Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Batareda wani lura da jinin da yake fita ba khadija tabita ta danne ta fara dukanta ta ko ina,
Duk da bawai khadija tafi ƙarfin fareeda bane amma tariga tayimata dabaibayin da bazata taɓa iya mirginawaba gakuma azabar da kanta yakemata na daku dayayi ya fashe,
Da ƙarfi zayyad ya finciko khadija daga jikin fareeda amma innna ta riga da ta manne ajikin fareedan sai da yayi dagaske kafin ya fincikota ta faɗo jikinsa,
Fisge fisgwn datakeyi sai ta koma jikin fareeda yasa Dr zayyad ɗaga hannunsa ya kwaɗa mata mari,
jin azaba dakuma raɗaɗin saular marin yasaka khadija wawurar hannun yaya zayyad tareda danna masa wani mahaukacin cizon dayasakashi saurin tureta daga jikinsa,
Aikuwa a fusace tasakeyin kan fareeda datake kwance jini na zuba daga goshinta da bakinta,
Shima zayyad a fusace yasakeyin kan khadijar tareda rarumota ya matseta a ƙirjinsa,
Kolowar dasukeyine yasak maɓallin rigar zayyad ɗin buɗewa wanda hakan yabayyyana shatin lafiyayyen ƙirjinsa ta inda babu best ɗin,
Aikuwa khadija ta sake daidaita tsakiyar lafiyayyun gashin dasuke baje a ƙirjinsa ta sake manna masa wani cizon tareda jan gashin ƙirjinnasa da ƙarfi,
bai san sadda yasaki ƙara ba tareda turata baya da ƙarfi ta faɗi,
ya zuwa yanzu khadija ta tabbatarda sosai ran yaya zayyad ɗin yaɓaci kuɓa muddin tabari ya damƙeta zai iya yimata lomai ma a gaban ballagazar karuwarsa dan haka a guje tamiƙe tareda banka ƙofar office ɗinsa ta ahige tareda maidawa ta rufe,
A fusace zayyad ya biyo khadijan amma ganin ta rufe yasa yakoma kan fareeda dan bata taimakon gaggawar jininda yake fita daga kanta,
Wata nurse ce tashigo kiran dr kasancewar anata jiransa amma ganin halinda fareeda take ciki yasata ruɗewa cikin sauri ta nufeta,
sosai shima ƙirjinsa ke masa azaba amma ganin nurse ɗinnan yasakashi daurewa tareda bata umarnin taimaka fareeda da tretment shi kuma ya juya yasakawa ofgice ɗinsa mukulli ya rife khadija tareda wucewa gurin yiwa patiente ɗinsa aiki,
To a ɓangaren merry kuwa tana can zaune tanata chat ɗinta abinta a zuciyarta tana ayyana irin wulaƙancin dazata ga iyayen zayyad ɗin sunyowa fareeda,
Ganin shirun ya fara yawane takumasan da ace ansamu yadda takeson da tuni ƴan uwan zayyad sunyo fatali da farreda ne yasata ɗaukar wayarta ta kira wata nmb,
Bugu biyu aka ɗaga tareda cewa,
"ranki ya daɗe"
Itama ba tareda damuwa da rashin sallama ko amsawa ba tace,
"yawwa,wai meke faruwa acikin asibitinnanne"
"kinga ɗaxu rashin katin kirane yasa ban faɗamiki ba anfa sallami ƴan uwan oga dan tun ƙarfe ukky ma suka tafi,
Cikin zafin nama ta miƙe daga kwancoyar datake a jikin kujerar mota tareda cewa cikin faɗa,
"gsky banga amfanin biyanka danake ba inbanda rainin hankalo da rashin mutunci nizaka yiwa haka,watakam ma yaudarata kakeyi kenan dama a banza nake biyankane dazaka ringa faɗamin wai bakada kati,"
Sosai take zuba riean masifa kafin cikin tashin hankali ta kashe wayar tareda neman lambar fareeda,
dolene tasan ko a wanne hali ake cikin dan kuwa zata iyayin koma meye muddin akan soyayyar zayyad ne,
Bata burin yin tozali da wani farincikin tsakanin zayyad da wata macema bare kuma fareedar,
jin ringing ɗin wayar fareedar a kusa da itane yasata sake jin wani mugun haushi,
A fusace ta ɓalle murfin motar tareda fitowwa cikin eani yanayi mai wuyar fassara,
