Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raini dakuma disgi uwa uba kuma halayensa da kwata kwata basuyimata ba,mutum sai shegiyar masifa,
"mtsssss"
Ta ja wani mugin tsaki a zuciyarta,itafa anacewa mace tana canza namiji amma ita kanta tasan duk wadda ta auri yaya zayyad wahala kawai zatasha dan bazata taɓa iya canzaahiba,musamman na ace su samu wadda taje mutuwar sonsu kamar aminatu,
tabbb ai wllhy zatasha wahala,hakan yasa ma yanzu dazaran lokacin dawowarsa ya yi take barmusu part ɗin ta nufi part ɗin aunty maimuna,

ƳAR MUTAN MURAYECE ALHERIN MUTANEN DAURA GARKUWAR MUTANEN MASHI😃😄😛😝😛RAƁA DANNIN MUTANEN KANO*DR ZAYYAD*
*38&39*

*NA*
*HAJARA MURAYE*
( *MRS AMINULLAHY)*


*SADAUKARWAR*
*TEAM KHADIJA*




kamar dai yau data kama alhamis kuma yakasance da yawan ƴan matan gidan basa makaranta hakan yasa yau ma khadija tunda ta tashi bata komaba ta fara gyara ɗakinta kamar ko wanne lokaci ta wanke bayi kafin ta nufi babban falon hajiya,
kasancewar jiya ansha fira sosai an ɗan ɓaɓɓata falon dayawa yasa taɗanji ranta babu daɗi amma dayake tasan dolene a kanta yasa ta fara aikin tanayi tana mita,
ta gama tattare komai zata fara shara hajjaju ta fito daga ɗakinta da tarin yar kwalemar maganungunan gargajiyarta datayi na cover,
kasancewar fakan sharar yacika tsautsayi yasa hajiya zubarda ɓurɓushin magani akan kafet dake tsakiyar falon wsnda khadijan ke niyyar duƙawa ta nannaɗe kafin ta fara sharar,
har ta buɗa baki da niyyar gaisheda hajiyar amma ganin hakan yasata canza akalar maganar tat cikin ɗan faɗa,
"Gsky hajiya bakya kyautawa abinda kikeyi,yanzu fisabilillahi bayan ɓata falonnan dakukayi jiya duk bai ishekiba saikin haɗa da zubarda shara da gangan haba hajiya kamar dai ba'a tausayina,"
Ta idashe maganar da shagwaɓa,
Tunda ta fara maganar hajiya tayi sararo tana kallonrta har sai da takai aya kafin hajiyar ta yi mata wani kallon tsaf tareda kama haɓa ta fara magana,
"ohhhh ba shakka wata kam gani sarkin ƙazamai ko? lallai hadiza wllhy kinsamu ƴanci,watakam dan kinga kwana biyu na hana zaidu akanki shine zaki fara tatamin ruwan fetsara ko?"
"Ni wllhy hajiya lamarinki na bani mamaki kamar bake bace kikace indai kincika ke lika haifi ubana bazaki sake kiran suna na ba amma wai abin mamaki kin kasa cikawa,"
Khadijar ta faɗa tana ɗan taɓe baki kafin taci gaba,
Ko danma akan mema zan ta wannan haƙilon bayan na tabbatar wllhy hakiya ko rayukan mutum goma aka baki mudfin kikayi minti goma bakijini ba ko bali kira ni da wannan ruɓaɓɓen sunan ba wllhy sai kin mutu"
Itama hajiyar a rene ta yi tafi tareda yin ƴar shewa tace,
" yau naga masifa ni rabi!"
"yo wai ke nan hadiza ji kike inba ke bazan iya rayuwa ba kome?"
"hmmm hajiya kenan,to ai wllhy va takaran ni ba ko suna aka canzamin sai kin ida margayawa,"
Da azama hajiya tasake gyara tsayuwarta kafin tace,
"yo wai hadiza bangabe ma'anar idawa ba yanzun kina nufin kice ni saura ce?"
Wata iriyar daeiya khadija tayi da saida ta kaita ga duƴawa,sai da tayi mai isarta kafin tace,
"hmmm gajiya kenan,to keda kina nufin rayuwarki mai tsayice,uhmmm tabbb!aikuwa wllhy ki canza dan kuwa mun kusa shan gumbar ki dan kin kusabin tsohon mijinki,"
