha hangar jikinsa aiwatarda hakan,
Kara tsuke fuskarsa yayi tareda basarwa tacigaba da abinda yakeyi,
"Hajiya baba Iro baiahigoba" khadija ta tambaya,
"Eh baishigoba" hajiya tabawa khadijar amsa tareda cigaba da cewa,
"Kiyi sauri ki karya ke muke jirafa"
"Hajiya nifa ba Ku zanbi ba ni baba irone zai kaini"
"Bangane irone zai kaikiba Hadiza to Iro dai tuni kilama ya isa kasuwa"
Sharrrrrrrr kwalla suka fara zuba a icon khadijar tuni kuma tafara yayyarfa hannuwa tareda bubbuga kafafu,
"Ni wllhy hajiya bazan bikuba ai dai baba ironne yace injirashi zaizo mutafi ni kawai mutafi ko adan sahu zan taho" khadija tafada ashagwabe tana turo baki,
Jin ta ambaci Kalmar Dan sahu yasa zuciayr Dr zayyad wani irin harbawa da baisan meyasa hakanba,
Afusace yadago kansa gamida galla mata wata mahaukaciyar harara,
Shiru kuwa tayi da bakinta tuno kashedin jiya dayayimata akan yimasa gardama,
Aranta tayi tunanin tunda ga hajiya gakuma aminatu ai babu abinda zaiyimata hakan yasa aahagwabe tasake cewa,
"To hajiya mutafi innaje asibitin zanyi break din"
"Hmmm ai Hadiza dabansan halinki da abinciba wllhy nasan komunje can dinma ba ci zakiyiba"
"Wllhy hajiya zanci"

Zayyad ne yadago idonsa yakalleta suka hada ido,
Saurin janye nata tayi tareda yin Mimi da baki,
Sosai yakura mata ido kusan minti daya kafin yayi murmushi akasan ransa na zaki gane,
Azahiri kuwa kara hade ransa yayi tareda cemata,
"Ki soyomin kwai"
Haka kawai yacemata yamaida kansa jikin wayar tareda cigaba da abinda yakeyi18