Sai dai kuma wani tunani daya ɗarso mata a zucoya wanda uasakata saurin komawa cikin motar kamar mahaukaciya tasake rarumo wayarta tareda sake nemo lambar mutumin dasukayi waya dashi a ɗazu,
Bugu biyu wayar tayi aka ɗaga daga can ɓangaren amma saidai wanda aka kira ɗinne yana amsa wata wayar hakan yasa ta katse wayar tareda sake kiran nmbr fareedar,
Sake jin ring ɗin wayar datayi akusa da ita ne yasaka sake ƙumewa da wani mugun haushi, ko kafinkitan ya tsinke ta katseshi cikin gaggawa tareda sake maida kiran kan nmbr ɗazu,
Har yanzu dai ana amsa kura da wayar acewar batiriyar da take saita naurar kiran,
Da ƙarfi ta willar da wayar tareda ɗora kanta akan stiaring motar zuciyarta ce kemata wani irin tafarfasa,
ring ɗin da wayarta ne da taji yasakata ɗaga kanta da sauri tareda wawuro wayarta batareda ta tsaya dubawa ba ta ɗauka ko sallama babu ta fara magana,
"wai yazanta kiranka amma kaƙi ɗaga wayata iro nifa gsky nafara saka maka ayar tambaya da zargi akan lamarin ka da ba haka kakeminba,"
"yanzu dai yakamata ki ajiye duk wannan kifara faɗamin dalilin kiranki kafinnan sai kiyi faɗan hajiyata"
Daga ɗayan ɓangaren aka faɗa cikin raha kafin aka cigaba da cewa,
"batun kuma kisaka ayar tambaya akaina ko kice kinfara zargina ai bai tasoba saboda dani dake gabaki ɗayanmu babu mai gaskiya dan haka aiki nakeyimiki kinabiyana bawai iko kike daniba"
Sanin halin wanda take wayar dashine yasata sauko da murya a hankali kafin tafara magana cikin sigar lallashi,
"pls iro rainane a ɗan ɓace amma kayi haƙuri,yanzu dai dan allah inason sanin halin da ake ciki a cikin asibitin tsakanin fareeda da zayyad saboda yanzu tashiga kuma banji sakamakon danaso jiba,"
Ɗan taɓe baki yayi kafin yacemata,
"badamuwa yadda kikace"
D a sauri tace,
"yawwa iro na gode"
Kafin ta sauke wayar da wata ajiyar zuciya mai nuna tsabar rashin jin daɗin yanayi,
A ɓangaren wanda ka kirawo da iro kuwa koda merry ta kashe wayar sainaga yavigaba da magana batareda yasaukeba,
Sai dai kuma abinda yayi matuƙar bani mamaki shine,
Yanayin maganarsa zai tabbatar maka ba da merry yake magana ba saboda yana magana ne da girmamawa..........ƳAR MUTAN MURAYE CE GARKUWAR MITANEN DAURA ALHERI MUTANEN MASHI,
INA MIƘA GAISUWA GA KAFATANIN ƳAN 2014 CANDY DATE MUSAMMAN MASHI DA SHARGALLE
32&33

cikin wayar da iro yakeyine aka ɗanyi wani murmushi tare ɗan jan iska kafin akace,
"ba damuwa malam iro nagode za ka iya zuwa kayi aikinka"
"badamuwa hajiya"
Ya faɗa kafin yakashe kiran tareda yin hanyar dazata sadashi da cikin asibitin,
A ɓangaren merry kuwa ana ɗaukarta aka nufi wani ɗan madaidaicin ɗaki da ita dan gyara mata ciwon dayake jikinta,
Shima zayyad ɓangaren aikinsa ya nufa,
Dan haka har aka gamawa fareeda treatment bai zo ba yana gurin aikinsa,
to itama dai fareedan bata tsaya jiransa ba dan ana gamawa ta kwaso takalmanta a hannu ta nufo hanyar fitowwa,
A daidai bakin ƙofa sukayi kiciɓis da iro wanda yadaɗe da sanin fareeda amma ita bata sanshiba,
Sai dai ganinta da wannan uwar flaster yayi matuƙar bashi mamaki,
Amma dayake shima ya iya kanshi sai atake ya ɓoye mamakinsa tareda cewa,
"sannu baiwar allah"
A hankali ta ɗan ɗaga laɓɓanta da yanayinta zai tabbatar maka kawai tana dauriyane,
"yawwa nagode"
Kawai tafaɗa tareda yin gaba tabarshi a tsaye,
da sauri iro yajawo wayarsa tareda latso layin merry,
Ai kuwa bugu ɗaya ta ɗaga taredayin saurin cewa,
"lafiya dai iro?"