"hmmm Allah sarki hadiza!aikuwa duk ranar da na muru na tabbatar sai kinfi kowa yin kuka hakan yasama nake roƙon allah yasa na yi tsawon ran gani na aurar dake ga wanda zai lallasheki ko bayan mutuwata"
I tama khadija murmushi tayi tareda zama kusada hajiya hannunta ɗauke da tsintsiyar data gama tattara shara ta ɗaura kanta a gefen kafaɗar hajiya tareda cewa,
Ai insha allahu ma hajiya bazaki mutu ba muna nan tareda ke masoyiyata,
Wani ɗan murmushi hajiya tayi mai kamada yaro yarone tareda cewa,
"Allah ya shirya minke hadizata"
"Yawwa hajiya in tambayeki mana?
"Allah yasa na sani"
"Wai meyasa bazaki iya kirana da khadija kamar kowwa ba? wllhy banason hadizar nan sunanfa tsaffine"
"To zan koya insha allahu,yanzu dai kije kigama kitafi ki taya ummanju aikinta,"
miƙewa tayi ta nufi hanyar fita ta zibar dasharar kafin ta kwashe tasake zubarwa ta hau moping,
A haka suna ta fira da hajjaju har ta gama duk abinda zatayi kafin ta koma ɗakinta tayi wanka tareda turare jikinta da turaren garwashi kafin ta shirya jikinta cikin wata atamfa mai kyau datasha ɗinkindoguwar riga,
Rigar sakakkiya ce sosai dan gaka bata wani kamata ba kokaɗan sai dai tayi mata kyau sosai,
Gashinta ta taje tarda kamashi ta ɗaureshi can ƙasa sosai kafin ta murza ɗaurin daya fito mata da gashin,
Gsky ko ita kanta tasan tayi kyau dan sosai takeson faranta ran amminta,
Plate shoes ta saka wanda yayi daidai da kayanta tareda da ɗaukar turare tasake shafe jikinta gaba ɗaya,
Aikuwa a take ta fara saki wani fitinannen ƙamshi,
Ganin babu hajiya a falo yasa ta ɗan leƙa ɗakin hajiyar saidai jin alamar motsin ruwa a banɗakin ya tabbatar mata fa cewar wanka take,
Hakan yada bata wani tsaya jirantaba ta fice rɓta nufi ɓangaren umma,
A hanya ta ga aminatu da fateema aikuwa cikin fara'a da sakin fuska ta tarbeau yareda dafa kafaɗar aminatun taba cewa fateema,
" Dama yanzu zanje gurinku mu tafi part lin aunty maimuna musha fira,amma tunda yanzu gaku mu ƙarasa ku rakani ingaisheda su umma da su mama,"
Kawai gani tayi aminatu tayimata kallon banza tarrda ture hannunta a fisace ta kalki fateema,
"dallah fateema kizo muje inkuma bazakijeba ni inyi tafiyata"
Aminatu ta faɗa tana balbale khadija da harara,
cikin sanyi fateema tace,
"haba aminatu bai dace ba gaskiya abinda kikeyi,yakamata ace idan wani abu khadija tayi miki kisanar da ita bawai kiyi mata haka ba"
da tsabar fushinita aminatun tasake hayayyaƙowa,
"bazan sanarba fateema!inhar bazaki tahoba ni kinga tafiyata"
Ta faɗa tanayin gaba,
A wani mugun fusace khadija ta jawo aminatu baya tareda turata baya da ƙarfi tayi taga'taga zata faɗi Allah yasa tayi tsaye,
Cikin tsabar ɓacin rai da masifa ta fara magana,
"ke kin isa ki faɗamin kuma ki tafi ban mayar miki ba,wllhy ko haihuwarki ba'a yiba,kuma daki faɗi abinda nayimiki da karki faɗa uwar ubansu ɗaya!matsalarkice ke tashafa,sgashasha kawai,"
Tana ƴarasa maganarta ta balbalesu da harara gabaki ɗayansu tagi gaba,
Itama aminatun gaba tayi abinta dan kiwa tasan halin khadija,
A tsaye suka bar fateema sororo tana nazari kafin ta sauke gwauron numfashi ta nufi part ɗi aunty maimuna,