saroro ta tasaya tana kallonsa dan tabbatarda maganar daga bakin Wanda tafito,
Baiko sake daga ido yakalletaba barekuma tayi tunanin zai sake maimaita abinda yafada,
Itama bata damu da maimaitawar tasaba tajuya gurin hajiya tareda sake maimaita,
"Hajiya Dan allah muje can na karya"
Shekeke hajiya ta kalleta,
"Wai Hadiza meyasa bakida kunyane"
"Mekuma nayi hajiya"
Khadija tafada cikin shagwabe fuska,
"Hadiza injiyemiki ranar dazan mitu nabarki cikin wayannan mutanen dasuka tsaneki sanadin rashin kunyarki"
Hade rai hkhadija tayi tareda cewa,
"Wai yanzu kema hajiya kinyadda banada kunyar kamar yadda suke fada,toyanzu menayimikine hajiya"
"Yanzu ba zaidune yace ki soyamasa kwaiba"
Zaro ido khadija tayi tareda kallon hajiya tace,
"Hajiya bafani yaceba,bakiga wadda yasaka tuni ta tashiba,"
Sai alokacin hajiya takai dubanta gurin da aminatu take,
Wayam tagani bakowwa agurin hakan yasa ta girgiza kanta alamun gamsuwa,
Shikuwa Dr zayyad da tunda Amina ta tashi yaganta Yakuma tabbatar da cewar tasan ba it's yasakaba hakan yasa baisakeyin maganaba yacigaba da abinda yakeyi,
Itama khadija guri ta nema tazauna tanata hada rai ita adole ranta abace yake,
Lokaci ziwa lokaci zayyad yakan Dan saci kallonta ta Kasan ido lallaima wannan yarinyar amma badamuwa,
Duk hara far datake antayawa yaya zayyad yanaganinta takasan ido amma baima nunamata yasan da zamantaba,
Har aminatu ta hada kwan,
Sosai ta tsaida hankalinta wajen dakuma baje basirarta wajen siye zuciyar yaya zayyad din da daddadan suyar kwan dayaji albasa da magi,
Tana gama ta hadamasa da ruwan ya'yan itatuwa kasanvewar tasan cewar shi ma'abocin son sune,
A plate ta juye kwan akalla zaikai gusa boyar sai kamshi yake tashi ta hada da kofin ruwan ya'yan itatuwan ta nufi falo,
Har kasa taduka tareda ajiyewa Dr zayyad agabansa tace,
"Gashi yaya"
Saida yadan basar tareda shan kamshi kafin yadago kansa da Dan murmushi afuskarsa yace,
"Thanks"
Sosai amimatu taji dadin yadda karon farko tafarantamasa amatsayin soyayya ba'a matsayin yan uwantakaba,koba komai dai tasan zata kasance mai nasara,
Wani farrrrr tayi da idonta tareda rausaya jikinta yayinda zata tashi,
Sosai tabawa khadija haushi akan abinda tayi tunda duk akan idon khadijar tayi,
Musamman ma data kasance Wanda takeyi dansa ko kulawa da itama baiyiba,
Batun yauba khadija ta fuskanci aminatu da abubuwa dayawa akan yaya zayyad din datake sai dai zuwa yanzu abinnata yafara canzawa kamar wata mai hauka,
Lallaikam aminatu naso ta tsoma kanta awahala muddin yakasance abinda khadijar take tinani shine azuciyar aminatu,
To inba wahala ba meye abin so anan,
Tasaci kallon Dr zayyad,
Kwata kwata batagano makusarsaba amma fa ita Sam baimataba,
To ma mutumin da yagama tsufa agida meye abinso ajikinsa,
Lallai aminatu kina tareda wahala muddin kikace wannan sarkin takamar zakiso,
Duk tana zancennan me acikin zuciyarta India akarshen zancen zucinnata taja wani uban tsaki,
"Mtsssss"
Gabaki daya afalon kowwa yajita,
Amma Dr zayyad ko dago kansa baoyiba barema yanuna yasan meyake faruwa,
Aminatu CE tazauna kusada ita tareda cewa,
"Yadai sister lpy"
Tafada da alamun tura haushi ita adole Dr zayyad ya yaba da nata kokari,
"Nifa gsky banason takura badamar into Abu saikun tankani to daga nayi tsaki kuma sai gabaki daya ki tsuramin na mujiya"
Hajiya zatayi magana tags zayyad ya ajiye wayarsa tareda kallon khadija,
Sosai rashin kunyar yarinyar take bashi haushi ada,
Sabanin yanzu datake bashi mamaki,to itadai ba abin ka kama dukantaba,
Kallon sakanni yayi mata kafin yacemata,
"Zo nan"
Tuni jikinta yayi sanyi tajuya ta kalli hajiya,
Dauke kai hajiya tayi kamarma batasan meyake faruwaba kafin daga bisani tadauki yar radion ta tareda yin daki karma khadijan taganta tayi tunanin zata shiga shirginsu,
Dr zayyad kuwa baisake ko kallontaba,
Hakan yasata tashi ahankali tareda fara Jan kafafunta kamar kwai yafaahemata aciki,
Sosai yaya zayyad yakure yatsun kafarta da kallon batareda kowwa yasan da hakanba kasancewar ta Kasan ido yake kallonnata,
Ahankali takaraso tareda dukawa agabansa tace cikin Dan turo baki,
"Gani"
Shima cikin isa da takama yagama shan kamshi kafin yace,
"Eat"
Yacigaba da latssa waya batareda yakalletaba,
Saidata dauki lokaci kafin tace,
"Nakoshi"
Sosai ran aminatu yakai makura abaci, wait dama khadijace zataci break din data tsaya bata lokaci tahadashi Dan farincikin zuciyarta,
Wani zazzafan hawayene yatahomata Wanda bata shiryawa zuwansaba,
Aboye tawayance ta share hawayenta,
Dr zayyad kuwa ganin khadija dagaske zata bata masa lokaci yasa yasake kallonta ido cikin ido yace,
"I said eat"
Sosai ta firgita da kallon dayayimata sai dai kuma kwata2 batason cin komai kasancewarta ba ma'a boviyar cin abinciba,
"OK yaya pls zanci"
"OK now"
"Dan allah yaya pls wllhy banasonci in munje asibitin zanci kaji pls Dan allah"
Sosai halittar shagwabar khadija ta fito fili Wanda hakan yafara canza yanayin Dr zayyad,
Ysayawa tayi cak yanayimata wani mayataccen kallo Wanda shi kansa baimasan yanayiba,
Khadija kuwa ganin yatsaya kallontane yasa tayi tunanin kamar kara hassala yayi hakan yasa tasake mararaice fuska tareda yin kneeldown agabansa ita kanta batasan ta bankaro kirjintaba sakamakon Dora hannunta datayi akanta yasa ta bankaro kirjinta sosai gabansa idanunta sun fara kawo ruwa alamar zatayi kuka take cewa cikin narkakkiyar muryar shagwaba,
"Kaji yaya pls"
Wani uban tsalle bananar Dr zayyad tayi tareda dawowa mazauninta tazauna,
Gabaki daya jin bananarsa yayi tacika gajeren wandonsa sai uban nishi takeyi da kokarin fasamasa wando tayo waje,
Idanunsane suka kada sukayi jawur tini jarabarsa ta motsa,
Gabaki daya jin yake kamar yakamo yarinyar yarungimeta,
Sallamar yaya al'ameen CE tadawo da Dr zayyad daga duniyar dayake cikin amma fa Har yanzu a feeling din dayakeji babu abinda yaragu,
Basarwa yayi tareda amsa sallamar Dan uwannasa tareda Dan sakar masa murmushi aiya fuska danbaikai koda cikin ransaba bare zuciya kasancewar azahiri dakuma badini wata dankararriyar shawar yarinyar ke tasomasa,
Shima yaya al'ammen din bawani zama yayiba atsaitsaye auka gaisa kasancewar yanzu haka daga gurin aiki yake jikin ammine yakawoshi zai dubata kuma Yakoma baking aiki,
Bayan sun gaisa yadubi khadija tareda cewa "yadai sarkin laifi,hala kinyi abinda kika sabane"
Kamar kuwa jira take tace,
"Wllhy babu abinda nayimasa fa kawai Dan nakicin abincine kuma wllhy nakoshi"
Tunda yafara maganarta yaya zayyad yadauke kansa daga gareta kwata2,
Hakan yasaka yaya al'ameen ma yayi murmushi tareda cewa,
"Tokici mana aizai hakura inkinci"
Kumburo baki takarayi tareda cewa cikin shagwaba,
"Kaima dai yaya wllhy fa nakoshi"
Tuni aminatu takai makurar karshe abacin rai duk danne kwallar datake hakan bao hanasu ambaliya akan duskartaba sai dai takan danyi kokarin gogesu batareda kowwa ya fahimtaba,
"Yaya al'ameen sannu da zuwa andawo lpy"
Aminatu tafada tanadan sadda kanta kasa,
Sai yanzu yaya al'ameen ya lura da aminatun cikin sakin fuska

Please Login or Register in order to submit comment