"gata nan ta taho,saidai fa naganta da flaster a goshinta da alama dai wani abu yana faruwa,
Wani ƙasaitaccen murmushin mugunta merry tasaaki,
Duk da dai batasan waye yayiwa fareeda hakan ba amma dai hakan yayimata daɗi sosai,ganin fareedar na tahowwa yasatayi saurin cewa Iro,"ok badamuwa sai munyi waya"tunkafinma ta kashe wayar iron yarigata yin sairin kashewa tareda sake latso wata nmbr da bana ko tantama matar ɗazunce,itama dai bugu biyu ta ɗaga da sallama abakinta kafin iron ya amsa mata tareda fara koro mata bayani,
"ranki yadaɗe yanzu haka daga cikin asibitin nake kiranki kuma naga budurwar zayyad tafito amma fa da alamun anyi mata dukan tsiya sai dai fa bansan wanda yakeda alhakin yin hakan ba,nadai ganta anyimata drasiing na ciwukan fuskarta,"
A hankali me maganar tace," badamuwa iro ni nasan wanda yayi mata amma inason ka bincika min ko zakaga khadija acikin asibitin,dan inada tabbacin khadija ce kaɗai zata iyayin wannan aikin itama saidai inko yarinyar ce tayimata wani abu dan nasan halinta sosai"
to ranki yadaɗe, sai dai fa amma bansan lhadija ba,"
"kanuɗe wayarka yanzu inturo maka hotonta"
"Ok"
A can ɓangaren khadija kuwa tun tana risgar kuka a takure a jikin kujera har ta gaji ta malale akan tiles ɗin office ɗin tanata shaɓaɓa baccinta da yake tafe da ajiyar zuciya tsabar kukan datasha,
To shima dai dr zayyad haka yayi aikin yagama bawani kuzari a tattaredashi saidai abinka da wanda ya ƴeare ta wannan fannin ansamu sa'ar aikin sosai inda akayi lafiya aka kuma gama lafya,
tunda fareeda ta doshi motar merry ke ƙuramata ido da kallon mugunta saida ya matso sosai kafimn cikin duniyaci merry ta buɗe motar akiɗime tareda kallonta cikin mamaki tace,
"Subahanallahi! sannu ƙawa yadai? meyasa meki haka?"
Har cikin rai fareeda najin daɗin yadda merry ke nuna kulawarta amma duk da haka bazata fasa aniyarta na watsar da ƙawancennan nasuba dazaran tasamu zayyad ɗinta a hannunta dan tasha alwashin ko a bikinsu ƴan uwan zayyad bazasuga mery a matsayin ƙawartaba barema suyi mata wani kallon ƴar iska,
ta ɓotan da merry tayine yasata saurin dawowa hankalinta,
"ƙawata ko zayyad ɗinne yayimiki haka?"
A hankali tace,
"Haba dai merry zayyad da dukana kuma!