Tunawa da nasihar ammi yasa ta tsaya bakin ƙofa ta daidaita fuskarta daga fushi kafin tashiga cikin part ɗin da sallama,
Umma babba ce kaɗai a falon hakan yasa ta nufi kusa da ita ta zauna tareda ɗan jingina da jikinta kafin tace ,
"umma ina kwana"
Cikin so da ƙauna da tsantsar jin daɗin data rasa dalilin da idan taga khadijar take shiga cikinsa,tasake jawota jikinta sosai tareda cewa,
"lafiya ƴalau ɗiyata ya kika tashi"
"lafiya ƙalau ummanah"
Suna haka aunty zainab da aunty ruƙayya suka shigo daga ɗakinsu,
Suma zama sukayi aunty ruƙayya na tsokanar umma tanacewa,
"watakam umma ananiƙar ki tazo shine zaki watsaddamu ko"
Cikin fara'a umma take cewa' "eh kuma kubari taku uwar tazo"
"ai wllhy umma basai tazoba myma yaji zamuyi mukoma gurinta"
A haka dai akayita raha kafin khadijan ta tashi tafito,
Haushin aminatu ne yasa taƙi shiga part ɗinsu dan a tunani ta ko zata gamu da itane,
Da sallama tashiga part ɗon ammi,
Kamar yadda tayi tunani a falo ta sameta a zaune cikin shiga ta kamala,
Sidai kuma da ka kalli fudkarta zaka san tana cikin damuwa,
hakan yasa khadija saurin ƙarasawa kusa da ita tareda tambayarta,
"ammi lafiya naganki a haka"
"Lafiya ƙalau khadija me kika gani"
"ya zakice lafiya ammi bayan na ganki cikin damuwa"
a hankaki ta ɗan ƴaƴalo murmushi kafin tace,
"wllhy kinga wayar yayankuce naketa kira tun safe amma har yanzu najita shiru tana ring bai ɗagaba"
Har ga allah khafija ta zata yaya mamman ammi take nufi hakan yasa tace,
Kuma ai ɗazu da sassafe najishi yana yiwa hajjaju magana,to ammi ke ammi ina kike tunanin yaya mamman zao shiga?"
ta faɗa cikin damuwa,
Ammi cikin sake bayyanar da damuwa tace,
"nifa ba shiba"
"to ammi wa"
"Ok mamman ne kalai yayanku"
Ammin ta faɗa a ɗan tunzure,
Sai lokacin gane tashar da ammin ta nufa,
Kayy gsky ammi da ɗorawa kai take yanzu dama wancan gardin ne yasa hankalinta tashi haka?
lallai kuwa tanada aiki wama yasani ko a wani gidan karuwan ya kwana yasa yaƙi ɗaga wayar,
Da sauri ta furta,
"astagafirullah"
Tunowwa da hadiain ma'aiki SALALLAHU ALAIHI WASALLAM,
ɗan taɓe baki tayi kafin ta miƙe tana cewa ammi,
"naji kamar su fateena a gidan",
tunda ta fara abinta ammi tana kallonta har taɓe bakin datayi hakan yasa tana kai ƙarsgen maganarta ammi tace mata,
"khadija zo nan"
A hankali ta koma ta zauna kusada ammin,
Ammi tasoyiwa khadija faɗa saidai kuma taga kamar lamarin khadija da zayyad bayajin faɗa hakan yasa ta canza akalar faɗan nata zuwa nasiha,
a hankali ta jawo hannuwanta biyu ta riƙe tareda ƴura mata idanu ta fara magana,
"yanzu khadija abinda kikeyi yakamata,shin bbakisan zayyad ɗan uwanki bane,meyasa kike haka,ko sokike a ringa kallonki a marar tarbiyya mai faɗa da yayanta, shifa zayyad ba tsanarki yayi ba halayenkine bayaso kuma dakin bari zakiga kun daidaita yanayimiki kamar kowwa,
Koba komai zayyad ya ɗaukeni tamkar uwa ke maizaisa bazaki ɗaukesa yaya ba,"
sosai ammi tayiwa khadija nasiha kafin tace taje part ɗinsu tagani ko yana nan,
Hrar ga allah jikinta yayi sanyi da nasihar ammi amma ita wllhy batason haɗuwa da yaya zayyad ko kaɗan,sai dai bazata taɓa iya faɗawa ammi tsakaninta dashiba amma taci alwashi yaƙu da abinda takeyimata,
A sanyaye ta miƴe ta nufi ha yar fita,

Yau zayyad ya tashi da wani shegen zazzaɓi da mura wanda hakan yasa ya kasa fitowwa daga ɗakinsa dan gaskiya sosai yakejin zazzaɓin,
A takure yake cikin bargo yanata kyarma,sosai yake kyarmar dan hatta bargon jikinsa ya ɗauki ɗumi ga shi haƙoransa sai kaɗuwa suke,
Duk yadda yaso ya ɗaga hannunsa ya ɗauki wayarsa datake rurin neman taimako ya kasa duk kuwa da kiran dayakeji da ring daban daban amma yakasa ɗauka,
Gashi gabaki ɗaya ƙannensa ya haramta musu shigarmasa ɗaki barema wani yasan bashida lafiya,
MURAYE GIDA😝😛😝MASHI GARINMU
_____________💕💕💕💕💕💕💕💕💕 *DR ZAYYAD*
*40&41*


*MALLAKAR*
*HAJARA MURAYE*
*(MRS AMINULLAH)*


💕💕💕💕💕💕💕💕
*nakune* *TEAM ZAYYAD ** *ina bada** *gaisuea*



__________________tunda khadija ta taho taketa faman kumbura tana cika tana batsewa a haka har ta isa part ɗin yaya zayyad ɗin,
ta daɗe a bakin ƙofa tana shawara da zuciyarta kafin tayi ƙundum balar kutsa kanta cikin part ɗin,
A hankali ta gama ƙarewa babban falon kallo wanda gabaki ɗaya ya hargitsa shi sai kace wanda aka yi wasan tsere acikinsa,
Taɓe bakinta tayi tareda cewa,
"ƙazami kawai"
Da sauri ta ɗan dafe bakinta tareda waigawa gefe da gefe kafin tasaki bakinta tareda yin wani guntun tsaki,
Ganin baya falo yasa ka ta juya da nufin komawa ta faɗawa ammi baya nan,
Har ta fara tafiya sai kuma taɗan fara jiyo sautin nishi kamar na marar lafiya,
Hakan yasata saje kasa kunnenta dan tabbatarea,
Tabbas nishi takeji,to amma waye bashi da lafiya kuma ba'a saniba,
Da sauri ta nufi inda take jiyo sautin tareda ƙara miƙa kunnenta daidai ƙofar ɗakin yaya zayyad,
Tabbas a ɗakinne,but amma yaya zayyad bashi da lafiya shine bazai kira ya faɗa ba kuma ayita kiran wayarsa amma yaƙi ɗagawa,
cabbb ɗin gaskiya mugun halin yaya zayyad sai shi,
Yanzu dan tsabar mugun hali kana a hannun allah amma ciwonma dai ka nuna masa miskilanci,aikuwa zaka gasu dan wllhy inda kace haka zakayi to kana tareda wahala,
Tana kaiwa nan a tunaninta ta taɓe bakinta tareda yin hanyar waje abinta ba tareda ta damu da shiga taga a wanne hali yakeba,
koda ta koma part ɗinsu ta iske ammi a tsaye da waya a hannunta still tana sake kiran yaya zayyad ɗin,
Da sauri ammi tayo wajenta ganinta dawo, ko kafin tayi magana ma ammi ta tareta dacewa,
"baya nan ko khadija!innalillahi!wai ina zayyad ya shigane"
Saroro khadija tayi tana kallon ammi da zuea yanzu har hankalinta ya tashi,
Wai me hakan yake nufi kenan ammi tafison yaya zayyad akanta,
cabbbb aikuwa wllhy ba'a isa ba!tunda hakane kuwa wllhy bazata taɓa faɗawa ammi halinda yaya zayyad yake cikiba gwara ma ya mutu kowwa ya huta da baƙar azabarsa,
D sauri ta ɗan ƴaƙalo murmushi tareda cewa,
"Kayyy ammi ki nutsu mana ni wllhy har tsoro kike bani kin wani damu da shi amma shi dayake baidamu dakeba yama bar wayarsa a ɗaki kinata faman kira,shinefa dana ga kintashi hankalinki na ɗauki wayar tasa nakira yaya fu'ad nake tambayarsa shine yacemin yanzu haka auna tareda yaya zayyad ɗin wayar ya manta a gida, shinefa ma yaya zayyad ɗin yace nacemiki ya manta wayarne amma kiyo haƙuri da wuri ya fita shiyyasa bai shigoba,"
Tunda ta fara maganar ammi ta tsareta da idanu gani alamun kamar batada gaskiya,sai da takai ƙarshen zancenta kafin ta fara ƴan kyafce ƙyafce,
"anya kuwa khadija?"
Gabanta ne yayi wani mummunan faɗuwa,amma dayake tana kan dokin mugunta ne yasa ta dakewa tareda cewa,
"wllhy Allah kuwa ammi da gaske nake"
"Shikenan"
" Ni bansaki rantsuwa ba"
Cewar ammin,
Wata nannauyar ajiyar zuciya khadija ta sauke tareda dafe ƙiji tace,
"waiii allah na godemaka"
Ai kuwa karaf a kunnen ammi,da sauri ta juyo tareda cewa,
"khadija!"
Cikin kiɗima da burcewa da in'ina tace,
"naaaaam ammi"
"menaji kince?!"
"Ammi hamdala fa nayi"
ta faɗa a shagwaɓe,
Sosai ammi ta kasa yadda da maganar lhadija hakan yasa tace,
"wuce kije ki ɗaukomin wayar yayannaku,"
Ƙuuuuuuuuuuuuu,
cikin khadijar yayi wani masifaffen kaɗawa aikuwa ba shiri tajingabanta yayi wani mummunan faɗuwa,
"Ammi in ɗauko wayar"
"yess hakanace!"
Ammi ta faɗa tareda tsare gida da tabbatarwa,
kamar wadda ƙwai ya fashewa haka ta fara tafiya,
A ranta tana,yau na shiga ukku shikenan naga takaina, a haka har ta fice daga falon,
A ƙofar falon ta tsayantana ƴan ƙyafce2,
"yanzu ya zanyi ni khadija,"
T ɗan ɗauki pan mintina kafin dabara ta faɗomata aikuwa da sauri tayi part ɗin hajiya ko waigowwa batayiba,
Sai da ta ganta a falon hajajju kafin ta dafe ƙirjinta tareda sauka wata ajiyar zuciya tace,
"Alhamdulillahi! nasamu na kuɓuta"
"Daga hannunwa"
taji muryar hajiya ta daki dodon kunnenta,
Da sauri ta ware idanunta dan harga allah bata san hajiya na falonba,
Ta tsorata sosai amma ganin hajiyarce yasa ta saki jikinta tareda labartawa hajiyar duk abinda ya faru,
Amma sai ta ɓoye mata cewar ta ji yaya zayyad ɗin ba lafiya, T dai cemata,
"wai ammi ce ta aikwni indubo mata yaya zayyad a ɗakinsa dan kawai ta kirashi bai ɗaga ba,kuma wllhy kindaisan halinshi sarai gajiya innashiga zai iya kasheni shinefa na lame sai da na ɗan jina kafin na dawo naɗan samu ƙarya nayimata dacewar na je sai wayarsa amma nakira yaya fu'ad yacemin suna tare,wai bata yadda ba saina ɗauko mata wayar, nikuma nayo nan,"
"dan allah hajiya kice ina firowwa kika kirani"
"A'a ni wllhy bazaki koyamin ƙaryaba kajimin ja'irar yarinya"
Da sauri khadija ta matso jikin hajiya tareda dafa cinyoyinta,
"haba hajjajuna ai wllhy nasan bazaki taɓa bari wani abu yasameni ba namasan zaki faɗa ko sweet heart"
"Hmmm yaudara dai ba wani abu ba hadiza kin iya ta"
A haka dai khadija ta lallaɓa hajjaju daga nan suka shiga wata hirar abinsu,