wllhy wata mahaukaciyar yarinyace ni ina tunanin ko sonshi take ma amma ni banga menayimataba"
Da sauri merry ta karɓe zancen dacewa, "kodai ƴar uwarsa ce"
"Gsky bana wannan tunanin dan banga wata alama ta hakanba"
"to yanzu haka zamu ƙyale wannan maganar tadakeki amma ba wani mataki"
"Hmmm merry kenan kina tunanin zayyad zai ƙyaletane bayan kuma yasan metayimin? tunima yacilla ta office ɗinsa ya kulleta inaga dai saiya gama aikinsa zai eaiwayi matakin dazai ɗauka dannaga shima yana cikin shirin aikine"
Sosai merry take ƙoƙarin gaɗiye baƙin cikinta da duniyancin tausayin fareedar kafin tace,
"Shikenan amma dai gsky naso ace mu muka ɗauki mataki dakanmu"
" Badamuwa merry na yadda da zayyad a yadda yakesona bazai taɓa batin wani ya takaniba"
Wani sakaran kallo merry tayiwa fareedar tareda faɗawa motat a zuciyarta kuma tace,
"sha'sha'sha kawai"
itama fareeda motar tashiga ta zauna da ƙyar alamun jikinta yafara tsami,
Sai kusan magarib kafin zayyad yanufi office ɗinsa a gaggauce har yanzu zuciyarsa na riƙe da abinda yafaru,
mukulli yasaka ya buɗe office ɗin a hankali ya tura yashiga,
Sosai yayi mamakin yadda yaga yariyar kwance akan tiles tanata shirga bacci kamar babu abinda yadameta,
jɓtsayiwa yayi a kanta yana ƙaremata kallo duk da bawai sosai yake iya ganin fuskartaba,
Sai dai kuma jin yadda take sauke numfashin wahala da wata shahhekar kuka yasan da alama bataji daɗin kwanciyarba ga kuma yadda gabaki ɗaya tabi ta duƴunƙune jikinta acikin hijabi,
A hankali yakai hannunsa ya fara janye cukui kuyen datayiwa fuskarta,
da dabara yasamu gyara mata hijabin tareda ƙurawa kyakkyawar fuskarta idanu,
A karo na farko daya nutsu da kallon tsarin fuskar mutum da tsanfsar kyau,
A gsky kyawun halittar fuska baifiya birgeshiba kamar yadda kyawun tsarin jiki ke ɗaukar masa hankali,
Sai dai a yau karon farko yaji kyawun fuska ta birgeshi yakuma ɗauki hankalinsa sosai fiyeda yadda kyaeun jikin da tsarin halitta kan ɗauki hankalinsa,
har yau yakasa gaskata abinda zuciyarsa keyimasa a lokuta da dama na shekaru masu tarin yawa,
Dyk da yasan zuciyarsa akan daidai take amma bazai taɓa gaskata ta ba koda yasan abinda take buƙata baitaɓa zama haramun agaretaba amma shi yana ɗaukar abin a matsayin ƙasƙantar da kai,
duk yana zntukannan da zuciyarsa ne yayinda yake ƙurawa fuskar khadijan idanu datayi fayau da zanen shatin ruwan hawaye akan ta,
Shi kansa ya tabbatarwa kansa khadija kyakkywace sannan kuma tanada diri mai ɗaukar hankali fiyeda tunaninsa,
A hankali yakai hannunsa daidai saitin jajayen labbanta tareda ɗora yatsansa,
taishin dayajine yasakashi lumshe idanunsa tareda sake ƙoƙarin murzawa,
A hankali laɓɓan suka fara motsi da alamun a ddu'a takeyi ,
Ko kafin ya ankara ta buɗe dara'daran idanunta fess akanshi,
Firgigit ta miƙe tareda fara ja da baya cikin alamun tsoro,
shi kuwa zayyda idan ka klleshi zaka iya rantsewa bashi bane yanzu yagama susuta akan kallon fuskarta ya wani haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba,
ƙara gyara tsayuwarsa yayi tareda harɗe hannuwansa akan ƙitjinsa yacigaba da ƙureta da mayun idanunsa,
A zhiri fuskar zayyad zaka iya rantsuea mummunan fushine akanta da kuma ysabar tsanar khadijan,
Sai dai kuma a baɗini wani yanayine daya ɗauki dogon lokaci yana masa yawo da gizo yake daɗa ninkuwa acikin zuciyar tasa ,
Ya nada tabbacin abinda yarinyar tayimasa zai sakamasa tsanarta,to amma meyasa kome takeyimasa bayajin wannan tsanar saina wani yanayi daya kanji wanda yake namijin ƙoƙari wajen dannesa,
tuno yadda sukayi ɗazu yasa wani ƙayataccen murmushi ya kusan suɓucemasa,
amma yayi wata muguwar dakiyar hana murmushin fallasa asirinsa tareda sake murtuke fiskarsa,
A hankali yafara takowwa yazuwa inda take,
A kiɗime ta fara bashi haƙuri cikin zazzaƙar muryarta tareda buɗe baki da niyyar zunduma masa ihu,
da sauri ya ɗaura yatsansa alan laɓɓansa tareda yimata shhhhhhiiiiiiii,
Aikuwa a take ta rufe bakinta da tafukan hannayenta dasuke ɗauke da maroon ɗin ƙunshi tareda haɗoye kukanta,
Saida yazo dab da ita har numfashinsu na bigun juna kafin ya ɗauki hanninsa ya ɗaura kan bango dayake yafita tsayi sai yayimata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa,
Sun ɗauki dogon lokaci ahakan kafin a hankali ya buɗe bakinsa cikin wata murya mai wuyar fasaarawa yace,
"khadijar"
D a ƙarfi amon ya daki dodon kunnenta,batamasan sadda ta haɗiye wani arnen yawuba tareda jin wani rugugin duka da ƙirjinta yayi,
A karon farko a duniya taji yaya zayyad ya kira sunanta,kiranda tunda aka haifita babu kiran data taɓaji sama da wanda yayimata a yau,
Dama haka yaya zayyad ya iya kiran sunanta? zata iya rantsuwa a duniya babu wanda ya iya kiran sunan sama da yaya zayyad ɗin,
hmmm dama haka ya iya kiran sunanta amma ahine dan baƙar mugunta bazai iya kiranta dashiba sai dai ya ringa cemata wani ke kamar ɗiyarsa ta fari,
nannauyar ajiyar zuciyar dayasaki mai tafe da iska ce ta mai dota cikin hayyacinta,
Aikuwa a razane ta ɗago idanunta,karaf suka faɗa cikinnashi kamar anyimusu trasfer zayyad yaji wani abu yafito daga idanun khadijar batareda ya ankaraba yashige cikinnasa idanun,
Lumshesu yayi a hankali tareda buɗewa,
Wani yanayi yaji mai kamada an karyamasa gabaki ɗaya garkuwar jikinsa,
A hankali yasauke hannunsa tareda jan ƙafafunsa baya a hankali gabaki ɗaya ki yake kamar anyimasa duka,
Cikin takunsa maikamada na maiyin sanɗa yaja ƙafafunsa tareda ɗaga laɓɓansa a hankali yace,
"muje gida"
yanajin lokacinda ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tareda cewa masha allahu,
bai wani ysaya saurarentaba kawai wayarsa ya ɗauka da laptop sai mukulli,
Ganin yadda jikinsa yayi sanyi sai kuma khadijan taji duk aba daɗi koba komai dai ɗan uwantane kuma sai takeji ajikinta kamar ya muzanta,hakan datajine yasata saurin kai hannunta ta karɓi jakar laptop ɗinsa daga hannunsa,
jin ta kama jakar yasan nufinta tunda ya tabbatar itaɗin tarbiyyar ammi ce hakan yasa ya sakarmata tareda miƙa mata wayarsa,
kallonsa ta ɗanyi kafin ta karɓa
A hankali ta taɓe bakinta a ranta tace,
"mugu dai bazai taɓa canzawa ba, watakam ga par dako?,
Ganin ya fita yasata fitowwa da sauri shima ya rufe office ɗin suka nufi parking space.................ƳAR MUTAN MURAYE GARKUWAR MUTANEN DAURA ALHERIN MUTANEN MASHI,😎😝😜RAƁA DANNIN MUTAN KANO34&35


A can gidan kuwa tunda akan sallami su ammi aka koma gida gabaki ɗaya gidan ya hargitse da murnar dawowar ammi daga asibiti,
to dayake da yamma ne yaran gidan na kowwa yana gida haka aka haɗu a parta ɗin ammi anata hira da yimata sannu,
Koda ciwon ammi yakasance na marasaa son hayaniya amma tanajin daɗin kulawar da ƴan gidan ke bata,
Musamman ma yanzu da aka haɗu a part ɗunta anata shan hira hadasu hajjaju,
Ana tsaka da hirarne ma ƴan ɗanbatta suka zo haba nan fa aka shiga hira dayake gabaki ɗayansu sukazo aunty shamsiyya yaya shms yaya faisal dakuma noor,
Tunda sukazo yaya shams yake neamn par uwarsa watam khadija dan a zahirin gaskiya kowa yasan shaƴuwarsa da khadijar dakuma shirin daauke yi sosai,
Dan yaya shams mutum ne lan gayu mai kuma taƙama da aji da gayunsa,
To itama gogan taku aminatu dai tun ɗazu take baza idanu dakuma tambayar inda khadijan ta tafi duk da dai su ƴan gidan sun zata har yazuwa wannan lokacin tana makaranta,
Amma ganin har yamma tayi sosai sai aka fara tunani kota wuce aaibitinne kasancewar babu waya a hannunta,
sosai hankalin aminatu yasake tashi jin ance khadija na tareda yaya zayyad tuni wata mugiwar tsanar khadijan tasake baibaye zuciyar aminatun gsky dolene ta nunawa khadijar kuskurenta kida kuwa hakan zai kasancewa silar watsa duk wata kyakkyawar alaƴa dake cikin a halin dolene zata mallaki burin zuciyarta watau yaya zayyad,
Ganin anata jajanta shirun khadijar yasa aunty maimuna ɗaukar wayarta ta kira yaya zayyad wanda a lokacin fitowwarsa kenan daga aikin tiater dayayi,
ganun wadda ke kiransa yasa ya ɗauka cikin ɗan sakin fuska ya amsa sallamarta kafin ta fara magana,
"zayyad wai dama ko khadija ta zo nan asibitinne dan ba waya a hannunta kuma batasan ansallami ammi ba gashi har yanzu kusan magrib bata dawoba"
Sai da takai ƙarshen maganarta har ta ɗauka ma bazai yi maganaba kokuma layin ya tsinke kafin can taji ya fara magana,
"kayyy auntynmu gsky ki ringa ragewa mana,haba tunda kika ɗauko zance kin ƙi saukew,ok ni baku damu daniba tun jiya bana gida amma yanzu kun kirani saboda wannan farfeluwar yarinyar ko?"