________________________________________________
A ɓangaren ammi kuwa tunda khadija ta fita take tantama akan abinda khadijan ta faɗa sai dai kuma bata taɓa kama khadija da laifon ƙarya ba hakan yasata ɗan samu natsuwa da rashin ɗaga wayar zayyad ɗin,
Sai dai kuma gani shiru khadija bata dawoba yasa ta leƴawa ɗakin da su ummy suke suna ta shan hira abinsu,
Ganin babu khadija yasa ammi cewa ummy taje part ɗin yayansu tagano mata ko lafiya ta aiki khadija amma shiru,
Ai tsalam aminatu ta tashi jin an ambaci part ɗin su yaya zayyad dakuma khadija,
ko kafin ummy ta ɓiƙe tuni tayi waje,
Hakan ba ƙaramin mamaki yabawa ummy da fateema harma da ammi ba,
Amma ganin ba fuskar magana a gurin ammin yasasu yin shiru tareda miƙewa dan cika umarnin ammin,
Tuni aminatu ta kama hanyar part ɗinau yaya zayyad dan ko kafin su ummy su fito hatma ta ɓacewa ganinsu,
Koda suka fito babu wanda ya tanka gameda abinda aminatun tayi har suka isa part ɗinsu yaya zayyad,
Da sauri suka ƙarasa cikin ɗakinnasa dan jin yadda aminatu ke fitarda sautin siririn kuka,
To suma ba ƙaramin tayar musu da hankali lamarin yaya zayyad ɗin yayiba dan gabaki ɗayansa ya faɗo daga kan gadonnasa yana kwance shaɓe,shame cikin amai,
Sosai lamarin zai baka mamaki ta yadda gabaki ɗaya ya fita daga hayyacinsa sai numfashin da yake fitarwa da ƙyar,
da gudu ummy da fateema suka fito hankali tashe suka nufi part ɗin ammi,
Koda suka ƙarasa ammin tana tsaye dai still da wayar a hannunta ya zuwa yanzu fa hankalinta yayi gagarumin tashi,
cikin tsabar kiɗima ummy takw cemata,
"ammi yaya zayyad!"
sosai gaban ammi yake faɗuwa da sauri tariƙe ummyn tareda girgizata,
"ummy meyasamu zayyad ɗun!"
Ammi ta faɗa cikin kiɗima,
daƙyar ummy ta iya daidaita kan ta kafin tace cikin haki da ƙaguwa,
Ammi yaya zayyad yanacan kwance cikin amai kamar marar galihu rai a hannun allah"
Ko kafin ta kai ƙarshema tuni ammi tayi hanyar part ɗin yaya zayyad ɗin aguje,
kamar wasu taɓaɓɓu haka suka sake kwasa fateema tayi part ɗin umma ummy kuma tayi part ɗin hajjaju.........ayi manage ba yawa

ALHERIN MUTANEN DAURA ƳAR MUTAN MIRAYE CEhaka suka gama ysare-tsaren sukafin merry ta tsinke wayar tareda yin wani ihu ta faɗa kan gado cikin wani irin shauƙi mai kamada anyimata wahayin godan aljanna,
A hankali ta tashi tana wani rangaji ta nufi windown dake ɗakin tareda saka hannunta dayaci uban bliching ta yaye labulen ɗakin gamida kutsa kanta jikin ƙarafan tana shaƙar tatacciyar ni'imtacciyar iskar gari,
Da wani salo tafara kaɗa idanunta tareda yin fito da bakinta cikim salon iya bariki da duniyanci,
ta jima a haka kafin ta saki windown tareda dawowa baya ta zauna akan kujera kafin ta ɗauki kwalbar syrup ɗin data saba kwankwaɗa,
Lallai tau tana cikin farinciki marar misali dalilin nasarar datake ji tana tattare da ita,
A hankali ta ɗaga laɓɓanta tareda furta kalmar,
"Zayyad nawane ni kaɗai bazan taɓa barin wata ta kusanceshiba,"
A haka dai tayita surutanta kafin ta ci gaba da bankar surup ɗinta,
A ɓangaren fareeda ma tana ajiye wayar murmushi tayi tareda furta,
"da sannu zan gama amfani dake merry na mallaki abinda nakeson mallaka kafin na watsadda ke,danna ci alwashin ko gate ɗin gidana bazaki raɓa ba saboda muddin dangin zayyad suka ganki bazasu taɓa amincewa zayyad shi ne ummul aba'isin lalata rayuwata ba"
Itama dai a haka taciga ba da ƴan surutanta lafin ta ɗauko emblope ta fara shirya hotunansu itada zayyad,
_____________________________________________________tinda suka fito khadija take raɓe-raɓen bin bayan hajajju har suka isabakin part ɗin ammi,
jim hajiya nata tafiya kamar ba'a binta yasata tsayawa tare da juyawa,
Aikuwa a baya taga khadija ta toge ta wani manne a jikin bango,
Ganin haka yasa hajjaju cewa,
"aa lafiya naga kin wani maƙale a baya"
Amma kamar ba da khadija take magana ba,
"wllhy kika sake saina komawa ta"
Da sauri khadijan ta matso tareda kama hannun hajiya idanunta taf da hawaye tace,
"dan allah hajiya karki bari ammi ta dakeni wllhy nayi nadamar abinda na aikata"
"Hmm hadiza kenan ashe kinajin tsoro kuma kika aikata"
"haba hajiya ba kinyimin wa'azi ba kuma ainace insha allahu bazan sakeba"
"To shikenan muje ai kindai san mudfin muna tare babu abinda zatayi miki"
Da haka khadija tayi shahadar bin hajajju suka kutsa kai cikim falon ammin,
tana cikin falon kuwa akan dining tana haɗa kayan

Please Login or Register in order to submit comment