a hankali aunty maimuna ta saki wani tattausan murmushi wanda yake daidai da saukar mashi ko takobi a ƙahon zuciyar mama dakuma aminatu kafin taci gaba da cewa,
"haba babban yaya aikai uba ne kuma ƙaton tuzuru kaga kuwa bakada wanda zai nemeka"
"hmmmm aunty kenan,ok tunda gaka ne itama wadda kike nema ai batada aure kinga kenan kinyi sonkai"
"Dr zayyad kenan ko dai khadija batada aure ai natabbatar tanada wanda zai haukace da nemanta muddin kuwa akace ta ɓata ƙilama daga ranar yadaina cin abinci"
"to indai hakanne nima ai inada budurwa,"
"hmmmn ai budurwa ba dahir bace"
"kinga kenan itama saurayi ba dahir bane dan haka one'one"
"Hmmn to kasani ita ko ba saurayine zai nemetaba?"
Aunty maimuna tayi wannan furucin cikin comfidence ɗinta kafin yaya zayyad ma cikin ƙardin gwiwarsa yace,
"to waye zai nemeta faɗamin aunty"
"kaine!"
lafazin daya daki zuciyoyi da dama musamman daya kasance gabaki ɗaya falon kowwa hankalinsa da sauraronsa yana kan aunty maimunar da muhawarar ta da yaya zayyad ɗin,
"ni kuma!"
"ƙwarai kuwa kaine zayyad!"
Auntyn tafaɗa da ƙwarin gwiwa kafin ta cigaba da cewa,
"ka manta babban wa uba!kaga kenan idan khadija ta ɓata sai kafi kowwz shiga tashin hankali shin kagayamin kai wanene yayanka?"
zukata da dama sun sauke ajiyar zuciya sai dai kuma kowwa da inda tashi ta dosa musamman mama da aminatu sai kuma yaya zayyad kafin yacigaba da cewa,
"wallahi aunty maimuna bakida dama,toshikenan tunda banada yaya idan naɓata ai zakifi kowa jin jiki musamman ma ace mutuwa nayi"
"gsky kam zanfi kowwa amma bazanfi khadija ba saboda ita tarasa jigo"
ƙit ta katse wayar tabarshi da waya a hannunsa wanda sai da ya daɗe yana juyata kafin yanufi office,
Itama aunty maimuna tana sauke wayar ta kallesu da murmushi kafin tace,
" ba damuwa tana tareda yaya zayyad"
jin kiran sallar magrib yasa suka fara tashi dan sauke faralinta akan lokaci,


a hankali suke tafiya har suka ƙarasa bakin motar yaya zayyad,
ɓangaren driver yazauna wanda sanin halinsa yasa ita ma ta buɗe mangaren mai zaman banza ta zauna,
sai da tayi addu'a kafin yayiwa motar key ya daidaita ya fara tafiya a hankali kamar wanda akayiwa duka,
Sunyi nisa sosai da tafiya amma motar ta ɗauki shiru kowwa da abinda yake ayyanawa acikin zuciyarsa,
Musamman ma yaya zayyad dayakejin wani yanayi mai wuyar fasaarawa,dan bazai taɓa cewa acikin farinciki yake ko baƙin ciki ba,
S hankali yakai hannunsa

Please Login or Register in order to submit comment